Skip to main content

Posts

Showing posts with the label Dandalin Ma'aurata (Couple's Corner)

JAN HANKALI GA SABUWAR AMARYA

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Zaman Aure: Jan Hankali Ga Sabuwar Amarya_*
Zaman auren kusan ya fi kowanne zama dadi, haka kuma ya fi komi wuya, domin Hausawa ma suna fadar zo-mu-zauna-zo-mu-saba! Aure idan zamansa ya yi dadi za ka ga ana jin dadi, ana sam barka tsakanin amarya da ango da mahaifan ango da mahaifan amarya. Har ma ana gasa wurin kyautata wa kowane bangare, kowa zai rika kokarin ganin ya kyautata wa wani bangare domin nuna masa jin dadinsa da godiya a kan diyaucin da aka nuna masa. A wannan lokacin za ka sami ango yana wani haske, yana ciccika, yana kasaita tamkar wani basarake, ko wata agwagwa. Yayin da ita kuma amarya za ka ga tana sheki da wani irin kumbura tamkar kazar Turawa. Haka za ka ga tana wani irin annuri da sakin fuska. A wannan lokacin ko iska ta kada sai ta yi masa dariya, to, balantana wani ya yi mata magana ta wasa ko ta zolaya. Shi ango kada ma ka tona bangarensa, domin shi kam wannan zarafin ya koma wani dan karamin tauraro ko kuma ya koma tamkar mota kirar sa…

YADDA ƊAKIN MA'AURATA YA KAMATA YA KASANCE A LOKACIN SADUWA

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Yadda Ya Kamata Dakin Ma'aurta Ya Kasance A Lokacin Saduwa_*
Ya kamata dakin ma'aurata ya kasance kamar haka; A duk yayin da suka nufi saduwa da junansu a cikin dare ne ko rana. Kamar yadda sunnar Manzon Allah ta tsara kamar haka;
1. Dakin ya kasance babu wani mutum a cikin ko da yaro ne.
2. Daki ya kasance a lokacin mai nutsuwa.
3. A samu karancin mutane a kusa da wajen.
4. Dakin ya kasance a kulle yake.
5. Sannan a kashe fitilar cikin dakin.
6. Abin kwanciyar ya kasance ba mai motsi ba.
7. Dakin da abin kwanciyar su kasance mafi dadin kamshi.
8. Ma'aurata su kwanta a tube ba tare da tufafi ba, amma ba laifi ba ne in sun kwanta da kaya a jikinsu.
9. Su kwanta a cikin mayafi guda daya, amma ba laifi ba ne in sun kwanta a mayafi daban-daban.
10. Su ambaci sunan Allah kafin su fara saduwa.
11. Daki ya kasance ba hayaniya.
Wabillahi Taufiq. Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shig…

ILLAR RASHIN TSAFTA A GIDAJEN MATAN AURE

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Illar Rashin Tsafta A Gidajen Matan Aure_*
Akwai abubuwan da yakamata mu lura da su, mu inganta su a wurin gina tsaftarmu. Misali wanka, wanki, wanke kai, goge dattin kunnuwa, wanke baki, wanke hannu, yankan farce, da sauransu.
A nan ina so mata su gane cewa muna da daraja da kima dole sai mun tsaya mun lura da abubuwa a cikin zamantakewar aure sannan gidanmu zai gyaru, mu kwato wa kawunanmu ‘yancinmu a hannunmu domin addinin musulunci ya fi kowane addini tausaya wa mace a tarihin dan adam.
Amma abin da ke ban mamaki sai ka shiga gidan mace ka ganshi kaca-kaca, babu sha’awa, kazanta ta tare tun daga tsakar gidanta da dakunanta da ban-daki har ita kanta. Ga tulin kayan wanki da wanke- wanke kuda suna bi ko kayan wanki a jibge, yara kuwa sai ka gan su dukun-dukun, hanci dagaje- dagaje da majina. Idan ma girki take yi sai ka gan shi a bude ko an bude murfi an bar shi a kasa ana face majina, wannan yana daga cikin abin da maza suka tsana. Kuma koma wane ne ransa ba…

MACEN DA TA KE ƘAUNAR MIJINTA

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Macen Da Take Kaunar Mijinta_*
Ita ce Wanda a har kullum burinta bai wuce ya zata sa mijinta farin ciki.
Ita ce wanda koyan nau'ikan girki don natsuwan mijinta.
Itace mai kwalliya don ta kawar ma mijinta hankali daga matan banza.
Tana sadaukar da lokacinta don faranta ma mijinta rai.
Tana kawar da duk wani abu wanda tasan mijin baya so.
Itace wanda takeyin komai don gamsar da mijinta a shimfida.
Wabillahi Taufiq.
Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*

Me Ake Nufi Da Soyayyar Gaskiya?

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Me Ake Nufi Da Soyayyar Gaskiya?_* Kowane mai rai na bukatar Soyayyar gaskiya, sai dai mutane kadan ne ke sa’ar gamuwa da masoyan gaskiya a cikin dan kankanin lokaci.
Ya zaka bayyana soyayyar gaskiya?.. Soyayar gaskiya aba ce da tafi komi dadi da kuma faranta ma dan adam rai a lokacin da mutum ke cikin soyayya.
Dan kawai ka hadu da wani ko wata waddan kake kauna ba shine soyayayyar gaskiya ba, ko da wanda kake so ma najin irin yadda kake ji ba lallai son gaskiya ne ba.
Amma bincike ya nuna hakan shine mataki na farkon soyayyar gaskiya.
A cikin mataki na farko akwai yadda, domin kuwa babu soyayyar da zata kai labari idan babu yadda a tsakanin masoyan.
Idan yadda ta shiga tsakanin masoya, to lallai babu sauran wata damuwa ko tunani na daban akan abokin soyayya.
Amma idan yaddar bata zo daidai ba, to ana iya samun matsala ko kuma rabuwa.
Soyayyar gaskiya abuta ce tsakanin saurayi da budurwa ko mace da namiji mai karfin gaske, saboda idan kana matukar so da kaunar masoyi…

HIPS UP

💃🏻💃🏻 *HAMSHAKIYAR MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI*💃🏻💃🏻💃🏻

_HIPS UP_
_Hallau dai mun sake zo maku da ingantaccen maganin hips shima dai hadine na gargajiya wanda basuda side effect acikin shi yana taso da hips sosai acikin sati daya zakiyi mamakin yadda hips dinki zai ciko_  _Jaraba 'yar uwa don samun damar shiga jerin mata masu aji_💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Zafafan kayan mata masu kyau da inganci sayen daya ko sari daga yar mutan sokoto 09035027743

HANYAR SAMUN YARO NAGARI 1

👳🏻‍♀️ *HANYAR SAMUN YARO NA GARI 01* 🧕🏻
Gabatarwa: Bismillahi Rahmanirraheem. Yabo da jinjina sun tabbata ga Allah S.W.T, Allah ya yi salati da Taslimi ga Annabi S.A.W da iyalansa da sahabbansa sa wanda suka bisu da kyautatawa. Bayan haka: Wannan littafi ne da muke gabatar dashi mai taken HANYAR SAMUN YARO NA GARI wanda shi ne burin duk wani uba a dorin qasa. Kuma shi ne wanda Allah ya fadama mala'iku cewa zai sanya shi a matsayin khalifah a doron kasa. Muna fatan Allah ya mana jagora yasa ya amfanemu daku baki daya.
📜 *ABUBUWAN DAYA KUSA*📜
⏹️ Gabatarwa
1. Tarbiyyar kafin ayi aure ▪️Zamantowar uwa ko uba na kirki ▪️Zaben uwa ko uba ba qwarai ▪️Bin dokokin shari'ah wajen neman aure ▪️Daura aure na shari'ah 2. Tarbiyar bayan daura aure ▪️Adduah ga ango da amarya ▪️Tausasama amarya daren farko ▪️Yima amarya adduah ▪️Sallah da amarya ▪️Adduah lokacin saduwa ▪️Walima ta Shariah ▪️Adduar samun yaro na gari
3. Tarbiyyar bayan daukan cikinsa zuwa lokacin haihuwa ▪️Godiya gameda samun ciki ▪️Ya…