Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

Showing posts with label Hikayoyi Da Tatsuniyoyi (Myths/Folktales). Show all posts
Showing posts with label Hikayoyi Da Tatsuniyoyi (Myths/Folktales). Show all posts

LABARIN KALALA DA KALALATU


MAGANA JARI CE 

LABARIN KALALA DA KALALATU

Akwai wani mutum wai shi Kalala, yana da matarsa wadda a ke kira Kalalatu. Kalala Allah ya yi shi wani irin mutumin da ne, ba abin da ya fi da ki illa a yi masa abinci ya ci shi kadai. Da suna ci tare da wani makwabcinsa, sai makwabcin ya zama wani iri ne mai mita. Ya kan rika cewa Kalalatu ba ta iya miya ba, wai kullum miyarta daga ta cika gishiri sai ta cika ruwa.


Da Kalala ya ga tsegumin ya faye yawa sai ya bar kai abincinsa wurin makwabcin. Ya rika fita karauka yana nemo baki, yana kawowa gidansa suna ci tare.


To, Kalalatu ba ta kaunar wannan dabi’a ta mijinta, domin bisa ga misali, ran da Kalala ya yanka kaji biyu, iyaka Kalalatu ta sami cinya, domin duk Kalala zai kai wurin bakin da ya jawo ne su cinye. 

Ta yi, ta yi ta hana shi wannan tabi’a, ya ki hanuwa. Saboda haka sau da yawa in ya ba ta dahuwa sai ta tsame rabi ta cinye, in Kalala ya yi magana ta ce ya kone ne, ko kuwa ta ce ta sauke ta shiga daki dauko kwano, kafin ta fito ta tarar kyanwa ta cinye rabi. Dalilai dai irin wadannan marasa kan gado ga su nan kullum Kalala na ta sha, amma saboda hakurin da Allah ya zuba masa ba ya cewa kome.


Ran nan, ko ina Kalala ya sami kudi sai ya tafi kasuwa ya nemo dakwalen kaji guda biyu ya sawo. Ya yiwo cefane ya kawo gida, ya ce wa Kalalatu ta soye kajin nan gaba daya. 

Ta tashi, bayan ya fige ya gyara mata, ta sa tukunya ta shiga suya. Abu ga dakwalen kaji, duk kitse ya cika tukunya, sai wani abu su ke coi, coi, coi, in tana juya su. Duk kuwa kwadayi ya kama ta, da ma ga ta idonta idon nama sai ka ce kura sai yawu ke zuba dalala. 

Ta sa dan yatsa ta dandana ta ji ko gishiri ya yi daidai, sai ta ji abin dadi ya kamo ta har ga keya, ta ce, “Kai, wadannan kaji yau suna shirin ganin wata irin gajerar suya. Amma dubi duk yawan kajin nan, rabona bai fi cinya ba daga cikinsu. Ka san dai halin mai gidan nan ya miskile ni.”


Ta ci gaba da suya kanshi na jifarta, ta yi kamar ta jure ta kasa, sai ta fara tsame tana ci, wai ta kau da mugun yawu. Kafin su soyu ta kusa cinye rabin kaza. Da ta sauke sai ta je ta gaya wa mijin sun soyu.


Kalala ya ce, “To, sai ki cire cinya guda, taki ke nan. Saura kuwa a ajiye, har in je in samo abokan ci.”


Kalalatu ta ce, “To.” Ta tafi ta cinye yar cinyar da aka ce ita ce tata, ta tsuguna tana kallon saura, sai mai ke zuba nash, nash.

 Ta ruga wajen kofar zaure ta leka ko ta hango mijin tafe da bakin, ba ta ga kowa ba. Sai ta komo wajen kaji ta kura musu ido. 

Sai ta ce, "Af, ashe ma fika fikai guda biyu sun kone tun dazun, bari ma in cinye na dayar don su zo daidai, kada mai gida ya gane." Sai ta fiffizge ta lakwame. Ta sake rugawa bakin zaure ta gani ko mijin na tafe, ba ta ga kowa ba. 

Ta dawo ta tsaya bisa kwanon kaji ta ce, “Shin mai gidan nan zai zo dai? Ga kaji har sun fara yin sanyi. To, ni Kalalatu, yanzu in ya zo ya tarar wannan kazar duk na fiffige ta, ya tambaye ni in ce me? Ba abin da ya fi sai in cinye ta gaba daya, in ya zo in ce kyanwar gidan nan ta sace ta." Sai ta tsuguna ta cinye ta sarai, ta kwashi kasusuwa ta kai masai ta zuba.

Ta koma kofar zaure ta hanga, ba ta ga mai gida ba.

 Da ta ga haka sai ta dawo, ta ce, “A bari ya huce shi ya kawo rabon wani. Bari in karkare cinye guda, kowa ya huta, in ya so in ya dawo kome ta tafasa ta kone.”

 Sai ta kama kazar guda kuma ta lakume. Ta nufi randa ta debi ruwa ta kora, ta yi gyatsa, ta ce, “Madalla, kome ta ke zama ta zama.”
Ta zauna ke nan, 

sai ga mai gida ya shigo. Ya ce wa Kalalatu, “Yi maza ki nika yaji ki barbada musu, kin san yanzu lokacin sanyi ne, ba abin da ya fi yaji amfani. Na manta ne in gaya miki ki nika yaji dazun. Yi hakuri, yau dai kin sha aiki.”


Kalalatu ta ce, ‘‘Ai ba kome, ku dakata mini dai kadan.”

 Ta shiga daki tana ta shawarwarin abin da za ta ce wa mijin ya faru ga kaji. Tana can cikin daki, 

sai Kalala ya dauki wuka ya nufi manika yana wasawa kararas, kararas, wai don ta yi kaifi ya sami ta yanka kaji kanana kanana, in an kawo.
Kalala na can na ta fama da washin wuka, sai Kalalatu ta ji ana sallama. 

Ta yi farat ta fita bakin zaure wajen mai sallama, ta dube shi ta rike baki, ta ce, “Kai bako, kai ne mai gidan nan ya kirawo wai ku zo ku ci abinci?”

Bako yace, “I, Allah ya saka muku da alheri.”


Kalalatu ta ce, “Kai, tafi can, sakarai, ba ka san abin da a ke ciki ba. Kana tsammanin mutum mai hankali ya sa a yi masa abinci ya fita karauka neman abokin ci? In kana kama gabanka ka ruga, tun da wuri ka ruga. Ka ji shi can yana washin wuka, kunnenka guda zai yanke. Kullum haka ya ke yi, motsattse ne.”


Bakon nan, ko da ya saurara ya ji Kalala na washin wuka sai ya dafe keya ya zura a guje. 

Kalalatu kuma ta ruga wajen Kalala, ta ce, “Ga irin jaye-jayen naka nan, ba ka san irin mutanen da ka ke jawowagida ba.
Kalala ya ce, “E? Mahaukaci ne?”


Kalalatu ta ce, “Mahaukaci mana, ko ba mahaukaci ba ne ai barawo ne, da barawo ko da mahaukaci ai duk tafiyarsu ke nan. Kajin da na barkada wa yaji, ko da ya gan su sai na ga ya yi wuf ya fizge, ya shafa a guje da su. Ga shi can ya mika, ya tasar wa kasuwa."


Kalala ya fusata, ya ce, “Allah wadan dan banza! Mutanen duniya ba wanda ke iya musu. Da ma ya bar mini ko da guda daya, ai da na sami ta kalaci. Dakwalen kajin nan duk ya cinye shi kadai? Bari in leka ko na hango shi, mu raba.” Sai ya ruga wajen zaure ya hanga, sai ga bakon nan can ya tattake da gudu kaca kaca kaca yana korar iska.

 Kalala ya ce, “Kai abokina! Kai tsaya, don Allah ko guda daya ka ba ni! Wallahi su ke nan, mai dakina ko lasawa ba ta yi ba, ka dauke.” Bako ya yi kamar bai ji ba.


Kalalatu ta ce wa mijin, “Bi shi mana, a guje dai na san ba ya tsere maka.

 Duk wahalan nan da na sha ta zama a banza, ko lasawa ban yi ba, ai ka san ka dauki alhakina.”


Sai Kalala ya runtuma a guje da wukarsa a hannu, ya bi bako yana kira, “Tsaya don Allah, daya kadai na ke so, na bar maka daya!”


Bako tsammani ya ke Kalala na nufin kunnensa daya kadai ya ke so ya yanka. 

Ya waiwaya sai ya ga ya taso masa da wuka tsirara a hannu.


Saboda haka ya kara mai, ya dai yi wa Kalala fintinkau yana ji yana gani.


Da Kalala ya ga abin ba girma, sai ya juyo ya nufo gida da wukarsa a hannu, yana kutawa, yana Allah ya isa. 

Da matar ta gan shi ya dawo yana zage zage sai ta tarye shi, ta ce, “Ya ba ka? Ka ga irin abin da na ke gaya maka nan tuni."

Kalala ya ce, “Ko tarad da shi na yi? Wannan akwai dan banza da gudu! Ga shi kamar tsoho, amma daya zura sai ganinsa a ke kamar ba ya taka kasa. 

