Showing posts with label Fina-Finai (Films). Show all posts
Showing posts with label Fina-Finai (Films). Show all posts

NI MUSULMI NE, MATATA HINDU CE, YARANA KUMA INDIA CEDaga Salim Idris 


"Matata mabiyar addinin Hindu ce, ni musulmi neh, 'ya'yanmu kuma qasarsu INDIA ita ce addininsu" cewar Jarumi Shahrukhan

Jarumin wanda akewa laqabi da KING OF ROMANCE ya jima ba'a ganshi a fim ba tun bayan fitar fim dinsa ZERO wanda AANAND L RAI ya bada umarni. Fim din bai yi abin kirki à kasuwancinsa ba wanda yasa tun daga lokacin Shahrukhan bai fadi fim din da zaiyi nan gaba ba.

An ga jarumin kwanan nan ya fito a wani shiri da akeyi na talabijin mai suna DANCE PLUS 5 yana magana akan addini. Shahrukhan yace basa yin hirarraki akan addini a gida tare da iyalinsa. Ya qara da cewa indai yazo cike gurbin addini a fom din makarantar 'ya'yansa, INDIA yake rubutawa a wajen. 

An sha jin jarumi Shahrukhan à baya yana cewa suna yin bikin kowane addini a gidansa kuma basa banbancewa. 
Daga qarshe jarumin yace "Ni ba mai yin sallah biyar a rana bane amma ni musulmi ne. Na yadda da abubuwan da addinin musulunci yake koyarwa kuma na yadda addini ne mai kyau"
Share:

ZAGIN DA ME BADA UMARNIN SHIRIN FIM ƊIN KABIR SINGH YA KE SHA ZAI ZAMA ƘALUBALE GA DUK WANI MAI SHIRYA FIM


ZAGIN DA ME BADA UMARNIN SHIRIN FILM DIN KABIR SINGH YAKESHA ZAI ZAMA KALU BALE GA DUK WANI ME SHIRYA FILM:

By Abba India Dala.

Wannan Director Me Suna Sandeep Reddy Vanga Yayi Rubutu A Shafin sa Kan Rashin Jindadinsa Akan Wani Fyade da Akayi Har Yake Ganin Ayi Gaggawar Hukunta Wadanda Sukayi Amma Hakan yasa Yabar Baya da kura Domin Kuwa Da Yawan Mutane Suna Cewa Munafinci ne Yasa Shi Haka Dan Suna Ganin ya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Nunawa Jama'a Cewa Ba Wani Abu Bane ga Fyade Kamar Yanda Yayi A Wasu Fina-Finan sa Guda Biyu Watau ARJUN REDDY da KABIR SINGH ga Duk Wanda Ya Kalli Film Wadannan Fina-Finai da Zaka ga Cewa Ma Wasu Munanan Halin na Matasa Irinsu :- Shaye-Shaye, Rashin Ganin Girman na Gaba, Yawan Fushi da Rashin Daukar Shawara da Saurin Lalata Yara Yan Mata. Duk Wadannan ya Nuna Ba Wani Abu Bane Domin Duk ya Nuna su Acikin film dinsa Musamman na kwanan nan watau Kabir Singh Wanda Shiyasa Nima Film din bai min ba ta Fannin Labari.
To Hakan ne Yasa Wannan Director yake ta Shan Suka Akan ya Nuna shima baiji Dadi ba game da Wannan Fyade da ta Faru a Garin Hyderabad.
GA YANDA ABIN YA FARU:

Wannan Labarin Ban Tausayi Da Taba Zuciya ya Faru a Kasar India Kasancewar Mummunar Aika-aika da Akayi Akan Wata Matashiyar Likita Me Kimanin Shekaru 26 Me Suna PRIYANKA REDDY Wadda Wasu Mutum Hudu Sukayiwa Fyade Kuma Suka Konata😭😭 Tabbas Karshen Rashin Imani kenan.
Ance Bayan Dr Priyanka ta Fito Daga Wajen Aiki Wajen Misalin karfe 9:30 Zata dau Irin Dan Karamin Babur din nan da Suke Hawa (Scooter) Domin ta tafi Gida Se Tataras Taya ta Samu Matsala Hakan Yasa ta Fara yunkurin Yanda Zatayi Maganin Matsalar Inda Acikin Mutum Hudu dinnan Shi yazo yasa Abinda Tayar ta Samu Matsala Bayan tazo taga Abin yazo Yace Zai Kai Mata Gyara Sannan ya dawo Yace Duk sun tashi wani yake Sanar mata Bazata Samu kowane Wajen Gyara Yanzu a Bude BA Haka dai, Hakan ne Yasa Sukayi Nasara Akanta Daman Kamar Yanda Yan Sanda Suke Bincike Sun Bayyana Inda Duk mutum Hudu dinnan Sun Fito Daga Garin Narayanpet Kuma Sunayensu:-
Mohammad Areef da
Jollu Naveen da Chennakeshavulu da kuma Jollu Shiva.

To Sedai Muce Allah Ya Kyauta ya Gyara Zukatan mu Daga Yin Aiki Mara Kyau.

By #AbbaIndiaDala
Share:

RANI


        RANI

Sallama a Gareku abokaina
Ina yini ya aiki da rana?
Ya iyaye, yayyi da ƙannena?
Ni dai makafci ne in kun tuna
Na iya sarrafa kalmomi da magana
Ina canja salo kamar riguna
Yau ma nishaɗi nake yi da Murna
Domin a karon farko a ruhina
Zan bayyana zancen da ke raina
A ƙarƙashin so kuma ra'ayina
Ina fatan zaku ji idan kun zauna
In yaso daga baya ma tattauna. 

Na daɗe da shiga bege tsawon ƙarni
Na zamo sahoro a cikin ƙarni
So kawai nake yi ba Damina bare rani
Gashi babu alamun nasara a gare ni
Amma hakan bai sa na yi gurnani
Ba balle ma in yi gunguni 
Farko dai muryarta ce ta jawo ni
Idanuwanta kuma suka ƙamar da ni
Murmushinta shi ne ya sumar da ni
Iya kafcenta kuma ya sace ni
Ban gajiya da kallonta tsawon yini
Idanuwana kan ƙame a kanta kamar gini.

Maganar gaskiya tana da farin jini
Ban damu ba ko da za ta ƙi ni
Ni dai kumatunta suna burge ni
Shigarta a kullum tana ɗasa ni
Na sha mafarkin gashi ta aure ni
Na yarda in aure ta ko zata dinga zane ni
Kamar yadda ta yi wa wasu a mardaani
A wasu lakuta na kan yi ta tunani
Yadda za'a yi in cire son da yayi rauni
A zuciya kuma gashi babu magani
Seriously I gotta say that I love Rani
Kuma ban damu ba ko da zata raina ni.

A sanda naji ance ta yi aure
Haka na sulale a jikin ƙyaure
Fatata tayi kaushi kamar ɓaure
Ji nake kawai tawa ta ƙare
Kamar wata kazar da aka banƙare
Na kasa yin zuciya kamar kare
Na kasa tashi ma balle in ware
Sai na koma gefe na takure
Tunanuka a ƙwaƙwalwa suka kaure
Damuwa ta sa na koma kamar zare
Idan na tuna gashin kanta kamar fure
Sai in ji na gaji da kwanan zaure

A rayuwar kafce irin ta sinima
Tun daga yara har sahun su Mama
Kogin sonta kaɗai na ƙunduma
Wuƙar sonta a zuciyata ta luma
Hakan yasa hasken idanunta nake nema
Na yi haƙuri amma na kasa dauwama
Sai da dai yau na yanke shawara
In fito fili kowa ya sani ƙarara
Cewa na taɓa gangarawa wata gangara
Wacce maimakon ta kai ni Zamfara
Sai dai kawai na tsinci kaina a shara
Gashi kan so yau na shahara.

<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring 
Share:

LUGUDEN LUGWIGWITA AGWALUMA

LUGUDEN LUGWIGWITA AGWALUMA

A kwanaki kaɗan da suka gabata ne dai masu ruwa da tsaki na wani sabon shirin Masana'antar bulbula soyayya gami da sambaɗe-Sambaɗe ta birnin in-da-yaya mai suna Talala-da-biye-biye suka saki hoton farko na wannan shi wanda yake ɗauke da hoton shahararriyar masifaffiyar jarumar nan watau Kan-gwangwani. A hoton farkon dai da aka fitar an nuno jarumar ta canja siffarta gaba ɗaya daga sanda zuwa AGWALUMA. 

Sai dai a maimakon a yaba wa jarumar a matakin farko dangane da irin wannan ƙoƙari nata, sai ga shi mutane daga ko'ina suna ta yi mata luguden laƙumar agwaluma gami da latse-latsen lemo. Babu irin tofin ala-tsinen da bata sha ba. Sai dai wani rahoto da ke yawo ya bayyana cewa mafi yawancin masu suka da caccakar yanayin da jarumar za ta fito a cikin shirin wai masoya Jarumi hantaru ne. Jummai gantali dai da Hantaru kusan shekaru uku kenan suka ɗauka suna bata kashi da cece-kuce. 

