Skip to main content

Posts

Showing posts with the label Fadakarwa (Awareness)

DANCING FOR NY HUSBAND 1

*DANCING FOR MY HUSBAND*

RUBUTU NA 0️⃣1️⃣

_✍️Wannan itace sabuwar shegantakar da shigo cikin wannan al'ummar ta musulmi_
إنا لله وإنا إليه راجعون!!!😔

Yan uwana Musulmai, idan muka kalli irin rayuwar da muke yi a yanzu zamu ga ta sha bambam da ta baya saboda fitintinu sun mana yawa, mune cikin yawan yaƙe-yaƙe, kashe-kashe, tsanantawa a wajen rayuwa, da kuma rashin adalci na shuwagabanni, tsadar rayuwa, tashe tashe hankula, kidnapping, fashi, sata, rashin albarka acikin rayuwa da makamantansu wanda hakan yay ta haifar da tambayoyi da yawa daga wajen mutane kan cewa: *_Mai Ya Kawo Wannan Musifun? Musamman mu anan arewacin Nigeria!?_*
*Mai muka yi muka cancanci wannan? Ina muka dosa ne acikin rayuwar nan? Kuma mene ne za mu yi don hana faruwar wannan alamura?*
Yayin da masu hankalin cikinmu suka zurfafa tunani da tantance abinda ya haufar mana da wadannan fituntinu se suke kokarin gano amsar wadannan tambayoyi.👇

shin muna yin rayuwarmu ne ta fuskar bin maganar Allah - (Alqur’ani) - da kum…

KIYAYE ABINDA YAKE DAIDAI SHI NE MAFI WAHALA A WANNAN ZAMANI

*KIYAYE ABIN DA YAKE DAIDAI SHINE MAFI WAHALA A WANNAN ZAMANI!*

Abu ne mai sauki mutum ya ya ɓata dare baki ɗaya yana kallo da chartings da downloadings da sauraron waƙoƙi. Amma abu ne ami wahala a gare shi ya ya tashi yayi sallar tahajjud a daya biya ukun dare, balle yaje sallar asuba.
Abu ne mai sauki a wajen 'yan matan yanzu da burgewa su saka kaya matsattsu da fidda tsiraicinsu da shapes din jikinsu. Amma abu ne mai matukar wahala a wajensu su saka hijjabi da niqabi su rufe jikinsu da kyau.
Abu ne mai sauki a wannan zamanin ƙawata alfasha da yi mata kwaskwarima da daukanta wayewa da burgewa wajen yadawa acikin mutane da kuma koya musu ita, ta hanyar mace ta dinga rawa a gaban mijinta ko suna rungumar juna da sunan wai soyayya, amma abune mai wahala a wajen irin wannan mutanen yin Umarni da kyakkyawa ta hanyar da ya dace da koyarwar addinin islama! 
Abu ne mai sauki yanzu ayi gulma a ci naman wani wanda yayi daidai ko akasin haka. Amma abu ne mai wahala wajen kare da tsare mutuncin…

RUFE MASALLATAI SABODA ANNOBAR CORONAVIRUS

RUFE MASALLATAI SABODA ANNOBAR KORONA
Rubutawar Abdulmajid Muhammad Umar
22/Ramdana/1441 Birnin Madina, KSA Da sunan Allah Mai rahama, Mai jin kai. GABATARWA Godiya ta tabbata ga Allah, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad SAW da alayensa da sahabbansa gaba daya. Bayan haka, hakika duniya ta samu kanta a wani yanayi wanda ya canja abubuwa da yawa; na addini da rayuwa. Duk da cewa malamai a wannan zamani sunyi sabani akan hukucin rufe masallatai, hakan bai hana a yi rubutu kan hukucin hakan a ilmance.
KAFIN NA TSUNDUMA CIKIN AINIHIN BAYANI KAN RUFE MASALLATAI, AKWAI WASU MUHIMMAN GINSHIKAN DA YA KAMATA MAI KARATU YA SANI; Allah Ya kara mana fahimta, Ya ba mu kirji mai yalwa, Ya kara mana sani a addini, Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce, Ya ba mu ikon bin ta, Ya nuna mana karya karya ce Ya ba mu ikon guje mata.
Na Farko: A Musulunci akwai hukunce-hukunce da suke banbanta tsakanin daidaikun mutane ko wani bangare na mutane da kuma gaba daya al’uman gari ko kauye; misali:  Misali Na Farko: Kira…

BARKA DA DAWOWA GIDA MALAM BELLO YABO

*BARKA DA DAWOWA GIDA MALAM BELLO YABO* 
Ahlus Sunna a Nigeria shi ne wanda yake aiki da Hadisan Annabi (saw) tare da bin Alƙur'ani, kuma bai kasance Ɗan Ɗariƙa ko Ɗan Shi'a ko Ɗan Boko Haram ba.
Daga cikin babukan da Hadisan Annabi (saw) suka zo da yawan gaske, akwai babin mu'amala da shugabanni. In ka cire babin Tsarki da Sallah, wannan babin yana daga cikin babukan da Hadisai masu yawa suka zo suna bayani a kansa. Saboda haka bai kamata a ce Ahlus Sunna ya manta da waɗannan Hadisai ko ya jahilce su ba.
A cikinsu Annabi (SAW) ya shiryar da mu yadda za mu mu'amalanci shugabanni, saboda ya san al'ummarsa sun zo ne a ƙarshen zamani, lokacin da kwaɗayin abin Duniya zai yawaita, ake neman mulki da faɗa a kansa ido rufe. Kuma da ma mulki da dukiya su ne suke janyo fitina a tsakanin mutane, har ya kai ga zubar da jinane da asarar rayuka da haifuwar fitina a tsakanin al'umma.
Annabi (SAW) ya nuna mana cewa; za a samu shugabanni masu ƙirƙiro munanan abubuwa, masu aikata …

AMURKA TA ƘIRƘIRO CORONAVIRUS, TO AKA YI VIRUS ƊIN YA KE KASHE SU?

*AMURKA TA KIRKIRO CORONA-VIRUS, TO YA AKAYI VIRUS DIN KE KASHE MUTANEN AMURKA?*
Wannan jawabin Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto yayi su cikin darasin da ya gabatar ranar asabar da wanda ya gabatar a satin da ya gabata, ku daure ku karanta har karshe
Mutane da yawa sun kasa faimtar wacece Amurka, Amurka fa, wacce muke magana a kanta, muna magana ne akan 'yan kungiyar asiri na "Freemasons" (Masoniyyah), Illuminati, wadanda suke so su kafa "World Totalitarian Government", gwamnatin duniya, wanda ba ma cikin Amurka za'a ajiye Headquarter dinta ba, a cikin Kasar Isra'ila ne za'a ajiye, kuma "Greater Israel" wacce zata game har Makkah da Madinah, inda za'a rusa dakin Ka'abah a kori mutane daga garin Madinah, shekaru 40 masallacin Annabi a mayar dashi dakin ajiye dabbobi, zoo, don haka bala'i ne mai girma za'a fuskanta nan gaba, idan akace Allah mutane ba su ma san me ake nufi ba a lokacin 
Wallahi wajen kafa wannan gwamnatin duk abi…

KWANAKIN WATAN RAMADAN SUN ƘARE

KWANAKIN WATAN RAMADHAN YA KARE, AMMA HAKKOKIN ALLAH BA SU KARE WA AKANKA SAI RANAR DA YAKININ KA (MUTUWAR KA) TA RISKE KA.
ALLAH Yace'; ka bauta wa UBANGIJIN ka har sai yakini (mutuwa) tazo maka !
ALLAH shine UBANGIJIN watan RAMADHAN, da kuma watan shawwal kuma shine UBANGIJIN dukkan sauran watanni na sheka gaba-daya !
Ka zamto mai tsoron ALLAH cikin dukkanin watanni kuma ka kiyaye addinin ka cikin dukkan rayuwar ka, domin addinin ka shine kan dukkan abunda kake da shi a wurin UBANGIJIN KA tsarkakakke maɗaukaki, kuma riko da addini shine zai tseratar da kai daga wuta, don haka ka kiyaye addinin ka kayi riko da shi cikin dukkanin watanni da kuma lokuta ! 
Muna fara BIBIBIYAR watan watan RAMADHAN ne da godiya ga ALLAH, sai kuma istigfa'ri, sa'annan mu bi ta da farin ciki da falalar ALLAH da ya bamu ikon azumtan ta da kuma tsayuwar ta zuwa karewar ta ! 
Muna farin ciki da wannan ni'imar da ALLAH ya azurta mu ne, ba wai muna farin ciki bane da karewar ta, muna farin ciki da sam…

TSAKANIN MU DUK DA BANBANCINMU 28

*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//28📿*
*GINSHIQI NA 27*
*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*
HANYAR GYARA
Mun yarda da cewa wane ya saki hanya a maganganunsa ko a ayyukansa? Amsar ita ce "I" to shiriya yake buqata yanzu, galibin wanda yake sakin hanya gani yake kamar ya fi ka zama daram a kanta, sai dai a hankali in ka nuna masa kuma aka yi dace da shiriyar Ubangiji sai ya ga kuskurensa ya karbi gyaran, to kai mai gyaran in ka sami mai kuskure a tsakiyar 'bata kar ka matsa ta kowace hanya sai ya bar kuskuren nan take, ka bi a hankali, ba buqatarka a ce ka fadi gaskiya komai dacinta albashi mutum ya tafi da kuskurensa ba, ko kai ne kadai kake iya gaya wa wane gaskiya kai tsaye, a'a, burinka dai shi ne a bar kuskuren a koma kan abinda yake daidai.
A wani hadisi na Anas bn Malik yake cewa: Wata rana muna zaune a masallaci tare da Annabi SAW kwatsam sai wani baqauye ya shigo ya kama fitsari, nan take sahabbai suka yi masa ca! "Kai! Kai!!" Sai Annabi SAW ya ce "Kar …