Showing posts with label Girke-Girke (Cookings). Show all posts
Showing posts with label Girke-Girke (Cookings). Show all posts

BURABUSKO


*BURABUSKO*


KAYAN DA ZA KI TANADA

1. Gero 
2. Mai 
3. Gishiri

YADDA ZA KI HADA
Ki sami gero ki wanke shi ki rage domin tsakuwar ta fita, sai ki shanya ya bushe. Idan ya bushe sai ki kai a barzo miki a inji. Ki dora ruwa a kan wuta kamar rabin tukunya, sai ki kawo madambaci ki dora akan tukunyar, ki shimfida buhun algarara ko kuma jarida akan madambacin. Sai ki kawo barzazzan geronki da kika bakace kika fitar da dusar ki zuba a cikin madambacin, ki yayyafa ruwa akai. Idan kina so ma kina iya jika kanwa ‘yar kadan ki yayyafa ruwa akan geron saboda ya yi laushi sosai. Sai ki bar shi ya turaru. Idan ya dauko turaruwa zaki ga ya fara curewa, sai ki sauke daga kan wuta ki zuba mai da gishiri ko magi ki mitststsika domin ya warware. Sai ki rage ruwan daya ke cikin tukunyar ki bar shi dai-dai yadda zai yi miki. Sai ki dauko turarren geronki ki zuba a cikin ruwan, sai ki dan juya kamar kina rude, amma wannan da kauri. Sai ki kawo leda ki rufe, sannan ki kawo murfin tukunyarki ki dora akai. Idan ya yi zaki ji gidanki ya turare da kamshi, kuma idan kin taba zaki ji yayi laushi.

Umman amir and minaal👩🏻‍🍳👩🏻‍🍳👩🏻‍🍳
Share:

HANYOYIN RAGE ƘARNI A KITCHEN


*Mieererh's Kitchen* 🥙🥗🥬🌮🍲🍝
 
HANYOYI 1⃣0⃣ MASU SAUKI DA ZASU RAGE MIKI.KARNI A KITCHEN

1⃣Yana da kyau ace mace ta ware roba kara dazata dinga fasa kwai sannan ki ware cokali ma yadda duk sanda zaki abinda ya shafi kwai da ita zaki using
2⃣Ki ware roba babba ta wanke nama ko kifi duk sanda zaki amfani dasu da ita zaki
3⃣Ki ware tukunyar tafasa nama ko kifi ko ganda da kayan ciki ya zamana ta abinci da ta miya daban
4⃣Kisai tukunya ki barta ta dafa shayi karki dafa komai sai shayin saboda gujewa karni
Idan anci kifi ko abin karni 
5⃣Ki daina sa soso direct kina wanke kwanon zaki zuba omo a kwanon sai kisa hannu a hankali ki fara wankewa
6⃣Ki dinga zubawa ruwan zafi omo kina zuba cokulanki na abinci dukka su jiko hakan yana kashe karni ki dinga yawan yin hakan koda ba abincin zaku ci ba
7⃣Duk sanda zaku sha tea ki matsa lemon tsami da ruwan dumi kisa a cup din ki barshi zuwa wasu mintina kanki gama aiki zakiji cup din in an zuba tea din yana kamshi
8⃣Karki dinga sawa miyar ki kanwa dinga sa baking powder tana gyarata tsaf ta rage tsaminta
9⃣Idan kinyi amfani da abin karni a hannunki ki dinga goga tuka ta kasan murhu
1⃣0⃣ Danyar citta da tafarnuwa maganine sannan suna gyara abinci 

*AMIEERERH* 09039004777
Share:

KOYI YADDA AKE HAƊA FANKE


Fanke

Abubuwan hadawa

Fulawa
Sugar
Yeast
Mai
 Yanda ake hadawa

Da farko uwargida za ki tankade fulawarki a roba mai kyau mai murfi.
Sai ki zuba yeast da sugar da ruwa ki kwaba ya kwabu sosai(ya yi ruwa-ruwa in da zai rika kamun hanu) sai ki rufe a wuri mai dumi.
Ya sami kamar awa 1 ko 2 , idan ya yi sai ki dora kaskonki a wuta kisa mai ya yi zafi.
Anan sai ki rinka deban kullin da ludayi kina sawa a cikin mai kina soyawa ya yi jan suya. Ana iya ci da shayi ko wani lemo
Sai mun hadu a girki na gaba. Na gode
Share:

YADDA AKE HAƊA ƘOSAN DOYA


KOSAN DOYA

KAYAN HADI

Doya
Kwai
Nama
Fulawa 
Albasa 
Attarugu
Gishiri 
Maggi

YADDA ZA'A HADA

Ki fere doya ki dafa ta sai ki daka sama sama ko kuma ki murmushe sannan ki samu albasa da attarugu ki jajjaga ki hada da doyarki da kika daka ki sa maggi da gishiri, ki tafasa nama ki jajjaga a turmi ki kwashe ki zuba a ciki ki juya sosai sai ki dinga mulmulawa kina tsomawa a ruwan kwai sai ki jefa a fulawa ki saka a cikin man gyada mai zafi ki soya shi, idan yayi brown sai ki kwashe daga cikin man gyadan,,wannan girke kam ba za'a bawa yaro mai 'kiwiya ba

Share:

YADDA AKE HAƊA SAMOSA


Yadda ake Samosa

Abubuwan hadawa

Fulawa (flour)
Kwai
Nama
Maggi
Onga
Kori (Curry)
Gishiri
Man gyada
Attarugu
Albasa
Karas (carrot)
Baking powder
Yadda ake hadawa

Da farko zaki wanke namanki ki tafasa shi da albasa da maggi da gishiri da dan korinki. Ki yi shi tamkar danbun nama.
Sai ki goga karas din ki, ki kuma soya shi
Sai ki zuba fulawarki a roba ki saka baking powder da dan gishiri ki kwaba. Ki murza ta murzu sosai ta yi fadi.
Sai ki rika yankawa kina zuba namanki da karas kina nadewa kamar dan kwali
Sai ki dora mangyadarki a wuta ya yi zafi
Idan yayi zafi sai ki dinga jefa nadadden samosanki kina kisoyashi
Share:

ƘOSAN DANKALI DA NAMA


Kosan Dankali + nama

KAYAN HADI

Dankali
Nama
Kwai
Attaruhu
Albasa
Maggi
Gishiri
Man gyaďa
Fulawa ko garin busashen buredi

YADDA AKE HADA WA

Da farko ki wanke nama ki zuba a tukunya sai ki zuba maggi da gishiri ki tafasa sai ki kwashe ki zuba a turmi ki jajjaga tare da albasa da attaruhu idan yayi laushi sai ki kwashe a kwano ko roba,sannan ki dawo kan dankalin turawa ki tafasa yayi laushi sai ki murmushe shi ko kuma ki jajjaga a turmi sai ki kwashe shi a cikin kwanon da kika kwashe naman da kika jajjaga sai ki ďauko kwai ďanye ki fasa a kai, ki zuba fulawa ko garin busashen buredi a ciki ki sa gishiri da maggi ki juya sosai, ki ďauki farantin suya ki zuba man gyada ki ďora a kan wuta ki dinga ďiba kina zuba wa a cikin man gyada mai zafi idan ya soyu zaki ga yayi brown sai ki kwashe kiyi wa Oga yayi breakfast dashi.

KOSAN DANKALI

KAYAN BUKATA

Dankalin turawa 
Nama
Fulawa
Kwai 
Albasa 
Attarugu
Gishiri 
Maggi
Man gyada

YADDA AKE YI

Ki jajjaga albasa da attaruhu ki kwashe a kwano ko roba sai ki ďauki dankali ki tafasa ki zuba a turmi ki daka shi amma kar ya yi laushi sai ki kwashe a cikin kwanon da kika zuba jajjagen attaruhu da albasa ki tafasa nama shi ma ki daka a turmi duk ki hada da sauran kayan hadin ki juya, sai ki dinga mulmulawa kina tsomawa a ruwan kwai ki juya shi a cikin fulawa ki jefa a cikin man gyada mai zafi ki soya , akwai daďi matuka...
Share:

MU LEƘA KITCHEN

LEMON DANYAR SHINKAFA DA DANKALI. 
Danyar shinkafa 
Dankali 
Dabino
Madara 
Sugar
Citta
Kaninfari 
Falavor
Yadda za ki haďa shi shi ne, idan kika sami Danyar shinkafa, wato ta tuwa .sai ki jika ta tare da dabinonki wanda kika rigaya kika bare, sannan daman Dankalinki ma kin rigaya kin bare shi, sannan kin yayanka yadda zai yi mi ki saukin markađe. To shi ma sai ki hada shi a cikin Danyar shinkafarki tare da dabinonki da Dankalinki, Bayan kin hada su guri guda dukkaninsu sannan kin sanya cittarki tare da Kaninfarinki, sai ki hada ki markađa.Bayan kin markađa.Bayan kin markađa kayanki, sannan sai ki tace, sannan sai ki kawo suganki ki zuba daidai yadda kike bukatarsa .sannan sai ki kawo Falavor ki zuba .Bayan kin gama hada lemonki kin ji komai ya yi miki daidai, sannan sai ki sanya shi a cikin gidan sanyi don karawa lemonki armashi ga mai🏠. FURA ME AYABA🍺🍺

INGREDIENTS:
1.Fura 3 idan manya ne kuma 2
2.Yoghurt
3.Peak milk 1
4.Banana 1

PROCEDURE:
Ki samu fura mai kyau, ki zuba a blender, ki zuba yoghurt,  da peak milk, sai ki yayyanka Ayaba guda daya ko rabi. Daga nan sai ki nike su, kada ki sa ruwa, zaki ga yayi kitibir, kuma dadi ba a bawa yaro mai kiwiya, Idan kina so zaki iya sa dan ruwa, ko ki kara peak daya na ruwa yanda zai saki, amma kada ki sa ruwa in so samu ne. Kuma zaki iya dan sa sugar idan kina so  but gardi da dadin shi ba sai an sa sugar ba, Sai ki sa Fridge before maigida ya dawo.

Sannan in so samune ki gasa masa kaza mai dadi, ko kiyi masa suya, ko stick meat. Zaki ga yanda zai sa shi Nishadi, gashi da kosarwa, saboda dadi zai dauka ba Fura ba ma yake sha.FRIED RICE WITH POTATOES 

INGREDIENTS 
Rice 
Potatoes
Egg
Carrot 
Green pepper 
Maggi
Onga (stew or any coloured spice)
Oil
METHOD 
1- Parboil the rice (so that yayi wara-wara, idan d starch sosai you can wash with tap water, sai ki tsiyaye, then u keep aside) 
2- Cut the potatoes ( zaki iya yanka shi duk yand kike so), then u fry it ya soyu sosai). 
3- Sai ki kwashe chips din, ki tsiyaye man. Sai ki rage mai kadan a cikin pot din, ki juye chips din a man si ki fasa eggs a ciki, kiyi ta stirring dinshi, idan suka soyu tare sai ki kwahe a container
4- Ki mai pot din a wuta ki kara sa mai kadan, sai ki juye su onion, green pepper(yankakke) & grated
Carrot stir them well. Idan suka dahu, sai kisa maggi, ki juye rice din aci kiyi stirring dinsu tare. 
5- Saiki juye chips & egg dinki a ciki, kiyi stirring dinsu. Then kisa onga stew kadan don ya bada colour, shima kidan yi stirring. Sai ki rufe, ki lowering wuta. After like 5-10 minutes sai ki kashe. SNACKS🍪🍩🍞🍘🎂🍰 
CONTENT:
Cake
Chocolate buns
Corn flakes cookies
Coconut biscuit 
Coconut wafers 
Egg custard
Coconut kisses 
Chocolate pudge 
DoughnutsCAke🍩🍰
Kayan hadi:
Kwai 6
Bota gwangwani 1
Sikari kofi 1
Filawa kofi 2
Madara kofi 2 
Madara kofi 1/2
Hoda rabin cokali
Gishiri 1/6 cokali
Digin flavour 
YADDA AKEYI:
A fasa kwai, butter da sikari har se sun narke, sai a zuba garin madara, hoda, filawa, ayi ta motsawa har se ta damu sosai, kada a zuba ruwa.
A shafa butter a gwangwanin cake, a zuba hadin a cikin gwangwanin a gasa a obin.CHOCOLATE BUNS:
Kayan hadi:
Filawa kofi 1
Sikari 1/4 kofi 
Butter cokali 2
Madara cokali 4
Garin cocoa cokali 2
Hoda 1/2 cokali 
Vanilla 1/4 cokali 
Kwai 2
Yadda ake yi: 
A hada hoda, filawa da hodar cocoa a cakuda. A hada sikari, butter da kwai a buga har sai sunyi lakwab-lakwab. Sai a zuba madara ta ruwa da filebon vanilla essence tare da dan gishiri kadan, a motsa sosai sannan a zuba hadin su filawa dasu cocoa. A kwaba sosai sai ya zama kamar kwallo. Sai a yanka shi yadda ake so a gasa. COOKIES:
Kayan hadi : 
Filawa kofi 2
Bota gwangwani 1
Sikari 1/2 kofi 
Vanilla powder cokali 2
Jam 1/2 kwalba 
Yadda ake yi :
A kada butter da sikari har se yayi lukub-lukub sai a rika zuba filawa da flavour ana juyawa har sai filawar ta zama kamar kwallo. A yanka a murza su kanana suyi rawon, ayi kananan hudoji da yar yatsa a rabi, a saka su duka akan farantin gashi a gasa. Idan sun gasu sai a dora mai hudojin akan marasa hudojin, a kuma zuba jam a cikin duka hudojin. CARROT JUICE
Carrot, milk, sugar. Ki sami carrot mai kyau wanda ake ci ba wanda ake sawa a salad ko girki ba, ki wanke, ki niqa ki tace, zaki iya kankare carrot din idan kinga yana yana da datti. Sai ki sami madara peak ki juye a ciki, ki sa sugar, ki sa a fridge yayi sanyi. Yana da dadi sosai, musamman idan yaji madara.


ZOBO DRINK
🍷🍷
Zobo, bawon abarba, pineapple flavor, sugar, busashshen inibi (grape) Ki samu zobo ki zuba a tukunya, ki dauraye abarban da kyau, sai ki cire bawon ki zuba acikin zabon, ki sa ruwa ki barsu su dahu sosai. Yana fara tausa zaki ji kamshi, idan ya tausa sosai sai ki sauke ki barshi ya huce, sai kit ace su amma kada yayi tsululu, sai ki sa flavor da sugar, kisa a fridge yayi sanyi.


MIXED FRUITS DRINK
🍇🍍🍐
Pineapple, orange, flavor, sugar (optional). Wash and peel fruits. Cut into pieces and put In a juice extractor /blender to get the juice mixture, add moderate amount of water, stir very well and flavor/suger chilland serve. 


KUNUN AYA
Aya, lemon, ginger, flavour, sugar, kanumfari, dabino, milk(optional) Add water to aya, ki barshi ya kwana (overnight) in d morning wash aya n add ginger, dabino n kanumfari (cloves) blend add water n sieve add suger, lemon n flavor (coconut or milk) serve chilled.


MILK N BANANA DRINK🍌🍨
Milk (evaporated), banana, orange, sugar. Mix orange juice n milk cut banana into small pieces n add to milk add suger n serve.


FRUIT SQUASH
Pineapple, pawpaw, orange, watermelon, lemon, grape, sugar, flavor Wash n peel each fruit, cut into pieces n blend till smooth add water n sieve add sugar n flavor serve chilled.


MUSHAKKAR
🍉🍓🍈
Pawpaw, pineapple, watermelon, banana, orange, lemon, sugar. Blend pawpaw, watermelon, pineapple, and orange to a smooth paste after washn and removen the seeds, cut banana into small pieces and add sugar and lemon to taste.


GINGER JUICE
🍹🍹
Ginger, dabino, pinapple, caprison, flavor, sugar. Blend ginger, dabino, pineapple add water and sieve, add caprison, flavor and sugar. Maimakon sugar u can add pineapple fosterclark.


SOY MILK
Soya beans, sugar, flavor. Zaki jika waken ki ya kwana a cikin ruwa sannan sai ki rege ki cire tsakuwar, sai ki kai a markada miki idan an dawo dashi sai kit ace ruwan ki cire dusar ki dora kan wuta yayi ta dahuwa, idan ya dahu sai ki sauke ki barshi yasha iska sai kisa sugar da flavor kisa a fridge yayi sanyi.


CARROT AND MANGO SMOOTHIE
1 mango chopped, 1 cup fresh carrot juice, ½ cup ice cubes Puree ingredients in a blender until smooth.


PINEAPPLE JUICE
🍍🍍
Pineapple, orange, sugar or honey, ice cubes. 

Share:

MIYAR HANTA


MIYAR HANTA

Ingredients

Attaruhu
Albasa
Tafarnuwa
Danyar citta
Curry
Mai
Maggi
ki wanke hantar ki yankata kanana ki sa a tukunya ki dafa da
albasa da citta da magi,ki jajjaga attaruhu da albasa da danyar
citta da tafarnuwa da mai ki zuba akai idan hantar ta dahu,kiyi
ta juyawa kisa magi da curry da gishiri,in tayi ki sauke,idan tayi
miki kauri zaki iya kara ruwa kan ki sauke.

Ameenah Nasidi's Kitchen🍖🍗🍲
Share:

YADDA AKE JUICE ƊIN GYAƊA


*MATAN AREWA*

🖍🌿🖍🌿🖍🌿🖍*SATURDAY TEAM*


🌿🖍🌿🖍🌿🖍🌿


*ONLY JUICE*


*JUICE DIN GYADA*
🌿🖍🌿🖍🌿🖍🌿

*KAYAN HADI*
🌿🖍🌿🖍🌿🖍🌿


*Gyada*

*Citta*

*kanunfari*

*Girfa*

*cinnamon*

*Sugar/zuma*

*Flavour*

*METHOD*

Da farko uwar gida zata samu gyadar ta ta bare, in a bare take ta tsince datti, da ko tsakuwa in akwai, an fi son yi da irin gyaradr nan mai jan baya sosai, cikkn fari,kk danyar gyada yafi gardi, sai ta samu ruwa mai dan dumi,ba mai zafi sosai ba ki kwara kai,sai in ya taso, bawon ya kumburo a cikin ruwan ki sa hannnu biyu ki ta murzawa,sai ya fita sai ki mai irin wankin wake,ki cirw bawon, ki bi ki tsince jan, yanda zai haske , sai ki wanke ginger din ki, ki kankare, ki qara wanke wa, sai ki farfasa cinnamon dan kadan ki daka,ki ki debo kanunfari dan daidai, da girfa bayan itama kin dan daka,ki zuba akan wannan gyadar a markado maki,in so samu kiyi a blander a gida, kar a sa maki akan wani abu, ko yai qarnin inji, in kin markada ki sa rariya mai tsafta ki tace,sosai, sai ki zo zakiji yana tashn qamshi a haka ma,ki zuba sugar, ko zuma,ki sa flavour, woww😋😋😋ba'a bawa yaro mai qiwa, ayyukan da yake wa jiki na gyara yana da yawa. TESTED AND TRUSTED😍 a juye a ba mai gida, in ya danyi sanyi,ko a sha a haka.


  *HAERMEEBRAERH*
🌿🖍🌿🖍🌿🖍🌿
     🌿🖍🌿🖍
         🌿🖍
           🌿
Share:

SPICED CHICKEN PEPPER SOUP

SPICED CHICKEN PEPPER SOUP
Ingredients
Zabuwa
Kaza
Water
Pepper soup seasoning
Mint(chopped)
Garlic(crushed)
Chillies(chopped)
Crayfish(ground)
Onion(chopped)

Yadda Za'a hada
Wash d meat(zabuwa da maza) and put it in a pot with a little water, season with salt, chopped onion, chillies and crushed garlic and boil for 20 minutes. Add d pepper soup seasoning and continue to cook for another 20 minutes to till chicken becomes tender, add d crayfish and mint leaves, stir and simmer for 8 minutes add season to ur taste and bring it down. Aci Dadi lafia make u no forget Meenah...😋😜

Ameenah Nasidi's kitchen🍖🍗🍲


Share:

MATA RAHAMA

*MATARAHAMA*
               &
*NISAULKHAIR*
              *GROUP*
*WEDNESDAY* *DUTY* *TEAM*


🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚

*YADDA* *AKEYIN* *AWAWRA*
*KAYAN* *HADI*
*WAKEN* *SOYA*
*RUWAN* *TSAMI*
*KO* *ALIF*
*RUWA*
Dafarko xaki samu wakenki kitsince datti kiwanke saiki jiqa idan yajiqu sai awanke niqa asa ruwa dai dai atace sai ajuye atukunya adora kan wuta rufe idan yafara tafasa xa acire murfin tukunyar domin kada yaxube kuma xa a tsaya akusa ana diban ruwan tsami ahannu ana yayyafawa ko alif duk wanda kika samu haka xaki cigaba dayi har yayi domin kinasa ruwan tsamin xaki ga yafara saki yana duddunqulewa ahaka har yahade jikinshi yabar ruwa bakomi dama can dakika qare tata kin wanke saiki dauko kyallen tattarki kisamu roba mai fadi ki axashi akai kina debo awararki kina xubawa daga nan saiki daure kirataye ko kisagale awani guri har ta tsane saiki yanka yadda kikeso kisa mai awuta ki soya daga nan kisa yaji ko ki jajjaga tarugu tattasai da albasa kisoyasu kisa gishiri mai dan dano amma xakiyita da yan ruwa ruwa yadda xatashiga cikin awarar saici


🌶🌶🌶🌶🌶🌶🌶🌶🌶🌶🌶🌶🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲


*YADDA* *AKE* *ADARAR* *WANKEN* *SUYA*
*KAYAN* *HADI*
*WAKEN* *SUYA*
*SUGAR*
Dafarko xaki gyarashi aniqa atace kamar yadda kikayi na awara sai dai wan nan xaki taceshi da kauri shima kidora kan wuta kibarshi yatafasa har yacire gafin wake saiki sauke yahuce kitace kisa sugar asha ko asa ana urar sanyi idan antashi sha asha kingama madararki

🍶🍶🍶🍶🍶🍶🍶🍶🍶🍶🍶🍶🥛🥛🥛🥛🥛🥛🥛🥛🥛🥛🥛🥛

Share:

ƘOSAN ƘWAI


*KOSAN KWAI*

HANTA 
TARUGU
KAYAN DANDANO DAN KAMSHI 
KWAI
ALBASA
GARIN ALKAMA 
MAI

Zaki dafa hanta bayan kin yanka ta kanana tare da kayan dandano Dana kamshi

Snn ki fasa kwai ki kada sosai kisa albasa da tarugu tare da kayan dandano dana kamshi ki Kuma kadawa

Saiki zuba garun alkama da hanta ki Kuma kadawa kaurin yayi kamar kullin kosai 

Ba a so yay gudaji aciki 

Snn ki dora mai a wuta in yay zafi ki rage wuta ki fara soyawa kamar yadda ake suyar kosai 

*UMMU JAAPAR MY KICHEN MY PRIDE*
Share:

KUNU DA GARIN ALKAMA

KUNU DA GARIN ALKAMA

INGREDIENTS
*Alkama
*Madara
*Siga
*Ruwa


YADDA AKE HADAWA
     Bayan an barza alkamar, sai a debo garin daidai yadda ake bukata, sai a zuba a cikin ruwan zafi, za a bar shi a kan wuta ya dahu yadda ake bukata kafin a sauke. Bayan an sauke shi sai a zuba madara a sanya siga a ciki.
    Za a iya shan a haka bayan an zuba masa madara da siga. Za a iya ba yara da jarirai a matsayin abin da zai kara musu kuzari da lafiya.

Ameenah Nasidi's Kitchen🍖🍗🍲

Share:

KUNUN GYAƊA MAI AYABA

*KUNUN GYADA MAI AYABA*
Ingredient:
Gyada
Ayaba
Gero
Sugar
madara

Yanda akeyi:
Zaki gyara gyadarki kisoyata sama sama kiwanketa kisamu manyan ayabarki ki maikyau ki markadesu kidora akan wuta kibarta dahu idantafara fitarda kumfa kidauko garin nikakkiyar gyadarki 2tbspn kixuba acikin kunun gyadar ki kawo kullun kamu na gero kamar 3spn kidamashi da ruwa kizuba akai zakiga yagame jikinshi yadanyi kauri kisauke idan yakisha kizuba sugar da madara .
Asha lapia .
😋😋😋😘

KUNUN GYADA

Step2 :

Gyada 
Farar shinkafa
Madara
SugarZaki gyara gyadarki kiwanketa kimarkadeta kullu kitace idan kin tace kedurata akan wuta idan tadahu kiwanke farar shinkafarki 1/2spn kizuba kibar shinkafar tadahu saiki sauke kizuba madara da sugar kisha.


*KUNUN GYADA 🍶*

Step3:

Gyada 
Kwakwa
Farar shikafa
Coconut flavour
Madara
Sugar

*yanda akeyi*:

*Zaki dibe bayan kwakwar ki kigurjeta idan gyara gadarki kinniketa kidorata akan wuta yatafasa sau biyu kidauko shinkafarki kizuba idan tadahu kidauko gogaggiyar kwakwarki da coconut flavour dinki kixuba akai kibarshi yayi 2 minute akan wuta kisauke kixuba sugar da madarar ruwa peak milk kisha kokibama mai gida yanada dadi sosai yar'uwa kigwada kigani karki bari baki labari😀😋😋.*

Share:

KUNUN ZAƘI

Kunun zaki
Ingredients
Gero
Chitta (ginger) fresh or dry 
Kananfari 
Dankali (sweet potato)
  Ki jika geronki in ya jiku ki wanke shi tas sanan ki rege sabo da kasa, kidaka dankalin da citta da kananfari ki zuba aciki ki kai markade already ruwanki NA a wuta in an markada se ki kwaba kulun kaman za ki yi koko, sanan ki raba kulun ki biyu daya yafi dayan yawa kadan,se ki dama wanda Ba yawan kaman koko in ya huce sanan ki zuba sauran kulun ki juya ki barshi ya huce sosai then ki tace da zannin tata kisa sugar da ice ko kuma a sa a fridge ya yi san yi a sha.

Share:

ƘAYATATTUN GIRKE-GIRKE


*KAYATATTUN GIRKE GIRKE GROUP*🥐🥐🥐🥐

*STROMBOLY*🥐🥐🥐🥐

*KAYAN HADI*

Kwai
Butter
Sugar
Yeast
Gishiri
Fulawa
Man gyada 
Baking powder
Madara mai dumi

*YADDA ZA KIYI*

Yar uwa da farko ki zuba fulawa, sugar, gishiri, yeast da baking powder a waje guda sai ki juya su da kyau, sannan ki sa butter da kwai ki juya dan ya hade jiki, ki dauko madara mai dumi ki juye a ciki ki kawo ruwa mai dumi kina zubawa kina juyawa, idan kwabin ya fara dan'ko sai ki dai na zuba ruwa ki cigaba da bugun sa kina juyawa, idan kika ga yayi tauri sai ki kara ruwa ki cigaba da kwabawa, sai kisa murfi ki rufe ki bari ya taso sannan ki yanka ki murza da kwalba dan yayi fadi (kamar shape din rectangle mai kusurwa hudu) sai ki zuba jajjagen kayan miya da dakakken nama ko kaza a ciki, sannan ki nannade shi kamar taburma, sai ki kama bakin biyu ki hade su (yayi kamar shape din doughnut)kisa hannu ki mammanna yadda zai kama sosai sai ki dauko wuka ko kitchen scissors ki tsatstsaga saman ki dauko kwai ki shafa mishi sama sama sai ki kunna oven idan ya fara zafi sai ki saka a farantin gashi ki gasa.... 😋😋😋

*KAYATATTUN GIRKE GIRKE GROUP*🥐🥐🥐🥐

Maman Usman 
+2348032629076

Ban hana a tura wa yar uwa ko kuma group ba amma duk wacce ta canza min post ban yafe ba
Share:

MANGO JUICE

MATAN AREWA
SATURDAY TEAM
    🍸🍸🍸🍸
ONLY JUICE😎
     🍸🍸🍸
By littlefisart✍

🍸🍸🍸🍸🍸🍸
        MANGO JUICE
🍸🍸
Mangwaro🍸
Cucumber🍸
Lemon tsami🍸
Suga🍸
Flavor🍸
🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸
        Its testing😋
🍸🍸🍸🍸🍸
Ki bare mangonki ki yayyankasu yan dai dai,sann kisamo cucumberki shima kiyyyankashi, kidasu guri guda ki markadesu,kada kitace,sannan seki matse ruwan lemon tsaminki akai,dan kadan seki zuba flavor da suga 😋
🍸🍸🍸🍸😋
Saturday team 
Matan arewa
Only juice😋
🍸🍸🍸🍸🍸
     By little fisart✍💋

Share:

DABARUN SARRAFA NAMA 05

🌹Dake Ake🌹
*DARAJARKI ABINCINKI*

*DABARUN SARRAFA NAMA-5*

*TSIRE*
kayan hadi
Nama
kuli kuli
barkono
Kayan kanshi
maggi
gishiri
man kuli

da farko uwargida zaki sami namanki amma banda kashi
ki gyarashi
uwar gida in kina bukata zaki iya samun harda mai kitse 
saki yanyanka yadda kike bukata
saiki samu kuli kulinki 
ki hadashi da kayan hadinki 
bayan nan saki samu tsinkenki ki tsaftace shi
daga nan saiki tsirashi a tsinken bayan kin gama kidansa laima a jikin naman
saiki dunga sakashi a jikin kuli kuli kina dankarashi a jikin naman
sannan ki yayyafa man gyadarki a jikin naman
saki sa wayrki a wuta amma karki saka wutar da yawa
saboda karya kone
kuma ya gasu a hankali
in kuma uwargida nada
oven shikenan saiki saka tsiranki a ciki ki gasa

akwai kuma wani method din zaki iya samun albasa da sweet paper
[koran tattasai]
saiki yanyanka round round
sai dauko namanki daya albasa daya
sweet paper daya nama daya kigasa.
kinga Hjy kin bada style yadda zaki burge maigida
ngd 
19/8/2019
Rubutawa:-Binta Murtala[Ummu Ahmad]

Shiryawa da yadawa:-Cibiyar wayar dakan Mata 

🌹Dake Ake Global Consultancy🌹

Share:

DABARUN SARRAFA NAMA 04

🌹Dake Ake🌹
Darajarki abincinki

*DABARUN SARRAFA NAMA*-4

*Gas meat*
kayan hadi
Nama zalla
Gishiri
Maggi
kanunfari
masoro
cinnamon
Albasa

Dafarko zaki samu namanki
musanman mara kitse
saiki gayarashi
amma inasi na sanar da uwar gida shi Gas meat yan bukatar albasa mai yawa
kuma baasa kayan miya
To idan kin gyara namanki saiki zuba kayan hadin dana fada a sama
[abinda yasa nace ayi amfani da kayan kanshi da albasa sbd shi Gasmeat in uwar gida tasanshi zakiga ba kayan miya acki idan kina bukatar yaji to masoro zai baki dandanon yaji amma bana barkono ko atturuhu ba]
kuma masoro yana da amfani ajiki ba cutarwa ba

daga nan saiki sa kayan dandano yadda kike bukata
idan kinada tukunya ko kasko non-stick
saiki zuba. da albasarki mai yawa kusan daidai da naman saiki ta juyawa haryayi dan romo romo
kuma ya dahu
 uwar gida kinga
maimakon Alhaji ya tafi wani guri sayan Gasmeat to uwar gida ta iya
nagode.
19/8/2018
Rubutawa:-Binta Murtala{Ummu Ahmd}

Yadawa:-Cibiyar wayar dakan mata


🌹Dake Ake Global Consultancy🌹
Share:

YADDA AKE DAMBUN KUSKUS

*TAURARIN MATA GROUP*

🌟🌟🌟🌟🌟🌟
🌟🌟
*DAMBUN KUS-KUS (COUSCOUS)*

*kayan hadi :*

🌷Couscous
🌷Zogale
🌷Carrot
🌷Cabbage
🌷Gyada
🌷Mai
🌷Attaruhu ko Tattasai
🌷Albasa
🌷Tafarnuwa
🌷Maggi

*YADDA AKEYI:*

```Da farko zaki samu couscous dinki saiki jika shi na kamar minti 7,idan ya jiku saiki tace ruwan ya tsane,saiki samu steaming pot dinki,ko abinda kikeyin danbu,saiki dauko zogalenki,gyada,carrot,cabbage,maggi,curry,nama da attaruhu da albasarki da ki yayyanka su sai ki zuba ki juya da sauran spices din da zaki saka ki hada akan couscous din ki juya sosai ko ina yaji,
sai ki kawo ruwan dumi ki yayyafa da Mai sai ki zuba a madanbaci ko steamer ki dora a wuta ki bashi minti30 zaki ji yana kanshi kuma zaiyi laushi,idan yayi laushi saiki sauke sai zuba ci😋😋😋```

*ZY MARIAM TIJJANI ADAM*
Share:

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive