Showing posts with label Dandalin Ma'aurata (Couple's Corner). Show all posts
Showing posts with label Dandalin Ma'aurata (Couple's Corner). Show all posts

FAHIMTAR BANBANCI

_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_

      _*💗KUNDIN MA'AURATA // 03💗*_
.
             _*FAHIMTAR BAMBANCI*_
_Idan ya kasance ko yaushe maza ne a gaba, dole sai abin da suka ce a gida shi ne za a yi, abin da suka kawo kuma in ba a karba ba ya zama matsala, sannan mace ba ta isa ta yi aiki ba sai sun yarda, in ma suka ga dama sai ka ga sun han ta, tanan za a iya cewa sun yi kaka-gida sun qwace wa mace haqqinta, masamman in ya kasance alqalin da zai yanke hukuncin bai da basira, domin in muka koma baya za mu ga hatta wajen neman aurennan mace na jira ne sai an furta ana son ta, sannan namijin ya riqa zuwa gidanta zance ba ita ta zabo shi take zuwa zance in sun gama ta kamfato kudi ta bashi ba, hidimomin da ake yi har zuwa ranar daura aure duk ba ruwanta da su._
.
_Macen duk da ta dauki nauyin wannan har zuwa daura auren, kuma ta ci gaba da daukar nauyin gidan ka je ka leqo abin dake faruwa, ka ga wanda yake da haqqin yanke hukunci a gidan, asali matsalolin da muke fama da su a yau, ba sa rasa nasaba da qoqarin da muke yi na tsallake wajibin da yake kammu zuwa karbe na abokin zamammu, in haka ne kuwa to zai yi matuqar wahala a zauna lafiya, kenan mace ta san wajibobinta, shi ma namijin ya san inda ya kamata ya tsaya da inda zai wuce, kar ka yi mamaki wata macen ta ce maka maigidanta yana yawan fushi kuma ba ta san dalili ba, don ba ta sami cikakken lokacin da za ta zauna da shi ba bare ta karance shi, amma wace duk take aiki a wani wuri ta san oganta da kyau da duk abubuwan dake damunsa don tana da cikakken lokacin karantarsa._
.
_Anan ba cewa nake yi kar mace ta je aiki ba, ina qoqarin cewa ne ba ta sami cikakkakken lokacin da za ta karanci gidanta sosai ba, galibin maza abin da ya sa suke ta samun taho mu gama kenan da iyalinsu ba wai tsabar kishin ba ne, ina koyarwa a wata makaranta wani mutum ya janye matarsa, mun ji zafin hakan gaskiya don tana da hazaqa matuqa, ga zuwa makaranta a kan kari, koda wasu ba su zo ba ita za ka riske ta a cikin aji, dalilin wannan sai hukumar makaranta ta yi qoqarin sanin ko an yi masa laifi ne wanda ya sa ya yi yunqurin janye ta, amma sai ya ce ba ya samun kulawar da ta dace ne, kullum tana waje, kafin ya farka barci har ta fita, in ta dawo kuma sai ta mai da hankali kan ayyukan da aka ba ta a makantar, a taqaice dai sai da ta sauko ta yarda ta gyara wasu abubuwa sannan aka daidaita._
.
   _*YADDA MUKE GANIN JUNANMU*_
_Farkon kokawar da mace za ta yi ita ce: Namiji bai son yawan koke-koke, in ma ya tsaya ya saurara din sai ka ga abin da zai yi kawai shi ne ya gama sauraron matsalolin ya fara fadin hanyoyin da za a warware su" ita mace abin da take so shi ne a nuna damuwa da halin da take ciki, kuma a ba da cikakkiyar kulawa, sannan a fahimci cewa lallai matsalar da suke fadinnan fa tabbas matsala ce, to shi gogan duk bai yi haka ba ya fara binciken warware matsala amma ba ta hanyar da ta dace ba, a qarshe ba za a iya warware matsalar ba._
.
_A irin wannan halin za ka riski wasu matan sun fita harkarsa, wanda a qarshe su ma sai su fara wasu dabi'u da gangan don tura masa haushi, wata kuwa takan dage ne sai ta nuna masa abin da take so, wanda yin haka shi yake kawo hayaniya a tsakaninsu koda yaushe, haka za su yi har su gama ba tare da wani ya fahimci dan uwansa ba, a qarshe dai akan fi liqa wa namijin ne laifi, masamman in ya kasance masu kallon abubuwan dake faruwa mata ne, ta bangaren namijin kuwa za ka taras galibin abin da suke fara kokawa a kai shi ne: Ita mace kullum qoqarinta sai ta canza masa rayuwa qarfi da yaji, kamar irin bai san abin da yake yi ba ne ita za ta nuna masa ya-kamata, wato dai tana nuna cewa ita ce a gabansa ta fi shi hankali da tunani, ita za ta ce masa ya yi kaza ko ya bar kaza, ciki har da zumuntarsa._
.
_Duk da cewa shi yana ganin ya gaya mata ba sau daya ba ba sau biyu ba ba ya son irin surutan da take yi, amma abin ya ci tura, ita tana ganin taimaka masa take yi, shi kuma a fahimtarsa kullum qoqarin mallake shi da maishe shi saiwar sala take yi, to da wahala su fahimci junansu, amma gaskiyar maganar tana baya, shi kullum yana waje, tunaninsa yadda za a maida naira daya ta zama biyu, da yadda za a warware duk matsalolin cikin gida, don haka tunaninsa da tsantsar abin dake faruwa a cikin gidan kadan ne, ita kuwa mai dakinsa da take gida ba ta da wani abu sai shi din, dole ta fi shi sanin abin dake faruwa a gidan, da ma alaqarsa da 'yan uwansa, da sauran abubuwan da suka shafi zumunta, da za mu yarda mu karanci juna ba shakka za mu warware matsaloli da daman gaske._
.
     _*YADDA NAMIJI YAKE JIN KANSA*_
_Namiji kamar yadda aka san shi yana da qoqarin hangen nesa, da jajircewa wurin isa ga abin da yake so, wasu mazan ba sa so ma a san abin da suke ciki bare wani ya yi qoqarin amshe musu abin da suke nema, ko kuma su ce sun isa gare shi ne da guminsu, ba tare da wani ya sanya musu hannu ba, to ko a gida ma irin wannan yakan faru tsakanin mutum da iyalinsa, wani yakan yi mata iyaka ya hana ta shiga lamarin 'yan uwansa, ko kasuwancinta ko wasu abubuwan da yake ganin ba su shafe ta ba, in ya zama haka to zai yi wahala ka ga ya zauna da ita ana tattauna wasu abubuwan da yake ganin shi kadai suka shafa banda ita, amma kuma da a ce ita matar za ta nemi shawararsa a irin wadannan matsalalolin za ka ga yana qoqarin nuna mata cewa kaza ya kamata, kaza kuskure ne, ashe ba wai yarda ya yi da cewa irin wadannan maganganun sun shafi mutum ne shi kadai ba, gani yake yi ba zai bari ta shugo masa ba._
.
_A irin wannan yanayin shi yana gani tausayawa ce da qauna za ta sa ya ba ta shawara, amma ba zai yarda ita ta nuna tausayawa da qaunar ta wannan bangaren ba, wasu kenan daga cikinsu ba duka ba, babban abin kula a ciki shi ne, in fa ya ba ta shawara dole ta karba ta yi aiki da ita ba za ta yi gardama ba, don yin hakan rashin girmamawa ne da ba shi matsayin da yake ganin ya kai, to in muka lura da wannan sai mu gane cewa ashe babban dalilin tunkude shawarwarinta ya raina tunaninta ne, ko guje wa yin kafada da kafada da ita kan shugabancin gida, in muka koma farko, mace tana qoqarin fadin matsalolin da ta sami kanta ne a ciki, tana son a saurare ta a ba ta shawara a sanyaya mata rai, shi kuma sai ya yanke ta ya fara ba ta mafita, ko ma ya nuna mata cewa sakacinta ne, a nan dole ta yi fushi._

_*✍🏼Baban Manar Alqasim*_

Share:

GWARZON NAMIJI 02


🌴**GWARZON=NAMIJI**🌴
(02)


1=KAUNA --gwarzon namiji shine kadai ke nunawa mace kauna bawai soyayya ba don akwai gagarumin banbanci tsakanin kauna da soyayya,

Misali wanda yake kaunar ka shine kadai zai zauna dakai a kowanne yanayi kake, 
shine wanda kana shiga wata matsala yana kara kaunarka, kauna itace me saka tausayi wanda duk wani yanayi da mutum ya shiga me kaunar sa bazai taba juya masa baya ba,
 haka zalika shine zaiso 'yan uwar matarsa yaso 'ya'yanta, 

2 BIYAN BUKATUN MACE --wajen biyan bukatun iyalinsa kuwa baya bada uziri yakanyi duk yanda zaiyi don farin cikin iyalinsa, shine wanda baya dogaro da dukiyar matarsa, domin namiji baya zama gwarzo matukar matarsa tana daukar nauyin kanta kona yaransu komai kankanta, 


3 ME GAMSARDA MACE-- gamsar da mace lokacin saduwa yana karawa namiji kwarjini awajen mace akasin haka kuma yana kawo raini wanda wannan ba dabi'ar gwarzon namiji bane domin shi ya kanyi kokarin magance duk wata matsala da zata hanashi gamsar da iyalansa, matsalar daga wurinsa ne ko daga wajen matarsa.
 
Nasara ko faduwa bata samun namiji saida sahalewar mace, mace itace alkiblar namiji komai jarumtar sa itace rauninsa, kuma domin samun daraja a wajenta dole sai namiji ya zama gwarzo wanda yake rikeda akalar zuciyarsa bawai wanda zuciyarsa ke rike akalar saba, 

_Zamu chigaba da yardar Allah..._

Rubutawa✍🏼
Tareda tsarawa=
(Dr. Auwal Muhammad Azare)

Gabatarwa =
(Usaini Amfanima) 

Daga *MIFTAHUL ILMI* WhatsApp 
Ga masu sha'awar shiga wan nan zaure sai su aiko da cikakken Suna ta WhatsApp zuwa ga lambar mu 07036073248 ta WhatsApp.
Share:

GWARZON NAMIJI 01


🌴**GWARZON=NAMIJI**🌴
(01)
Da sunan Allah me rahma me jinkai tsira da aminci su kara tabbata ga manzon tsira manzon rahma (SAW) ina farin cikin gabatarda wannan littafin tareda fatan zai amfanar da al’umma allah yasa albarka acikinsa

Akowanne zamani Allah yana kawo jarumai gwaraza wadanda suke sadaukar da farin cikinsu domin farin cikin iyalansu, daga cikinsu ne ake samun gwarzon namiji wanda duk yanda al'umma takai ga lalacewa tofa wadannan basa kasa a guiwa wajen nuna kyakyawar mu'amala ga iyalansu,

Akwai abu uku da gwarzon namiji yakeda wanda shine ma babba makasudin da yasa kowacce mace ke fatan samunsa, haka zalika sune abu mafi girma da mace keso wajen namiji,


_Zamu chigaba da yardar Allah..._

Rubutawa✍🏼
Tareda tsarawa=
(Dr. Auwal Muhammad Azare)

Gabatarwa =
(Usaini Amfanima) 

Daga *MIFTAHUL ILMI* WhatsApp 
Ga masu sha'awar shiga wan nan zaure sai su aiko da cikakken Suna ta WhatsApp zuwa ga lambar mu 07036073248 ta WhatsApp.

Share:

MATSALOLIN MA'AURATA DA KUMA MAGANIN SU


*_Matsalolin ma'aurata da kuma maganinsu ._* 

Tare dani _*Ibrahim so dole ...*_     

     _Kashi na 01_ 

    *Dacewa da juna ko rashin dacewa da juna.* 

Babbar matsala ta farko da ake samu a Rayuwar Aure shine idan ya kasance ka auri macen da bata dace da kai saboda daya daga cikin wadannan dalilai:
1. Macen da aka aura maka ita ba dan tana sonka ba, sai san anfi qarfinta a gidansu.
2. Macen da ka aura wacce ka tabbata dan abin duniya (kudi, suna, sarauta dss) ta aure ka.
3. Macen da kaima ba dan soyayya ka aure ta ba sai dan sha’awa, kyawunta, dangantakarta dss
4. Macen da kake tunanin ta aure ka ne kawai saboda bata da wani zabin.
5. Macen da bata gama yin hankali ba.
Wadannan da ma sauran dalilai da yawa wanda sukan kawo rashin dacewa tsakanin ma’aura suna kawo babbar matsala a Rayuwar Aure, wanda yawanci sai bayan anyi auren ake gane haka, lokacin da an riga an makara da ayi wani gyara akai. Saboda haka ina kira garemu ‘Yan Mata da Samari mu daure mu yaqi zuciyoyinmu mu auri masoyan da muka tabbatar zabin zuciyoyinmu ne kuma sun dace damu domin samun ingantacciyar Rayuwar Aure! .


Zaku iya bayyana mini ra'ayoyinku a :-

Ibrahim kkhalil bashir.com/Facebook .

Sasha bhai Singh.com/Facebook .

WhatsApp :- 09072875288

Kira :- 07030308254
Share:

AKWAI MATSALA BABBA GA MA'AURATA


AKWAI MATSALA BABBA GA MA'AURATA*.

🌻Matukar MA'AURATA ba sa ganin girman iyayen junansu to akwai matsala a zamantakewar su Kam. 

🌻Ya za kayi da wadanda suka Haifa maka wacce zata iya zama sanadiyyar cikar Addinin ka, suka ki yarda su mallakawa kowa ita sai kai kadai a duk fadin duniyar nan, idan har baka girmama su ka darajasu kuma ka gode musu ba? 

🌻Ya za kiyi da wadanda suka Haifa miki Wanda zai zama Shugaba kuma abin Alfaharinki wajan nuna soyayya da kulawa gareki, sannan yazamto garkuwa ne ga mutunci da darajar ki, idan har baki girmama su ba.? 

KUJI TSARON ALLAH KU KYAUTATAWA SURUKANKU. 
Allah yakyautata.

✍🏻 Idris M Rismawy
Share:

INTERNET MARRIAGES


INTERNET MARRIAGES
.
About two or three years ago on this platform, I said 'Whoever brings her marriage to facebook, will be divorced on YouTube and will observe her Iddah period on instagram'. When we keep advising people to take their marital life off the internet, people think we are preaching an extreme version of Islam or it's because African men are not romantic. We are all aware of the ongoing saga in the last few days about the highly glorified romantic couple on earth. Many of our sisters both the married and teens alike have been following their pages, downloading their videos and pictures for years now, perhaps some women even wish their husbands were like him, perhaps many of our sisters have been crushing on him, yet the same people are now criticizing him, such is life. 
.
If you place your marriage in public, people will have an opinion in your marriage; when it falls, when it rises, when it's jolly, when it's tough, when it enjoys wealth and when it suffers poverty, because you were the one that submitted your marriage for public scrutiny in the first place, so you have to keep explaining to people, without getting paid for it. 
.
I have always expected since all this years that people who are close to them would advise them about Gheerah and secrecy, even though women in their nature loves to be displayed and celebrated, the companions were the best of generations and had the best of marriages, yet they concealed it, but Allah still made their marriages apparent to us because those were the real blessed marriages. Ateekah bint Zaid radiAllahu anhaa was an extremely beautiful female companion, when she was under Umar, he disliked her idea of going to the mosque so that she won't be seen by other men, when she was under Zubair Ibn Awwam too, he tried to discourage her, infact one night, Zubayr hid in a dark spot, when Ateekah was passing on her way to the masjid for Ishaa, Zubayr poked her at the back, out of fear, she ran back home and since then she never went to the masjid again, so one day Zubayr enquired about the reason, and she told him that 'people have become corrupt' . Zubayr smiled and said 'I was the one who touched you', but the message has been passed. This was narrated in At'tabaqat of Ibn Sa'ad. 
.
The companions were shy of people seeing their spouses but the men of today proudly show off their spouses to the world. When you play ball with her, you post it. when you eat with her, you post it. The prophet salalahu alayhi wassalam said: 
Be secretive in your affairs, for it's true that the fortunate person is always envied. (As'Saheehah)  
We know what envy means and it leads to nothing but hatred, jealousy and the evil eye against such people. You all taught that all their followers loved them, but we can all see the hate comments and mockery being bombarded at them now. Either their marriage is a scam or not, it is not for us to condemn them or conclude until they prove themselves. I hope our sisters have learnt a lot from this Shenanigan, if you bring your marriage to the net, everybody will automatically become your e-inlaw. 
.
People now post their pregnancy conception news online, I hope you will also post the miscarriage if it happens ? 
People now report their spouses in online groups that contains thousands of people, how can thousands of people advise you at the same time, which of the thousand advices will you choose?  
May Allah not put us in a situation where we will now have to prove our marriage to the world with documents before people believe or disbelieve in our marriage.
Share:

BA MAZAN BA, BA MATAN BA


BA MAZAN BA, BA MATAN BA:!

Zaku taya ni shaida cewa an wayi gari a yau,akasarin maza idan sun tashi neman wadda zasu aura, babban abin da ya dame su game da macen shi ne "kyau". 

Abin da zai kara baka haushi kuma shine, dĂ  yawan su suna son kyakkyawar ne don su rika yawo da ita a gaban mota suna nunawa jama'a, ana cewa kai wane fa ya hadu,domin ya dauko hadaddiya! Kaga kuwa idan kana neman "sakarci" lamba daya, to shi ne wannan.

Haka zaka ga mace ita kuma, da yawansu
idan an zo maganar aure babban abin da ya dame su "kudi". 

Ba kowa ce ma ta damu da kyakkyawa ba a nan, a'a su dai kudi! To kada in jaku da nisa, wallahi duk namijin da ya auri mace saboda kyau kawai, bata da ilimi da tarbiyya sai kyau kawai, kada ya sa rai zai samu kyakkyawar rayuwar aure. 

