Showing posts with label Fadakarwa (Awareness). Show all posts
Showing posts with label Fadakarwa (Awareness). Show all posts

BIKIN VALENTINE: RANAR MASOYA KO RANAR MAGUZAWA?


BIKIN VALENTINE: RANAR MASOYA KO RANAR MAGUZAWA?

BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allaah mai girma da ɗaukaka. Tsira da amincin Allaah su ƙara tabbata ga Manzon Allahu, Annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallam, mutanen gidansa, sahabbansa da ma dukkan wanda ya biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

GABATARWA

Bikin Ranar Masoya, watau Valentine's Day a turance kenan kamar yadda ake kiransa, biki ne da akan yi shagalinsa a kowace ranar 14 ga watan Afrilu, ma'ana dai sau ɗaya ake yinsa a cikin shekara.

Ita dai wannan rana, rana ce wacce miliyoyin mutane daga dukkan sassan duniya suke murnar zagayowarta a kowace shekara. Duk da cewa an ɗauki wannan rana a matsayin ranar murnar tunawa da wani waliyyin kiristoci ne mai suna Valentinus, irin wannan rana a yau ta kasance ana alaƙanta ta ne da bikin soyayya, nishaɗi da kuma jin daɗi a mafi yawancin wurare a duniya. 

A irin wannan rana, masoya a ko'ina a faɗin duniya kan aikawa juna saƙonnin katuka, fulawoyi, kyaututtuka ko wasu abubuwa makamantan haka domin dasawa ko haɓaka alaƙarsu da juna. A ƙarƙashin haka, akan haɗu a bukukuwa da dama da akan tanada domin irin wannan biki a tsakanin samari da 'yan mata ko ma'aurata domin nunawa juna ƙauna, in da hakan ke kaiwa zuwa ga munanan kalamai waɗanda su kuma su ke kaiwa zuwa ga mummunan aiki. Allaah ya tsare mana Imaninmu. 

GA JERIN WASU ABUBUWAN DA A KE YI A RANAR BIKIN VALENTINE. 

*. Sanya jajayen tufafi tare da bayyana tsiraici. 

*. Bayyanar da farinciki da jin daɗi a wannan rana, kamar yadda a ke yi a sauran bukukuwa.

*. Musayar jajayen fulawoyi waɗanda ke alamta soyayya. 

* . Rubuta kalmomin soyayya da amfani da lafuzzan da ke motsar da sha’awa ajikin katin. 

*. Aika da saƙonnin batsa da rashin kamun kai ta hanyar saƙo ko kuma ta hanyar wayar tafi da gidanka.

*. Musayar kyaututtukan da suka haɗa da fulawa da alawa da dai sauransu a tskananin ma’aurata ko samari da 'yan mata. 

*. Aikawa da katin gaisuwa (greeting cards). 

*. A wasu ƙasashen, akan shirya ƙasaitaccen biki inda mata da maza ke cakuɗewa da juna, a yi rawa, a yi shaye-shaye, ayi murna, wani lokaci kuma, a haɗa da masha’a.
 
Sai dai kafin mu tafi da nisa, bari mu ji taƙaitaccen tarihin shi wannan biki a farkon samuwarsa. 


TAƘAITACCEN TARIHIN BIKIN VALENTINE 

Daga ranar 13 ga watan Fabarairu har zuwa ranar 15 na wannan wata, maguzawan ƙasar Rum sun kasance suna yin wani bikin maguzanci da suke kira da Lupercalia. A yayin gudanar da wannan biki, mazajen cikinsu kan yanka akuya ko kare sannan su shafe jikunansu da jinin kuma su riƙa dukan matayen cikinsu da fatun dabbobin da suka yanka nan take ba tare da sun wanke jinin ba. A wannan biki, su kan sha kowane irin kayan maye su dinga yawo a cikin gari tsirara yayinda 'yan matan garin za su zo su jeru domin mazajen su zo su jibge su da fatun dabbobin da suka yanka. 

Dalilin wannan duka kuwa shi ne, matan wancan lokacin sun yarda cewa yi musu wannan duka maganin rashin haihuwa ne kasadin.

Bayan an gama wannan, sai kuma a rubuta sunayen duk 'yan matan garin a saka a cikin tulu ko kofin gilashi. Daga nan sai samarin garin su dinga zuwa suna ɗaukan sunayen. Duk wacce saurayi ya ɗauki sunanta, to shikenan ta zama tashi a wannan biki, wasu kuma sanadin aurensu kenan. A irin wannan rana zina ba laifi ba ne a wurinsu. Wannan biki dai ya fara aukuwa ne tun kimanin ƙarnuka goma sha bakwai da suka gabata 

Sai dai kuma kiristoci na wancan lokacin a Rum ba sa son irin wannan biki domin ya saɓa wa addininsu, hakan ya sa Faparoma Gelasius I (492–496) ya soke wannan biki na Lupercalia. Bayan ya soke wannan biki ne sai ya samar da wani sabon bikin, shi ne bikin tunawa da wani shahidin su mai suna St. Valentine wanda aka kashe a ranar 14th ga watan Fabarairu. 

To amma me ya haɗa wannan biki na kiristanci kuma da bikin ranar masoya? Domin samun wannan amsa, bari mu je ga tarihin shi kanshi Valentine ɗin A taƙaice. 


TAƘAITACCEN TARIHIN SAINT VALENTINE 

Masana sun yi saɓani dangane da wane Valentine ne Paparoma Gelasius I ya ƙaddamar da wannan rana domin tunawa da mutuwarsa. Dalili kuwa shi ne: malaman kiristoci da su ka mutu da dama sunansu Valentine, sai dai akwai guda biyu da suka fita daban waɗanda kuma duk sun mutu ne a ranar 14th ga watan Fabarairu, ko da yake dai ba a shekara ɗaya bane. 

Amma wanda aka fi danganta wannan biki da shi, shi ne Valentine na Rome. Shi dai wannan Valentine ɗin wani malamin addinin kiristanci ne wanda Sarki Claudius II ya sa aka kashe a cikin ta hanyar datse masa kai a cikin ƙarni na uku. 

 Zance mafi ƙarfi dai ya nuna cewa sarki Claudius II, wanda bamaguje ne ya haramtawa sojojin lokacinsa yin aure, saboda a cewarsa, tuzuran sojoji sun fi bayar da abinda ake nema daga sojoji fiye da masu aure. Sai dai duk da wannan doka da sarkin ya kafa, Saint Valentine sai ya ci gaba ɗaurawa sojojin aure a ɓoye, wannan dalili ne ya sa aka kama shi kuma aka kashe shi. Wannan kisa da aka yi masa ne ya sa aka dinga girmama shi a tsakanin 'yan uwansa kiristoci. Shi ma ɗayan Valentine ɗin dai ana tsammanin ya mutu ne a kan wannan dalili. 

Sai dai kafin a kashe Valentine, a yayin da ya ke zaman kaso, ya kamu da son 'yar wanda ya sa aka kama shi. To a cikin kurkukun ne ya rubuta mata wasiƙa tare da bayyana mata irin son da yake mata. A ƙarshen wasiƙar ne ya sa hannunsa da cewa: “from your Valentine” (Ma'ana daga Valentine ɗin ki) wannan shi ne asalin yadda kalmar ta samu zama a cikin bikin masoya na duniya da ake yi a yanzu. 

Wannan jajircewa ta Saint Valentine ya sa Cocin katolika suke girmama shi, har ma coci suka gina a cikin shekarar 350CE a inda ya mutu da kuma ta hanyar bikin ranar Valentine wanda a wancan lokaci biki ne na addininin kiristanci da a koyaushe ake jinjinawa Saint Valentine a matsayin wanda ya yaɗa ƙauna kuma ya ba soyayya muhimmanci a kiristance. 

Hakan yasa da Faparoma Gelasius I ya zo sai ya yamutsa abun ta hanyar daidaita ranar bikin Valentine da kuma bikin Lupercalia domin ya daƙike bikin maguzawan Rum na wancan lokaci. 

Sai dai ungula fa ba ta canja zani ba. Domin kuwa banbancin bukukuwan kawai shi ne su kiristoci suna sanya kaya kuma ba sa dukan mata da ɗanyar fata ne kawai, amma shaye-shaye ba'a daina shi ba, kamar yadda kuma ba'a daina alaƙanta bikin da ranar masoya ba. 

 KO MENENE HAƊIN BIKIN VALENTINE DA HOTON ƊAN YARO MAI FUFFUKE RIƘE DA KWARI DA BAKA? 

Shi wannan yaro da akan ga hotonsa a jikin katukan bikin ranar masoya watau Valentine, a zahirin gaskiya ba yaro bane. Ɗaya ne daga cikin ababen bautar Rumawa da a turance ake kiransa da Cupid. Shi ɗa ne ga abar bautar So da kuma kyau wato Venus. Ya shahara matuƙa a labaran kunne-ya-girmi-kaka inda ake cewa yana harbin mutane da aljannu da kibiyarsa ta so wanda hakan ke sa mutum ya ji kawai nan take ya kamu da son wani. Daga cikin dalilan da suka sa ake sanya shi a jikin katukan saƙonnin bikin Valentine kuwa shi ne, saboda masu aika saƙon suna fatar ya harba kibiyar ta soki zuciyar wanda suka aikawa da saƙon domin ya kamu da son su. Allaah ya kiyaye mu. 

BIKIN RANAR MASOYA A MUSULUNCI.

Manyan malaman Musulunci na wannan zamani kaf sun aminta dangane da haramcinsa, kamar yadda majalisar malaman Saudiyya duk sun haramta wannan biki bisa madogara ta shari'a. Domin Addininmu ya hana mu yin tarayya da kafurai a bukuwan da suka kebanta da su. Baya ga kamanceceniyar da wannan zai haifar ta wannan ɓangare tsakanin musulmi da waɗanda ba musulmi ba, shi wannan biki ta kowace fuska in ka kalle shi yana keta alfarmar shari’ar musulunci ne, bugu da ƙari akwai fasadi mai yawa da wannan biki ya ƙunsa domin kuwa su kansu kiristocin suna ƙorafi da wasu munanan abubuwan da ake aikatawa a irin wannan rana. 