Mu dai anan sai dai mu ce Allaah shi sauƙaƙa. 

<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring 


Share:

TARIHIN JARUMI NANDAMURI KALYAN RAM

An Haifi Jarumi Nandamuri Kalyan Ram a ) 5 ga watan July shekara ta 1978), Yaka sance Jarumin India ne Shi Sannan Kuma Mai daukar Nauyin shiri Wanda akafi Sanin Aikinsa a Masana'antar Telugu cinema .Ďane ga Jarumi Sannan kuma Dan Siyasa Nandamuri Harikrishna , Mahaifiyarsa Lakshmi. Sannan Kuma Jikane ga N. T. Rama Rao, Wanda yaksance shima Jarumi Sannan kuma kwararren dan Siyasa . Sai kuma Jarumi Jr. NTR yaka sance Kani ne ga Jarumi NKR . Sannan yanada Kamfani mallakar Kansa Wanda ya bawa Suna bayan Mutuwar Kakansa Mai Gayayi NTR , An bawa Kamfanin Suna . N.T.R. Arts. Jarumin ya kafta roles a wasu fina finai da ya zama Kwari kamar su Athanokkade, Hare Ram, Pataas, Ism da 118. Sannan kuma yanada Kamfani nasa na VFX company wanda aka bawa Suna da "Advitha Creative Studios",Kamfanin da aka samarda fina finai masu himma kamar su Legend, Nannaku Prematho da Krishnashtami.
An haifi Nandamuri Kalyan Ram a 5 July 1978 Shekarun sa 41 an haifeshi a garin Hyderabad, India a yankinTelangana, India)
Mazaunin: sa Hyderabad, Telangana, India .
Kasar sa ta haihuwa: india.
Inkiyar sa : NKR.
Inda yayi karatu :MS at Illinois Institute of Technology, Chicago, US,BE a Coimbatore .
Aikin sa : Jarumin Film , Mai daukar Nauyin Shiri.
Shekarar da ya Fara Film 1989; 2003–
Matar sa :Swati
Ya'yansa : Sourya Ram da Taraka Advitha
Mahai finsa :Baban shi Harikrishna Nandamuri
Mahaifiyar sa :Lakshmi Nandamuri.
Dan uwan sa na jini: Jr. NTR
Yayar shi : Nandamuri Suhasini.
Kakan shi: N. T. Rama Rao .
Kawun sa :Nandamuri Balakrishna .
Wani Kawunsa kuma :N. Chandrababu Naidu .
Antin shi :Daggubati Purandeswari .
Dan uwan sa :Nara Lokesh .
Dan uwan sa kuma :Nara Rohit .
Wani dan uwan nasa :Taraka Ratna .

Share:

SHARHIN FIM ƊIN VIVA


SHARHIN FINA-FINAI (18)

Kamar yadda aka saba a kowacce ranar Asabar muna gabatar da sharhin fina-finan Indiya, a inda a kowane sati muke zaƙulo fim ɗaya muke gabatar da sharhi da kuma irin darasin da yake koyarwa. To a wannan satin ma dai munzo muku da wani ƙayataccen fim mai cike da ɗumbin tausayi, kyau da kuma nishaɗantarwa mai suna "VIVAH" wanda haɗaɗɗen jarumin nan wato Shahid Kapoor da kuma kyakkyawar jarumar nan mai suna Amrita Rao suka jagoranta.
     Kamar kullum da koda yaushe ni AUWAL IBRAHIM KJ (AIMAR) tare da taimakon ɗan uwa abokin aiki HAIMAN RAEES nake gabatarwa.

GABATARWA

Vivah fim ne na soyayya da akayi shi da yaren Hindi wanda ya fita a 2006, Sooraj Barjatya ne ya rubuta ya kuma bayar da umarni. Shahid Kapoor tare da Amrita Rao ne suka jagoranci fim ɗin yayin da Rajshri productions ne suke shirya suka kuma rarrabashi.
     Fim ɗin Vivah na bada labarin wasu mutane biyu, da kuma rayuwarsu tun daga baiko zuwa aurensu da kuma abinda ya biyo baya. Vivah shine fim na 4 wanda Shahid Kapoor da Amrita Rao suka fito tare. An fitar dashi a 10 ga Nuwamba 2006, an sami gagarumar nasara ta fuskar kasuwancinsa duk da cewa ya sami sharhi kala biyu daga wajen masu sharhi 6 domin wasu sun yaba sosai wasu kuma sun kushe tsarin labarin. Koma dai yayane an sami nasara sosai dashi. 