Sai fĂ  in Allah Ya taimakeshi ya iya ilimantar da ita da tarbiyyantar da ita, wanda wannan kuma yana da wahala sosai.

Haka duk yarinyar da ta hangi kudi kawai a gun wanda zata aura, bata damu da ilimi ko tarbiyyarsa ba, wallĂ hi duk abin da ya biyo baya na rashin kwanciyar hankali, kada ta tsaya neman dalili, don gashi na gaya mata.

Allah Ya sanya mu daga cikin masu yin aiki da sani, amin

Rubutawa : Habib Jafar Madobi
Share:

TAMBAYAR SAKI BA TARE DA WANI LAIFI BA


TAMBAYAR SAKI BA TARE DA WANI LAIFI BA.


Annabi Muhammad S.A.W yana cewa duk Matar da ta tambayi Mijinta Saki ba tare da Wani Laifi ba, toh haramun ne gareta taji kamshin Aljannah, kuma Allah na fushi da ita Mala'ikun Allah Wanda basu Sabon Allah suna tsine mata. Duba cikin (Tirmizy 1199, Da Abu Dawud 2209).

Wannan Hadisan suna karantar damu cewa Allah ne yace ayi Saki, amma fah duk Ranan da ke Mace kika budi bakin ki kikacema Mijin ki ya sake ki ba tare da wani Hujjah mai karfi Wanda Shari'a ta yadda dashi in kin fada ya Sake ki hakan yayi daidai ba, ko kuma ba tare da wani Laifi ba. Haka kawai sharrin shedan da kuma sharrin kawaye ko kuma sharrin abokan zaman ki suka zuga ki ke kuma kika yadda da shawaran su har kika budi baki kika cema Mijin ki ya sake ki yau ke kin gaji da zama dashi. Toh Manzon Allah yace Allah ya Haramta miki jin Kamshin Aljannah, kuma Allah na Fushi dake ah Wannan lokacin, kuma Mala'iku nata tsine miki. Fushin Allah barai bar kanki ba tsinuwan Mala'iku barai kare kanki ba, har sai kin bama Mijin ki Hakuri akan abinda kika furta kuskure kikayi ya yafe miki kafin nan ki samu sawa ba. Allah ya tsare mu Ameeen.


Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah 
WhatsApp Group.

Muhammad Tukur Jalingo
Domin Shiga Wannan Group Mai Tarin Albarka Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Ta Wannan Number
08164223447.
This Group Is Only For Women.
Share:

SHAWARWARI GA SAMARI MASU BUƘATAR AURE


shawarwari-ga-samari-masu-bukatar-aure

 sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348141712330

Aure babban ni’ima ne a rayuwa. Aure alama ce ta cikar Dan Adam. Aure shi ne silar yaduwar al’umma. Sannan uwa uba Sunnar Ma’aiki (SAW). Ina samari masu neman aure? Ga shawarwari gare ku:

Da farko dai kafin ka fara neman aure, kamata yayi ka sami natsuwa kuma ka nemi yarinyar kirki, ko a cikin ‘yammata nagari ka nisanci guda 3, su ne kamar haka:

(1). Tagari ce amma ba ta sonka
(2). Uwarta ba ta da tarbiyar muslunci ko kadan
(3) Uwar ita ma ta gari ce amma tana nuna maka matsananciyar adawa.

Sannan idan ka tashi neman aure ka sani cewa, ko motar da take karfe wacce za ka rika hawa ta kai ka duk inda ka keso a lokacin da kake so, dole sai ka samo lafiyayyiya sannan ka koyi yadda ake sarrafa ta, da yadda za ka lallaba ta har ta jima maka sosai. Dole ka rika kula da ita wajen kwalliyarta da gyaran injinta lokaci zuwa lokaci gwargwadon yadda wanda yayi ta ya tsara, kana wanke ta kuma kana ba ta irin man da take sha wanda zai gyara injinta. Kuma in ka tashi yin tafiya ba ka kure maleji ba, bare ta makale maka a cikin daji ko ta saka ka yi hatsari da sauransu.
To haka mace take, idan ka aura kai ma dole ka mike da yin wasu hidimomi matukar kana da bukatar ganin lafiyarta da kwanciyar hankalinka, da zama mai dorewa. Mace za ta rika yi maka hidima, amma kai ma maigida na kwarai akwai naka irin hidimar.

Shin ka auro wacce take sonka ?
Share:

BAYANIN AURE DA SAKI DA MAJIƁINTANSU 11


BAYANIN AURE DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL'I SHAYARWA.

Fitowa ta 011 Kuma na Karshe. A Babin Aure.

Ci gaba da Bayani daga inda muka tsaya:KHUL'I, shi khul'i Saki ne wanda babu kome a cikin sa, sai bayan wani auren da Matar za ta yi da yardarta bawai shiryawa akayi ta yi ba, 
     Mace Baiwa da aka 'yanta tana hannun Bawa, wato tana Matarsa, toh sai a ba ta Zabi ko dai ta ci gaba da zama da shi ko kuma ta rabu da shi, Wanda duk ya sayi Matarsa Auren ya warware. Sakin Bawa Saki biyu ne kadai, haka nan iddar Baiwa Haila biyu ce kadai zata yi, kaffarar Bawa kamar ta 'Da' take, wato babu wani bambanci.

Amma ban da haddodi da Saki, a nan akwai bambanci, duk abin da ya shiga cikin Yaro na Nono a cikin shekara biyu (2) na shayarwa, 
   Toh ya tabbatar da Haramci ko da na tsotsa daya yayi, amma abin da ya sha na Nono bayan wucewar shekara biyun bai tabbatar da Haramci ba, sai dai idan ya kusa da cikar sa shekara biyun, kamar da wata daya ko biyu, a wani zancen an ce idan aka yaye yaro kafin cikar sa shekara biyu, ya Saba da cin abinci ya manta da Nono toh duk abinda aka shayar da shi na Nonon Mace a wannan Lokacin ba zai tabbatar da haramci a kansa ba, Haramcin yana tabbata ta hanyar 'dura wa yaro Nono ta Hanci ko ta Kunne, duk Matar da ta shayar da wani yaro Nono, toh 'ya'yan wannan Matar da 'ya'yan Mijinta gaba daya na farko da na baya duk 'yan'uwan su ne, Babu Aure a tsakanin su gaba dayan su, amma ya halatta ga dan'uwansa ya Auri 'ya'yanta.

Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah
WhatsApp Group.

MUHAMMAD TUKUR JALINGO
Domin Shiga Wannan Group Zaki Iya Turo Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Ta WhatsApp Number Namu Kamar Haka
08164223447.
This Group Is Only For Women Please.
Share:

BAYANIN AURE DA SAKI DA MAJIƁINTANSU 10


BAYANIN AURE DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL'I DA SHAYARWA.

Fitowa ta 010

Ci gaba da Bayani daga inda muka tsaya: LI'ANI; li'ani a tsakanin Namiji da Mata Ana yin sa ne a cikin Hukuncin kin karbar Ciki da aka yi da'awar tsarki kafin sa, ko kuma mijinta na ganin ta ita Matar tana yin Zina da wani kuru-kuru ba Jita jita ba, wato ka ganta kamar Mashiyyi(Mashi) a cikin kuratandu. Ko kaman turmi da tabariya,
       An yi sabani a cikin tsayar da hukuncin Li'ani saboda Kazafi, idan Miji da Mata suka rabu ta hanyar Li'ani, to ba za su sake yin Aure ba har Abada. Idan suka zo yin Li'ani sai Mijin ya fara, ya ba da shaida Sau 4 tsakani da Allah cewa lallai ba cikinsa ba ne, wannan Cikin wani ta hanyar Zina, ko ya gan ta tana yin Zinan, sannan ya cika shaida ta biyar da cewa: idan ba haka ba ne, Allah ya tsine masa,

Sannan kuma ita Matar ta zo ta bayar da Shaida 4 itama, ta cika ta biyar da cewa: idan ba haka ba ne, Allaha yayi Fushi a kanta" kamar dai yadda Allah mai tsarki da daukaka ya fada a cikin Al Qur'ani.
    Idan Matar ta ki bayar da shaidar bayan Mijin ya bayar sai a Jefe ta idan katangaggiya ce, mai Aure ce ko kuma a yi mata Bulala Dari idan ita ba katangaggiya ba ce, idan kuma Miji ne yaki bayar da shaidar sai a yi masa Bulala Tamanin haddin Kazafi kenan kuma Shari'a ta ba shi dan, wato idan an yi Mai bulala tamanin saboda yayiwa Matarsa Kazafin yin Zina sai a dauko Dan a ba shi, Mace tana da damar ta fansa kanta daga Mijinta ta hanyar Mayar masa da Sadakinta Wanda mijin ya bata, ko abin da bai kai Sadakin ba ko kuma wanda yafi Sadakin nashi, idan bai kasance cutarta yake yi ba, idan kuwa ya kasance cutarta yake yi toh Khul'i ya tabbata kuma lallai ya Mayar mata da Sadakinta__________

Ku biyo mu a fitowa ta gaba in Allah yakaimu.

Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah
WhatsApp Group.

MUHAMMAD TUKUR JALINGO
Domin Shiga Wannan Group Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Ta Numbern WhatsApp Namu Kamar Haka
08164223447.
This Group Is Only For Women Please.
Share:

BAYANIN AURE DA SAKI DA MAJIƁINTANSU 09


BAYANIN AUREN DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL'I DA SHAYARWA.

Fitowa ta 009

Ci gaba da Bayani daga inda muka tsaya: Ikon Sakin Aure a hannun Bawa yake ba a hannun shugabansa ba, babu ikon Sakin Aure ga yaro karami, Matar da aka mallaka mata lamarinta da wadda aka ba ta zabi, 
      Wato tsakanin zama da rabuwa gaba dayansu suna da damar yanke hukuncin da suka fi so muddin sunada mazaunin haka, amma shi Mijin yana da damar musu hukunci, da kuma wadda aka mallakawa lamarinta ta yanke idan ya wuce Saki daya, kaman misali kai kana tare da Matar ka, zama yayi dadi, kawai sai kace mata yanzu ka bata wannan damar ya zama hukunci gareta, cewa duk lokacin da ta so zata iya yankewa kanta hukuncin Saki, bi ma'ana ta Saki kanta da kanta, toh idan yau tace ta Saki kanta, toh ta Saku indai ta furta da bakinta tace na Saki kaina, toh Sakin ya tabbata, inda Sakin barai tabbata ba, shine ita tace ta Saki kanta Saki uku kai tsaye, toh nan ne zaka iya yanke hukuncin ka, kace Kai daya ne ko Saki biyu, toh muddin ka bama matar ka wannan hukuncin a hannunta, ranan da ta bushi iska tace toh yau na Saki kaina Saki daya, toh saki ya tabbata Saura ma biyu kenan. amma ita wadda ake bai wa zabi ba ta da wani hukuncin da za tayi akan Saki uku, Sannan shi miji ba shi da ta cewa akai, indai ta furta saki daya, duk wanda yayi Rantsuwa akan cewa ba zai Sadu da Matarsa ba Har Sama da wata 4, to ya zama mai ila'i kenan, Saki ba zai tabbata a kansa ba sai bayan Wucewar Ajalin ila'in, Ajalin ila'i shine Wata 4 ga 'Da, wata 2 kuma ga Bawa, har zuwa lokacin da mai hukunci zai tsayar da shi. Duk Wanda yayi wa Matarsa Zihari, toh bai halatta ya Sadu da Matarsa ba, har sai bayan yayi kaffara ta hanyar 'yanta Baiwa Mumina wadda take Kubutacciya ga barin duk wani aibu,

Kuma ta zama babu tarayya a cikinta da wani, kuma babu wani kamshi-kamshin 'yanci a tare da ita, idan bai Sami Baiwa ko bawan da zai 'yanta ba, toh sai yayi Azumin wata 2 a Jere, idan kuma bai sami iko ba, sai ya ciyar da mabukata Sittin, ya bada Mudu biyu ga kowane mabukaci, kuma ba zai Sadu da ita ba da daddare ne ko Rana har sai kaffarar shi ta kare a kansa, idan kuma ya Sadu da ita Kafin ya gama kaffarar sa, sai ya tuba ga Allah mai Girma da Daukaka, idan ya gama da ciyarwa ko Yin Azumi, toh sai ya sake dauko ta daga tushe. Babu laifi a iya 'yanta Bawa ko Baiwa mai Ido daya ko Mara Uba a kaffarar Zihari, ko da yaro karami aka 'yanta ya isa, amma Wanda ya girma kuma ya isa yin Sallah da Azumi shi aka fi so a kaffara na Zihari______

Ku biyo mu a Fitowa ta in Allah yakaimu.

Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah 
WhatsApp Group.

MUHAMMAD TUKUR JALINGO
Domin Shiga Wannan Group Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Ta Number WhatsApp Namu Kamar Haka
08164223447.
This Group Is Only For Women Please.
Share:

BAYANIN AURE DA SAKI DA MAJIƁINTANSU 08


BAYANIN AURE DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL'I DA SHAYARWA.

Fitowa ta 008

Ci gaba da Bayani daga inda muka tsaya,: Ana yin Raddin Mace(wato a ce an fasa auren Mace a dawo da kudin da aka bayar na Sadaki da Sauransu)
     Saboda wasu dalilai kamar haka, da kukurta da ruwan Dumi, wato kukurta mai kunkumbura fuska, da cutar Farji, kamar kashi a Farji da sauransu. Idan Mijin ya riga yayi Khul'i da ita bai sani ba, to sai ya ba ta Sadakinta, Sannan ya je wajen Ubanta ya karba abin sa, haka nan idan dan'uwanta ne ya Aurar da ita, sahihi ma sai ya biya Mijin Sadakinsa da ya bayar, amma idan waliyyi ne Wanda ba ya cikin dangi ya Aurar da ita, toh ba zai biya komai ba babu abinda za'a ba ta sai rubu'in (1/4) na dinare.

Ana jinkirtawa mara lafiyar Zakari har zuwa shekara daya domin ya Nemi Magani, idan ya warke ya iya Saduwa da Matar a shekarar shikenan,
    Idan kuwa bai warke ba sai a Raba Auren a tsakanin su, idan kuma ta yarda ta ce ita tana sonshi a haka zata zauna dashi, shikenan sai a barta, Wanda ya 'Bata kuwa aka daina ganin sa, Ana deba masa ajilin shekara hudu ne daga ranan da ta kai Maganar gaban Hukuma, in an gama bincikensa a duk inda ake tsammanin za'a same shi, ba'a same shi ba, sai a yanke mata wannan hukuncin, sannan sai ta yi idda irin iddar da Mace takeyi Na Tabaka, in ta gama Sannan ta yi Aure idan ta dama, amma ba za'a gaji dukiyarsa ba har sai bayan wani Zamani mai tsawo wanda ake hasashen cewa ba zai Kai wannan Zamanin a Raiye ba, (misali kamar idan a lokacin da ya 'Bata yana da shekara Arba'in da Haihuwa, toh sai a deba masa Kimanin shekara Saba'in ko Tamanin wato za'a deba masa sheKara 30/40. Sannan sai a kaddara ya Mutu a raba gadonsa)

An haramta Neman Mace a cikin idda, amma babu laifi a yi hannunka mai sanda da kyakkyawan zance Wanda Shari'a ya yadda dashi, Wanda ya Auri Budurwa, toh yana da damar ya zauna a wajen ta a Dakinta har na kwana 7 bai je wajen Sauran Matansa ba, kaman Wanda yanada Mata sai ya Kara Aure toh haka zaiyi kafin nan yaje Dakin Uwar Gida da sauran Matan.
       Idan Bazawara ce kuwa sai yayi kwana uku a wajenta, kada ya hada 'yan'uwa biyu ta hanyar mallaka da Saduwa, idan yana so ya Sadu da daya, toh sai ya haramtawa dayan kodai ya Sayar da ita ko ya daura mata Fansa ko 'yar'uwarta da 'yarta ba su halatta gare shi ba. Ita kuma ta haramta ga iyayensa da 'ya'yansa kamar dai yadda suka haramta ta hanyar Aure______

Ku biyo mu a fitowa ta gaba in Allah yakaimu.

Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah
WhatsApp Group.

Muhammad Tukur Jalingo
Domin Shiga Wannan Group Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Ta WhatsApp Number Namu Kamar Haka
08164223447.
This Group Is Only For Women Please.
Share:

BAYANIN AURE DA SAKI DA MAJIƁINTANSU 07


BAYANIN AURE DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL"I DA SHAYARWA.

Fitowa ta 007

Ci gaba da bayani daga inda muka tsaya: SAKI 3 a Kalma daya. Wanda duk ya Saki Matarsa Saki Uku a Kalma 'daya ya Aikata Bidi'a. Amma kuma Sakin ya Tabbata. Wannan matar ta haramta gare shi har sai taje ta auri wani Namijin ba shi ba.
    Amma a Wannan Zamanin an samu wasu malamai suna kafa Hujjojin cewa ai Auren na nan zaa iya maidashi Saki daya, wannan kuskure ne babba, saboda Saki ya tabbata kuma babu wani hanyar da za'a gyara shi idan ba dai ta sake auran wani kuma sahihim Aure bawai Auren bayan wata guda ka sakemin Matana Zan sake auren ta ba. Daman Annabi Muhammad Saww, yana cewa, Nan gaba Malamai zasu Halattawa Jama'a yin Zina karara, kuma gashi a yanzu tana faruwa: bawai malamai zasu ce muku kuje kuyi Zina yin shi Halal bane, a'a ta gefen Yin Saki uku ne zasu halatta muku yin Zina, domin duk Wanda yayiwa Matarsa Saki Uku kuma a Kalma daya matar ta saku, kuma a yanzu babu wani aure a tsakanin su, toh idan an ce an gyara Auren daga Saki Uku ya koma daya don haka kuje ku ci gaba da Zama a matsayin Miji da Mata. Babu shakka indai kun je kun ci gaba da zama a haka Har kana iya Saduwa da Matar. Toh wallahi Zina kawai kuke yi ba Aure ba. Saboda a yanzu ta haramta gareka, dalilin wannan sakin da akayi mata. Ke kuma a matsayin ki na Mace komin son da zakiyiwa Mijin ki a lokacin da Saki Uku ya shiga tsakanin Ku, kada ki yadda ki sa ke ki koma gidan shi, idan bawai kin sake yin wani Auren ba ne, ki ce ke zaki koma gidan Mijin ki na Da saboda an gyara Auren. Ki tabbata idan kin koma gidan shi toh zaman Zina kuke yi ba Aure ba. Dolen ki, ki hakura har lokacin da Allah zai kawo miki Miji kiyi Aure kuma Sahihim Aure ba Shiri ba. Idan kinyi auren ace Mijin ne yace ya gaji da zama dake saboda haka ya Sake ki. Shikenan zaki iya dawowa gidan tsohon Mijin ki Ya Aure ki. Amma idan bahaka ba koda plan kuka shirya wani ya Aureki daga baya sake ki domin ke ki koma gidan Mijin ki, har gobe kuna gidan Jiya ne, Wajibi ne a kanku Ma'aura biyu kuyi koyi da Sunnah wajen Sakin Matan ku, kada kai ka biyema Sharrin shedan da son zuciyar ka, ka Saki matar ka Saki Uku a kalma daya kace kuma kai yanzu kana son ta dawo, ai babu dawo kam

Saki na Sunnah yin shi Halal ne, shi ne a Saki Mace Saki daya kuma a lokacin tana cikin tsarkin ta, Wanda baka Sadu da ita ba.
   Sannan ba zai sake yin wani sakin ba har sai iddarta ya kare, yana da damar yin Bikon wadda take yin haila muddin dai ba ta shiga haila na uku ba, idan Mijin ki ya sake ki bayan sati biyu ko kwana ki kadan ne, ya zo yace shi fah ya mai dake, toh fah kin koma a yanzu ke matarsa ne, ko iyayen ki na son komawan ki ko ba su so, indai yace yau ya mai dake toh kin dawo Matarsa, sai dai idan ya sake cewa ya Sake ki. akwai Wanda wai idan Mijinta ya Sake ta, kuma ya zo yace shi ya mayar da matarsa iyayen Matar ko yan Uwanta basu yadda Matar ta sake komawa gidan wancan, ah haka zasu hanata a karshe kawai sai a daura mata Aure da wani mijin dabam ba tare da ta koma gidan Mijin ta ba. Kusani cewa duk Wanda yayi irin wannan Jahilcin, toh fah ya Daura Aure akan Aure. Kuma Mijinta na farkon nan yana da dama ya kaisu kotu alkili yabashi Matar shi yadawo da ita gidan shi, kuma idan suka kuskura sukayi Jima'i har Matar ta Haihu toh 'Dan wancan ne ko yara nawa suka Haifa yaran wancan ne saboda Matar shi ne, saboda daman shi bai sake Furta wani kalman Saki gareta ba, aka Aurar da ita. Saboda Haka Shari'a ta bashi wadannan Yaran, nashi ne, wajibi ne ga iyaye su san Shari'a kafin nan su yanke hukunci akan Aure. Saboda Ana yin kuskure mai girman gaske, wani ya rabu da Matar sa tun ba yau ba, amma har gobe suna tare a matsayin Ma'aurata kuskure ne kuna aikata Zina ne kawai.

Idan 'ya ce, bata yi haila uku ba, zaka iya maida Matar ka, idan kuma ba ta yin Haila saboda yarinya ce ko kuma shekarunta sun wuce na yin Haila,
    Toh sai ya sake ta duk lokacin da ya ga dama, Saboda haka bara ka Sadu da Matar ka a yau anjima shedan ya shiga tsakanin ku nan take kace ka Saketa ba, wannan kuskure ne. Haka nan mai ciki ita ma a iya Sakin ta a ko wanne lokacin mutum ya so, Ana iya komar da Mai ciki muddin ba ta haihu ba, amma idan kabari har ta Haihu toh sai sabon Aure, ko a yau ka sake ta matukar baka ce mata ka komar da ita da yamma can ba, da safe sai ta haihu, toh ta fita daga Matar ka. Sai ka sake biyan wani Sadaki a daura muku Aure kafin nan ta zama Matar ka, saboda haka shi iddar mai ciki a lokacin da aka saketa, shine ta haihu, da zarar ta haihu ta fita daga iddarta.

Ita kuma yin idda da watanni, Ana iya komar da ita muddin iddar ta bai kare ba, abin nufi da Alkar'u shine tsarki. An hana sakin Mace a cikin haila kaman yadda mukayi bayani a Sama, idan kuma yayi Saki din to sakin ya tabbata,
   Amma za a tilasta masa ya komar da ita muddin iddarta bai kare ba. Wadda bai Sadu da Matarsa ba kuwa, ya iya Sakin ta duk lokacin da ya ga dama. Saki daya yana mayar da ita ko biyu, amma ba'ina, Saki uku kuwa yana haramta sai bayan wani Auren. Wanda yacema matarsa, ke sakakkiya ce, toh yayi Saki daya ne a kansa, har sai in yayi niyyar fiye da haka, yan Uwa Musulmai muyi Hattara Aure ba abin wasa bane______

Ku biyo mu a fitowa ta faba in Allah yakaimu.

Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah
WhatsApp Group.

Muhammad Tukur Jalingo
Domin Shiga Wannan Group Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Ta WhatsApp Namu Mai Dauke Da Wannan Number
08164223447.
This Group Is Only For Women Please.
Share:

BAYANIN AURE DA SAKI DA MAJIƁINTANSU 06


BAYANIN AURE DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL'I DA SHAYARWA

Fitowa ta 006

Ci gaba da Bayani daga inda Muka: KHUL'I; Khu'il Saki ne Wanda babu kome a cikin sa, ko da ba a Ambaci maganar Saki a cikin sa ba, Khul'i Shine, idan Matar mutum ba ta shi wani Abu wanda yayi mata Khul'i da shi, wato ya tube igiyar Aurensa daga wuyanta.
     Wanda yace da Matarsa ke Sakakkiya ce Saki batti, toh Saki uku ne, ko ya sadu da ita ko bai Sadu da ita ba, idan ya furta mata haka, toh Saki uku kenan, sannan idan yace da matarsa, ai ke kubatacciya ce, ko igiyar Aurenki ma tana wuyanki, toh duk wannan Saki uku ne in dai ya Sadu da ita, idan kuwa bai Sadu da ita ba sai a nemi bayaninsa, wato Saki nawa yake nufi? matar da aka saki kafin a Sadu da ita lallai ne a ba ta Rabin Sadakin ta, sai dai idan ta yi masa rangwame ita da kanta, toh shikenan, amma idan batayi mai rangwame ba dolen shi ya bata Rabin Sadakin ta,

Idan bazawara ce, ko kuwa Budurwa ce, toh wannan lamarin yana Hannun babanta, haka nan Ubangida ga kuyangarsa.
    Wanda duk yayi Saki, toh yakamata yayiwa matar 'Yar kyauta ta jin dadi, haka yadace da Shari'a, yakamata ace indai ka Saki matar ka, a kalla in baka bata kyautar kudi ba, ka dauko 10,000/20,000 ka bata kyauta, idan Kai Mai Arziki ne ma yakamata ka bata kyautar gida da abin hawa, da kudi, haka Shari'a yace, idan baka da karfi kuma, ko 5,000/2,000 da abinci ka dauko ka bata ka bata hakuri, amma a wannan Zamanin wai Auren So da kauna akayi, amma idan an zo Rabuwa kaman Wuta da Auduga, za'a rabu kace nace cikin bacin rai kowa najin haushin kowa, wani yana ce ya Saki Matarsa, to da Asar da bakaken magana zai kore ta daga gidan shi, ko tausayi babu, Addini bai yadda da haka ba. Wajibi ne Mazaje a gyara saboda wannan halayya ce irinta Jihilai Wanda basu san Addini ba. amma kuma shi kyautawa Mace idan ka Saketa ba za a tilasta masa ace dole sai yayi ba, amma dai idan kayi hakan yanada kyau kuma yin haka zai kare muku wani dankon do da kauna ce. wadda bai Sadu da ita ba kuwa kuma ya riga ya yanke Sadakin da za a ba ta, toh babu Mutu'a a gareta, 

Haka nan ma Wadda aka yi Khul'i da ita, ita ma babu Mutu'a gareta, idan mutum ya mutu ya bar matar da bai yanka mata Sadaki ba, kuma baiyi khul'i da ita ba, toh tana da gado, amma babu Sadaki gareta, idan kuwa yayi Khul'i da ita, toh za a bata Sadakin ta daidai da matsayinta, idan ta yarda da wani Abu da aka kayyade mata_____

Ku biyo mu a fitowa ta gaba in Allah yakaimu.

Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah
WhatsApp Group.

Muhammad Tukur Jalingo
Domin Shiga Wannan Group Mai Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Zuwa Ga WhatsApp Number Namu
08164223447.
This Group Is Only For Women Please.
Share:

BAYANIN AURE DA SAKI DA MAJIƁINTANSU 05


BAYANIN AURE DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL'I DA SHAYARWA.

Fitowa ta 005

Ci gaba da Bayani daga inda muka tsaya: LI'ANI. Wanda duk yayi Li'ani da Matarsa to ba za ta sake Halatta Gare shi ba har Abada, haka nan Wanda ya Auri Mace a cikin Idda kuma ya riga ya Sadu da ita a cikin Iddar wani, toh ta haramta Gare shi. Idan an Saki Mace ganta kaji kana sonta, toh kada kayi magana da ita cewa kana sonta kai tsaye, saidai zaka iya cewa idan fa tagama kana ciki, sai kabarta haka, kada kullum idan kun hadu a hanya tana Iddanta kayi ta Kawo mata maganar soyayya kana nuna cewa kana sonta, Haramun ne. Saboda haka idan ka fada mata tun farko kai kana ciki idan ta gama. Toh bai halatta ka sake wani zance nuna kana sonta ba sai lokacin da ta gama Iddarra.
    Babu Aure ga Bawa ko kuyanga sai da Izinin shugabansu. Mace ko Bawa ko Wanda ba Musulmi ba, ba sa daura wa Wata Mace aure, bai halatta ba ga mutum ya auri Mace don ya halatta ta ga Wanda ya yi mata Saki uku, kuma ma ko an yi irin wannan Auren bai halatta ta ga Mijinta na farkon nan Wanda yayi Saki uku a kanta.

Auren Mai Harama da Hajji hakan Bai halatta ba, Haka nan bai halatta ba Gare shi ya 'daurawa kansa aure ko ya 'daurawa Wani aure duk bai halatta ba.
   Auren mara lafiya bai halatta ba, Ana warware wannan auren koda an daura shi, idan kuwa ya Sadu da Ita, toh lallai ne a ba ta Sadakinta daga cikin Sulusin Dukiyarsa a fitar da shi da farko, amma ba na cikin gado ba. Idan mara lafiya ya Saki Matarsa, toh Sakin ya tabbata, kuma tana da Gado in dai ya Mutu a cikin wannan halin rashin lafiyar. Wanda ya Saki matarsa Saki uku ba ta sake halatta gareshi ba, ta hanyar mallaka ko Aure har sai ta Auri namijin ba shi ba, kuma zama waje guda ne misali zaka yi tafiya sai ka zo ka shiga moto sai ka ga matar ka a cikin moton itama zatayi tafiya, toh bai halatta kai ka shiga moton kuyi tafiyar tare ba sai dai ka chanja wani moton, wallahi akwai aiki babba gare ku masu yin Saki uku, wani zai saki Matar shi daya daya har uku, amma kullum suna tare zaka ce Ma'aura ne, wannan Haramun ne haramun ne babba, idan ba da wani Uzuri mai karfi Wanda Shari'a ta yadda cewa ya 'kebe da ita ba, haka kawai don yana jin son ta ko tana jin Son shi sai su hadu a wani waje guda domin yin zance, hakan ya sabawa fadin Allah da Manzon Allah______

Ku biyo a Fitowa na gaba In Allah yakaimu. Zamuyi magana akan Saki a kalma guda shin yaya Auren nasu yake akwai gyara ko babu, ku biyo mu

Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah
WhatsApp Group

Muhammad Tukur Jalingo
Domin Shiga Wannan Group Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar ku Ta WhatsApp Mai Wannan Number
08164223447.
This Group Is Only For Women Please.
Share:

BAYANIN AURE DA SAKI DA MAJIƁINTANSU 04


BAYANIN AURE DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL'I DA SHAYARWA.

Fitowa ta 004.

Ci gaba da bayani daga inda muka tsaya: Auren Tafwidi Halal ne, Tafwidi shine Miji da Mata su yi Aure ba tare da yanke Sadaki ba, wato Miji yace nawa ne kudin Sadakin ki? Toh zasu iya yin Auren su ba tare da an Shirya hakan ba. Amma kuma ba zai Sadu da ita ba har sai ya ba ta Sadakinta ta damke su a hannunta kafin nan ya Sadu ita,
     Sannan Idan ya ba ta Sadakin da ya dace da Matsayinta, toh lallai ne ta karba, idan kuwa ya Kara akan Wanda yadace da ita, toh sai a ba ta zabi, idan ta ce ba ta son sa a yanzu, toh sai a Raba su, sai dai idan ya lallashe ta ta yarda ko kuma ya Kara mata wani Sadakin, to lallai ne ta yarda. Idan wani tsakanin Miji da Mata ya yi Ridda, to sai a warware wannan Auren, amma da Saki za'a warware kada ace ma Matar toh maza tafi gidan ku a yanzu babu Aure tsakanin ku, Aa ya saketa.

A wani zance kuma aka ce Auren ya warware kansa ba tare da anyi Saki ba. Kawai abinda yadace idan hakan ta faru toh ayi Saki a bata Takardan Sakin ta.
   Idan kafirai biyu suka Musulunta sai su ci gaba da zama a kan Auren, idan daya daga cikin ne ya Musulunta, toh wannan ya Warware auren su, ba tare da Saki ba, saidai idan itama zata Musulunta. Sannan idan kuma ita Matar ne ita ce ta Musulunta, toh shi ne ya fi cancantar ta, idan ya Musulunta kafin ta gama Idda, idan shi ya Musulunta Alhalin ita Matar Bakitabiya ce, toh sai ya ci gaba da rike ta a matsayin Matarsa, 
       Idan kuwa bamajusiya ce ta musulunta bayan Musuluntarsa ba tare da 'bata lokaci ba, toh sai su ci gaba da Auren su, idan kuwa an sami lokaci mai tsawo ne, toh ta yi masa Nisa kenan saidai ya Nemi wata. Idan Mushriki, ya Musulunta alhalin yanada Mata fiye da 4 tare da shi, toh sai ya zabi guda 4 daga cikin Matan nashi, sauran kuma ya rabu da su_____

Ku biyo mu a Fitowa na Gaba in Allah yakaimu.

Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah
WhatsApp Group.

Muhammad Tukur Jalingo
Domin Shiga Wannan Group Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Ta Number WhatsApp Namu 
08164223447.
This Group Is Only For Women Please.
Share:

BAYANIN AURE DA SAKI DA MAJIƁINTANSU 03


BABAYANIN AURE DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL'I DA SHAYAREA

Fitowa ta 003

 Tsaya ka/ki karanta Watakila zai Amfane ka/ki


Ci gaba da bayani daga inda muka tsaya: Annabi Muhammad SAW, ya haramta duk abin da ya haramta saboda dangantaka ta Jini a wajen yin Aure, a dalilin dangantaka ta Shayarwa kuma ya hana a 'hada Mace da 'Yar uwarta ko 'Yar uwar Ubanta.
       Wanda duk ya Auri Mace, toh da zarar an 'daura Auren kafin ya Sadu da ita Matar ta Haramta ga iyayensa da 'ya'yansa, kuma shi ma iyayen sun Haramta a gare shi, 

Amma 'ya'yanta, ita matar, ba za su Haramta gare shi ba Har sai ya Sadu da Uwar Tukuna, ko kuma ya dadi da ita ta hanyar Aure ko Mallaka.
      Halal ba ya haramta saboda Zina, Allah mai tsarki ya Haramta Saduwa da Kafirai wadanda ba Ahlul-kitabi ba ta hanyar Aure ko Mallaka,
       Amma ya halatta a Sadu da Ahlul'kitabi ta Hanyar Mallaka, kuma ya halatta a Sadu da 'ya'yansu ta hanyar Aure, Saduwa da kuyanginsu kuma bai halatta ba ga 'Da ko bawa ya Sadu da su.

Bai Halatta Mace ta auri bawanta ko Bawan danta ba. Haka nan bai Halatta ga Namiji ya Auri kuyangarsa ko kuyangar dansa ba.
       To amma ya Halatta gare shi ya Auri kuyangar Mahaifin sa da kuma kuyangar Mahaufiyar sa. Ya halatta mutum ya Auri 'Yar Matar Baban sa Wadda ba 'Yar Ubansa ba ce, kaman misali Agolan baban ka idan 'yarta ta maka kuma takai Aure ya halatta ka nemeta ka Aura
        Ya Halatta ga 'Da da ya Auri Mata 4 'ya'ya Musulmai ko Ahlul-kitabi, ya halatta ga 'Da idan bai Sami ikon auren diya Mace ba, kuma yana jin tsoron kada yayi Zina da diyar Mutane, ya fada ga halaka, toh ya Auri kuyanga. Ko kuma ya kama yin Azumi kaman yadda Annabi yace.
       Wajibi ne mutum ya ji Tausayin Matar sa, sannan yayi Adalci a tsakanin Matan sa. Ko kuma matar sa idan daya ne. Ciyarwa da wurin zama duk suna kansa gwargwadon ikonsa, ke kuma sai kiji tsoron Allah kada ki ga Mijin kawar ki yana yiwa kawar ki goma sha biyu, gashi Mijin ki baya miki haka, kice dole dole sai Mijin ki ya miki irin abinda wancan Mijin kawar kin yake mata. Duk abinda ya miki komin kankantar shi ki karba kiyimai godiya ki sa masa Albarka kice Allah yasa gobe ma a Kawo irin shi ko fiye da haka, kada ki yadda ko da na minti guda ce kina nuna fushin ki ga Mijin ki akan baya miki kaman yadda akeyiwa wasu matan. Idan kullum kina sawa Mijin ki albarka kuma kullum kina nuna wadatuwar ki gare shi kina faran ta masa ran shi, Dalilin wannan Addu'ar naki indai kullum haka kike yiwa Mijin ki sai ki ga kullum idan yafi Allah na budamai kofofin Samun shi. Amma ya kawo kince bayayi ba. Ko kuma baya miki Alhalin yana iya kokarin sa. sannan ke baki taba ce masa kin gode da irin kokarin da yake yi ba, saboda baya miki irin yadda Masu kudi sukeyiwa matan su. Toh yaya Allah barai jarrabeku da kullum babu ba? Ke kullum kina cikin wahala Mijin ki ma haka. Yadace Kisan me zakiyi ki samu Rahamar Allah a Ranan Alkiyama, bawai kisan me zakiyi duniya ta samu gareki ba.
          Babu rabon kwana ga kuyangar sa ko Ummawaladarsa, babu ciyarwa ta dole ga Mace har sai ya Sadu da ita ko kuma sai an same shi da ita suna tare kuma ta zama Wanda a lokacin za'a iya kwatantawa da har ya iya Saduwa da ita. Kai kuma wajibi ne Gare ka kaji tsoron Allah ka tausaya matar ka a koda yaushe. Ka tallafa matar ka tamkar ka siyo Tomatir Wanda yagama Nuna kuma yana cikin irin kwandon nan ance ka dauko ka sa shi a Daki, yaya zaka yi? 

Shi ne a lokacin zaka gama iya tallafa wannan kwandon saboda kada tomatir din su faffache. Ko kuma kaman misali ace ka siyo kwaiyi dayawa an sa ma su a leda, nasan barakayi garaje wajen ganin ko da guda daya ne ya fashe ba, haka yadace da Shari'a ka tsaya dakyau wajen tausayama Matar ka, 
      Kada kai a waje ka tsaya kanata furta mata abinda idan ta zo gidan ba shi zata tarar ba, kayita mata kariyan cewa zaka kula da ita sosai kaman yadda kai kake kula kanka, kace Kai bara ka taba so ka ga abinda ya taba lafiyarta ba. Ka zo kullum dukan diyar mutane kake yi babu dare babu rana, Annabi Saw yana cewa akan ya dauki Hannun shi ya bugi Matar shi wallahi gara Hannun ya Rube yanke ya yarda shi. Annabi ya fada haka saboda irin tausayawa Matan shi da yake yi. 
     Ina ga kai kuma kullum kana cikin Zunubi, amma baka tausayawa matar ka ko kadan, rabonta da taji ka yabeta ko kwalliyarta ko Girkinta, watakila tun lokacin da ta taba kawoma wani girkin da tayima tun tana gidan su, wannan ba koyarwan Annabi bane, Mazaje yadace gareku idan ka Nunawa Mace so da kauna tun a waje, kuma kai kullum kana cewa idan ta zo gidan ka zaka mata fiye da wannan zaka nuna so da kauna gareta, toh wajibin ka ne ka cika Alkawarin haka indai kana son ka samu tsira a Ranan Alkiyama.
      Ka tsaya dakyau ka tausayawa Matar ka. Misali Idan kaje Hotel na inda ake siyar da Abinci zaka ga wanda ta dafa Tuwon bawai ita ne zata siyar ba, haka Wanda ta kwance tuwon bawai ita ne zata Siyar ba, hakan Wanda ta share wajen saida Abincin bawai fah ita ne zata zauna ta siyar da abincin ba, haka kuma Wanda tayi wanke wanke nan ma bawai ita ne zata siyar ba, haka kuma Wanda zata kaiwa customer abincin bawai ita ne mai siyarwa, harda ma Mai karban kudin.
       Ka duba duk wannan aikin mutane nawa a hotel sune masuyi kuma suce sun gaji, amma gashi Matar ka ita kadai tana yin Aikin fiye da Mutane nawa harda kayan ka sai ta wanke su ta goge, don Allah dan Uwa Idan baka ji tausayinta ba, kayi mata godiya itama taji dadi tasan lallai tana kokari a gidan ba, wacece zaka je kayiwa godiya ko ka tausayawa toh? Gashi kuma a waje hakan kake fada mata kuma kake nuna mata, matukar ka ganta cikin wani dan karamin damuwa hankalin ka yayita tashi kanata nuna damuwar ka, ita kuma tana jin dadin ta samu Wanda zai bata kulawa, amma meyasa tunda a yanzu ta zama mallakin kane baka yin idan kake Nuna mata a waje_____

Ku biyo mu a Fitowa na in Allah ya kaimu.


Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah 
WhatsApp Group.

Muhammad Tukur Jalingo
Domin Shiga Wannan Group Mai Tarin Albarka Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Jihar Kai tsaye ta WhatsApp Number namu
08164223447.
This Group Is Only For Women Please.
Share:

BAYANIN AURE DA SAKI DA MAJIƁINTANSU 002


BAYANIN AURE DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL'I DA SHAYARWA.

Fitowa ta 002

Ci gaba da bayani daga inda muka tsaya. Allah mai tsarki da daukaka ya Haramta mata Auren dangi bakwai, bakwai kuma na shayarwa da Surukuta. Allah Mai Girma da daukaka yace: 'yan'uwanku da 'yan'uwan iyayen ku Mata da 'yan'uwa iyayen Ku Maza da 'yar 'Dan uwa da 'ya'yan uwa.
        Wadannan su ne wadanda aka Haramta daga 'yan'uwa na dangi haramun ne duk yadda kakai ko kikai ga son su babu Aure tsakanin ku. Wadanda aka haramta ma kuma ta hanyar shayarwa da Surukuta su ne a cikin Fadin Allah Ta'ala cewa: "Da iyayen ku ne wadanda suka shayar da ku, da 'yan'uwanku da kuka sha Nono Tare da su, da Iyayen Matan ku Wanda kuke Auren su, da agololin ku wadanda kuke tare da su a gidajen ku wato 'ya'yan Matan Ku wadanda kuka Sadu da su.

Idan kuwa ba ku riga da kun Sadu da su ba, toh babu laifi an chanja sheka zuwa kan yaran, amma idan kun riga da kun Sadu da iyayen su, toh Haramun ne ku Auri Agololin ku, da Matan 'ya'yan ku na cikin Ku, da kuma Wanda kuka hada 'yan'uwa biyu a lokaci guda sai dai abin da aka riga aka yi ya wuce wato a lokacin Jaliya. Allah Ta'ala yace: "kada ku Auri Matan da Iyayen ku suka Aura"_____

Ki biyo mu a fitowa na gaba in Allah yakaimu.

Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah
WhatsApp Group.

Muhammad Tukur Jalingo
Domin Shiga Wannan Group Mai Tarin Albarka Zaki Iya Turo Mana da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Ta WhatsApp namu Mai Dauke Da Wannan Number
08164223447.
This Group Is Only For Women Please.
Share:

BAYANIN AURE DA SAKI DA MAJIƁINTANSU 001


BAYANIN AURE DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL'I DA SHAYARWA

      Fitowa Na (001)

Yadda Samari Suke Kawo Kayan Lefe Da Sadakin Su ah Wajen Budurwa, Su Rinjayi Budurwa Da Sunan ai Yanzu Kin Zama Matar Shi Domin Ya Kawo Komai, Saboda Haka Sai Budurwa Ta Bada Kanta Saurayi Ya yi Jima'i Da ita. Daga nan kuma idan ba'a yi Sa'a ba sai ya Gudu ya bar su da Sadakin da Kayan, Domin Ya Samu abinda yake so Shi. Toh Zina kuka yi, Domin Baki Zama Matar Ba Tukun, Koda ya kawo wadannan abubuwan Dukka, Ku biyo mu Cikin Rubun Mu. 

