Showing posts with label Girke-Girke (Cookings). Show all posts
Showing posts with label Girke-Girke (Cookings). Show all posts

Tuesday, 13 August 2019

DABARUN SARRAFA NAMA 05

🌹Dake Ake🌹
*DARAJARKI ABINCINKI*

*DABARUN SARRAFA NAMA-5*

*TSIRE*
kayan hadi
Nama
kuli kuli
barkono
Kayan kanshi
maggi
gishiri
man kuli

da farko uwargida zaki sami namanki amma banda kashi
ki gyarashi
uwar gida in kina bukata zaki iya samun harda mai kitse 
saki yanyanka yadda kike bukata
saiki samu kuli kulinki 
ki hadashi da kayan hadinki 
bayan nan saki samu tsinkenki ki tsaftace shi
daga nan saiki tsirashi a tsinken bayan kin gama kidansa laima a jikin naman
saiki dunga sakashi a jikin kuli kuli kina dankarashi a jikin naman
sannan ki yayyafa man gyadarki a jikin naman
saki sa wayrki a wuta amma karki saka wutar da yawa
saboda karya kone
kuma ya gasu a hankali
in kuma uwargida nada
oven shikenan saiki saka tsiranki a ciki ki gasa

akwai kuma wani method din zaki iya samun albasa da sweet paper
[koran tattasai]
saiki yanyanka round round
sai dauko namanki daya albasa daya
sweet paper daya nama daya kigasa.
kinga Hjy kin bada style yadda zaki burge maigida
ngd 
19/8/2019
Rubutawa:-Binta Murtala[Ummu Ahmad]

Shiryawa da yadawa:-Cibiyar wayar dakan Mata 

🌹Dake Ake Global Consultancy🌹

DABARUN SARRAFA NAMA 04

🌹Dake Ake🌹
Darajarki abincinki

*DABARUN SARRAFA NAMA*-4

*Gas meat*
kayan hadi
Nama zalla
Gishiri
Maggi
kanunfari
masoro
cinnamon
Albasa

Dafarko zaki samu namanki
musanman mara kitse
saiki gayarashi
amma inasi na sanar da uwar gida shi Gas meat yan bukatar albasa mai yawa
kuma baasa kayan miya
To idan kin gyara namanki saiki zuba kayan hadin dana fada a sama
[abinda yasa nace ayi amfani da kayan kanshi da albasa sbd shi Gasmeat in uwar gida tasanshi zakiga ba kayan miya acki idan kina bukatar yaji to masoro zai baki dandanon yaji amma bana barkono ko atturuhu ba]
kuma masoro yana da amfani ajiki ba cutarwa ba

daga nan saiki sa kayan dandano yadda kike bukata
idan kinada tukunya ko kasko non-stick
saiki zuba. da albasarki mai yawa kusan daidai da naman saiki ta juyawa haryayi dan romo romo
kuma ya dahu
 uwar gida kinga
maimakon Alhaji ya tafi wani guri sayan Gasmeat to uwar gida ta iya
nagode.
19/8/2018
Rubutawa:-Binta Murtala{Ummu Ahmd}

Yadawa:-Cibiyar wayar dakan mata


🌹Dake Ake Global Consultancy🌹

Tuesday, 30 July 2019

YADDA AKE DAMBUN KUSKUS

*TAURARIN MATA GROUP*

🌟🌟🌟🌟🌟🌟
🌟🌟
*DAMBUN KUS-KUS (COUSCOUS)*

*kayan hadi :*

🌷Couscous
🌷Zogale
🌷Carrot
🌷Cabbage
🌷Gyada
🌷Mai
🌷Attaruhu ko Tattasai
🌷Albasa
🌷Tafarnuwa
🌷Maggi

*YADDA AKEYI:*

```Da farko zaki samu couscous dinki saiki jika shi na kamar minti 7,idan ya jiku saiki tace ruwan ya tsane,saiki samu steaming pot dinki,ko abinda kikeyin danbu,saiki dauko zogalenki,gyada,carrot,cabbage,maggi,curry,nama da attaruhu da albasarki da ki yayyanka su sai ki zuba ki juya da sauran spices din da zaki saka ki hada akan couscous din ki juya sosai ko ina yaji,
sai ki kawo ruwan dumi ki yayyafa da Mai sai ki zuba a madanbaci ko steamer ki dora a wuta ki bashi minti30 zaki ji yana kanshi kuma zaiyi laushi,idan yayi laushi saiki sauke sai zuba ci😋😋😋```

*ZY MARIAM TIJJANI ADAM*

Sunday, 7 July 2019

DABARUN SARRAFA NAMA 03

🌹Dake Ake🌹
Darajarki Abincinki

DABARUN SARRAFA NAMA -3
Dambun Nama

Dafarko zaki samo namanki zallah
bamai kitse ko kashi ba
 gyrashi
ki hada

Albasa
Attaruhu
kayan kanshi[Citta,kanunfari,masoro,cinnamon,maggi,gishiri,mangyada]
 bayn kin hadasu a tukunya ki zuba ruwa yadda naman zai hade da kayan da kika zuba su dahu sosai
bayan ya dahu kuma ya tsotse ruwansa
saiki sauke
hanya biyu ce
ko in zaki iya ki cigaba da juyashi harya fara ragargajewa [yafi wahala]
kodai ki juyeshi a turmi ki daka
ko kuma ki zuba a injin bature ki nika
daga nan saiki zuba mai a kasko yayi zafi kisa albsa ya soyu saiki zuba nikakken namanki
kita soyawa sai yayi yadda kike bukata
 daga nan saki juye a container mai tsafta
yawwa daga nan sai ci😋😋
nagode
19/8/2018
Rubutawa:-Binta Murtala[ummu Ahmd]

Yadawa:-Cibiyar wayar da kan mata
ta
🌹 Dake Ake Consultancy🌹

Friday, 5 July 2019

DABARUN SARRAFA NAMA 02

🌹Dake ake Global🌹
*DARAJARKI ABINCINKI*

*DABARUN SARRAFA NAMA*-2
 SUYAR HANJI

Da farko dai zaku zauna dan Allah ki nutsu ki gyara hanjinki ki code kashin dake ciki ki wanke shi akwai wani abu acikin ciki ana ce masa littafi mai shafi shafi
to shima sai an kiyaye saboda yana da kashi aciki sosai sannan tunbi shima yanada matsala
dan haka uwar gida saiki kiyaye bayan kin gyara kin wanke
saiki zuba a dan kwando dan ruwan ya dan tsane
sai ki zuba a kasko
ki hada kayan kanshinki
Citta
kanunfari
masosro
barkono
tafarnuwa
cinnamon
gishiri
maggi
albasa
dadai sauran kayan kanshi da kike bukata

kuma sannan uwar gida saikin kiyaye wajen sa gishiri da Maggi a kayan ciki.saboda shi yana da saurin jin gishiri
yanzu zaiyi yawa

Sannan bayan ya dauko soyuwa uwar gida saikin rage wuta saboda zai iya babbakewa kinga kuma ai baiyi daidaiba
kuma ba kima gurin maigida.Nagode

19/8/2018
.
Rubutawa:-Binta Murtala[Ummu Ahmad]

Yadawa:-Cibiyar wayar da kan Maaurata

🌹Dake ake🌹

Tuesday, 2 July 2019

DABARUN SARRAFA NAMA

🌹Dake ake Global🌹
*DARAJARKI ABINCINKI*


Assalamu alaikum Warahamatullahi Wabarakatuhu

*DABARUN SARRAFA NAMA-1*
yanuwa yau zamu yi bayani akan yadda zamu sarrafa naman sallah yadda ya sawwaka

Allah ya mana jagoranci
da farko dai bara mu fara lissafa hanyoyin da Allah ya nufemu da sani
1.Soya nama
2.Dambun nama
3.Gas meat
4.Tsire
5.Balangu
6.Meat & Potatoes
7.Paper soup

yawwa zamu dau ko wanne daya bayan daya
muyi bayaninsa .
19/8/2018

✍binta murtala.
🌹DAKE AKE🌹

Thursday, 24 January 2019

Fresh Fish

🌹🌹 *DAKE DAKE*🌹🌹

*DARAJARKI ABINCINKI*

*FRESH FISH*
_kifi_
_Albasa_
_Mai_
_Fulawa_
_Attaruhu_
_Gishiri,maggi,kayan qamshi_

_Da farko zaki samu kifinki ki wanke shi ki cire qaya kiyanka gunduwa gunduwa,seki samu fulawarki kisamata maggi,albasa,gishiri,attaruhu,kayan qamshi,duk ki cakuda seki dama shi yadan yi ruwa ruwa kadan bada yawaba,seki dora mai awuta idan yayi zafi seki rage wutar sannan ki dakko kifin nan kidinga tsomawa acikin hadin fulawar nan kina sawa a mai.

*BARRISTER*