Skip to main content

Posts

Showing posts with the label Fassarar Kalaman Fim

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN SINGHAM RETURNS

Fassarar Kalaman Fim Ɗin Singham Returns

Shekarar Fita - 2014
1. Zarurat se zyada roshni insaan ko andha bana deti hai. 
Haske mai yawa ka iya sa mutum ya makance. 
Amole Gupte
2. Joh police waala bahar se jitna correct hota hai na ... andar se utna hi corrupt hota hai.  Iya yadda ɗan sanda yake dai-dai a fili... Iya gurɓacewarsa kenan daga ciki. 
3. Sher aatank machata hai aur zakhmi sher tabaahi.  Damisa yana samar da tsoro, kuma raunannen damisa na haifar da ta'adi. 
Ajay Devgan
4. Kis kaam ki hai yeh vardi ... joh ek police waale ko mazboot nahi, majboor banati hai.  Menene amfanin wannan kakin... Wanda ke sa ɗan sanda ya rasa makama ba ƙwarin gwiwa ba. 
Ajay Devgan
5. Sabki ulti ginti chalu!
Ka fara ƙirga kwanakinka ta baya! 
Ajay Devgan
6. Agar samay manushya ka mitra ban gaya, toh jeevan mein bahut upar pahunchata hai ... lekin agar shatru ban gaya, toh hamesha ke liye upar pahunchata hai. 
Idan lokaci ya zama abokin mutum, sai ya kai shi sama can ƙololuwa a rayuwa... Idan kuwa ya zama maƙi…

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN JAI HO

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN JAI HO 
Shekarar Fita - 2014

1. Ek sachche desh bhakt ko hum fauj se nikaal sakte hai ... lekin uske dil se desh bhakti nahi. 
Muna iya cire mai kishin ƙasa ne kawai daga rundunar soji... Amma ba za mu iya cire kishin ƙasar daga zuciyarsa ba. 
Sunil Shetty
2. Aam aadmi sota hua sher hai ... ungli mat kar ... jaag gaya toh cheer phaad dega
Talakan gari tamkar zaki ne da yake bacci... Kada ka takura masa... Saboda idan ya farka to zai lalata komai. 
Salman Khan 
3. Aap thank you mat kahiye ... instead teen logon ki madad ki jiye aap ... aur un teeno se kehna ki woh teen aur ki madad karen ... duniya badal jayegi
Kada ka ce nagode... A madadin hakan ka taimaki mutum uku... Sannan ka ce mutum ukun suma su taimaki mutum uku... Duniya za ta canja. 
Salman Khan
4. Mere parivar se ulajhne se pehle mere baare mein jaan lete ... toh achcha hota
Da ka nemi sanin ko ni waye da ya fi maka, kafin ka takali ahali na. 
Salman Khan 
5. Agar koi bhi kuttagiri ki na ... toh mere bhai tujhe ku…

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN ROWDY RATHORE

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN ROWDY RATHORE
Shekarar Fita - 2012
 1. Jisne bhi yeh socha ki main dar gaya ... woh saala arthi pe apne ghar gaya 
Wanda duk yake tunanin na tsorata ne... To wawan shi zai koma gida a akwakwu. 
Akshay Kumar

 2. Don't angry me!
Kada ka fusata ni. 
Akshay Kumar 

 3. Naam sunte hi pichwaade mein bhukamp aa gaya na?
Ashe jin sunan ba kamar jin tsawa bane a mazaunanka? 
Akshay Kumar
 4. Sau saal zinda rehne ke liye sau saal ki umar zaroori nahi ... sirf ek din mein aaisa kaam kar jao ... jisse duniya tumhe sau saal tak yaad rakhe
Domin a rayu tsawon shekaru 100 ba ka buƙatar sai ka shekara 100... Ka yi wani abu a yini ɗaya... Ta yadda duniya za ta tuna da kai har na tsawon shekaru 100. 
Yashpal Sharma
 5. Pyar karne ke liye pechaan ki nahi ... dil ki zaroorat hoti hai. 
Ba ka buƙatar sanin mutum domin ka faɗa soyayya... Zuciya ka ke buƙata. 
Akshay Kumar 
 6. Meri sirf ek hi khawaish hai ... jab maut mere samne aaye tab main darra hua na lagon ... bas mera haath meri mooch ko t…