Tunda kuwa hakane, to babu shakka dole mu ƙauracewa wannan biki. 

Saboda faɗin Allaah ta'ala: 

بِسمِ اللَّهِ الرَّحمٰنِ الرَّحيمِ

۞ يا أَيُّهَا الَّذينَ آمَنوا لا تَتَّخِذُوا اليَهودَ وَالنَّصارىٰ أَولِياءَ ۘ بَعضُهُم أَولِياءُ بَعضٍ ۚ وَمَن يَتَوَلَّهُم مِنكُم فَإِنَّهُ مِنهُم ۗ إِنَّ اللَّهَ لا يَهدِي القَومَ الظّالِمينَ


Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku riƙi Yahudu da Nasara majiɓinta. Sashensu majiɓinci ne ga sashe. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, lalle ne shi, yana daga gare su. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai.

(Ma'ida: 51)


لا يَتَّخِذِ المُؤمِنونَ الكافِرينَ أَولِياءَ مِن دونِ المُؤمِنينَ ۖ وَمَن يَفعَل ذٰلِكَ فَلَيسَ مِنَ اللَّهِ في شَيءٍ إِلّا أَن تَتَّقوا مِنهُم تُقاةً ۗ وَيُحَذِّرُكُمُ اللَّهُ نَفسَهُ ۗ وَإِلَى اللَّهِ المَصيرُ


Kada muminai su riƙi kafirai masoya, baicin muminai. Kuma wanda ya yi wannan, to, bai zama a cikin komai ba daga Allah, face fa domin ku yi tsaro daga gare su da 'yar kariya. Kuma Allah yana tsoratar da ku kana. Kuma zuwa ga Allah makoma take.

(Ali Imran: 28)

Kuma manzon Allah Sallallahu alaihi wa sallam yana cewa:
 “Dukkan wanda yayi kamanceceniya da wasu mutane, to yana cikin su”.

Kenan wannan hujja ce ƙarara kan haramcin yin wannan biki. Allaah ya ganar da mu. 


ME YA KAMATA MUSULMI SU YI DANGANE DA RANAR BIKIN VALENTINE? 

1. Da farko dai duk wani musulmin kirki ya kamata ya nuna ƙiyayyarsa ga wannan biki ko tarayya a cikinsa ko halartar wurin da a ke yinsa. 
 2. Ƙauracewa ko bijirewa duk wata ƙofa wacce za ta taimaka wajen ci gaban wannan biki ta kowace fuska. 
 3. Bayyanar da ƙyamar bikin a fili tare da ƙin shiga duk wani abu da ya jiɓince shi. 
 4. Kada ka/ki yi wa kowa murnar ranar kuma ko an maka kada ka amsa, in ma da hali ka zaunar da mutum ka bayyana masa dalilanka na ƙin wannan bikin. 
 5. Yi wa Juna NASIHA dangane da wannan kauce wa irin wannan biki. 

A ƙarshe, ina roƙon Allaah da Ya tsare mu da tssrewarsa, Ya karemu da karewarsa, Ya shiryar da mu daga Shiriyarsa, kuma Ya azurta mu da kyakyawar fahimta. Ya Allaah ka yi mana maganin abinda ya fi ƙarfinmu, Ka yafe mana laifukanmu kuma ka azurta mu da gidan Aljanna.

Aameen Thumma Aamen.

Haiman Raees
08185819176
Haimanraees@gmail.com 
Share:

SUNAYEN ZAMANI


*SUNAYEN ZAMANI*

Gaskiya abin tir ne da ashsha dangane da yadda wasu musulmai suka kaucewa tsarin koyarwar addini, yana da matukar kyau mu dinga taka tsan-tsan wajen sanin kalar sunan da za mu raďa wa yaranmu, domin haqiqa suna yana tasiri a kan wanda aka sa ma wa, wato ya kan bi tsatsan asalin mai sunan, wannan shiyasa babu wasu sunaye da suka fi dace wa musulmi ya sa wa yaransa fiye da sunan *Annabawa* da *sahabbai,* da kuma sunayen da Annabi (SAW) ya yi mana suggesting irinsu *Abdullahi* da *Abdurrahman,* etc. 
.

Amma su wasu musulmai a yau waďanda suka jahilci addini ko suka biye wa son zuciya gani suke a waďancan sunayen tsofaffi ne, _they were outdated,_ sai suka koma ga qago sunaye marasa inganci suna saka wa yaransu, wani ma sunan idan ka bi diddigin sanin ma'anarsa sai ka samu cewa suna ne na wani abin qi ko wani dabba ko dai wani abu da be dace da kimar ďan adam musulmi ba, wani sunan kuwa a fina-finai da littafai kawai ake tsakuro su sai a laftawa yaro, shiyasa sai ka ga yara suna ta tasowa da mutacciyar zuciya irin ta 'yan zamani, domin tun fari ba a gina su a kan kwadayin koyi da Annabi da sahabbai ba, shiyasa ma duk mai addini aka koma yi masa kallon ďan gargajiya mara wayau, Allah Ka tsare mu. 
.

Don haka 'yan uwa nasiha ta gare ku, Abba da Umma ku ji tsoron Allah ku sanya wa yaranku sunan da za ku yi masu kwaďayin su gaji asalin mai sunan, kada ku sanya masu sunaye marasa ma'ana ko wanda ma'anarsu ta munana. 


Allah Ya sa mu dace. 
.

*Ayyub Musa Giwa.*
*Abul Husnain.*

*🕌Islamic Post WhatsApp.*
*08166650256.*
Share:

LUWAƊI A AL'UMMAR MUSULMI


*Luwadi a al’ummar musulmi.*😢😢


Luwadi a wannan zamanin ya zama kamar ruwan dare a tsakanin Matasa. Sun biye ma sha'awa irin ta shaidan wacce ta mamaye zukatansu, Sun afka cikin mafi munin Qazantar laifin da aka taba aikatawa adoron Qasa.

Ina gujewa masu irin wannan dabi’ar domin zasu fuskanci tashin hankali a duniya, a lahira kuma za’ayi musu azaba linki biyu. Yanzu har akwai wata sha’awa tsakanin namiji da namiji? Haba mutane, ina zamu tafi da wannan masifar? 

Hakika duk a cikin nau'o'in zina da danginta, Luwadi shine mafi Muni, kuma mafi Qazanta. Kamar yadda Allah yake gaya mana acikin Alqur'ani, sutaul-ankabut aya ta 27

وَلُوۡطًا اِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهٖۤ اِنَّكُمۡ لَـتَاۡتُوۡنَ الۡفَاحِشَةَ مَا سَبَـقَكُمۡ بِهَا مِنۡ اَحَدٍ مِّنَ الۡعٰلَمِيۡنَ‏

Ma’ana; “ka tuna Annabi lut (As) lokacin da yace wa mutanensa "me yasa kuke yin irin wannan alfashar? Babu wani wanda ya rigaku aikata irin wannan alfasha daga cikin talikai (HALITTU BAKI DAYA)".

Kuma acikin suratu An-naml aya ta 55, Allah yace; 

ﺍَـﺌِﻨَّﻜُﻢۡ ﻟَـﺘَﺎۡﺗُﻮۡﻥَ ﺍﻟﺮِّﺟَﺎﻝَ ﺷَﻬۡﻮَﺓً ﻣِّﻦۡ ﺩُﻭۡﻥِ ﺍﻟﻨِّﺴَﺎٓﺀِ​ؕ ﺑَﻞۡ ﺍَﻧۡـﺘُﻢۡ ﻗَﻮۡﻡٌ ﺗَﺠۡﻬَﻠُﻮۡﻥَ 

Ma’ana “ku kuna zuwa ma mazaje ta fannin sha’awarku maimakon mata, bari dai ku mutane ne wadanda suka kasance jahilai".

Acikin irin wannan halin ne, Annabin Allah yayi baki a gidansa, daga nan sai mutanen nasa suka zo suna masu gaggawa, akan sai sunyi luwadi da wadannan bakin kamar yadda acikin suratu-huud aya ta 78 Allah yake cewa; 

ﻭَﺟَﺎٓﺀَﻩٗ ﻗَﻮۡﻣُﻪٗ ﻳُﻬۡﺮَﻋُﻮۡﻥَ ﺍِﻟَﻴۡﻪِ ؕ ﻭَﻣِﻦۡ ﻗَﺒۡﻞُ َﺎﻧُﻮۡﺍ ﻳَﻌۡﻤَﻠُﻮۡﻥَ ﺍﻟﺴَّﻴِّﺎٰﺕِ ؕ​ ﻗَﺎﻝَ ﻳٰﻘَﻮۡﻡِ ﻫٰٓﺆُﻟَﺎۤﺀِ ﺑَﻨٰﺘِﻰۡ ﻫُﻦَّ ﺍَﻃۡﻬَﺮُ ﻟَـﻜُﻢۡ​ ۚ ﻓَﺎﺗَّﻘُﻮۡﺍ ﺍﻟﻠّٰﻪَ ﻭَﻟَﺎ ﺗُﺨۡﺰُﻭۡﻥِ ﻓِﻰۡ ﺿَﻴۡﻔِﻰۡ ؕ ﺍَﻟَﻴۡﺲَ ﻣِﻨۡﻜُﻢۡ ﺭَﺟُﻞٌ ﺭَّﺷِﻴۡﺪٌ .

Ma’ana; da mutanensa suka je masa suna gaggawa zuwa gare shi, kuma a gabani, sun kasancence suna aikata munanan ayyuka. Yace “ya mutane na, wadannan ‘ya’yana ne sune mafiya tsarki a gareku. Kuji tsoron Allah kar ku wulakantani a cikin baqi na. Shin babu wani namiji shiryayye daga gare ku?”.

Kunga anan har ‘ya’yansa mata yayi musu tayi, amma suka ce basu yadda ba. Kamar yadda wasu malamai sukace, ya gabatar da ‘ya’yansa mata ga wadannan mutanen domin ya fanshi bakin sa. Amma mutanen suka ki amince wa.

Acikin suratu-hijr aya ta 70 ya kara ce musu;

قَالَ هٰٓؤُلَاۤءِ بَنٰتِىۡۤ اِنۡ كُنۡـتُمۡ فٰعِلِيۡنَؕ‏

Ma’ana; “idan kun dage akan sai kunyi, toh ga ‘ya’ya na nan.

Amma duk da haka suka ki, daga karshe Allah yayi musu azabar da bai taba yiwa wata al’umma kafinsu ba. Allah ya aiko da Mala'iku suka ciccibe garin zuwa sama, suka watsa narkon azaba sannan suka Kifar dasu.

Acikin Suratu Huud (as) Allah yace:

ﻓَﺠَﻌَﻠۡﻨَﺎ ﻋَﺎﻟِﻴـَﻬَﺎ ﺳَﺎﻓِﻠَﻬَﺎ ﻭَ ﺍَﻣۡﻄَﺮۡﻧَﺎ ﻋَﻠَﻴۡﻬِﻢۡ ﺣِﺠَﺎﺭَﺓً ﻣِّﻦۡ ﺳِﺠِّﻴۡ

Ma’ana "Yayin da al’amarinmu yazo, sai muka sanya saman birnin ya zama kasanta(kamar juyin waina) sannan mukayi musu ruwan duwatsun wuta na sijjeel".

Allah ya azabtar dasu abisa zunubansu, kuma duk wanda yake aikata irin wannan mummunar alfashar toh ya sani shima irin wancen hukuncin ne dashi, domin kaima an aiko maka da annabi kamar yadda aka aikowa da su ma wadancen mutanen.

LUWADI Mummunar Annoba ce wacce ta kauce wa hanyar da Allah ya halicci dukkan halittunsa akai. Don koda dabbobi ba zaka tarar suna yin irin wannan abun ba.

Allah ya tsare mana imaninmu😭😭
Abdulhadi Dankama
Share:

SHAYE-SHAYE A TSAKANIN MATAN HAUSAWA

SHAYE SHAYE A TSAKANIN MATAN HAUSAWA. 

Yawaitar ta'ammali da kayayyakin gusar da hankali da mata ke yi a yanzu, na daya daga cikin manyan matsalolin da al'ummar Hausawa ke fuskanta.
Yara mata da shekarunsu suka kama daga 18-45 ne suka fi aikata wannan mummunar dabi'a. Akwai dalilai masu yawa da ake ganin sune musabbabin haddasawa matan Hausawa tsunduma cikin wannan mummunar hanya ta shaye-shaye. Daga cikin wadannan dalilai akwai:
Rashin aure
Tsantsar damuwa
Auren dole
Damuwar da auren ke haifarwa. 

Wannan dabi'a ta shaye-shaye a tsakanin matan Hausawa, a iya cewa bak'uwar aba ce, wadda a 'yan shekarun da suka gabata sam ba a santa ba, akwai tabbacin cewa kwanan nan ta kutso kai cikin al'ummar ta Hausawa, sakamakon su ne suka fi kowa matsalolin aure a tsakankanin takwarorinsu wato k'abilun Yoruba, Igbo, Kanuri da kuma Fulani.
Duk da kasancewar matsalar shaye-shayen mata ta zamo ruwan dare game duniya, sakamakon babu wata al'umma a yanzu da za ta bigi k'irji ta ce ta tsira daga wannan mummunar dabi'a, sai dai ace wata ta fi wata.

WANE DALILAI NE SUKA FI SA MATAN HAUSAWA SHAYE-SHAYE? 
Shaye-shaye na nufin shan dukkan wani abu da zai iya jawo buguwa, ko daukewar barci, ko karin wani karfi na musamman ko gusar da hankali. Jaridar Vanguard News ce ta rawaito hakan a wani gangamin wayar da kan matasa da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta k'asa (NDLEA) ta gabatar a jami'ar Bwari a watan March na wannan shekarar. 

Wani bincike da Medlineplus ta k'asar Amurka ta gabatar, ya nuna cewa binciken National institute on drug abuse ta k'asar Amurka ya baiyana cewa, shaye-shayen magunguna ba bisa ka'ida ba, babban tarnak'i ne ga lafiyar kowacce al'umma. Miliyoyin mutane suna rasa rayukansu, ko su kamu da cututtuka masu yawan gaske.

Dalilai da yawa ne dai ake ganin su ne suka sanya mata tsunduma cikin harkokin shaye-shaye. Daga cikin manyan dalilan akwai:

RASHIN YIN AURE A KAN LOKACI
Sanannen abu ne yadda Hausawa suka dauki aure, hasali ma aure shi ne abu mafi muhimmanci a bahaushiyar al'ada.
Rashin samun mijin aure a lokacin da mace ta kai minzalin yin auren na zama babban sanadin haifar da shaye-shaye ga mata. Wannan matsala ce babba da ke tunzura rayuwar 'yan mata su fara ta'ammuli da kayan gusar da hankali. Damuwar da al'uma kama daga iyaye, 'yan uwa, kawaye da sauran jama'a da suke d'orawa macen da bata yi aure ba na saka matan su fara amfani da kayan gusar da hankali. Haka kuma mata da yawa da ba su da aure kuma ba sa so su fada cikin harkokin zinace-zinace, su kan yi amfani da magungunan gusar da hankali domin ya taimaka mu su wajen rage sha'awar maza da za su iya ji. Shan kayan maye na ba su damar mancewa da kuma tsai da duk wani yanayi da za su iya ji a jikinsu.

DAMUWA
Tsantsar damuwa sakamakon rashin wani abu na jefa mata cikin shaye-shaye. A wannan rukuni an fi samun matan aure a ciki, wadanda yawanci ba sa samun kulawar da ya kamata daga wajen mazajensu, wato ba su da lokacin yin hira da su ko jin wasu matsalolinsu. Hakan ya kan tunzura matan su fara shan kayayyakin da za su gusar musu da hankali, domin su samu damar mance kaso da yawa na matsalolin da suka addabi rayuwarsu.

GASA/KWAIKWAYO

Jinsin mata a dabi'ance jinsi ne ma su gasa da kwaikwayo, wato hanya ce mai sauki na samun yawaitar mata ma su shaye-shaye, sakamakon wata ta ga wata kawarta ko makociyarta ta na yi. A nan akwai buqatar bayar da kulawa ta musamman ga mata da sa ido koyaushe akan hanyoyin da mata ke bi don gudanar da rayuwarsu.

NAU'O'IN KAYAN MAYE DA MATA SUKA FI AMFANI DA SU
Mata ba su cika amfani da kwayoyi ba, sai dai magunguna na ruwa wato syrup. Wadannan magunguna sun hada da: Emzolyn
Benelyn
Coplin
Codin, da kuma wasu kad'an da su kan yi amfani da tabar wiwi da k'wayoyi kamar su Tramol da sauransu.

ILLOLIN DA SHAYE-SHAYE YAKE YIWA JIKIN MACE
Daga cikin manyan matsalolin da shaye-shaye ke haifarwa ga mata sun had'a da:

HANA HAIHUWA
Mata ma su shaye-shaye na fuskantar barazanar rashin haihuwa, domin kuwa ya na raunata mahaifarsu yarda ko da ma ciki ya shiga ba ya iya zama. 

HAIHUWAR YARA MARA SA LAFIYA
Akwai barazanar haihuwar yara marasa koshin lafiya, idan ma har an samu haihuwar kenan, ana haifar yara da wani nak'asu a jikinsu ko kwakwalwarsu.

RAUNANA GARKUWAR JIKI
Shaye-shaye na matukar raunana garkuwar jikin mace, da hana su kuzari ta hanyar haddasa musu cututtuka iri-iri.

RAGE DARAJA A CIKIN AL'UMA
Shaye-shaye na rage darajar mace a cikin al'uma, ya na sawa a gujeta a kyamaceta. Idan budurwa ce yana hanawa a aureta, idan kuma mai aure ce yana jawo rabuwar aure. 

RASHIN SON KUSANTAR NAMIJI
Matan da suke shaye-shaye ya na rage mu su sha'awa, ya na sa su ji ba sa so maza su taba su ko su kusancesu da gaske. Ya na hana garkuwar jikinsu karbar duk wani sako da namiji zai aika gareta. 

SAUYAWAR GABOBIN JIKI
Ana gane mata ma su shaye-shaye ta hanyar kankancewar idanuwansu da canzawar launin idon, labbansu na bushewa kuma hakoransu na lalacewa har ma su rube wani lokacin. Ya na sa rama da bushewar jiki, yana saukar da gashin mace, ya lalata kyakkyawar surarta. 

YAWAN RASHIN LAFIYA
Matan da suke shan kayan maye su na da yawan laulayi, ko yaushe cikin ciwo suke, sabo da sun riga sun raunata garkuwar jikinsu. K'ashinsu kuma yana rage k'wari, dan haka akwai yiwuwar saukin samun karaya a k'ashinsu. 

A karshe zuwa ga duk wanda abin ya shafa, akwai bukatar d'aukar kowane irin mataki da ake ganin ya dace, domin yak'ar wannan mummunar d'abi'a da ta kutso kai cikin al'umarmu.

Aysha Bilkisu Umar 
8/6/18.

Share:

BA MAZAN BA, BA MATAN BA


BA MAZAN BA, BA MATAN BA:!

Zaku taya ni shaida cewa an wayi gari a yau,akasarin maza idan sun tashi neman wadda zasu aura, babban abin da ya dame su game da macen shi ne "kyau". 

Abin da zai kara baka haushi kuma shine, dà yawan su suna son kyakkyawar ne don su rika yawo da ita a gaban mota suna nunawa jama'a, ana cewa kai wane fa ya hadu,domin ya dauko hadaddiya! Kaga kuwa idan kana neman "sakarci" lamba daya, to shi ne wannan.

Haka zaka ga mace ita kuma, da yawansu
idan an zo maganar aure babban abin da ya dame su "kudi". 

Ba kowa ce ma ta damu da kyakkyawa ba a nan, a'a su dai kudi! To kada in jaku da nisa, wallahi duk namijin da ya auri mace saboda kyau kawai, bata da ilimi da tarbiyya sai kyau kawai, kada ya sa rai zai samu kyakkyawar rayuwar aure. 

Sai fà in Allah Ya taimakeshi ya iya ilimantar da ita da tarbiyyantar da ita, wanda wannan kuma yana da wahala sosai.

Haka duk yarinyar da ta hangi kudi kawai a gun wanda zata aura, bata damu da ilimi ko tarbiyyarsa ba, wallàhi duk abin da ya biyo baya na rashin kwanciyar hankali, kada ta tsaya neman dalili, don gashi na gaya mata.

Allah Ya sanya mu daga cikin masu yin aiki da sani, amin

Rubutawa : Habib Jafar Madobi
Share:

PARENTS PLEASE TAKE NOTE


PARENTS NOTE:
THESE ARE SOME OF THE SUBSTANCES YOUTHS NOW
 TAKE.

– Lipton soaked with Regal gin
– Tramadol
– Codeine
– Dry pawpaw leaves
– Hypo in Lacasera
– Tom Tom in Lacasera
– Spirogyra
– Rephnol
– Gum
– 10 days Urine
– Methylated spirit in codeine
– Methylated spirit in Coke
– Dry plantain leaves
– Cannabis (Igbo) in Regal gin
– Burnt Tyres
– Burnt Bitumen

Please be observant about these substances mentioned above. Always visit your child's bedroom without any awareness of your visit. Check every thing in that room to see he doesn't hide such drugs in his room. You can equally send him far away for you to search their rooms. Very important pls.
*NOTE*:This applies to both male and female child.PARENTS NOTE:
THESE ARE SOME OF THE SUBSTANCES YOUTHS NOW
 TAKE.

– Lipton soaked with Regal gin
– Tramadol
– Codeine
– Dry pawpaw leaves
– Hypo in Lacasera
– Tom Tom in Lacasera
– Spirogyra
– Rephnol
– Gum
– 10 days Urine
– Methylated spirit in codeine
– Methylated spirit in Coke
– Dry plantain leaves
– Cannabis (Igbo) in Regal gin
– Burnt Tyres
– Burnt Bitumen

Please be observant about these substances mentioned above. Always visit your child's bedroom without any awareness of your visit. Check every thing in that room to see he doesn't hide such drugs in his room. You can equally send him far away for you to search their rooms. Very important pls.
*NOTE*:This applies to both male and female child.
Share:

KU AURAR DA 'YA'YANKU IDAN SUN BALAGA

KU AURAR DA ƳAƳAN KU (Maza ko Mata) IDAN SUN BALAGA....
.
.قال عمر بن الخطاب رضي الله عنه:

 *"زوجوا أولادكم إذا بلغوا، لا تحملوا آثامهم".*

ذكره ابن الجوزي في أحكام النساء ص 304

وذكر ابن الجوزي عن بعض السلف أنه قال: "كان يقال العجلة من الشيطان إلا في خمس، إطعام الطعام إذا حضر الضيف، وتجهيز الميت إذا مات، *وتزويج البكر إذا أدركت*، وقضاء الدين إذا وجب، والتوبة من الذنب إذا أذنب" (أحكام النساء ص304).
.
Ma'ana:
Umar dan Khaddab (r.a) yace: "Ku aurar da yaranku [maza ko mata] idan sun balaga, kar ku dauki zunuban su". [Ma'ana, idan suka lalace laifi na kanku].
.
Sannan Ibnl Jauziy (r.h) yace:........ "ya kasance ana cewa gaggawa daga shaidan ne, amma ban da gurare 5...". Daga ciki yace: "aurar da mace da zarar ta kai".

Ahkamun Nisa', shafi na 304
.
Sun fadi wadannan maganganu shekaru aru-aru. Yau an wayi gari maza da mata na cikin sha'awa da lalacewar da suna bin wasu hanyoyi don kauda sha'awar su a boye inda iyaye ko wasu ba za su gan su ba, saboda rashin aure. Musamman yanzu lokacin wayoyin Android.
*"Dukkan Ku Masu Kiwo Ne, Kuma Dukkan Ku Se An Tambaye Ku Akan Abinda Aka Baku Kiwo"*. Inji Annabi (s.a.w)
.
Ba'a taba al'ummar da sha'awa ta yi yawa cikinta ba kamar al'ummar da muke ciki. Yau idan ka nemi taba jikin mace se ka ga kamar daman jira take ka taba. Idan itama ta nemi taba jikin namiji se ta ga kamar daman jira yake ta taba. Sha'awa ta ko ina: ga waya; ga TV; ga kan layi da bakin titi da kasuwa. Ba'a son a yi auren kuma ana son a biya bukata. Wasu ko na son auren amma bidi'o'i sun dabaibaye auren sun tsadar da shi ya fi karfin talaka ko da mutumin kirki ne. *Allah Ya Kyauta*
.
Da na yi sharing wannan a WhatsApp, akwai wadanda suka ce min inama iyayen su su gani su kirasu a zauna maganar aure! Wannan zai nuna maka cewar wasu tsoron isarda maganar ga iyayen su ya hanasu magana, saboda ba'a bude musu kofar hakan ba. Ba'a tambaye su aka ji ra'ayin su ba. 
.
*_Abu muhd_*
*10/11/2018*

Share:

MUSULMI BA KANWAR LASA BANE


*Musulmi ba Kanwar Lasa ne ba*😂😂😂

Wani bayahude ne yayi shiga (wato
dressing) irin na Musulmai, ya taso
ya taho garin Musulmai musamman
wai domin ya chanza musu Fahimtar
addini, ya sanya musu kokonto
acikin addininsu.
Yazo zai shiga garin sai yaga wani
mai kiwon Tumaki agefen gari.
Aransa sai yace "Yawwa! Bari in fara
ta kan wannan jahilin!".
Sai ya matso kusa da Makiyayin nan
yayu masa sallama, shi kuma ya
amsa masa. Bayahuden nan ya rika
jansa da hira har suka dade suna
hira, tumakin kuma suna gefe suna
kiwo.
Acikin hirar tasu sai bayahuden yake
cema wannan Makiyayin "Kaga
Alqur'ani yana da wuyar haddacewa.
Watakil saboda akwai ayoyin da aka
maimaitasu ne acikinsa. Wasu an
maimaitasu sau biyu ko uku, ko
sama da haka ma. Shi yasa Ayoyin
Alqur'ani sukayi yawa sosai har Hizifi
60".
Shi dai Makiyayin yana binsa da
"Na'am" "Na'am". Sai yace "To kaga
yanzu da za'a taru acire duk ayoyin
nan masu wuya, da kuma ayoyin da
aka maimaita, watakil da an rage
yawan hizifin zuwa 50 ko 40. Mai
zaka ce akan haka?".
Sai Makiyayin nan yace masa "To ai
kaima akwai Maimaici ajikinka.
Domin akwai gabobin jikinka
wadanda aka maimaita maka irinsu.
Misali kamar hannaye biyu, Qafafu
biyu, idanuwa biyu, Kunnuwa biyu,
da sauransu".
"Yanzu kaima mai zai hana mu kaika
wajen Hukuma ayanke maka su,
domin nauyinka ya ragu, kuma koda
abincin da kake ci ma zai ragu".
Da Bayahuden nan yaji haka sai yayi
shuru ya sunkuyar da kansa. Bai sake
cewa komai ba. Ya juya ya tafi yana
cewa "Lallai Musulmai suna da zurfin
hankali da hikima.Yanzu wannan fa
Makiyayi ne ba Malami bane. Da
ache Malami na samu ban san irin
amsar da zai bani ba!".
✍🏻 *Dr.Mansur Ibrahim Sokoto*
Share:

KU AURAR DA 'YA'YANKU IDAN SUN BALAGA


KU AURAR DA ƳAƳAN KU (Maza ko Mata) IDAN SUN BALAGA....
.
.قال عمر بن الخطاب رضي الله عنه:

 *"زوجوا أولادكم إذا بلغوا، لا تحملوا آثامهم".*

ذكره ابن الجوزي في أحكام النساء ص 304

وذكر ابن الجوزي عن بعض السلف أنه قال: "كان يقال العجلة من الشيطان إلا في خمس، إطعام الطعام إذا حضر الضيف، وتجهيز الميت إذا مات، *وتزويج البكر إذا أدركت*، وقضاء الدين إذا وجب، والتوبة من الذنب إذا أذنب" (أحكام النساء ص304).
.
Ma'ana:
Umar dan Khaddab (r.a) yace: "Ku aurar da yaranku [maza ko mata] idan sun balaga, kar ku dauki zunuban su". [Ma'ana, idan suka lalace laifi na kanku].
.
Sannan Ibnl Jauziy (r.h) yace:........ "ya kasance ana cewa gaggawa daga shaidan ne, amma ban da gurare 5...". Daga ciki yace: "aurar da mace da zarar ta kai".