Bar shi ya je ya ci, ban dai yarda masa ba duniya da lahira. Allah ya isa. Daga yau ko sai yau, ba na sake kiran dan kowa ya ci abincina, tun da duniya ta sake. Mts, Allah wadai! Talaka dai ba aboki ne ba, ko ka so shi, ran biki kwa Bata.”


Share:

SARKI MALHANU DA 'YAN MATA

SARKI MAHLANU DA 'YAN MATA
 

A wani lokaci mai tsawo daya gabata, anyi wani
mutum wanda yake da 'ya'ya biyu. Dukkan su
yan mata ne, kuma sun isa aure.

 

Rannan sai wannan mutum ya tsallaka ruwa
izuwa wani gari domin ziyara. Da isar sa sai yake
jin labarin sarkin Garin wanda hamshaki ne yana
neman aure, kuma an gwada dukkan yan matan
garin amma basuyi masa ba.

 

Dawowar sa gida keda wuya sai ya sanar da
iyalinsa. Babbar 'yarsa wadda sunan ta
Mpunzikazi, tace zata je domin auren sarki.

Mahaifinta yayi murna da haka, ya turawa yan
uwa da abokansa na arziki don suzo a rakata
izuwa garin ta yadda zata zamo matar sarki,
amma sai mpunzikazi tace tafi son a barta taje
ita kadai.

Washe gari taci kwalliya ta kama hanya, tana
cikin tafiya sai ta hadu da Bera. Bera ya matso
gareta yace "kina so na nuna miki hanya?''. Sai
kuwa mpunzikazi tayi tsaki, tace "gafara nan,
waye kai da zaka nuna min hanya?"

Daga nan
bata kara bi takansa ba ta wuce.

Shikuwa sai
cewa yayi "indai a haka zaki to bazaki ci nasara
ba".

Tayi gaba kenan, sai ga kwado yazo gareta.

Kwado yace "idan kinaso zan nuna miki hanya".

Sai kuwa ta daka masa tsawa, tace "kai kauce,
har ka isa kayi magana da matar sarki?"

Sai kwado yace kije gaba, zakiga abinda zai faru"

Taci gaba da tafiya kenan sai ga wani yaro yana
kiwon dabbobi.

 

Da ganinta sai ya matso kusa
yana cewa "yayata ina zuwa haka?"

Mpunzikazi taja tsaki tace " waye kai da zaka
kira ni da yayarka? Kai kauce kabani wuri."

Yaro ya kara cewa "ina jin yunwa, ko zaki
taimakeni da abinda zanci?"

Sai kuwa ta kara daka masa tsawa tace " ka
kauce ka bani wuri fa nace!!!"

Sai yaro yace " ai kuwa indai haka zakiyo, to ba
zaki dawo ba"

Mpunzikazi dai ta wuce gaba.

Tayi gaba kenan,
sai ga wata tsohuwa tana zaune bisa wani
dandamalin dutse.

Tsohuwa tace "sannu da zuwa
'yar nan ga shawara zam baki: idan kika je gaba
zaki ga bishiyoyi suna miki dariya, kada ki sake
kiyi musu dariya.

 

Zaki ga kabakin madara da
zuma, kada ki sake kisha, sannan zakiga wani
mutum wuyansa a saman kansa, yana dauke da
ruwan sha, ko yayi miki tayi kada kisha".

Sai kuwa Mpunikazi tayi tsaki tace " wannan
mummunar tsohuwa da rigima take, ko meye
ruwanta dani oho?"

Ai kuwa wucewar ta keda wuya, sai ga bishiyoyi
na dariya, nan itama ta kyalkyale musu da dariya.

Taga kuttun zuma da madara, ta zauna ta
sharba, taga mutumin da wuyansa ke saman
kansa ya bata ruwa ta karbe tasha.

Bayan duk an gama wannan ne ta iso kofar
garin.

Zata shiga kenan sai ga wata budurwa
zata debo ruwa, ashe yar uwar sarkin ce.

Budurwar tace da mpunzikazi "yar uwata ina
zakije ne haka?"

Mpunzikazi tace " wacece ke da kike min
wannan tambayar? To nice matar da sarkin ku
zai aura"

Sai budurwar tazo gare ta tana cewa "tsaya na
nuna miki ta hanyar da zaki shiga garin" Amma
ina, mpunzikazi bata kula taba, ta wuce kurum
abinta.

Da shigarta garin sai mutanen garin suka
tambayeta abinda a kawota, ita kuma ta fada
musu, sai akace mata sarki baya gari yanzu,
amma ga hatsi ta girka masa abinci, idan ya
dawo zaici.

Haka kuwa akayi. Bayan ta gama abinci zuwa
yamma, sai ga guguwa na kadawa, alamun sarki
ya dawo kenan.

Zuwa can aka ce tazo sarki zai ganta. Da
shigarta inda sarkin yake sai ta tsorata, domin
kuwa wani katon maciji ta gani mai kawuna
biyar, a yaren su ana kiransa 'Makanda Mahlanu'.

Ta ajiye masa abincin data girka yaci, sai kuwa
yace abincin ba dadi don haka bata cancanci
zama matar sa ba, nan take ya kanannadeta ya
kashe ta.

 

Labari sai yazowa yan uwanta cewa batayi
nasara ba.

Hakan yasa kanwarta shirin cewa
itama zata jarraba. Sunan ta mpunzanyana.

Ubanta yace zai tara mutane suyi mata rakiya,
tace to baba babu matsala. Da ranar tafiya tazo
sai suka fita suka kama hanya. Can sai ga bera a
gaban su. Bera yace "yarinya ko kina so na nuna
miki hanya?"

Mpunzanyana tace "ai kuwa zanji dadi idan ka
nuna min ta inda zamu bi". Daga nan sai ya nuna
musu inda zasu bi, suka wuce.

Sunyi gaba kenan sai ga wata tsohuwa. Tsohuwa
tace "yarinya bari na baki shawara, idan kika yi
gaba zakiga hanya ya kasu biyu, babba da
karama, to karamar zaki bi"

Mpunzanyana tace
"Nagode babata, zanyi kamar yadda kika ce"
Haka kuwa akayi kamar yadda tsohuwa ta fada,
suka bi karamar hanya.

 

Daga nan kuma sai ga
kwado. Kwado yace " bari na baki shawara, idan
kika je garin zakiga wata budurwa a bakin kofa,
ki girmamata yar uwar sarki ce, za kuma ace kiyi
ma sarkin abinci, ki tabbata kinyi abinci mai dadi,
sannan idan kika ga sarkin kada ki tsorata"
Mpunzayana tayi godiya ta wuce.

Bayan sun isa kofar gari, sai ga budurwa yar
uwar sarki. Ta tambaye su abinda ya kawo su,
mpunzayana ta fada mata, sai kuwa budurwar ta
nuna musu ta hanyar da ya kamata su shiga
garin.

 

Shigar su keda wuya aka gabatar musu da hatsi
domin tayiwa sarki abinci kafin dawowar sa.

Mpunzayana ta natsu tayi girki mai kayatarwa.

Zuwa yamma sai taji guguwa na tasowa, alamun
sarki ya dawo kenan.

 

Ta dauki abinci ta nufi inda akace mata yake.

Ta
ganshi katon macici mai kawuna biyar, amma ta
dake ba tare da taji tsoro ba, ta gabatar masa da
abincin. Da macijin yaci abincin sai yaji dadin sa,
yace hakika itace matar dazai aura.

Kawai sai
taga yayi birgima ya rikide izuwa santalelen
saurayi.

 

Akayi biki gagarumi, ya sanyata a gidan sarauta
tare da duk yan uwanta. Ya zama yana matukar
kaunar ta.

Shikenan, kurunkus..

 

Share:

KURA DA KARE


Kura da Kare
Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

Akwai wani mafarauci ana ce da shi Fautaranga, sai wata rana ya je gidan namun daji (dabbobin daji) ya ce da wa za mu farauta? Sai kura ta ce ni, sai ya ce da ita “dama ke nake nema”, sai suka tafi tare da kura. Suna cikin tafiya sai kura ta ce da shi tana jin yunwa, sai ya ce da ita ta bari sai sun ƙara gaba zai bata abinci.

Suna cikin tafiya sai suka isa wani kogi, sai ya ce da ita ta sha ruwa iya shanta. Da ta sha ta ƙoshi, sai shi kuma ya kafa bakinsa ya shanye dukkan ruwan kogin. Bayan ya shanye sai suka ɗebo kifayen cikin kogin suka cinye. Suna nan har dare ya yi, saboda haka da za su kwanta barci sai Fautaranga ya ce da kura “kar ki kwanta a bayana ina tusar ƙashi” sai kura ta ce bata yarda ba sai ta kwanta. Suna kwance can cikin dare sai kura ta ji ƙashi ya zo ya cake ta ya koma, sai ta tashi ta koma gabansa ta kwanta, da ta kwanta sai da gari ya waye sai kura ta ce da shi ashe dama abin da ka faɗa gaskiya ne ba ƙarya ba?

