Showing posts with label Fina-Finai (Films). Show all posts
Showing posts with label Fina-Finai (Films). Show all posts

FINA FINAN ALGAITA DUKA WAƊANDA SU KA FITO KASUWA

FINA-FINAN ALGAITA DUKA WADANDA SUKA FITO KASUWA

ALL ALGAITA DUBBED MOVIES (FILMS)

ALGAITA DUB STUDIO
^^^^MASUBURBUDAR FASSARA^^^^
.
.
.
1. YAKI DA RASHIN ADALCHI
2. DAN TAWAYE
3. MUNNA
4. NEMAN DUNIYA
5. DAN BASAJA
6. KO'OHO
7. MAI TABARGAZA
8. RAINA KAMA
9. MASHEKI
10. ZAKIN ZAKUNA
11. HATSABIBI
12. DAMISA
13. BARKONO
14. MAI TAURIN KAI
15. MAI KISHIN KASA
16. SARKA
17. BAKIN RIJIYA
18. MAI GASKIYA
19. MARA TSORO (DABAANG)
20. ZUBAR JINI
21. CHAKWAKIYA
22. IZZAR MULKI
23. BABBAN YARO
24. MARAR TABBAS
25. BABBAN YAYA
26. GIDAN KURKUKU
27. INUWA
28. MASS
29. NINJAN KISA
30. SURYA UBAN DABA
31. KISAN GILLA
32. YAKIN KWATO ƳANCI
33. KARON BATTA
34. DOLAYE UKU
35. GADARA
36. SHUGABA
37. KADDARA
38. ASHOK MADAKIN KATTI
39. KUNAMA
40. NAMIJIN ZAKI
41. BIRNIN MATSAFA
42. TARIHIN ANNABI YUSUF
43. TSOHUWAR GABA
44. GABAR GADO
45. TAKUNKUMI
46. MAI ADDA
47. MAKASHIN MAZA
48. FUSATACCE
49. HANYAR MADARAS
50. SANSANI
51. BOTORAMI
52. TARKO
53. GHAJINI
54. DODON ƳAN GATARI
55. SOYAYYAR BEBAYE
56. SA MAZA GUDU
57. BANZA FALALU
58. HATSARI DA RAI
59. SOJA
60. KANSAKALI
61. MAKAHON SO
62. MALIN
63. SHARI'A SABANIN HANKALI
64. MAI KASHI
65. JUYIN JUYA HALI
66. RUWA A JALLO
67. 300 SPATA
68. ZOBEN SIHIRI
69. GARARRIYAR SOYAYYA
70. ZAKI KO DAMISA
71. KOMAI TA FANJAMA
72. ANNOBA
73. MAI SUBURBUDA
74. POLICE ƊAN TA'ADDA
75. HANZARI
76. SANGAMI
77. GOSULO
78. MAI LASISI
79. JARUMAN ƘASA
80. FARCEN GUMURZU
81. GASKIYA 'DAYA CE
82. FUSKA BIYU
83. RUKON AMANA
84. BADA'KALA
85. TSANANIN SO
86. HAMAGAWA
87. GARUJE
88. ZAKIN MATA
89. AJ SARKIN ASKA
90. DAN MANYA
91. CHAKWAKIYAR AURE
92. ƘALUBALE
93. JAHADI
94. YA'KI DA CIN HANCI
95. SHAHARA
96. 'YAN GARGAJIYA
97. TAFIYAR AJALI
98. JININ SARDAR
99. RAMIN KARYA
100. KWANTON 'BAUNA
101. MASHI
102. UBAN ZUGA
103. SOYAYYAR MAHAIFI
104. AKASI
105. GARDAMAMME
106. UKUBAR MATA
107. ZARGI(morah)
108. FARMAKIN ADALCHI
109. JAMI'IN TSARO
110. JANWAAR(dabba)
111. KIRIKOU
112. MACHASKALI
113. SAI NA RAMA
114. TAWAGAR MAKARYATA
115. TAWAGAR TANTIRAI
116. DOKA DA ODA
117. BARA'AR 'YAN TAWAYE
118. KETA IYAKA
119. ASHOW SADAUKI
120. HARƘALLA (The Expandables)
121. ZAZZAFA
122.CHAKWALKWALIN CHAKWAKIYA
123. KAUNAR ZUCIYA
124. JAMI'IN SIRRI
125. ATTAJIRI
126. AHALIN DAMBE
127. YAN UKU
128. JIGON TALAKAWA
129. BURIN ZUCIYA
130. MAYAUDARI
131. SIYASA AKIDA
132. MIZANI
133. BIRNIN TARIHI
134. GADAR ZARE
135. IKON SHARRI
136. IZINI
137. TAQADARI
138. QAUNA BIYU
139. SANSANIN ARTABU
140. JAMI'AN TAKIFE
141. JAN WUYA
142. MAGE A CIKIN DOGAYE.
143. BAKAR ANIYA
144. MAZANTAKA
145. JAMI'IN KARIYA
146. CHAKWAKIYA MAI ZAFI
147. KAFCEN FANSA
148. MUGUN GANI
149. SABABI
150. DAMBEN MAZA
151. HIKAYA
152. DAMBU
153. KWARIN GWIWA
154. KOMAR HUKUMA
155. JA GABA
156. DODON SU
157. SARKIN RUWA
158. TARTSATSI
159. GAGARE
160. ZAFIN HANNU
161. DAN ADAM BUTULU
162. MUNNA MAZARI
163. UWAR WATSI
164. SHARRIN CIKIN GIDA
165. ZAKARAN GASA
166. AKAFTA

Wanne daga cikinsu ne baka Kwamashe ba?
.
.
A sako na gaba zamu antayo muku da JADAWALIN fina-finan Algaita na 2018 a cikin hoto insha Allahu.
.
.
To ai hikenan Akafta 🎬

Share:

TARIHIN RAYUWAR JARUMA LARA DUTTA

TARIHIN RAYUWAR JARUMA # LARA_DUTTA
kamar kowacce larabar tsakiyar mako da muka saba kawo maku shirin mu ,da yake bayani akan jaruman film na bollywood wadanda suka fara harkar film daga 1990s zuwa wannan lokaci ko kuma wadanda tauraruwar su ta haska a wannan zango ,yauma cikin ikon ALLAH mun zo maku dauke da tarihin rayuwar jaruma LARA DUTTA.
An haifi jaruma LARA DUTTA ranar 16/04/1978 takasance jarumar fina finan india wacce take fitowa a bangaren bollywood ,sannan takasance mai sanaar tallata kayan kawa wato (modelling) a turance,kuma jarumar tazamo er india ta biyu data sami nasarar lashe kyautar kyau ta MISS UNIVERSE wacce akayi a qasar CYPRUS shekarar 2000.
tafara fitowa a filmdin ANDAAZ 2003 tareda da jaruma priyanka chopra da kuma AKSHAY KUMAR filmdin yasamu karbuwa sosai a wajen masu kallo (audience) gami da samun yabo daga bakin masu sharhi (critics),sannan da filmdin tasami nasarar lashe kyautar FILMFARE AWARD Ta sabuwar jaruma mafi nuna hazaqa a shekara wato (filmfare award for best female debut),dukda filmdin ANDAAZ shine filmdin ta na farko da yafita amma bashine na farko ba wajen fara aikin jarumar ,A 2002 jarumar tafara amsar (signed ) aikin filmdin ARASATCHI wanda aka shirya da yaren TAMIL ,sai dai filmdin yasami tsaiko wanda baisami fita ba sai a shekarar 2004.
jarumar ta taka rawar fitowa a matsayin KAJAL cikin filmdin ANDAAZ wanda dubban mutane suka yaba da qoqarinta na iya aikin jarumar dukda kuwa shine filmdin ta na farko,abu mafi jan hankali kuwa shine yanayin yadda voice dinta ke fita a filmdin.
Daga nan ba sake ganin jarumar ba a screen sai a waqar AISA JADOO ta filmdin KHAKEE 2004 wnda shine karon farko da jarimar tayi fitowa ta musamman (comeo appearance) a rayuwarta cikin films ,bayan nan ashekarar tafito a fina finai kamar BARDHASHT da kuma AAN MEN AT WORK wadanda duk sunyi faduwar baqar tasa a kasuwancinsu (flop),sannan kuma fina finai kamar INSAN ,elaan gami da JURM basu amsu sosai ba a kasuwancinsu (average) filmdin MASTI shine filmdin jarumar da yafi amsuwa a shekarar.
A wata interview da akayi da jarumar anyi mata tambaya meyasa bata fito cikin filmdin GRAND MASTI ba,wanda shine cigaban filmdin MASTI ta bayyana cewa "nasami offer tayin aikin filmdin amma na bar aikin ne saboda ciwon da yake damun mahaifiyata (illness) a lokacin "
kafin jarumar tafara yin filmdin ANDAAZ sai da tafara fitowa videon waqa da mawaqi ABHIJEET BHATTACHARYA yasaki mesuna TU CHALU HAI RE.
shekarar 2005 zuwa 2010 nan ne lokacin da tauraruwar jarumar tafi haskawa wadda tafito a manyan fina finai kamar kaal,NO ENTRY wanda tafito tare da jarumi salman khan,anil kapoor FARDEEN KHAN,celina jaitly,da kuma ESHA DEOL ,sannan tafito a filmdin DOSTI FREIND FOREVER tareda jarumi BOBBY DEOL ,filmdin bai samu karbuwa sosai ba INDIA amma yazamo fbiggest grosser
TALK SHOW
jarimar ta bayyana cikin wasu SHOW da aka gabatar kamar RANDEZVOUR wanda jaruma SAMI GAREWAL ta gabatar da kuma KOFFE na KARAN JOHAR wanda tagabatar da season one katrina kaif tayi season two,SHOW dinta na qarshe yafito ne a 2010wanda suka tare da mijinta .
EARLY LIFE
An haifeta ranar 16/04/1978 bana tana da shekaru 41 aduniya ,a garin GHAZIABAD dake jihar UTTER PRADESH ,mahaifinta mesuna L K DUTTA yakasance yaren PUNJAB kuma tsohon WING COMMANDO ,sunan mahaifiyata JENNIFER DUTTA,sannan tana da en uwa mata biyu SABRINA da cheryl dutta .
A 1981 suka bar garinsu suka koma BANGLORE anan ne jarumar tafara karatu,ta kammala karatun degree dinta na farko a UNIVERSITY OF MUMBAI wacce takaranci ENGLISH/HINDI.
bayan wadannnan yarukan jarumar tanajin yaren PUNJAB da KANNADA
PAGEANTRY
kyautukan kyawu da jarumar ta lashe a ciki da wajen qasar INDIA .
GLADRAGS MEGAMODEL INDIA 1995 winner .
MISS INTERCONTINENTAL 1997 winner .
FEMINA MISS INDIA 2000 winner
MISS UNIVERSE 2000 winner
PERSONAL LIFE
sunyi soyayya tareda wani abokin yarintarta mesuna KELLY DORJI daga baya kuma suka kama soyayya da wani baturen AMERICAN me buga kwallon BASEBALL ,mesuna DEREK JEFER.
daga karshe a sept 2010 sukayi engaged da wani dan kwallon TENNIS a INDIA mesuna MAHESH BUPHATHI wanda kuma sunyi aure a 16/02/2011,a garin GOA.
ranar daya ga watan august 2011 ta sanar cewa ta sami juna biyu ,wanda ranar 20/01/2012 ta haifi yarinya mesuna SAIRA BUPHATHI
JERIN FINA FINAN JARUMA #LARA_DUTTA
2003 ANDAAZ
mumbai se aaya mera dost
2004 KHAKEE C/A
MASTI
bardhasht
arasatchi TAMIL FILM
AAN men at work
2005 INSAN
ELAN
JURM
KAAL
NO ENTRY
2086 DOSTI freind forever
ZINDA
ALAQ c/a
bhagam bhag
FANAA C/A
2007 jhoom barabar jhoom
PARTNER
OM SHANTI OM C/A
JUMBO
2008 RABNE BANADI JODI C/A
2009 BILLU
do knot disturb
BLUE
2010 HOUSEFUL
2011 CHALU DILLI
DON.2
2013 DAVID
DAVID TAMIL FILM
2015 singh is bling
2016 FITOOR
AZHAR
2018 WELCOME TO NEW YORK
2019 BEECHAM HOUSE

Share:

SHARHIN FIM ƊIN BUNNY


SHARHIN FIM ƊIN BUNNY 

Bunny fim ɗin faɗa ne da aka fitar a India cikin harshen Telugu a shekara ta 2005. Shirin, wanda shi ne fim na uku da jarumi Allu Arjun ya yi bayan Gangotri da Arya ya samu karɓuwa matuƙa. 

An fassara wannan shiri da harshen Oriya inda aka sa masa suna Dharmayuddha, da yaren Hindi kuma Bunny The Hero, da Malayalam kuma aka bar shi da sunan shi. Da aka maimaita shi da harshen Bengali kuma sai aka sa masa suna Challenge. Hakanan kuma an fassara wannan shiri zuwa harshen Hausa in da aka sa masa suna Cinnaka, kuma wannan shi ne fim na biyu da na fara ɗaura muryata domin yin fassara. Kuma daga wannan fim ne jarumi Allu Arjun ya samu laƙabin Bunny. 


Umurni: V. V. Vinayak

Ɗaukar Nauyi: M. Satyanarayana Reddy

Rubutawa: V. V. Vinayak

Sauti: Devi Sri Prasad

Mai horaswa: Chota K. Naidu

Tacewa: Gowtham Raju

Ranar fita: 6 April 2005

Tsawon Shiri: Mintuna 139 

Harshe: Telugu

Kasafi: ₹15 crore (US$2.1 million) 

Kasuwanci: ₹35.5 crore (US$5.0 million)(Share) 100 Days.


LABARIN SHIRIN 

Somaraju hamshaƙin ɗan kasuwa ne da ke zaune a Visakhapatnam, yana da wani ɗan uwa mai suna Mysamma wanda shi ne ya ke jagorantar harkokin kasuwancin sa a Hyderabad. Somaraju yana da wata kyakkyawar 'ya da yake matuƙar so mai suna Mahalakshmi. 

Bunny wanda aka fi sani da Raja ya samu damar shiga kwalejin da da Mahalakshmi ta ke karatu in da ya samu nasarar burge ta tun a ranar farko. A hankali dai har ta faɗa kogin soyayyarsa. Somaraju bai so hakan ba, amma da ga ƙarshe dai ya amince da auren su. Kasancewar a al'adar su mata ne ke biyan sadaki, sai Raja ya ce shi dukiyar Somaraju ya ke so gaba ɗaya a matsayin sadakin. Da ga nan ne fa sai aka fara bayyanawa mai kallo dalilin da ya sa Raja ya ke so ya amshe wa Somaraju dukiya. 


Mahaifin Raja wani mutum ne mai suna Ranga Rao Bhupathi Raja kuma ɗan uwan Somaraju ne ta ɓangaren uwa, a taƙaice ma dai kawun Mahalakshmi ne. Bhupathi Raja babban mutum ne da yake da filaye masu yawa da kadarori, bugu da ƙari yana da mutane sosai kuma yana da ƙafa a gwamnati. Yayin da a ka haifi Mahalakshmi, sai mahaifiyarta ta buƙaci Bhupathi da ya zo domin ya raɗa wa yarinyar suna da sauran al'adun da akan yi a biki irin wannan. A hanyarsa ta zuwa taron ne Somaraju da wasu 'yan daba su ka kai masa farmaki su ka raunata shi har kowa ya yi tsammanin ya mutu. Amma Bhupathi bai mutu ba har sai da ya raɗa wa yarinyar da aka haifa suna Mahalakshmi, ba a jima ba da yin hakan ya faɗi ya mutu ba tare da ya faɗa wa kowa abinda ke faruwa ba. 


Raja sai ya fahimci hakan da ga baya bayan mariƙinsa wato Rangaswamy ya bayyana masa cewa ba shi bane mahaifinsa na gaskiya. A ƙoƙarin ceton Raja ne ma suka sadaukar da ɗan su domin shi ya rayu. A ƙarshe dai, domin ƙwato haƙƙinsa, Raja ya gwabza da Mysamma kuma ya auri yarinyar. 


JARUMAN SHIRIN DA MATSAYIN SU 


Allu Arjun - Bunny/Raja

Gowri Munjal - Mahalakshmi

Prakash Raj - Somaraju

Sarath Kumar - Ranga Rao Bhupathi Raja

Mukesh Rishi - Mysamma

Raghu Babu - 

Sharat Saxena - Rangaswamy

Sudha - Matar Rangaswamy

Seetha - 

Ahuti Prasad - DCP Venkhayya

Rajan P. Dev - Chief Minister Gudumba Chatti

Chalapathi Rao - 

M.S. Narayana Daiva Sahayam


Venu Madhav - 

Fish Venkat - 

Jenny - Lecturer

L. B. Sriram - Doctor

Chitram Seenu - Abokin Bunny

Dil Ramesh - 

Sravan - Tarun


WAƘOƘIN SHIRIN 


1. "Maro Maro" 
2. "Jabilammavo" 
3. "Va Va Vareva" 
4. "Mayilu Mayilu" 
5. "Kana Padaleda" 
6. "Bunny Bunny"

<••••••••••••••••••••••••••••>
      Haiman Raees 
<••••••••••••••••••••••••••••>

        08185819176

Twitter: @HaimanRaees 

Instagram: Haimanraees 

Facebook: Haiman Raees 

Haimanraees@gmail.com 

Miyan Bhai Ki Daring
Share:

HAPPY BIRTHDAY RAANI

HAPPY BIRTHDAY RAANI

Gaisuwa gareki Rani
Sarauniya gareni
Tauraruwar ƙarni
Abar biɗar zamani
Murmushinki na birgeni
Muryarki na ƙayatar da ni
Kafcenki na kafceni
Takunki na ɗasa ni. 

Ni dai komai naki ya min 
Kyautar nishaɗi tuni kin min 
Duk dai ƙusa tuni an min 
Soyayyarki babu mai iya cire min
Ƙwarin gwiwarki ya min 
Nauyin damu ki kan rage min 
Da murmushinki idan kika min 
Ni ke zama ko da matan duniya za su mutumin. 

Allah sarki, kowa ya san ina sonki 
In shirinki zai fito sai in ta ɗoki 
Da kika haihu sai da na ɗanyi biki
Saboda ƙaunar da na ke gareki 
Bana gajiya da kallon shirinki 
Bani ƙosawa da jin Muryarki 
Ji nake kamar Rahul ina na kalli kumatunki 
Kowa ma ya kira ni Raj In har zan ga idanuwanki. 

Happy birthday mai mardani
Fatan nasara gareki mai zamani 
Nasan cewa bakya cin makani
Amma tabbas kina da kyan gani 
Hakan yasa kika sheƙeni 
Kuma na yarda ba batun guna-guni
In kina son wani abu sanar dani 
Zan zamo gareki kamar aljani. 

Asha shagali lafiya 
Allah dai ya ƙara lafiya 
Ya bada sa'ar tafiya 
Ki kame dukka nahiya 
Kowa yace Sarauniya 
Gareki yau mu ke mubaya'a 
Haiman dai tuni yayi niyya 
Zuwa ƙasa ta Indiya 
Domin zuwa gaida gimbiya. 

<••••••••••••••••••••••••••••>
      Haiman Raees 
<••••••••••••••••••••••••••••>

        08185819176

Twitter: @HaimanRaees 

Instagram: Haimanraees 

Haimanraees@gmail.com 

Miyan Bhai Ki Daring

Aaraha Hoon! 


Share:

AN TAƁA YIN FIM AKAN CUTAR CORONAVIRUS


*An tabayin film din daya nuna cutar covid-10 ( coronavirus ) shekaru goma da aula wuce* 

Fim din wanda aka saki a 2011 da bai shahara ba sosai sai bayan buular cutar coronavirus a 'yan kwanakin nan.
Duk da cewa akwai manyan 'yan fim da suka fito a cikinsa kamar su Matt Damon da Jude Law da Gwyneth Paltrow da Kate Winslet da kuma Michael Douglas, a wancan lokacin fim din shi ne na 61 cikin jerin fina-finan da suka fi samun kudi.
Amma Contagion ya bayar da mamaki a lokacin da ya fara shahara a manhajar Apple's iTunes Store inda aka yi ta sauke shi a Amurka, sannan kuma aka yi ta neman fim din a Google.
Kamfanin da ya yi fim din Contagion Warner Bros. - ya ce shi ne na 270 cikin fina-finansa mafi shahara a watan Disambar 2019, a lokacin da aka fara samun rahoton bullar cutar a China.
Wata uku bayan nan, sai ga Contagion ya zama cikin 10 na farko.
Duk dai saboda coronavirus ne, kuma kamanceceniyar da ke tsakanin cutar da fim din ta bayyana karara ne bayan shekara 10 da yin fim din.
Meke cikin fim din?
A cikin fim din, wata bakuwar cuta mai kisa ta kashe wata mata 'yar kasuwa (Paltrow), bayan matar ta samo cutar a yayin wata tafiya zuwa China.
Kasancewar sunan China da ya fito a fim dinne ya sa yake kara yin tashe a makonnin da suka gabata, inda masu kallo suke ta neman Contagion.
Wani abin sha'awa game da yadda fim din ke kara tashe shi ne yadda aka nuna Gwyneth Paltrow (jarumar 'yar Amurka) ta wallafa hotonta tana sanye da takunkumin rufe fuska a cikin jirgin sama ranar 26 ga watan Fabrairu.
Sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram ya ce: ''A kan hanyar zuwa Paris. Fargaba? Tsoro? Shiru? Annoba? Farfaganda? Haka Platrow za ta yi barci da wannan abin a fuskarta cikin jirgin nan.''
''Ina cikin jaruman fim din nan. Ku kula da kanku. Ban da musabaha. A dinga wanke hannu akai-akai,'' a cewar jarumar, wadda ke da fiye da mabiya miliyan shida a shafukan sada zumunta.
Kamanceceniya
Akwai kamanceceniya sosai da abin da ya faru a fim din Contagion.
Jaruma Paltrow ta kamu da cutar mai suna MEV-1, daga wani mai dafa abinci na Hong Kong bayan yin musabaha da shi, shi kuma ya samu cutar a jikin alade a lokacin da yake sarrafa namansa, shi kuma aladen ya samu da kwayoyin cutar ne a jikin jemage.
Bayan haka ne ta shiga jirgi ta dawo gida cikin tsananin rashin lafiya inda ta mutu ba da dadewa ba. Bayan nan ma danta ya mutu, amma mijinta bai kamu da cutar ba.
Ko a gaske, masana lafiya suna ganin cewa cutar ta samo asali ne daga dabbobi a garin Wuhan na China a Disambar 2019.
Ana ganin cewa cutar ta samo asali ne daga jemagu kamar yadda aka yi a fim din Sars epidemic na 2002, daga haka sai ta fara yaduwa zuwa mutane da wasu hallitu.
Har yanzu ba a cimma matsaya ba kan ko wacce dabba ce ta fara yada cutar kamar yadda alade ya fara yada cutar a cikin fim din, sai dai hukumomi a China sun nuna wata kasuwar dabbobi da ke a garin Wuhan inda suka ce daga nan ne cutar ta samo asali.
Kamar yadda ake yada cutar a gaske ta hanyar gaisawa da hannu da kuma kusantar juna, a fim din Contagion ma ta haka ake yada cutar.
Killacewa
A lokacin da ake zargin an samu barkewar cutar a cikin fim din, an ga ma'aikatan hukumar tattara bayanai kan cututtuka suna killace jama'a.
A cikin fim din, an killace jama'a a a garin Chicago na Amurka kamar yadda aka yi a China a halin yanzu.
A yanzu haka an killace jama'a da dama a arewacin yankin a kokarin da ake yi na dakile yaduwar cutar ta Covid-19.
Fargaba da Tasiri
Tunawa da kuma dawo da fim din Contagion ya bai wa Scott Z Burns mamaki matuka wanda shi ne marubucin fim din.
Amma a wata tattauna wa da jaridar Fortune ta yi da shi, ya bayyana cewa ainahin abin da yasa ya rubuta fim din shi ne domin ya ankarar da jama'a cewa irin wannan cutar za ta iya barkewa a cikin al'ummarmu.
''Kamanceceniya tsakanin Contagion da coronavirus ba su da wani muhimmanci saboda ba da gangan muka yi ba,'' in ji Burns.
Barkewar cutar a wannan karon ya jawo yada labaran bogi inda wasu ke cewa an kirkiro wannan cuta ne a matsayin makami mai guba.
Shi kansa Burns, wanda shi ne marubucin fim din ya zama abin zargi.
A wata hira da ya yi da New York Times ya bayyana cewa wasu mutane na zarginsa kan cewa ya shiga kungiyar asiri ta wadanda ke kokarin juya akalar duniya.
''Na tuna a lokacin da na damu kan cewa yaduwar labaran bogi na da hatsari kamar cutar.''
Hujjoji a kimiyance
Za a iya yin bayani kan fim din Contagion kan yadda Mista Burns ya yi kokari wajen bayar da hujjoji a kimiyance.
Sai da ya tattauna da manyan likitoci da kuma jami'an Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, a lokacin da yake rubuta fim din.
Ya bayyana cewa sun ba shi shawarwari matuka.


 *Sasha bhai Singh (( secret super star ))*
Share:

SHAH RUKH KHAN


SHAHRUKH KHAN 👊👊👊👊👊👊
*************************************
*************************************

SWADES was the 1st Movie to be Shot in NASA. 

JAB TAK HAI JAAN was the 1st movie to be Shot in Discovery Channel Headquarters. 

FAN was the 1st movie to be Shot in Madame Tussauds. 

@iamsrk is the only actor whose movies were shot in these Places.

Only 2 Indian Movies were named in the '100 Best Films Of World Cinema' and DEVDAS in one of them.

MY NAME IS KHAN opened more than 20 Overseas Markets for Bollywood. 

Those Countries are:- 
Belgium
Ghana
England
Lebanon
Norway
Sri Lanka
Korea
Singapore
Beirut
Russia
New Zealand
Bahrain
Egypt
Hong Kong
Peru
Spain
Poland
Taiwan
Scotland
Turkey
Nigeria
Netherland

@iamsrk got World's Biggest Superstar tag by 
Forbes
CNN America
BBC America
BBC London
Google
Wikipedia
London Live
Time Magazine
La Times
Davos
Times Of London
Discovery Channel
Nat Geo
One News
Sky News
T&t World
Cgtn China
Global China

@iamsrk got named in the Book 51 Famous Indian People.
In South Africa, KUCH KUCH HOTA HAI made more money than Titanic at the time of its premiere.

 According to a survey conducted by India Today, 14% Indian Considers @iamsrk as the biggest Role Model, beating prime minister Narendra Modi and legendary cricketer sachin Teldunkar 

 According to an Old Survey, Indian youth thinks that SRK is the Best Indian Role Model

According to an Online Poll, @iamsrk is one of those 20 Most Admired Men in the World. 
 @iamsrk is one of the most Prominent People From India.

@iamsrk movies in overseas this decade :- 

MNIK- $23.5M
Ra. One- $10.8M
Don 2- $11.2M
JTHJ- $13.2M
Chennai Express- $19.3M
HNY- $16.7M
Dilwale- $26.6M
Fan- $10.3M
Raees- $14.5M
JHMS- $10.6M
Zero- $11.09M 

Only Actor to give Back to Back 11 movies which collected $10M+ in Ovs.

@iamsrk Won 

🔹Best Indian Citizen Award in 1997
🔹Padma Shri Award in 2005 
🔹Global Personality Award at FICCI in 2010 
🔹Greatest Global Living Legend in 2013

@iamsrk Interaction With Hollywood Singers - 

🔳Akon
🔳Akcent 
🔳Sha
Share:

SHARHIN FIM ƊIN TANHAJI


Daga mahangar #NayaakBhai :Sharhin Film Din
#Tanhaji
VERY IMPRESSIVE MOVIE a gsky film din Tanhaji the unsung warrior ya hadu ainun shiri ne da aka tsara labarinsa da kyau ta inda bazaka so matsawa wani waje ba yayin kallansa zakuma ka ringa kosawa wajan san ganin wuri na gaba daga farkonsa har izuwa karshe komai yayi, kama daga rawar da jarumai suka taka, bayarda umarni da da sauransu, rawarda Ajay, Saif, Kajol da Sharad Kelkar suka taka a bangarorinsu kusan ba wani jarumi ko yan wasa dazakai tunanin zasu fisu dacewa...
Bayan nasarar Bahubaali film din South da akayi Padmavaat masu sharhi dayawa sun Bayyana Padmavaat amatsayin Tamkar da Bahubaali yan South sun kalubalanci yan North wato Bollywood Kan salon iya finafinan yaki ne inda suka Bayyana Padmavaat amatsayin mayarda jawabi ga masana'antun South... Ni a ganina Tanhaji shine amsar Bollywood ga masana'antun kudancin indiya ta fuskar finafinan yaki..
So masoya finafinan kudancin indiya I respect Bahubaali 1da2...ba Ina magana bane Kan kawo kudin film ba Dan Finafinai da sukayi nasarar girgiza Box Office unexpected irin Bahubaali a Tarihin Finafinan indiya kadan NE irinsu Mughal E Azam, Sholey, Hum Aapke Hain Koun.. Maganar tsaruwa da kayatarda mai kallo yasa na kwatanta su.... Wanda ke tantama kan kayatuwa da kyan shirin Tanhaji Yana iya naimansa ya masa kallo a hankalce na Natsuwa Dan tabbatarda kyawunsa..
Naba Tanhaji taurari5*cikin5*
Share:

SHARHIN FIM ƊIN NAYAAK


SHARHIN FIM ƊIN NAAYAK 


Naayak (Hausa: Shugaba) fim ɗin faɗa ne daga kudancin ƙasar India wanda aka fitar a cikin shekara ta 2013. An fassara wannan shiri a cikin harshen Hausa inda aka sa masa suna Masheƙi. 

MA'AIKATAN SHIRIN 

Umurni: V. V. Vinayak

Ɗaukar Nauyi:. DVV Danayya & S. Radha Krishna

Labari/Tsarawa: Akula Siva

Sauti: S. Thaman

Horar Da 'Yan Wasa: Chota K. Naidu

Tacewa: Gautham Raju

Kamfanin da ya shirya: Universal Media

Kamfanin da yaɗa: Errabus Inc.
(United Kingdom & Europe)

Universal Media
(United States)

Ranar Fita: 9 January 2013

Tsawon shirin: mintuna 151 

Ƙasa: India

Harshe: Telugu

Kasafi: ₹35 crores

Kasuwanci: 


MATASHIYA 

Jarumi Ram Charan ya fito a matsayi biyu ne a cikin wannan shiri. Na farko Cherry, injiniyan na'ura da ke zaune a Hyderabad, sai kuma Siddharth Naayak wanda shi kuma matashin shugaba kuma jagoran talakawa ne a Kolkata inda yake yaƙar wani baƙin mugun ɗan siyasa mai suna Rawat. Shirin yana bada labari ne kan yadda Cherry ya taimakawa Siddharth domin yin nasara akan azzalumai. Wannan shi ne shiri na farko da Jarumi Ram Charan ya fara fitowa a matsayi biyu shi kaɗai. 

An fara shirya fim ɗin ne a ranar 9 ga watan Nuwambar 2011, yayinda aka fara ɗauka ta farko a ranar 7 ga watan Fabarairun 2012. Mafi yawancin shirin an ɗauke shi ne a garin Hyderabad da Kolkata, yayin da aka ɗauki wasu Waƙoƙi biyu a birnin Dubai, Iceland da kuma Slovenia, Hakan ya sa Naayak ya zama fim ɗin ƙasar India na farko da aka fara ɗauka a Slovenia. An kammala ɗaukar wannan shiri ne a ranar 29 ga watan Disambar 2012. An saki shirin ne a lokacin bikin Makar Sankranti kuma an haska shi a jikin Majigai guda 1589. Fim ɗin ya samu yabo sosai daga masu sharhi da 'yan kallo baki ɗaya, kuma ya taɓuka abin arziƙi a harkar kasuwancinsa. 

LABARIN SHIRIN. 

Siddharth Naayak ya kashe ƙanin Ministan tsakiya Rawat watau Taxi Seth tare da muƙarrabansa domin ceto mutanensa guda uku. Daga nan sai Rawat ya sa jami'an 'yan sanda da su nemo shi domin a kashe shi. 

A can Hyderabad kuma, akwai wani injiyan na'ura mai suna Cherry wanda kamar su ɗaya sak da Siddharth. Watarana sai kawun Cherry watau Jilebi, wanda kuma shi ne Shugaban kamfaninsu na CgTrix ya faɗa wata gagarumar cakwakiya, domin kuwa ya harzuƙa yaran ɗan dabar da ake jin tsoro watau Babji. Cherry dai ya samu damar ceto kawunsa Jilebi daga Babji ta hanyar hila da yaudara, amma a garin haka sai ya kamu da ƙaunar ƙanwar Babji watau Madhu. Bayan Cherry ya ceci wasu yara daga hannun wani ɗan-ta-kife, sai Madhu ta karɓi soyayyarsa. Wannan abu kuma sai ya harzuƙa Babji har ta kai ga ya yanke shawarar kashe Cherry, amma sai ya firgita yayin da ya ga wanda yake tunanin cherry ne ya kashe shugaban 'yan sandan yammacin Bengal gaba ɗaya. Hakan ya sa suka ɗauka cewa Cherry ne yayi Kisan, alhali kuwa Siddharth ne yayi. 

Da taimakon Jilebi dai jami'in' yan sanda mai bincike daga CBI su ka tafi baje-kolin Kumbh Mela da ke Haridwar domin su kama Cherry. Rawat na cikin aikata aiyukan bikin al'ada sai wannan Jami'i na CBI ya kama Cherry, a daidai lokacin ne kuma Siddharth ya fito daga cikin ruwan da ke zagaye da wurin ya soki Rawat da mashi mai baki uku sannan kuma ya yi artabu da dogaran Rawat. Amma sai Jami'in 'yan sandan ya kama shi ya tafi da shi, hakan ya wanke Cherry daga dukkan zargi. 

Daga baya sai Cherry ya samu cikakken labarin wannan mutum mai kama da shi. Siddharth ya ziyarci gidan yarsa ne a Kolkata domin ci gaba da karatunsa. Yana matuƙar son wannan ya tasa da mijinta da kuma surikarsa watau Nandini. Hasali ma dai Nandini da Siddharth suna son juna har ma an fara maganar aure. 

Ana cikin haka, sai surikinsa wanda ya kasance likita ne ya ya gano cewa fa ƙanin Rawat na biyu wato Badvel yana ba wa yara mata ƙanana sha ka fashe yana tirsasa su yin karuwanci. Yayinda ya kai ƙorafi wa 'yan sanda, bai san cewa ɗan sandan abokin Badvel bane. Hakan ya sa Badvel ya sheƙe shi domin ya sanya shi yayi shiru. Siddharth fa sai ya kasa jurewa wannan al'amari, hakan yasa shima ya sheƙe Badvel, wannan ya sa ya zama sananne cikin ƙiftawar ido. 