Ahkamun Nisa', shafi na 304
.
Sun fadi wadannan maganganu shekaru aru-aru. Yau an wayi gari maza da mata na cikin sha'awa da lalacewar da suna bin wasu hanyoyi don kauda sha'awar su a boye inda iyaye ko wasu ba za su gan su ba, saboda rashin aure. Musamman yanzu lokacin wayoyin Android.
*"Dukkan Ku Masu Kiwo Ne, Kuma Dukkan Ku Se An Tambaye Ku Akan Abinda Aka Baku Kiwo"*. Inji Annabi (s.a.w)
.
Ba'a taba al'ummar da sha'awa ta yi yawa cikinta ba kamar al'ummar da muke ciki. Yau idan ka nemi taba jikin mace se ka ga kamar daman jira take ka taba. Idan itama ta nemi taba jikin namiji se ta ga kamar daman jira yake ta taba. Sha'awa ta ko ina: ga waya; ga TV; ga kan layi da bakin titi da kasuwa. Ba'a son a yi auren kuma ana son a biya bukata. Wasu ko na son auren amma bidi'o'i sun dabaibaye auren sun tsadar da shi ya fi karfin talaka ko da mutumin kirki ne. *Allah Ya Kyauta*
.
Da na yi sharing wannan a WhatsApp, akwai wadanda suka ce min inama iyayen su su gani su kirasu a zauna maganar aure! Wannan zai nuna maka cewar wasu tsoron isarda maganar ga iyayen su ya hanasu magana, saboda ba'a bude musu kofar hakan ba. Ba'a tambaye su aka ji ra'ayin su ba. 
.
*_Abu muhd_*
*10/11/2018*
Share:

MA SU FAƊIN GASKIYAR WANNAN ZAMANI


*MASU FAƊIN GASKIYAR WANNAN ZAMANI*
 
Wannan zamani namu yana da wahala, Allah ya tsare mu daga fitinunsa...!!
*-* Iya sukar mutane da ganin ba wanda yake kan dai-dai sai ni, shi ne fadin gaskiya.
*-* Ya kamata musulmi ya zama mai kyautata ma ƴan uwansa zato.
*-* Yadda kake aiki don fatan al'umma ta gyaru, to ka tabbatar wasu suna nan suna yi, ko ka sansu ko baka san su ba.
*-* Musulmin da ke shiga cikin ƴan uwansa ya jure akan halayersu yafi musulmin da ba ya shiga cikinsu. 
*-* Yawan zargi na fassara mummunan halin mai yin sa.
*-* In ƙasarka ta shiga matsala ƙoƙarin gyaranta za ka yi ba tunanin barinta ba, domin duk inda za ka suna maka kallon daga can ka fito, saboda haka ba za su ganka da mutunci ba.

Allah ya shiryatar da mu. 

*Daga: ✍ Sheikh Basheer Lawal Muhammad Zaria Hafizahullah.*
Share:

WANENE NAMIJI A YAREN MATA?


WANENE NAMIJI A YAREN MATA?
👇👇👇👇👇👇👇👇

  Kalmar Namiji a yaren malam bahaushe shine Kishiyar jinsin mace.
  Amma a wajen mata, idan kaji ance Namiji, to shine Wanda fa yake iya gamsar da iyalinsa a wajen Surrunsu na Aure.
 Mace an halicceta da bukatar da Namiji. 
 Matsalar dai guda daya ce, idan kaji ance Matar Aure tana Zina, ko Matar Aure ta kai mijinta kotu a raba Aurensu, Sabida matsala guda daya Tak. 
👉 Ya Kamata Mu sani cewar Ba Aure yana Nufin ciyar da mace abinci Sau ukku a rana bane. 
 Sabida haka wani Namijin yana iya yin Alfahari cewar yana ciyar da iyalinsa abinci a rana sama da sau biyu ko sama da sau ukku. Kuma Sai kaga yana fahari da yin hakan. Amma a wajen mace hakan ba burgewa bane. Kai Asalima wannan ba shine gwarzontaka ba a wajen mata. Gwarzontaka shine, ka biya maka Bukatarta a Wajen da kuke kebancewa.
👉 Wani Namijin yana Alfahari wajen daukar Matar sa a mota tsaleliya ya kaita unguwa, wayyo!!! Wallahi idan har kana da matsala a wajejn kebancewa ba burgeta kakeyi ba. Asalima ita a wajenta A Larura take baka kanta. Musamman ma idan bazawara ce, Wadda mijinta na baya wanda Suka Rabu ko wanda ya mutu ya barta ka aura ya fika gwarzontaka. Idan kuna tarewa shi zatana tunowa a zuciyarta. Cewar Kamar shine yake Neman ta, idan tayi haka ne ma zataji ta Dan gamsu kadan, tinda baza tayi Alfahari da kai ba a wannan bangaren.
👉 Wani Namijin Kuma yana Alfahari ne idan ya dawo daga kasuwa zaizo da Kayan morewa Rayuwa, hakan yana ganin yana birge iyalinsa. Wallahi a Banza indai a wajen kebancewa baka iya komi. Sai kaji mace tace ban rasa ci ba, ban rasa sha ba, ban rasa sutura ba, Sai Abu daya tak☝ka zama Sorry.
👉 Wani Namijin kuma yana ganin shi Dan Gayu ne. Zaisa sutura kala-kala, Amma kuma Idan ya kebance da iyalinsa sau dai a hankali. Kwalliyarka Bata mata kyau, Sabida kana da matsala guda daya☝. Sai take ganin Kamar kwalliya Bata biya kudin sabulu ba. Sai taga cewar idan wani ne yasa, zaifi dadin kallo ba kai ba, Sabida bashi da wata Nakasa a jikinsa.
👉 Kana iya Alfahari kai Hamshakin Dan Kasuwa ne, wata kuma tana ganin Kamar kai Dan wahala ne. Sabida a bangaren kebancewa baka iya komi ba.
  
👇👇👇👇👇👇👇👇
 Abinda ya rage maka shine. 
- Matsalar Rashin dadewa? Akalla bala iya Minti 30 bare Awa daya ko sama da haka. Kaga kana bukatar Delay kenan.
- Matsalarka Itace, gabanka Kamar Na yara yake?
 Kaga kana bukatar Enlargement.
- Matsalar shine halittarka Bata da kauri? 
 Kaga kenan kana bukatar Enlargement.
- Matsalar shine halittarka Bata da tsawo? Kana Bukatar enlargement.
 ALLAH DAYA GARI BANBAN.

 Karka boye mana Matsalar ka. Ka kira wannan number 08108605876 ko ka Tintibemu ta whatsapp zamu saita maka Al'amarinka, Amma fa da ikon Allah.
 Amarya da Uwar gida zasuyi Mana Addu'ah.

 Kasuwarmu Online ne, Aikawa mukeyi ta hanyar mota, har inda kake kuma cikin sauki.
 Idan baka Shirya ba, Dan Allah kar kayi contacting Dinmu.

Allah shine magani.

ZAUREN SUNNAH ISLAMIC MEDICINE CENTER 08108605876
Share:

NASIHOHI ZUWA GA SOJOJINMU 02


NASIHOHINMU ZUWA GA SOJOJINMU 02

Kai dan uwa musulmin soja ko Dan sanda ko wani jami'in tsaro ko mai gwagwarmaya Dan Al'umma... Wanda Allah yasa ka kasance a kasar musulmai, kayi yaki da gwagwarmayarka Dan Allah da daukaka Kalmar Allah sai Allah ya taimakeka a cikin al'amuranka, kada kayi yaki ko gwagwarmaya Dan kawai kare kasarka ko kare yan kasarka, A'a bayan haka anason ka cakuda Niyyarka ta yin yaki da Niyyar kare Addinin Allah (s.w.t) da mabiya Addinin Dan Daukaka Kalmar Allah (s.w.t).

Shaikh Muhammad Ibnu Sãlih al-Uthaimeen [Rh] yana magana akan yadda ya kamata mayaki (soja ko waninshi) musuli da yake a kasar musulmai ya kasance sai yace:

"...يجاهد أعداء الله لتكون كلمة الله هي العليا، لا لأجل أن يدفعوا عن الوطن من حيث إنه وطن، لأن الدفاع عن الوطن من حيث هو وطن يكون من المؤمن والكافر، حتى الكفار يدافعون عن أوطانهم، لكن المسلم يدافع عن دين الله، فيدافع عن وطنه لا لأنه وطنه مثلا، ولكن لأنه بلد إسلامي، فيدافع عنه حماية للإسلام الذي حل في هذه البلد.

“...Musulmai zasu yaki makiya Allah dan Kalmar Allah ta kasance itace a sama, ba wai dan kawai su kare kasa dan tana kasa ba, domin tsantsar kare kasa dan kasancewarta kasa ana samun hakan daga mumini da kafiri, hatta kafirai suna kare kasashensu, amma shi musumi -anason ya kasance- yana kare Addinin Allah ne, Misali ya kasance yana kare kasarshi ne amma ba dan kawai kasar tana kasarshi ba, A'a sai dan kasancewar kasar kasar musulunci ce, Dan haka sai ya bawa kasar kariya dan kare musuluncin da yake cikin kasar.”

KUMA YACE:
يجب على طلبة العلم أن يبينوا للناس أن القتال للوطن ليس قتالا صحيحا، وإنما يقاتل لتكون كلمة الله هي العليا، وأقاتل عن وطني لأنه وطن إسلامي، فأحميه من أعدائه وأعداء الإسلام، فبهذه النية تكون النية صحيحة، والله الموفق.
(شرح رياض الصالحين ١/ ٣٥)

“Ya zama wajibi akan daliban ilmi su bayyana wa mutane cewa yaki dan kasa ba ingantaccen yaki bane, kawai ana yin yaki ne dan Kalmar Allah ta kasance itace a sama, Zan yiwa kasata yaki ne dan kasancewarta kasar musulunci, dan in kare kasata daga makiyanta da makiyan musulunci, DA WANNAN NIYYAR NE NIYYA ZATA KASANCE INGANTACCIYA, Allah ne mai datarwa.

✍Abubakar Ibrahim Assalafy.
Share:

NASIHOHI ZUWA GA SOJOJINMU 01


NASIHOHINMU ZUWA GA SOJOJINMU 01

An karbo hadisi daga Sayyidna Abu musal-ash-ariy [R.a] yace:
سئل رسول الله -صلى الله عليه وسلم- عن الرجل يقاتل شجاعة، ويقاتل حمية، ويقاتل رياء، أي ذلك في سبيل الله؟ فقال رسول الله -صلى الله عليه وسلم-: من قاتل لتكون كلمة الله هي العليا فهو في سبيل الله.
     (البخاري ٢٨١٠ و مسلم ١٩٠٤)

“An tambayi Annabi (s.a.w) dangane da mutumen da yake yaki dan ya nuna jarumtaka, da kuma Wanda yake yaki dan kabilanci, da kuma Wanda yake yaki dan riya, waye a cikinsu Wanda yake yaki Na Fisabilillahi (Dan Allah)? Sai Annabi (s.a.w) yace: «WANDA YAKE YAKI DAN KALMAR ALLAH TA KASANCE ITACE A SAMA TO SHINE YAKE YAKI DAN ALLAH»”

A cikin wanna hadisi Annabi (s.a.w) ya karantar da cewa Duk Wanda zaiyi yaki da wata manufa wadda ba daukaka Kalmar Allah (s.w.t) bace to ba Dan Allah yake yakin ba,

Dan haka abinda ya kamata shine duk wani musulmin Soja ko Dan Sanda dasauran jami'an tsaro da masu gwagwarmaya da kai komo Dan Al'umma, suyi kokarin kudurce yi Dan Allah da daukaka Kalmar Allah a Zukatansu, idan sukayi haka zasu samu Lada da La'ada, Zasu samu Lada a wajen Ubangijinsu Allah (s.w.t) da kuma La'ada a wajen Gwamnatin da ta daukesu aiki.

Abin nufi dai su kudurce yi Dan Allah a zukatansu sai Allah ya duba kyakkyawar Niyyarsu ya taimakesu.

Dan haka: Kai dan uwa musulmi Soja ko Dan sanda ko Dan gwagwarmaya...: Kada kayi Yaki Dan Kawai Nuna Jarumta, Ko Dan kawai Kare Kasarka/Kabilarka, ko Dan kawai Samu matsayi ko Nuna matsayinka...!

Allamah Ibnu Uthaimeen [Rh] yace:

فقد سئل الرسول صلى الله عليه وسلم عن الذي يقاتل على أحد الوجوه الثلاثة، شجاعة، وحمية، وليرا مكانه.
     أما الذي يقاتل شجاعة: فمعناه أنه رجل شجاع، يحب القتال، لأن الرجل الشجاع متصف بالشجاعة، والشجاعة لابد لها من ميدان تظهر فيه، فتجد الشجاع يحب أن الله ييسر له قتالا ويظهر شجاعته، فهو يقاتل لأنه شجاع يحب القتال.
     الثاني: يقاتل حمية، حمية على قوميته، حمية على قبيلته، حمية على وطنه، حمية لأي عصبية كانت.
     الثالث: يقاتل ليرا مكانه، أي ليراه الناس ويعرفوا أنه شجاع، فعدل النبي صلى الله عليه وسلم عن ذلك، وقال كلمة موجزة ميزانا للقتال فقال: «من قاتل لتكون كلمة الله هي العليا فهو في سبيل الله»
(شرح رياض الصالحين ١/ ٦٤-٦٥)

“Hakika an tambayi manzo (s.a.s) dangane da Wanda yake yaki Dan dayan ababe uku:
1-Nuna Jarumta.
2-Dan Kabilanci.
3-Dan Nuna matsayinshi.
   Wanda yake yaki Dan Nuna Jarumta ma'anarshi shine: Dan ace shi mutum ne jarumi da yake son yaki, domin jarumin mutum ya siffantu da Jarumta, ita kuma Jarumta dole ne a samu filin da za'a bayyanata, Sai kaga Jarumi yana son Allah ya hore masa yaki Dan ya Bayyana Jarumtarshi kawai, Sai yayi yaki Dan kawai shi jarumi ne yana son yaki.
   WANI KUMA: Yana yaki ne Dan Kabilanci, Kabilancin Mutanenshi, ko Kabilancin Zaurensu/yarensu, ko Kabilancin kasarshi, ko wani nau'in Kabilancin daban.
   WANI KUMA: Yana yaki ne Dan aga matsayinshi (a Jarumta da iya yaki) Dan mutane du ganshi su San cewa shifa Jarumi ne.

Sai Annabi (s.a.w) yayi Adalci a dangane da hakan ya fadi kalma takaitacciya da zata kasance ma'aunin yaki yace: «DUK WANDA YAYI YAKI DAN KALMAR ALLAH TA KASANCE ITACE A SAMA TO SHINE YAKE YAKI DAN ALLAH».

Allah yayi mana muwafaqa.

✍Abubakar Ibrahim Assalafy.
Share:

RASHIN BIYAYYA DA KYAUTATAWA IYAYE YANA DAGA CIKIN MAFI GIRMAN ZUNUBAI


RASHIN BIYAYYA DA KYAUTATAWA MAHAIFA YANA CIKIN MAFI GIRMAN ZUNUBI

Hakika Annabi ﷺ ya yi mana umarni kamar yadda Allah da kansa yayi mana umarnin akan yin biyayya da kuma kyautata mahaifa,da kuma hani daga sabawa masu da kuma cutar dasu,sabawa mahaifa da rashin kyautata masu yana cikin mafi girma zunubai da akewa yiwa Allah anan duniya.Annabi ﷺ ya baiyana mana illa da girman laifin mai sabawa Mahaifansa, ga kadan daga cikin su:-

*1-"Mai Cutar da mahaifansa Tsinanne ne inji Manzon Allah ﷺ *.

Daga Abu Hurairaita R.A yana cewa :-
"Annabi ﷺ yana cewa:-
*(La'antacce ne mai cutar da mahaifansa ko mai sabawa mahaifansa)*.
@ﺍﻟﻄﺒﺮﺍﻧﻲ ﻓﻲ " ﺍﻷﻭﺳﻂ
" ‏( 8497 ‏)
@ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ " ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ‏( 2420 )

*2-"Allah bawa kallon mai sabawa Mahaifansa a ranar alqiyama*.
Daga Ibn Umar R.A yana cewa:-
"Manzon Allah ﷺ yace:
*(Mutane guda ukku Allah bazai kallesu ba a ranar alqiyama:-
-Mai sabawa mahaifansa
-Wanda baya kishin iyalinsa...............)*
@ﻭﺭﻭﻯ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ ‏( 2562 ‏)
@ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ " ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ "

*3-"Mai sabwa mahaifa baya shiga aljanna"*.
Daga Ibn Umar R.A yana cewa:-
"Manzon Allah ﷺ yace:
*(..............Mutane guda ukku bazasu shiga aljanna ba a gobe alqiyama:-
-Mai sabawa mahaifa
-Mai kwankwadar giya
-Mai yin gorin abinda ya bada)*
@ﻭﺭﻭﻯ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ ‏( 2562 ‏)
@ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ " ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ "

*4-"babu mai shiga aljanna sai ya kasance yana biyayya ga mahaifansa kuma baya saba masu"*.
Wani mutum yazo wajan Annabi s.a.w sai yace Ya Manzon Allah ﷺ
"Na shaida babu abin bautawa bisa hakki da gaskiya sao Allah kuma kai Manzon Allah ne, kuma nayi salloli biyar na farilla kuma na bada zakka kuma nayi azumin watan Ramada?? Sai Annabi ﷺ ya ce:
*(Wanda ya mutum akan haka yana tare da Annabawa da Shahidai Siddiqai a ranar alqiyama matuqar bai sabawa Mahaifansa ba)*.
@ﻭﺭﻭﻯ ﺃﺣﻤﺪ ‏( 24299 ‏)
@ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ " ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ " ‏( 2515 ).

*5-"Allah baya karbar aiyuka na mai sabawa mahaifansa inji Manzon Allah ﷺ "*
Daga Abi Umamah R.A yana cewa:
Manzon Allah ﷺ yace:
*(Mutanan guda ukku Allah baya karbar aiyukan su na farilla da na nafila:-
-Mai sabawa Mahaifansa
-Mai gorin abinda ya bayar
-Wanda yake karyata Qaddara)*.
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻋﺎﺻﻢ ﻓﻲ "ﺍﻟﺴﻨﺔ " ‏( 323 ‏)
@ﺳﻠﺴﻠﺔ ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ " ‏( 1785 )

*6-"Sabawa mahaifa yana cikin mafi giraman zunubai inji Annabi s.a.w*.

Manzon Allah ﷺ yana cewa:-
*(Shin bazan fada maku ba mafi girman zunubi ba??)*sai Sukace:Eh ya Manzon Allah ﷺ ,sai yace;
*(Yin shirka da Allah da Kuma sabama Mahaifa)*ya kasance yana Kishingide sai ya tashi zaune sannan yace;
*(Ku saurara da maganar zur da Shaidad Zur)*
@ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻰ صحته.
Allah ka nisantar da mu daga aikata abinda zai sanya mu sabawa Mahaifanmu.Allah ka jikansu kamar yadda suka kulamu lokacin muna yara.

*Allah ka gafarta ma mahaifan mu baki daya*
Share:

ILLAR FUSHI

*ILLAR FUSHI*

Fushi tamkar tabin hankali ne Karshen shi kuma nadama ne, Inji *Aliyu Bin AbiTalib (R.A)* Ka lura duk wanda *fushi* ya shafe shi yakan fidda shi daga dabi'a irin ta mutane 

*FUSHI* shine tarkon abin da shaidan yafi amfani da shi wajen halaka dan adam. Inji Ibnul Qayyim.Ka lura in mutum yana cikin *fushi* to yakan iya aikata komai... a fusace Sannan ba'a gane mutum mai hakuri sai a lokacin *FUSHI* . Maganin fushi *manzan Allah* (s a w) yace idan kai *fushi* idan kana tsaye ne *kazauna* idan kana zaune ne *ka kwanta* ko kuma *kabar wurin* da aka saka kai fushin. 

*Ya Allah* kasa mu iya hadiye *fushin* mu, mu iya yafe ma "yan uwan mu dan mutsira ranar gobe kiyama. 

*ALLAH* ka jikan iyayenmu da yanuwanmu,da abokan mu, *Ya ALLAH* ka sa mu gama da duniya lfy.
*BARKA DA WARHAKA*

Share:

MU JI TSORON ALLAAH

MUJI TSORON ALLAH

((TAKAWA)) "Hattara 'Yan Mata Wajen Aikata Alfsha da Sunan Shan Minti" (1)

Fitowa Na 017

Takawa; Takawa shine jin Tsoron Allah a duk inda rayuwar Musulmin kwarai ya kasance, wannan Shi ake kira Takawa, ya ke Yar Uwa na Musulma, kada misali kina a matsayin ki na Musulma, kinada Martaban ki da Kimar ki da Dajarar ki mai tarin Girma da Kimar ki da Mutuncin ki a wajen Allah mai Girma da daukaka, da ma wajen wanda su kasan Allah da Manzon Allah, ki tsaya ki wasar da kanki ko wanne filawa ya samu nashi ruwan. 
      Idan kina cikin gidan ku ga tsoron Allah kamar yaya har ma zaki iya yiwa wasu yan Uwanki Nasihar kada suyi abu kaza da abu kaza, domin yin Shi Haramun ne babba, amma da zaran kin bar cikin gidan ku, kin fita waje duk wannan Tsoron Allah'n da Nasihar ki duk kin bar su a cikin gidan ku, yanzu kin fita waje babu Kalan Alfashan da ke baki aikatawa, har kin addabi Jama'ar gafen wasu Unguwan, inda wani ko wata wanda ta san ki ta san komai naki inda zata ganki a wannan halin, sai ta tsaya tanata mamakin ki, domin ke ne kike yin Nasiha Allah yace abu kaza Haramun ne, amma gashi idan kin fita waje inda wasu yan unguwan ko mutanen gidan ku basu iya ganin ki, kin zo kina aikata abubuwa dabam dabam iya son ranki, to idan mutanen unguwan ku ba ganki ba, to Mala'ikun Allah sun gani kuma sun rubata, sai mu ga da ganin Mala'ikun Allah da na mutane wanne zai fi tasiri a ranan Alkiyama, 
      Ko kuma Misalin ke Matar Aure ce, in kin fita waje ga ki kinan Mumuna ga kalmar Allah a bakin ki kamar na Manyan Malamai, amma kuma kina sa kafar ki, idan kin dawo cikin gidan ki, to wannan Tsoron Allah'n da kike nunawa Jama'a a waje, duk kin bar su a can, yanzu kin dawo gidan ki duk kin fitini kowa yaran ki ma ba ki bar su ba, Mijin ki ma baki Bar Shi ba, kowa kin addabe shi wajen furta musu Kalmar da Shari'a bai yadda da shi ba, ko kuma ke a gidan ki kina nunawa Mijin ki ga Tsoron Allah'n ki a fili, amma kina fita waje kindawo Shu'uma kenan komai kina iya aikatawa ko a jikin ki. 

To a zahirin gaskiya, ba shi ake kira Takawa ba, an Tambayi Umar Allah yakara yarda gare shi, shin menene Takawa? Yace Misalin Takawa shine kina cikin Tafiya cikin dokar Dajin da yake da 'Kayoyi cikinta, kuma gashi Kafar ki babu Takalmi, to yaya zaki yi Tafiyar a wannan lokacin? 
       Ai a Lokacin sai kin tsaya sib, kin daidaita Sahu sosai hankalin ki ya tattaru waje guda, kin duba dakyau ina ne babu 'kayan nan, wajen ne kafar ki na farko zai fara sauka, sai ki sake dubuwa ina ne inda babu 'kayan sai ki sake ajiye dayan kafar ki, a haka ne zaki yi tayi har ki fita daga cikin wannan Dajin ba tare da wani 'Kaya ya tsoke ki ba, Umar yace wannan shine Misalin TAKAWA, 
 
Duk abinda Allah da Manzon Allah ki kaji ance ko kika karanta cewa lallai an yi Hani akai cewa aikata shi Haramun ne ga hukuncin shi, to sai Takawar ki ya sa ki ki guji wannan abun, Misalin yin Zina Haramun ne, to karma ashe kin kusan ce shi koda wasa, kusantar Zina shine yawan Kalamai na Batsa, yawan kallon hotuna wanda suke sirara ne, kollon videos na Batsa, Rungumar Namiji a matsayin ki Na Mace Musulma ta ko wanne fanni ne, Taba Jikin Namiji wanda shi ba Muharramin ki bane, yanzu harda Shan Minti ake yi, idan ma ke bakiyi Namiji zai ce baki waye ba, ko kuma kawar ki ta addabe ki cewa kai ya waye amma ke har yanzu baki waye ba, 
       Ina wayewa ana nan bayan kin sabawa Allah da Manzon Allah, ai babu Jahilcin da ya wuce wannan, gara ma ita da batayi sau dubu Dari taki wayewa nesa ba kusa ba, kuma kina mutuwa a wannan halin idan baki tuba kika daina ba, babu abinda zai hana daga Kabarin ki baki ga Azaban Allah Kala Kala ba, ai Shan Mintin ma a wajen wasu ke baki iya ba, kenan haka zakiyi ta ganin azaban Allah Kala Kala kamar yadda wata ko wani zai ce miki ai baki iya ba a sake chanja wani Kala, haka Mala'ikun Allah zasu yi ta chanja miki wani Kala Azaban har Ranan tashin Alkiyama,
       Wallahi kimar ki na Diya Mace Musulma wallahi ya wuce ki tsaya da Saurayi ba Auren ki yayi ba, ki tsaya ki bashi ko da tafin Hannun ki ne ya taba, Kimar ki ya wuce haka, wallahi 'Yan Mata kuyi Hattara kasani cewa Zaku mutu, sannan kisani cewa Zakiyi Aure nan gaba, Namiji mai Mutunci barai taba tsayawa yace zai yi irin wadannan abubuwan dake ba, duk wanda yace zai taba Jikin ki ko zai rungume ki ko zai yi Shan Mintin da ke, da suna Lallai shi yana son ki ne yana kaunar ki, yace miki ai yin hakan shine zai kara tabbatar miki da cewa ai yana kaunar ki, to ki Tambaye shi kiji, shin idan Kawan shi ne ko Kuma Misalin ace Diyar shi ne, Wani Namiji ya zo zai yi mata irin haka zai yadda ya bar su? Ki tamabaye shi haka, idan Yace Eh, kema kin san sauran, idan yace A'a kin san wani mataki yake a wajen ki, ya ku 'Yan Uwa na Mata kuyi Hattara a daina yaudaran ku da kalmar so da kauna, alhalin ba haka yake a cikin zukatan su ba, kawai suna neman wani biyan bukatan su ne, kuma da sun biya bukatan su shikenan sun bar ki babu yadda kika iya kuma, 
    ana shin zarafin ku da sunan ana son ku, ku kuma kuna yadda da abinda ake furta muku, baraki taba gane cewa lallai abinda kike yi ba daidai bane sai Lokacin da kika yi Aure kika Haihu, 
      Saboda haka, kin ji An ce Miki shan Giya ko kuma shan Wani Kayan Maye wanda zai gusar miki da hankalin ki a Lokacin guda Haramun ne, to duk wadannan abubuwan, sai Takawar ki ya sa ki, ki ki jinin wannan abun, 

Zalunci babu kyau, yin Gulma ko shaidar Zur Haramun ne, sai Takawar ki ya sa ki ki guji wannan, zuwa Fati ko Kauyawa Dance da dai Sauran su, Haramun ne tunda bawai ana cewa Allah yace Annabi yace a wajen ba, sai Takawar ki ya hanaki zuwa irin wadannan wuraren, kallon Batsa ko maganar Batsa Haramun ne, sai Takawar ki ya hanaki aikata su, sauraron wakoki Haramun ne, idan bawai na yabon Annabi bane, sai Takawar ki ya hanaki, 
        Idan har kin dauki Kafar ki kin bar cikin gidan ku to sai inda Allah yace Takawar ki yasa ki haka, idan kina yin magana a kullum ke bakin ki baya fadan abinda Shari'a bai yadda da shi ba, Takawar ki ya saka ki yin haka, abinda Allah yayi Hani ki hanu baki yin shi saboda Tsoron Allah, kada kiyi Allah ya kama ki a Ranan Alkiyama da laifin kin aikata abu kaza saboda yau azaba ya tabbata a kanki, kuma ke abinda Allah yace ayi kina yin shi akan lokacin sa kamar yadda Annabi yace ayi, ke baki Sakaci wajen yin shi saidai inda karfin ki bai je ba, da dai Sauran su, idan kin kasance a haka, to kinada Takawar ki, kuma indai kin tsaya a wannan hali naki, har Allah ya dauki Ranki da kina jin Tsoron shi, shiyasa kike bin duk wani hani da yayi, ki ga kin kare kanki daga aikatawa, to kin huta__________

Ku Biyo Mu a Fitowa Na Gaba in Allah Yakaimu. 

Daga Zauren Muslim Woman Mata Zallah 
WhatsApp Group. 

MUHAMMAD TUKUR JALINGO 
Domin Shiga Wannan Group Zai Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Kai Tsaye Ta WhatsApp Number Namu Kamar haka 
08164223447. 
This Is Only For woman Please.


Share:

ABOKAI NAGARI

✍🏻 *SHEAKH AMINU IBRAHIM DAURAWA KANO*

ABOKAI NA GARI 

Abokai iri uku ne :

1- Abokin tayi daɗi, abinda ya kawo shi abota da kai domin ya amfana da kai, ranar da yaga babu amfanin zai kama gabansa. 

2- Abokin aiki, wannan abota da shi, iya wajan aiki ne da zarar am gama aiki shi kenan sai kowa ya kama gaban sa. 

3- Abokin mai daraja mutunci, wanda zai kasance tare da kai, a dukkan mawayacin hali, ko kana da shi ko babu, shi yana kaunar ka saboda Allah kawai, ba domin wani abu na duniya ba. 
Wannan irin abokin yana da wahalar samu, idan ka samu irin sa ka riƙe shi da kyau. 

Idan za kayi abota kayi da masu hankali
Domin 
idan baka nan zasu kare mutunci ka. 
Idan basu ganka ba zasu nemeka. 
Idan ka samu zasu tayaka murna. 
Idan kayi kuskure zasu gyara maka. 
Idan za suyi addu'a ba zasu manta da kai ba. 
Idan baka da lafiya zasu duba ka suyi maka addu'a. 
Idan ka shiga wani hali zasu nuna damuwa da alhini. 
Idan sun ganka suna murna. 
Idan kayi kuskure za su yi maka gyara, cikin hikima. 
Idan zaa cuce ka zasu taimake ka.
Idan ka mutu zasu yi maka addua, kuma su taimaki iyalanka a bayanka.
Wanda ya rasa abokai na gari yayi asara. 
Allah ka bamu abokai na gari.

Shin muna da irin waɗannan abokan?

Share:

GIVING CHARITY TO WARD OFF CALAMITIES


Giving charity to ward off calamities

In the Name of Allah, the Most Gracious, the Most Merciful.

Abu Hurayrah, may Allah be pleased with him, narrated that the Prophet said, 

“There is no day in which the slaves rise in the morning except that two angels descend; one of them says, 'O Allah! Compensate the one who spends.' The other angel says, 'O Allah! Destroy the wealth of the one who is stingy.'” [Al-Bukhari and Muslim]

It is also confirmed that charity repels calamities, as stated in the hadeeth, “Doing good (to the people) protects one from misfortunes, secret charity extinguishes the anger of the Lord, and keeping ties with kinship increases one’s life span.” [At-Tabaraani - Al-Albaani classified it as hasan (good)]

Also, Anas, may Allah be pleased with him, narrated that the Prophet said, 

“Doing good (to the people) protects one from misfortunes, calamities, and destruction; and the people of goodness in this worldly life will be the people of goodness in the Hereafter.” [Al-Albaani classified it as saheeh (sound)]

Moreover, the hadeeth reported by Al-Bukhari and Muslim about the solar eclipse reads, “The Prophet said,

'When you see that [i.e. the eclipse], supplicate to Allah, say Allahu Akbar, pray, and give charity.'”

Ibn Daqeeq Al-‘Eed , when interpreting this hadeeth, said, “This hadeeth is evidence that charity is desirable when someone fears something in order to repel the misfortune that he fears.”

Imaam Ibn Al-Qayyim said in ‘Iddat As-Saabireen, “In charity, there are numerous benefits which no one can enumerate but Allah, among which is that it protects one from misfortunes and repels trials to the extent that it repels tribulations off an oppressor (i.e. charity repels tribulations even if it was given by an evil or an oppressive person). 

Ibraaheem An-Nakha'i said: 'They (the righteous predecessors) held that charity protects the oppressed man, wipes out the sin, preserves wealth, brings forth sustenance, brings joy to the heart, and necessitates having trust in Allah and thinking well of Him in the same manner that stinginess is mistrust in Allah.

Charity repels the devil, purifies one’s soul and develops it, endears the slave to Allah and to His creation, and conceals all his defects in the same manner that stinginess conceals every good trait.

Charity increases one’s life-span, incites people to supplicate for the person and to love him, repels the torment of the grave from the person, provides shade for him on the Day of Judgment, intercedes for him with Allah, eases the difficulties of this world and the Hereafter for him, and makes it easier for him to do all good deeds; indeed, its benefits are many times more.'”

Therefore, there is no harm in giving charity in order to attain what is confirmed in the Sharia as a promise to repel a calamity from the person who gives charity.

We ask Allah to make us charitable and save us from calamities. Aameen.

Allah knows best.
Share:

LALATA DA ƊALIBAI MATA A JAMI'O'I


LALATA DA DALIBAI MATA A JAMI'O'I

Idan Bera Da Sata...

Daga Maje El-Hajeej Hotoro

LAKCARA ba Mala'ika ba ne ba kuma Annabi ba ne da Allah Ya tsare shi daga dukkan sabo. 

Lakcara mutum kamar kowa da kwayoyin halittar SHA'AWA suke gudana a cikin jinin jikinsa.

Ba zai iyu ki sa fitinannun Tufafi masu farautar zuciya ki tashi nonuwa kamar kwan Kurciya. Ki baje duwawu kamar dutsen Dala da Goron dutse, ki shiga ofishin Lakcara kina kwarkwasa da iya shege don ki ci jarabawa ba. 

Kin ki karatu daga yawon banza da na wofi sai chatting da sa Hotunan TSIRAICI a Instagram, sannan a zo ana zagin lakcarori sun lalata ki ba. Dama can ke shegiyar kanki ce wacce taje Jami'a don ta bayar a ba ta.

Mu yakin mu akan matan kirki ne masu MUTUNCI da suka je Jami'a don Su yi karatu su ci jarabawa su zama abin alfahari gan al'umma. Wadanda BUNSURAYEN lakcarori ke yi musu barazana don yin lalata da su ta dole ko su kayar da su jarabawa.

Amma ke da kika dauki Jami'a a matsayin dandalin WAL BA NI WAL BA KA ba dake mu ke ba.

'Ya'yan Albarka a ci gaba da karatu a dage da addu'a gami da bin IYAYE. Idan matan aure ne a bi MIJI a kyautata shiga ta MUTUNCI a guji hulda da marasa MUTUNCI.

Allah Ya tsare mana IMANIN MU.
Share:

HANYOYI GOMA DON FITA DAGA BALA'I DA ƘUNCIN RAYUWA


HANYOYI GOMA DON FITA DAGA BALA’I DA KUNCI
DA DAMUWA

_(Sheikh Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo)_

Babu ko shakka kowa a yau ya san al’ummar
musulmi a duniya suna cikin halin kunci da
damuwa,don haka wajibi ne malamai da daliban
ilimi su ci gaba da haskawa al’umma hanyoyin da
ya kamata su bi don samun mafita daga wannan
bala’i da musifa.
Ga wasu hanyoyi goma da zamu runguma da izinin
Allah,Allah zai yaye mana wadannan musifu:


1-Kyautata imani da Allah da nisantar abin da yake
tauye imani.
Allah ya yi alkawarin
taimakon bayinsa muminai, da basu nasara akan
abokan gabarsu.Don haka matukar akwai imani da
Allah a zukatan bayi to Allah ba zai tozarta su ba.

2-Tuba da Istigfari
da Komawa zuwa ga Allah.

3-Yawaita ayyuka na kwarai,saboda ayyukan
kwarai sukan kawo wa zuciya nutsuwa,kamar
yadda munanan ayyuka sukan kawo wa zuciya
bakin ciki da damuwa da kunci.

4-Yawaita Sadaka : musammam ma a boye
ba tare da an sani ba,ya tabbata a hadisi Manzon
Allah S.A.W ya ce “Aikata kyawawan ayyuka suna
kawar da munanan abubuwa,sadakar boye tana
kawar da fushin Ubangiji,sada zumunci yana kara
tsawon rayuwa, dukkan aikin alheri sadaka
ne, masu aikin alheri a duniya,su ne ma’abota
alheri a lahira,masu munanan ayyuka a duniya, su
ne masu ma’abota mummuna a lahira,farkon
wadanda za su shiga Aljannah su ne masu aikata
kyawawan ayyuka”.Dabaran i ne ya rawaito shi.

5-Addu’a:
ba don addu’a ba da mutane da yawa sun
halaka.Allah
madaukakin Sarki yana jarrabar bayinsa da bala’i
don su koma gare shi,su kaskantar da kai da
addu’a, idan suka koma zuwa gare shi,suka
kasakantar da kai sai ya yaye musu.

6-Umarni da kyakkyawan aiki da hana mummuna :
Allah ba zai halaka al’umma ba,matukar akwai
masu umarni da kyakkyawan aiki da hana
mummuna.

7-Nisantar Zalunci Allah ya halakar da al’ummu da
yawa saboda zalunci.Mafi
girman zalunci shi ne shirka da kafirci,sai
zaluntar bayin Allah a cikin dukiyarsu da
mutuncinsu da jininsu,mu nisanci zalunci mu
zauna lafiya.

8-Zikiri wato ambaton
Allah,da baki da zuciya da gabbai.Da ambaton
Allah ne zukata suke nutsuwa.

9-Neman ilimin addinin musulunci :Al’umma
tana tsira daga halaka idan akwai malamai a
cikinta, wadanda za su kama hannunta daga duhu
zuwa haske, daga shirka zuwa
tauhidi,daga bidi’a zuwa sunnah.Duk al’ummar da
ta bar ilimin addini ta shagala
da na rayuwa to tana tare da kunci da bakin
ciki da rashin kwanciyar hankali.

10-Hakuri da Juriya : Hakuri wajen bin Allah,hakuri
wajen barin sabon Allah, hakuri akan abin da Allah
yabkaddara,samun nasara yana tare da hakuri. .

*Allah ka kara mana hakuri wajen yi maka da’a, da
barin abin da ka hana, ka yafe mana
kurakuranmu*.


*_Gabatarwa_*:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
Zauren
*Miftahul Ilmi*

Ga masu sha'awar shiga zauren *MIFTAHUL ILMI* a Whatsapp sai a turo da CIKAKKEN SUNA Zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsapp.
Share:

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...