Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

Showing posts with label Darussan Rayuwa (Life Lessons). Show all posts
Showing posts with label Darussan Rayuwa (Life Lessons). Show all posts

KISSAR WANI MUTUM DA YA SABA MA ALLAH SHEKARU 40

KISSAR WANI MUTUM DA YA SABA MA ALLAH SHEKARU 40:An ruwaito cewa zamanin Annabi Musa, Alaihis salam, fari (rashin ruwan sama) ya samu Bani Isra'ila, sai suka taru su dubu saba'in ko fiye da haka suka je wurin Annabi Musa, suka ce: Ya wanda Allah ya yi magana da shi, ka roka mana Allah Ya shayar da mu ruwan sama. Sai Annabi Musa ya tashi ya fita tare da su zuwa filin da ke wajen gari. 

Daga nan Annabi Musa Alaihis salaam, ya ce: "Ya Ubangiji ka shayar da mu ruwan sama, Ka yada RahamarKa a gare mu, Ka tausaya mana saboda dabbobi da kananan Yara da suke cikin mu da tsofaffi... 

Annabi Musa Alaihis salaam ya ci gaba da cewa:" Yaa Allah kar ka haramta alherin da ke wurin Ka, saboda laifinmu". 

Sai Allah Ta'ala Ya ce: "Yaa Musa a cikinku akwai wani bawa shekara arba'in yana saba mun, ku umurce shi ya fita daga cikinku, domin saboda shi na hana ku ruwa". 

Sai Annabi Musa ya ce: "Yaa Allah ni mutum ne mai rauni, kuma muryata ba za ta isa ba saboda yawan su ya kai dubu saba'in ko fiye da haka. Sai Allah ya ce da shi kai dai ka yi kira ni ne mai ikon isarwa. 

Sai Annabi Musa ya juya yana kira cikin mutane yana cewa: Ya kai wanda ka yi shekaru arba'in kana saba ma Allah, ka fita daga cikinmu, domin saboda kai aka hana mu ruwan sama.

Lokacin da wannan bawa ya duba hagu da daman shi bai ga wanda ya fita ba sai ya fahimci lallai shi ake nufi, sai ya fadi a cikin zuciyar shi: idan na fita a cikin wadannan mutane shi ke nan asirina ya tonu; kuma idan na zauna za a hana su ruwan sama. Sai ya shigar da kansa cikin rigar shi yana mai nadama akan munanan ayyukansa yana cewa: Yaa Allah na saba maka tsawon shekara 40 amma ka yi mun jinkiri ba ka kama ni ba, to yanzu gani na zo maka a matsayin mai da'a don haka Yaa Allah ka karbe ni. Wannan bawan Allah bai gama magana ba sai ga sama ta hada hadari kuma Allah Ta'ala Ya saukar da ruwa. 

Sai Annabi Musa Alaihis salaam ya ce: "Yaa Allah ga shi Ka shayar da mu alhalin babu wanda ya fita daga cikinmu". 

Sai Allah Ta'ala Ya ce: "Yaa Musa na shayar da ku ne saboda bawan da ya hana ni in shayar da ku, domin ya tuba ya dawo gare ni. 

Sai Annabi Musa ya ce:" Yaa Allah ka nuna mun wannan bawa mai da'a kuma mai tuba?".

Sai Allah Ta'ala Ya ce: "Ban tozarta shi ba alhalin yana saba mun sai yanzu da ya tuba zan tozarta shi?".

Domin ganin inda na ciro kissar za a iya duba littafin قصص التائبين na فضيلة الشيخ محمود المصري. 

Allah Ta'ala Ya ba mu ikon tuba daga zunubanmu kuma Ya gafarta mana. 

Dan uwanku a Musulunci: 
Sheikh Umar Shehu Zaria
Share:

Yi Haƙuri


YI HAƘURI

Daga Phisio Tim YouTube channel video 

Fassarawa

 Jamilu Abdurrahman 


Yi haƙuri!

Barka da zuwa zamanin mutane masu girman kai. Zamanin da mutanensa kan iya yarda su rasa alaƙar da suka yi shekara ɗaya zuwa uku suna ginawa, kawai saboda yi haƙuri!

Zamanin mutanen da mace ta gwammace ta kwashe kayanta daga gidan mijinta ta koma gidan iyayenta a maimakon ta ce: yi haƙuri!

Zamanin da namiji ya gwammace ya rasa iyalinsa matuƙar zai samu jin cewa shi ya fi wani. 

Barka da zuwa zamanin da mutanensa kowa akan dai-dai yake. Zamanin da mutanensa ba sa taɓa yarda sun yi kuskure, zamanin da mutanensa suka san komai. Zamanin da mutanensa su ke ganin cewa sun isa, alhali sun jahilci yadda za su jure zama da juna. 

Zamanin da mutanensa suka gwammace su yi ta gardama na tsawon shekaru a maimakon su furta kalmar yi haƙuri!

Barka da zuwa zamanin da mutanensa suke ɗaura wa wasu laifukansu. Zamanin da mutanensa ke ganin su ke kan dai-dai a koyaushe kuma suke ƙoƙarin yi wa wasu hukunci.

Zamanin da mutanensa ke ganin rashin dai-dai a tattare da wasu kawai banda kawunansu. Zamanin da mutanensa suka gwammace su yi ta gardama a maimakon su ce: yi haƙuri!

Barka da zuwa zamanin da mutanensa ke taƙama da son kai. Zamanin da mutanen cikinsa ke so ko da yaushe mutane su ke basu haƙuri. Zamanin da mutanensa saboda ganin mutuncin kawunansu suka gwammace su ci gaba da rayuwa ba tare da wasu da Allah ya turo musu ba, maimakon su yi sulhu da abokan zaman su. 

Zamanin da mutanen cikinsa suka gwammace su yi baran-baran da abokansu da masu taimakonsu a maimakon su ce yi haƙuri ka manta da aibu na. 

Zamanin mutane masu ji-ji-da-kai. Zamanin da mutanensa ke ganin sun sha ƙarfin su ce: yi haƙuri! 

 Ku saurari labarai ku ji kuma ku ga yadda mutane da dama ke kashe masoyansu, aure ya mutu kuma ahalin da a da yake cike da farinciki yau ya koma mahauta, saboda muna jin cewa bai cancanta ace mu ce yi haƙuri ba

Shin ko za ku iya min wata alfarma ku furta kalmar Yi haƙuri?

Ya kuka ji da kuka furta kalmar?

Shin sunanku ya canja ne? Shin kalar fatarku ko tsayinku sun canja ne? Shin gyaran gashin da kuka yi ko kwalliya sun canja ne? Shin da kuka furta kalmar asusun bankinku ya yi ƙasa ne? Shin jinannakin ku sun rage ne yayin da kuka furta kalmar? Ko kuma kun kamu da Covid19 ne da kuka furta kalmar? 

Hmm, to mai yasa ku ka zaɓi ku rasa wannan kyakkywar budurwar ko saurayin saboda girman kai? Mai yasa ku ka zaɓi ku rasa wannan tarayyar mai ban mamaki, abota da kuma waɗanda ubangiji ya aiko domin su taimake ku a rayuwa? 

Kada ku manta fa shi girman kai rawanin tsiya ne. Wasun mu da dama sun rasa abokan zamansu saboda ya zama mana abu mai wahala mu ce: yi haƙuri! 

Shin ko kun san cewa kalmar yi haƙuri ka iya canja rayuwarku har abada? Kawai ku dinga faɗarta akai-akai, ku yarda da ni babu wani mummunan abu da zai faru. 

A duk sanda kuka furta kalmar sai dai fa a samu sulhu, za a sake samun zaman lafiya da lumana. Abota za ta sake ginuwa yayin da sabbin al'amuran ban mamaki za su ci gaba da wanzuwa.

Ku yi haƙuri, in har wannan saƙon ya saɓa muku. Na zo da salama ne. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 

Share:

DEAR


*Dear rich,*

Never make the mistake of thinking that your poor relatives visit you only because they are in need of something. In most cases, they come to greet you for the benefit of kinship and nothing more. Hence, do not frown your face when you hear them knocking. 
More so, never have the impression that because Allah has blessed you with riches, you are too big to pay visit to less endowed relatives or that when you visit them, they will be expecting something from you and hence you stop visiting. Sometimes, you stopping by alone is enough to make them happy.

*Dear less financially endowed,*

Never make the mistake that when you visit your rich relatives, they will have the impression that you visit only because you need something from them. Hence, you decide not to visit them. 

*Dear all,*

In doing what is right, never worry yourself about what others think about you. Hence, keep the ties of kinship only for the sake of Allah and do not let shaitan use your social status to keep you away from your relatives.
Share:

HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 28

*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*


 ```// 28```
.
DA WA KAKE MA'AMALLA?
Idan ka ce ba za ka yi ma'amalla da wane ba to qila ka yi da shi ne a baya ba ka ji dadi ba, ma'ana dole yanzu a kiyaye, ka qaru da ilimi kenan, ba a cewa ba za a yi ma'amalla da mutum ba sai in an yi a baya ba a ji dadi ba, haduwa da mutane mabambanta hanya ce mafi sauqi da za ta qara maka ilimi wurin isa ga inda kake so, in mutum mahauci ne, yana da kyau ya san komai game da kiwon dabbobi, wannan kuma sai a wurin fulani, ta hanyarsu zai san dabbobin da suke da lafiya, da masu kitse ba naman kirki, da lokacin da ya kamata a sayi dabba ko lokacin da bai kamata a yanka nau'i kaza ba.
.
Yana da kyau kuma ya yi mu'amalla da Majema, domin zai riqa sayar musu da fata, tanan ne zai san irin fatun da suke buqata, da kudinsu, da lokacin da aka fi buqatar fatun, zai yi mu'amalla da Yarbawa kasancewarsu ma'abota ganda, suna sayen fatu da yawa su je su gyara suka riqa sayarwa, har ila yau zai yi mu'amalla da masu sana'ar sayar da gasasshen nama, wannan a matsayin misali ne, duk wani mai sana'a za ka taras akwai mutanen dake kewaye da shi wadanda yake amfani da su wurin aiwatar da aikinsa daidai, koda kuwa ma'aikatan gwamnati ne, za ka taras akwai kyakkyawar alaqa ta aiki tsakanin ma'aika kaza da kaza.
.
Ba abin mamaki ba ne ka ga ma'aikatar haraji tana mu'amalla da jami'an tsaro, masamman masu fararen kaya don tabbatar da kowa ya bi doka da oda wajen biyan harajin, idan wasu suka gano cewa ma'aikata kaza ba ta ba da haraji akwai wadanda za su yi bincike mai zurfin gaske a kansu, in an kawo su gaban quliya suka yi biyayya shikenan, to haka ma mutum a qashin kansa da yake neman aure, yana so ya yi nasara a cikin aikinnan, mata wato maqwabtan yarinyan za su taimaka, samarin dake kusa da ita, malaman dake koyar da ita a boko da islmaiyya da wurin sana'anta, in mai yi ce, duk za su iya ba ka abinda kake nema, kenan haduwa da wasu a gefe babban ginshiqi ne da zai taimake ka wajen cika burin ka.
.
Mutumin da yake son ya gwanance kuma ya ci nasara a aikinsa na likitanci yana da buqatar sanin injiniyoyi, kafintoci, ma'aikatan wutar lantarki, malaman makaranta, likitoci da sauransu, duk mutanennan za su amfane shi, injiniyoyin za su nuna masa irin ginin da yake buqata da yadda zai yi ginin ya dauki majinyata da dama a dan wuri kadan, qila a rushe tsohon ginin a sake wani da tsari mai kyau, malaman makaranta za su riqa turo dalibansu bisa wani alqawari ko yarjejeniya da za a yi ta rage kudin, da masu shagunan gwajin jini ko daukar hoton jikin mutum, ba nau'in mutanen da ma'aikaci ba zai amfana da su ba.
.
.
A duk lokacin da ka fara ma'amalla da wasu mutane dole ka koyi wasu abubuwa daga wurinsu, ko dai ka dauki ilimi ko darasi, in Allah ya sa ka yi dace da abinda kake so a wurinsa ka sami ilimi kenan, sai ka natsu ka koyi abubuwa da dama a wurinsa, in kuma akasin haka ne za ka dauki darasi sai ka san yadda za ka guje wa irinsa, ko ya aka yi dai mu'amalla da mabambantan mutane za ta taimaka wa mutum a harkokinsa na yau da kullum.
.
KA SAN MAHIMMANCINKA
Tabbas mun bambanta a rayuwarmu dabi'ummu da ma yadda muka dauki kammu, wannan ya sa wani yake jin cewa ba zai iya hada inuwa da wane ba don shi talaka ne, ko ba zai iya zama da wannan ba don shi mai arziqi ne, har ka ga wani ya shigo dakinka yana qoqarin zama a qasa, sai ka yi tsayuwar daka kafin ya yarda ya zauna a kan kujera, a ganinsa bai kai wannan matsayin ba, to rashin adalcinmu a yau duk matsayin da ka ba wa kanka haka wasu za su dauke ka, mun karanta cewa kowa a ofis dinsa shi ne babba don wurin aikinsa ne, in mai kudi ya kira ka faskare anan kai ne babba in ba ka yi masa ba ba zai iya yin abinda yake buqata ba, amma saboda rashin tsari irin namu ba ma fahimtar hakan.
.
Sai mu dauka tunda muna da kudi sai yadda muke so, in mutum ya ga ba zai yi ba mu canja shi mu kawo wani, muna sane da cewa in makewayin Alhaji ya cika ba zai fito ya tube riga ya kware matsuguninsa ya fara yasa ba, ba zai iya wannan aikin ba, sai dai ya nemo gwanaye a fannin, to idan su ma suna neman kudinka kai ma fa kana neman hidimarsu, kuma kai ka fara buqatarsu kamata ya yi ka ba su wannan girman, anan mun sami matsala ta rashin girmama juna, in mutum ya hau motarka sai ya riqa ji kamar ta gidansu, don zai ba ka kudi, ya manta cewa za ka yi masa hidima, in ya zo shagonka sai ya fado maka duk abinda ya ga dama don zai fidda kudinsa, shi ma fa zai karbi kayanka ya tafi da shi, yanzu an kai ko ofishin 'yan sanda mutum ya shiga in dai mai kudi ne sai ka dauka ba mai laifi ba ne, hankalinsa a kwance.
.
Tunda duniyar ta juya kai ma'aikaci ko mai sana'a ka lallaba kayanka, ban ce ka qasqanta kanka ba, in akwai halin da za ka lalla ba mutum kuma ka jawo hankalinsa a kaikaice zan so ka yi, shi kyakkyawan hali ko mugu yana son sa, matuqar za ka girmama kanka wasu ma za su girmama ka, sai in ka hadu da irin wadancan mutanen sai ka mu'amalance su ta wata fuskar amma kar ka yarda ka yi asararsu, akwai wani mai shago in na zo siyan kayan da ba shi da shi zai bar shagonsa ya sayo min a duk inda zai samu, wani sa'in ko ba ni da kudi zai yi amfani da nasa ya sayo min in na samu in mayar masa, ba fa yaron gidana ba ne ba a kamfanina yake aiki ba, wannan ya sa ba zai yuwu na sayi wani abu a wurin wani ba matuqar yana da shi.


Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```

Share:

HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 27

*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*


 ```// 27```

.
2) YI AMFANI DA DAMARKA A LOKACINTA
Da yawanmu ba mu san mahimmancin lokaci ba, inda za ka lura da masu wasan tseren dauka-sauke za ka ga kowa nasara yake son ya ci, amma dole ya san me zai yi, kuma cikin minti nawa? Dole ya yi qoqarin kammala duk zagayennan a cikin 'yan mintocin da yake da su, in ba haka ba komai qoqarinsa a banza ne yake yi, ma'ana ya riga ya saki hanyan nasara kenan, a addini ma za ka ji ana cewa yi kaza kafin kaza ya same ka, shi ya sa a darussan baya muka ce 'yan siyasammu da za su yi shekaru qasa da hudu su sauka, me suka iya yi wa jama'a wanda zai lamunta musu dawowarsu? 
.
In kuma wadanda dawowar da ma da wahala kamar kansiloli me suka yi wanda zai lamunta musu damar shiga takarar shugaban qaramar hukuma? In kuma mai koyon sana'ar hannu ne shekara nawa kake zaton za ka yi? Shin wadannan shekarun sun isheka ka gwanance? Ka fara samun wadanda in ka bar wannan wurin za su biyo ka duk inda kake saboda jin dadin aikinka? In ba haka ba ne to ka sake lissafi, kai za ka qiyasta lokacin da kake son ka yi, sai in asali dama yanayin sana'ar a qiyasce lokacinta yake, ko kuma sai maigidanka ya sallame ka.
.
Har da haka, kana da damar da za ka diba wa kanka shekarun da kake buqatar ka zama wani abu a fagen, yadda wasu masu buqatar aikin da kuke yi ba sa iya sakewa da kowa sai kai, mutumin da nasara ke gabansa zancen hutu kowani lokaci ba nasa ba ne gaskiya, shi ma yana cikin tsarin da ya diba wa kansa, lokacin aiki daga kaza suwa kaza, zumunta lokaci kaza, abokai lokaci kaza, in bai yi aure ba qila yana da lokaci kaza don wace zai aura, in kuma ya yi to iyalin nasa na buqatar lokaci kaza, sai an hada da haka don zomo ba ya kamuwa daga zaune, in dai ba za ka shigar da hutu lokacin aiki ba, to bai dace aiki ya riqa shiga lojacin hutu ba, tsari yana da amfani.
.
Mukan ce wane dan boko ne, amma za ka taras ya fi kowa jin dadin rayuwarsa saboda irin tsarin da ya yi, kasuwanci ko aikin ofis ko na masana'anta ko ma'aikata ko wata sana'ar hannu duk suna buqatar lokaci, in kana koyon aiki ka cire qyuya ko gani-gani, ka sanya haquri banda sauri, komai lokacinsa na zuwa.
3) ME KAKE HANGOWA? Ka ga dai sana'ar da kake yi za ka taka ka hango nasara, kai ka samo ta ka gina ta daidai tsawon da kake ganin za ta isheka, kai ka hango inda take kafin ka dauki hanyarta, bai dace ba a ce ka yarda wanda bai da irin wannan tsaunin da ka taka wai shi ne zai hango nasaraka ya gaya maka ga hanyar da za ka bi.
.
To in kuma shi ma ita yake nema fa? Ba laifi ka saurari mutum, amma ka san irin shawarar da yake ba ka, in mai kyau ce ka amsa in kuma ka san ba ta da kyau duk da haka ka biye musu ka saki hanyar da ka tabbatar da ingancinta a qarshe za ka fahimci cewa hanyar kwana ta yi da kai ta dawo da kai baya, kana buqatar hankali da natsuwa da jajurcewa da samun qarfin gwiwa, sai dai duk wayonka ka yi qoqarin tattaunawa da masu ruwa tsaki a cikin harkar, ko ka abokance su ka sanya ido a irin yadda suke gudanar da tafiyarsu.
.
4) Banda yanke qauna, ka yi zaton cewa wannan sana'ar ba za ta kawo maka abinda kake so ba, bayan ba ka jima da shiga ba, na ga wanda ya shiga soja, ko wata hudu kyawawa bai yi ba ya gudu, wai wahala kawai ake ci ga wasa da rayuwa, na ga wani tela da ya fara gwanancewa, shi ma ya watsar da sana'ar, ya raina abinda yake samu, kuma bai ajiye wata ba, na ga wace karantarwa take yi ta watsar da aikin wai ayyuka sun yi mata yawa, sai ta koma sana'ar da ba ta kai koyarwar daraja ba.
.
A kullum mutum ya sani cewa ba sana'arka ce nasarar ba, amma ita ce za ka taka wurin hango ta, iya bisanta iya inda za ka iya hangowa, sai ka san irin ginin da za ka yi mata, da kuma qarfinsa da bisansa, ka shirya kenan, amma in ka gaya wa kanka cewa tana da nisa ba za ka iya hango ta daganan ba, zai yi wuya ka yarda ka gina don ka san wahalar banza za ka yi, anan ka yanke qauna akan abinda ba ka tabbatar ba ya sa ka sha wahala a banza kenan.
5) Kar ka riqa nuna wa mutane fuskar rashin cin nasara a kullum, ba laifi ba ne in ka sha wahala ka gaya musu, kamar yadda ba na ganin duk dadi za ka sha sai ka kwashe ka gaya wa mutane.
.
Amma fa wadanda suke qarqashinaka su riqa sanin abinda kake ciki, ba wai ka gaya musu ba, su ji a jikinsu cewa tabbas an sami alkhairi, dan gutsura ka ba su don qarfafa gwiya, kai ka san irin abinda zai dace da su, kudi ne ko sutura da abinci, ko wasu kayan qyale-qyale? Da haka za su fahimce ka in ka yi musu bayanin halin qunci da kamfani ya shiga, don kana yi din in aka samu, in ba ka yi ba kowa zai san cewa tabbas ba ka samu din ne ba, ka yi qoqarin maida komai ga Allah, samu ko rashi, in ba haka ba wasu lokutan za ka yawaita samun sabani da jama'a.


Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```

Share:

HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 26


*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*

 ```//26 ```

KAI NE FARKO

In har za mu nemo hanyar cin nasara a rayuwa kai ne farko, domin kai ne za ka fara laluben inda take ka hau hanyar nemanta, wasu cikinmu suna ganin cewa in ka ji ana maganar nasara to a neman aure ne ko wasan motsa jiki, tabbas an fi samun nasara idan akwai gasa, amma wace gasa ce ta wuce mutum ya sami abinda yake so a rayuwa? Duk masu qoqarin cin nasarannan da kake ji kowa haqilonsa shi ne ya sami abinda yake so a rayuwa, na zauna da wanda bai da wani zance sai ya zama mai kudi, ma'aikacin gwamnati ne, ya qi komawa makaranta ya qaro karatu, arziqin mahaifinsa ya karye bare a yi maganar gado, baida sana'a bare mu ga nau'in sana'ar da kuma gudunta wurin isa ga nasarar da yake nema.
.
Akwai qananan sana'o'i wadanda masu kudinmu na yau duk sun yi su, amma sun yi sana'o'i da yawa a bayansu, na ga wani mai arziqi aka ce wanki-da-guga ne silar arziqinsa, da na bincika sai na ji ya yi wasu sana'o'in barkatai a tsakiya, na ga wani matashin dakta a ilimi da na tambaye shi yadda aka yi ya isa wannan matsayin, sai ya fara ba ni tarihinsa wanda na ji har qasashen maqwabtammu ya zaga don neman nasara a rayuwa, ya sheda min cewa burodi yake sari yana sayarwa, ya yi wasu sana'o'in kafin ya dawo ya riqi karatun da yake dogoro a kansa yanzu?
.
Kai dai ka lura wace sana'a ce za ka fara don ta zama maka gada wurin isa inda nasara take? In ka tara masu kudi kowa za ka ji hanyar arziqinsa saban ce, akwai shahararrun mawaqa da na gani suka ce daga almajirci suka zarce, ka ga dai kamata ya yi a ce sun zama malaman Qur'ani, to ba su kadai ba, na ma ga wasu masu abin hannunsu, arziqi ya kankama kuma suka ce daga almajirci suka fara, kowa kuma ya san almajirci ba sana'a ba ne bare a fara tunanin yana kawo arziqi ko bai kawowa, uwayensu kan turo su ne sai yadda hali ya yi, ko karatu ko wani abin, duk abinda yaro ya fara bude ido da shi to shi ne zai zama mafarin tafiyarsa da zai riqa takawa yana hango nasara da shi.
.
1) Yanzu dai a matakin farko ka fara amincewa kana son ka dogara da kanka, ba wai jira kake a raba gado ka samu a sama ba, ko hakan ne ma ka sani in har aka ba ka kasonka dole ka riqa ririta shi kana qara yawansa, qoqarin da za ka yi wurin ba wa dukiyar kariya ta rurin qara yawanta ya fi wanda za ka yi a lokacin da kake neman na kanka wahala, don haka yi qoqari ka kama sana'a, fitar da burin cewa za ka gaji kudi, ko tsammanin wani zai taimake ka, yi qoqari neman na kanka ya zama maka jiki kafin ka riqe wata dukiya da za ta shigo maka daga baya, da za ka riqe kantinka da ka habbaka shi shi cikin shekara 17, ka miqa shi ga wanda mai san kan sana'ar ba, ka ba shi shekara daya tal ka dawo ka ga inda ya kai.
.
Yi qoqari ka gano inda ka fi rauni, in ba ka son abokanka su riqa ganinka kana qananan sana'o'i to ka nemi irin sana'ar da za ka zauna wuri guda kamar tela, tsaron kanti da sauransu, kar ka dauki kabu-kabu ko yaron mota ko sayar da gwanjo wuri -wuri, ka amince wa kanka tabbas kana son sana'ar, kuma za ka iya yin alfahari da shi a ko'ina ne, in mace ce kake nema ka gamsar da zuciyarka cewa da sana'ar za ka ciyar da ita, daganan sai tsarin yadda za ka tafiyar sana'ar ba tare da tsoron komai ko kowa ba.
.
In ka fara sana'ar za ka ga wasu matsaloli a tsakiya kar ka damu, ka sami qarfin gwiwa kawai, ina yaro na yi sha'awar bara yadda na ga sa'o'ina yara suna neman na kansu kuma suna iya yi wa kawunansu wasu abubuwan duk da cewa suna nesa da mahaifansu, mu kuwa muna gaban uwayen ba iya tsinana komai, ranar farko da na fita aka kama ni a gida na ji jiki, bayan wasu lukuta kuma na yanke zama yaron mota, har na sami wanda zan riqa bi, amma da yaron gidansa ya zo haka ya ce min na sauka, daganan na karaya na koma gida, banda wannan ma na taba zuwa gona na siyo rake na je kasuwa, don in sayar in sami na rufin asiri, amma ni da kaina na saka rakennan a gaba na shanye kayana, wanda na sayar kuma na cinye kudin, shi ma dai ban ci nasara ba.
.
Bayan na qara wasu 'yan shekaru sai na fahimci da a ce na sauko da kaina qasa na bi dayan abokaina da yake dayan sana'o'in da na yi dinnan, na koyi aikin sosai, na kuma san yadda zan yi manejin rayuwa qila da hakan bai faru ba, amma duk da haka na gode wa Allah, domin na yi karatun rayuwa, wajen fadi tashina na sami wurin da na maqale har na kawo matsayin da nake ciki yanzu, akwai wani yaro da ya yi rayuwa kusan irin tawa amma ya fi ni natsuwa, ban san sana'o'in da ya yi a baya ba, amma na fara ganinsa da 'yan faya-fayen bidiyo na wasan Hausa yana yawo da shi, da yake yana samun ciniki a kasuwar unguwarmu sai ya yi wani dan shago dan mitsili wanda ko shi bai iya shiga, sai dai ya jera faya-fayen in za a saya ya ciro wa mutum ya ba shi.
.
A hankali ya fara kawo man shafawa da 'yan turarurrukan mata yana sayarwa, maganar da muke yi, ya kama shago a daya hannun ya maqare shi da nau'ukan turare, yana kan hanyar nasara, akwai wata mata da na san ta auri wani mutum, mu a waje muna kallon soyayyar da suke sha kuma tsuna burge mu, amma a cikin gida auren na lilo yana qoqarin balgacewa, ba abinda ta rasa na ci da sha da sutura, kudi kuma sai dai ta ba wasu, komai take so gashinan, sai dai tana da matsalar shimfida, 'yan uwanta ba su ganin wannan wani abu ne, na ce ita ce da kanta za ta fara nemo wa kanta hanyar nasara.

Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Share:

HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 25


*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*