GUNDARIN LABARIN

Poonam matsakaiciyar yarinya ce da take zaune a wani ƙaramin gari dake Madhupur. Bayan rasuwar mahaifanta, a lokacin tana 'yar ƙarama, kawunta Krishnakant ya ɗauki nauyin maye gurbin mahaifinta a cikin rayuwarta. Saidai kuma matar kawun nata bata amsheta ba a matsayin' ya saboda tana kishin cewa tafi ɗiyarta mai suna Rajni kyau duba da ita Rajni ta kasance mai duhun fata da kuma kuma bata kai Poonam kyau ba. A ɗaya ɓangaren kuma, akwai wani sanannen ɗan kasuwa mai suna Harishchandra wanda yake a garin New Delhi, yana da 'ya' ya maza guda 2 : Sunil wanda ya auri mata mai suna Bhavna, sai kuma ɗayan mai suna Prem wanda yake shi mutum ne mai magana mai taushi da kuma ilimi.
     Sauƙin kai da kyakkyawan halin Poonam su suka burge Bhagatji, wanda yake harƙallar kayan ƙawa (jewelry) kuma aboki na kusa ga Krishnakant. Sai Bhagatji ya ɗauki maganar auren Poonam ya gabatar da ita domin Prem. Lokacin da Harishchandra ya faɗi ra'ayinsa gama da batun, da farko sai Prem ya ƙiya a cewa yayi yarinta da yin aure a yanzu saboda yana buƙatar maida hankali kan aikinsa tukuna. Sai Harishchandra yayi ƙoƙari ya shawo kan Prem akan ya fara samun Poonam kafin ya yanke hukuncin komai.
     Saboda girmamawa ga buƙatar mahaifin nasa, sai Prem ya amince da cewa zai je ya sami Poonam domin fahimtarta sosai daga nan sai ya yanke hukunci. Sun ziyarci dangin Krishnakant kuma sun bar Prem da Poonam su fahimci juna. Duk da cewa tattaunawar tasu ta farko mai wahala ce, amma daga baya sun amince da suyi aure saboda suna son junansu. Sai Prem da Poonam suka yi baiko sannan suka shirya yin aure nan da wata 6. Sai Krishnakant ya gayyaci dangin su Prem domin zuwa shaƙatawa a garin Somsarovar, dan haka Prem da Poonam sun sami damar da zasu fahimci juna sosai.
     Prem da Poonam sun kasance cikin tsananin soyayya a lokutan rayuwarsu. Duk da kasancewar sun zo daga mabanbantan tunaninnuka game da rayuwa amma suna son ganin alaƙar tasu tazo daidai ga juna. Kuma sun gano muhimmancin da zoben baiko wanda suka bawa junansu yake dashi da kuma dama ta musamman da suka samu kan juna sanadiyar hakan. Sun fara son junansu da kuma kasancewa a tare. Madallah da ɗawainiya da kuma kwantar da hankalin da 'yan uwansu suka dingi yi a gare su. Bayan wasu kwanaki sai Harishchandra da iyalansa suka koma gida domin halartar taron gaggawa game da kasuwancinsu, wanda ya bar Poonam da Prem zaɓin sadarwa ta hanyar waya da kuma wasiƙa. Sai Prem ya shiya cikin kasawancin ahalin kuma ya ɗauki wani muhimmin aiki a Japan. A yayin dawowa, ahalin sun taho da Poonam domin su bashi mamaki tare da murnar baikon su.
     Kwana biyu kafin ainihin auren, sai gobe ta tashi a gidan Krishnakant. Duk da cewa Poonam ta fice daga gidan akan lokaci, sai ta fahimci cewa Rajni da har yanzu tana cikin gidan sai ta koma cikin domin ceto ta. Poonam ta sami mummunar ƙuna a jikinta sanadiyar a sanadiyar hakan. Da aka kaita asibiti sai likitan yake sanar da mahaifin nata cewa a irin haka ne iyalai kanyi watsi da nasu. A take a wajen ya kira Prem cikin takaici a yayin dashi Prem ɗin ya baro Madhupur domin halartar bikin. A lokacin da yake ƙoƙarin saka hannu akan takardar yarjejeniya domin yi mata aiki, sai kawai ya fashe da kuka domin ba zai iya yin hakan ba. Sai ga Prem yazo da niyar ya auri Poonam duk da irin ciwukan da suke jikinta ya taho da ƙwararren likitoci daga Delhi. A take a wajen ya aure ta kafin ayi mata tiyatar. Tare da taimakon waɗannan likitocin na Delhi, asibitin yayi nasarar yin aikin wa Poonam. Bayan zaman wata 1 da rabi a asibitin, sai ga Rama (matar kawunta) tazo domin ɗaukar Poonam a matsayin 'yarta bayan ta fahimci irin sadaukarwar da Poonam ɗin tayi domin ceto 'yar tata.
     Daga baya, Poonam da Prem sunyi aure kamar yadda al'ada ta tanadar sannan suka wuce gida domin gudanar da sabuwar rayuwa. Fim ɗin ya ƙare ne a inda Poonam da Prem suke murnar daren farkon su a matsayin ma' aurata.