Daga nan sai ya ce da kura yanzu za mu je wajen wasu giwaye guda goma, idan mun je ki zage su, idan suka biyo ki sai ki yi tsalle ki faɗa cikin cikina. Da suka je sai kura ta zagi giwayen nan, da suka biyo ta da gudu sai ta yi tsalle ta faɗa cikin Fautaranga. Shi kuma sai ya kama giwayen nan ɗaya-bayan-ɗaya ya yayyanka su.

Kura kuma daga cikin maharbin nan sai ta wuce hancinsa ta taras da kasuwa tana ci a ciki, a cikin kasuwar sai ta je gurin mai tsire ta ce da shi za ta yi masa talla, sai ya ɗora mata tallar a faranti. Can sai Fautaranga ya kira kura ya ce “kura”, ya ji shiru, ya sake cewa “kura”, ya ji shiru, sai ya fyato ta (kamar yadda ake fyace majina) da farantin talla a kanta, da ya ga haka sai ya ce da kura ta je ta mayar da faranti ta fito su tafi.

Sai kura ta mayar da farantin, shi kuma mai tsire ya bata tsire ladar talla, da kura ta karɓa sai ta zauna ta cinye tsiren, bayan ta cinye sai ta fito suka ƙara gaba.

Da za su tafi sai aka ɗorawa kura cinyar giwa ta kasa tafiya, sai ya ɗauka ya raba shi kashi uku ya ɗora mata kaso ɗaya, shi kuma ya ɗauki dukkan sauran. Daga nan sai suka tafi gida.

Da suka iso gida sai ya bata kasonta ya ce ta je ta soya ta ci. Da ta soya ta ji daɗi, sai ta kira kare ta ce su zo su koma farautar, sai ta je aka haɗa mata hancin laka. Suna cikin tafiya sai kare ya ga zomo, da ya ga zomon sai ya ce da kura in ɗauka? Sai kura ta yi masa shiru, shi kuma sai ya faki idonta ya ɗauka ya jefa a ruzu.

Bayan sun yi doguwar tafiya, sai kare ya ce da kura yana jin ƙishirwa, sai suka je kogin da suka sha ruwa da Fautaranga, sai kura ta ce da kare ya sha iya shansa, kare ya sha, daga nan sai kura ta kafa kanta ta kasa shanye ruwan wannan kogi, da ta kasa sai kare ya ce da ita ya kika kasa shanyewa? Sai ta ce ai yanzu bana jin ƙishirwa. Sai kura ta ce da kare su shiga su kamo kifi, bayan da suka samu ɗan abin da suka samu, sai kura ta ce su ci gaba. Suna cikin daji dare ya yi musu, sai kura ta ce da kare “kar ka kwanta a bayana ina tusar ƙashi”, sai kare ya kwanta, har gari ya waye kura bata yi tusa ba. Sai kare ya tambayeta ya aka yi baki yi tusar ƙashin ba? Sai kura ta ce ai yau bata ci abinci ba shi ya saka. Daga nan sai ta ce da shi za su je wajen wasu giwaye, idan sun je kare ya tsokano giwayen nan idan sun biyo shi ya yi tsalle ya faɗa cikin hancinta.

Da suka isa sai kare ya tsokani giwaye, da suka biyo shi sai ya yi tsalle ya dira a kan hancin kura (hancin taɓo), sai hancin ya ruguje, daga nan sai kura ta ce kowa ya yi ta kansa, ka bi ta tudu na bi ta gangare. Da suka iso gida sai kura ta je gurin Fautaranga ta gaya masa cewa sun je wajen giwayen nan amma sun biyo su da gudu. Sai ya ce da ita, me ya hana ki zuwa ki karɓi magani a wajena kafin ku tafi?

Daga nan sai kare da kura kowa ya kama gabansa, da suka isa gidajensu sai kare ya ɗauko zomon nan ya fara suya, da kura ta ji ƙanshi sai ta laɓaɓo gidan kare ta taras da shi yana suya. Sai kura ta tambaye shi ta ce “kai kuma wa ya baka nama ka ke soyawa?” Sai kare ya ce da ita suya aka bashi idan ya gama ya suɗe kaskon. Sai ta ce da shi tana son naman idan kuma ya hanata ta cinye shi duka shi da naman. Sai ta ce za ta je ta dawo kafin ya gama.

Fitar kura ke da wuya sai kare ya je ya ɓoye naman nan a ɗaki, sai ya suɗe kaskon ya tofa yawu da majina a ciki, ya soya, ya ajiye. Da kura ta dawo sai ya bata sai ta suɗe, sai ta ce “kare wannan naman da daɗi idan aka baka zaka bani?” Sai ya amsa mata da cewa ai tuni aka bashi ya cinye.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya
Share:

KWAƊI DA SARKIN SU


KWADI DA SRKIN SU
GATANAN GATANANKU
Wai wasu kwadi ne suke zaune a cikin wani tafki cikin jin dadi da walwala, ba abin da suka nema suka rasa, idan sun gaji da wasansu cikin ruwa sai su tsallaka kan tudu su sha iska. Ba su damuwar kowa, kuma babu wani abu da yake damun su. Suna nan haka sai wasu daga cikinsu suka ce, ina amfanin zamanmu haka babu wani Sarki da zai rika mulkinmu, ba mu da wasu dokoki da za su tafiyar da tsarin rayuwarmu.

Allah kuwa ya amshi addu'arsu! Ana nan wata rana sai wani dan guntun reshen bishiyar da take bakin tabkin ya karye, ya fado kwatsam a gefen tabkin. Kwadi suka tsorata suka fada ruwa da gudu. Sai wasu daga cikinsu suka ce ai
Sarkin da suke roko a turo musu ne Allah ya turo musu. Kwadi na cikin ruwa suna jira su ji irin dokokin da Sarki zai shata musu, suka ji shiru, su kuma suna jin tsoron su matsa kusa da shi. Ana nan dai har wani mai karfin hali daga cikinsu ya matsa kusa da reshen itacen nan da ya fado, sannu-sannu har ya kai ga taba shi, icce bai motsa ba, har ya hau kansa, yana rawa, itace dai bai motsa ba. Da saura suka ga haka, sai duksuka fito suka haye kan reshen itace. Sai ya kasance koyaushe nan ne wurin zaman kwadi tare da sabon Sarkinsu. Sai dai kwadi ba su yi murna da wannan Sarki da aka turo musu ba, suka nuna sun fi son Sarki mai rai, mai motsi, wanda zai rika shata musu dokoki, kuma ya shimfida mulkinsa.

 Wannan buri na kwadi ya sa Allah ya yi fushi da su. Kwaram ran nan sai ga wani zalbe zai wuce ta wurin, sai ya ga kwadi da yawa bakin tabki, shi ke nan abin nema ya samu, dama wurin neman abinci zai tafi. Sai ya tsaya bakin tabkin nan ya rika kamakwadi yana cinyewa. Da kwadi suka ga zalbe ya dame su da kisa haka, ya hana su sakat, sai suka ce wannan wane irin Sarki ne aka turo mana. Mu dai mun fi son zamanmu na da. DA MULKIN
ZALUNCI GWAMMA ZAMA BABU
SARKI!
***

Kurungus kan dan bera, ba
don gizo ba da na yi karya...

 

 
Share:

SARMA SARMA DUDUF

Sarma Sarma Du Duf
Gata nan ga ta nan ku...

A wani a gari da akwai wata yarinya wacce tace ita baza ta aure kowa ba sai mara taba jikin shi!!! ko wani namiji ya zo wajen ta sai tace A’a yana da tabo a jikin sa.

Haka dai ko da yaushe take yi har watarana wasu doddani su biyu suka ji labari. Sai suka je gidan tururuwa suka yi wanka suka zama samari masu kyau.

Suka kama hanya sai garin da yarinyar take. Da suka isa sai suka karasa gidan su yarinyar. Aka yi masu sallama da ita ta fito. Da ta duba na farko ashe tururuwa ta chije shi a wuya dan haka sai tace ay shi yana da tabo. Sai ta duba jikin dayan sai taga babu tabo a jikin sa ko guda daya sai ta yarda cewa zata aure shi.

Suka yi aure sai ya kai ta gidan sa wanda suke zaune tare da maman sa. Ranar farko bayan sun kwanta bacci ita da kanwarta, sai kuwa suka ji a bakin kofa ana “sarma sarma du duf” ashe uwar mujin nata ce.
yarinya: wane ne nan yake mana sarma sarma du duf?

uwar miji : uwar mijin ki ce taki miki sarma sarma du duf

yarinya: me kike so ki ke mana sarma sarma du duf?

uwar miji : wuta nake so nake maki sarma sarma du duf

sai yarinyar ta debo wuta a kasko ta mika mata

yarinya: gashi nan ki diba ki bar mana sarma sarma du duf.

Da ta mikawa uwar mijin, sai uwar mijin ta kase wutar ta sake tambayar. Suka yi ta sake maimaita wa uwar mijin ta kara kashe wutar. Suna tayin haka har gari ya waye sannan aka hakura. kuma duk hakan da ake yi lokacin uwar mijin ta zama dodanniya.

washe gari da rana sai kanwar ta tafi kai wa mijin yayarta abinci a gona sai kuwa ta gansu sun zama dodanni suna ta cin kwadi, ita kuma sai ta kama waka tana cewa “;mijin yata ci da kwadi, mijin yata sha da kwadi”

Haka kullun wannan abu yake faruwa yake faruwa tsakanin yarinyar da uwar miji, da kuma kanwar matar and mijin matar.

Rannan dai matar da kanwar ta suka gaji sai suka yi shawara cewa su gudu. Safiya nayi kuwa suka bi ta wani rami suka gudu. Da suka isa gida sai tace ita bata son auren.

Daga sannan bata kara duba tabo jikin namiji ba idan yazo wajen ta...har dai a karshe ta aure wani daga cikin masu zuwa wajenta.
 

Share:

GIZO DA ƘOƘI DA KANTU


Gizo da Ƙoƙi da Kantu
Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

Wata rana ce dai, wata rana ce dai, da Gizo da Ƙoƙi da Kantu, suka shirya suka tafi daji farauta. A kan hanyar su ta tafiya, sai suka ci karo da ruwa. Da suka shiga ruwan nan don su tsallake shi, sai Kantu ya fara marmashewa, sai Gizo ya ce da shi, kai Kantu, idan ka ci gaba da marmashewa zan cinye ka. Shi ke nan, sai Kantu ya daure, suka ci gaba da tafiya. Can sun shiga tsakiyar ruwa, sai Kantu ya sake marmashewa, sai Gizo ya juyo ya cinye shi.

Bayan Gizo da Ƙoƙi sun tsallake ruwa, sai Gizo ya ɗaura lilo a gindin wata bishiya yana ta fillawa/hillawa. Can yana cikin lilo yana jin daɗi, sai ya hango wani damo, sai ya bi shi da gudu ya kama damon nan, ya yanka, ya gasa, ya hana ƙoƙi ko hanji.

Da Gizo ya koma ya hau lilonsa yana ta hillo, can sai ya ji cikinsa ya fara ƙugi, sai ya ce da Ƙoƙi cikinsa yana ciwo. Saboda haka sai Ƙoƙi ta goya shi dan ta kai shi gurin mai magani.

Ƙoƙi tana cikin tafiya sai ta zo gindin wata babbar bishiya, tana zuwa gindin wannan bishiya sai ta ji wata tsuntsuwa tana cewa:

Tsuntsuwa: Ke Ƙoƙi ina za ki?
Ƙoƙi: Za ni gurin maganar nan.
Tsuntsuwa: In kin je ki ce Gizo ya ci damo ba zai yi rai ba.

Shike nan sai Ƙoƙi ta ci gaba da tafiyarta. Tana nan tana ta tafiya, sai ta sake isowa gidin wata bishiyar, sai ta sake jin muryar tsuntsuwar nan tana cewa:

 Tsuntsuwa: Ke Ƙoƙi ina za ki?
Ƙoƙi: Za ni gurin maganar nan.
Tsuntsuwa: In kin je ki ce Gizo ya ci damo ba zai yi rai ba.

Da Ƙoƙi ta ji haka sai ta ce da Gizo, kana dai ji an ce ba za ka rayu ba ko? Gizo ya yi shiru ya kasa cewa komai. Ƙoƙi kuma ta ci gaba da tafiya. Tana cikin tafiya ta sake isa gindin wata bishiyar, sai ta sake jin muryar tsuntsuwar nan tana cewa:

Tsuntsuwa: Ke Ƙoƙi ina za ki?
Ƙoƙi: Za ni gurin maganar nan.
Tsuntsuwa: In kin je ki ce Gizo ya ci damo ba zai yi rai ba.

Ai kuwa kafin tsuntsuwar nan ta gama rufe bakinta Gizo ya tsuge da zawo. Da Ƙoƙi ta ga haka, sai ta sauke shi daga bayanta, ta zuba masa ido tana kallon abin mamaki. Ba jimawa sai damo ya ce da Gizo, “ta ina zan fito?” Sai gizo ya ce da shi, “fito ta hammata”. Sai damo ya ce, “in fito ta hammata warin hammata ya dame ni. Ta ina zan fito?” Sai Gizo ya ce, “fito ta ciki”. Sai damo ya ce, “in fito ta ciki hanji ya tare ni. Ta in azan fito?” Sai Gizo ya ce, “fito ta, taka shi”. Sai damo ya ce, “in je kashi ya taɓa ni. Ta in azan fito?” Sai Gizo ya ce fito ta hammata. Shike nan sai damo ya fito ta hammatar Gizo. Yana fitowa sai Gizo ya mutu.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.
Share:

GIZO DA NOMAN GYAƊA

Gizo da Noman Gyaɗa
Wata rana Gizo da Ƙoƙi, abin duniya ya yi musu zafi. Sai Ƙoƙi ta ce da Gizo, “Ina ga da za mu yi noma da mun samu sauƙi”. Da Gizo ya ji haka sai ya ce, “Ƙwarai hakan ya dace”. Sai Ƙoƙi ta ce, “to me ka ke ganin zamu noma? Mu shuka shinkafa ne, ko alkama, ko kuma acca?” Sai Gizo ya ce, “a’a, mu shuka gayaɗa kawai”. Sai suka yarda akan cewa za su shuka gyaɗa. Amma ashe shi Gizo yana nufin ya yiwa Ƙoƙi wayo da wannan shawara tasa.

Da aka tashi yin shuka, sai Gizo ya ce da Ƙoƙi, ai ba a shuka gyaɗa sai an soya ta. Sai Ƙoƙi ta amince ta soya gyaɗa, ta baiwa Gizo ta ce ya je ya shuka. Da Gizo ya je gona dan yin shukar gyaɗa, sai ya ɗaura lilo a jikin bishiya, ya hau lilon nan yana cin gyaɗa, yana rera waƙa kamar haka:

……………………….

Da haka-da haka, yau ya je gona, gobe ya je, har wannan gyaɗa ta ƙare, ba tare da ya shuka ba.

Da damina ta yi nisa, sai ƙoƙi ta fara tambayarsa maganar gona, shi kuwa Gizo sai ya hau bada labari yana cewa, “Ai gonar nan ta yi kyau sosai”.

Da kakar gyaɗa ta fara yi, sai Ƙoƙi ta ce da Gizo ya fara ciro musu wannan gyaɗa su riƙa ɗan taɓawa kafin a farɗe ta. Saboda haka a duk lokacin da Ƙoƙi ta buƙaci gyaɗa sai Gizo ya je gonar mai gari ya yago ya kai mata. Sannu a hankali Gizo ya kusa cire gyaɗar gonar mai gari baki ɗayanta.

Wata rana sai mai gari ya gane cewa ana cirar masa gyaɗa, saboda haka sai ya zuba masu gadi a gonar suka ɓoye a gurin da ba mai ganinsu. Can sai ga Gizo ya zo cirar gyaɗa. Caraf, masu gadin nan suka cafke Gizo, suka tafi da shi gurin mai gari. Daga nan aka yanke masa hukunci, aka kore shi daga gari.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya

Share:

LABARIN YUSUF DA BALA

Yusufu da Bala

Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

Akwai wasu yara su biyu; Yusufu da Bala, wata rana ana biki a gidansu, sai aka aike su su je daji su yanko yakuwar miya. A kan hanyarsu ta tafiya sai suka ci karo da wani ƙaton zakara da ganga rataye a wuyansa. Sai zakaran ya tambaye su, “Yara-yara ina za ku je ne?”, sai suka ce da shi, “Za mu je mu yanko yakuwa ne”, sai ya ce, “Na yi muku ɗan kiɗa ku ji?”, sai suka ce, “e”, sai ya fara”.

Tamagungun-tamagungun muƙut sai ya haɗiye su.

Can a gidansu yaran kuwa, aka ga yara sun jima basu dawo ba, saboda haka sai iyayensu mata suka bisu, sai suma suka haɗu da wannan zakara. Da zakara ya gansu kawai sai ya fara waƙa:

Zakara: Ku-ku-ku ina za ku, tarmanamana
Mata: Neman ‘ya’yanmu za mu tarmanamana
Zakara: Su ‘ya’yan ina za su, tarmanamana
Mata: Ɗiban yakuwa za su, tarmanamana
Zakara: Ɗiban yakuwar mene, tarmanamana
Mata: Ɗiban yakuwar taushe, tarmanamana
Zakara: In yi muku ɗan kiɗa ku ji? Tamagun-tamagun, muƙut sai ya haɗiye matan suma.

Da jama’ar gari suka ga shiru, yara basu dawo ba, haka nan ma iyayensu mata, sai dukkan mutanen garin har da sarkinsu suka fita neman su. Da suka haɗu da wannan zakara suma duk sai ya haɗiye su.

Can sai ga wani mutum shi kaɗai ya fito daga wani garin, yana kan hanyarsa ta tafiya, sai ya haɗu da wannan zakara, da suka haɗu, sai zakara ya yi yunƙurin haɗiye wannan mutumi, bai gama haɗiye shi baki ɗaya ba, sai wannan mutumi ya hango waɗannan jama’a da wannan zakara ya haɗiye, ganin haka dama hannun mutumin nan akwai wuƙa, saboda haka sai ya ƙara dagewa har sai da ya farka cikin wannan zakara ya faɗi matacce, sauran jama’a kuma kowa ya fito ya kama gabansa.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya

 

Share:

YARINYA DA ƘAWAYENTA

Yarinya da Ƙawayenta
Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

Wata ce dai, wata ce dai, za su tafi wasan kalangu wani gari mai suna Dahira da ita da ƙawayenta. Sai ta je gurin ummarta, ta ce da ita ta bata zaninta za su je wasa. Sai ummar tata ta ce ba zan ba ki ba sai kin samo min ‘ya’yan ɓaure. Shike nan sai ta tafi daji, ta je gidindin ɓaure ta ce da shi:

Yarinya: Ɓaure, ɓaure gareka na zo.
Ɓaure: In ba ki me?
Yarinya: Ka ba ni ‘ya’ya.
Ɓaure: Ki kai wa?
Yarinya: In kai wa inna.
Ɓaure: Ta ba ki me?
Yarinya: Ta ban zani na, mu je mu wasa a Dahira.

Da ɓaure ya ji abin da yarinya ta ce, sai shi ma ya ce ba zai bata ba sai ta kawo masa kashin shanu, ta zuba masa taki. Daga nan sai ta tafi garke. Ta je ta samu shanu ta ce da su:

Yarinya: Shanu, shanu gurinku na zo.
Shanu: Mu ba ki me?
Yarinya: Ku ba ni kashi.
Shanu: Ki kai wa wa?
Yarinya: In kai wa ɓaure, ya ba ni ‘ya’ya na kai wa inna, ta ban zani na mu je mu wasa a Dahira.

Sai suma shanu suka ce ba za mu baki ba sai kin samo mana ciyawa mun ci sannan mu ba ki kashi. Daga nan sai ta tafi daji, ta ce:

Yarinya: Kai daji gurinka na zo.
Daji: In ba ki me?
Yarinya: Ka ban ciyawa.
Daji: Ki kai wa wa?
Yarinya: In kai wa shanu su bani kashi, in kai wa ɓaure ya bani ‘ya’ya, in kai wa inna, ta ban zanina mu je mu wasa a Dahira.

Sai daji ya ce to ga ciyawar nan ki ɗebi yadda ki ke so. Sai yarinyar nan ta ɗebi ciyawa, ta kai wa shanu suka ci, suka yi ka shi ta ɗiba, ta kai wa ɓaure, shi ma ya bata ‘ya’ya masu kyau, ta ɗiba ta kai wa ummarta. Da ta kai wa ummarta ta 

Share:

WASU MUTANE HUƊU

Wasu Mutane Huɗu
Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

Akwai wasu mutane huɗu, mai ƙaton ciki, mai siririyar ƙafa, mai ƙafafun itace, da mai ƙaton kai. Wata rana suka tafi shan kanya a daji, kowanensu ya hau bishiyar kanya. Suna cikin shan kanya, sai mai ƙaton kai ya hango mai gona yana zuwa, sai ya ce da sauran, “ga mai gona can yana zuwa”. Sai kowane ɗayansu takai-takai.

A garin sauka, sai mai ƙaton kai ya maƙale. Shi kuma mai ƙaton ciki a garin dariya cikinsa ya fashe. Mai ƙafafuwan itace kuma, a ƙoƙarin dirowa daga bishiya ƙafafuwan suka karye. Shi kuma mai siririyar ƙafa, a ƙoƙarin zuwa gida ya faɗa ramin gyare ƙafar ta maƙale a ciki.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.

Share:

ƁARAWON GWAL

Ɓarawon Gwal
 

gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

Akwai wani mutum, wata rana ba shi da kuɗi, sai ya samu labarin wata mayya kuma tana da gwalagwalai na ado. Sai mutumin nan ya shirya zuwa sata gidan matar nan, sai ya hau dokinsa. To dama yana da karnuka guda uku a gidansa, a cikinsu akwai mai suna Kasau, da kuma mai suna Cinyau, da kuma mai suna Lasau. Sannan kuma yana da mata biyu. Da zai fita, sai ya ɗaure karnunkan nan a gida, kuma ya ce kar a sake su.

Da ya fito daga gida sai ya tafi wajen masu fasa dutse, sai suka ba shi dutse ya saka a jakarsa. Sannan ya wuce wajen masu faskaren itace, suma suka bashi ya saka a jaka, sai kuma ya je wajen masu sai da ƙwai, suma suka ba shi ya saka a jaka. Daga nan sai ya rankaya sai gidan mayyar nan.

Da zuwansa gidan mayyar nan sai ya yi sallama sannan ya ce da ita, shi baƙo ne yana neman gidan da zai riƙa yin aikin wanke-wanke. Da matar nan ta ji haka sai ta ce to ba komai ya zo ya riƙa yi mata wanke-wanken.

Ana nan, ana nan, wata rana da daddare, matar nan ta shiga ɗaki tana barci, sai mutumin nan ya laɓaɓa ya shiga ɗakin da ta ke ajiye gwalagwalai ya ɗebo ya je ya hau dokinsa. Bayan ya hau dokin zai fita, a garin sauri sai dokin nasa ya bugi wani bulo, sai bulon ya ɓalle daga jikin gini, sai ginin ya zube. Ƙarar zubar ginin nan sai ya farkar da mayyar nan. Tana leƙowa sai ta ga mutumin nan da kaya a kan doki. Sai shi kuma ya zaburi dokin nan ya fita da gudu, ita kuma mayyar nan sai ta bishi, yana gudu a kan doki, ita kuma tana bin sa.

Da mutumin nan ya ga alamar mayyar nan za ta kamo shi, sai ya buɗe jakar nan ya fito da dutsen nan ya jefe ta da shi, saura ƙiris ya buge ta, amma ta samu ta tsallake, ta kuma ci gaba da bin sa da gudu. Da ya ga ta tsallake, sai ya sake fitowa da itacen nan ya sake jifanta da shi, shi ma ta samu ta tsallake. Yana gudu tana bin sa. Can da ya ga babu dama sai ya fito da ƙwan nan ya jefe ta da shi, ita kuma ta cafke ƙwan nan ta shanye.

Mutumin nan dai gudu ya ke yi a kan dokin, mayyar nan kuma tana bin sa har sai da ta iso mutumin nan ta kama ƙafar dokin nasa ta cinye.

Da mutumin nan ya ga mayyar nan ta kama ƙafar dokin nan ta cinye, sai ya sauka daga kan dokin ya ci gaba da gudu a ƙasa har sai da ya kai gindin wata bishiya ya kama ya haye kan bishiyar nan. Da ya hau kan bishiyar sai ya kama kiran karnukan nan nasa yana cewa, Kasau, Cinyau, Lasau. Kasau, Cinyau, Lasau. Can sai karnukan nan suka fara haushi.

Da amaryar mutumin nan ta ji karnuka sun fara haushi, sai ta ce da uwargidan, ni fa zan kunce karnukan nan. Sai uwargidan ta ce ita babu ruwanta a ciki.

Can kuma da mayyar nan ta gama cinye dokin nan, sai ta sake biyo mutumin nan. Da mutumin nan ya ga mayyar nan ta kusa zuwa gindin bishiyar da ya ke, sai ya sake kiran karnunkan nan, ya sake cewa da su, Kasau, Cinyau, Lasau. Kasau, Cinyau, Lasau. Sai karnukan nan suka sake yin haushi. Da amarya ta ji haushin karnukan nan sai kawai ta sake su. Tana sakinsu, sai suka fita da gudu, har sai da suka riga mayyar nan zuwa gindin bishiyar nan, suna zuwa, sai mutumin nan ya sake cewa, Kasau, Cinyau, Lasau. Kasau, Cinyau, Lasau. Saboda haka mayyar nan tana zuwa gindin bishiyar nan sai Kasau ya kasheta, shi kuma Cinyau ya cinye ta, Lasau kuma ya lashe sauran jininta da ya zuba a gurin.

Daga nan sai mutumin nan ya sauko daga kan bishiyar nan, ya shiga kasuwa ya sayi nama, ya sayi ƙuli/ƙarago, ya sayi suturu, ya tafi gida. Yana zuwa gida sai ya ce da matan nan nasa, wacece ta kunce karnukan nan? Sai uwargida ta ce amaryarka ce ta kunce su, sai ya ce to kowacce ta tafi ɗakinta. Sai ya fito da ƙuli/ƙaragon nan ya baiwa uwargida, ita kuma ta karɓa ta shiga ɗaki tana ci. Ita kuma amarya ta shige nata ɗakin tana cewa ba ita ta kunce karnukan nan ba, sai ya bita ɗakinta, ya fito da suturar nan ya bata ta saka. Da uwargida ta leƙo ta ga kayayyakin nan a jikin amarya, sai ta ce, oho! Dama abin haka ne? Sai ta ce to ni na tafi gidanmu.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.

 

Share:

GIZO DA ƁAURE

Gizo da Ɓaure
Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

A wani gari an yi wani attajirin sarki, yana da wata babbar gonar ɓaure. Wata rana wannan sarki yana zaune a fadarsa tare da fadawa ana fadanci, sai ya ce da su, “Ina so a samo min wani mutumin da zai tsinken mini ɓaurena kuma ba tare da ya sha ko ɗaya ba. Idan ya gama zan aurar masa da ‘yata tare da gara mai yawa a matsayin ladan aikinsa”. Da fadawa suka ji haka sai suka saka sanƙira (magawata) ya yi shela (yekuwa) a gari cewa sarki yana neman jama’ar gari a fada.

Da magawata ya yi shela jama'ar gari suka ji sai dukkansu suka taru a fada, da Gizo ya hango wannan taron mutane sai shima ya je ya samu guri ya zauna. Bayan jama’a sun taru sai sarki ya sanar da su dalilin wannan taro. Da kowa ya ji wannan buƙata ta sarki sai aka yi shiru kowa ya kasa magana. Can sai Gizo ya ce da sarki shi zai iya.

Daga nan sai sarki ya sallami jama’a, ya kuma saka fadawa suka raka Gizo zuwa gonar ɓaure. Gizo ya je ya taras da ɓaure ya nuna likif yana ƙanshi. Gizo ya hau tsinkar ɓaure kuma yana sha. Dama yana da tsinken sakatar haƙori da kuma madubi a jakarsa. Idan ya yi aiki sai ya dakata ya sha ɓauren nan sannan ya fito da madubi ya sakace haƙori ya kurkure bakinsa. Idan jama’a suka zo wucewa sai Gizo ya tsiri tofadda yau (yawu ko miyau). Haka Gizo ya yi ta aiki, ashe bai sani ba wata kurciya tana kallonsa.

Da Gizo ya gama aiki sai ya je ya sanar da sarki cewa ya gama. Sarki ya sake haɗa Gizo da dogarawa su kuma ya basu buhuna su je su ɗebo ɓaure. Da suka je gona suna ɗura ɓaure a buhu shi kuma Gizo yana ta tsirtar da yau (yawu ko miyau). Da dogarawa suka ga Gizo yana ta tsirtar da yau sai suka tambaye shi Gizo me yasa ka ke ta tsirtar da yau? Sai ya amsa da cewa ai warin ɓauren nan ne baya so.

Da dogarawa suka koma ga sarki sai suka gaya masa cewa lallai Gizo ya yi aiki mai kyau kuma bai ci ɓauren nan ba, saboda sun ga cewa a lokacin da suke ɗura ɓauren a buhu shi Gizo warin ma damunsa yake yi.

Daga nan sai sarki ya ce da Gizo ya je ya gyara gida. Bayan ya gyara gida aka ɗaura musu aure da ‘yar sarki. Aka haɗa masa goma-ta-arziƙi a gararsa. Aka haɗa amarya da tsofaffi ‘yan ɗaukar gara suka kama hanyar tafiya gidan Gizo.

Bayan sun kai amarya gidan Gizo sun ɗan zauna suna hutawa kafin su watse, sai kurciyar nan ta zo ta hau kan danga tana waƙa tana cewa:

Kai Gizo, kai Gizo,
A can ka ci ɓaurenka,
Har ka kurkure bakinka,
Har ka manto jallonka.

Kurciyar nan ta yi ta maimaita wannan waƙar har sai da matan nan suka ji. Da suka ji sai suka ce kai kutsaya ku ji waƙar da kurciyar can take yi. Da Gizo ya ji haka sai ya ce kai kurabu da ita shirmenta take yi. Sai mata suka ce wane irin a rabu da ita kuma, sai suka yi shiru suka ji abin da kurciya take faɗa tsaf! Da suka ji sai suka ce da Gizo, dama ka ci ɓauren ka yi ƙarya ka ce baka ci ba. Daga nan sai suka kwashe gararsu da amaryarsu suka koma da ita gida.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.

 

Share:

MARAYA DA MATAR UBANSA

Maraya da Matar Ubansa
Gata nan gata nan ku. Ta zo mu ji ta.

Akwai wani yaro sunansa Janiya Jannati. Shi Janiya maraya ne, babarsa ta mutu, yana zaune tare da matar ubansa. Ita kuma wannan mata bata son wannan yaro. To dama babarsu tana da dukiya, kuma an raba musu gado. Daga cikin abubuwan da ya gada akwai wata saniya mai magana.

Wannan mata kullum tana ta haƙon yadda za ta kashe yaron nan. Ashe duk abubuwan da take ƙullawa, saniyar nan ta sane da ita. Wata rana sai matar nan ta shirya cewa za ta zuba magani a cikin abinci ta baiwa yaron nan ya ci ya mutu. Sai saniyar nan ta ce da shi:

Janiya, Janiya, Janiya Jannati.
Za a baka tuwo da magani, Janiya Jannati.
Tuwon nan idan an baka, Janiya Jannati.
Kar ka ci, ka zo turkena, Janiya Jannati.
Ka tona rami ka zuba, Janiya Jannati.
Ka bar ɗan saura, Janiya Jannati.
ka mayar ka ce ka ƙoshi, Janiya Jannati.

Shike nan, sai aka baiwa yaron nan tuwo da magani a ciki. Sai ya tafi turken saniyar nan, ya haƙa rami, ya binne. Ya bar ragowa, ya mayar da akushin ya ce ya ƙoshi. Matar nan ta kashe kunne tana sauraron mutuwar yaro, amma shiru ka ke ji kamar an shuka dusa.

Ana nan, ana nan, sai wata rana ta sake dabara, ta ce za ta zuba magani a kunu, ta bashi. Da yaron nan ya je gurin saniyar nan sai ta ce da shi:

Janiya, Janiya, Janiya Jannati.
Za a baka kunu da magani, Janiya Jannati.
Amma idan an baka, Janiya Jannati.
Kar ka sha kunun ka zo turkena, Janiya Jannati.
Ka haƙa rami ka zuba, Janiya Jannati.
Amma ka bar ɗan saura, Janiya, Jannati.
Ka mayar da akushin ka ce ka ƙoshi, Janiya, Jannati.

Da aka baiwa yaron nan kunu, sai ya tafi turken saniyar nan ya haƙa rami, ya juye a ciki, ya bar ragowa ya mayar ya ce ya ƙoshi. Matar nan ta karɓi akushin nan tana ta murna. Ta saurara cikin dare ko za ta ji cikin yaro ya murɗe ya mutu. Shiru, bata ji komai ba. Sai abin ya ɗaure mata kai.

Ana nan, sai ta sake dabara ta ce, bari ta kai shi ɗakinta ta ƙona shi cikin dare. Da yaron nan ya je baiwa saniyar nan abinci, sai ta ce da shi:

Janiya, Janiya, Janiya Jannati.
Yau za a ƙona ka a ɗaki, Janiya Jannati.
Amma idan aka kai ka ɗaki, Janiya Jannati.
Kar ka yi barci, Janiya Jannati.
Idan matar ubanka ta fita, Janiya Jannati.
Ka cire rigar ɗanta ka saka, Janiya Jannati.
Ka saka masa taka, Janiya Jannati.
Ka tura shi makwancinka, Janiya Jannati.
Kai kuma ka koma nasa ka kwanta, Janiya Jannati.

Da dare ya yi, sai matar uban nasa ta ce da shi, Janiyana, na ga ɗakinka sauro yana damunka, yau ka zo ku kwana a ɗakina tare da ɗan’uwanka. Sai Janiya ya ce da ita to, zan zo.

Da dare ya yi, sai Janiya ya tafi ɗakinta, ya kwanta a kan shimfiɗar da ta yi masa. Sai ya yi likimo, kamar yana barci, can tsakar dare, sai ya gan ta, ta taso saɗaf, saɗaf, ta fice waje. Kafin ta dawo sai ya ta shi a hankali ya cire kayan jikinsa ya saka wa ɗanta, shi kuma ya saka na ɗan nata. Sannan ya ɗauke shi a hankali ya kai shi makwancinsa, shi kuma ya koma makwancin ɗan nata ya kwanta. Yana gamawa sai ga matar nan ta shigo da wuta. Tana zuwa, ba ta yi wata-wata ba kawai sai ta zuba wa ɗan nan nata ba ta san shi ne ba. Da ɗan ya ji zafi, sai ya riƙa sowa yana cewa, iya ni ne fa, ita kuma tana cewa, mutu dan ubanka, yau jaraba ta ƙare. Yaron nan ya ƙone ƙurmus. Da gari ya waye, sai ta ga ashe ɗanta ta ƙona. Sai ta haɗiyi zuciya ta mutu.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.

 

Share:

TATSUNIYA


 

GATA NAN GATA NAN KU... Gizo ne dai, gizo ne dai yakasance rago malalaci baya aikin fari balle na baki, kullum sai dai yaci ya sha ya kwanta yai ta sharar barci. Abincin da suke ci ma matarsa koki ce ke siyo musu a kasuwa in takai tallan daddawa. To wannan lalaci na gizo yana damun koki tun tanahakuri dashi har ya fara kureta, kwanci tashi wata rana an wayi gari ana ta faman lafta ruwansama kamar da bakin kwarya, bayan an gama ruwa kowane manomi ya dauki kayan aiki ya tafigona amma gizo yana can a kwance abinsa yanata sharar barci.koki tazo ta ganshi sai haushi ya kasheta sai ta debo ruwa mai sanyi ta kwara masa; haba kan kace me ai tuni gizo ya tashi firgigi yana makyarkyata don tsoro. sai koki tace "tashi ka tafi gona shege kawai malalaci, kai dai wallahi kaji kunya" dakyar dakyar dai koki ta takura masa ya tashi, sai yace to dakata "zani gona amma da sharadi, a gaskiya sai kin soya min gyada (amaro) ina aiki ina ci". sai koki tace bakomai sai ta tashi ta soya mashi ta bashi da ruwa mai sanyia gora.Koda gizo ya isa gona sai yaje ya tayo igiyar kalgo yaje gindin wata katuwar bishiya mai sanyi ya daura lilo ya hau yana lilo yana rera waka yana kuma watsa soyayyar gyada a baki abinsa, haka yayi tayi har rana tayi sai ya sauko daga lilon sai ya share wuri a tushen bishiyar yakwanta yana ta sharar barci abinsa har bayan la'asar sannan ya dawo gida yana nishi wai shi sarkin noma. koki na ganinsa ta rugo da gudu tatarbeshi tana masa sannu da zuwa sannan ta bashi ruwa da abinci ya kara labtawa, sannan yazauna ya fara sharawa koki karya, har yana ce mata wai shi tunda yake bai taba noma irin na yau ba, ai ko sarkin noma bazai iya yin aikin daya maka a yau ba, koda koki taji haka sai ta buga guda tace "ahayye ayyururui lallai bana duk garin nan ba wanda zai fimu dibar hatsi, sannan taci gaba da zugashi.Haka dai kullum gizo yakeyi ita kuwa koki bata sani ba tana tsammanin abinda yake fada mata gaskiya ne.kwanci tashi har hatsin mutane ya fara nuna, har wasu sun fara kawo hatsi gida amma su gizo ba labari abin har ya fara damun koki.Wata rana gizo ya tafi gona kamar yadda ya saba sai yaga wani mutum a gona ya lafta huda,saboda tsiya irin ta gizo ko sannu bai mishi ba sai da ya bari mutumin ya tashi sai yaje ya tugo tafasa da yawa yazo duk ya dasasu a gonar mutumin nan. Koda ya dawo gida sai yace ma koki ta hau saman bishiya ta hango gonar gyadarsa, sai kuwa koki ta hau saman bishiyar dake tsakiyar gidansu sai yace mata "kinga gonata caaan" wato ya nuna mata gonar daya dasa tafasa, ai kuwa koki na ganin haka sai murna ta kasheta tana tsammanin cewa gonar gizo ce. Saboda murna koki har tana fadowa daga saman bishiyar, amma ko damuwa batayi ba, tana ta tsalle abinta tana cewa lallai bana zamu ci gyada wohoho.Kwanci tashi har manoma sun fara tsinko gyadarsu amma gizo wayam ba labari, in koki tace mishi suje gona gewaya su gani ko gyadar tayi sai ya rika cemata bata kosa ba tukun. Tofa da gizo dai yaga asirinsa zai tonu sai wata rana ya tafi gonar sarki sata, ya tugo gyada mai tarin yawa ya kaiwa koki yace wai daga gonarsa ya ciro. Wata rana yayan sarki sun zo gewaya sai sukaga anyi musu barna a gona ashe dama a lokacin gizo yana cikin gonar ya boye acikin wani kuttu basu ganshi ba. A tsiya irin ta gizo sai ya raya a ransa cewa bari ya basu tsoro sai ya shake murya ya fara rera wata waka yana cewa"Kuttu, kuttu, kuttu banban kuttu, kuttu maci yayayen sarki har sarkinma kansa"'haba koda yayan sarki sukaji wannan abu sai suka firgita sukace kafa me naci ban baki ba, suka ruga gida suka fadi gaban sarki suka bashi labarin abinda suka jiyo a gona.Sai sarki ya umurci wazirinsa da fadawa suje sugano ko menene a gonar. Ai kuwa nan da nan fadawa suka shirya suka hau dawaki aka garzaya sai gonar sarki, suna iso wa gizo ya gansu sai ya kara boyewa dakyau sai ya shake murya ya fara rera musu waka kamar haka:"Kuttu, kuttu, kuttu banban kuttu, kuttu maci fadawan sarki, kuttu maci wazirin sarki har sarkinma kansa"'haba koda su waziri sukaji wannan abu sai suka firgice suma kota kan dawakinsu ma basu biyo ba, ba abinda kake gani sai manyan riguna sun cika hanya ana shekar gudu, har rawanin waziri yana faduwa ai waziri ko kula rawanin bai yi ba. Sukaje gaban sarki suka fadi suna haki. Sarki ya hararesu yace yau ga kartin banza kawai wannan abin kunya har ina ace 
Share:

AUREN BAREWA DA MUTUM


 

Auren Barewa da Mutum

Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

Akwai wata barewa da ta rikiɗe da zama mace mai kyawun gaske; son-kowa ƙin-wanda ya rasa. Wata rana sai ta ɗauki akushinta (kwatashi) ta kai shi tsakiyar karofi ta ajiye. Sai ta ce da mutanen da ke wurin, “duk wanda ya ɗauki tsakuwa, ya jefa ta daga nan (ta tsaya a daidai wani guri), ta buɗe wannan akushi, to shi zai zama mijina”.

Da mutane suka ji haka, sai suka yi ta jefa tsakuwa. Wannan ya jefa bai buɗe ba, wancan ya jefa bai buɗe, sai can daga ƙarshe aka samu wani ya yi sa’a ya jefa, akushin ya buɗe.

Sai wannan barewa ta ce, “yawwa, yanzu na samu miji”. Saboda haka sai suka rankaya tare da wannan mutum zuwa garinsu dan a ɗaura musu aure da wannan mutum. Bayan an ɗaura aure, sai ta tare a gidan mijinta.

Duk sanda ranar girkinta ta zagayo, akan tura ta gonad an ciro kuvewar miya. Idan ta je gonar sai ta yi birgima a ƙasa, ta rikiɗe ta koma barewa, ta kira ‘yan’uwanta ta hanyar rera waƙa kamar haka:

Cinkalkalkal, cinkalin kalaya
Turmin ‘yankale ya yi furen ceɗiya
Tudu na korar tudu da ƙaho
Ban da kwatsa-kwatsa
Ban da ƙanana.

Idan ‘yan’uwanta suka ji haka sai su fito, su zo su taru, su cinye kuɓewar da take gonar. Sai su yi bankwana da ita su koma gida. Ita kuma sai ta yi birgima ta koma mutum, ta ɗauki zanenta ta ɗaura, ta koma gida tana cewa, “ai dama da gangan aka tura ni ciro kuvewar nan, gashi nan na je ban samo komai ba”.

Da mijin nata ya ga haka, wata rana sai ya bi bayanta bata sani ba. Da isarsa gona sai yaga tana birgima. Bayan ta gama birgima sai ya ga ta koma barewa. Daga nan kuma sai ya ji tana waƙa, bayan gama waƙartata, sai ya ga bareyi sun fito suna cin kuɓewar da take gonar. Shi kuma da ya ga haka sai ya fasa su. A lokacin da yake fasa su, ya ga matar tasa ita ma ta gan shi. Daga nan sai ya dawo gida.

Da barewar nan ta ga abin da ya faru, sai ta yi wuf, ta yi birgima ta koma mutum ta ɗebi kuɓewa ta nufi gidan mijin nata. Da isar ta gida sai mijin ya ce:

Miji: “Wacece wannan?”
Barewa: “ni ce”.
Miji: “ina za ki?”
Barewa: “ɗaki”.
Miji: “a’a, koma daji”.
Barewa: “na ƙi”.

Daga nan sai ya ɗauki sanda ya bita da gudu, ya kora ta daji. Tun daga wannan lokaci bata sake koma masa gida ba.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.

 
Share:

GIZO DA BOTORAMI


Gizo da Botorami
Ga ta nan ga ta nan ku.

Ta zo mu ji ta.

 Gizo ne da Botorami. Sai ran nan Botorami zai yi tafiya, sai ya ce, “To Gizo, tsaya - ga amfanin gonata nan, zan yi tafiya ƙauye. Ga shin nan amana duk abin da ya yi ka kwashe mini ka kai mini gari”. Sai Gizo ya ce, To, “sai ka dawo”, daman da Botorami sai ya tafi sai ya ce, Shi ke nan, sai Gizo ya noma gonar sa amfanin gonar yayi kyau. Shi kuma Botorami hatsinsa bai yi kyau ba ya fara lalacewa. Sai Gizo ya yanke masa ya je ya ajiye. Wadanda suka danyi kyau ya saka su a saman damin marasa kyau kuma ya saka a kasa. Haka ya samu audugarsa ma duk bat yi ba, sai ya sa ta. Wacce ta isa ya yayyaɗa a sama ya ɗaure. Gero haka, dawa haka, maiwa haka, duk dai. Shi ke nan sai ya kai rumbu sai ya ajiye. Gizo kuma nasa ya yi shar-shar, ya yi kore shar abin sha’awa. Sai ya kai rumbu sai ya ajiye. Sai ran nan Botorami ya dawo. Sai ya ce da Gizo. Au! Har ka gyara kayan amfanin gonar. Sai ya ce, eh. Sai ya ce, To shi ke nan. Sai Botorami sai ya je ya ga ta sama mai kyau. Sai ya ce, ìTo na ga amfanin gona, na gode, na gode, madalla, madalla. Sai ya ce, ìTo shi ke nan.íí Sai ran ran gidan Botorami zaía yi girki. Da ya je ya buɗe dawa sai ya ga duk ba ta yi ba, ta sama ce ta yi kyau. Ya buɗe gero haka, ya buɗe dawa haka, ya buɗe gyaɗa haka. Sai ran sa ya baci bai ji dadi ba.         

  Sai ya ɗebe mai kyan, marar kyan sai ya bar ta a rumbu sai ya bunka wa runbun wuta. Shi ke nan sai ya je ya fara kuka, ya ce, Lailaha illallahu, Gizo ba ka san abin da ya same ni ba.

 Sai ya ce, Ban sani ba. Ya ce, To duk kayan nan nawa mai kyau duk sun ƙone, na yi gobara. Sai ya ce, To shi ke nan, Allah ya kiyaye, Allah ya tsayar nan. Da safiya ta yi sai ya ce, To, a je a duba amfanin daya kone. Sai ya ce, To shi ke nan. Dama kuma Botorami ya zuba kuɗi a cikin rumbun daya kone. A tona, sai kuɗi. A tona, sai kuɗi, a tona, sai kuɗi. Sai Gizo ma sai ya ce, To ni ma bara na ƙone nawa ko ni ma zan samu kuɗi. Duk sai ya ƙone nasa mai kyan, da ya ƙone nasa mai kyan, sai ya je ya sa wa Botorami kuka. Ya ce, Ni ma na yi irin taka. Sai Botorami ya ce, To Allah ya kiyaye. Ya ce, To sai a je a duba amfanin gona. Shi ke nan, aka je aka dudduba duk ba a samu kuɗi ba sai toka. Sai Gizo ya sa kuka.

Kurunkus kan dan bera  

 
Share:

BANZA TA KORI WOFI


Banza Ta Kori Wofi

Wani saurayi ne da gidansu ke kusa da makabarta, kullum idan ya hawo mota ko babur baya biya, ana zuwa daidai makabartar nan sai ya ce a sauke shi, ana sauke shi sai ya nuna ai shima mataccene, fatalwa ya yi ya fito yawon shakatawa, kawai sai ya shige makabartar.

Ana cikin haka ne wata rana ya hawo babur din wani dan achaba me shegen naci, bayan sun zo daidai makabartar sai saurayin nan yace, “Tsaya na sauka anan” yana sauka sai yai kokarin shiga makabarta kamar yadda ya saba, amma sai Dan achaba ya rike shi ya ce ya ba shi kudinsa, to anan ne saurayin nan ya ce da shi shi fa fatalw ne ba me rai bane kuma gida ya kawoshi (wato makabarta).

Nan take Dan achaba ya ce to su shiga ya ba shi kudinsa. Haka kuwa aka yi, suna shiga abokin namu ya je kan wani kabari yace, “Danlami bani naira tamanin (#80) na ba wa wannan Dan achaban kudinsa”, ai kafin ya gama rufe baki kawai sai suka ga wani hannu ya bullo da naira dari (#100) yace, “Karbi wannan ka ba shi, ya ba mu chanji, ni ma ragowar kudina ke nan.”

Ai da Saurayin nan da Dan achaba sai kowa ya cika rigarsa da iska yayi takansa. Ashe wani Mahaukaci ne yazo ya kwanta a ciki, banza ta kori wofi ke nan.

A ganinku, tsakanin saurayin da Dan achaba wa zai fi wani gudu?
Share:

ALHAJI DA HAJIYA


Alhaji da Hajiya
Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

A wani gida a wani gari, akwai alhaji da hajiya a gidan, kuma akwai wani ɓarawo yana da sunaye da yawa, sai ya je gurin mai gadin gidan. Da mai gadi ya gan shi sai ya tambaye shi sunansa, sai ɓarawo ya ce sunansa salati, sai mai gadi ya tambaye shi gurin wanda ya zo, sai ya ce gurin alhaji ya zo, sai ya ce da shi ya wuce.

Da ɓarawo ya shiga gurin alhaji sai alhaji ya tambaye shi gurin wanda ya zo, sai ya ce gurin hajiya ya zo. Sai alhaji ya tambaye shi sunansa, sai ɓarawo ya ce sunansa Alanta, sai alhaji ya ce da shi ya wuce. Daga nan kuma sai ya wuce gurin hajiya. Da ya isa gurin hajiya sai ta tambaye shi sunansa, sai ya ce da ita sunansa dambu, sai ta ce da shi gurin wa ka zo? Sai ya ce da ita gurinki na zo, sai ta ce da shi “me ka zo yi”, sai ya ce “sarƙar wuyanki zan sace”. Sai ya shaƙe mata wuya zai ƙwace sarƙar, sai ita kuma ta fara kururuwa tana cewa, “alhaji dambu ya shaƙe ni”. Sai alhaji ya ce da ita “kora da ruwa”, har sai da ɓarawon nan ya cire sarƙar gwal ɗin da ke wuyan hajiya ya fita.

Bayan fitarsa sai alhaji ya shiga gurin hajiya, sai ta gaya masa abin da ya faru. Sai alhaji ya fito waje da sauri yana kururuwa yana cewa “Mai gadi kama Alanta”. Sai shi kuma mai gadi ya fara taka rawar alanta. Da alhaji ya iso wajen mai gadi ya gaya masa abin da ya faru, sai mai gadi ya fito waje da gudu yana kururuwa yana cewa “Jama’a ku kama salati”, sai mutanen gari suka fara salati.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya
Share:

JATAU DA MUTUWA


JATAU DA MUTUWA
Wai wata rana Mutuwa ta zo wa Jatau tace masa lokacinka yayi, sai Jatau yace gashi kuwa ban shirya ba, Mutuwa tace ko baka shirya ba lallai yau tafiya zaka yi, don sunanka ne na farko a saman takardata, jatau yayi rarrashin duniya akan mutuwa ta kyaleshi mutuwa taki.

Da ya fahimci mutuwar ba zata kyaleshi ba sai dabara ta fado masa sai yace wa mutuwa to me zai hana ki bari in dan kawo maki abinci ki ci kafin mu tafi? Mutuwa ta zauna Jatau ya tafi kawo mata abinci.

Da yaje wurin dauko abincin sai yasa maganin bacci cikin abincin ya kawo wa mutuwa, da mutuwa ta ci abincin sai ta kama bacci, da jatau yaga tayi bacci sai ya dauko takardar da sunayen mutane suke sai ya goge sunansa daga saman takardar ya rubuta a kasan takardar.

Da mutuwa ta farka daga bacci sai tace wa jatau saboda jin dadin karramawarda kayi mini da kuma dadin abincinka da naji har nayi bacci, ba zan fara sunayen mutane daga saman takardar ba zan faro daga kasan takardar. Jin haka sai Jatau ya fadi sumamme.

Darasi

Don haka yan uwa kun ga dai ko a cikin tatsuniya babu mai iya canja lokacin mutuwarsa, idan lokaci ya yi to dole ne a amsa kira, ko ka shirya ko ba ka shirya ba. Don haka ko da yaushe mu zama cikin shiri kada mutuwa ta riske mu ba mu shirya ba.

Allah ya sa mu cika da imani
Share:

HANKAKA DA KURTATTAKI


 
Hankaka Da Kurtattaki
Wata rana kurtattaki na koto a gonar wani bakauye, suna tone shukar da ya yi suna cinyewa, sai ga hankaka ya zo zai wuce. Ya ce musu, “Na hore ku da ku tone abin da manomin nan ke shukawa duka ku cinye.”

Sai suka tambaye shi me yake shukawa. Hankaka ya amsa musu, “Irin rama.”

Kurtattaki suka kada fiffike suna yi wa hankaka dariya, “Me za mu yi da irin rama ga dawa da gero.”

Kwanci tashi rama ta fito har ta girma. Manomi ya cire ta ya kware bawon ya yi zare. Da zaren rama ya tufka raga wadda ya kafa tarko cikin gonarsa, kurtattakin nan duka suka fada cikin tarkon. Suna cikin kici-kicin yadda za su yi su kubuta sai ga hankaka. Ya dube su ya ce, “Ashe ban gaya muku ku tone irin ramar nan ba tun kafin ya fito? Ga abin da nake yi muku gudu nan!”

Manomi ya kama kurtattaki ya kashe, da ma sun addabe shi da barna. Hankaka ya wuce yana cewa, “KU KAWAR DA MUGUN IRI, KO YA GIRMA YA KAWAR DA KU!”

 
Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form