Shi Aure Ba Ya 'Daurewa Sai Da Waliyyi Da Sadaki Da Kuma Shaidu Biyu Adalai, idan Shaidun Ba Su Shaida a Wajen 'Daurin Auren Ba, toh ba Zai taba Saduwa Da Matar Ba Har Sai Sun Shaida Tukuna, Sabanin Abinda Yake Faruwa ah Yanzu, Yan Uwana Samari Mu Gyara Rayuwar Mu, Kai Ka Kawo Kayan Lefe a Wajen Yarinya Ka Bada Sadakin Ka komai Ka Gama Yi, an Sa Muku Ranan Sai Shekara Mai Zuwa Ko Kuma Nan Da Wata uku Masu Zuwa, Kayi Ta Rudin Yarinya Cewa ai Yanzu ita Matar Ka Ce, Ka Yita Rinjayarta Har Ta Zo Ta Mika Ma Kanta Ka Sadu Da ita, kai Kana Ganin Kamar Matar ka Ne, toh Ka Tabbata Cewa Kayi Zina Ne Karara ko Shakka Babu, Domin Kafin ta Zama Matar ka Komai ma Kayi Da ita, sai abinda Muka Ambata a Sama ya Auku Kafin nan, nan ma idan da Shaidun za su Ce Su fa Ba su Shaida Ba, toh Bai Halatta Ka Sadu Da Ita Har Sai Shaidun nan Sun bada Shaidar Eh Sun Shaida Kafin nan take Zama Matar Ka, Duk inda ka so ka je kayi Jima'i ita, amma wai don ka Kawo Sadakin ka da Kayan Lefen ka, ba shi ne Yake Nuna Cewa Yanzu Matar Ka Ba Ce, har kai kana iya taba ko ina ah Jikinta waya ce ma haka Sunnah ya koyar, taba jikinta ma da Kake yi Haramun ne mai Girman Gaske, Shi Ma Zina Ne, domin Kala Kala ne, Farji shine yake Gaskatarwa, mu kiyaye Dokokin Allah Yan Uwana Samari.
             Mafi 'karancin Sadaki Shine Rubu'in (1/4) Na Dinare Ya Halatta Ga Uba Mahaifi Ya Aurar Da 'Yarsa Budurwa Ba Tare da Izininta ba, ko da Ba Ta Balaga, idan Ya Ga Dama Kuma Ya iya Neman Shawaranta. Toh Wannan Zamanin Abinda iyaye yakamata Suyi Kenan, idan tanada wanda take so kuma duk Wani Abinda Shari'a Yace an Tabbatar da Cewa wanda Take son yana tare da su, shikenan sai abi Zabin ta, idan kuma Sabanin Shari'a Ne, Ke Kuma Budurwa Sai Kiyi Hakuri ki Bi Umurnin Iyayen Matukar suma sun miki Zabin da Shari'a ya Yarda da shi, sai kiyi Hakuri kiyi abinda suka ce Domin bara su zaba miki abinda zai Cutar da ke ba. Amma kuma idan su ma ba suyi zabin abinda Shari'a yace ba kawai sun bi son Zuciyar su, toh nan kuma sai a sake chanja Zani, Saboda Haka Iyaye Yakamata Kuyi Gaggawan Aurar Da Diyar Ku Daga Lokacin Da Ta Bukaci Yin Auren, Idan Kun Ki Aurar Da Suna Karatu Zasuyi tukuna, toh Zakuyi ta Haifar Zinace Zinace ne kawai a bayan kasa, ke kina ganin kin bama 'Yarki Tarbiya nagari bara tayi Zina ba, ba ki sani ba Rana tsaka ta Hadu Shedanin Saurayi Sha'awa shi kuma daman a kusa yake, duk yadda zata yi dole sai tabi abinda wannan Namijin zai ce mata, Domin kun ce mata ba Yanzu zatayi Aure ba, yar ki nata Zina da Wani Kullum ke baki sani ba, ita kuma ta daina kawo muku labarin zata yi Aure tunda ta samu abinda take so, amma idan kun Aurar da su ah Lokacin su, su je in ma za su yi Makarantan su je wannan ita da Mijinta ku kin fita Hakkinta, 
             idan ba Uba Ne Mahaifi ba zai Aurar Diya ba, misali irin wanda aka bai wa Wasiyya ne ko wakili, to ba zai taba Aurar da Budurwa ba sai ta Balaga kuma ta yi Izini Izininta Shine ta yi shiru ah Lokacin da ake Tambayar ta kina son waye idan tana son shi kenan, Uba ko waninsa ba Za su Aurar da Bazawara ba sai da Yardata, kuma lallai ta yi izinin da magana, kenan ita zata kiyi Magana ne ah maimakon Shiru.
              Ba a Aurar da Mace Sai da izinin Waliyyanta ko kuma wani mai Cikakken Hankali daga cikin 'Yar'uwan ta Kamar wani Mutum daga cikin danginta ko Sarkin Gari. An yi Sabanin Ra'ayi Dangane da Matar da Take Mara Matsayi, Ko ta iya Shugabantar da wani Mutum Ajnabi, Wato Wanda ba Danginsu ba, a kan Aurenta. 
              Da na Ciki Shi ne Ya fi Uba Mahaifi Cancantar Waliccin Mace, Shi Kuma Uba Ya fi 'Dan'uwa, to daga nan Duk Wanda ya fi Kusanci da Ita daga 'Yan'uwa Asibai Shi Ya fi Cancantar Waliccinta, idan 'dan'uwa na Nesa ya Aurar da ita, toh yayi ya Halatta ga wanda aka bai wa Wasiyya Ya yi Wa Yaro Karami Namiji Aure wanda aka ba shi iko, Amma bai Halatta Gare Shi Ba shi iko, amma bai Halatta gare shi ya Aurar da Yarinya Karama ba har sai dai idan Ubanta ya Umurce shi da Aurar da ita. 

Dangin na Nesa Zawul-arham, Wato Marasa Gado, ba sa cikin Waliyyai a Aure, Waliyyan Aure su ne dangi na Kusa, Wato Asibai, Bai Halatta wani ya Nemi Aure a kan Neman wani 'dan'uwan sa Musulmi ba, kuma kada ya taya wani abin Shayarwa a kan Tayinsa ah wajen Budurwa da yake Nema kenan, 
            Wannan yana Haramta ne idan suka Karkata ga junan su suka kusa daidaitawa ah Tsakanin su, toh Haramun ne kai ka ta so kace yanzu kana son ta kuma kaima Auren ta zakayi, Sabanin zamanin mu na Yanzu. Auren Shigari Wato Auren Farji Da Farji, Bai Halatta Ba, Kamar Yadda ah Yanzu Wasu Matan Suke Yi, har Suna Cewa Su Namiji Baya Iya Biya Musu Bukatar Su Ta Wajen Jima'i Kamar Yadda Mace Yar Uwan Su Zata biya Musu Bukatar Su Kuma Su Gamsu, Subhanallahi, Da Auren Mutu'a, Shi Ma Bai Halatta ba, irin Wanda 'yan Shi'a Suke yi, Shi Ne a yi Aure Zuwa dan Wani Lokaci kayyadadde, 
                  Kamar Misalin ace ya Aure ki na Sati Biyu ko Uku ko wata 2,toh wannan kwanan kin na Cika Shikenan kin Rabu dashi, koda bai ce ya Sake ki ba. 

Haka nan Auren Cikin idda Shi ma bai Halatta ba, da Auren da aka daura shi a kan Garari ko a wajen daurin Auren ko dangane da Sadakin duk bai Halatta ba, kamar Misali wai kwana kin can an Daura Aure ah Facebook Kudin Sadaki da Kayan Lefe da Waliyan duk ah Facebook aka gama shi, Yanzu Aure Sunnah Na Allah Da Manzon Allah Shine Yadawo Kamar Wani Wasan Yara, Shiyasa Allah yaketa Jarraban mu da wasu Musifu wanda bamu can da su ba, domin abubuwan yanzu sai kara yawa suke yi, Kiyama Ya Kusato mu sai dogon Buri.
         Haka nan yin Sadiki da wani abu da bai Halatta a sayar da shi a Shari'a ba, to duk Auren da ya baci a Dalilin bacin Sadakinsa sai a Warware shi kafin Miji Ya Sadu Matar idan Kuma Ya Riga ya Sadu da Ita, to Auren ya Tabbata, sai a bayar da Sadakin da ya dace da Matsayin ta, kuma duk Auren da ya baci tun a wajen daura shi kuma aka warware shi bayan ya Sadu da Matar, to lallai ne a bayar da Sadakin da aka kayyade a Tsakanin su sai an bata wannan Sadakin, 
              Kuma Haramci yana afkuwa da irin wannan Auren kamar yadda yake afkuwa da Auren Sahihi, Wato ba zai Aure ta ba har sai bayan tayi wani Auren, toh amma irin wannan Auren baya Halatta wadda aka Saki uku ga wanda ya sake ta, kuma irin wannan ba ya katange Ma'aurata biyu, wato Namiji da Matar Suna nan a Matsayin Saurayi da Budurwa _________

Ku Biyo Mu Ah Fitowa Na Gaba In Allah Yakaimu. 

Daga Zauren Muslim Woman Mata Zallah 
WhatsApp Group. 

MUHAMMAD TUKUR JALINGO 
Domin Shiga Wannan Group Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Kai Tsaye Ta WhatsApp Number Namu Kamar Haka 
08164223447. 
This Group Is Only For Woman Please.
Share:

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...