SHARHIN FIM ƊIN

Kamar yadda ragowar fina-finan kamfanin Rajshri productions ƙarƙashin Sooraj R. Barjatya suke nunawa tun daga kan fim ɗin "Maine pyaar kiya, Hum Aapke Hain koun, Hum Sath Sath Hain, Main Prem Ki Diwani Hoon" to shima dai Vivah ba a barshi a baya ba domin yabi sahunsu dangane da irin salon labarin shima yana magana ne akan ahali da irin matsolalin da ake samu daga wani ko wasu.
     A fim ɗin zamu ga cewa a can gidan Krishnakant matsala na faruwa saboda matarsa Rama taƙi yarda da cewa Poonam 'yar tace tana kishi da ita dan tafi 'yarta kyau da kuma haske gashi kuma ta sami miji mai inganci zata aura. A inda taci gaba da nuna adawarta ga Poonam har sai lokacin da tsautsayi ya abku na gobara ta ceto yarinyarta ita kuma ta sami ƙuna, sannan ta gane kurenta. To ina amfanin irin wannan da mutum baze gane muhimmancinka ba sai lokacin daka cutu a dalilin tseratar da nasa.
     Ta ɗaya ɓangaren kuma munga yadda Prem ya nunawa Poonam so na gaskiya bayan sun fahimci juna ya tsaya mata a lokacin da take tsananin buƙatar hakan, bai guje mata ba dan ganin cewa ta nakasa sai ma taimakawa da yayi wajen ganin anyi mata aiki mai kyau.
      Daga ƙarshe ina mai fata da addu'ar Allah ya haɗa mu da masoyan gaskiya waɗanda zasu zauna damu a kowane hali, ba wai sai muna dashi ko yanayi mai kyau shine suke tare da mu da zarar an sami akasin haka sai su juya mana baya. AMEEN YA ALLAH

TAURARIN SHIRIN

Shahid Kapoor - Prem
Amrita Rao - poonam
Anupam Kher - Harishchandra
Alok Nath - Krishnakant
Seema Biswas - Rama
Samir Soni - Sunil
Lata Sabharwal - Bhavna
Manoj Joshi - Bhagatji
Amrita Prakash - Rajni

By : AUWAL IBRAHIM KJ (AIMAR)
Share:

TARIHIN JARUMA JHANVI KAPOOR


_*Tarihin jarumai*_ 


*Takaitaccen tarihin jaruma jhanvi kapoor* 

               _Tare dani_ 

 _*ibrahim so dole Sasha bhai Singh*_ 

An haifi jaruma jhanvi kapoor a 7 march 1997 a Maharashtra dake Mumbai ta kasar india.

Sunan mahaifinta boney kapoor kapoor Wanda ya kasance mai daukar nauyin fina-finai( producer ) ne na masana'antar film ta kasar india wato Bollywood . Sunan mahaifiyarta srivedi wadda itama ta kasance jaruma a masana'antar ta Bollywood .

Kuma ta kasance daliba a makarantar Dharubhai Ambani international school ta garin Mumbai na kasar india. Bayan ta gama ta tafi Lee strasberg Theatre and film Institu Los Angeles, USA domin koyar kafce. Physical Appearance. Jaruma ta fara fitowa a cikin film mai taken Dhadak da akayi shi a shekarar 2018 wacce itace ta fito a matsayin jaruma a cikin film din. Kuma film din anyishine kan soyayya kuma tafito ne tare da mashin jarumin nan kuma kani ga jarumi ( shahid kapoor ) wato ishat kattar, film din anyishine a yaren Hindu kuma mai-maici ne na wani film da akayi shi a shekarar 2016 Marathi film sairat . kuma film din ya kasuwancinsa na worldwide ya karbi kudi kimanin dalar amura 1.1 billion.

