Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

Showing posts with label Fassarar Kalaman Fim. Show all posts
Showing posts with label Fassarar Kalaman Fim. Show all posts

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KABHI KABHIEFassarar Kalaman Fim Ɗin Kabhi Kabhie


Shekarar Fita - 1976


• Aapne kabhi apni aankhen dekhi hai? ... jahan dekhti hai ek rishta kayam kar leti hai

Shin kin taɓa kallon idanuwanki kuwa?... Duk inda suka kai duba, alaƙa suke ginawa. 

 Amitabh Bachchan

• Kabhi raste mein mil jao toh katrakar guzar jana ... hum mein is tarah takna jaise pechana nahi tumne ... hamara zikr jab aaye toh yun anjaan ban jana ... ki jaise naam sunkar bhi hum mein jana nahi tumne

Idan ki ka ganni a hanya to kauce ki wuce... Ki kalle ni kamar ba ki san ni ba... Idan kuwa har sunana ya fito daga bakinki cikin rashin sani... Ki ɗauka cewa ba ki sanni ba ko da kin ji sunana. 

 Amitabh Bachchan

• Tera haath, haath mein ho agar ... toh safar hi asle-hayaat ha i ... mere har kadam pe hai manzilein ... tera pyar gar mere saath hai

Da ace hannunki nawa ne... To tafiyar ita kanta rayuwa ce... Kuma akwai bigire a kowane takuna... Idan soyayyarki ta kasance tare da ni. 

Amitabh Bachchan

• Mere dil ka woh hissa ... kambakht mera kab tha

A wannnan ɓangaren na zuciyata... Jahannama ba tawa bace. 

 Amitabh Bachchan

• Meri baat ka meri humnafas, tu jawab de ki na de mujhe ... teri ek chup mein joh hai chupi, woh hazaar baaton ki baat hai

Ya ke rayuwata ko da ba ki bani amsar tambaya ta ba... Shirun da ke ɓoye tare da ke ya bani amsar tambayoyi dubu. 

 Amitabh Bachchan

• Meri zindagi ka har ek pal, tere husn se hai judha hua ... tere honth thirke toh subah hai, teri zulf bhikre toh raat hai

Kowane lokaci na rayuwata, manne yake da jikinki... Duk sanda laɓɓanki suka motsa to safiya ce, duk sanda kika buɗe gashinki kuma dare ne. 

Amitabh Bachchan

• Is duniya mein aadmi insaan ban jaye ... toh bahut badi b aa t hai

• A wannan Duniyar, idan mutum ya zama ɗan adam... Ba ƙaramin al'amari bane. 

Shashi Kapoor

• Tum insaan ke roop mein devta ho ... yah devta ke roop mein insaan

Shin kai ubangiji ne a siffar mutane... Ko kuma mutum ne a siffar ubangiji? 

Rakhee Gulzar

• Zindagi chand sawaal aur kuch jawaab hi toh bankar reh jaati hai

A ƙarshe rayuwa kan zamo wasu 'yan tambayoyi ne kawai da wasu amsoshi. 

 Rakhee Gulzar

• Main zara romantic kisam ka aadmi hoon ... s ha adi ke baad ishq karna toh chhod diya hai ... is liye biwi se romance karke kaam chala leta hoon

Ni mutum ne mai soyayya kaɗan... Kuma na daina kula mata tun da na yi aure... Hakan ya sa na ke rayuwata ta hanyar kula matata. 

 Shashi Kapoor 

• Aap sooch kuch aur rahen hain ... pooch kuch aur rahen hain

Abin da kike tunani daban... Abin da kike tambaya daban. 

 Amitabh Bachchan


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com


Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN DILWALE DULHANIA LE JAYENGE


Fassarar Kalaman Fim Ɗin Dilwale Dulhania Le Jayenge


Shekarar Fita - 1995

• Toh kya hua agar maine jhoot sirf tumhe paane ke liye kaha tha ... toh kya hua agar tumhare chehre ke sivah mujhe koi aur chehra dikhai nahi deta ... toh kya hua agar tumhare naam ke sivah mujhe koi aur naam yaad nahi rehta ... toh kya hua agar yeh awara tumhe deewano ki tarah pyar karta hai ... toh kya hua ... pyar sab kuch toh nahi hota na. 

Sai me don na yi ƙarya saboda in same ki... Sai me don bana iya ganin fuskar kowa face taki... Sai me don bana iya tuna kowane suna face naki naki... Sai me don wannan taƙadarin yana sonki kamar hauka... Sai me... Tun da dai so ba shi ne komai ba. 

Shah Rukh Khan 

• Mohabbat ka naam aaj bhi mohabbat hai ... yeh na kabhi badli hai aur na kabhi badlegi

Har zuwa yau dai shi so sunan shi so... Sunan bai canja ba kuma ba zai taɓa canjawa ba. 

Anupam Kher 

• Koi bhi ullu ka patha sirf ek angoothi pehanakar tumko mujhse nahi cheen sakta ... tum meri ho, sirf meri. 

Babu wani sokon da zai iya ƙwace min ke ta hanyar sa miki zobe a hannu... Ke tawa ce, tawa kawai. 

Shah Rukh Khan 

• Main ek Hindustani hoon ... aur main jaanta hoon ki ek Hindustani ladki ki izzat kya hoti hai. 

Ni ɗan Indiya ne... Kuma na san irin darajar da 'yar Indiya ke da shi. 

Shah Rukh Khan 


• Joh shaadi waale ghar mein seva karta hai ... usko bahut sundar dulhan milti hai

Masu taimako a gidan da ake ɗaurin aure... Sukan samu kyawawan mata. 

Shah Rukh Khan 

• Agar yeh tujhe pyar karti hai toh yeh palat ke dekhegi ... palat ... palat!

Idan har tana sonka to za ta juyo ta kalle ka... Juya... Juya... 

Shah Rukh Khan

• Jab ladki jawan ho jaati hai na ... toh maa uski maa nahi rehti ... sehali ban jaati hai

A yayin da budurwa ta tasa... To mahaifiyarta ta tashi daga matsayin mahaifiya kuma... Ta zama ƙawarta kenan. 

Farida Jalal

• Bade bade deshon mein aaisi choti choti baatein ... hoti rehti hai

A manya-manyan birane irin waɗannan ƙanana-ƙananan abubuwan... Na ci gaba da faruwa. 

Shah Rukh Khan

• Ja Simran ... ja jeele apni zindagi ... ja beta ja
Go Simran ... go live your life ... go my child go

Amrish Puri 

• Agar tum galat raaste par chaloge ... toh ho sakta hai shuruvat mein tumhe bahut kamyabi mile, bahut khushiya mile ... magar anth mein tumhari haar hogi ... aur agar sahi raaste par chaloge ... toh bhale hi shuruvat mein tumhe kadam kadam par thokarein mile, musibaton ka samna karna pade, pareshani ho ... magar anth mein hamesha jeet hogi

Idan ka hau kan mummunar hanya... Ta yiwu da fari za ka samu nasara sosai da farinciki.. 
Amma a ƙarshe ba za ka yi nasara ba... Idan kuwa ka hau hanyar daidai... Ta yiwu da fari za a ƙi yarda da kai a kowane taku, za ka fuskanci ƙalubale da matsaloli... Amma a ƙarshe kai me za ka yi nasara. 

Shah Rukh Khan 

• Dimaag mein kitaaben bharne se jeben thodhi bharti hai

Ba ka iya cika aljihunka (da kuɗi) ta hanyar cika ƙwaƙwalwarka da Littattafai.

Anupam kher

• Zarooraton ne par kaat diye hai ... roti paon ki zanjeer ban gayi hai

Buƙatu sun datse fuka-fukaina, biredi ya zama sasarin ƙafata.

Amrish Puri 

• Fail hona aur padhai na karna ... hamare khandaan ki parampara hai

Faɗuwa da rashin karatu... Al'adun ahalinmu ne. 

Anupam Kher 

• Tumhari jaisi ladki ke saath, mere jaise ladke ka hona ... bahut zaroori hai

Abu ne mai muhimmanci wa budurwa kamar ki ta samu gaye kamar ni. 

Shah Rukh Khan 

• Ek pal mein beta bana liya ... aur doosre hi pal mein paraya kar diya

Lokaci ɗaya kun maida ni ɗanku... A lokaci na gaba kuma sai kuka maida ni baƙo. 

Shah Rukh Khan 


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KARAN ARJUN

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KARAN ARJUN

Shekarar Fita - 1995 


• Paison ke mamle mein main pehdaishi kamina hoon ... dosti aur dushmani ka kya, apno ka khoon bhi pani ki tarah baha deta hoon

Idan ana batun kuɗi to ni cikakken ɗan ƙwal uba ne... Bar ta abokai ma, jinin mutanena ma zubar da shi nake yi kamar ruwa. 

Amrish Puri 

• Main toh budhi ho gayi, meri aankhen kamzor ho gayi ... lekin mera vishvas kamzor nahi hua

Na tsufa, idanuwana sun yi rauni... Amma imanina bai yi rauni ba. 

Rakhee Gulzar

• Main toh samajhta tha ki duniya mein mujhse badkar kamina aur koi nahi hai ... lekin tumne end mauke par aaisa kaminapan dikhaya hai ... ki hum tumhare kaminepan ke ghulam ho gaye hai

A da ina tunanin ni ne babban ɗan iska a duniya... Amma a ƙarshe kun nuna min yadda iskanci yake... Ta yadda har ma na zama bawanku a iskanci. 

Amrish Puri 

• Hum khandani Thakur hai ... hamari ragon mein khoon ke saath saath zid aur ahankaar bhi daudta hai

Ni shugaba ne daga babban ahali... Haɗe da jini, kangara da izza ce ke gudana a cikin jijiyoyina. 

Amrish Puri 

• Bhavnao ki chot jab dil par lagti hai ... toh nafrat ki jwala badakh uthti hai

Yayin da aka baƙantawa mutum... Wutar ƙiyayya ke ruruwa. 

Rakhee Gulzar

• Kiss gaalon pe nahi ... hoton pe kiya jata hai

Ba a kumatu ake sumba ba... A laɓɓa ake yi. 

Shah Rukh Khan

• Tere saare khandaan ki maut ... mere haath ki lakeeron mein likhi hai

Mutuwar ahalinku gaba ɗaya... Rubuce yake a layukan tafin hannuwana. 

Amrish Puri 

• Zindagi mein joh hota hai woh socha nahi hota ... aur joh socha jata hai woh kabhi hota nahi ... aur joh kabhi nahi hota, woh kabhi kabhi ho jata hai

A rayuwa abin da ke faruwa ba shi ake tunani... Kuma abin duk da aka yi tunani ba ya taɓa faruwa... Kuma abin da bai taɓa faruwa ba, wani lokacin shi ke faruwa. 

Kajol 

• Bhudhape mein jism bekaar ho jaate hai ... lekin tune toh apni zindagi hi bekaar kar di

A yayin tsufa jiki kan zama maras amfani... Amma ke rayuwarki kika mayar maras amfani. 

Amrish Puri

• Mere bete aayenge, mere Karan Arjun aayenge ... zameen ki chaati phad ke aayenge, aasman ka seena cheer ke aayenge

Yarana za su zo, Karan da Arjun ɗina za su zo... Za su keta ƙirjin ƙasa su zo, za su keta ƙirjin samaniya su zo. 

Rakhee Gulzar

• Hamare ghar ki bahu betiyan jab kabhi beizzati ke daldal mein kadam rakhti hai ... toh hum unhe haveli ki char deewari mein zinda chunwa dete hai

A duk lokacin da 'ya'ya mata ko surikai mata suka tafka abin kunya a ahalinmu... Binne su muke yi da ransu a ƙusurwoyi huɗun gidan. 

Amrish Puri 

• Waqt ka marham ... zindagi ke har zakhm ko bhar deta hai

Lokaci shi ne maganin da... Ke cike kowane gurbin ciwo. 

Rakhee Gulzar

• Mere dushmano ko sar chupane ke liye jagah dene waalon ... main tumhari chittaon ko jalne ke liye jagah nahi doonga

Ku da ke ba maƙiyana wurin zama... Ni ko ƙaburburanku ba zan ba wurin ƙonawa ba. 

Amrish Puri 

• Marte insaan ki antim ichcha poori karna ... is sansar ka sabse bada punya hove hai

Cika burin mamaci... Shi ne nagarta mafi girma a duniyar nan. 

Ashok Saraf

• Daulat se insaan keemti bistar khareed sakta hai, magar neend nahi khareed sakta ... daulat se insaan roti khareed sakta hai, magar bhook nahi ... daulat se insaan jism khareed sakta hai, magar sacha pyar nahi khareed sakta

Mutum na iya siyan gado mai tsada in yana da kuɗi, amma ba zai iya siyan bacci ba... Mutum na iya siyan biredi in yana da kuɗi, amma ba zai iya siyan yunwa ba... Mutum na iya siyan jiki idan yana da kuɗi, amma ba zai iya siyan soyayyar gaskiya ba. 

Kajol 

• Apne raaste se kaanto ko hata dena aur dushmano ko mita dena ... hamare khandan ki parampara hai

Kawar da ƙayoyin hanyar mu da kuma kau da maƙiyanmu... Waɗannan su ne al'adun gidanmu. 

Amrish Puri 

• Aaisi maut maroonga is kamine ko ... ki bhagwan yeh punar janam waala system hi khatam kar dega

Zan kashe wannan ɗan iskan ta yadda... Ubangiji ma da kansa zai daƙile wannan tsarin na sake haihuwar mutum. 

Amrish Puri 

• Pyar mein jab tak maut se na khelo ... milne waali zindagi ka mazaa nahi aata

Matuƙar ba ka yi wasa da mutuwa ba a soyayya... To babu wani jin daɗi a rayuwar da ka samu. 

Shah Rukh Khan 

• Daayan haath jeb mein rakh lo seth ... varna zindagi bhar aapko baayen haath se khana, khana padega

Bar hannunka a cikin aljihu... Ko kuma ka koma cin abinci da hagu har tsawon rayuwarka. 

Salman Khan 

• Khoon ki Holi khelne waale, aaj main dekhti hoon ... khoon kiska behta hai aur laashein kiski girti hai

Ka yi bikin Holi da jini, amma yau zan gani... Jinin waye zai zuba kuma gangar jikin waye za ta faɗi. 

Rakhee Gulzar

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com


Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN SULTAN

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN SULTAN

• Shekarar Fita - 2016


• Asli wrestler woh nahi hota joh medal uthaye ... asli wrestler woh hota hai joh zindagi se lade aur usse haraye

Ɗan kokawa na asali ba shi ne wanda ya ɗaga lambar yabo ba... Ɗan kokawa na asali shi ne wanda yake faɗa da rayuwarsa kuma ya yi nasara a kanta. 

Salman Khan 

• Izzat aur guroor mein dhaage bhar ka pharak hove hai

Banbancin da ke tsakanin girmamawa da kuma girman kai ba shi da kauri kamar zare. 

Anushka Sharma

• Hindustan apno ka, rishton ka, mitti ki value ka desh hai

India ƙasa ce ta waɗanda kake so, waɗanda kake mu'amala da su kuma darajar ƙasarka ce. 

Parikshat Sahni

• Manne lage hai ki angrezi mein ladki jaldi pate hai ... I love you bolo aur uske baad seedha kiss hove hai

Ina jin cewa budurwa ta fi saurin faɗawa da wuri idan ka yi mata turanci... Kawai ka ce mata I love you nan take sai sumba ta biyo baya. 

Salman Khan 

• Maine usse ladte huye dekha hai ... uske zor mein hosh hai aur hosh mein josh hai ... jeetna uska shauk nahi, uski aadat hai ... aur harana uski aadat nahi, uska hunar hai ... uski aankh mein bijli aur baazu mein dum hai ... uska ek daav, dus ke barabar hai

Na ganshi yayin da yake faɗa... A cikin faɗan nasa akwai wayar da kai, kuma a cikin wayar da kan akwai soyayya... Cin nasara ba wai aikinsa bane, halinsa ne... Yin nasara ba halinsa bane, basirarsa ce... Akwai walƙiya a idanuwansa da kuma ƙarfe a damatsansa... Naushinsa ɗaya shi ne goman na wasu. 

Parikshat Sahni

• Kahi baar dard ka ilaaj dard hi hove hai

Sau da dama maganin zafi shi ne zafin kansa. 

Anushka Sharma

• Wrestling koi khel nahi hai ... yeh woh dangal hai joh insaan apni zindagi mein apne aap se ladta hai

Kokawa ba wasa bane kawai... Yaƙi ne da mutum ke yi a rayuwarsa da kansa. 

Salman Khan 

• Agar tune aaj give up kiya ... toh shayad bahar se zinda reh jaye ... magar andar se mar jayega hamesha ke liye

Idan ka karaya yau... To wataƙila ka rayu... Amma ta ciki za ka zama matacce har abada. 

Anushka Sharma

• Kisaan aur pehalwan mein ek hi cheez ek jaise hove hai ... woh hai maati

Abu ɗaya ne ya kamanta manomi da ɗan kokawa... Shi ne ƙasar da aka haife su a ciki tare.

Salman Khan 

• Asli pehalwan ki pehchaan akhade mein nahi, zindagi mein hove hai ... taki jab zindagi tumhe patke toh tum phir khade ho ... aur aaisa daanv maro ki zindagi chitt ho jaye

Mafaɗacin gaske ana iya gane shi a rayuwa, ba wai a filin dambe ba... Saboda ka miƙe yayin da rayuwa ta kada kai... Sannan ka yi wasa irin yadda sai ka yi nasara akan rayuwa. 

Salman Khan 

• Woh dus maarenge aur tu ek maarega ... us ek mein dus ka vazan hoga

Zai doke ka sau goma, za ka dake shi sau ɗaya... Wannan ɗaya zai maye gurbin goman. 

Randeep Hooda

• Koi tumhe tab tak nahi hara sakta ... jab tak tum khud se na haar jao

Babu mai iya kada kai... Har sai ka rasa kanka. 

Salman Khan 

• Khud ko Shahrukh Khan samjhe hai ke? ... Shahrukh ka mazaak mat udhao ... manne bahut pasand hai ... jab woh ladki ke aankh mein aankh daalke dekhe hai na toh andhi ladki bhi patt jaave hai

A tunaninka kai Shah Rukh Khan ne?... Kada ka yi ba'a wa Shah Rukh... Ina son shi sosai... A duk sanda ya kalli idanun yarinya, to ko makauniya ce sai ta kware masa. 

Salman Khan 

• Sapne dekhna achchi baat hai ... par kahi baar unke peeche daudte daudte na apne peeche choot jaate hai

Abu ne mai kyau ka zama mai mafarkai... Amma a wasu lokutan idan ka biye musu sai ka rasa masoyanka. 

Anushka Sharma

• Yeh joh tumhari society hai na ... is mein aaj bhi ladkiyan ghunghat ke peeche janam leve hai aur wahin mar jaave hai

A cikin wannan al'ummar taku... Har yau mata ana haihuwarsu ne a bayan labule kuma a nan suke mutuwa. 

Anushka Sharma


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN JODHAA AKHBAR

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN JODHAA AKHBAR

• Shekarar Fita - 2008


• Sikka girne par awaaz hoti hai... uthate waqt nahi

Akan samu ƙara ne kawai yayin da sule ya faɗi ƙasa... Ba lokacin ɗauka ba. 

Hrithik Roshan

• Kisi bhi insaan ka dil jeetne ke liye ... uske mann mein jhankna padta hai ... uski choti choti khushiya, choti peedayein, vishvas aur dhadkano se judna padta hai

Domin cin galabar zuciyar mutane... Akwai buƙatar ka leƙa cikin zukatansu... Kana buƙatar ka haɗu da ƙananun farincikinsu, ƙananun matsalolinsu, imaninsu da kuma bugun zukatansu. 

Aishwarya Rai

• Zindagi ki khushiyo ka batwara ... shunk aur azaan ki awaaz se tay nahi hota

Rarrabuwar farincikin rayuwa... Ba yanke shawara ce na buga tambari da ƙarfin mulki ba. 

Hrithik Roshan

• Har prem ki buniyaad vishvas hai

Imani shi ne tubalin kowace soyayya. 

Aishwarya Rai

• Har mazhab ka ehtram aur bardaash karne ki chahat hi ... aane waale Hindustan ko sunhera bana sakti hai

Mutunta kowane irin addini da kuma burin jure shi... Shi zai maida Indiyar gobe babbar ƙasa. 

Hrithik Roshan

• Uttarte hue suraj mein bhi bahut tapish hoti hai

Ranar da ke gab da faɗuwa ita ma tana da zafi. 

Hrithik Roshan

• Hukm ki tameel ho!

Dole ne a cika umurnina!

Hrithik Roshan

• Pani aur tamannao ki taseer ek hai ... aage badhte jaana

Burin ruwa da kuma muradi duka ɗaya ne... Ci gaba da tafiya. 

• Fateh karne aur raaj karne mein bahut fark hota hai

Akwai babban banbanci a tsakanin yin nasara da kuma mulki. 

Hrithik Roshan

• Hum Hindustan ko galat haatho mein nahin jaane denge

Ba zan taɓa bari Indiya ta faɗa mugun hannu ba. 

Hrithik Roshan

• Wafaadari ka jazba kabhi kabhi insaan ko gustakh bana deta hai

Son gaskiya wani lokacin kan sa mutum ya zamo ƙaƙarfa. 

Hrithik Roshan

• Yeh hamara mulk hai ... aur hum iske jism par loot ke zakhm nahin dekh sakte

Wannan ƙasata ce... Kuma ba zan iya jure ganin alamomin zamba a jikinta ba. 

Hrithik Roshan

• Jung ki sabse azeem khubi ... bina shamsheer aazmaye dushman ki deewar gira dene mein hai

Mafi kyawun fannin yaƙi... Shi ne ka karya katangar maƙiya ba tare da ka ɗaga Takobi ba. 

Hrithik Roshan

• Kitna bhi chamke ... peeth peeche har aaina kaala hi hota hai

Duk iya ƙyallin da zai yi... Kowane madubi baƙi yake daga baya. 

Ila Arun


©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com


Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN WAR

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN WAR

• Shekarar Fita - 2019


• Mauka mile toh goli chala dena, sochna mat ... main nahi sochunga

Idan ka samu dama ka harba harsashin, kada ka yi tunani... Saboda ba zan yi tunani ba. 

Hrithik Roshan

• Hum bhi chal rahe the ... saaye bhi wahan the ... ishaare the kitne ... samajhdaar kahan the

Tafiya nake yi... Hatta inuwata ma tana nan... Akwai alamomi da dama... Amma ina mutane masu basira suke? 

Tiger Shroff

• Sabse pehle watan ... uske baad watan ... aur aakhir mein watan

Ƙasata ce a farko... Bayan nan kuma sai ƙasata... Kuma daga ƙarshe hallau ƙasata dai. 


Tiger Shroff

• Match khatam hone se pehle jeetni ki poori koshish karo ... bhaago, daudo, khelo, ladho, sab kuch ... par ek baar match khatam ho jaaye toh yeh mat socho ki tum haare ya jeete ... balki apne aap se yeh poocho, ki did I give it my very best or not ... aur agar tumhara jawaab haan hai ... then you're a winner

Ka yi iya ƙoƙarinka wajen ganin ka yi nasara a wasan kafin ya ƙare... Ka yi gudu, tsere, wasa, faɗa ka yi komai... Amma da zarar wasan ya ƙare, to kada ka yi akan ka yi nasara ko ka faɗi... Maimakon haka ka tambayi kanka shin na yi duk abinda zan iya ko a'a... Idan har amsarka ta zama eh... To kai ne ka yi nasara. 

Hrithik Roshan 

• Aap kisi aur tak pahunche ... usse pehle main aap tak pahuchunga

Kafin ka kai ga wani... Ni zan kai gareka. 

Tiger Shroff


©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com


Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KICK


FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KICK

Shekarar Fita - 2014

Fassarawa - Jamilu Abdurrahman

• Pehda toh main bhi sharif hua tha ... par sharafat se apni kabhi nahi bani

Nima kaina da gaskiya aka haife ni... Amma na kasa ci gaba da rayuwa da gaskiyar. 

Nawazuddin Siddiqui

• Mere bare mein itna mat sochna ... dil mein aata hoon ... samajh mein nahi

Kada ki yi tunani a kaina... A cikin zuciya nake... Amma ina da wuyar fahimta. 

Salman Khan

• Rishtey ko mazboot hona chahiye ... majboor nahi

Kamata ya yi ace alaƙa ta zama abu mai ƙarfi... Ba abinda za a kasa taimakawa ba. 

Salman Khan

• Ek ek paisa gin lena thook laga ke ... yeh ho na ho hum toh traditional kaminey log hai
Count every note with your 

Ka ƙirga kuɗin da yawu... Ta yiwu shi ba haka yake ba, amma mu 'yan iskan gargajiya ne. 

Nawazuddin Siddiqui

• Machli chahe kitni bhi tezz ho ... ek baar kaante mein phas jaye toh kilo ke bhav bikti hai

Komai hanzarin kifi... Da zarar ya shiga ƙugiya, to a kilo za a siyar da shi. 

Randeep Hooda

• Izzat, zillat, shohrat aur maut ... upar waale ke haath mein hai

Daraja, tozarci, arziƙi da mutuwa... Duk a hannun ubangiji suke. 

Mithun Chakraborty

• Aap devil ke peeche, devil aapke peeche ... too much fun

Kana Bayan shaiɗan, shaiɗan na bayanka... Nishaɗin ya yawaita. 

Salman Khan

• Mujhse joh dushmani modh leta hai ... uspe uparwaala reham toh kar deta hai, magar main nahi

Wanda duk ya zama maƙiyina... Ubangiji na iya yafe masa... Amma ba ni ba. 

Salman Khan

• Koi umeed bar nahi aati, koi soorat nazar nahi aati ... maut toh ek din moiyan hai, neend raat bhar kyun nahi aati ... pehle aati thi haal-e-dil pe hassi, ab kisi baat pe nahi aati

Babu wata fata da za a yi, babu kuma wani sulhu da za a samu... Mutuwa ƙaddara ce da sai ta zo watarana,amma me ya sa na kasa bacci tsawon dare... Da fari dariya nake yi akan damuwar zuciyata, amma yanzu kuma na kasa dariya akan komai. 

Nawazuddin Siddiqui

• Main case aur face kabhi nahi bhoolta hoon

Ba na manta taƙaddama da kuma fuska. 

Randeep Hooda

• Jisse zindagi ki parvah hoti hai ... maa kasam maarne ka mazaa us hi ko aata hai

Irin masu damuwa da rayuwa ɗin nan ko... Na rantse da mahaifiyata kashe su akwai daɗi. 

Nawazuddin Siddiqui

• Chehre par gussa, mann mein gaali ... goli bhi chalali ... phir bhi dono haath khali

Akwai fushi a fuskarka, tsinuwa kuma a cikin zuciyarka... Har ma ka harba harsashi... Amma duka hannayenka fayau suke. 

Salman Khan

• Meri vardi pe medal bahut lage hai ... par daag sirf ek

Akwai lambobin girmamawa da yawa a jikin kakina... Da kuma datti guda ɗaya. 

Randeep Hooda

• Dawai aur shaadi mein badi similarity hoti hai ... dono agar time pe na mile na, bahut mushkil ho jaati hai

Akwai babban kamanceceniya a tsakanin magani da kuma aure... Idan har ba ka same su akan lokaci ba, to za ka fuskanci gagarumar matsala. 

Saurabh Shukla

• Woh jeena bhi koi jeena hai jis mein kick na ho

Rayuwar duk da babu nishaɗi a cikinta ba rayuwa bace. 

Salman Khan

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 
Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN DIL TO PAGAL HAI


FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN DIL TO PAGAL HAI

Shekarar Fita - 1997

Fassarawa - Jamilu Abdurrahman 

• Rahul, naam toh suna hoga?

Rahul, na san kin taɓa jin sunan ko? 

Shah Rukh Khan 

• Rahul, naam toh yaad rahega na?

Rahul, shin za ki tuna da sunana? 

Shah Rukh Khan 

• Hamare sapno ka saathi aur hamara jeevan saathi ... kabhi ek nahi hota

Abokan tarayyarmu a mafarki da na zahiri... Ba sa taɓa zamowa ɗaya. 

• Main usse bahut pyar karti hoon ... ek din ke liye nahi ... ek pal ke liye nahi ... zindagi bhar ke liye

Ina son shi sosai... Ba wai na rana ɗaya ba... Ba wai na wani ɗan lokaci ba... Face na dukkan rayuwa baki ɗayanta. 

Madhuri Dixit

• Main kisi ladki wadki se pyar nahi karta ... sirf ladkiya mujhse pyar karti hai

Ni ba na faɗawa soyayya da 'yan mata...'yan mata ne kawai suke faɗawa soyayya da ni. 

Shah Rukh Khan

• Kahin na kahin, koi na koi mere liye banaya gaya hai ... aur kabhi na kabhi main usse zaroor milongi

A wani waje, an halicci wani saboda ni... Kuma watarana tabbas zan haɗu da shi. 

Madhuri Dixit

• Pyar bahut baar ho jaata hai ... lekin mohabbat sirf ek baar hoti hai. 

Akan iya faɗawa soyayya sau da dama... Amma tsunduma cikin ƙauna yana faruwa sau ɗaya ne kawai. 

Aruna Irani

• Kehdo ki tumhe nahi lagta ki hum dono ek doosre ke liye bane hai ... kehdo ki jab main tumse door jata hoon, tum mujhe palat kar nahi dekhti ... kehdo ki jab main tumhe choota hoon, tumhe kuch nahi hota ... kehdo ki is waqt tum meri baahon mein nahi aana chahti ... ek baar meri aankhon mein dekho aur aakhri baar kehdo ki tum mujhse pyar nahi karti

Ki faɗa min ba kya jin an halicce mu ne domin juna... Ki faɗa min in na yi nesa da ke, ba kya waigawa ki ganni... Ki faɗa min a duk sanda na taɓa ki, ba kya jin komai... Ki faɗa min ba kya son zuwa cikin hannayena a yanzun nan... Ki kalli idanuwana kuma ki faɗa min a karo na ƙarshe cewa ba kya so na. 

Shah Rukh Khan

• Kisi ko pyar karna aur ussi se pyar paana ... bahut kam logon ko naseeb hota hai

Ka so wani mutum kuma ka samu soyayya daga wannan mutumin... Mutane ƙalilan ne ke da sa'ar samun hakan. 

Karisma Kapoor

• Kya tumne kabhi bhi ... ek din ke liye bhi ... ek pal ke liye bhi ... mujhse pyar kiya tha?

Shin kin taɓa jin... Ko da na yini ɗaya ne... Ko da na ɗan wani lokaci ne... Cewa kina so na? 

Shah Rukh Khan


©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 
Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN BAAHUBALI: THE BEGINNING

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN BAAHUBALI THE BEGINNING

Shekarar Fita - 2015

Fassarawa - Jamilu Abdurrahman

• Is rajya mein sirf do log uska naam lete hai ... tum aur main ... tum ki apni maut se pehle usse aakhri baar dekh pao ... main taa ki ek baar aur usse apne haathon se maar paon

A wannan jahar mutane biyu ne kawai ke ambaton sunansa... Ke da ni... Ke saboda ki sake ganinsa a karo na ƙarshe kafin ki mutu... Ni kuma saboda in sake kashe shi da hannaye na. 

Rana Daggubati

• Balwan ko aur balwan karo ... isse chalaaki nahi, rajneeti kehte hai

Mayar da masu ƙarfi mafiya ƙarfi... Wannan shi ake kira siyasa ba wayo ba. 

Nassar

• Ek raja ka dharam sirf shatru ko maarna hi nahi hota ... praja ko bachana bhi hota hai

Aikin sarki ba kashe maƙiya bane kawai... Harda kare mutanensa. 

Ramya Krishnan

• Kayarta ke vikul hai mere yeh aasoon aur peedha ke toh bilkul bhi nahi ... yeh mera rakht hai joh ghoolkar bhav ban gaya aur meri aankhon se behne laga

Hawayena na barranta daga dolanci ne ba na jin raɗaɗi ba... Wannan jinina ne ya rikiɗa daga yadda nake ji yake fitowa ta cikin idanuwana. 

Tamannaah Bhatia

• Yudh mein saikadon ko maarne waala nayak hai ... lekin joh kisi ek ke bhi pran bachaye woh devta hai

Wanda ya kashe mutane da dama a filin daga shi ake kira da jarumi... Amma wanda ya ceci rayuwa ko da guda ɗaya ne shi ubangiji ne. 

Ramya Krishnan

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 


Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN SINGHAM RETURNS

Fassarar Kalaman Fim Ɗin Singham Returns


Shekarar Fita - 2014

1. Zarurat se zyada roshni insaan ko andha bana deti hai. 

Haske mai yawa ka iya sa mutum ya makance. 

Amole Gupte

2. Joh police waala bahar se jitna correct hota hai na ... andar se utna hi corrupt hota hai. 
 
Iya yadda ɗan sanda yake dai-dai a fili... Iya gurɓacewarsa kenan daga ciki. 

3. Sher aatank machata hai aur zakhmi sher tabaahi. 
 
Damisa yana samar da tsoro, kuma raunannen damisa na haifar da ta'adi. 

Ajay Devgan

4. Kis kaam ki hai yeh vardi ... joh ek police waale ko mazboot nahi, majboor banati hai. 
 
Menene amfanin wannan kakin... Wanda ke sa ɗan sanda ya rasa makama ba ƙwarin gwiwa ba. 

Ajay Devgan

5. Sabki ulti ginti chalu!

Ka fara ƙirga kwanakinka ta baya! 

Ajay Devgan

6. Agar samay manushya ka mitra ban gaya, toh jeevan mein bahut upar pahunchata hai ... lekin agar shatru ban gaya, toh hamesha ke liye upar pahunchata hai. 

Idan lokaci ya zama abokin mutum, sai ya kai shi sama can ƙololuwa a rayuwa... Idan kuwa ya zama maƙiyinsa, to wa ubangiji zai kai shi har abada. 

Amole Gupte
 
7. Insaan umar se nahi, karamo se bada hota hai. 

Mutum yana girma ne ba wai da shekarunsa ba, yana girma ne da ayyukansa. 

Anupam Kher

8. Main yahan investigation karne aaya hoon ... do kaudi ka pravachan sunne nahi

Na zo nan ne domin in yi bincike... Ba wai don in saurari surutai ba. 

Ajay Devgan 

9. Aaj rajneeti mein sabko insecurity hai ... is liye sabko security hai

A yau babu tsaro a siyasa... Shi ya sa kowa ke da matakan tsaro. 

Anupam Kher

10. Tu system mein hai aur hum khud system hai. 

Kana cikin tsarin, ni kuma ni ne tsarin. 

Zakir Hussain

11. Dhoom machani hai machao ... lekin bike ki gatti par nahi ... apni future ki pragati par. 

Idan kana so ka yi nishaɗi to bismillah... Amma ba da gudun babur ɗinka ba... Maimakon hakan da gudun cigaban rayuwarka. 

Ajay Devgan. 

12. Manushya joh hai woh aata hai jaane ke liye ... aur hum andar ja rahe hai bahar aane ke liye. 

Ɗan Adam na zuwa ne kawai don ya tafi... Kuma muna shiga ciki ne kawai domin mu fito waje. 

Amole Gupte 


©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 


Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN JAI HO


FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN JAI HO 

Shekarar Fita - 2014


1. Ek sachche desh bhakt ko hum fauj se nikaal sakte hai ... lekin uske dil se desh bhakti nahi. 

Muna iya cire mai kishin ƙasa ne kawai daga rundunar soji... Amma ba za mu iya cire kishin ƙasar daga zuciyarsa ba. 

Sunil Shetty

2. Aam aadmi sota hua sher hai ... ungli mat kar ... jaag gaya toh cheer phaad dega

Talakan gari tamkar zaki ne da yake bacci... Kada ka takura masa... Saboda idan ya farka to zai lalata komai. 

Salman Khan 

3. Aap thank you mat kahiye ... instead teen logon ki madad ki jiye aap ... aur un teeno se kehna ki woh teen aur ki madad karen ... duniya badal jayegi

Kada ka ce nagode... A madadin hakan ka taimaki mutum uku... Sannan ka ce mutum ukun suma su taimaki mutum uku... Duniya za ta canja. 

Salman Khan

4. Mere parivar se ulajhne se pehle mere baare mein jaan lete ... toh achcha hota

Da ka nemi sanin ko ni waye da ya fi maka, kafin ka takali ahali na. 

Salman Khan 

5. Agar koi bhi kuttagiri ki na ... toh mere bhai tujhe kutta bana ke chhodega

Idan ka yi abin da zai dame ni... Ɗan uwana zai maida kai kamar kare. 

Tabu. 

6. Aaise logon ki maut unka sarr kaatne se nahi ... balki sarr jhukane se hoti hai

Mutane irinsa ba sa mutuwa don ka fille musu kai... Suna mutuwa ne kaɗai yayin da kansu ya duƙa ƙasa. 

Danny Denzongpa

7. Army mein rehkar ya politician bankar hi desh ki seva ki jaye ... yeh zaroori nahi hai

Ba lallai bane don yi wa ƙasa aiki sai ka shiga aikin soji ko siyasa ba. 

Tabu 

8. Zindagi mein agar tarakki karni hai toh no entry aur signal ke baad khade rehna seekho ... pehle khade rahoge toh sirf haath malte rahoge

Idan ka na so ka yi nasara a rayuwa, to ka tsaya a bayan alamar ko hanyar shigar... Idan ka tsaya a gaban hakan, to babu abin da za ka samu. 

Aditya Pancholi

9. Burai ek zehar ki tarah hoti hai, joh bahut jaldi phail jaati hai ... aur achchai dawa ki tarah, joh waqt toh leti hai lekin asar zaroor karti hai

Zalunci kamar dafi yake, da sauri yake tafiya... Adalci kuma kamar magani yake, yana ɗaukar lokaci tabbas yana aiki. 

Mahesh Thakur

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 


Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN ROWDY RATHORE

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN ROWDY RATHORE

Shekarar Fita - 2012

 1. Jisne bhi yeh socha ki main dar gaya ... woh saala arthi pe apne ghar gaya 

Wanda duk yake tunanin na tsorata ne... To wawan shi zai koma gida a akwakwu. 

Akshay Kumar


 2. Don't angry me!

Kada ka fusata ni. 

Akshay Kumar 


 3. Naam sunte hi pichwaade mein bhukamp aa gaya na?

Ashe jin sunan ba kamar jin tsawa bane a mazaunanka? 

Akshay Kumar

 4. Sau saal zinda rehne ke liye sau saal ki umar zaroori nahi ... sirf ek din mein aaisa kaam kar jao ... jisse duniya tumhe sau saal tak yaad rakhe

Domin a rayu tsawon shekaru 100 ba ka buƙatar sai ka shekara 100... Ka yi wani abu a yini ɗaya... Ta yadda duniya za ta tuna da kai har na tsawon shekaru 100. 

Yashpal Sharma

 5. Pyar karne ke liye pechaan ki nahi ... dil ki zaroorat hoti hai. 

Ba ka buƙatar sanin mutum domin ka faɗa soyayya... Zuciya ka ke buƙata. 

Akshay Kumar 

 6. Meri sirf ek hi khawaish hai ... jab maut mere samne aaye tab main darra hua na lagon ... bas mera haath meri mooch ko taav de raha ho aur mere chehre par ek muskurahat ho. 

Burina kawai shi ne... Kada in tsorata yayin da mutuwa ta zo gaba gare ni... A maimakon haka hannuna ya zama yana murza gashin bakina tare da murmushi a fuskata. 

Akshay Kumar

 7. Main nahi darta ... maut darti hai mujhse.

Ba na tsoron mutuwa... Mutuwa ita ke tsorona. 

Akshay Kumar

 8. Joh main bolta hoon woh main karta hoon ... joh main nahi bolta woh main definitely karta hoon. 

Duk abin da na ce zan aikata sai na aikata... Abin da ban ce zan aikata ba kuwa tabbas sai na aikata. 

Akshay Kumar

 9. Sachche police officer ki vardi bhi apni duty nibhati hai. 

Hatta Kakin jami'in Ɗan Sanda na gaske ma cika aikinsa yake yi. 

Akshay Kumar

10. Joh bura kaam karte hai ... darr unki nas nas mein hota hai. 

Masu aikata miyagun ayyuka... Kodayaushe a cikin tsoro suke. 

Akshay Kumar.

11. Dekh ke darr gaya ... ya darr ke dekh raha hai?

Ka tsorata da ka ganni... Ko kallona kake yi a tsorace? 

Akshay Kumar

12. Tereko jab gussa aata hai tu chilata hai ... main udata hoon. 

Idan ka fusata abubuwa kake fasawa... Ni kuma fashewa nake yi. 

Akshay Kumar

13. Aurat ka khaas khayal do hi umar ma bahut rakhna padta hai ... ek jab uski umar hovat hai satrah, tab saala badh jaata hai khatra ... aur jab aurat hovat hai tees, oo saali ban javat hai cheez

Kana buƙatar kulawa da mace sosai a yayin da ta kai shekaru iri biyu... Lokacin da ta kai shekara 17 saboda a lokacin ne take da haɗari sannan... Da kuma lokacin da ta kai shekara 30, saboda a wannan lokacin ne ta zama zazzafa. 

Nassar


•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman 
•----------•✬(✪)✬•----------•

    +2348185819176Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KAL HO NA HO


FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KAL HO NAA HO 

Shekarar Fita - 2003
 

Aaj ... aaj ek hasi aur baant lo ... aaj ek dua aur maang lo ... aaj ek ansoon aur pee lo ... aaj ek zindagi aur jee lo ... aaj ek sapna aur dekh lo ... aaj ... kya pata, kal ho naa ho. 

Yau... Ki ɗan ƙara yin murmushi ɗaya yau... Ki ƙara yin wata addu'ar yau... Ki ɗan ƙara sha yau... Ki ƙara rayuwa yau... Ki ƙara ganin wani mafarki yau... Wa ya sani, ba lallai ne gobe ta zo ba. 

Shah Rukh Khan 

2. Pyar ka pehla kadam dosti hai, aur aakhri bhi ... bus beech ke kadam reh gaye hain. 

Matakin farko na soyayya shi ne abota kuma shi ne na ƙarshe... Matakan da ke tsakani ne kawai suka rage. 

Saif Ali Khan 

3. Tumhare paas joh hai tumhare hisaab se kam hai ... lekin kisi doosre ke nazar se dekho ... toh tumhare paas bahut kuch hai. 
 
Abin da kike da shi kaɗan ne a ganinki... Amma da zaki kalle shi a matsayin wani can daban... Kina da abubuwa da yawa. 

Shah Rukh Khan 

4. Main aankhen band karta hoon toh tumhe dekhta hoon ... aankhen kholta hoon toh tumhe dekhna chahta hoon ... tum paas nahi hoti ho toh tumhe chaaron taraf mehsoos karta hoon ... har pal, har ghadi, har waqt. 

Idan na rufe idanuwana ke nake gani... Yayin da na buɗe su kuma ke nake son gani... Nakan jiki a ko'ina idan ba kya nan... A kowace daƙiƙa, a kowace sa'a, a kowane lokaci. 

Shah Rukh Khan 

5. Jitna tum ladki ke peeche bhaagoge utna hi woh tumse door bhaagegi ... agar tum ladki ke peeche nahi bhaagoge toh woh confuse ho jayegi aur tumhare peeche bhaagegi ... yeh pata karne ke liye ki woh confuse kyun hai

Idan ka cika bin yarinya sai ta dinga gudunka... Idan baka binta kuma sai ta ruɗe daga nan kuma sai ta fara binka... Saboda ta gano me ya sa ta ruɗe. 

Shah Rukh Khan 

6. Main tumhe zindagi bhar pyar karoonga aur marte dam tak pyar karoonga ... aur uske baad bhi

Zan so ki har abada kuma zan so ki har in mutu... Har ma da bayan hakan. 

Shah Rukh Khan 

7. Pyar toh bahut log karte hai ... lekin mere jaisa pyar koi nahi kar sakta kyun ki kisi ke paas tum joh nahi ho

Mutane da yawa suna soyayya... Amma babu wanda yake soyayya irin tawa, saboda ba su da ke. 

Shah Rukh Khan 

8. Soocho, soocho ... aur soochne ke liye main tumhe apni saari zindagi deta hoon

Ki yi tunani, ki yi tunani... Kuma ki yi tunanin zan baki dukkan rayuwata. 

Saif Ali Khan.


©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 

Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KHILADI 786


🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻AKSHAY KUMAR FANS NIGERIA 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻


FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KHILADI 786


Shekarar Fita - 2012 

1. Main har test pass karke dikhaonga ... chahe yeh mera blood test kyun nah lele

Zan yi nasara a kowane gwaji.. 
Ko da kuwa jinina za su gwada. 

Akshay Kumar 

2. Oye kake Punjabi na toh chup chap aate hain, na hi chup chap jaate hain. 


Ayya ɗan uwa 'yan Punjabi ba sa zuwa da shiru, kuma ba sa tafiya da shiru. 

Akshay Kumar 

3. Unki gali mein hum aaye ajeeb ittefaq hai ... phool toh pheka unhone ... magar gamla bhi saath hai. 

Gam-da-katar ne me ban mamaki da na biyo ya layinta... Ta jefe ni da fulawa... Amma tare da tukunyar fulawar. 

Akshay Kumar 

4. Rishteydari taqat waalo ke saath nahin ... sharafat waalo ke saath ki jati hai

Alaƙa ba ƙullata ake yi da mutane masu ƙarfi ba... Ana yinta ne da mutane masu gaskiya. 

5. Awara kutta Mercedes ke peeche bhaag toh sakta hai ... lekin usse chala nahin sakta

Gantalallen Kare yana iya gudu a bayan Marsandi... Amma be isa ya tuƙa ta ba. 

Himesh Reshammiya 

6. Duniya mein teen cheezen hoti zaroor hai lekin kisi ne dekhi nahin ... bhooton ka sansar, sacha wala pyar aur Bahattar Singh ki raftaar

A duniyar nan akwai abubuwa guda uku da tabbas akwai su amma babu wanda ya taɓa ganinsu... Duniyar fatalwoyi, so na haƙiƙa da kuma saurin Bahattar Singh. 

Akshay Kumar


•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman 
•----------•✬(✪)✬•----------•

    +2348185819176

💫 *AKKIANS NA ALFAHARI DA KU* 💫
Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KOYLA


Fassarar Kalaman Fim Ɗin Koyla


 Shekarar Fita - 1997

 1. Gareebon ke mooh mein zabaan hote hue bhi ... woh ameeron ki duniya mein goonge bankar jeete hai. 

Duk da cewa talakawa suna da murya a maƙogwaronsu... Suna rayuwa ne a matsayin bebaye a duniyar masu kuɗi. 

Johnny Lever

 2. Abhe kamzor dil ke kabutar ... astabal ke khabeez!

Kai raunanannen tantabara... Azzalumin mutumin bargar dawakai. 

Johnny Lever

3. Main inteqam ka ek aaisa dahekta hua koyla hoon ... jiski uthti hui aag ki lapton mein tum sabki zindagiyan aa chuki hai ... aur is jalte hue koyle ki aag mein tum sab bari-bari jalkar raakh ho jaoge. 
 
Ni tamkar gawayin ɗaukar fansa ne da yake ruri... A harshen wutar da dukkanku rayukanku su ka kamu a ciki... Kuma a cikin wannan wutar gawayin dukkanku za ku babbake ku zama toka ɗaya bayan ɗaya. 

Shah Rukh Khan

 4. Ghaas aur dushmani kahin bhi aur kabhi bhi pehda ho sakte hai. 

Ciyawa da adawa suna iya girma a ko'ina kuma a kowane lokaci.

Amrish Puri

 5. Do kadam kya, sau kadam peeche hatt ja ... lekin aaj na tu apni maut se peecha chhuda sakta hai ... na maut ke saaye se. 

Ba taku biyu ba kawai, kana iya ja da baya da taku ɗari ma... Amma a yau ba za ka iya tserewa mutuwarka ba... Ko kuma wa inuwar mutuwar. 

Shah Rukh Khan

 6. Main hoon Mr. Tolmol, baat karun main gol-gol ... khol doon main sabki pol

Ni ne Mista Tolmol, na kan yi magana a rikice... Kuma na kan tona asirin kowa. 

Johnny Lever

 7. Bacha maa ki kok mein baad mein panapta hai ... humra ghulam pehle banta hai

Yaro yana girma a mahaifar mahaifiyarsa ne daga baya... Amma da fari sai ya zama bawa na tukun. 

Amrish Puri

8. Main teri ek ek saans maut ke bazaar mein bechkar aaya hoon

Na siyar da dukkan numfashinka a kasuwar mutuwa. 

Shah Rukh Khan


•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman 
•----------•✬(✪)✬•----------•

    +2348185819176
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Twitter: @jamiluwriter 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Instagram: Jamiluwriter 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Facebook:
https://m.facebook.com/JamiluWriter/
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Tumblr: Jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Bakandamiya: Jamilu Abdurrahman 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Telegram: https://t.me/Jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
LinkedIn: https://www.linkedin.com/in/jamilu-abdurrahman-36b882118
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Haimanraees@gmail.com
──────⊹⊱✫⊰⊹────── 
Share:

SANARWA!


SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!


'Yan uwa da abokan arziƙi ina muku barka da warka, ya kuke? Kuma ya aka ji da al'amuran yau da kullum? Allah ya taimake mu baki ɗaya.

Ina mai sanar muku cewa na dakatar da duk wasu rubututtukan da nake yi da suka shafi Fina-Finan Indiya sakamakon gabatowar watan Ramadan. Sai dai hakan baya nufin ba za'a ga sauran rubututtukana ba, hasalima in shaa Allah idan mun rayu zuwa bayan Sallah cikin ƙoshin lafiya, akwai abubuwan ban mamaki da za su biyo baya. Ɗaya daga cikin waɗannan sabbin abubuwa kuwa shi ne, aikin fassarar Waƙoƙin Indiya da na ke yi zai ɗauki wani sabon salo da zubi, da tsari irin wanda ba shi aka saba da shi ba, amma kuma zai ƙayatar matuƙar.

Hallau kuma dai, a kwanakin baya na ba wa mutane damar turo sunayen waƙoƙin da su ke so a fassara musu domin shigar da su a cikin jadawalin aiyukana, mafi yawancin waɗanda aka turo min na riga na fassara su, yayin da saura kuma su ke kan hanya. Don haka, duk wanda ya ke da wata waƙa da ya ke so a fassara masa, to kai tsaye yana iya turo cikakken sunan waƙar da kuma fim ɗin da aka yi waƙar zuwa gare ni ta duk hanyar da ya ga ta fi masa sauƙi, in shaa Allah ni kuma zan fassara masa ita da zarar na samu damar yin hakan.

Ina matuƙar godiya ga kowa da kowa bisa shawarwari da na ke samu da kuma goyon baya, kuma ina fatar hakan ya amfane mu baki ɗaya. Allah ya kawo mana sauƙin wannan musiba ta coronavirus, Aameen. 

•┈┈••✾•◆❀◆•✾••┈┈•
      Haiman Raees 
•┈┈••✾•◆❀◆•✾••┈┈•

         08185819176
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Twitter: @HaimanRaees 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Instagram: Haimanraees 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Facebook: Haiman Raees 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Tumblr: Haimanraeesposts
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Bakandamiya: Haiman Raees 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Haimanraees@gmail.com 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────

Miyan Bhai Ki Daring 
Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN RAEES


FASSARAR KALAMAN FIM DIN RAEES
1. Joh dhande ke liye sahi woh sahi ... joh dhande ke liye galat woh galat ... isse zyada kabhi socha nahi.
* Abin da ya dace da kasuwanci ya dace... Abin da bai dace da kasuwanci ba bai dace ba... Ban taɓa tunanin wani abu bayan haka ba.
Shahrukh Khan
2. Koi dhanda chota nahi hota aur dhande se bada koi dharam nahi hota.
* Babu wani kasuwanci da yake karami kuma babu addinin da ya fi kaduwanci
Shahrukh Khan
3. Baniye ka dimaag ... miya bhai ki daring
* Ina da kaifin kwakwalwa kamar ɗan kasuwa... Kuma ba ni da tsoro kamar jarumi.
Shahrukh Khan
4. Gujarat ki hawa mein vyapar hai saheb ... meri saans toh rok loge ... lekin is hawa ko kaise rokoge.
* Iskar garin Gujrat cike ta ke da kasuwanci yallaɓai... Kana iya tsayar da numfashina... Amma ta yaya za ka iya tsayar da iska?
Shahrukh Khan
4. Aaj kal din ache chal rahe hai tere ... Din aur raat logon ke hote honge ... sheron ka zamana hota hai.
* A kwanakin nan ranakunka suna tafiya daidai... Ranaku da darare na mutane ne... Damisoshi kuwa zamunna ne nasu.
Shahrukh Khan
5. Saboot le aaiye ... le jaiye ... Raees hazir hai.
* Ka kawo shaida... Sai ka tafi da ni... Raees a shirye yake.
Shahrukh Khan
6. Raees ka aur mera rishta bada ajeeb hai ... paas reh nahi sakta aur saala door jaane nahi deta.
* Alaka ta da Raees abu ne mai ban mamaki... Ba ya iya zama kusa da ni kuma ba ya iya rabuwa da ni.
Nawazuddin Siddiqui
7. Ek din naak mein nakel daalke kheench ke leke jaaunga tujhe main yahan se.
* Watarana sai na cusa sanda a hancinka na yi waje da kai daga nan.
Nawazuddin Siddiqui
8. Chai ki daru?) ... Daru, chai ke glass mein.
* Shayi ko giya?... Giya, a gilashin shayi.
Shah Rukh Khan & Nawazuddin Siddiqui
9. Pabandi hi bagavat ki shuruvaat hai.
* Iyakancewa shi ne farkon tawaye.
Nawazuddin Siddiqui
10. Insaan ke ek kande par farishta aur doosre kande pe shaitan behta hota hai.
* A kafaɗar kowane mutum akwai ɗan aiken ubangiji a ɗaya kafaɗar kuma ɗan sakon shaiɗan ne ya ke zaune.
11. Battery nahi bolneka!
* Ka da ka kira ni da mai gilashi!
Shahrukh Khan
Haiman Raaes
08185819176
Infohaiman99@gmail.com
Aa raha hoon!
Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN VEER ZAARAFassarar Kalaman Fim Din Veer Zaara

Shekarar Fita - 2004

1. Sarhad paar ek aisa shaksh hai ... joh aapke liye apni jaan bhi de dega
 
A ɗaya ɓangaren na iyakar ƙasa da ƙasa... Akwai wani... Wanda zai iya bada rayuwar sa saboda ke 

 Shahrukh Khan

2. Sachi mohabbat zindagi mein sirf ek baar hoti hai ... aur jab hoti hai ... toh koi bhagwan yah khuda usse nakamyab nahi hone deta
 
So na gaskiya yakan faru ne sau ɗaya a rayuwa... Kuma idan ya faru ... Ubangiji Yakan Sa ya zamo mai nasara. 

Shah Rukh Khan 

3. Woh kehte hai yeh tera desh nahi, phir kyun mere desh jaisa lagta hai ... woh kehta hai main us jaisa nahi, phir kyun mujh jaisa woh lagta hai
 
Sunce nan ba ƙasa ta bace, to amma yaya akayi tayi kama da ƙasa ta...? Ya ce ni ba irin sa bane, to amma yaya yake kama da ni? 
  
Shah Rukh Khan 

4. Mere desh ki har maa ... aap jaisi zaroor hai
 
Kowace uwa a ƙasa ta... Kamar ke take 

Shah Rukh Khan 

5. Woh kehte hai ki woh koi nahi thi, phir kyun mere liye duniya se woh ladti hai ... woh kehte hai main us jaisa nahi, phir kyun mujh jaisi woh lagti hai
 
Sunce ita ba komai bace a gare ni, amma me yasa take faɗa da duniya akai na...? Sunce ni ba irin ta bane, amma me yasa take kama da ni? 

Shah Rukh Khan 

6. Ek aurat ki mohabbat aur ek mard ki mohabbat mein bahut fark hota hai
 
Akwai Banbanci Sosai a tsakanin soyayyar Namiji Da Soyayyar mace 

 Kiron Kher

7. Mohabbat kitaabon mein hoti hai, shayari mein hoti hai ... zindagi mein nahi
 
So Yana Wanzuwa ne kawai a littattafai da Waƙoƙi... Ba a rayuwa ba 

Kiron Kher

8. Azaadi har insaan ka paidayashi haq hai
 
'Yancin Kai Haƙƙi ne na Kowane mutum. 

 Rani Mukherjee

9. Yeh khuda ke roop mein insaan hai ... yah insaan ke roop mein khuda
Shin shi mutum ne a siffar Ubangiji... Ko kuma Ubangiji ne a Siffar mutum? 


 Rani Mukherjee

10. Aadmi di zindagi vich jab sahi aurat aa jandi hai na ... tab woh zindagi poori tarah jeenda hai
Yayinda mace Tagari ta shiga rayuwar mutum... A sannan ne zai rayu da cikakkiyar rayuwa. 

Amitabh Bachchan

# HappyBirthdaySrk
# NASRUN MINALLAAHI ƘAREEB
# SRKUNIVERSENIGERIA
# SHAHRUKHKHANFANSNIGERIA 
<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring 
Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN DILWALE 2015


Fassarar Kalaman Fim Din Dilwale (2015)

1. Hum shareef kya hue ... poori duniya hi badmash ban gayi
A Yayinda na zama mutumin Kirkiri... Duniya kuma sai ta ƙara Lalacewa. 

Shah Rukh Khan

2. Dil toh har kisi ke paas hota hai ... lekin sab dilwale nahi hote
Kowa yana da Zuciya... Amma ba kowa ke da taurin rai ba

Shah Rukh Khan

3. Aaj ek baad mujhe apna chehra mat dikhana ... jaan le loonga

Kada in Sake Ganin Fuskar ka daga yau... Zan kashe ka

Shah Rukh Khan 

4. Dhokha mere saath hua hai ... joh karna hai main hi karoonga
An riga an cuce ni... Duk abinda ya dace inyi, zan yi shi. 


# HappyBirthdaySrk
# NASRUN MINALLAAHI ƘAREEB
# SRKUNIVERSENIGERIA
# SHAHRUKHKHANFANSNIGERIA 
<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring 


Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN DON


Fassarar Kalaman Fim Din Don (2006)

Shekarar Fita- 2006

1. Bahar tumhari aunty bahut saare uncles ko lekar aayi hai

Gwaggon ka Ta Sayi Kawunnai Da Yawa a Waje

(Shah Rukh Khan)

2. Kuch kaam aaise hote hai jin mein fayda yah nuksaan nahi dekha jaata ... bus unhe karna zaroori hota hai

Akwai Wasu Abubuwan da baka bukatar Riba ko faduwa a cikin su... Kawai dole ne Kayi Su

(Shah Rukh Khan)

3. Mera intezaar toh gyarah mulkon ki police kar rahi hai lekin ... Don ko pakadna mushkil hi nahin ... namumkin hai

'Yan Sanda Daga Kasashe 11 Suna Jira Na amma... Kama Don Ba wai Wahala Kawai yake da shi ba... Abu ne da ba zai Yiwu ba.

(Shah Rukh Khan)

4. Don ke dushman ki sabse badi galati yeh hai ... ki woh Don ka dushman hai

Babban kuskuren Maƙiyin Don Shi Ne... Shi Maƙiyin Don Ne

(Shah Rukh Khan)

5. Mujhe do tarah ki ladkiyan pasand nahi aati ... ek woh joh mere pass aane mein bahut derr lagaye aur doosri woh joh bahut jaldi aa jaye

Bana Son Kalar 'Yan Mata Biyu.. Na Farko Masu ɗaukan Tsawon Lokaci Kafin Su zo Gare ni Da Kuma Masu Zuwa Gare Ni Da Sauri

(Shah Rukh Khan)

6. Mujhe junglee billiyan bahut pasand hai

Ina Son Magunan Daji Sosai

(Shah Rukh Khan)

7. Log Don ko nahi ... duniya ko chhodte hai

Mutane Basa barin Don... Sai dai Su Bar Duniya

(Shah Rukh Khan)

8. Mujhe jahan pahunchna hai uske liye yeh raftaar bahut zaroori hai

Wannan Saurin Na Dole Ne Domin Inda nake so In Je

(Shah Rukh Khan)

9. Yeh tum janti ho ki yeh pistol khali hai ... main janta hoon ki yeh pistol khali hai lekin ... police nahin janti ki yeh pistol khali hai

Kin San Cewa Babu Komai a cikin Wannan bindigar... Na san Cewa babu komai a cikin wannan bindigar Amma... 'Yan Sanda Basu San cewa Babu Komai a cikin wannan Bindigar Ba.

(Shah Rukh Khan)

# HappyBirthdaySrk
# NASRUN MINALLAAHI ƘAREEB
# SRKUNIVERSENIGERIA
# SHAHRUKHKHANFANSNIGERIA 
<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring


Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form