Showing posts with label Ilimin Addinin Musulunci (Islamic Studies). Show all posts
Showing posts with label Ilimin Addinin Musulunci (Islamic Studies). Show all posts

Tuesday, 12 March 2019

ALLAAH YA SANYA TSAYAR DA ADALCI A BAYAN ƘASA...

Allah Ya Sanya Tsayar Da Adalci A Bayan Kasa Ya Zama Sharadin Samun Zaman Lafiya Da Cigaba Mai Dorewa!

Daga Imam Murtadha Gusau

Talata, 12 Mayu, 2019

Bismillahir Rahmanir Rahim

Lallai dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna yabon sa, muna neman taimakon sa, kuma muna neman gafararsa. Muna neman tsarin Allah da kariyarsa daga sharrin munanan ayyukkanmu. Duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, kuma duk wanda Allah ya batar babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa lallai babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad, bawan sa ne kuma Manzon sa ne. 

Salati da sallamawa da tsira su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa da matansa da duk wanda yayi imani da shi kuma yayi aikin kwarai har zuwa ranar tashin kiyama.

Bayan haka:

Ya ku bayin Allah! Ku sani, lallai Allah Ya umarce mu da tsayar da adalci a bayan kasa, kuma ya sanar da mu cewa, da adalci ne sama da kasa suka tsayu. Kuma shine ginshiki da tushen samun zaman lafiya da cigaba masu dorewa a cikin al'ummah. Sannan nagartattun malamai, salihan bayin Allah, irin su Shaikhul Islamu Ibn Taimiyya da Sheikh Usman Dan Fodio da Malam Abdullahin Gwandu sun shaida muna cewa:

"Allah yana taimakon daular da ta tsayar da adalci koda kafira ce, a yayin da Allah yake durkusar da daular da take zalunci koda Musulmi ke shugabancin ta."

Ya ku 'yan uwana masu daraja! Darasin mu na yau yana bayani ne akan muhimmancin adalci, wanda a yau mu al'ummar Musulmi yake neman yayi karanci a tsakanin mu.

Allah Madaukaki Ya umurci Musulmi da su tsai da adalci ta kowane hali, inda Yace: 

“Ya ku wadanda suka yi imani! Ku kasance masu tsayin daka domin Allah, masu shaida da adalci. Kuma kada kiyayya da wadansu mutane ta dauke ku akan ba zaku yi adalci ba. Kuyi adalci shine mafi kusa da takawa.”

Kuma Allah Yace: 

“Kuma idan kun fadi magana to kuyi adalci, kuma koda ya kasance ma’abaucin zumunta ne….”

Kuma Allah Ya sake cewa:

“Lallai Allah Yana umurninku da adalci da kuma kyautatawa…”

Kuma Allah Yace:

"Hakika mun aiko Manzannin mu da hujjoji bayyanannu, kuma mun saukar masu da littafi da ma'auni (na tsayar da adalci) domin mutane su tsayar da adalci tsakaninsu..."

Kuma Allah ya fada a Hadisil Qudusi cewa:

"Na haramta zalunci ga kaina, kuma na sanya shi ya zama haramun a tsakanin ku, saboda haka kada ku zalunci junanku."

Ya ku Jama'a! Adalci shine, bai wa kowa hakkinsa da Shari'a ta tabbatar masa, ba tare da nuna ko wane irin banbanci ba. Kuma duk inda ake tsayar da adalci, to lallai zaka samu zaman lafiya, son juna, walwala, cigaba da jin dadi a cikin al'ummah da tsakankanin jama'ah sun yawaita. A Musulunci, tsayar da adalci yana daga cikin manyan kyawawan dabi'u. Wannan ya nuna kenan duk inda Musulmi suke, indai har Musulmin gaskiya ne, to zaka same su sun rungumi adalci.

Kuma Alkur'ani Mai girma ya bayyana karara cewa Allah ya umurci mutane da dukkan al'ummomi masu neman zaman lafiya da cigaba, su mu'amalanci juna da kyakkyawar mu'amala, tausayi da tsayar da adalci a duk halin da suka samu kansu a ciki. Kuma kowa yana sane da cewa, Allah yana son adalci, kuma yaki jinin zalunci, kuma baya son azzalumai.

Ya ku bayin Allah! Lallai ku sani, Allah ya wajabta wa dukkanin mutane, suyi kokari wurin ganin cewa an tabbatar da adalci a bayan kasa, domin samun zaman lafiya mai dorewa. Shi yasa Allah ya aiko Annabawa, kuma ya hado su da dokoki, domin su taimakawa mutane wurin tsayar da adalci. Wahayin da suka karba daga Allah ya nuna hanyar da za'a bi a tsayar da adalci a cikin al'ummah. Misali, yiwa talakawa adalci, maza da mata, kai hatta makiyan mu an umurce mu da yi masu adalci.

Wajibi ne Musulmi su hadu, su hada kai domin su dakatar da rashin adalci da zalunci a cikin al'ummah. Wannan aiki ne da Allah ya dora masu. Abune da sam bai dace ba Musulmi su zuba ido, su rungume hannuwansu, suna kallo ana tafka zalunci da rashin adalci ba tare da sun dauki matakin da ya dace wurin tsayar da shi ba.

Ya ku 'yan uwana masu albarka! Kamar yadda kuka sani, aiki da dokokin Allah da shari'arsa wajibi ne a wurin dukkan Musulmi ta ko wane hali. Sannan duk Musulmi yasan da cewa siyasa ta kasu kashi-kashi, akwai siyasar Musulunci sannan akwai wadda ba ta Musulunci ba. Misali, siyasar Dimukradiyya ai ba tamu bace mu Musulmi. Domin a Musulunci muna da tamu siyasa, wato ta Shari'a. Kawai mun samu kan mu cikin wani yanayi ne mu Musulmin Nigeria. Sai aka wayi gari muna yin siyasar Dimukradiyyah a bisa lalura. Wannan tsari na Dimukradiyyah, bakon tsari ne a Musulunci, da muka amince muyi shi, amma a bisa lalura. Kenan ya zama wajibi in dai har muna son zaman lafiya mai dorewa a tsakankaninmu, muyi wannan tsari a bisa dokokin sa da tsarin sa da masu shi suka tsara shi a kai, na ganin cewa duk wanda yaci a bashi, wanda Allah ya ba a bashi, kar ayi wa kowa kwace da nuna fin karfi! Domin matukar aka kaucewa wannan, to lallai zamu jefa kan mu cikin tashin hankali, fitina da rudani. Allah ya kiyaye, amin.

Ya ku bayin Allah! Bari in tambaye mu don Allah, shin yanzu abubuwan da suka gudana a wannan kasa tamu mai albarka Nigeria, na zaben da aka gudanar na Gwamnonin jihohi, shin akwai niyyar tabbatarwa da wasu adalci kuwa? Amsa ita ce: ga alamu, a'a.

Kuma shin me yasa ne dukkanin jihohin da akace zabe bai kammala ba, jihohi ne da ake ganin jam'iyyar adawa ta PDP ta ke kan gaba? Shin me ake shirin yi anan? Shin ana son a murde masu ne? Shin ana da niyyar tabbatar da adalci a wannan al'amari? Amsa dai ita ce: bamu ga alamun hakan ba!

To wallahi, muna kira da babbar murya, kuji tsoron Allah, kar ku jefa mu cikin rikici da tashin hankali! Don Allah duk wanda Allah ya ba mulki ku bashi, kar kuce zaku murde, ku hana masa. Kuyi wa kowa adalci. Wannan shi zai sa mu samu zaman lafiya da cigaba mai dorewa.

Ina mai girma Shugaban kasar mu Muhammadu Buhari? Kar kayi shiru akan wannan al'amari, kasa baki don Allah, ka nuna masu duk wanda Allah ya bai wa a bashi. Ka tuna fa, kirarin ka shine MAI GASKIYA. Kar ka bari wasu miyagu su bata maka tafiyar ka. Yi kokari yadda ka fara lafiya ka gama lafiya! Kar ka yarda a danne hakkin wasu. Ka sani, Allah yana kallon ka, sannan duniya tana kallon ka!

Ina kwamitin zaman lafiya na su mai girma tsohon shugaban kasa AbdulSalam Abubakar, su Mai Alfarmah Sultan, su Reverend Matthew Hasan Kuka, su John Onaiyekan? Ya kamata ku sa baki a cikin wannan al'amari, ku tabbatar da cewa duk wanda yaci zabe an bashi, domin tabbatar da samun zaman lafiya a kasar mu mai albarka, Nigeria.

Ina Sarakunan mu suke? Kune fa iyayen wannan al'ummah! Ya zama wajibi ku bada gudummawar ku wurin ganin an kaucewa tashin hankali. Duk wanda Allah yasa yaci zabe a bashi hakkinsa.

Ina Malaman mu na Musulunci? Shin kun manta da umurnin Allah na tsayar da adalci?

Ina Fastoci suke? Shin ina zancen tabbatar da adalci da kuke karantawa a littafin ku?

Duniya fa tana kallon abunda yake faruwa a Nigeria! Kuma dukkanin mu muna sane da illar da rashin adalci yake haifar wa mara dadi. Don Allah mu hadu muyi wani abu akai.

Irin abun da muke gani, da abubuwan da suke faruwa, yanzu dai kam babu wata Dimukradiyyah a Nigeria. Misali:

1. A Jihar Kano an ce zabe bai kammala ba, saboda jam'iyyar PDP ta adawa ce ke kan gaba!

2. A Jihar Sokoto an ce zabe bai kammala ba, anan ma PDP ce ke kan gaba!

3. A Jihar Plateau ma an ce zabe bai kammala ba, nan ma PDP ce ke kan gaba!

4. A Jihar Adamawa an ce zabe bai kammala ba, nan ma PDP ce ke kan gaba da kuri'u mafiya rinjaye!

5. A Jihar Bauchi an ce zabe bai kammala ba, nan ma don sun ga PDP ce ke kan gaba!

6. A Jihar Benue ma haka, sun ce zabe bai kammala ba, saboda Jihar PDP ce!

7. Haka abun yake a Jihar Rivers, an dakatar da duk wasu harkokin zabe, saboda Jihar PDP ce!

Amma saurara kaji wani abun mamaki, ikon Allah:

1. A Jihar Kaduna an ce zabe ya kammala, saboda APC ce tayi nasara!

2. A Jihar Niger zabe ya kammala, saboda APC tayi nasara!

3. A Jihar Kebbi, zabe ya kammala, saboda APC ce tayi nasara!

4. A Jihar Katsina, nan ma zabe ya kammala, saboda APC ce ta lashe zaben!

5. A Jihar Gombe, zabe ya kammala, saboda APC tayi nasara!

6. A Jihar Jigawa, zabe ya kammala, nan ma saboda APC ce ta ci!

7. A Jihar Nasarawa, zabe ya kammala, saboda APC ce tayi nasara!

8. A Jihar Kwara, zabe ya kammala, saboda APC ce tayi nasara!

9. A Jihar Borno, anyi kammalallen zabe, domin APC ce ta cinye!

10. A Jihar Yobe, nan ma babu matsala, domin ta APC ce!

11. A Jiha ta Zamfara ma anyi kammalallen zabe, saboda jam'iyya mai mulki ta APC ta ci zabe!

Ya ku 'yan uwana masu daraja! Yanzu don Allah zaku gaya mani cewa, wannan abun gaskiya aka bi wurin tabbatar da shi? To in dai har ku kun yarda, ni dai kam wallahi, sam ban amince ba.

Maganar gaskiya wannan sharri ne da magudi da rashin adalci irin na 'yan siyasa. Kuma wadannan 'yan siyasar da ke kokarin tafka rashin adalci, wallahi, basa son zaman lafiyar Al'ummar su, musamman ma arewa. Suna son su jefa mu cikin wani sabon tashin hankali da rikici. Allah ya tsare, ya kiyaye, kuma Allah ya mayar masu da aniyar su, amin.

Don Allah me yasa ne duk inda jam'iyyar APC ta lashe zabe suka sanar da cinye zaben, amma kuma duk inda jam'iyyar PDP ta ke kan gaba suka ce wai ba'a kammala zabe ba?

Kuma wai a haka ne za'a gaya muna wai ana yin Dimukradiyyah. Wace Dimukradiyyar kenan? Dimukradiyyah ko dai yaudara?

Wallahi bai kamata ku rinka wahalar da jama'ah ba, matukar kun san kama karya da rashin adalci zaku yi. Yanzu don Allah abunda ya faru a Kano ba abun kunya bane? Ace irin wadannan mutane sune suke jagorantar al'ummah Musulma irin Kano?

Muna Addu'a Allah ya ceto yankin mu na arewa da Nigeria baki daya, daga sharrin da wadannan mutane ke kokarin jefa su, amin.

Ta yaya zaku ce kuyi amfani da karfi ku kwace mulki daga hannun wadanda Allah ya bai wa, sannan kuce kuna son zaman lafiya? Zaman lafiyar naku ne? Ba Allah yake da shi ba? Sannan ya baku idan kun tsayar da adalci?

Amma babu komai, ku da Allah, da kuma jama'ar Nigeria masu kokarin ganin an tabbatar da adalci ga kowa da kowa!

Ya ku 'yan uwana masu daraja! Ina kara tunatar da ku, Allah Madaukaki Ya siffanta kan sa da cewa Shi Mai umurni ne da yin adalci, Mai kuma hanin yin zalunci ne. Yace a cikin suratun Nahl aya ta 90:

"Lallai Allah yana yin umurni da yin adalci, da ihsani, da yin kyauta ga ma'abucin kusanci, Yana hanin aikata alfasha, da munkari, da zalunci, Yana muku wa'azi kila za ku wa'azantu."

Sannan Ya haramta wa kanSa zalunci, ya kuma haramta wa bayinsa yin zalunci.

Sannan lallai yana daga cikin abin da addinin Musulunci ya shahara da shi: haramta zaluntar Jama'a. Kuma lallai yana daga cikin abin da addinin Musulunci ya shahara da shi: wajabta taimakon wanda ake zalunta.

Babu ta yadda za ayi Musuluncin mutum, da mutuntakar sa su cika matukar ba ya kokarin tunkude wa al'ummar sa zalunci da rashin adalci.

Sannan lallai abu ne da yake wajibi a kan dukkan wani mai iko, yayi dukkan abin da zai iyayi na halal domin ya tunkude wa al'ummar sa zalunci da aukuwar tashin hankali da fitina.

Imamul Bukhari ya ruwaito Hadisi cikin Sahihin sa daga Sahabi Anas Dan Malik Allah Ya kara masa yarda ya ce:

"Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi yace: "Ka taimaki dan uwan ka yana azzalumi ko yana wanda aka zalunta" sai wani mutum ya ce: Ya manzon Allah zan taimake shi in yana wanda aka zalunta (in kwato masa hakkinsa), to amma in yana mai zalunci ta yaya zan taimake shi? Sai yace: Ka hana shi yin zalunci wannan shine taimakon ka gare shi."

Sannan Imamu Muslim ya ruwaito Hadisi daga Sahabi Jabir Dan Abdullahi yace:

"Wasu yara biyu sun yi fada da juna, daya daga cikin Muhajirai yake, dayan kuwa daga cikin Ansarawa, sai Muhajirin ya daga murya ya nemi taimakon Muhajirai, shi kuwa ba'ansaren ya daga murya ya nemi taimakon Ansarawa, sai manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya fito yace: Wane irin kirayen jahiliyya ne haka? Sai suka ce: Ya Manzon Allah yara ne biyu suke fada da juna, sai dayan su ya doki dayan su a duburarsa. Sai (Annabi) yace: Babu laifi, mutum ya taimaki Dan uwan sa yana azzalumi ko yana wanda ake zalunta, in ya kasance azzalumi ne sai ya hana shi yin zaluncin, wannan shine taimakon sa gare shi, in kuma ya kasance wanda ake zalunta ne sai ya taimake shi."

Sannan zunubi ne babba mutum ya ga ana kokarin wulakanta wasu muminai a gaban sa, kuma ya kame hannayen sa da bakin sa, ba tare da yayi wani yunkuri domin ya kawo masu agajin da zai iya ba.

Ya ku 'yan uwana Musulmi! Kuma yana da kyau ku sani, a dokokin Musulunci, da kuma aqidah da manhajin Ahlis-Sunnah wal Jama'ah, duk wanda Allah (SWT) ya ba mulki, ko ta wace hanya ne, kuma ko da baka so ya zama shugaba ba, to kayi hakuri, kayi masa da'a da biyayya, matukar bai umurce ka da sabawa Allah ba. Sannan kayi masa Addu'a da fatan Allah ya bashi ikon yin adalci ga kowa da kowa, hatta wadanda basu tare da shi. Kuma kayi masa Addu'ar Allah ya bashi ikon sauke nauyin da ya dora masa. 

Ya Allah, ina rokon ka, don tsarkin sunayen ka, kayi wa dukkanin shugabannin mu jagora akan tafarki madaidaici da ka yarda da shi, amin.

Wassalamu Alaikum... Dan uwanku:

Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jihar Kogi, Nigeria. Za'a same shi ta: gusaumurtada@gmail.com ko kuma 08038289761.

Saturday, 9 March 2019

ALLAAH GIVES POWER AND LEADERSHIP TO WHOM HE WILLSANYA AKWAI MAZA A GIDAJEN KUWA?

*ANYA AKWAI MAZA A GIDAJEN KUWA*?

🧕🏻Yanzu mata suna fita waje, suna bayyana surorin jikinsu ga mutanen waje, ba tare da sun rufe jikkunansu yadda shari'ah tace ba.Wasunsu ma matan Aure ne.

🤔 Abin tambaya anan : Shin anya akwai Maza acikin gidajen da matan nan suke kuwa? Shin kodai mazajen gidan sunaso ne Allah ya haramta musu Aljannah sbd Sun Zama *Dayyus* (Mara Kishin iyalansa). 

*" Dukkaninku makiyaya ne, kuma dukkaninku sai abintambaya ne dangane da kiwon da Aka bashi. "* 

_Allah yasa mudace kuma yakara tsare mana imaninmu kuma yasa mucika da kyau da Imani._

✍🏻 *Idris M Rismawy*

ƘARYACE-ƘARYACEN WATAN RAJAB

KARYECE-KARYACEN WATAN RAJAB 

*_HADISAI MARAR SA INGANCI DA HADISAN KARYA GAME DA FALALAR WATAN RAJAB_*

HADISI NA FARKO 
1-(Yin azumin yinin farko na watan Rajab,yana kankare laifukan shekara ukku,a yini na biyu kaffarar shekara biyu,a yini na ukku kaffarar shekara guda,sannan daga nan kowane yini yana kaffarar wata guda)
Wannan Hadisine mai rauni bai inganta ba
@ﺿﻌﻔﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺿﻌﻴﻒ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ - ﺭﻗﻢ : ‏( 3500 )


HADISI NA BIYU
2-(Ya kasance idan ya shiga watan Rajab yana cewa; ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺑﺎﺭِﻙْ ﻟﻨﺎ ﻓﻲ ﺭﺟﺐٍ ﻭﺷﻌﺒﺎﻥَ ، ﻭﺑﻠِّﻐﻨﺎ ﺭﻣﻀﺎﻥ )
Shime Wannan Hadisine mai rauni bai inganta ba daga Manzon Allah SAW ba.
@ﺿﻌﻔﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺿﻌﻴﻒ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ – ﺭﻗﻢ :‏( 4395 ).


HADISI NA UKKU
3-(An kira watan Rajab ne da suna Rajab saboda yana tattaro alkhairi mai yawa ga watan Sha’aban da Ramadhana)
*Shime Wannan Hadisine mai rauni bai inganta ba daga Manzon Allah SAW ba*.
@ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻣﻮﺿﻮﻉ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻠﺴﻠﺔ ﺍﻟﻀﻌﻴﻔﺔ - ﺭﻗﻢ :‏( 3708 )

HADISI NA HUDU
4-(Fifiko da falalar watan Rajab akan sauran watanni,kamar fifiko da falalar alqur’ani ne akan sauran zikirai)
*Shime Wannan Hadisine mai rauni bai inganta ba daga Manzon Allah SAW ba*.
@ﻗﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﺣﺠﺮ ﻣﻮﺿﻮﻉ ﻓﻲ ﺗﺒﻴﻴﻦ ﺍﻟﻌﺠﺐ - ﺭﻗﻢ :‏( 25 )

HADISI BA BIYAR 
5-(Darare guda biyar ba’a mayar da addu’o’insu;daren farko na watan Rajab…………)
*Shime Wannan Hadisine mai rauni bai inganta ba daga Manzon Allah SAW ba*.
@ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻣﻮﺿﻮﻉ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻠﺴﻠﺔ ﺍﻟﻀﻌﻴﻔﺔ - ﺭﻗﻢ : ‏( 1452 )


    ALLAH NE MAFI SANI 


MU HAƊU A DARASI NA GABA INSHA ALLAH


Monday, 21 January 2019

SIGOGIN ISTIGHFARI KALA TAKWAS

*_SIGOGIN ISTIGHFARI KALA TAKWAS NE_*

Manzon Allah, tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, yace:
*_(Na rantse da wanda raina Ya ke hannunSa, Allah! Ina neman gafararSa, kuma ina tuba zuwa gare shi,a kowace rana sama da sau saba'in)_*.

Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce:
(Ya ku mutane! Ku tuba zuwa ga Allah. Domin ni ina tuba a kowace rana zuwa gare Shi sau dari).

SIGA TA FARKO
Shugaban Istighfar gaba daya shine:
_ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﻧﺖ ﺭﺑﻲ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ﺧﻠﻘﺘﻨﻲ ﻭﺃﻧﺎ ﻋﺒﺪﻙ ﻭﺃﻧﺎ ﻋﻠﻰ ﻋﻬﺪﻙ ﻭﻭﻋﺪﻙ ﻣﺎ ﺍﺳﺘﻄﻌﺖ ﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺷﺮ ﻣﺎ ﺻﻨﻌﺖ ﺃﺑﻮﺀ ﻟﻚ ﺑﻨﻌﻤﺘﻚ ﻋﻠﻲ ﻭﺃﺑﻮﺀ ﻟﻚ ﺑﺬﻧﺒﻲ ﻓﺎﻏﻔﺮ ﻟﻲ ﻓﺈﻧﻪ ﻻ ﻳﻐﻔﺮ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ_.

*_Allahumma anta rabbee la ilaha illa ant, khalaqtanee wa-ana 'abduk,wa-ana 'ala 'ahdika wawa'adika mas-tata'ata, a'uzu bika min sharri ma sana'atu, abuu-u laka bini imatika alai, wa abuu u bizanbi, faghfir li fa-innahu la yaghfiruz-zunuba illa anta_*.

Manzon Allah (SAW) ya sunnanta mana karanta wannan istighfari sau daya,safe da kuma yamma _Sannan kuma yace:*
*_(Duk wanda ya karanta shi da safe yana mai imani dashi,idan ya mutu kafin yamma, zai shiga aljanna. Kuma idan ka karantata da yamma kana mai imani da hakan, idan ka mutu kafin safiya zaka shiga aljanna in sha Allah)_*
@Sahihul Jami'i.

SIGA TA BIYU
_ﺍﺳﺘﻐﻔﺮ ﺍﻟﻠﻪ_
*_ASTAGH FIRULLAH_*


SIGA TA UKKU
_ﺭﺑﻲ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ_
*_RABBI GHFIRLI_*

SIGA TA HUDU
_ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﻇﻠﻤﺖ ﻧﻔﺴﻲ ﻓﺎﻏﻔﺮ ﻟﻲ ، ﻓﺈﻧﻪ ﻻ ﻳﻐﻔﺮ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ_
*_ALLAHUMMA INNI ZALAMTU NAFSI FAGHFIRLI FA INNAHU LAA YAGHFIRUZ ZUNUBA ILLA ANTA_*.

SIGA TA BIYAR
_ﺭﺏ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ ﻭﺗﺐ ﻋﻠﻲ،ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﺘﻮﺍﺏ ﺍﻟﻐﻔﻮﺭ_
*_RABBI GHFIRLI WA TUB'ALAYYA INNAKA ANTAT TAUWABUL GHAFUR_*

SIGA TA SHIDA
_ﺭﺏ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ ﻭﺗﺐ ﻋﻠﻲ ، ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﺘﻮﺍﺏ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ_
*_RABBIGH FIRLI WA TUB'ALAYYA INNAKA ANTAT TAUWABUR RAHEEM_*


SIGA TA BAKWAI
_ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﻇﻠﻤﺖ ﻧﻔﺴﻲ ﻇﻠﻤﺎ ﻛﺜﻴﺮﺍ ﻭﻻ ﻳﻐﻔﺮ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ، ﻓﺎﻏﻔﺮ ﻟﻲ ﻣﻐﻔﺮﺓ ﻣﻦ ﻋﻨﺪﻙ، ﻭﺍﺭﺣﻤﻨﻲ ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﻐﻔﻮﺭ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ_
*_ALLAHUMMA INNI ZALAMTU NAFSI ZULMAN KATHIRAN WALA YAGHFIRUZ ZUNUBA ILLALLAH, FAGHFIRLI MAGHFIRANTAN MIN INDIKA, WARAHAMNI INNAKA ANTAL GHAFURUR RAHEEM_*.


SIGA TA TAKWAS
_ﺍﺳﺘﻐﻔﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﻫﻮ ﺍﻟﺤﻲ ﺍﻟﻘﻴﻮﻡ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻪ_

*_Astaghfirul lahal lazi la ilaha illa huwal hayyul-qayyum wa atubu ilaih_*

*Ina rokon Allah Ya sanya ni da ku a cikin bayinSa ma su yawaita istighfar, Ya kuma ba mu lada da matsayin da ya ke ba ma masu yawaita istighfar, amiin.*

*Dan Allah a tura wa 'yan uwa dan su amfana da shi.*

Wednesday, 9 January 2019

Is Virginity a Virtue or Shame?

‎● Is Virginity a Virtue or Shame?


Most people have different views and perspective on virginity. Some say:
‎● Virgins are pretenders.
‎● Virginity is not chastity, its lack of opportunity.
‎● Who will still be virgin in this 21st century?
 *SUBHANALLAH* 
‎Virginity used to be seen as a pride, but today, the virgins are even shy to proclaim it because they will become a laughing stock to people.  

The greatest women ever, were proud of their virginities:
‎● Allah said about Mariam [عليها السلام], She said:
"How shall I have a son, when no man has touched me and I am not unchaste?" 
[Surah Al-Mariam v.20]

‎● Aisha [رضي الله عنها] said:
"Oh Messenger of Allah, If you were to stop for a rest in a valley and you find trees that have been grazed and another ungrazed tree, which of the trees would you make your camel eat from?
He [ﷺ] said, "From the ungrazed tree."
She said, "I am that ungrazed tree."
[Sahih Al Bukhari]
Aisha was the only virgin lady that the Prophet [ﷺ] married amongst his wives.

Even the virgins among men were proud of it.
When Safwan Ibn Muattal [رضي الله عنه] was accused of commiting zina with Aisha, he said:
"Wallahi, ever since I was born, I have never opened the garments of a woman before." [Bukhari, vol. 3, book 48, no. 829]

Those days, when a lady gets disvirgined, her friends will mock her and tease her, but this days, when a woman is still a virgin, her friends will criticize her and advise her to get rid of it.

If you are a virgin out there, don't feel depressed, be proud of yourself and don't be tempted by the brainwashed loose women and men who want you to become like them, because they have lost their pride, they merely exchange their virginity for a bottle of Pepsi, cheer ups money etc.
Be proud of your virtue because a million bottles of Pepsi cannot buy your virginity. Refuse all the sugar coated-tongues, *because your charming prince is coming soon.* 
So do not fear the blame of the blamers.

Allah says: "Bad women are for bad men and bad men are for bad women, good women are for good men and good men are for good women." [Surah Nur v.26]

Do not mind those unrepentant men and women who cheaply gave out their virginities as birthday and valentine gifts.
Celebrities life, fashions & marriages shouldn't shun you away from the Islamic guidelines.
Marry a righteous man or woman from good home because its the good roots that produces the sweet fruits.

Finally, virginity and chastity is not for women alone, its for men too. So, do not let a fool kiss you and do not let a kiss fool you.
Stand out in the crowd and don't try to fit in, this is what it means to be one in a million.

 *May Allah make us amongst those who repent to Him The Most Merciful The oft Forgiving* .

SABUBBAN SHIGA ALJANNA

أسباب دخول الجنة 
SABUBBAN SHIGA ALJANNAH
1- التوحيد والإخلاص. 
Kadaita Allaah da iklasi.


2- الإنفاق في سبيل الله. 
Da ciyarwa aciikin hanyar Allaah


3- الخلق الحسن. 
Kyakykyawan dabi'a


4. الإصلاح والإحسان إلى الناس. 
 Daidaita tsakanin mutane da kyautatama mutane


5- إماطة الأذى عن الطريق. 
Kawarda abin cutarwa daga hanya


6- محبة المؤمنين في الله. 
Son muminai saboda Allaah


7- الحياء. 
Kunya


8- ذكر الله تعالى. 
Ambaton Allaah Madaukaki


9- الإحسان إلى الجار. 
Kyatatama makwabci


10- شكر الله على نعمه. 
Godema Allaah akan Ni'imar Sa


11- كثرة السجود. 
Yawaita Sallah(nafila)


12- التواضع لله. 
Qanqan da kai ga Allaah


13- صلة الرحم. 
Sada Zumunci


14- بر الوالدين. 
Biyayya ga iyaye


15- قراءة القرآن والعمل به 
Karanta Qur'ani da aiki da shi


16- الأمر بالمعروف والنهي عن المنكر. 
Umarni da kyakykyawa da hani da mummuna


17- الرفق بالحيوان. 
Tausasa ma dabbobi


17- الذكر عقب الصلوات. 
 Ambaton Allaah bayan kare sallah


18- طاعة الرسول صلى الله عليه وسلم. 
Biyayya ga Manzon Allaah tsira da amincin Allaah su tabbata agare shi.


20- الصبر. 
Hakuri


21- الصدق. 
Gaskiya


22- المحافظة على الصلوات الخمس. 
Kiyaye sallolin farillai biyar


23- عيادة المريض. 
Duba mara lafiya


 24- الدعاء. 
Addu'a


25- إفشاء السلام وإطعام الطعام. 
Yada sallama da ciyar da abinci


26- تعلم القرآن وتعليمه. 
Koyon Qur'ani da koyar da shi


27- الصلاة على النبي صلى الله عليه وسلم. 
Salati ga Annabi tsira da amincin Allaah ya tabbata agare shi


28- التعاون على البر والتقوى. 
 Temakekeniya akan nagarta da tsoron Allaah


29- الدعوة إلى الله. 
Kira zuwa ga hanyar Allaah


30- حسن الظن بالله تعالى
Kyautata zato ga Allaah


انشرها لتكون صدقة جارية لك.
Yada wannan don ya zama maka SADAKA mai gudana.