A fannin bayanan halitta kamar yadda masana suka bayyana jarumar ta kasance tana da nauyin 50 kg . kuma idonta ya kasance ruwan kasa mai dubu wato ( dark Brown ) kamar yadda masana suka bayyana . kuma kalar gashin yakasance baki ( black ) jarumar yakasance tana yawan ziyartar wajan motsa jiki na gym .

 *A bangaren dangan taka da wanana jarumar take dashi da mutane daban-daban kamar haka :-*

Jaruma jhanvi kapoor ta fito daga Ahalin Hindu Punjabi khatri da suke a Maharashtra Mumbai na kasar india. Jarumar tana da yar'uwa maisuna khushi kapoor . kuma ta yan'uwa kamar haka :- 
Arjun kapoor half-brother da Anshula kapoor half-siblings.
   Jaruma jhanvi kapoor tana da saurayi mai suna Shikhar pahariya da kuma Akshat Rajan sannan sai jarumi ishan kattar Wanda sukafito a cikin film din ta na farko wato Dhadak.

 *Acikin abubuwan da jarumar takeso da wadanda bataso sune kamar haka:-* 

 _A bangaren abinci_.. 
 _Jarumar tanason cin Muttom da abincin Rajastani cuisines , da kuma Italian dishes.


 _A bangaren jaruman da take so, duk da jarumar ta kasance matashiya dole zakuga tanason jarumar da dama a masana'antar ta Bollywood sune kamar haka_ :-_

 _Ga jerin jaruman da jarumar takeso kuma takes on kallon fina-finasu_ :- 

Dilip kumar , salman khan, shahid kapoor, madhubala, waheeda Rahman, nutun, and kareena kapoor khan.

 *A bangaren fina-finan da jarumar take so sune kamar haka* :-

Dilwale dulhaniye le jayenge, Hum dil de chuke sanam . wadanann sune films din da jarumar takeso.

Jarumar fashion designer din da takeso shine manish malhotra. Facts 

Film dinta na farko shine Dhadak da tayishi a 2018 kuma sun fito a tare da ishan kattar Wanda kanine ga jarumi _shahid kapoor_ .

 *Jerin fina-finan jarumar da zasu fita anan gaba.*

 _Gunjan sexena dazai fita a shekarar 2020._

 _Roohi Afza dazai fita a shekarar 2020_ 

 _Ghost stories dazai fita a shekarar 2020._

 _Dostana 2 dazai fita a shekara 2020_

 _*Wadanan sune jerin fina-finan jarumar dazasu fita .*_


 *A bangaren shafukanta na sada zumunta* .

Jhanvi Kapoor (@janhvikapoorr) | Twitter
https://twitter.com › janhvikapoorrJanhvi Kapoor (@janhvikapoor) • Instagram photos and videos
https://www.instagram.com › janhvikapoor


Janhvi Kapoor - Home | Facebook
https://m.facebook.com › ... › Actor
Janhvi Kapoor. 241K likes. Janhvi Kapoor is the daughter of Sridevi, an ageless diva of Indian Cinema. She is the elder daughteSfans_

*Takaitaccen tarihin jarumai ....*_ 


 *Duka-duka anan ne na takaita wannan kafce na tarihin jarumai ...•.......* 

 _*Jinjina ga duk kanin mutanen da suke karfafa mana gwiwa da groups-groups*_ 


 ****🇳🇬 *Sasha bhai singh* 🇮🇳*** 

 *🇳🇬🇳🇬MJL fina-finan india 🇮🇳 🇮🇳* 

 *🇳🇬 muleka india 🇮🇳* 

 *🇮🇳 Indian wale fans of 9ja 🇳🇬* 

 *🇮🇳Bollywood fans 🇮* 🇳

 *🇮🇳🇳🇬Taskar Bollywood Aminchi radio 103.9 fm📻* 

 *🎧Atif aslam of fans 👨‍🎤* 

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••>>
 *Www.Sasha bhai singh.com/facebook* 

 *Www.Sasha bhai Singh.com/Instagram* 

 *Whatsapp.09072875288* 

 *Call :- 07030308254* 

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<
Share:

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...