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KAL HO NA HO

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KAL HO NAA HO 
Shekarar Fita - 2003
Aaj ... aaj ek hasi aur baant lo ... aaj ek dua aur maang lo ... aaj ek ansoon aur pee lo ... aaj ek zindagi aur jee lo ... aaj ek sapna aur dekh lo ... aaj ... kya pata, kal ho naa ho. 
Yau... Ki ɗan ƙara yin murmushi ɗaya yau... Ki ƙara yin wata addu'ar yau... Ki ɗan ƙara sha yau... Ki ƙara rayuwa yau... Ki ƙara ganin wani mafarki yau... Wa ya sani, ba lallai ne gobe ta zo ba. 
Shah Rukh Khan 
2. Pyar ka pehla kadam dosti hai, aur aakhri bhi ... bus beech ke kadam reh gaye hain. 
Matakin farko na soyayya shi ne abota kuma shi ne na ƙarshe... Matakan da ke tsakani ne kawai suka rage. 
Saif Ali Khan 
3. Tumhare paas joh hai tumhare hisaab se kam hai ... lekin kisi doosre ke nazar se dekho ... toh tumhare paas bahut kuch hai.  Abin da kike da shi kaɗan ne a ganinki... Amma da zaki kalle shi a matsayin wani can daban... Kina da abubuwa da yawa. 
Shah Rukh Khan 
4. Main aankhen band karta hoon toh tumhe dekhta hoon ... aankhen kholta …

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KHILADI 786

🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻AKSHAY KUMAR FANS NIGERIA 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KHILADI 786

Shekarar Fita - 2012 
1. Main har test pass karke dikhaonga ... chahe yeh mera blood test kyun nah lele
Zan yi nasara a kowane gwaji..  Ko da kuwa jinina za su gwada. 
Akshay Kumar 
2. Oye kake Punjabi na toh chup chap aate hain, na hi chup chap jaate hain. 

Ayya ɗan uwa 'yan Punjabi ba sa zuwa da shiru, kuma ba sa tafiya da shiru. 
Akshay Kumar 
3. Unki gali mein hum aaye ajeeb ittefaq hai ... phool toh pheka unhone ... magar gamla bhi saath hai. 
Gam-da-katar ne me ban mamaki da na biyo ya layinta... Ta jefe ni da fulawa... Amma tare da tukunyar fulawar. 
Akshay Kumar 
4. Rishteydari taqat waalo ke saath nahin ... sharafat waalo ke saath ki jati hai
Alaƙa ba ƙullata ake yi da mutane masu ƙarfi ba... Ana yinta ne da mutane masu gaskiya. 
5. Awara kutta Mercedes ke peeche bhaag toh sakta hai ... lekin usse chala nahin sakta
Gantalallen Kare yana iya gudu a bayan Marsandi... Amma be isa ya tuƙa ta ba. 
H…

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KOYLA

Fassarar Kalaman Fim Ɗin Koyla

 Shekarar Fita - 1997
 1. Gareebon ke mooh mein zabaan hote hue bhi ... woh ameeron ki duniya mein goonge bankar jeete hai. 
Duk da cewa talakawa suna da murya a maƙogwaronsu... Suna rayuwa ne a matsayin bebaye a duniyar masu kuɗi. 
Johnny Lever
 2. Abhe kamzor dil ke kabutar ... astabal ke khabeez!
Kai raunanannen tantabara... Azzalumin mutumin bargar dawakai. 
Johnny Lever
3. Main inteqam ka ek aaisa dahekta hua koyla hoon ... jiski uthti hui aag ki lapton mein tum sabki zindagiyan aa chuki hai ... aur is jalte hue koyle ki aag mein tum sab bari-bari jalkar raakh ho jaoge.  Ni tamkar gawayin ɗaukar fansa ne da yake ruri... A harshen wutar da dukkanku rayukanku su ka kamu a ciki... Kuma a cikin wannan wutar gawayin dukkanku za ku babbake ku zama toka ɗaya bayan ɗaya. 
Shah Rukh Khan
 4. Ghaas aur dushmani kahin bhi aur kabhi bhi pehda ho sakte hai. 
Ciyawa da adawa suna iya girma a ko'ina kuma a kowane lokaci.
Amrish Puri
 5. Do kadam kya, sau kadam peeche hatt …

SANARWA!

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!


'Yan uwa da abokan arziƙi ina muku barka da warka, ya kuke? Kuma ya aka ji da al'amuran yau da kullum? Allah ya taimake mu baki ɗaya.
Ina mai sanar muku cewa na dakatar da duk wasu rubututtukan da nake yi da suka shafi Fina-Finan Indiya sakamakon gabatowar watan Ramadan. Sai dai hakan baya nufin ba za'a ga sauran rubututtukana ba, hasalima in shaa Allah idan mun rayu zuwa bayan Sallah cikin ƙoshin lafiya, akwai abubuwan ban mamaki da za su biyo baya. Ɗaya daga cikin waɗannan sabbin abubuwa kuwa shi ne, aikin fassarar Waƙoƙin Indiya da na ke yi zai ɗauki wani sabon salo da zubi, da tsari irin wanda ba shi aka saba da shi ba, amma kuma zai ƙayatar matuƙar.
Hallau kuma dai, a kwanakin baya na ba wa mutane damar turo sunayen waƙoƙin da su ke so a fassara musu domin shigar da su a cikin jadawalin aiyukana, mafi yawancin waɗanda aka turo min na riga na fassara su, yayin da saura kuma su ke kan hanya. Don haka, duk wanda ya ke da wata waƙa da ya ke …