 ```// 25```
.
WASU SHARUDDA

Idan ka sami kanka a wani kamfani ko masana'anta, ko shagon sayar da kaya, kai ko gidan aure mace ta sami kanta, da sauran wurare wadanda mutum zai yi aiki a qarqashin wani in dai zai kiyaye wasu sharudda akwai alamun nasara tattare da shi:-
1) Kar mutum ya so kansa sosai, in sana'ar na buqatar mutane ya dauke su, kuma ya yi musu farali da nafila komai nasa zai tafi daidai, za su kare masa amana, kuma su yi aiki tuquru don ganin an cimma abinda ake nema.
.
Cin nasara a aure kan samu ne in mace ta iya tattalin gidanta, ta gina tabbatacciyar soyayya tsakaninta da maigidanta yadda ba a jin wani labari sai wanda zai faranta rai, ba ta kanta ko jikinta ba, sai auren ya yi nasara, in ka yi niyyar aikata alkhairi ka sami damar yin ba ya nufin ka ci nasara, sai ikhlasi ya tabbata a aikin, yadda ba ka ba shedan damar kutsawa ba bare ya wargaza maka aiki, in ka nuna wa wani shi ma ya yi sai ka sami ladarka da nasa ka yi babbar nasara kenan, da ka yi rowa tabbas ladarka kai kadai za ka tashi da ita.
.
2) Ya zama dole ka san ko kai waye, ka kuma san inda za ka tura kanka, ka tabbatar ka dace da wurin, in ba haka ba kai da kanka za ka ga alamun rashin cin nasara, koda kuwa mutum ne mai son yin magana a kan addini amma bai tsaya ya karance shi sosai ba, zai riqa samun matsala kuma masu abin ba za su daga masa qafa ba, sai a yi ta dauki ba dadi tsakaninsu, qarshe gaskiya ta yi halinta, to bare aiki inda gajiyawarka za ta bayyana a sarari, kodai a kore ka ko ka kori kanka, ba yadda mutum zai karanci Larabci a zo neman malaman Turanci ya kai takardunsa, sai in ya shirya jin kunya.
.
3) Dun inda za ka yi aiki ka sani cewa nan ne wurin da arziqinka yake, anan ne za ka riqa samun na rufin asari har ka ciyar da iyalinka ka yi zumunci, don haka ya zama maka dole ka bi doka da oda don samun zaman lafiya a tsakaninka da masu wurin, in ka ja aka kore ka shi kenan sai dai ka nemo wani wurin, misali malami ne ya nemi aikin soja, tun wajen gwaji ya fara cewa ba zai sa gajeren wando ba, ba zai tsaya yana kallon al'aurar mace ko ya mannu da ita ba bare ya riqe hannunta inda hakan ta taso, ba zai yanke gemo ba sabon Allah ne, wadannan duka gaskiya ne, kuma mutum zai kiyaye duk wadannan a gidansu, in ya zamanto sojoji ba su yarda da wani ba zai ci duka ne a banza kuma dole ya yi abinda ake so, in ya bari bai ci nasarar abinda ya kawo shi ba.
.
4) Mutum ya riqa yi wa kansa hisabi, shin ina yin wannan aiki kamar yadda ya dace kuwa ko akwai kuskure? Ya yi qoqarin kallon kansa yadda yake a bara, wasu 'yan canje-canje aka samu zuwa yau? Shin tafiyar tana sauri ko tana ta-ta-ta? Ya kalli abokan aikinsa, suna tafiya tare yadda ya dace ko sun yi masa nisa? In wurin nasa ne ya lura da ribar da yake kintatowa ya samu ko da saura? In harkar ba ta sauri kamar yadda wasu da suka fara take yi musu meye matsalar? Wuri ne ko jari, ma'aikata, albashi, ko yanayi? Ko riba ya samu ya yi qoqarin gano musabbabi don ya lazimce shi.
.
5) Dole ne kowani ma'aikaci ko shugaba a wuri ko mai mahallin gaba daya ya dubi alaqarsa da kowa don samun ci-gaban wuri, in ka san siyasar wuri sai ka zauna da kowa lafiya kuma ka yi aikinka, mun taba yin wata Islamiyya a cikin arna, da muka kyautata mu'amalarmu da su an tashi yaqi za a qona wurin, maqwabtanmu su suka ba mu kariya yadda ba a qona ta ba, na ga mutumin da uwayen matarsa ba sa qaunarsa, amma kuma ba su isa su yi gulmansa a gaban 'yarsu wato matar mutumin ba, kenan ya kyautata zama da ita, hakan ta sa ya yi nasara, ko kamfani kake da shi in ka kyautata mu'amalla da ma'aikatanka su kansu za su ba ka kariya ciki da waje.
.
6) Shiga irin wace ta dace da yanayin sana'ar, shigar da malamammu na addini suke yi, in za a kwatanta ta da wace malaman makarantun boko suke yi akwai bambanci, shigar kowa kan sa aga qimarsa a wurin aikinsa, kamar lauyoyi, likitoci, masu kayan sarki, da sauransu, ba yadda bakanike cikin kayan aiki ya kama hanyar sakatariyar qaramar hukuma ya ce lallai yana son a girmama shi a matsayin babban baqo, ba zai ci nasara ba, yanzu ko baburan haya dake yawo a kan titunanmu kana ganin direbobinsu za ka iya ganewa, saboda irin shigar da suke yi, sanya kaya irin wace ta dace da wuri takan sanya a ga qimar mutum, koda ba sa ba ka sha'awa daure ka kalli aikin da kake yi ka sanya su dominsa.
.
7) Idan kana son ka ci nasara a rayuwarka dole sai ka yi wa harshenka linzami, kuma ka qimanta na gaba, kar ka zama sabon masinja, maganar da ba taka ba kar ka shiga, in manyanka na magana ja bakinka ka tsuke, kar ka yarda a ji magana a wani wurin a ce kai ka kai ta, banda yawan kukan ba ka da kudi ko an qi yin albashi da sauransu, ba ka fi kowa matsala ba amma sun yi shiru mai zai sa ba za ka haqura ba? Wasu da dama sun kasa cin nasara a rayuwarsu saboda azalbabi da shiga rigingimun da ba su zama musu dole ba, na ga matar da maigidanta ya sake ta a dalilin rigingimun da take hada masa kullum, aikinsa kenan ban haquri, har dai ya ga za ta kifar da dan sauran mutuncin da ta rage masa ya iza qeyarta, auren bai yi nasara ba, a kiyayi jayayya da shugaba, yakan yi saurin hana cin nasara a rayuwa.

Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Share:

HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 24


*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*


 ```// 24```
.
AIKINKA

Za mu iya kasa qananan ma'aikata zuwa gida biyu, akwai wadanda suke aiki don neman abin sakawa a bakin salati, da kuma wadanda suke yi don tsare dukiya ko tarata, manufar kowa game da aikin akwai bambanci, dagewa da mai da hankali wurin wanda yake aiki don neman abinci bai kai kamar mai yi don tara dukiya ba, shi ya sa ko kyauta za a yi sai ka ga bambanci a tsakaninsu, na taba jin wani babban mutum da na san yana da wani babban kamfani yana ta bala'i a kan Naira hamsin, ya ce in mai kayan ba zai sayar a Naira 500 ba a dawo masa da kudinsa, don me za a qara masa Naira 50?
.
Babban abinda ya kamata mutum ya tsare shi ne aiki koda ba nasa ba ne, kwanannan nake ji wani asibiti sun dauki wata daliba daga gwaji saboda tsabar hazaqarta da dagewarta, na ga wasu lakcarori su ma an dauke su saboda hazaqarsu a dakin karatu, suna gamawa aka dauke su aiki, a duk lokacin da kake aiki ana kallonka, kar ka ce don ba naka ba ne ba za ka wahala ba, in ma naka din ne jajurcewarka wani babban jigo ce da za ta taimaka maka wurin ganin ka isa inda ake buqata.
.
Ba wani ma'aikaci wanda bai sha wahala ba kafin ya kai ga gaci, bari mu dubo wasu 'yan abubuwa ko na ce sharudda wadanda su ne ginshiqan cin nasara masamman a rayuwarmu ta baya-bayannan, duk wani ma'aikaci yana da kyau ya sani cewa ba wani aiki a duniya wanda ake fado masa ta sama, komai yana da farko, in ba ka sani ba kuma kana son cin nasara to ka nemi a nuna maka a matsayinka na sabon ma'aikaci, kar ka yi girman kai, alamun ka shirya aikin kenan, in mutum na neman aiki zai jigata, in ya samu bai nufin yanzu hutu sai ya nade hannu ya ci arziqi, yanzu ya kamata ya fara aiki.
.
Samunka da aiki yana nuna cewa aikin ma ya same ka, in kai ne mai wurin sai ka yi tsayuwar daka wurin ganin ya habaka, kar ka yi zaton shikenan yanzu hutu ya zo, idan kana zama wa wani a kantinsa ne sai yau ya yaye ka, ya bude maka wani dan qwarya-qwaryan kanti kar ka ce "Yauwa 'yanci ya zo, na farko dai sai lokacin da na fito kuma ina da zabi a lokacin da zan koma gida, zan ci abinda nake so, kudin duk da na samu nawa ne sai yadda na yi da su, in ka yi hakan haqiqa ka yi gaggawa, da dan sauran tafiya a gabanka.
.
Wannan wata gada ce da ka tsallake daga dukiyar wani zuwa taka, lokacin da aka mallaka maka kudin gado bayan da kana fama da talauci kar ka taba zaton ka haye, gada ka samu, in ka taka a hankali ka haye, in ka yi gaggawa ka auka ciki, kudin ko shagon da aka ba ka asali na wani ne, za ka dan dauki lokaci kafin ka maida su naka, zan ba ka misali, wani lebura da ya yi aikin wuni tun da safe har maraice kafin ya sami 2,000 a matsayin ladar wahalarsa, kai kuma ka yi rakiya ne a ka miqo maka wannan kudin, cikin sauqi za ka ce a zare maka tsire na dari biyar, shi kuwa ba zai sha wahala tun safe ya kashe dari biyar a kan tsire kacal ba, wanda ya bude shago ya ce ya zama naka, ku ka sami gado, ko ka zama shugaban qaramar hukuma ko kansila za ka dan dauki lokaci kafin ka maida kudin naka, in dan siyasa ne qila sai ya sauka gaba daya kudin sun girgiza kafin ya fara jin cewa nasa ne.
.
Gaggawa ce ke damun mutanenmu, na san wanda ya gaji miliyoyi yanzu ya koma abin tausayi kamar ba shi ne jiya yake fantamawarsa ba, na ga wani dan siyasa wanda ya sami kudi ya yi gidaje ya mallaki kadarori da dama, yanzu ko gidan kansa bai da shi, wani ma gidan ma ya raba biyu ne ya sayar da rabi yadda zai samu ya iya ririta rayuwar, wani bawan Allah ya yi ritaya aka ba shi kudinsa tsibi a hannunsa, ya sami wasu bayin Allah suka ba shi shawarar cewa ya yi shago don kar kudin su qare a banza, ya karbi shawararsu ya fasa daki daya daga cikin dakunansa ya mai da shi shago, ya maqare shi da kaya, kusan komai kake so yana da shi, yanzu aiki ya kamata ya fara tuquru, don ya tabbatar da nasarar da yake ganin ya samu.
.
Sai ya yi kuskure, ba ya iya futowa shagon sai rana ta raba, kafin taran dare kuma ya rufe, sai mutane su zo sayen kaya ba shi, in an aika masa ya ce ba zai fito ba, aka yi ta kukan hakan har aka gaji aka fita harkarsa, da dai ya ga kamar abubuwa na dan ja baya sai ya dauki ma'aikaci, shi ma bai zabo qwararre ba, ya hada irin tarhon kusa dinnan, in an zo sayen kaya sai a buga masa ya fadi kudin, shi ba zai iya zama a shagon ba ya zama babba, ba a jima shagon ya lalace aka rufe shi gaba daya ya koma dakin kwana, na ce ya yi gaggawa ne, na san wanda ya tarairayi abinda ke hannunsa yanzu ana ganinsa a matsayin mai isasshen jari.
.
Idan ka sami jari a rana guda na tsabar kudi wadanda ba ka zata ba, yi qoqari ka zuba su a banki ka manta da su, ka dawo ka fara neman abinda ranka ya natsu da shi kuma yanayin da ake ciki ya karba, sannan ka zauna da wadanda ke cikin harkar ka gani kuma ka tambayi fa'idoji da matsalolin dake cikin harkar, sannan ka qimanta masaniyarka da qoqarinka in zai yuwu ka shiga, sai ka ajiye cewa yanzu ne za ka fara neman nasara ba wai da samun wannan kudin har ka cimmata ne ba, sai ka sanya Allah a gaba ka yi ta roqon ya ci gaba da agaza maka kamar yada ka faro tun farko.

Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Share:

HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 23


*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*


 ```// 23```

.
DABI'UN WASU
Haka Allah ke yin wasu sai dai ka yi haquri da su ba za ka iya canja su ba, amma kai da jinsu ka san akwai matsala, ba za mu ce ba za su ci nasara a rayuwarsu ba, amma tsakani da Allah ba sa jin dadin nasarar koda sun same ta, misali: In mutum ya shiga neman aure zai taras da wasu ko cimmasa, wanda Allah ya ba wa nasara shi zai aura kansu, qalu-balen ya rage ga yadda za a zauna da matar, in suka zauna shiru cikin son juna ya yi nasara, in gidan ya koma fagen yaqin basasa to bai yi nasara a auren ba tunda har lokacin zuciyarta na wani wuri akwai yuwuwar koma masa, kuma kwanciyar hankalin da ake nema ba zai samu ba.
.
Kai oga a kamfani ko kanti ko gidan haya ka sani fa cewa wanda yake kawo maka kudinnan ba wani qarfin da kake da shi wanda ba shi da shi, amma Allah ya ba ka nasara a hannunka wanda shi bai da ita, kasancewarta a hannunka shi ya sa komai ya samu zai ba ka, sai dai ka gutsura ka ba shi, don haka ka lura da hidimar da yake yi maka ka yi haquri, na ga wani yaro sai bude wa wani tsoho wuta yake yi, yana ta zage-zage, amma tsohon ya sunkuyar da kai qasa ya kasa cewa komai, laifinsa ya yi barci a wurin aiki matar gida ta dawo ta yi ta horn bai sani ba.
.
Sai da suka wuce sannan baba ya fara magana a hankali yana cewa "Sai haquri Alhaji, wallah barcinnan bai jima da dauke ni ba, ba ma iya runtsawa da daddare saboda gudun sakaci a aiki" a ganina zai iya jawo hankakin baba ba tare da ya bude masa wuta ba, nan gaba ko dai ya kori shi a dalilin bacin rai ko baban ya haqura, amma saboda sanin dabi'arsa baba ya ja bakinsa, yanzu nasara ake nema har a wurin aiki, musayar yawu ko ban haquri zai iya sawa a kore shi.
.
Kar ka taba azawa cewa masu irin wannan bala'in ransu na yi musu dadi ne a lokacin da suke zage-zage, ai ba sa iyawa sai hankali ya tashi rai ya baci, kenan zafin da za ka ji a lokacin da suke wulaqanta ka su ma fa suna ji, sai dai qila nasu yakan dan yi saurin sauka kafin su qara yi da wani, duk wanda hakan ta zama masa dabi'a ba ka da yadda za ka yi da shi, sanya nasara a gabanka, ka mai da qalu-bale baya, ka yi qoqari cimma burinka, ba wani amfani ga yin fada da maigida ko musayar yawu.
.
Shi ma maigidan ya yi qoqari ya duba al'amarinsa, in ya ga ya saki mace daya, ya qara sakin wata, ko in maigida ya kori ma'aikaci daya, ya sake iza qeyar wani lallai ya gane cewa ko bera na da sata to fa daddawa ma na da wari, da wahala a ce sam shi ba ya laifi sai wani, a kullum shi ne mai gaskiya, akwai mazan da ba su taba rabuwa da matansu ba, kullum cikin soyayya, kamar yadda ake samun ogogin da ba su taba korar kowa ba, ma'aikaci ko masu zaman haya kullum yabonsu suke yi.
.
Wanda ya ga ya mallaki komai amma koda yaushe yana cikin qunci sai fada da mutane to ya yi qoqarin yaqar abinda ke damunsa kar ya hana shi cin nasara, na taba barin gidan haya saboda masifar maigidar, kana gidan haya ne amma ba ka da ikon ka yi baqi, kuma matarka ba ta isa ta yi hurda da wata matar ba, mutum uku sun bar gidan a gabana, ni ma a dole na haqura na nade kayana na qara gaba, ban jima da barin gidan ba aka ce wasu mutum 3 su ma sun qara gaba, cikinsu har da wanda ya zauna a dakina, watansa biyu kacal, mai gida na ta fuskantar matsaloli a lamuran sana'arta ta kasa gyarawa.
.
KAI MA ZA KA IYA
Me ke kawo mutuwar zuciya? Ko na ce shekararka nawa kana karen mota, 10? Me ya hana ka zama direba? A shekarun da ka bata dinnan ka mallaki motar kanka kuwa? Amsar dai karen mota ne har yanzu, kuma bai ma gwanance a tuqin ba, bai kuma roqi wani ya koya masa ba, kenan bai yi tunanin zai iya zama direban ba, ya yanke qauna da cin nasara a rayuwa, in ba haka ba, akwai makarantun koyon tuqi mai zai hana ya shiga wata makaranta? Ko yana jira ne ogansa ya koya masa, to in kuma ogan ya fi jin dadin aiki tare da shi zai yi wahala ya so rabuwarsu, ya gwammace ya yi ta qara masa kudi don ya riqe shi.
.
Ni gaskiya na fi ganin laifin direban saboda rashin motsawa, in kana haya ne ai kana son ci-gaba me kake yi ba ka hau kan hanya ba? In haya kake yi me ka yi don ganin ka mallaki gidanka na kanka, wata qila ma ka gina wasu ka zuba masu hayan? Akan sami masu karbar mota a wurin direba su farauto masa fasinjoji su kawo masa, shi mai nemo fasinjojin mai ya hana shi samun motar da zai riqa daukar fasinjojin da kansa? Meye bai sani ba? Masu ba da motocin a yi musu haya ko tuqin, ko garuruwan da za a riqa kai fasinjoji? Jiya ake gaya min wani shahararren likitan fida a Kano wanda aikinsa na farko shi ne miqa wa likita kayan fidar, amma yanzu ya zama babba.
.
A daidai wannan lokacin na tuna wani babban hakimi wanda na san shi lokacin da yake masinja, yanzu ga shi ya zama babba, duk wani da ka sani ya ci nasara a rayuwarsa akwai hanyoyin da ya bi, akwai wanda ya ce min yana sha'awar siyar da filaye ne, na ce ba zai iya ba, ya ce don me? Na ce ko masu sana'ar bai sani ba bare ya san ta inda zai bullo mata, nan take ya lissafo min kusan mutum biyar, na ce ka taba zama ko hira da dayansu? Ya ce a'a, na ce wurina za ka zo kana hirar bayan kana sane da cewa banda wata masaniya da mai sana'ar ma bare na ba ka shawarar da za ta taimake ka? Abinda zan iya kenan na karya maka gwiwa kuma na kusa yi din.

Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Share:

HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 22


*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*


 ```// 22```

.
ME YA DACE?

Kowa da ka ni yana da abinda yake damunsa, kuma abu ne sananne ba zai taba yuwuwa a ce mutum ya boye duk abinda yake damunsa ba, ko bakinsa bai fada ba wani lokaci fuskarsa za ta bayyana, mukan boye amincewarmu ta bayyana kamar yadda take hankatso damuwarmu, amma wani sa'in dole sai mutum ya yi qoqarin shawo kan zuciyarsa da abinda yake damunsa, don kar harshensa ya riqa kubucewa ya debo masa aikin da bai shirya masa ba, na ga wani mutum da abokan kasuwancinsa suke gudunsa a dalilin abubuwan da suke damunsa, ba wai fada yake yi da mutane ba ko zage-zage kamar mahaukaci, a'a.
.
Da ka dan zauna da shi na wasu 'yan daqiqoqi zai fara fado maka matsalolinsa, wallahi ban da lafiya, duk kudina na kashe su a magani, wurin aikina kaza-kaza, 'yan uwana duk masu kudi ne ba sa taimaka min, na yi asarar kaza da kaza, kudi duk in na samu sai su watse a banza, wane ne ya yi min baki, mahaifana kaza da kaza, mutane sun riga sun saba da shi, ba wani abu yake nema a wurinsu ba kuma ba wani abu za su ba shi ba, amma ba sa son jin irin wadannan koke-koken marasa kan gado, da wahala ka ji mutum yana yi wa kansa fata ta gari, a kowani lokaci sai yi wa kansa mummunan fata yake
.
Wani kuwa iya abinda zai iya gaya maka shi ne "Alhamdu-lillahi" wani ya ce maka "Harkar ce sai godiyar Allah!" Ko zai qara maka wani abu sai dai ka ji ya ce "Abubuwa duk sun tsaitsaya amma in sha Allah komai zai gyaru, akwai alamun alkhairi nan kusa ba da jimawa ba" haka zai fara kallo wasu hanyoyi da za abi a fita, ya fara tunanin kawo sauyi a harkar, ko dai ya canja wurin zama, ko ya sauya kayan ko dai ya qawata ta ta wurin shigo da sabbin tsare-tsare, irin wadannan ba su cika dauwama a halin ni-'ya-su ba, don ba su yarda da cewa akwai abinda bai da mafita ba, ba su yarda da cewa lamarinsu yana hannun wani dan-adam ne ba bare ya takura su, rayuwa kullum a birgimar hankaka take, wata rana ka ga fari wata rana ka ga baqi.
.
Duk lokacin da mutum ya yi karo da wani abu mai kyau ya san cewa ba abinda yake dauwamamme, wata rana zai ga abinda ba shi yake so ba, sai ya yi masa shirin ko-ta-kwana, in zai zo din ma yakan zo masa da sauqi, wanda yake ganin cewa wani zai iya yi masa wani abu to duk lokacin da mummunan abu ya same shi zai ce wannan mutumin ne, a maimakon ya fara tunanin cewa jarabawa ce wace hanya zai bi ya cinye ta sai ya fara tunanin wane ne ya yi masa kaza dole ya rama, kuma ya ce "Shikenan ya gama da ni sai dai Allah ya isa kawai" ko ya ce za a yi musu hisabi a ranar qiyama, batun neman mafita kuma ya qare.
.
YA ZA KA KALLI MATSALOLINKA?
Duk wanda ka kalla yana da fuskar da yake kallon matsalolinsa, yana da hanyar da yake tunani ta daban, wani za ka taras addini ya yi masa tasiri, duk abinda ya same shi ko yake son yi zai kawo Allah a matakin farko, irin wadannan ba su cika rigima da mutane a kan abu qarami ba, cikin sauqi za su warware babbar matsala su ce maka "Ba komai, haka Allah ya so" su ma din akwai bangaren da sukan yi kuskure, abinda ya kamata su dauki mataki don kare faruwar abin a gaba ga shi sun bar shi ya wuce sakaka, wasu kuma ba sa son ka kawo musu Allah a duk lamarin da ya shafi san'arsu, a tunaninsu maganar Allah a addini kawai ake samunta ba ta hada hanya da kasuwanci ba, in mutum ya yi daidai ya ga daidai in ya yi kuskure ya taba ya ji, da yawa wadannan ba sa cin nasara a rayuwa.
.
Haka za ka sami kowa da fannin da yake tunaninsa, to kai abinda ya kamace ka shi ne ka kalli mutum da sifar da ta dace, ka kalli hanyar da yake tunani, ka kalli wayewarsa da iliminsa, ka kalli komai nasa, mace ce ko namiji, yaro ne ko babba, ya matattararsu take? Bai yuwuwa kai da aka haife ka a Kano ka tashi a cikin Hausawa, qila ma mahaifinka ne limamin masallacinku, ka sami wannan tarbiyyar, ka ce abokin sanarka ko mai maka aiki da ya taso a Kudancin Kaduna ba ma musulmi ba ne kana son ya yi maka irin ma'amallar da kai ka taso a ciki, kuma kana da tabbacin ba wahayi za a yi masa ba, za ku yi ta samun sabani ne, in maigidanka ne qila ka rabu da shi, in dan gidanka ne qila ka kore shi.
.
Ba yadda za a yi mutum ya riqa kallon kansa wurin yanke hukunci a kan wasu, ba dole ba ne a sami fahimta iri guda, amma kallon mutum a dabi'arsa zai taimaka, wata abokiyar aikina, daga kudancin Kaduna, ba a yi wata ba take gaya min irin wahalar da ta sha da mahaifiyarta, ina son na ba ta haquri ta dibo ashar ta hado da mahaliccin gaba daya sai da na girgiza a lokacin, ba arziqi na yi qoqarin kulle hirar gaba daya, ita da kanta ta fahimci ban ji dadin maganar ba sai ta fara qoqarin gyarawa, na tabbata in ba subutar baki ba ba za ta qara irin wannan a gabana ba, hanzarin da na yi mata ita ba musulma ce ba, ba ta da kawaici irin namu na Hausawa, ba ta da tarbiyyar girmama uwaye, shi kansa Allan ma ba su bi hanyar da za su kadaita shi ba bare su ba shi sauran sifofinsa da ya kebantu da su.
.
To bayan wannan ma a matattarar da muke ma, ko ciki guda ne akwai abinda ake kira Kebantattun Halaye ga Kowa, wato "Individual Deferences" a Turance, ko "Fruuq Fardiyya" a Larabce, irin wadannan halaye ko ciki daya yara suka fito, wato 'yan biyu za ka taras kowa da dabi'unsa, in haka ne kuwa dole sai mun riqa yi wa juna hanzari, in mutum ya kwabsa maka a matsayinka na shugaba ka kalli sauran ayyukan da yake yi kawai ka yi masa rangwame, in kuma kai ne yaron gida to ka yi masa hanzari, ka gane irin halin wadatar da yake ciki da matsayinsa, wanda in kai ne ba za ka yi haka ba, shikenan ya wuce sai a kalli gaba kuma.

Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Share:

HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 21


*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*


 ```// 21```

.
QOQARIN KAWO GYARA

In kana son kawo gyara a ma'aikatarka ko wurin sana'anka na yau da kullum dole ne ka riqa sanya ido, duk kuma wanda ya yi kuskure a gyara masa, sai dai gyarar kan yuwu ne wajen nuna masa kuskurensa, galibin abinda muke yi shi ne in mutun ya yi kuskure a dinga zaginsa da harshe can sama kowa na ji, ko matarka da ka auro in dai za ka juri daga mata murya za a kai lokacin da za ta shiga ramawa, samun mutum a kebe cikin natsuwa gyara ne, yi masa kwarwa cikin mutane kuwa kunyatawa ne.
.
QARFAFA GWIWA DA KALMOMI MASU DADI
In har kana da masu aiki a qarqashinka ka zama mai yawan raha a tsakaninsu amma ta wurin yin amfani da kalmomi masu dadi yadda mataimakanka ba za su damu ba, aqalla za su ruqa dariya ne a duk lokacin da ka cakali wani, irin su "Katafila sarkin aiki" ko "Agogo da aiki aka san ku" da dai sauran kalmomi masu dadi wadanda suke qarfafa gwiwa, to bare kuma in wani sha'ani na gama-gari ya taso kamar Azumi ko Salla babba ko qarama, ka daure a yanka dabba, in babban wuri ne ana samun kudi a raba wa ma'aikata danyen nama, in qaramin wuri ne a yanka rago a soye shi yadda kowa zai ci ya san ya ci nama, wannan qarfafa gwiwa ne, ka yi qoqari ka halarci duk wani taro irin wannan.
.
TA'AZIYYA BIKI KO SUNA
A matsayinka na babba ka daure ka halarci duk wani wurin farin ciki ko baqin ciki na ma'aikatanka, kai babba ne, wannan tabbas ba ja, amma duk wani qaramin da ya gan ka a wurin wani abu nasa zai ji dadi sosai ba kadan ba, masamman abinda ya shafi baqin ciki kamar mutuwa, asarar dukiya da sauransu, to bare kuma a ce ka dan guntsila wani abu ka miqa masa, kar ka raina qanqancin abinda za ka yi, ka duba girman tasirinsa ne a zuciyar wanda ka ba wa, nakan ji ana cewa "Alhaji fa ya zo" wani za ka ji ana cewa "Ai dabi'arsa ce, lamarin ma'aikatansa nasa ne" in da zai yi tunani duk wahalar da suke sha duk da cewa suna samun abin rufin asiri qarshe dai komai wurinsa zai dawo, ba domin gudummuwar da suke badawa ba komai cak zai tsaya.
.
SANYA GASA A TSAKANIN MA'AIKATA
Ka yi qoqarin sanya wata gasa a tsakanin ma'aikatanka, lura da wadannan 'yan bokon, duk da cewa muna kallon su marowata ne, amma abinda suke yi yana yin tasiri sosai a zuciyar ma'aikatansu, sukan yi wasu 'yan alluna a qarshen shekara su rubuta sunan mutum su ba shi a matsayin wata lambar yabo da take jinjina masa a kasancewarsa wanda ya fi kowa zuwa da wuri, ko rashin fashi, ko tsafta, ko ladabi da biyayya, ko aiki tuquru da sauransu, irin wadannan kyaututtuka suna da tasiri ba qarami ba a zukatan ma'aikata, kowa zai yi ta hanqoron a ce ya samu, ba kuma zai samu din ba sai ya aikatu, da haka sai aiki ya bunqasa, to bare a ce ana saya wa mutane motoci da mashina ko talabijin da wayoyin hannu da sauransu.
.
Wanda bai samu kyauta ba bai dage ba kenan, in babban kamfani ne ko saudiya sai a kai wani, duk da cewa mutum daya ya samu, amma zai zaburar da sauran ma'aikatan idan suka ji cewa dagewarsa ce da jajurcewa silar samun kujerarsa, in qaramar ma'aikata ce za a iya saya wa talaka qaramin buhu na shinkafa, ko galan din manja ko na man-gyada, ko dai wani abinda zai jawo hankalinsa, wannan ya fi masa wata lambar yabo, da yawammu ba mu san qimarta ba, ba mu cika wani lura da cewa nan da nan za mu murtsuke ci ya qare kenan ba.
.
DORA WA MUTANE NAUYI
Ita kuma wata dabi'a ce mummuna da ta zama dole mutum ya guje ta a matsayin shugaba ko abokin aiki, za ka taras wani kullum cikin hanzari ne "Don Allah wane dan riqe min wuri kaza ina son na yi kaza" ko ka ji yana cewa "Don Allah yau ba zan sami damar zuwa ba amma wane dan kama min kaza" in hakan ya fara yawa ko ka nema ba mai kula ka, za ka taras duk wanda ka kama yana zillewa saboda an maimaita ba daya ba ba biyu ba, ko shugaba ne ya yawaita dora wa ma'aikatansu wasu ayyuka a wajen abubuwan da suka san sun zama musu dole tabbas za ka taras sun noqe, ko in suka ji motsinsa kowa ya kama gabansa, ba laifi ya faru sau daya ko biyu amma ba a hade ba kuma kar ya yi tsawo, in ka dora wa mutane aiki to yagar musu wahalar aikinsu ka matsa su karba koda sun qi, shi ne zai ba ka garantin ka nema wata rana.
.
Idan kuma ka shugabanci wani bangare na jama'a a cikin ma'akata, taka ce ko aiki aka ba ka, ka yi qoqari wurin tabbatar da an yi aikin cikin nishadi, a maimakon ka zabo wanda ka raina ka labta masa kaya ka jira ya yi shi kadai, yi qoqari ka kira taro, koda ka san yadda za a yi ka dan dakata, ka fito da aikin sarari, ka nemi shawarar abokan aikin naka kan yadda za a tafiyar da shi, a maimakon mutum guda ya yi shi kadai, wanda hakan kuma zai dauke shi wani dan lokaci, ka yi qoqari ka kasa musu yadda kowa zai yi da kyau, kuma cikin nishadi sannan a dan qanqanin lokaci, buqata ta biya kenan, sannan shugaba ya riqa samun lokaci yana zaunawa da ma'aikatansa yana tattaunawa da su.
.
Abinda ya fi komai mahimmanci ma ya riqa shiga cikin aikin, in zai yuwu kar ya bari a sami wani bangare na kamfanin wanda ba ya shiga a yi da shi ko a ce bai san kansa ba, wannan sifar shugaba na qwarai kenan wanda tabbas nasarar yake nema kuma aiki yake yi tuquru don isa gare ta, ba wai mutum ya yi ofishi a gefe sai dai a riqa kawo masa takardu yana cikewa ko tattaunawa da abokan ciniki ba, na yi karantarwa a wata makaranta wace hedimastan lokaci-lokaci yakan hutar da wani malami shi zai koyar don ya ga fahimtar 'yan ajin da duk inda suka tsaya a karatunsu, dan lokaci kadan za ka gan shi a qofar tagarka yana kallon abinda kake yi wa daliban, in ya ga kuskure za ka ji kira a ofis, ya gyara maka cikin tsanaki.


Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Share:

HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 37

*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA // 37*

MATAKI WANI IRI?

Kar ka taba cewa sai ka sami komai dari bisa dari ko ka dauki mataki, ka dubi kanka ka gani, ba komai kake yinsa yadda kake so ba, wani sa'in da kanka za ka gane ba daidai kake tafiya ba bayan ka gajiyar da kanka, akwai wanda ya fara sana'a ko shekara bai yi ba ya ce ya ga kamar ba zai kai labari ba sai ya canja, kafin shekaru biyar ya yi sana'o'i kusan takwas, cikinsu ba ko guda daya qwaqqwara, na ce ya yi gaggawa, ko kogi da kake ganinsa cike da ruwa da yayyafi ya taru.
.
Banda wannan ma mutum ya leqa irin rijiyoyimmu na dauri wadanda aka yi musu tsarin kwakware zai ga cewa igiyar da ake jan ruwan a hankali ta ci kututturen ta raba shi biyu, har ta kai ga qarfen, shi ma ta yi masa illa tana qoqarin raba shi biyun, kai ma ka san ba aikin kwana daya ne ko biyu ba, yau da kullum kenan, mutum bai gaza ba idan ya zabi aikin da yake ganin zai iya yi a hankali, har ya kai ga inda yake so, in ma bai kammala ba ne ya yi qoqari ya sami matsaya, duk lokacin da ya dawo dorawa kawai zai yi daga inda ya tsaya, ba komawa baya zai yi ba.
.
Muna maganar cin nasara ne a duk bangarori na rayuwa, wata rana wani bawan Allah ya sami matsala da matarsa a gidan haya, sai ya yi qoqarin sakin matar, har ya ce mata ta tafi gidansu zai zo ya same ta, to Allah ya sa maigidan bai riga ya fita ba, matarsa ta gaya masa cewa mai haya a gidansu fa yana qoqarin sakin matarsa a kan kaza da kaza, sai maigidan ya kira shi dakinsa ya tambaye shi ko ya san ranar da ya yi aure? Yaron ya amsa cewa bai sani ba, sai ya ce masa "Shekara kaza kenan tun baka yi wayau ba, matarka ba ta wuce sa'ar diyata ta 3 ba, amma wallahi har yanzu fama nake da ita".
.
Ya ce "To ka taba jin na ce zan sake ta?" Yaron ya girgiza kai wato a'a, ya ce "To haka kowa ka gani yana zaune lafiya da matarsa haquri ya fi ka, ba wai tsabar zaman lafiya ne ya kawo haka ba, in bai yi haquri ba a qarshe sakinta zai yi, ya koma ya sake auro wata macen, sai ka ji ana yi wa mutum lissafin yawan matan da ya saka, wani mai gidan hayan ko yaushe yana cikin korar mazauna gidansa ne, haka wasu masu wuraren sana'a, yau in ka ga wannan gobe ka ga wani daban, wai yaran ba su da kyawawan dabi'u, wani kuma mota ce a gabansa, da wahala ya shekara da mota guda, kar ka yi zaton duk in ya rabu da motar zai kawo wace ta fi ta baya ne, wani sa'in gwara jiya da yau.
.
Wanda ya fi ban takaici ma qananan yara 'yan makaranta, yau ka gansu a wannan makarantar gobe a wata, a kullum cikin kai kuka ne, yaran sun kasa samun makaranta daya da za su yi karatu, ba wai yara ba hatta manyan, zan ba ka misali: Wata rana ina zaune a aji sai ga wata mata ta zo koyon Larabci take ce min ta shiga makarantu da dama, wasu da ta lissafo sun fi qarfin makarantarmu, saboda sanin malaman da suke koyarwa a ciki, amma na karbe ta duk da haka, sai ya kasance ba kullum take zuwa ba, in ta zo wannan makon qarshe wani makon za ta gaya maka cewa tana da sha'ani a wani qauyen, wata qila ma ba za ka gan ta ba samsam sai bayan mako biyu, ta ya mutum zai iya harshen bayan bai mai da hankali ya koya ba?
.
Can sai na ji wata na ba da labari wai wannan matar na surutu a wani wuri tana cewa ba wani bambanci tsakanimmu da saura, ta ce ga shi ta hada shekara ko kyakkyawar jumula da Larabci ba ta iya hadawa ba, amma kuma ba ta sheda musu cewa matsalar daga wurinta take ba, galibin matsalolinmu da za mu yi haquri mu bi tsari da komai ya yi kyau, na ga yarinyar da aka maimaita mata aji, amma uwarta ta saba gyale ta zo wurin malamar ajin ta gaya mata cewa diyarta na da qoqari ba wani dalilin da zai sa a koma da ita baya, duk bayanin da malamar ta so ta yi mata ta qi fahimta, haka dole aka kai yarinyar gaba kuma ba abinda take fahimta, uwarta ta ja mata.
.
Wani abokin karatuna da muke daki guda a wata qasa ya gano cewa yarinyar da aka damqa masa a hannunsa amana ba ta kwana a gida, kullum tana wurin samari, karatun ma ta bari ko an kore ta, haka ya kira ubanta ya gaya masa gaskiyar abinda yake faruwa, lokacin da uban ya gaya wa mahaifiyar a nan cibi ya zama qari, ta kira abokin karatun nawa ta wanke shi tas wai ya yi wa diyarta sharri, a qarshe ma ta zo qasar ta ce ya cire hannunsa a kan diyarta kar ya qara sanya baki a kan abinda ba a saka shi ba, anan kam ba ta taimaki diyarya ba.
.
Duk irin wadannan abubuwa in za a duba su da idon basira sai ka ga an yi aiki da rashin lissafi wurin neman nasara, kamar maza ne tare da iyalinsu, ga su mazaje ne amma ba mazakuta, kamar dai yadda matan suke fadi, sai dai ka ji ana tambayarsu "Har ka zo ne" shi kuma ya bata rai, in ya ji abin ya yi yawa ya fara neman maganin mazakuta, a maimakon ya ga likita, da yawan maza ba su da qarfi a kan qaramar cutar da za a iya magance ta, wallahi wasu amosani ne ya riqe mararsu, ko mabubbugar maniyyinsu, in an ba su shawarar su ga likita don ba sa jin zafi sai su ce maka su lafiyarsu lau, bayan ba lafiyar, shi ma wannan mummunan daukar mataki ne.

*Alhamdulillah*

Ga masu son cikakken rubutun a Dunkule cikin tsarin PDF sai a Dan dakacemu zuwa wani Dan lokaci Nan gaba.

Rubutawa :- Baban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

Ga masu sha'awar shiga miftahul ilmi a WhatsApp sai su Aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar mu 07036073248

Share:

HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 34


*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA // 34*
.
BAMBANCIN HANZARI DA GAGGAWA
Hanzari yana nufin ka qara saurin tafiyarka ne don ka isa zuwa ga nasara a daidai lokacin da ake buqatarka, gaggawa kuwa na nufin ka yi saurin aikata abu tun lokacin aikin bai yi ba, kenan hanzari ake buqata ga mai son cin nasara ba gaggawa ba, domin abinda ake so shi ne mutum ya iya samun abinda yake buqata da surar da yake buqata din, mun taba zuwa tambayar wani karatu na NCE sai aka ce mana akwai "regular" shekara 3, part time shekara 4 sai kuma long vacation shekara biyar, in mutum zai iya sai ya dauki ta shekara 3 don ya yi hanzari ya gama, in ba zai iya ba kuma ya dauka to ya yi gaggawa kenan.
.
Duk wata sana'a ko aiki da mutum zai kama ya tabbatar hanzari zai yi ba gaggawaba, wata mata da aka kawo mata kishiya sai ta fara nuna wa kishiyar cewa ita keda mijin, tana saka ta ayyuka daban-daban, har amaryar ta goge idanunta ta ce ita ba baiwa ba ce, daga ranar ta dena yin komai, har da wanda ya dace ta yi din ma, ta ce matsayinsu guda ne, na ce gaskiya uwargidan ma ta yi gaggawa, da ta yi haquri ta janyo yarinyar a jiki, ta nuna mata abinda ya dace, koda an gaya wa amaryar qarya da gaskiya in ba ta ga abinda ake gaya mata ba za ta sauko ta yi abinda ya dace, ba abinda mutum zai bi a hankali sai ya ga ribarsa ko meye kuwa.
.
Na ga wani mai aski yana ta fada, da yake rigimar ba tawa ba ce sai na ja bakina, wai yaron da ya zo koyon aiki ne ya tsaya sai an riqa raba kudin da ya samu kashi biyu ana biyansa, alhali ogan yana ganin yaron ne ma zai riqa biyan koya masa da ake yi, ni dai ban sa baki ba, amma na san mai koyon aiki a wasu wuraren shi ne ma yake biya ba shi ake biya ba, kamar dai yaron ya yi gaggawa, tunda ba a ce ya biya ba bai dace ya ce a biya shi ba, a qarshe dai sun rabu, ina da tabbacin cewa indai yaron zai ci gaba da haka ko ina ya je irin wannan rabuwar za a yi.
.
Wadansu sun shirya yin wani kamfani sai suja tara kudin farko a hannun daya daga cikinsu, kusan shi ake so ma ya riqa ajiye kudin, a qarshe dai wannan kudin bai fito ba, sai a albashinsa aka riqa cirewa a hankali, kuma an amshe tarin daga hannunsa, saboda bayyanar rashin gaskiya qiri-qiri, na ce ya yi gaggawa ne, da ya yi haquri akwai wasu kudi na masamman da ake bai wa duk mai tarin kudi, da ya rabauta da shi, wanda ya fi ba ni mamaki shi ne wanda ya je neman auren wata yarinya, an ba shi ita kuma an saka masa rana, sai da ya rage saura 'yan kwanaki kadan sai ta yi maganar kayan daki ya ce yana da wani qwararren kafinta.
.
Ashe gogan naka ya bi ta kan kudin ne, auren da bai dauru ba kenan, sai gashi ana ta wasan kurar boyo tsakaninsa da amaryar, gaskiya ya yi gaggawa, da ya bari ya aure ta tukun, komai nata inda soyayya nasa ne, gajin haquri ne, wata kuma maigidanta ne ya auro qawarta ba tare da saninta ba, ya ce in ta sani za ta iya dagula lamarin, a taqaice dai ba ta sani din ba sai bayan an daura, nan fa uwargidan ta tada bala'i har ya kai ga ta bar wa amaryar mijin, da dakinta da ma yaran da ta haifa, saboda kishi, na ce ta yi gaggawa, da za ta bi a hankali da ta riqe kayanta gaba daya.
.
Akan yi gwaji ne don tabbatar da ko mutum zai yi gaggawa, duk da cewa ina tababar maganar gwaji a neman aure, wasu matan sukan yi asarar miji na gari a dalilin gwaji, na tabbata ba shi ne hanya ta qwarai wurin zabin miji na gari ba, don da shi din ne da Annabi SAW ya zabar mana, amma bincike shari'a ta tabbatar, in dai namiji ne to mace ta bar shi da kininsa kawai, maqwabta abokan aiki, 'yan uwa duk za su iya taimakawa wurin bincike, kuma su din ne za su kawo abinda ya dace.
.
Wani dan abu ne ya shiga tsakaninsu ita kuma ta nemi saki a matsayinta na mace, gaulan naka ya ba ta duk da cewa namiji ne, a kullum suna tare, bayan ba aure a tsakaninsu, sai ya zamanto duk bayan 'yan kwana biyu sai ta dauko yaro ta zo gidansa wai ta kawo masa dansa ya gani, amma sai su kwashe sa'o'i biyu zuwa uku bai gama ganin yaron ba, na ce sun yi gaggawa, da sun yi haquri za su fahimci junansu, haka dai suka ci gaba har wanda tsautsayi ya fada masa ya aure ta, ba ta jima ta fice abinta ta koma inda ta fito.
.
Wasu kuma duk an yanke musu hukunci mai tsanani akan kashe wani da suke zargin cewa ya kashe musu qani, alal aqalla da sun danqa shi a hannun hukuma, a tunanina ba mutumin da zai wuce kwanakin da Allah SW ya diba masa, matuqar dai za su iya kashe shi a wannan lokacin to sun yi gaggawa, domin ko ba su tabe shi ba mutuwa zai yi, akwai abubawa da dama da muke rasawa a dalilin gaggawa irin wannan, ba laifi ba ne su yi hanzarin miqa maganar koto kafin bincike ya kai gare shi, amma kashe shi kam gaggawa ne

Mu kasance a rubutu na gaba da yardar Allah...

Rubutawa :- Baban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

→Ga masu sha'awar shiga miftahul ilmi a WhatsApp sai su Aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar mu 07036073248
Share:

HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 32


*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA // 32*
.
MUTANE KALA BIYU NE
Dangane da aiki ko sana'a mutane sun kasu zuwa gida biyu:-
a) Mai jin dadin aikinsa: Wannan kam yana son aikinsa kuma yana jin dadin ganin abinda yake yi, kullum alla-alla yake yi gari ya waye ya kama hanya, don ko kamin ya bar aikin ya dawo gida sai da ya tabbatar ya kammala aikin yau gaba daya, kuma ya shirya abinda zai taras gobe, yakan bar aikin ne cikin zaquwar dawowa ya taras da shi, wannan ya sa wani zai gama da na yau har ya dan rage na gobe ma yadda in ya zo aikin zai yi masa sauqi.
.
Irin wadannan mutanen ba su da wani tunani na rabuwa da aikin don suna jin dadinsa, koda kuwa wurin aikin nasu ne, ko nawani ne sukan yi ne a biya su, wani ma sai ka rantse da Allah wurin nasa ne saboda qaunar aikin da yake yi, na ga wani Basakkwace da ya riqe wa wani Bakano shago da amana, na yi zaton yaron wancan ne, ashe bariki ce kawai ta hada su, har dai Bakanonnan ya yi qarfi ya sayi wani shagon kusa da wannan ya maqare shi da kaya, koda ya tashi tarewa sai ya ce ya bar wa yaronnan nasa tsohon shi ya koma sabon, lamarin ya ba ni sha'awa matuqa, bai yi haka ba sai don ganin gaskiya da amanar yaron da kuma jajurcewarsa, na ga wuraren aiki da dama amma ban ga rabuwar da ta ba ni sha'awa kamar wannan ba.
.
Wanda duk yake qaunar aikinsa za ka taras kullum neman ci-gaban aikin yake yi, yana ta nemo hikima ta kowani bangare yadda zai habbaka aikin nasa, ko ya sauwaqe shi, ko ya inganta shi, ko kuma ya qawata shi ga idon jama'a, tunaninsa a kullum shi ne ci gaba, bai damu da cewa aikin nasa ne ko na ubangidansa ba, irin wannan ne sai ka ga a qarshe ubangidan nasa ya kyautata masa sanadiyyar aikinsa, na san wani da ya je koyon aiki a wurin wani abokina ko shekara cikakka bai yi ba har ya fara tunani da fadin cewa ogan nasa bai kai shi sanin kan aikin ba, wannan a ganina butulci ne da rashin sanin ya kamata, qila kuma zaman ba zai wani dade sosai ba, saboda raini ya fara shigowa tsakiya, duk inda aka fara samun irin wannan to kuwa akwai matsala.
.
b) Yana aikin ba don yana so ba: Wannan za ka taras don dole yake yi, irin bai sami wanda ya fi shi ba, ko an matsa masa ne a gida, ko kuma bai son zaman banza dole ya fara, ko shi dan na kashewa kawai yake nema bai dauke shi a matsayin sana'a ba, a irin wannan yana yi ba dole ne ya je aiki ba, a kullum yana neman dan dalili ne wanda zai maqale da shi ya qi zuwa aikin, ko in ya je din ya dawo gida ko ya wuce yawonsa, ko bai yi aikin komai ba za ka taras da shi a gajiye yake, in damina ta zo ko hadari ya gani ba zai fita aiki ba to bare a ce an dan yi yayyafi, na ga wanda ya qi zuwa aiki da aka tambaye shi dalili sai ya ce wai mai gadin abokinsa ne ya karye kuma abokin ya yi tafiya shi ne ya je ya dan zauna masa.
.
Shi abokin ya tafi aiki, koda shi ne ya karye bai da 'yan uwa ne da za su zauna masa bare kuma mai gadinsa? Abin gwanin ban mamaki, irin wadannan mutanen ba yadda za a yi su yi tunanin bunqasa aikin bare har su yi tunanin kawo ci-gabansa, za ka iya kwatanta dalibai biyu da suka je yi wa qasa hidima a wani kamfani, daya daga cikinsu ya dage yana ta aiki tuquru, a cewarsa yana qoqarin sanin madafan aiki ne, wanda tabbas haka abin yake, na biyun kuwa yana ganin shi yi wa qasa hidima yake, bai ga dalilin da zai riqa qarar da qarfinsa a kan wani qaton banza ba, yau in ya zo aiki gobe ya qi, wani lokacin ma ya ce bai da lafiya ya yi tafiyarsa sai bayan mako guda ya dawo, a qarshe kamfanin suka dauki wancan aiki yana kammala hidimarsa.
.
Shi ma dayan ya so a ce an dauke shi don kuwa ya iya aikin kamar wancan, amma ana qimanta mutum ne da abinda yake aiwatarwa, wanda bai sha'awar aiki in ka je wurin za ka gan sa da wayarsa yana lallatsawa, ko wasa da yara ko kallon talabijin, bai da wani lokaci da zai bata don ganin ci-gaban wuri, wani ma bai damu da a kore shi ba, kamar wani mai aski da na ga yana ba yaronsa kashi, wai ya bude shagon ya je yana yi wa maqwanmbcinsa mai nama aiki don a ba shi kudin da bai wuce Naira 50 ba, ubangidan nasa ya zane shi ya ce "Duk tsiyar da za ka yi wallahi ba zan kore ka ba, kuma sai ka yi aikinnan" ya kwaso ashar dinsa ya watsa, wai ashe uwarsa ta kawo shi shi kuma ya fi son inda zai yi aiki ne a biya shi wahalarsa ba wai wurin wani koyon sana'a ba, ka ga wannan da wahala ya yi wani abin azo a gani.
.
Ina ganin akwai bambanci tsakanin qwadugo da sana'a, duka aiki ne kowa kuma da hanyar cin abincinsa, amma galibi 'yan qwadugo sukan fita ne ba tare da sanin ina za su ko wani irin aiki za su yi ba, kamar leburorin da na sani, ma'aikatan gini ne, amma ba qananan ayyuka da ba su iya ba, su ne gini, fenti, ginan rami kamar masai da rijiya, sanya wuta a daki, tabbatar da masai na korawa da ruwa da sauransu, wata rana a samu da yawa wata rana a rasa gaba daya, akan sami ranar da babu ma gaba daya, irin wannan za ka taras hatta aikin akwai yanayin lokacin da aka fi samu, akwai lokacin da ba a samun komai ma, yadda mutum ya fita haka zai dawo hannu Rabbana.
.
Amma in ka koyi aiki mai wuri tabbatacce kamar fawa, qira, shago, kanikanci da sauransu kana da matabbata, in kai mai himma ne cikin dan lokaci qarami mutum zai yi nasa, sai ka ga ya zama wani abu, a qarshe sai dai shi ma ya sami yaron da zai zauna masa, in ya yi dace shi ma ya zama babba kenan, a lokacin zai ga amfanin qoqarin da ya yi, in ya sami yaro mai qwazo tabbas zai sami cikakken lokacin da zai huta, a wannan lokacin zai fara tunanin yanzu ya za a yi ya sake samun wani wurin ya zama yana wuri biyu tunda wannan ya sami mai riqe masa? Amfanin dagewa kenan a aiki.

Mu kasance a rubutu na gaba 

Rubutawa :- Baban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

Ku Danna link din dake Qasa don kasancewa damu a shafin telegram👇
https://t.me/miftahul_ilmi

→Ga masu sha'awar shiga miftahul ilmi a WhatsApp sai su shiga ta nan su aika da cikakken suna 👇
https://wa.me/2347036073248
Share:

HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 31


*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA // 31*
.
DUK ABU NAKA NAKA NE
Sakaci da rashin kulawa ko rashin sani su ne manyan abubuwan dake sanyawa mu rasa damar dake hannunmu ko mu bar ta wani ya qwace mana, da farko fara gina kanka tukun, yi qoqari ka sami ginshiqi mai qarfin gaske, kar ka yarda ka yi abu a kan jahilci, in kamfanin gyaran mashin za ka gina binciki kanka tukun, shin kana da kudin da zai ba ka damar aiwatar da wannan aikin? In ba ka da shi to ya za a yi ka samu? Ilimin aikin dai yana kanka kudin aiwatarwan ne ba bu.
.
Da farko tsaya ka karanci sana'ar da za ka fara, shiga ciki a matsayinka na mai koyo, yi qoqari ka san komai nata, kayan aiki, abubuwan da ake buqata, masu kyau da jabu, kudadensu, dadewarsu, bambance-bambancen dake tsakanin kamfanoni, lokutan da suka fi dacewa da inda ya kamata a yi saboda yawan mabuqata, ya zamanto dai a matsayinka na mai koyon aiki ba abinda ba ka sani ba, albashi in ka zo daukar ma'aikata da za su yi maka bayani kan kayan aiki da sauransu ba abinda ba ka sani ba, kuma ba wanda zai yi qoqarin cutarka ko bata maka aiki.
.
Na koyar a wata makaranta ta Misho, inda na ga hedimastan ko yaushe yana zagawa azuzuwa yana ganin darussan da ake koyarwa, da lokutan da ake koyarwan, wata rana ya amshi wani aji ya koyar ko ya yi musu tambayoyi don ganin shin abinda suke buqata malaman suke ba su kokuwa? Na yi mamakin qwaqwalwar mutumin yadda ya san komai kai har da sunan daliban, ba abinda malami zai fada wanda bai sani ba, sai na tambaya, ya aka yi ya san duk wadannan abubuwan? Sai aka ce ya koyar na tsawon shekaru da dama kafin ya kai ga riqe makarantar a hannunsa, ashe asali ma ba dan qasa ba ne, amma yana tsari mai qarfin gaske, koyarwar ta taimake shi sanin komai.
.
Idan ka gama sanin komai ya za a yi wani mutum ya zo maka daga waje ya mallake ka? Ba zai yuwu ba, na ga wata makaranta da wani ya so gudanar da ita, ya tanaji komai amma bai da kudi, sai suka hada hannu da wani mai abin hannunsa, a qarshe aka fara rigimar shin wa ma yake da makarantar tukun? Wanda ya fi qarfinka sai ya dauki hannunka ya mare ka da shi, kusan abinda aka yi kenan, mutumin farko da a ce yana da kudinsa sai ya ci gaba da gudanar da lamuransa shi kadai ba zai jawo kowa ba.
.
Duk abinda za ka yi in dai kai da qarfinka za ka yi aiki wani da dukiyarsa kar ka yarda a ce komai shi zai yi, wani zai ce kar ka damu, ko nawa kake so ni zan dauki nauyi, in ka yarda da wannan to ko shakka babu ka sayi wuqar yanka kanka, sanya taka dukiyar kuma ka yi aiki da qarfinka, ba yadda zai dawo wata rana ya yi farfagandar cewa komai nasa ne don shi ya yi, kai ma ka sanya kudinka, ka yi aiki da qwaqwalwarka sannan ka ba da lokacinka daidai gwargwado, abubuwan dake faruwa a duniya yanzu yadda ka san ba lahira a gaban mutane.
.
Akwai wata makaranta da wani ya so gudanarwa, shi ya ke da wuri a hannunsa, sai ya jawo wani babban malami wanda ya yarda da shi sosai, ya danqa komai a hannunsa, sai mutumin ya yi aiki da wannan damar ya maida mai wurin yaronsa ya yi ta yi masa bauta na tsawon shekaru, sai dai ya dan gutsuro a wata ya miqa masa, ba wanda ya san abinda ake ciki, a qarshe da yake mai wurin shi ma ba nasa ne na kansa ba sai mutumin ya kori shi wai bai gamsu da irin gudummuwar da yake badawa ba, idan kana da rai ba abinda ba za ka ji ba, wadannan su ne abubuwan da ni na gani da idona Allah ne kadai ya san abubuwan dake faruwa a wasu wuraren.
.
Da a ce mutuminnan ya koyo aikin, ya fara da kansa bai janyo kowa ba, shi yake gudanar da komai ba wanda zai zo rana tsaka ya mamaye masa wuri, balle ya tuhume shi da rashin gaskiya har a qarshe ya ce zai kore shi, duk sana'ar da za ka shiga yi qoqari ka san gabanta da bayanta yadda ba wani abinda zai boyu maka, kana da cikakken 'yanci, kana da duk wata dama da za ka dauki matakin da kake so, ba tare da wani ya yi aiki da qwaqwalwarka ya cuce ka ba, in kana gaya wa kanka cewa ba za ka iya kaza ba ina tabbatar maka daga lojacin da wani ya karbe maka wannan damar sai yadda ya yi da kai.
.
Za a kai yadda ba za ka iya zartar da komai ba sai abinda ya so, shi kuma abinda ya ce ka yi ba ka da makawa, ko kafin ka farga ya yi maka babbar illa, don duk abinda zai amfane ka ba zai yarda da shi ba, duk kuma wata hanya da za ka bi wace za ta nuna maka hanyar daidai ba zai yarda ka san ta ba, taka ta qare kenan, ka bude idanunka, ma'ana duk lokacin da ka gano cewa nasararka tana kan dakinka ne to ka gina matakalanka da kanka, ka hau da kanka ka ciro, ka sani in ka tura wani ya ciro maka to shi ma fa yana so.

Mu kasance a rubutu na gaba 

Rubutawa :- Baban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

Ku Danna link din dake Qasa don kasancewa damu a shafin telegram👇
https://t.me/miftahul_ilmi

→Ga masu sha'awar shiga miftahul ilmi a WhatsApp sai su shiga ta nan su aika da cikakken suna 👇
https://wa.me/2347036073248
Share:

HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 30

*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*


 ```// 30```
.
KANA SO?

Da yawammu inda muke samun matsala kenan, mutum ransa bai kwanta da abuba sabo saboda matsalar da yake hangowa amma saboda rashin samun wani, ko shawarar da wasu suke ba shi ko tilastawar uwaye sai ka ga ya dauka, a qarshe da wahala ka ga mutum ya ci nasarar abinda yake nema, ko shawara mutum zai ba ka ya dace a ce ya san abin sosai, in ba haka ba da matsala, ba yadda za a yi mutum dan boko futuk ba abinda ya sani game da addini a ce shi ne zai riqa fada muku halas da haram, da wahala ku ci nasara.
.
A addinance ma na ga wani hadisi na Musa bn Talha da ya jiwo daga babansa cewa shi da Annabi SAW sun wuce wasu mutane a kan dabinai ya tambaya cewa "Me wadannan suke yi?" Suka ce "Aure suke musu, suna hada maza da mata" ya ce "Bana jin wannan zai amfanar" sai suka gaya wa manoman, su kuwa suka dena, da aka gaya wa Annabi SAW abinda suka yi sai ya ce "In dai hakan zai amfanar su yi mana, ni fa kintatowa na yi, kar ku ce za ku kama ni da abinda na kintata, in dai na gaya muku wani abu na ce daga Allah ne to ku yi kawai, don ba zan taba yi wa Allah qarya ba, Muslim (2361)
.
Akwai abubuwan karatu a wannan hadisin, in mutum ya gaya maka abu kuma ka san bai da masaniya a kai in ka dauka ka ga dama ne, a addinance ga dai abinda Annabi SAW ya fadanan, a zamanance kuma bai dace ba ka ba da damar da za a cilla ka wani wurin, ko matsalolin da kake gani ana samu a aure ana ba wa wanda bai san abinda ke faruwa tsakanin ma'aurata ne ba damar ya tofa albarkacin bakinsa sai ka ga ya wargaza komai, qila mutuminnan yana yi mata alkhairai masu yawa, wadanda sun fi matsalolin nasa, amma saboda rigimar da ta rincabe tsakanin matar da shi in ta zo ba za ta fadi alkhairansa ba, masu ji kuma sai su zata ba wani aikhairi ne sai su ba da munanan shawarwari a qarshe a kasa cin nasarar abinda ake so a auren.
.
Na ga wata mata da aka dinga kai-komo a kotu kan alaqarta da mijin, uwayenta suka tsaya kai-da-fata sai an raba auren, saboda abinda 'yarsu ta gaya musu, alqali ya ba da biko ba a daidaita ba, a qarshe mijin ya ce ya bi, ya bi, amma ya kasa cin nasara don haka a yi mata yadda take so, ta yi wub ta ce wallahi tana son mijinta za ta koma, daga kotun ta bi mijin, ba ta koma gida ba bare su ce sai dai ta koma dakinta ita kadai, na ga wani mutum da wasu bayin Allah suka jawo shi don ya ci arziqi, da yake yana da masifaffen wayau sai ya yi qoqari ya maida kamfanin nasa, masu shi kuma suka koma yi masa aiki, sai da aka kwashe shekara 8 a cikin wannan halin, a qarshe ya qirqiro matsala ya kore su.
.
Wallahi da idona na gani ba labari aka ba ni ba bare na yi zaton gaskiya ne ko qarya, ya kwashe labari, gaskiya da qarya, ya kai wa wadanda ba su sani ba, su kuma suka ba shi shawara gwargwadon yadda suka ji ba tare da sun san haqiqanin abinda yake faruwa ba, gogan naka ya kai su qara kotu, sai ga reshe yana neman ya juya da mujiya, ba arziqi ya janye qarar nan take ya fara neman sulhu, a taqaice dai kamfanin ya balbalce, duk lokacin da za ka nemi shawara yi qoqari ka yi da wanda ya san abinda kake ciki dari bisa dari, in ba haka ba kuwa to za a yi ba uwa ba riba, in ka dauki shawararsa ka zo ba ka yi nasara ba cikin sauqi zai ce maka "Ai ban san haka ne ba, don Allah ka yi haquri" shi kam a wurinsa an gama kenan.
.
Akwai wani da ya gama sakandare ta boko sai ya yi shawarar sake wata ta Islamiyya, haka abokansa suka riqa cewa "Wannan ai demotion ne, ya za a yi mutum ya shekara 12 a sakandare?" Mutuminnan ya ce ya ji ya gani, ya nemi taimakon Allah ya duqufa, sai ga shi ya kammala, ya yi Diploma ya fara digiri, ya yi masters, masu maganar ba su kai inda ya kai ba, sai cewa suke "Ai wallahi ba mu san hakan ne ya fi ba, ai mu ma da mun bi ka mun yi tare" da ya biye tasu da shikenan ba-wan-ba-wan karatun dan kama, na yarda da shawara amma ga wanda ya san abu ciki da bai, sannan in ka san karatu bai dace da kai ba, ko sana'a ko wani aiki kar ka bi surutun jama'a bar shi kawai.
.
Ko aure ne ka ga ba ka so, ko ba a son ka haqura kawai, ba wani zancen kunya da qarairayi marasa amfani, kai ne za ka zauna da ita, samun zaman lafiya da fahimtar juna shi ne cin nasarar aure, in karatu kake so, ka ga wanda ranka ya natsu da shi riqe shi, kuma shi din ne za ka iya kar ka bi shawarwarin wani, zai fada maka ne kawai ya barka da shi ka yi ta taburzawa, in har ba ka sha'awar zama lauya ko alqali to tun farko kar ka karanta lauyanci ko alqalanci, in ba haka ba karatun ba zai yi amfani ba, sai mutum ya ce bai sha'awar koyarwa a ransa ko kadan, amma ka ga ya karanta Education.
.
.
Na ga mutum biyu wadanda suka koyi gyaran wuta da wuyarin don su sami na cin abinci, da suka so qaro karatu sai suka fada Electrical Engineering, abin ya ba ni sha'awa, ko yaranka ne za su yi karatu lura da inda suka fi mai da hankali ka ba su shawara, sai ka ga an yi nasara a karatun, na ga wani uba da yake son diyarsa ta karanta likitanci, amma ta ce ita sam ba za ta iya ba, ya damu matuqa, na ce idan ya matsa mata ba za ta yi abin kirki ba tunda tun asali ba ta so, na ga wani uba wanda kullum sai ya jibgi dansa a kan sana'arsa amma dan ya qi yi masa biyayya, shi bai son sana'ar uban, da zan iya ba da shawara da na ce uban ya bar shi ya zabi sana'ar da yake so.

Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```

Share:

HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 29


.*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*


 ```// 29```

MA'AIKACI DA WAYOYINSA

Wasu ayyukan sam ba sa yuwuwa sai da wayar, kenan ita ce jigon sana'ar gaba daya, wani sa'in za ka taras ba a buqatar wayar dole ka haqura ka ajiye ta matuqar kana son sana'arka ta ci gaba, da yawanmu ba mu san haka ba, in kai ne babba a wuri kuma kana da yara masu taimaka maka ba matsala ka daga wayarka kuma ka yi maganarka yadda kake so, in ba ka son yaran su riqa yin abinda kake yi to su sani fa cewa kai kadai kake da wannan hurumin, don kar su gan ka kana yi su ma su kwaikwaye ka, wani abokina ya taba gaya min cewa masinjansa kan shigo masa ofis ya yi ta waya yana dararrakunsa ya manta cewa a ofishin na gaba da shi yake.
.
Na zauna da wasu masu sana'a wadanda kiransu aiki ake yi daga wurare, in sun dawo wani ya sake kiransu, wani sa'in suna kan wani aikin za a kira su, kuskuren dake faruwa anan sai mutum ya kama waya ya kashe wai an dame shi, sai a yi ta kira ana samunta a kulle, har mutum ya yi shawarar canja abokin sana'a, wani kuma ba kashewar zai yi ba amma ba zai daga ba, kuma abokin kasuwancinsa ne sun dade suna tare, sai ya duba ya gani can ya yi tsaki ya jefa wayar wani wurin, a maimakon ya daga ya gaya masa gaskiya cikin sauqi "Wane na fito aiki ina wuri kaza tun lokaci kaza, qila na gama zuwa qarfe kaza, in na gama ban gaji ba zan kira ka" shikenan cikin sauqi.
.
Shi ya san matsalarka kuma zai yi maka hanzari, kwanaki wani ke ba mu labarin cewa mai yi musu aikin kafinta ya karbi qaramin aikinsu bai gama da wuri ba, suka ce sun yi masa hanzari saboda salla ta matso qila ya shiga wata saugar ne, sai aka sami wani kwantaragi da kudi mai tsoka aka yi ta kiransa ya qi daga wayar, wai ya sani cewa maganar baya za a yi masa, a qarshe dai ya yi asarar wannan aikin, ba yadda za ka ce ka san abinda mutum zai gaya maka, ko maganar zai yi maka qila akwai wata sabuwa.
.
Akan gaza kaiwa ga yin nasara a kan rashin sanin yadda za a tafiyar da waya, mutum ne zai nemi aiki ya kai cv dinsa wani wuri mai dauke da lambarsa, amma in aka buqace shi sai a sami wayar a kulle, wasu wuraren ba su da lokacin kiran mutum sai cikin dare, kai kuma za ka yi barci ka kama waya ka kulle, ina laifi ka sanya ta yi tsit yadda ko an kira ka qarar ba za ta dame ka ba, in ka shi ka ga kiran? An taba ba ni kudi a wata makaranta ta share fagen jami'a aka ce na gayyato wadanda suka sami nasarar tantancewa don su shigo su zana jarabawar da za ta ba su damar tsallakawa cikin makarantar, ashe a cikinsu akwai wasu mutane masu dabi'ar in ba su san lamba ba ba za su daga ba.
.
Na yi ta kiran wani bawan Allah amma ya qi dagawa, lokacin da na gama na juyo kansa na kira shi, da dagawarsa sai ya ce "Wrong number" bai ma ko ji muryata ba, har na haqura da shi saboda fusatar da na yi, sai na sake tunani, na san bai san ni ba bare na ce raini ne, gidadanci ne kawai irin na mutanemmu, ka ba da lambarka a kira ka bisa wani abinda kake so, ko wannan ya isa ka dan saurara ko ka canja dokarka, tunda ba ta Allah ba ce, na dan wani lokaci, albashi in ka sami abinda kake so sai ka dawo da ita, na sake kiransa amma sai ya dode ni, sai da na rubuta wasiqa na tura masa cewa daga wuri kaza ne ake magana kan abinda yake nema.
.
Ko minti daya ba a yi ba sai ga shi ya bugo yana ba da haquri da wasu hujjoji na banza, sai na ce masa ya yi haquri mun raina hankalinsa mun ba wani, hankalinsa ya yi matuqar tashi ya biyo baya a guje, sai da na gurza shi sosai don ya goge kafin na ce kar ya qara irin wannan sakacin a rayuwarsa, wanda yake neman aiki kashe waya ba tasa ba ce, na taba neman wani abu, amma na kasa canja wayata da na yi niyyar saye, duk tsoron kar a kira ni a dan mintocin da ba su kai biyu ba ba a same ni ba, na ga wata mata da za ta canja waya sai da ta zo wurimmu ta kawo kuka kar mu kira ta ba mu same ta ba, in mutum ba zai iya daga waya ba to ya saka ta ta yi tsit, yadda in ya waiwaye ta zai ga duk masu kiransa.
.
Maganin bera da na siya a wurin wani Inyamuri sai da ya ba ni lambar wayarsa ya ce bai zama wuri daya amma in na ji dadin maganin to na kira shi kawai, duk inda yake zai waigo ni ya kawo min, wadannan sun san kan sana'a, mutanemmu da dama suna yin sana'ar da zai yuwu a neme su, ana buqatar hidimarsu, amma abin haushi sai ka ji wai mutum bai da waya, wani yana da itan amma in za ka buga sau dubu ba za ka same shi ba, ga hanyar cin nasara ta wurin bunqasa sana'arsa amma abin haushi bai san yadda zai yi ba, akwai wani mai sayar da rake yakan zo masallaci gab da Magariba, ana buqatarsa sosai wani sa'in yakan yi salla a masallatan kewayen, duk buqatarsa da kake yi sai dai ka haqura ko ka ce wani wurin ba za ka same shi ba, bai da waya, in ma ya na kusa ba za ka hage shi ba gari ya yi duhu bai da haske.
.
Kamar masu sana'ar yawo irin wanzamai, masu tallar magunguna, kai harda ma'aikata kamar kafintoci, kanikawa, masu gyaran wuta duk ya kamata a ce suna aiki da waya, to bare masu hayar ababan hawa, hatta mahauta akan kira su su gyara wa mutum dabba in akwai sha'ani, bai dace ba a ce ka bar jama'a na ta jiranka kai kuma kana can kana ta waya da wasu, amma don ka saurari mutum na minti daya wannan na da matuqar mahimmanci, akwai mutanen da bai dace suna tsayuwa ga waya ba saboda yanayin sana'ar tasu, kamar dai direbobi, amma in suka sami wuri suka tsaya za su yi wayarsu yadda suke so ba tare da wata matsala ba.

Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Share:

HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 20

*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*


 ```// 20```

.
HANNU DAYA BAYA DAUKAR JINKA
Haka Bahaushe yake cewa, alokacin da ka so fara wata sana'a ko aiki naka na kanka ko kasuwanci dole za ka buqaci mutanen da za su taimaka maka wurin cika burinsu, misali wani tsohon ma'aikacin banki da ya yi wani qwarqwaryan shago, ya dora wani makusancinsa don ya tafiyar masa da shi, ya kawo duk abinda ake buqata masamman na'urannan ta bankin tafi da gidanka, wannan abu ne mai kyau matuqa tunda makusancinsa yana samu da shi, sai dai duk abinda da mutum zai tsara matuqar zai nemi taimakon wasu to ya tabbatar wadanda suka dace ne za a saka a wurin.
.
Taimakon na kusa da kai wajibi ne, akwai halin ma da za ka kawo shi kusa don ya riqa ba ka bayanin duk abubuwan dake faruwa, amma dagewa cewa naka ne kawai za ka sanya a wuri matsala ce babba wace za ta iya ruguza maka shiri, sai in ya cancanta da matsayin, wasu kan yi sha'awar sanya 'yan uwansu makusanta a wararen sana'a da kasuwanci alhali 'yan uwan ba su cancanci wurin ba, a qarshe sai ka ga an qare da nadama, kodai dan uwan ya aikata ma-sha-a, ko ya yi sama-da-fadi da dukiyar wasu ko handama da babakere, duka dai munanan abubuwa ne, ko dan uwanka yana da takarda ka tabbatar ya zauna a wasu wuraren dake da alaqa da aikin, ya naqalci komai, kuma yana da alqawari.
.
BIYAYYA
Alqqwari a aiki da tattali da tanadi koyonsa ake yi kamar yadda ake koyon aikin kansa, galibin masu kukan cewa sun dauko 'yan uwansu sun cuce su za ka taras ba wata horarwa ta masamman da suka samu kafin su shiga sana'ar, ba su koyi yadda za su yi ta'amuli da dukiyar wani ba ko kadan, abinda suka sani kawai yanzu za su shiga kudin dan uwansu, shi ya sa nan da nan sai ka ga abin Allah-wadai ya faru, a qarshe kuma su haramta musu ci gaba da ma'amalla da su har abada, su ce bare ya fi dan uwa, alhali su suka yi kuskure tun farko.
.
DAIDAI RUWA DAIDAI QURJI
A duk lokacin da ka ce kai da abin hannunka kawai za ka yi harka kana da matsala, amma kimanin shekara 3-4 da suka gabata na taba ganin wani malami yana bayanin cewa kar mutum ya taba karbar bashi a kan wata sana'a da zai fara, ya ririta abinda ke hannunsa kawai, na ga kuma wadanda suka yi masa raddi da cewa kashi 75 cikin dari na wadanda suka ci nasara ba da dukiyar hannunsu suka yi aiki ba, masamman masu manyan ma'aikatu da masana'antu, to dai duk abinda mutum zai yi kar ya taba yarda ya sha ta fi ciki, dole a ci bashi amma wanda za a iya biya ba wahala, kamar wanda za a gyara wuri a qara jari da makamantansu.
.
KULA DA MATAIMAKA
Duk lokacin da mutum yake ganin cewa shi fa zai rayu ko shi kadai ne kuma ba ya buqatar taimakon kowa to akwai matsala babba, amma abu mafi girma a ciki shi ne son kai, wato ya kasance mutum komai shi kadai yake so ya kwashe ba ruwansa da kowa, in kana da wurin sana'a kar ka yarda a ce kanka da iyalanka kadai ka sani, yi qoqari a ce hatta mai yi maka gadi yana da matsayi a wurinka, kuma kana ba kowa haqqinsa yadda ya dace, ko kwana daya mutum ya yi ba ka gan shi ba tambayi inda yake, za a gaya masa cewa ka tambayi halin da yake ciki, in bai da lafiya ne kuma ba za ka iya zuwa duba shi ba saboda wani zarafi yi qoqari ka kira shi a waya, in kana da dan wani abin hasafi ka yi masa, in ka matso kusa da ma'aikatanka ba za ka taba ganin abinda zai dame ka ba, mutum yana son alkhairi koda kuwa ba yawa.
.
IN GORA TA CIKA BA TA QARA
Haka Hausawa suke cewa, in ka ga mutum yana ji da kansa kuma yana nuna isa da fankama a wurin sana'arsa to bai shirya aikin sosai ba, matso kusa da ma'aikatanka ka janyo su jiki, komai ku riqa yi tare, za ka ga duk abinda ya taso sun iya samun qarfin gwiwar da za su tuntube ka ko ku tattauna tare, kar ka zama kamar dodo kowa na tsoron ya yi magana da kai, a irin wannan matsayin abubuwa da yawa za su yi ta faruwa ba ka sani ba, yanzu an fara fahimtar amfanin haka, akwai wani mai neman gwamna da mai neman dan majalisa da na gani, alla-alla suke yi su ji an yi rasuwa ko taron biki ko suna a duk yankinsu ka gan su a wurin, mafi yawancin tarurrukan da suke halarta ba gayyatarsu ake yi ba, amma suna so ne a gan su a yaba da qoqarinsu a qarshe a zabe su, dan majalisan ya ci, mai neman gwamnan ya fadi, dukansu biyun dai sun dena abubuwan da suka fara, na ce da sun sani su ci gaba, don gabar ta fi baya yawa.
.
MAGANIN MATSALA
Wasu fa ba su san yadda za su magance matsalolinsu ba samsam, idan mutum ya yi kuskure a wurin aiki sai maigidansa ya yi masa kaca-kaca a gaban jama'a, wani lokacin ma ya kore shi, na ji wanda yake iya bakin qoqarinsa wajen tsare hanyar cin abincinsa, amma da ya yi kuskure daya, haka maigidan ya zazzage shi kuma ya kore shi, ko aure mutum yake yin kuskure wajen gyara shi ko tantama ba na yi zai sami matsala wajen zama da mace, a shekarun baya na yi hira da wani tsoho wanda yake ce min ya yi aure so goma sha biyar, amma mata biyu na san shi da su, na ji matar da aka ce masu zaman haya a gidanta ba sa yin shekara sun gudu, saboda rashin iya ma'amalla, na ga wani mai sana'a duk wanda ya zo koyon aiki wurinsa sai ya gudu, bai iya ma'amalla da su ba.
.
Na ga malamin jami'an da ya yi hatsari dalibansa suke addu'ar Allah ya qarisa shi a asibiti, suka ce ina ma ya mutu tun daga wurin hatsarin, na ga wanda wani mutum ya jawo shi don su yi sana'a tare, amma ya munana ma'amallarsa, ya mayar da wurin nasa shi kadai, a qarshe ya sallami wanda ya kawo shi, ba a jima ba lamarin nasa balbalce, dole mu riqa kyautata alaqarmu da masu yi mana aiki ko masu aiki a qarqashimmu ko dalibammu matuqar muna son ganin ci gaba a rayuwarmu.

Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```

Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form