Ba'a daɗe da yin haka ba kuma, sai Siddharth ya ƙwace duk kadarorin Rawat ya rabawa talakawa. Rawat sai ya kashe minista kuma ya laƙa wa Siddharth laifin sannan ya caccake shi da wuƙa kuma ya jefa shi a kogi. 

Cikin sati ɗaya Rawat ya haye kujerar sabon minista. Amma bai san cewa Siddharth ya rayu ba kuma har ya fara shirin sheƙe Rawat. Bayan ya kammala karanta labarin Siddharth, sai Cherry ya yanke shawarar taimaka masa. Da shi da Jilebi sai su ka je magarƙamar da aka kulle Siddharth. Bayan ya gabatar da kansa, sai ya bayyanawa Siddharth Shirinsa. Da aka je kotu, sai Siddharth ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da shi. Alƙali sai ya yanke masa hukuncin kisa. 

Kwatsam sai Cherry ya antayo kotun inda ya bayyanawa Alƙali cewa shi ne Siddharth Naayak wanda aka yankewa hukunci kuma ba kowa bane face masoyinsa. Shi ma Siddharth sai ya faɗi daidai da abin da ya faɗa. Hakan ya jawo ruɗani a kotu 

Alƙali sai ya ce ya bawa cibiyar bincike ta CBI kwanaki goma su binciko masa wanene na gaskiyar. A cikin waɗannan kwanaki ne Siddharth ya samu ya dawo da Madhu, Babji da Jalebi Kolkata. 

Kashe gari sai Rawat ya kira Siddharth ya yi masa ƙaryar cewa ya sace wasu 'yan makaranta ya zo ya cece su, amma sai yayi rashin sa'a domin Cherry ya ji maganar don haka sai shi ya riga Siddharth tafiya. A can, Rawat da mutanensa sun yi masa shegen duka. Siddharth shi ma sai ya ce wajen bayan ya samu saƙo daga Rawat inda ya ceci Cherry kuma su ka kashe Rawat. Kotu sai ta kori ƙarar kuma aka wanke Siddharth. A ƙarshe, duka jaruman biyu sun samu damar kasancewa tare da 'yan matan su. 


JARUMAN SHIRIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO A CIKIN SHIRIN 

*. Ram Charan - Charan (Cherry)/Siddharth Naayak.

*. Kajal Aggarwal - Madhu.

*. Amala Paul Nandini.

*. Pradeep Rawat - Minista Rawat.

*. Brahmanandam - Jalebi.

*. Rahul Dev - Babji.

*. Jaya Prakash Reddy - kawun Babji 

*. Ashish Vidyarthi - CBI 

*. Posani Krishna Murali - Shukla Bhai.

*. Dev Gill - Baldev

*. Surekha Vani - Yayar Siddharth

*. Rajiv Kanakala - Surikin Siddharth

*. M. S. Narayana - Mashayin jami'in CBI

*. Raghu Babu - ɗan jagaliyar Babji

*. Anandhi - ƙanwar Raghu Babu

*. Ajaz Khan - Taxi Seth

*. Vineet Kumar - Dassu

* Venu Madhav - Venu

*. Tanikella Bharani - Alƙali 

*. Satyam Rajesh - ɗan jagaliya

*. Sudha - maman Cherry

*. Charmee Kaur 

WAƘOƘIN SHIRIN. 1. "Laila O Laila" 
2. "Kathi Lanti Pilla"
3. "Subhalekha Raasukunna" 
4. "Oka Choopuke Padipoya" 
5. "Nellorae" 
6. "Hey Naayak"

<••••••••••••••••••••••••••••>
      Haiman Raees 
<••••••••••••••••••••••••••••>

        08185819176

Twitter: @HaimanRaees 

Instagram: Haimanraees 

Haimanraees@gmail.com 

Miyan Bhai Ki Daring

Aaraha Hoon! 
Share:

TSOHON MINISTA KAYODE FAYEMI DA DINO MELAYE SUN FARA FIM A NOLLYWOOD


*Tsohon minista kayode fayemi da dino malaye sun fara film a nollywood* 

Mun samu labari cewa Mista Femi Fani-Kayode ya shiga harkar Nollywood, kuma har ya fito a wani shirin wasan kwaikwayo mai suna ‘Silent Prejudice’ da za a saki.
Femi Fani-Kayode ya na cikin Taurarin da su ka fito a kashi na biyu na wannan shiri na ‘Silent Prejudice’. Tsohon Ministan na Najeriya ba bako bane a wajen jama’a.
Fani-Kayode ya fito a cikin wannan wasa ne tare da kyakkaywar tsohuwar matarsa wanda ta yi fice a fagen fim watau Precious Chikwendu, da kuma wasu ‘Yan wasan.
Wannan ne fim na farko da fitaccen ‘Dan siyasar kasar ya yi. Kafinsa an samu ‘Yan siyasa irinsu tsohon Sanata Kogi, Dino Malaye da ya fito a wani wasan kwaikwayo.
Yanzu haka ana karasa kashi na biyu na wannan fim ne a Garin Abuja. A wasan kwaikwayon, an nuna irin kwamacalar da ke cikin sarautar kasar Osu ta Yarbawa.FFK, Dino, Chukwuemeka Ezeife, Ojukwu sun fito a shirin ‘Silent Prejudice’
Ana sa ran cewa fim din zai yi armashi idan ya fito nan gaba domin shugaban hhukumar da ke kula da hakkin Jama’a, Tony Ojukwu, ya na cikin wannan wasan.
Sauran ‘Yan siyasar da su ka shiga cikin fim din sun hada da shi Dino Melaye, tsohon gwamnan jihar Anambra Chukwuemeka Ezeife wanda ya yi mulki a 1992.
Chris Oge Kalu shi ne wanda ya shirya wannan dogon shiri. Taurarin da aka yi amfani da su sun hada da: Clems Ohameze, Amaechi Muonago da Monalisa Chinda.
Sauran wadanda su ka bayyana a fim din da zai fito a Ranar Asabar su ne: Chuks Chyke, Vitalis Ndubuisi, Steve Eboh, Ofiafuluagu Mbaka, da kuma Linc Edochie.


 **Sasha bhai Singh (( secret super star )* ) 


✍🏻Bahijja mahira SBS 

Share:

TINƘAHON HAWAN JAKI MAI HANINIYA


TINƘAHON HAWAN JAKI MAI HANINIYA

Masu rattabe da makafta barkanmu da sake arangama a cikin wani sabon kafcen wanda ni kafta'u jagoran makafta kan kafto muku loto-loto. A yau dai alƙalamin nawa ya dira ne kan jarumi a-jaye-dogon-yaro. Jarumin da a yanzu yake ƙwambo a masana'antar bulbula soyayya gami da sambaɗe-sambaɗe da ke birnin in-da-yaya. Hakan kuma ya faru ne tun bayan antayowar sabon kafcensa mai suna Tinƙahon-hawan-jaki. Shirin, wanda ya fita a cikin watan jan-ido ya ƙwamuso maƙudan matsabbai daga lalitar 'yan kallo fiye da yadda ake tsammani, wanda hakan ne kuma ya bashi damar ɗarewa kan kujerar tarihi irin wacce jarumin bai taɓa hawa ba. Shirin wanda ya ƙunshi jarumai irin su gaje, sumaila da sauransu, a yanzu shi ne kafcen ɗin da ya fi kowanne ƙwamuso citta a cikin wannan shekara a masusukar surfe citta da ke can ƙasar ta in-da-yaya.

Wannan ya sa na ji wasu na cewa akwai yiwuwar fa nan gaba wannan jarumi da shi da jarumi a-kashe-kunama da kuma Ragon-sin za su iya doke waɗannan jarumai uku da ake ji da su watau Shamharu, Sallau da Kuma Amshi. To ko ina aka baro Hantaru gwanin caskale da suburbuɗa a cikin wannan lissafi, sai ku taya ni duba, wai makaho da ya so gulma. Amma kafin nan, na fece!

<••••••••••••••••••••••••••••>
      Haiman Raees 
<••••••••••••••••••••••••••••>

        08185819176

Twitter: @HaimanRaees 

Instagram: Haimanraees 

Haimanraees@gmail.com 

Miyan Bhai Ki Daring

Aaraha Hoon! 
Share:

SHETTY POLICE UNIVERSE: THE INDIAN AVENGERS?

Shetty Police Universe: The Indian Avengers?

An daɗe ana tunanin cewa za'a wayi gari watarana Masana'antar Fina-Finai ta Indiya za ta fitar da wani shiri da zai ƙunshi manyan jarumai kwatankwacin na shirin kamfanin marvel watau Avengers. Wanda in ban manta ba, a shekarun baya har an fara maganar ƙila Fina-Finai irin su Krrish, Ra.one, Robot, Kick da makamantansu za su share fagen faruwar wannan al'amari, sai dai har izuwa wannan lokaci 'yan kallo ba su samu damar ganin wannan mafarki nasu a zahiri ba. Dalili mafi ƙarfi kuwa shi ne: fina-finan ba na kamfani ɗaya bane kuma ba mutum ɗaya ya bada umurninsu ba. 

To ga alama dai mai bada umurni watau Rohit Shetty ya zama mutum na farko a ƙasar Indiya da ya fara share wannan fage a ƙasar ta Indiya tun bayan da shirya fim ɗin Singham, Singham Returns da kuma Simmba. A bisa bayanan da suka bayyana da kuma abinda ya bayyana daga tallar shirin da aka saki, 'yan kallo za su ga jarumi Akshay Kumar a matsayin Jami'in ɗan sanda ne mai suna Veer Sooryavanshi wanda yake yaƙi da ta'addanci. Sai dai a cikin shirin, za mu ga jarumi Ajay Devgn hallau a matsayin Bajirao Singham wanda shima wani ɗan sanda ne da ya fito a cikin wani fim na daban wanda Rohit Shetty ne ya bada umurninsa. Hallau kuma dai, za mu ga jarumi RANVEER SINGH a cikin shirin a matsayin Sangram Simmba Bhalerao wanda shi ma wani ɗan sanda ne mai hali irin na sauran guda biyun kuma daga wani shirin can na daban. Duk a cikin wannan shiri.

A gefe kuma, akwai raɗe-raɗen cewa jaruma Rani, wacce ta fito a matsayin jarumar 'yar sanda mai suna Shivani Shivaji Roy a cikin shirin Mardani ita ma za ta fito a cikin wannan shiri mai suna Sooryavanshi. Wanda idan muka lura da waɗancan jarumai maza guda uku, su kaɗai kawai haɗa su a cikin fim ɗaya ba ƙaramin ƙoƙari bane, sannan haɗa su a irin yadda aka haɗa su a cikin shirin wani abu ne da Bollywood ba ta taɓa ganin irinsa ba. Amma kawo jaruma Rani a cikin shirin, wannan kuma wani abu ne da ya ma fi ƙarfin tunani, domin kuwa ba Rohit Shetty bane ya bada umurnin shirin. 

To sai dai kuma fa abin bai tsaya ga nan ba, wasu rahotanni da ba su da sahihanci suna bayyana cewa idan wannan shiri ya karɓu, to lallai Rohit Shetty zai iya tara wasu manyan jaruman 'yan sanda a cikin shirinsa na gaba watau Singham 3. Rahoton kuma ya ce, matuƙar Rani ta fito a cikin shirin, to akwai yiwuwar cewa Jarumi Salman Khan shima zai iya shigowa cikin tawagar a matsayin Chulbul Pandey daga cikin shirin Dabang, Yayinda Aamir Khan kuma ake tunanin zai iya shigowa a matsayin Surjan Singh Shekhawat daga fim ɗin Taalash.

Sai dai kuma, ba lallai bane hakan ya yiwu bisa duba da banbancin ra'ayi da kuma kamfanoni da masu bada umurnin shirye-shiryen. To amma Rohit Shetty mutum ne mai basira sosai, zai iya shirya sabbin shirye-shirye wa jaruma daban-daban akan 'yan sandan domin ya ƙara faɗaɗa duniyar tasa ta Shetty Police Universe.

Fatan nasara.

Aarahi hai Police

<••••••••••••••••••••••••••••>
      Haiman Raees 
<••••••••••••••••••••••••••••>

        08185819176

Twitter: @HaimanRaees 

Instagram: Haimanraees 

Haimanraees@gmail.com 

Miyan Bhai Ki Daring

Aaraha Hoon! 

Share:

SHARHIN FIM ƊIN I

SHARHIN FIM ƊIN I 

I fim ɗin India ne da aka fitar da shi a cikin shekarar 2015 a harshen Tamil. Shirin ya ƙunshi abubuwa da dama kama daga soyayya, tausayi, cutarwa, nishaɗi da kuma dambe. 

MA'AIKATAN SHIRI 

Umurni: Shankar

Shiryawa: V Ravichandran

D. Ramesh Babu

Tsarawa: Subha (kalamai)

Rubutawa da tsara labari: Shankar

Sauti: A. R. Rahman

Jami'in Shiri: P. C. Sreeram

Tacewa: Anthony

Kamfanin da ya shirya: Aascar Film

Yaɗawa: Aascar Film 

Global United Media (Kerala)


Ranar fita: 14 January 2015

Tsawon Shirin: minti 188
 
Ƙasa: India

Harshe: Tamil


Kasafi: est. ₹100 crore


Kasuwanci: est. ₹240 crore

 An fara ɗaukar wannan shiri ne tun a ranar 15 July 2012, amma sai da aka yi shekara biyu da wata takwas kafin aka kammala aiminsa. Mafi yawancin shirin a ƙasar Sin aka ɗauke shi. Sai dai an ɗauki wasu ɓangori muhimmai a Chennai, Bangkok, Jodhpur, Kodaikanal, Pollachi, Bangalore da kumaMysore. A yayin fitar shirin, an fassara shi izuwa harshen Telugu da Hindi, yayinda daga baya kuma aka fassara shi izuwa harshen Hausa. 

 Masana da masu sharhi akan fina-finai sun yabi irin rawar da jarumi Vikram ya taka a shirin, kuma sun yabi kayan aikin da aka yi amfani da su tare da sautin shirin da Waƙoƙinsa tare da kayan kwalliyar da aka yi amfani da su a cikin shirin. Sai dai sun caccaki yanayin tsarin labarin da kuma tsawonsa. Sai dai hakan bai hana shirin kawo maƙudan kuɗade a harkar kasuwancinsa ba, domin kuwa sai da ya kawo kimanin dala miliyan talatin da biyu a harkar kasuwancinsa na duniya baki ɗaya, watau (US$32 million) worldwide. Hakan ya sa shirin ya zama fim ɗin Telugu da ya fi kowanne kawo kuɗi a wancan lokaci kuma ya zama fim ɗin Vikram da yafi kowanne kawo kuɗi a wancan lokacin. Hallau kuma dai, shirin ya samar wa jarumin lambar yabo ta gwarzon jarumin shekara na FILMFARE watau Filmfare Award for Best Actor – Tamil. 

LABARIN SHIRIN 

Lingesan wani mai motsa jiki tare da tara ƙwanji ne daga Chennai wanda babban burinsa shi ne ya zama na ɗaya a Indiya, watau dai yana so ya kai matakin Mr. India. Cikin sa'a kuwa sai ya lashe gasar Mr. Tamil Nadu watau gwarzon yankinsa, wanda kuma hakan ya bashi damar shiga gasar lashe kambun Mr. India. 

Kwatsam sai ya kamu da son wata kyakkyawar 'yar tallar gidan talabijin mai suna Diya. Ba su daɗe da haɗuwa ba, sai Diya ta faɗa cikin matsala, domin kuwa abokin aikinta mai suna John ya tsula mata tsiya ta hanyar daƙile mata hanyoyin kasuwancinta saboda ta ƙi yarda yayi lalata da ita. 

A yunƙurinta na ganin cewa ta dawo da martabar aikinta, Diya sai ta yanke shawarar maye gurbin John da Lingesan a wata ɗaukar talla da za ta yi. Ɗaukar za'a yi ta ne a birnin Sin a daidai lokacin da za'a yi gasar Mr. India, amma sai Lingesan ya amince ya sadaukar da burinsa domin faranta mata. 

Kafin ƙiftawa-da-bismillah sai ga Lingesan ya canja nan da nan sakamakon kulawar da wata masaniyar salon Diya watau Osma Jasmine ta yi masa, wanda ita wannan osma ɗin irin matan nan ne da aka sauya wa halitta izuwa rabi namiji rabi mace. Da fari aikin ya ƙi musu kan gado saboda kunyar Diya da Lingesan ya ke ji, hakan ya sa mai bada umurnin ɗaukar ya baiwa Diya shawarar ta yi kamar ta kamu da son Lingesan domin ya zage ya bada abinda ake so. Hakan kuwa aka yi, kuma nan da nan aiki yayi kyau. Sai dai kuma ba'a daɗe ba Diya ta bayyana wa Lingesan gaskiyar magana. Jin haushin hakan ya sa ya maida hankalinsa kan aikin tallace-tallacen gidan talabijin ya ƙyale ta. A hankali kuwa sai gashi sun samu nasara sosai, har ya zama in dai za'a haɗa mace da namiji a talla, to su ne zaɓin farko ga kowa. Da sannu dai, sai Diya ita ma ta kamu da Lingesan har ma aka yi musu baiko. 

A kan harkarsa ta gina jiki gami da tara ƙwanji da kuma talla a talabijin, Lingesan ya samu maƙiya da dama, cikin su akwai John wanda tun daga lokacin da ya shigo harkar shi kuma lamura su ka kwaɓe mishi, har ta kai shi ga yin ƙananan tallace-tallace domin tsira da mutuncinsa. Akwai kuma Osma wacce ta kamu da son Lingesan har ta bayyana masa amma sai ya ƙi amincewa. Akwai kuma ɗan kasuwa Indrakumar wanda kamfaninsa ya samu giɓi sosai sakamakon ƙin yi musu talla da Lingesan yayi saboda rahotanni sun nuna akwai maganin ƙwari a ciki. A gefe kuma can a kwai Ravi wanda shima ya shiga gasar Mr. Tamil Nadu amma sai Lingesan ya yi nasara a kansa. Waɗannan mutum huɗun sai su ka shirya yadda za su ɗauki fansa akan Lingesan. 

A a saura kwana biyu a ɗaura aurensu, sai gashi da haƙoran Lingesan su ka fara zubewa a hankali yayin da fatarsa ita ma ta fara lalacewa. Hakan ya sa shi ya tuntuɓi abokinsa Vasudevan wanda likita ne kuma shi ne mai kula da ahalin su Diya. Vasudevan sai ya bayyana mishi cewa ya kama da wata mummunar cuta ce da ba'a san asalinta ba kuma ba ta da magani. Kamar wasa fa dai, abu sai ƙara gaba yake yi, fuskarsa da jikinsa duk suka fara lalacewa har dai ta kai ga ya koma mai ƙusumbi. A wannan hali, sai Lingesan ya yanke shawarar ɓacewa daga idon duniya tare da rayuwar Diya, ya cimma hakan ta hanyar ƙaryar cewa ya mutu, abokinsa Babu ne kawai da Vasudevan su ka san cewa bai mutu ba. 

 Lingesan sai ya roƙi Vasudevan cewa ya auri Diya, domin shi kaɗai ne ya san halinta kuma ya fahimceta, Vasudevan sai ya amince, inda aka sa ranar biki. 

A ranar bikin Diya sai wani likita mai suna Thiruvengadam ya bayyanawa Lingesan cewa, duk da abinda likita Vasudevan ya faɗa, a zahiri yana fama ne da mura irin ta H4N2 influenza wacce cutar "I"the virus ce ta samar da ita. A ta kuwa cutar ba'a taɓa samunta a ko'ina face in allurarta aka yi wa mutum. Lingesan sai ya fahimci cewa John, Osma, Indrakumar, Ravi da kuma Vasudevan su ne suka haɗa kai su ka yi masa allurar cutar. Ashe Vasudevan yana matuƙar ƙaunar Diya tun tana ƙarama. Kuma ya harzuƙa matuƙa da ya ji ta zaɓi wani a madadinsa, wannan ya sa ya haɗa kai da maƙiyan Lingesan su ka haɗa tuggun lalata masa rayuwa. 

Daga nan sai su ka zane Lingesan kuma suka ɗaure shi, amma ya samu sa'a ya fece. Jin haushin irin wannan yaudara da aka yi masa, sai Lingesan ya sace Diya a ranar ɗaurin auren ya ajiye ta a wani keɓaɓɓen gida ba tare da ya bayyana mata ko wanene shi ba. 

Tare da taimakon Babu, Lingesan sai ya yanke shawarar ɗaukar fansa a kansu ba tare da kisa ba. Da fari ta kan Ravi ya fara, inda ya yi sanadin da ya samu mummunar ƙuna. Daga nan kuma sai ya haɗa wani mai na musamman ya ajiyewa Osma ta shafa ba tare da ta sani ba. Hakan ya sa gashi ya firfito mata a jiki. Na gaba kuma shi ne Indrakumar, wanda ya sha harbi daga zuma. 

A ƙarshe kuma sai yayi faɗa da John akan wani jirgin ƙasa mai gudu inda a haka ya je ya lahanta kanshi. Daga nan kuma sai ya yi wa Vasudevan wayo shima ya yi wa kansa allurar cutar ta "I". Bayan ya cimma burinsa na ɗaukar fansa, sai Lingesan ya bayyanawa Diya halin da ake ciki. Duk da cewa da ji daban, ta bayyana mishi tana son shi duk da irin halin da yake ciki, kuma daga nan su ka yanke shawarar ci gaba da yin rayuwarsu a ɓoye. A ƙarshe dai Lingesan ya koma daidai bayan ya bi wani tsari na samun lafiya. 

JARUMAN SHIRIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO A CIKIN SHIRIN 

Vikram - Lingesan

Amy Jackson - Diya

Suresh Gopi - Vasudevan

Santhanam - Babu

Upen Patel - John

Ramkumar Ganesan - Indrakumar

Ojas Rajani - Osma Jasmine

M. Kamaraj - Ravi

Mahru Sheikh - Maman Diya

Azhagu - Mahaifin Lingesan 

T. K. Kala - Mahaifiyar Lingesan

Mohan Kapoor - Sushil

Srinivasan - Keerthivasan

Yogi Babu 

 
<••••••••••••••••••••••••••••>
      Haiman Raees 
<••••••••••••••••••••••••••••>

        08185819176

Twitter: @HaimanRaees 

Instagram: Haimanraees 

Haimanraees@gmail.com 

Miyan Bhai Ki Daring

Aaraha Hoon! 

Share:

SHIN JARUMA DEEPIKA ZA TA KOMA YIN FIM A KUDANCIN INDIYA NE?


SHIN JARUMA DEEPIKA PADUKONI ZATA KOMA YIN FILM A KUDANCIN INDIA NE?


Mutane Kadan ne Suka Sani Cewa Shahararriyar Jaruma Wadda tayi fice a Bollywood Har ta Kara Ci Gaba da Nuna Bajintar a Masana'antar Hollywood Watau DEEPIKA PADUKONE Cewa ta Fara Film dinta na Farko Daga Kudancin India Kuma Yaren Kannada Film me Suna AISHWARYA Wanda ya Futa a 2006.
Abin Birgewa Duk da Wannan Jaruma ta Kai Wani Matsayi Me nisa a Masana'antar Bollywood Wanda Itace Mafi Girma a Masana'antun Shirya Fina-Finai na India Amma duk da Haka da Kafar Sadarwa ta IANS, da Suka Hira da ita Suka Tambayeta ko Zata iya komawa Tace Ai Ita Yare Bazai Zama Shamaki a gareta ba Kawai Ita Kyawun Labari Takeso Idan ta Samu a Wane bangaren Yare ne Yi Zatayi.

By #AbbaIndiaDala
Share:

SHIN JARUMA DEEPIKA ZA TA KOMA YIN FIM A KUDANCIN INDIYA NE?


SHIN JARUMA DEEPIKA PADUKONI ZATA KOMA YIN FILM A KUDANCIN INDIA NE?


Mutane Kadan ne Suka Sani Cewa Shahararriyar Jaruma Wadda tayi fice a Bollywood Har ta Kara Ci Gaba da Nuna Bajintar a Masana'antar Hollywood Watau DEEPIKA PADUKONE Cewa ta Fara Film dinta na Farko Daga Kudancin India Kuma Yaren Kannada Film me Suna AISHWARYA Wanda ya Futa a 2006.
Abin Birgewa Duk da Wannan Jaruma ta Kai Wani Matsayi Me nisa a Masana'antar Bollywood Wanda Itace Mafi Girma a Masana'antun Shirya Fina-Finai na India Amma duk da Haka da Kafar Sadarwa ta IANS, da Suka Hira da ita Suka Tambayeta ko Zata iya komawa Tace Ai Ita Yare Bazai Zama Shamaki a gareta ba Kawai Ita Kyawun Labari Takeso Idan ta Samu a Wane bangaren Yare ne Yi Zatayi.

By #AbbaIndiaDala
Share:

MADHUBALA: THE TIMELESS BEAUTY AND TRAGEDY 3

MADHUBALA THE TIMELESS BEAUTY AND TRAGEDY (KASHI NA UKU) 

Zuwan film din Dilip kumar na farko wato JWAR BAHTA shine silar haduwar su. A sets na film din jinin su ya hadu, suka saba sosai. A hankali haduwar jini ya koma soyayya,. Abubuwa suka fara daukar salo mai ban sha'awa kai kace sun kusa aure.....ZUWAN NAYA DAUR ya zama sanadiyyar rabuwar su. Sun fito tare a film din NAYA DAUR, amma a yarjejeniyar contract na Madhubala, dole zata dinga fita outdoor shooting, A lokacin mulkin mallaka da mahaifin ta ya saba yi mata ya kuma tashi, yaki yarda da Hakan, Jarumi Dilip kumar ya so yabi raayin masoyiyar sa. Hakan yasa producer na film din B R Chopra ya kai maganar kotu, domin a tilasta musu su yarda da abinda suka rattaba hannu akai game da film din. Kotu ta tilastawa Dilip kumar ya girmama yarjejeniya, hakan yasa tilas ya goyi bayan Producer. Wannan ya janyo sabanin raayi tsakanin Dilip kumar da Madhubala... ITA TABI UMARNIN MAHAIFIN TA, SHI KUMA YABI UMARNIN KOTU... Daga nan Madhubala ta fita daga Film din, Aka musanya ta da jaruma Vyjayanthimala. A gefe guda tuni dama akwai wani sabanin raayi tsakanin Dilip da baban ta, a matsayin ta na wacce family din gaba daya suka dogara a kan ta, kuma Dilip kumar ya sanya sharadin cewa zata daina film bayan sun yi aure, a ganin mahaifin idan ta daina film ta wacce hanya zasu samu abin rufawa kansu asiri? Wani source din ma ya tabbatar da cewa, ATTAULLAH KHAN zai yi amfani da auren su ne wajan cimma wasu bukatun a fagen kasuwancin film kasancewar yana da kamfanin film da yake son rayawa. A ganin sa idan auren ya tabbata, zai iya amfani da su biyun wajan tada kamfanin sa ya zama shahararre. Se su koma karkashin sa, shi ya zama boss nasu. Abin da Dilip kumar ya ke ganin Sam ba zai dauka ba, musamman da yake yana kan number one star a Bollywood a lokacin. Duk wannan suka hadu suka kawo karshen soyayyar,

 Madhubala na yawan kuka a lokacin, saboda masifar son sa da take yi. Sukan yi magana ta telephone, ko za a samu mafita. Kamar yadda yar uwar ta Madhur ta bayyana

Dilip kumar kept saying, ‘Leave your father and I’ll marry you’. She’d say, ‘I’ll marry you but just come home, say sorry and hug him.’He refused, so Madhubala left him. That one ‘sorry’ could have changed her life. It was zid (stubborness and ego) which destroyed their love. My father never asked her to break the engagement or ever demanded an apology from him.

Matsalar ta zame mata biyu, tana fama da karayar zuciya wacce ta sha wahalar soyayya... A cikin wannan halin, tana shooting na wani film mai suna BAHUT DIN HUE cutar ta ta zuciya ta bayyana, ana kiran cutar da VENTRICULAR SEPTAL DEFECT. Cutar da ke bayyanar da huda a zuciyar dan Adam. Ta dinga Amai na jini. An kaita asibiti., likitoci suka bada shawarar ta huta a gado na tsawon wata uku. Se dai maimakon hutun, sae taci gaba da aikin films saboda a ganin ta, hutun wata uku zai sanya films din ta da aka fara shooting su shiga wani hali. A dalilin haka cutar ta cigaba da karuwa

 Issue na rashin lafiyar ta tun yana sirri a cikin family har abu ya fito fili har ta samu wasu failures a box office na dan lokaci, aka sa mata suna BOX OFFICE POISON
Role mafi girma da tayi a career nata A matsayin ANARKALI a film mai suna MUGHAL-E-AZAM ya fara ne a 1953... Bisa matsalar da take ciki reports sun nuna cewa DILIP KUMAR na daga cikin silar da yasa aka zabe ta ta fito a film din. Shooting na MUGHAL-E-AZAM ya dau kimanin shekara tara ana yi, tun bayan rabuwar masoyan, basu kara haduwa se a wajan shooting din. Se dai basa magana har sai inda scene ko dialogue ya hada su. Masana sun bayyana cewa shooting na MUGHAL-E-AZAM ya dan haska irin yanayin soyayyar su a rayuwar gaske. Saboda kamar yadda ANARKALI take kokarin bayyanawa a fili cewa bata son Salim duk da a zuciyar ta tana son sa, haka nan a gurin shooting ta dinga nuna kamar babu son sa a ranta, duk da a cikin zuciyar ta ba haka bane

Scene na karshe, inda matsanancin tsoro da dimuwa ya bayyana karara a fuskar ANARKALI musamman a kwayar idanun ta a yayin da ake ginin kasa a kewaye ta, domin rufe ta har ta mutu a haka.... Ya zama daidai da irin dimuwa da tsoro da take fama da shi a rayuwar gaske saboda tarfata da jikin ta ya fara yi sannu a hankali(wanda ya kalli Mughal-e-Azam zai fahimci me nake nufi) 
 Kafin late 50s, cutar ta tayi tsamari musamman saboda mawuyacin scenes da ta dinga yi a MUGHAL-E-AZAM. Director K Asif bashi masaniyar illar da dogon scenes na film din ya haddasa akan rashin lafiyar ta., tun daga doguwar tsayuwa da tayi a matsayin gunki wacce aka yiwa fenti har ya sa numfashi ke mata wahala, zuwa daurin ta aka dinga mata da ankwa na tsawon lokaci, har ma ta dinga jan wannan ankwar mai nauyi tana zagaye suna daure a jikin ta.... Kanwar ta Madhur ta bayyanawa Filmfare cewa

While shooting for Mughal-e-Azam she was tied with chains and had to walk around with them. That was stressful. By the end of the day her hands would turn blue. She’d even refuse food saying that she had to look anguished and weary for the jail scenes.”

Tayi soyayya ta karshe da kishore kumar, soyayyar da ta kai ga aure... Se dai bayan auren aka rasa inda soyayyar tayi.Ta samu kudi da daukaka, se dai tana bukatar wani a kusa da ita domin samun daidaito a kan al'amuran ta. Kishore kumar shi kuma yana bukatar tallafi na kudi sakamakon bashi da ya tara a kan sa na hukumar karbar haraji masu yawan gaske, har ta kai ga hukumar ta daga gidan sa domin sayarwa. Haduwar sae yaso ya bada ma'ana, se dai bai bayar ba,. A tunanin sa matarsa zata tallafa masa wajan settling na matsalolin kudi da yake fama da su a lokacin, se dai a gefe guda kuma bai san cewa cutar matarsa ta tsananta haka ba. A bisa Hakan ita ma kanta tana bukatar taimako.

 Ba dadewa da auren su ya kai ta London domin a duba lafiyar ta. Se dai bayan gwaje gwaje da bincike akan lafiyar ta, likitocin sun tabbatar da cewa Madhubala ba zata warke ba, kuma zata mutu bayan shekara biyu zuwa uku, kasancewar a lokacin ba a samu maganin warkar da huda ta zuciya ba.. sun yi wa yanayin mutuwar da zata yi hasashe da suna "SLOWLY AND PAINFUL DEATH"

Yar uwar Madhur tace

Due to her ailment, her body would produce extra blood, which would spill out from her nose and mouth. The doctor would come home and extract bottles of blood. She also suffered from pulmonary pressure of the lungs. She coughed all the time. Every four to five hours she had to be given oxygen or else would get breathless

: Wani zai yi tunanin cewa jin irin wannan rashin lafiyar a tare da matar sa zai ajiye komai nasa gefe guda ya tattara hankalin sa gun ta. Se dai sabanin Hakan ne.
 Kamar yadda kanwar ta 
Fada 

"Soon after that Kishore Bhaiyya left her at our home. He said that she was sick and needed care while he had to travel, work, sing and hence wouldn’t be able to give her time,"

Yayin da korafi ya fara karfi daga bangaren family na Madhubala don ganin halin ko in kula da yake nuna mata... kishore kumar ya maida cewa

 "‘I tried my best, I took her to London. But the doctors have said she won’t survive. What’s my fault?”
 Koda yake Madhur bata kalli kishore kumar a matsayin mutum mara kirki ko tausayi saboda barin yar uwar ta da yayi a gadon mutuwar ta ba, se dai a ganin ta tunda ya aure ta da masaniyar halin da take ciki, ya kamata ya kasance da ita har zuwa karshen ta. Ga abin da take fada game da haka

We’re not saying that he was wrong. Aapa was told by the doctors ‘you cannot have sex, you cannot have children’… But yet a woman needs emotional support no matter what. Aapa insisted that she wanted to be with him," "So he bought a flat at Quarter Deck, Carter Road where they stayed for a while. But she’d be alone most of the time. The sea breeze made her sicker. But she had tremendous willpower. She was supposed to live for two years. She went on to live for nine. She’d cry and say
 Mujhe zinda rehna hai, mujhe marna nahin hai, doctor kab ilaaj nikalenge?’ (I want to live; I don’t want to die.When will the doctors find a cure?)”Am sure I'll get operated someday

A kwanakin ta na karshe da jikin ta ya kara tsananta, mahaifin ta ya kira kishore kumar yazo yaga halin da take ciki amma yaki zuwa, saboda yana da event a Kolkata kuma yana tsoron cewa fasa tafiyar tasa zata sa organizers na event din su yi asarar kudi mai yawa. Mahaifin Madhubala cikin takaici yace "YOU'LL NEVER SEE HER AGAIN".......
Ta so ta dawo acting a shekara ta 1966 a inda ta so karasa film din ta CHALAK tare da Raj kapoor, wanda shooting kadan ya rage, amma Sam jikin ta ya kasa jurewa. Dole ta hakura da acting ta juya directing na film. A shekara ta 1969 ta fara directing film din farko mai suna FARZ AUR ISHQ,.. Se dai tun a pre production na film din Allah ya mata rasuwa wanda ya kama ranar 23 February 1969. A saboda haka ba a yi film din ba

Ta rasu kwanaki kadan da cikar ta shekaru talatin da shida(36 years). An binne gawarta a juhu Muslim cemetery dake garin Mumbai. A jikin kabarin ta, an yi alama da rubutu na wasu ayoyin Al qurani mai girma. Se dai a shekara ta 2010 aka share kaburburan su wanda ya hada harda na Muhammad Rafi, parveen babi, Naushad Ali, Talat Mahmud da sauran su...Shekara daya da rasuwar ta, aka maganin warakar cutar da ya zama ajalinta (ventricular septal defect) a inda patient din da aka yiwa theatre ya farfado cikin nasara.

ALHAMDULILLAH

ABDUL KING KHAN AKK

Share:

MADHUBALA: THE TIMELESS BEAUTY AND TRAGEDY 2

MADHUBALA THE TIMELESS BEAUTY AND TRAGEDY (KASHI NA BIYU)

A shekara ta 1942 a Bombay, wani dan kyakkyawan dogon saurayi mai suna ATTAULLAH KHAN wanda kamfanin sarrafa Tobacco dake garin Delhi suka kora daga aiki, ya fara amfani da mafi kyawu a cikin ya'yan sa yar shekara tara wajen samar musu mafita. Sunan yarinyar MUMTAZ JEHAN DEHLAVI wacce aka canzawa suna zuwa MADHUBALA.. An haifi wannan kyakkyawar jaruma a ranar sha hudu ga watan February 1933 wanda yayi daidai da ranar masoya wato VALENTINES DAY. Sunan mahaifiyar ta kuma Ayesha Begum Iyayen sun haifi yara guda goma sha daya, kuma Madhubala itace ta biyar.  

 Tun a yarintar ta, take ganin bakin ciki.Turnuke a cikin talauci, yan uwan ta maza guda biyu, da mata uku duk suka rasa ran su suna yara, babu wanda ya wuce shekara shida a cikin su duka biyar din. Studio mai suna BOMBAY TALKIES, wanda ya kasance mallakin Babbar tauraruwar jaruma DEVIKA RANI suka fara baiwa madhubala aiki a matsayin child artist tun tana yar karamar ta.A lokacin akan kira ta da BABY MUMTAZ. BASANTI shi ya kasance film din ta na farko. Daga nan tayi ayyuka da ɗan dama a matsayin child artist. SE DAI DUK DA HAKA..... TALAUCI YAKI BARIN GIDAN SU. A daidai wannan lokacin ne babbar jaruma ta lokacin wato DEVIKA RANI hankalin ta ya kai ga baiwa guda biyu da BABY MUMTAZ take dauke da su.... KYAU DA KWAKWALWA.. Wannan shine dalilin da ya sa ta shawarci yar BABY MUMTAZ da ta canza sunan ta zuwa MADHUBALA a matsayin sunan da zata yi amfani da shi a kan screen.. Wanda a turance yake nufin "honey belle" A Cewar DEVIKA RANI, duk sanda BABY MUMTAZ tayi murmushi, ta kan yi kama da flower mai rangaji.

Ba dadewa wani masanin ilimin taurari mai suna Kashmirwalle, yayi hasashe a kanta cewa wannan yar yarinyar zata samu daukaka, arziki da suna fiye da tunani.... irin wanda kaf dangin su babu wanda ya taba yin kwatankwacin su, amma zata hadu da bakin cikin rayuwa mai kunshe da rashin dace a soyayya, rashin soyayya a rayuwar aure.... Sannan baza ta Dade a duniya ba. Duk al'amuran nan se da suka kasance a kan ta.

Madhubala ta dawo Mumbai tare da family a inda ta zauna a irin gidajen dake kusa da ruwa. Ana nan kwatsam ranar sha hudu ga watan April 1944.. Madhubala da yan gidan su sun tafi kallon film a theatre aka samu explosion a nahiyar da suke .Gidaje da dama suka ƙone, ciki kuwa har da gidan su Madhubala. Aka yi asarar rayuka. Sanadiyyar haka suka kasance babu gida. Wata classmate dinta ce ta basu gurin zama a gidan su.. Bayan faruwar Hakan da kadan ne ta fara aiki a matsayin jaruma. An ganta a film din director kidar sharma mai suna Neel kamal wanda ta fito da babban jarumi Raj kapoor. A lokacin bata fi shekaru sha hudu ba.... Tun a wannan lokacin, murmushin ta kadai ya kan isar da sakonni da dama. Wa zai manta film dinta MAHAL, wanda ta fito tare da Ashok kumar? Haka nan babu wanda zai manta wakar Aayeega Aanewala. Koda yake jaruma suraiya ce first choice da aka so ta yi MAHAL., amma daga baya Kamal Amrohi ya bata dama....... DAGA NAN FA BATA KARA WAIWAYOWA Ba....... DULARI, BEQASOOR, TARANA, BADAL, acting din ta sun cancanci kallo daga maabota kallon films.( Ko da yake masana sun tabbatar da cewa tsananin kyawn ta ya sanya har ba a kula da talent din ta a fagen acting) .

Kyau, stardom, suka bayyana tare da Madhubala. Masoya suka fara kawo farmaki. Kai kace idan mace ta hada kyau da daukaka to se yadda ta ga damar sarrafa soyayyar ta. A bangaren Madhubala chakwakiya ce. : Maza wajen guda bakwai suka shigo rayuwar Madhubala suka fita suka barta a gadon mutuwar ta. Tun daga masoyin ta na yarinta wanda ta bawa kyautar jan rose flowers a Sanda zata koma Mumbai domin tabbatar da cigaba da wanzuwar soyayyar su, wannan flower ya ajiye har bayan mutuwar ta su ya kai ya ajiye a gefen kabarin ta. 
Director kidar sharma ya so ta a ganin farko, se dai bata so shi ba domin tana ganin ya mata tsufa. Director na film din MAHAL wato kamal Amrohi shi ya biyo baya, sun sha soyayya sosai, sukan yi awannni suna soyayyar su. A Cewar masana, wannan shine lokaci mafi farin ciki a rayuwar ta. Mahaifin ta ma yayi Na'am da soyayyar, a inda yake cewa

Aage chalke ein donho ki shaadi ho jaaye to mujhe koyi aitraaz nahin hai” (I have no objection if they marry each other in the near future.)

Rabuwar su yazo ne saboda Madhubala ta bukaci ya saki matarsa saboda bata so ta yi zaman kishi da wata. Matar kuwa ba wata bace illa jarumar Bollywood MEENA KUMARI. Kamal Amrohi yaki yarda da bukatar ta, yace se dai su zauna tare, Hakan ya jawo sanadiyyar rabuwar su
 Sun hadu da prem nnath a sets na badal bayan ta zama superstar. Alakar tasu bata fi wata shida ba.. Daga nan madhubala ta fara kaurace masa, a Cewar yar uwar ta Madhur, ta kaurace masa ne saboda ya nemi ta bar addinin ta zuwa nasa. Abin da Sam ba zai yiwu ba a gurin ta ba zai yiwu ba.

Apa [Madhubala] first fell in love with Premnath. The relationship lasted six months. It broke on grounds of religion. He asked her to convert and she refused.......... MU HADU A CI GABAN LABARIN

ABDUL KING KHAN AKK

Share:

MADHUBALA: THE TIMELESS BEAUTY AND TRAGEDY 1


" MADHUBALA THE TIMELESS BEAUTY" IDAN ANA MAGANAR KYAU DA TSARIN HALITTA A TARIHIN BOLLYWOOD DA KE AKE KWATANCE....
************************************************************************************************

MADHU, BEAUTY WITH TRAGEDY, ANARKALI OF INDIAN CINEMA, VENUS OF INDIAN CINEMA, THE TIMELESS BEAUTY, MORILYN MONROE OF INDIAN CINEMA duk suna daga cikin sunayen da ake mata lakabi 

... jarumar da industry bata taba ganin kyakkyawa mai cikar hallita kamar ta ba,Jarumar da ake kira BABY MUMTAZ, (lokacin yarinta), .Itace Jarumar da koda wanda suka saba ganin kyawawa ke santi a cikin kalaman su wajen bayyana ta.

A lokacin da shammi kapoor ya fara ido hudu da ita sai da ya dimauce da ganin kyan halittar wannan baiwar Allah. A inda yake cewa

"I was so nervous to work with her that I use to forget my dialogues. When I looked at her, I was lost and tongue-tied. She knew it too, she could see it and she helped me gradually. In no time, I was in love.. I said it then and still maintain i have never seen such beautiful woman, such perfection of face, form and skin. She was almost ethereal"

Masoyin ta Dilip kumar ya taba bayyanawa gidan jarida cewa

"She was extremely popular and I think the only star for whom people thronged outside the gates. Very often when shooting was over, there’d be a vast crowd standing at the gates just to have a look at Madhus beauty. It wasn’t so for anyone else. That was her personal effect on fans. Her personality was so vivacious,"

  Hasashe daga masana kyau da suka ganta a zahiri kuma suke raye har yanzu, sun tabbatar da cewa kaf hotunan ta dake zagayawa a yanar gizo, ko kusa basa nuna ainihin kyan da take da shi
 Madhubala ta taba fitowa a American magazine a 1952 wanda aka yi mata lakabi da "THE BIGGEST STAR IN THE WORLD".... AND SHE IS NOT IN BEVERLY HILLS. lokacin bata fi 19 years ba.

"She was aware of her beauty, a Cewar wani Filmfare editor kuma abokin mahaifin ta mai suna B K karanjia" ... Inda ya kara da cewa

"and because there were so many in love with her, she used to play one against the other. But it was out of innocence rather than shrewd calculation.”

Mace maabociyar saka farar Saari, mai yawan saka kayan adon gashi a kan gashin kanta. Maabociyar mu'amala da Gold da jewelry. Maabociyar raira poems irin na urdu. ta kan dauki yan uwan ta zuwa unguwa a motar ta hillman, Buick ko station wagon. Kullum sanye cikin Abaya, a wajan traffic idan yan sanda suka tsaida ta suka nemi ta bude lullubin ta, ta kan roke su cewa, pls ku barni a haka, in na bude mutane zasu yanyame ni. Rashin ganin ta sosai a baynar mutane ya sanya ta kara tsada, musamman idan wani dalili ya sa fuskar ta bayyana a wuri to se dai addu'a.

    Mahaifin ta baya barin ta zuwa Award function, ko premiere. Bata da kawaye ko abokai, amma bata taba korafi ba saboda tsabar biyayya ga mahaifin ta. Yar uwar ta Madhur take cewa...... ganin yadda mahaifin mu ya rikewa Madhubala wuta komai nata idon sa na kai, sai ake tambayar sa to me yasa ma ka yarda take yin film? Ya bada amsa cewa "yara na goma sha biyu, na rasa 'ya'ya na maza tun suna kanana, da sun rayu da su zasu tallafa mana. In na tsaya kallo, talauci sai ya kashe mu

    Director mai rike da kambun Academy Award, frank Capra da ya kai ziyara Bombay a wani interview da suke yi, kawai ya ganta a cover na magazine, a take yace "OH GOOD GOD!!! WHO IS THIS BEAUTIFUL GIRL, IS SHE AS BEAUTIFUL IN REAL LIFE? A nan fa ya sa a hada shi da mahaifin ta domin neman a bashi ita ya tafi da ita America ta dinga fitowa a manyan Hollywood films kuma a manyan roles, kuma da Hakan ya yiwu cikin sauki tunda tana da mai koya mata turanci... Se dai baban ta bashi da niyyar sakar mata mara daga rikon tsauri da yake mata... A inda ya maida martani cewa... She couldn't eat with forks and knives.

Shashi Kapoor ya taba kiranta “the sexiest woman I've ever seen” inda ya kara da cewa : “

"I recently saw Mughal-e-Azam and she once again succeeded in destroying me totally. It's a fatal attraction, its not just sexiness but that tremendous quality of projecting love." 

     Rayuwar Madhubala na dauke da wasu al'amura,.... Kyau, matsanancin riko daga mahaifi, cutar huda ta zuciya (ventricular septal defect), rashin dace a soyayya, auren da babu armashi, da Mutuwa a gado bayan jinyar na tsawon shekara tara.

    Mafi alhini a bangaren soyayyar ta shine wanda tayi da Dilip kumar, suna son juna, clash of interest da court case ya raba su, raunanniyar zuciyar ta mai dauke da huda, ya kara samun fami. A rayuwar ta, babu dark secret, babu kura a turnuke a cikin cupboard dinta, babu case na shaye shaye ko halin banza da ire iren su. Madhubalar ce kawai se halayyar ta ta kirki, biyayya, da yawan murmushi mai boye zuciyar da ta sha fama da jarrabawa kala kala har ta kai ga sanadiyyar ta.

    Da yawa se ake ganin wannan kyan, daukakar, suna, farin jini, sun zo ne tare da farashi mai matukar tsada wajan biya....... MU HADU A KASHI NA BIYU DAN GANIN KALUBALEN DA TA FUSKANTA A RAYUWA 

ABDUL KING KHAN AKK
Share:

SHAH RUKH KHAN DA RANVEER SINGH A FILM ƊAYA?


Jaridar Yau Da KuLLum...!


Srk Da Ranveer Zasu FitO A FiLm Guda...?


Wani Jita Jita Dayake YawO Akafafen Sada Zumunta Nabayyana Srk Da Ranver Sing Zasuyi Remake Na FiLm Din "Mr India" Wanda YafitO Daga Bakin Maibada Umarni ( ALi Abbas Zafar ) Wanda Hakan Ya HassaLa Jaruma Sonam KapOOr Bisa Ganin Rashin Girmamawa Ga Mahaifinta Wanda Shine YajagOranci FiLm Din Amatsayin ActOr' A 1987 Wanda FiLm Din Yasamu Nasara MatuQa A bOx Office Sannan Kuma Yadaga Jarumi AniL KapOOr. 
.
.
Jarumar Tabayyana Ba'ayiwa Babanta AdaLceba Wanda Kamata Yayi Sai Ansanar Dashi Kafin Afitar Da Lavarin Wanda Kuma Tabayyana Baisaniba. Haka Shima Maibada Umarnin FiLm Din 'Shekar Kapur. Yabayyana Masaba. 

Saidai Jama'a Sunga Sauri Irin NasOnam Wanda Bataji Daga Bakin Koda Daya Daga Cikin Jarumanba. Srk Ko Ramveer. Saidai Kuma Yiwuwar Wannan FiLm Din Abune Maiwuya Sbd Srk..
.
.
DafarkO Wasu Mutanen Naganin Srk Yadaina FiLm Da Sanjay Ne. SBD wani Ra'ayi Nakansa Wanda FiLms Dinsa Biyu Nabaya Duk Srk Yafara Nena Kuma Yaqiyinsu Sune. " *BajirawO Mastani*" Da *"Padmavaat"* Wadannan FiLm Duk Srk Yafaru KawOwa Amma YaQiyi Daga Baya Yanemi Ranveer. 

Sannan Kuma Abune Mai Wuya Yiwuwar FiLm Din Sbd YanasO Srk YafitO Amatsayin Amrish Wanda BayasOn Cigaba Da FitOwa A Mugu. Sannan Kuma Srk Bayayin Remake FiLm...


By_Ibrahim_khan_Srk
Share:

JARUMAN INDIYA 11 DA SU KA MUSULUNTA


Jaruman Indiya 11 da suka Musulunta

1. AR Rahman
Hakkin mallakar hotoJASON MERRITT
An haife shi a matsayin wanda ke bin addinin Hindu, daga bisani kuma ya karbi musulunci.

Ya sauya sunansa daga Dileep zuwa Rahman. Mawakin Indiya ne wanda ya lashe kyautar Oscar. Mutum ne kuma da tunaninsa ya karkata zuwa kin wanzuwar Allah, da farko, amma daga baya sai ya karbi musulunci ya kuma zama mai karfaffan imani da Allah.

Abin da ya ce game da komawarsa musulunci ba abin mamaki ba ne kamar yadda ake nunawa.

TALLA

"Mutanen gidanmu sun kadaita saboda haka lokacin da wasu karance-karance na Sufanci suka yi tasiri a kaina sai na musulunta".

Daga cikin wakokinsa da suka yi fice akwai Maa Tujhe Salaam.


2. Kamala SurayyaTa fito ne daga cikin iyalan da aka fi martabawa a kasar. Marubuciya ce, ta kuma musulunta ne a 1999. Ta sauya sunanta daga Madhavikkutty zuwa Kamala Surayya, bayan ta musulunta.

Ta musulunta ne bayan karanta wani littafi mai suna "The love Queen of Malabar''. Littafin dai ya janyo ce-ce-ku-ce a kasar.

3. DharmendraHakkin mallakar hotoSTR
Shahararren jarumin fina-finan Bollywood, kuma mahaifin Sunny Deol, Bobby Deol, Esha Deol da Ahana Deol. Ko da yake ya karbi musulunci, amma majiyoyi sun ce ba ya dabbaka shi.

Dalilin musuluntarsa shi ne, saboda ya auri jaruma Hema Malini, a al'adarsu mabiya addinin Hindu, ba a auren mata biyu, to sai kuma soyayya ta shiga tsakaninsa da Hema har suka shirya auran juna a wancan lokacin, to sai ya duba ya ga ai addinin musulunci ya bayar da damar auren mata fiye da daya.

Sai ya musulunta, sannan suka yi aure tun a 1980. Ya fito a fina-finai kamar Sholay da Jugnu.

4. Yuvan Shankar Raja
Mawaki kuma mai rubuta waka. Da ne a wajen shahararren mawakin nan Ilayaraja. Bai jima da karbar musulunci ba. Shekarunsa a 2018, 38.

Ya bayyana dalilin da ya sa ya musulunta. Ya ce "Mahaifina rikakken mabiyin addinin Hindu ne, kuma ya yi nisa wajen camfe-camfe ta yadda ko da gilashi ne ya fashe sai ya kira malamin duba.

Dukkan iyayena sun yi imani da camfi, to wata rana sai mahaifiyata ta mutu a hannuna bayan gajeriyar rashin lafiya, nan na yi tunani na ce ya aka yi haka, yanzu fa take numfashi, to yanzu tana ina?

Anan na fahimci cewa ba wanda zai karbi numfashinta face Allah (SWA)".

5. Mamta Kulkarni

Hakkin mallakar hotoASWAJITH ONLINE
Ta taka muhimmiyar rawa a fina-finan Bollywood. Mijinta Vicky Goswami ya fara musulunta, da za ta aure shi, sai ta musulunta ita ma.

Yanzu haka suna zaune a Nairobi, babban birnin kasar Kenya. Ta fito a fina-finai kamar Karan Arjun da kuma Beqabu.

6. Mahesh Bhatt
Hakkin mallakar hotoPUNIT PARANJPE
Furodusa ne kuma daraktan fina-finan Bollywood. Ya musulunta ne saboda ya auri matarsa ta biyu Soni Razdan, kasancewar a addinin Hndu ba a auren mace fiye da guda.

To sai dai kuma rahotanni sun ce duk da ya musuluntan ba ya dabbaka addinin. Mahesh Bhatt, mahaifine ga jaruma Pooja Bhatt da Alia Bhatt. Daga cikin fina-finan da ya shirya akwai Gumrah da Duplicate.

7. Hema MaliniHakkin mallakar hotoKRISTIAN DOWLING
Shahararriyar jaruma ce a fina-finan Bollywood. Matar Dharmendra, mahaifiyar jaruma Esha Deol.

Hema sun yi aure da Dharmendra a 1980, amma kafin su yi aure sai da ta musulunta saboda mijin nata ma ya musulunta.

To amma Hema, har yanzu ta na bin addinin Hindu ne. Hema ta fito a fina-finai kamar Dream Girl da kuma Seeta Aur Geeta.

8. Sharmila Tagore
Hakkin mallakar hotoFRANCOIS GUILLOT
Sharmila Tagore, ta musulunta ne sakamakon auran mijinta Mansoor Ali Khan a shekarar 1969.

Ta sauya sunanta daga Sharmila Tagore zuwa Ayesha Sultana bayan musuluntarta.

Ita da mijinta, sun haifi 'ya'ya uku, Saif Ali Khan da Saba Ali Khan da kuma Soha Ali Khan.

Sharmila Tagore ta fito a fina-finan Bollywood da dama da suka yi fice kamar Aradhana wanda suka fito tare da Rajesh Khanna.

9. Monica
Hakkin mallakar hotoASWAJITH ONLINE
Fitacciyar jaruma ce a fina-finan kudancin India. Ta sanar da Musuluntarta ne a 2014, amma tun a 2010 ta karbi Musulunci. Ta sauya sunanta zuwa MG Rehima.

Mahaifinta Hindu ne, mahaifiyarta kuma kirista ce.

10. Amrita Singh


Amrita Singh ta taka muhimmiyar rawa a fina-finan Indiya. Tsohuwar matar Saif Ali Khan ce inda suka haifi 'ya'ya biyu, wato Sara Ali Khan da Ibrahim Ali Khan.

Ta taso a matsayin mai bin addinin Sikh daga bisani ta Musulunta. Cikin fina-finanta da suka yi tashe akwai Mard da Aaina.

11. Hans Raj Hans
Hakkin mallakar 
Hans Raj Hans, mawaki ne a Indiya. Ya musulunta ne a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Pakistan.

A da yana bin addinin Sikh ne, daga bisani kuma ya Musulunta.

ALLAH YADAGA MUSLUNCI 

BY BASH KHAN 

KANO R/LEMO CITY
Share:

SHIN KO KUN TUNA DA ƘAYATACCIYAR WAƘAR JABRA FAN?


SHIN KUN TUNA QAYATACCIYAR WAQAR NAN JABRA FAN?

Wannan Kayatacciyar Waqar da Tayi Fice Kuma Ta Karbu Wajen Masoya Kallon Fina-Finan India Wanda Akayita Acikin Film din FAN na Babban Tauraro SHAH RUKH KHAN.

 Hukumar shariar nan ta kasa (National Consumer Disputes Redressal Commission) ta umarci kamfanin YRJ wanda suka shirya film din Fan na jarumi Sharukh Khan akan su biya AFREEN ZAIDI tarar rupee 15,000 sakamakon rashin saka wakar JABRA FAN da basuyi ba a film din.

Idan masu karatu basu manta ba a shekarar da film din FAN ya futa (2016) an samu kace nace daga masoya jarumin kasancewar wakar JABRA FAN ta samu karbuwa a zukatan jamaa amma babu ita acikin film din... Wannan tasa wata masoyiyar Jarumin AFREEN ZAIDI ta shigar da Producer film din kara na ya yaudareta, acewar ta ta bata lokacin tane don ganin wakar amma akarshe har film ya kare bata gantaba, wanda shi kuma ya saka wakar a tallan film din (Trailer). 

Bugu da Kari Kamar Yanda Kowa Ya Sani Wannan Film Yana Daya Cikin Jerin Fina-Finai da Aka Zo da Sabon Labari Sedai Duk da Haka Anyi Rashin Nasara a kasuwarsa Wanda Zamu Iya Cewa Daya Daga Dalilan Shine Rashin Saka Wannan Waqa Domin da Yawan Yan Kallo Sunso Su Kalli Waqar Nan Acikin Wannan Film Sabanin Yanda Aka Saka a trailer Kawai.

By #AbbaIndiaDala.
Share:

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive