Skip to main content

Posts

Showing posts with the label Darussan Hausa (Hausa Lessons)

BINCIKEN TARIHIN HAUSA 02

BINCIKEN TARIHIN HAUSA: LABARUN DA BISHIYOYIN KUKA KE SANAR MANA.SADIQ TUKUR GWARZO, RN. 08060869978 Kashi na biyu. 3. Kuka abinci da/ko Magani Ba a iya kasar hausa ba, akwai kabilun duniya mabanbanta da suke mu'amala da bishiyar kuka. Don haka sanin alakar dake tsakanin wasu kabilun da bishiyar kuka zai amfane mu wajen sanin alakar kakannin hausawa da kukoki. Misali, a kabilar Nkwici ta Kasar Malawi, ana kiran bishiyar Kuka da suna 'Bishiyar Rayuwa'. Saboda a cewar su, bishiyar na baiwa mazauna kauyuka mafaka a zamanin yaki yayin da mahara suka nufosu. Sannan ana amfani da ganyenta da kuma 'ya'yanta don yin abinci gami da magani. Har ila yau, akwai canfe-canfe da dama a tattare da ita. A kasar Madagaskar kuwa, an samu wata gagarumar Bishiyar kuka mai kimanin shekaru dubu uku, tsayinta zai tasamma kafa ɗari, faɗin ta kuwa an kiyasta sai mutane akalla goma sun kama hannuwan juna zasu iya rutsata. Mutanen yankin suna matukar girmama wannan kukar, har suna kiranta da 'Bi…

BINCIKEN TARIHIN HAUSA 01

BINCIKEN TARIHIN HAUSA: LABARUN DA BISHIYOYIN KUKA KE SANAR MANA.SADIQ TUKUR GWARZO, RN. 08060869978
Kashi na ɗaya.
Kasancewar akwai ilimi acikin kowanne abu, ya kamaci muyi duba ga bishiyoyin kuka don fahimtar iliman da suke sanar mana anan kasar Hausa. Domin kuwa kamar yadda masana kimiyyar duwatsu ke cewa akwai tarihi a kowanne dutse, haka ma akwai labari ga mafi yawan rukunonin bishiyoyin kuka anan kasar hausa. To amma, wanne labari bishiyoyin suke sanar mana? 1. Ana Gane wanzuwar birnin Hausawa daga kukoki. Hakika, kasancewar tun da jimawa, babu shahararrun gine-gine masu kafuwa cikin kasa a kasar hausa, muna iya cewa babu wani ma'auni dake tabbatar mana da wanzuwar tsohuwar rayuwa a kasar hausa sama da rukunin kukoki. Ko tantama babu, duk inda aka samu kukoki sun jeru reras, ko sunyi da ira, ko wani abu mai kama da haka, to akwai labarin cewa gari ya taɓa wanzuwa a wannan wuri. 2. Ana sanin Tsufan gari gami da tumbatsar sa daga kukoki. Akan haka, munyi duba ga tarihin wasu tsoffin gar…

DIDDIGIN ISAR HAUSAWA GWANJA DA KURMI

Diddigin Isar Hausawa Gwanja da Kurmi
Daga Sadiq Tukur Gwarzo 08060869978
Da Bukar Mada 08021218337
Cinikayyar Goro wata abar tunawa ce a tarihin k'asar Hausa. Domin kuwa abisa al'ada, kowacce al'umma tana ware wani abu muhimmi mai daraja domin yin musanyar cinikayya a matsayin Haja tun kafin a samar da kudade.
Tarihi ya nuna cewa ba'a bar kasar hausa a baya ba a wannan fage, domin kuwa al'ummatan zamanin daya gabace mu sun yi riko da Bayi, Gishiri, Wuri, Azurfa, Zinare da Goro duk a bisa irin wancan matsayi na musaya a fannin cinikayya da sigar mallakar abubuwa.
Watakila, wannan ne yasa hausawa na wancan lokacin suka bazama neman wadancan abubuwa masu daraja. Tarihi ya nuna an samu garuruwa da dama da suka kafu saboda zuwan mutane hak'ar zinare a yankunan, haka kuma labarin yadda hausawa ke tafiya fataucin bayi, gishiri duk sananne ne izuwa duk inda suka san zasu samu kayayyakin. A irin haka muke kyautata tsammanin bahaushe ya fara riskar yankunan da ake noman goro d…

BINCIKE A LUPUR

BINCIKE A LUPUR, TSOFFIN TSAUNIKAN DA MAGUZAWA SUKA TAƁA KAFA DAULA.
DAGA
SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
08060869978
Lupur, wani ɗan ƙauye ne dake daura da sabon garin Rano, koda yake ana iya cewa manyan tsaunikan nan masu tarihi ne suka raba ƙauyen da garin na Rano, watau duwatsun Ƙurƙubu, Ƙurgum, Damusu, da Mairamu.
Manyan ababen ƙayatarwa a ƙauyen sune duwatsun Jidal da kuma Tsiriri dake can ƙurya dashi, dukkaninsu kuwa suna da tsohon tarihi.
Don haka sai na yanke shawarar ziyartar gani da ido zuwa garin.
Kafin zuwana, na saurari labaru kala-kala game da waɗancan tsaunika. Daga ciki akwai masu cewa Fadar sarakunan farko na maguzawa na cikin tsaunikan Lupur ne, akwai koguna masu duhu da kuma ababen tsoratarwa aciki.
Ibrahim Haladu, shine matashin daya amince yayi mini rakiya zuwa cikin surƙuƙin waɗannan duwatsu. Haka kuma mahaifinsa Mallam Haladu tsoho ne, masanin tarihin wannan yanki, wanda har Maimartaba Sarkin Rano kan aiko mutane gareshi domin jin abinda ya sani game da tarihin tsohuw…

TUNAWA DA YAƘIN SANTOLO

TUNAWA DA YAKIN SANTOLO
(YAKI DON TABBATAR DA MUSULUNCI A KASAR HAUSA)
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
08060869978
Hakika, idan har Tarihin kasar hausa bazai cika ba sai an kalli tarihin kano, to haka ma tarihin kano da zuwan musulunci kano bazai taɓa kammaluwa ba har sai an sanya wani yanki na Santolo.
Santolo tsohuwar daular hausawa ce, tsohuwar masarauta ce wadda salsalar ta take tukewa da salsalar asalin hausawa.
A cikin zantuka masu yawa na maruwaitan tarihin kano, an gamsu cewar wani mai suna 'Dala' shine wanda ya soma zama akan dutsen da ayau ake kira dutsen Dala, a wajajen shekara ta 700 miladiyya, tun a wancan lokacin kuma wasu na ganin akwai mutane dake rayuwa a gefa da kuma kan wani dutse mai suna 'santolo', wanda kuma da alama, sunan ya samo asali ne daga mutumin daya soma rayuwa a saman dutsen.
Zuwa yanzu, babu takamaimen tarihin asalin kafuwar santolo, sannan kuma yana da wuya a iya lissafa tsawon zamanin da mutane suka soma rayuwa akan dutsen santolo, to a…

MAFIYA ALKHAIRIN MUTANE

MAFIYA ALKHAIRIN MUTANE.


Annabi SAW yana bayyana mana siffofi da Wadansu Halaye na Mutanan da suke zababbu awajan Allah.

Ga kadan daga cikinsu:

*1-Wanda yafiku kyawawan Halaye*

Daga Ibn Abas R.A Manzon Allah SAWyana cewa:
*(Zababbunku sune wadanda suke da kyawawan Halaye.......)* @Albany Ya Ingantashi

*2-Wanda yafi kowa kyawun biyan bashi*

Daga. Abi Hurairata R.A :Annabi SAW yana cewa:
*(Zababbe acikin ku shine wanda yafi kyawun biyan bashi)*
@ASSaheeha

*3-Wanda yafi alkhairi awajan iyalinsa*

Annabi SAW yana cewa:
*(Zababbe acikinku shine wanda yake abin alfahari awajan iyalinsa)*
@Albany ya Ingantashi.

*4-Wanda ya iya karatun alqurani kuma yake koyar dashi*

Manzon Allah SAW
yana cewa:
*(Zababbunku shine wanda ya iya karatun alqur'ani kuma yake koyar dashi)*
@Albany ya Ingantashi

*5-Wanda Musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa*

Annabi SAW Yana cewa:
*(Mafi alkhairin acikin musulmi shine wanda musulmi suka kubuta daga sharrin Harshensa da Hannayansa)*
@Saheehul Jami'i…

ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA 03

ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA
(KASHI NA UKU)
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO
Bunkasar Harshen Hausa
Abisa fahimta irin tamu, yaren hausa gamayya ce ta haifar dashi. Littafin Babil mai tsarki ya faɗi cewar shekaru da dama da suka gabata (misalin shekaru dubu takwas da suka gabata), mutanen duniya da harshe ɗaya kurum suke amfani, sai daga baya yaruka suka rinka samuwa ta yadda zuwa yanzu akwai kimanin yaruka dubu bakwai a faɗin duniyar nan. Ina tsammanin Littafin Alqur'ani maigirma bai yi magana irin wannan ba, amma duk da haka maganar data fito daga Babil na iya tabbatuwa a kimiyance tunda dai munsan cewa Allah Ubangiji ne ya saukar da littattafan duka guda biyu.
Samuwar harshen hausa na iya zamowa daga haɗakar kalmomi na waɗansu yaruka mabanbanta. Ma'ana, tana iya kasancewa karo-karon kalmomi daga yaruka daban-daban ne ya haɗu ya samar da yaren hausa kachokan ɗinsa, hakan kuwa na iya faruwa ne idan muka kalli hausawan su kansu zamuga cewa kabilu ne da dama suka …

ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA 02

ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA
(kashi na biyu)
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Faruwar wannan lamari yasa Gwamna Lugga ya tura sako ga kasarsu Ingila a rohoton da yake turawa gami da labarta musu abinda ya sami Kyaftin Moloney. Shine har yake faɗa musu cewa ba lalle ne ace tafintan Kyaftin Moloney da gayya yayi wannan kasassaɓar ba, amma watakila hakan ta faru ne saboda rashin samun wata fahimta da Kyaftin Moleney yayi dangane da yaren hausa tayadda har ya kasa tantance tsakanin abinda yake karantawa da abinda tafintan sa yake faɗa.
Don haka a karshe Lugga ya bada shawarar cewa a ganinsa mafitar kare aukuwar irin wannan hadari anan gaba shine turawan mulki 'yan uwansa su koyi hausa.
(D.J.M Muffet, concerning Brave Captain, London 1964.)
Ai kuwa hakan akayi, domin an samu cewa Ingila ta bada odar kowanne jami'inta ya fara koyon harshen hausa, an buga sanarwar fara yiwa jami'an mulkin mallaka jarabawar auna fahimtar harshen hausa a jaridar Northern Gazette ta ra…

ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA 01

ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA
(kashi na ɗaya)
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO
Kafin karni na sha tara, kuma kafin zuwan turawan mulkin mallaka kasar hausa, ɗaukacin masana sun haɗu akan cewa babu rubutun AaBaCaDa a kasar hausa, rubutun hausa da larabci (Ajami) kaɗai aka sani.
Shi kansa rubutun na Ajami, dattijo Marigayi Alh Muhammad Koki ya faɗa mana cewa yaji kaka-da-kakanni cewa asalin hausa babu rubutu har sai lokacin da larabawa suka kawo musulunci. A lokacin ne aka rinka amfani da rubutun larabci wajen sadarwa a rubuce. Har ma yace a wancan zamanin, idan kanaso ka tura wani sako ga wani ɗan uwanka dake rayuwa acan nesa dakai, sai dai kaje ka samu malami daya kware a fannin larabci, ka faɗi masa sakon shikuma yana rubutawa da alkalami a takarda, sannan ka biya lada, kai kuma ka naɗe sakon ka turawa ɗanuwan naka ta hanyar fatake. Shima ɗan uwan idan ya samu sakon, haka zaije ga malami wanda ya iya karatun larabci ya karanta masa sakon gami da fassarawa.
Sai Alhaji Muh…

NAZARIN JINSIN MACE DA NAMIJI A KALMOMIN HAUSA

NAZARIN JINSIN MACE DA NAMIJI A KALMOMIN HAUSA
rai_______namiji
mutuwa____mace
arziqi_____namiji
tsiya _____mace
hankali____namiji
wauta ____mace
taimako____namiji
mugunta____mace
qarfi ______namiji
ragwanta____mace
qoqari______namiji
kasala______mace
nema_______namiji
sata _______mace
tausayi______namiji
qeta ______mace
ruwa _____namiji
wuta ______mace
kuđi_______namiji
fatara_____mace
qoshi_______namiji
yunwa______mace
dađi _______namiji
wahala______mace
matsayi_____namiji
qasqanta____mace
karatu______namiji
waqa _______mace
aure_______namiji
zina _______mace
zumunce____namiji
gaba _______mace
kirki________namiji
masifa______mace
aiki _______namiji
caca _______mace
lemo________namiji
giya________mace
wasa_______namiji
rigima______mace
alqawari____namiji
yaudara____mace
Mata kuyi hakuri haka abin yake tun fil'azal 

ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA (KASHI NA UKU) DAGA SADIQ TUKUR GWARZO

ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA
(KASHI NA UKU)
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO
Bunkasar Harshen Hausa
Abisa fahimta irin tamu, yaren hausa gamayya ce ta haifar dashi. Littafin Babil mai tsarki ya faɗi cewar shekaru da dama da suka gabata (misalin shekaru dubu takwas da suka gabata), mutanen duniya da harshe ɗaya kurum suke amfani, sai daga baya yaruka suka rinka samuwa ta yadda zuwa yanzu akwai kimanin yaruka dubu bakwai a faɗin duniyar nan. Ina tsammanin Littafin Alqur'ani maigirma bai yi magana irin wannan ba, amma duk da haka maganar data fito daga Babil na iya tabbatuwa a kimiyance tunda dai munsan cewa Allah Ubangiji ne ya saukar da littattafan duka guda biyu.
Samuwar harshen hausa na iya zamowa daga haɗakar kalmomi na waɗansu yaruka mabanbanta. Ma'ana, tana iya kasancewa karo-karon kalmomi daga yaruka daban-daban ne ya haɗu ya samar da yaren hausa kachokan ɗinsa, hakan kuwa na iya faruwa ne idan muka kalli hausawan su kansu zamuga cewa kabilu ne da dama suka cakuɗu…

ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA (kashi na biyu) Daga Sadiq Tukur Gwarzo

ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA
(kashi na biyu)
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Faruwar wannan lamari yasa Gwamna Lugga ya tura sako ga kasarsu Ingila a rohoton da yake turawa gami da labarta musu abinda ya sami Kyaftin Moloney. Shine har yake faɗa musu cewa ba lalle ne ace tafintan Kyaftin Moloney da gayya yayi wannan kasassaɓar ba, amma watakila hakan ta faru ne saboda rashin samun wata fahimta da Kyaftin Moleney yayi dangane da yaren hausa tayadda har ya kasa tantance tsakanin abinda yake karantawa da abinda tafintan sa yake faɗa.
Don haka a karshe Lugga ya bada shawarar cewa a ganinsa mafitar kare aukuwar irin wannan hadari anan gaba shine turawan mulki 'yan uwansa su koyi hausa.
(D.J.M Muffet, concerning Brave Captain, London 1964.)
Ai kuwa hakan akayi, domin an samu cewa Ingila ta bada odar kowanne jami'inta ya fara koyon harshen hausa, an buga sanarwar fara yiwa jami'an mulkin mallaka jarabawar auna fahimtar harshen hausa a jaridar Northern Gazette ta ranar 30 …

ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA (kashi na ɗaya) DAGA SADIQ TUKUR GWARZO

ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA
(kashi na ɗaya)
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO
Kafin karni na sha tara, kuma kafin zuwan turawan mulkin mallaka kasar hausa, ɗaukacin masana sun haɗu akan cewa babu rubutun AaBaCaDa a kasar hausa, rubutun hausa da larabci (Ajami) kaɗai aka sani.
Shi kansa rubutun na Ajami, dattijo Marigayi Alh Muhammad Koki ya faɗa mana cewa yaji kaka-da-kakanni cewa asalin hausa babu rubutu har sai lokacin da larabawa suka kawo musulunci. A lokacin ne aka rinka amfani da rubutun larabci wajen sadarwa a rubuce. Har ma yace a wancan zamanin, idan kanaso ka tura wani sako ga wani ɗan uwanka dake rayuwa acan nesa dakai, sai dai kaje ka samu malami daya kware a fannin larabci, ka faɗi masa sakon shikuma yana rubutawa da alkalami a takarda, sannan ka biya lada, kai kuma ka naɗe sakon ka turawa ɗanuwan naka ta hanyar fatake. Shima ɗan uwan idan ya samu sakon, haka zaije ga malami wanda ya iya karatun larabci ya karanta masa sakon gami da fassarawa.
Sai Alhaji Muhammad …

FASSARAR FINA-FINAN INDIA ZUWA HARSHEN HAUSA: LALE MARHABAN DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA

FASSARAR FINA-FINAN INDIYA ZUWA HARSHEN HAUSA LALE MAHARBAN DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA.
Daga Abu Hidaya.
Babu shakka samuwar wadannan fina-finai cikin harshen hausa ba karamin ciyar da harshen hausa gaba zai yi ba.
Duba da yadda masu fassarar suke kokari wajen fassara ko wacce kalma da hausartacciyar Hausa.
Idan ana maganar Hausantaccen Fim din Hausa kamfanin "Algaita "Record" ko "Speedy Ventures" sune suka yi fice a wannan fage.
Kuma tabbas za'a matukar amfana da wannan sauyi domin cigaba ne a fagen bunkasar harshe.
Na dade ina kallon fina-finan Hausa wadanda masu ikirarin halattun kabilar Hausa ko abokan hausawa suka shirya, amma har yau in banda haushi da takaici babu abinda nake karuwa dashi,
domin mafi yawa daga cikin Fina-finansu babu hikima balle azancin magana.
Abin mamaki shine nakan iya zama da yara na kalli fassararren Fim din Hausa mu yi raha mu yi nishadi ba tare da jin kunya ko danasani ba.
Amma fim din da aka shirya cikin harshena yana min wa…

KALMOMIN DA MU HAUSAWA DA KUMA INDIYA DUK MUKA ARO DAGA LARABAWA

KALMOMI DA MU HAUSAWA DA KUMA INDIYAWA DUK MUKA ARO DAGA LARABAWA :
tare dani AbbaIndiaDala.
Hindi :IMAAN
Hausa :IMANI
Arabic :AL-IMAAN.
Hindi:HUKUMAT
Hausa :HUKUMA
Arabic :HUKUMAT
Hindi:AMANAT
Hausa:AMANA
arabic :AL-AMANAT
Hindi:DUNYA
Hausa:DANIYA
arabic:AL-DUNYA
Hindi:saboon
Hausa :sabulu
Arabic : Al-sabun
Hindi : zaalim
Hausa:Azzalumi
Arabic : Al-zalim
Hindi : mulk
Hausa :mulki
Arabic : Al-mulk
Hindi: chay
Hausa :shayi
Arabic : shayi
Akwai Su da yawa wadanda mukayi tarayya wajen aro su akwai kuma wadanda muka samu Banbanci su suka aro nasu daban daga can muma muka aro namu daban ..
Misalin wanda Hindi suka aro daga LARABAWA:-
Arabic----->Hindi :Qabool=KARBA
Arabic ---->Hindi:Ijazaat = IZINI..
Arabic ---->Hindi=waqt=LOKACI
Arabic --->Hindi:qarib=KUSA
Arabic ---->Hindi: izzat =MUTUMCI
arabic ----->Hindi:qaatil= MAKASHI
Arabic --->hindi :Imtihaan =JARRABAWA.
Dasauransu..

HARAMTATTUN KARIN MAGANAR DA HAUSAWA KE YI

HARAMTATTUN KARIN MAGANAR DA
HAUSAWA KEYI.
1- Dodo daya akewa tsafi.
2- Oh Allah nawa Annabi na uwata.
3- Taya Allah kiwo yafi Allah nanan.
4- Duk dadinka da Allah saiya
kasheka.
5- Kare da kudinsa sai yasha
lahaula.
6- Dasanin Allah malam yasha giya.
7- Allah ubana inji shegiya
8- Gafara Allah bamaguje ya taka
masallaci
9- Gwari kinsan Allah, tace ga- gida-
ga-gida .
10- Hmm..shakiyyi Allah na
tsoronka.
11- Katankatana mutuwar almuru.
12- Allah nadawo inji matar dan
cirani.
13- Banga alamaba ance da kuturu
Allah ya sawake.
14- Allah gyara makaho yace a
yaushe.
Don Allah a rinqa kiyayewa wajen
sanin abinda za'a fada a wajen karin
magana. Mu gujewa fadawa cikin
fushin Ubangiji ba tare da sani ba.
Allah Ya kiyashemu kuma Ya
tsaremuna Imaninmu.
FORWARDED AS RECEIVED, IN
AKWAI GYARA DON ALLAH KA/KIYI,Daga Wani Dan Uwanku a MUSULUNCI.

TARIHIN ASALIN HAUSA DA HAUSAWA

Taskar Hikayoyi
Tarihin Asalin Hausa da Hausawa.
Gudummuwa daga Maigirma farfesa Ibrahim Malumfashi.
GA TAWA GUDUNMUWAR!
Batun gaskiya shi ne, ba Bayajidda ko Abii Yazid ne ya
zo kasar Daura ba! Domin ba yadda za a yi ya kasance
haka in ba fatalwa ba ce shi! Abii Yazid bai taka kasar
Hausa ba. Ba kuma Balarabe ba ne in ma ya zo kasar
Hausa kamar yadda tatsuniyar Palmer ta samar, domin
shi Barbar ne. Ba kuma mutumin Bagadaza ba ne a
kasar Irak, mutumin yankin Tunisiya ne, haifaffen
yankin Afirka Ta Yamma a yanzu. Bisa wannan tunani
muna iya cewa ba shi ne ya zama Sarkin Daura a
shekara ta 1,000 da muka gani a cikin littafin Palmer
da aka buga a 1928 ba. An dai kirkire shi ne a cikin
littafin Palmer na biyu a shekarar 1936. Bisa wane
dalili? Shi ne ba za a iya tabbatarwa a halin yanzu ba!
Mun dauki wannan dogon lokaci muna bin wannan
tarihi da kuma tattace duk wani bayani domin mu kara
tabbatar da rashin ingancin wannan taririhi, duk da
cewa mun ce ana iya samun kanshin gaskiya a cikin

ASALIN INDA KALMAR HAUSA TA FITO

ASALIN INDA KALMAR 'HAUSA' TA FITO
(Tsakure daga Muk'alar Nazarin Tarihin Hausa)
Sadiq Tukur Gwarzo
Hakika, sanin inda kalmar hausa ta samo asali abin bukata ne a garemu, duba da yadda muke da kauna gami da soyuwar son jin tarihi mafi gaskiya na wannan harshe namu.
Idan wasu sunce asalin kalmar 'Bahaushe' wadda ake lakabawa wanda duk ya fito daga masu yara harshen Hausa, ta zone daga kalmar 'Baushe', ma'anarta kuma mafarauci, to sai muce ita kalmar hausa kuma daga ina ta samo tushiya?
Kalmar Hausa ance bakuwa ce, wai daga baya tazo. Ance ma masanin tarihi Leo Africanus ya tabbatar da cewa a zuwansa Katsina da Kano a karni na sha biyar, baiji ana faɗin sunan hausa ba, kuma da yaren gobiranci yaji ana magana.
Haka kuma manazartan littafin nan mai ɗauke da tarihin kano mai suna 'Kano chronicle' sun tabbatar da cewa tun daga zamanin Bagauda har zuwa kan Abdullahi Burja, ba'a amfani da kalmar hausa. Sai a wuraren karni na sha biyar, lokacin ɗansa…

Hausa Ta Riga Ta Zama Harshen Kasashen Duniya

HAUSA TA RIGA TA ZAMA HARSHEN K'ASASHEN
DUNIYA.
`
(M) Abba Muhd Danhausa.
`
Bana jin wata al'umma zata samu cigaban a zo, a
gani, ba tare da ta yi rik'o da harshenta da kuma
al'adunta ba, kamar yadda Farfesa Muhammad
Hambali Jinju (1990) ya ce, "Ilmantar da matasa cikin
harshe bako, misali Faransanci ko Ingilishi, ya
kasance ɗaya daga cikin dalilan lalacewar al'adu da ci
bayan ilmi da zamowar 'yan k'asa bak'i a cikin
k'asarsu.
`
Kamata ya yi Afirkawa su gane makircin Turawa 'yan
mulkin mallaka, tsofaffi da sababbi, kuma su binciki
harsunansu na kansu da al'adunsu nagari, su ciyar da
su gaba ba tare da ɓata lokaci ba. Harshe, kowane iri
ne, yana iya ci gaba da hanzari muddin masu shi sun
tsaya, tsayin daka, sun bincike shi kuma sun kare shi.
Wajibi ne Afirkawa su ci gaba da kasancewa Afirkawa,
ba Turawa Bakar Fata ba.
`
Samuwar harshen k'asa wanda kuma shi ne harshen
mulki da koyarwa ita ce ma'aunin girma da darajar
k'asa a i…