Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

Showing posts with label Kimiyya Da Fasaha (Science/Tech). Show all posts
Showing posts with label Kimiyya Da Fasaha (Science/Tech). Show all posts

MENENE CUT OFF MARKS?

*AREWA STUDENTS & ORIENTATION FORUM*

17th June, 2020.

 *Menene Cut Off Marks?*
Cut Off Marks wani Tsari ne Da Jamb Take Amfani Dashi Wajen Kayyade Adadin Makin Da Take so Dalibi Ya Samu Domin Kafin Abashi Admission A Makarantun Gaba Da Secondary.

Jamb Ta Bayyana 160 a Matsayin Cut Off Marks Domin Samun Damar Shiga Jamio'in Gwamnati, 

Saidai Kuma Naga Mafi Yawancin Dalibai Suna Tambaya Cewa Shin Harda BUK? 
Wasu kuma Suna Cewa Harda ABU dadai Sauran Makarantu,

Dalilin Wannan Rubutun Nawa Domin In Sanar Daku Cewa Wannan Cut Off Marks Na Hukumar Jamb Ne Ba Makarantu ba, 

Maana Jamb Ba Zata Yarda Abaiwa Kowanne Dalibi Damar Shiga Jamia ba Har Sai Makinsa Yakai 160.

Amma Fa Yanada Kyau Ku Sani Cewa Ko wacce Jamia Tanada Damar Da Zata Kara Adadin Makin Da Take so, 

Idan Jamia Taga Dama Ta Barshi a 160 Kokuma Ta Maidashi 170 ko 180 Kokuma 200 amma Babu Jamiar Gwamnati Da Zata Ba Dalibi Admission Muddin Baici 160 ba.

Sannan Ina Kara Jan Hankalin Dalibai Akan Mu Kara Dagewa Da Karatu Da Kuma Addua Domin Tunkarar Post Utme. 
Sannan Kada Mu Sakankance Kokuma ka Saka Rai Akan Cewa Makarantar Da kake Nema Zata Bar 160 A Matsayin Cut off Marks Dinta, 

Mafita Shine Ka Chigaba Da Bibiyar Asof Domin Jin Bayanai Da Kuma Cut Off Marks Na Makarantarku Idan An Fitar. 

Abdulkadir Anas Malumfashi 
©Asof 2020.


Share:

DUNIYAR GEOGRAPHY

DUNIYAR GEOGRAPHY TAREDA 


AREWA STUDENTS ORIENTATIO N FORUM.
DAGA: Usman Umar Dagona
(Winner Of Imaging National Chemistry Competition 2019/2020).

ASALIN NIJERIYA DA YAN NIJERIYA

Najeriya na zaune ne kusan a tsakiyar
nahiyyar Afirka, Shi yasa yake daukan lokaci Kadan a tafiyar jirgin sama zuwa kowanne
Yanki a nahiyar Afirka. Daga Legas zuwa Dakar na kasar Senegal sa’o’i kadan ne, haka zalika kuma daga Kano zuwa Tripoli ko Aljeriya a arewacin Afirka duk kasa da sa'oi hudu (4) zakaje. Tafiyar sa’a uku ne daga Kano zuwa Alkahira; babban birnin kasar Masar.
Kuma daidai da lokacin zuwa Addis Ababa na
kasar Etofiya.

Kasar Nijeriya tana zaune ne akan layukan longitude
digiri 3 zuwa 15 gabas da Greenwich, Najeriya
na zagaye da kasashe masu Magana da harshen
Faransa, inda kasar ke da iyaka da tekun Atlantic.
Najeriya na da iyaka da kasar Benin ta yamma,
kasar Nijar ta arewa da
kuma kasar Kamaru ta gabas.
Najeriya na zaune har ila yau akan layukan latitude digiri 4 zuwa 14 a arewacin equator.
Haka yasa Najeriya ke karkashin iskoki biyu na “westerlies” da kuma "easterlies” wanda hakan yakeda tasiri wajen kawo sauyin
yanayi a kasar. Wannan yankin latitude da
Najeriya take kai na mata amfani wajen samun ruwan sama, sanyi, zafi, da kurar hunturu. Wurin da kasar take wuri ne mai amfani
saboda ba'a kulle take ba watau "landlocked",
saboda tanada iyaka da teku wanda ke da matukar amfani wuri safara, samun ruwa don aikace-
aikace daban-daban, hakan ma'adinai
musamman man fetur, gwalagwalai da sauran su.

GIRMAN KASA

Mafi nisan tafiya daga gabas zuwa yamma a Najeriya kimanin kilomita dubu daya da dari
hudu ne (1400), sa’anan daga arewa zuwa
kudu kimanin kilomita dubu daya da dari daya
ne (1100). Najeriya na da fadin kasa da ya kai dubu Dari tara da ashirin da uku da dari bakwai
923700 Sikwaya Kilomota, Najeriya tayi girman
kasar Ghana sau hudu, sa’anan tayi girman
kasar Saliyo sau goma sha uku (13).

YADDA AKA SAMU NIJERIYA.
 
Najeriya ada ba kasa daya bace kamar yadda
muka santa a yau, Yankin ada na kunshe da garuruwa da dauloli manya da kanana. Daga
cikin wadannan dauloli, Daular Usmaniyya tafi
kowanne girma da shahara. A inda ta shafe gaba dayan arewacin Najeriya a karni na sha
tara. A yankin kudu kuwa akwai Oyo da Benin. A
kudu maso gabas akwai Inyamurai da Ibibio a kananan kauyuka. An samu Najeriya ne a
shekarar ta 1914 bayan hade kudanci da
arewacin Najeriya wanda turawan mulkin mallaka suka yi mutanen da suka fara amfani da sunan Nijeriya Sune: 
01- Flora Shaw da kuma 
02- Lady Lugard.

 A shekarar 1953 mutanen Najeriya sun kai miliyan
talatin da daya, a shekarar 1963 mutanen Nijeriya sun kai miliyan hamsin da biyar. A Kidayan
shekarar dubu biyu da biyu (2002) yawan yan Najeriya ya kai miliyan dari da arba'in. Tabbas Najeriya ce kasa mafi shahara da yawan mutane a nahiyar Afirka.

WASU DAGA CIKIN KABILUN NIGERIA.
Nijeriya na dauke da kabilu sama da dari uku da sittin, kadan daga cikin many an kabilun kasar sun hada da:

01- Hausawa wanda suke zaune a arewacin Najeriya musamman jihar Kano, Kaduna, Katsina,
Sokoto, da Naija.

02- Fulani: suna zaune tare da Hausawa ne amma sun fi yawa a jihar Filato da Adamawa. Fulanin asali dogaye ne, marasa jiki, suna da siraran hanci da gashi baki mai tsawo, Fatan jikin su nada haske.

03- Kanuri : suna zaune a arewacin Najeriya a
jihar Barno, Bauchi da Adamawa.

04- Yarbawa : Suna zaune a jihar Oyo, Ogun, Ondo da Legas. Dadin dadawa: Akwai Yarbawa a jihar Kwara
da kasar Benin.

05- Inyamurai : suna zaune a jihar Anambra, Imo,
Rivers da Delta

06- Inyamurai suna zaune a jihohin Anambara, Imo, Cross Rivers da sauransu.

07- Badawa: Suna zaune a Jihar Yobe da wasu Yankuna a Kano da Kaduna.

Sauran kabilun Najeriya sun hada da: Nufawa, Jukunawa, Gwari, Katafawa, Ibira,
Igala, Gwandara, Kaje, Tibi, Ijaw, Kabba, Ikulu,
Efik da sauran su.

Allah ya kara hada kan kasarmu NIJERIYA 👐👐👐
Domin tambayoyi da Shawarwari 09036547648
Usman Umar Dagona.
Share:

DARASIN BIOLOGY

*Biology*
*Darasi Na shidda 6*
*TRANSPORT SYSTEM*
Shi transport system yana magana kan zurgazirga (movement) ta bangarori jiki domin samar da abun da jiki yake bukata domin shi kuma jikin yaci gaba daaiki batare da matsala ba. 
*need for transport*
To idan har hakan yanada amfani kenan acikin jikin mu to dole yakasance yana da amfani domin rashin sa zaihaifar da matsala. Amfanin nasa sune kamar haka 
1.yana rarraba duk wani oxygen da ka shaka acikin jikinka.
2.yana rarraba duk wani nauin sinadarin abinci a dukkan jikinka (nutritional food)
3.yana fitar da duk wani gurbataccen abu wanda yakunshi fitsari dauransu (west product of metabolism)
4.yana fitar da enzyme da kuma hormones wainda suka gama aikinsu (inactive enzymes and hormones) sbd muna da ezymes da hormones da dama wainda ke taimaka mana wanda wani lokaci zasu bayyana ne domin yin aikinsu to dazarar sungama to shikenan Sun gama aiki sai wasu kalar su subayyana. 
5.yana rarraba sinadarin ion &mineral acikin jiki
6.yana rarraba zafi domin zafin jiki yadaidaita. 
*Materials for transport*
Ainafin kayayyakin da jikin yake transport dinsu 
(1) OXYGEN (2) CARBONDIOXIDE (3) NUTRIENTS (4) HORMONES &ENZYMES (5) IONS& MINERALS (6) WATER (7) MANUFACTURED FOOD (8) MINERAL SALT


*COMPOSITION OF BLOOD*
Kamar yadda muka sani shi jini yana da matukar amfani ajiki kana kuma yarabu gida 2
1 Blood cells or capsule. Wanda shi wannan yanayin jinin daskarre ne (solid)
2 Blood plasma. Wanda shikuma wannan blood din yana da ruwa (liquid)
*1 Blood cell or capsule*
Shi wannna sinadarin jinin yarabu gida 3
A)Red blood cell
B)White blood cell
C)blood platelet
A) shi red blood cell ana kiransa red sakamakon sinadarin ions dayamaida sa ja (red) ana kiransa da hemoglobin a turance. kana shi Red blood cell (erythrocytes) yana taimakawa wajen zirgazirgar oxygen daga hunhu zuwa cell din dake a jiki (transfer of oxygen)
B)white blood cells (leukocytes) shi wannan jini baida takamaiman kala (colourless) kana haka sharp dinsa (irregular sharp) kana yana taimakawa wajen bada kariya KO kuma yakar duk wata cuta 
C)platelets (thrombocytes)shi yana taimakawa wajen sa jini yai kauri (clotting blood)
 *blood plasma*
Shi wannan bangaren jini mai sinadarin ruwa ruwa (liquid)yana dauke da sinadarin ruwa kaso mafi yawa wanda yakai akallah 90%wanda yakunshi aguguwa da dama narkakku aciki wanda yahada da protein,food materials (glucose and amino acid)etc
*functions of blood*
Amfaninsa acikin jiki
1)TRANSPORT(2)IN NUTRITION(3)IN EXCRETION(4)HORMONES(5)PROTECTION(6)REGULATION OF TEMPERATURE(7)CLOTTIN OF BLOOD.
*Muhammad salisu company*
*umyu katsina*
@ASOF2020


Share:

HUMAN ANATOMY 3

DARASIN HUMAN ANATOMY KASHI NA UKU

DAGA ; Yusuf Muhammad 

RABE RABEN ANATOMY ( CLASSIFICATION OF ANATOMY )

Shima Dai Human Anatomy Kamar Sauran Kwasakwasai Yana da nasa Rabe Raben Inda Shima Ya Kasu Gida Biyu.
Nafarko Shi Ake Kira Da 
GROSS ANATOMY ( MACROSCOPIC ANATOMY ) :- Wannan Shi Ake Nufi Da Karatun Jikin Dan Adam Da Kuma Yadda Yake Forming Wanda Zamu iya Gani Da Idanuwan mu Mu kuma Iya Bambancewa Ba tare Da munyi Akai Da Wani Instrument, wajen Ganewa ba Misalin Macroscopic Ko Kuma Gross Anatomy Sune Kamar :- Internal Organ Da Kuma External Features.
Nabiyu Shi Ake Kira Da
MICROSCOPIC ANATOMY :- Shikuma Wannan Na Nufin Karatun Ɓangaren Jikin Dan Adam Wanda Kuma Yake Baza Mu Iya Ganewa Da Idanuwan mu ba Har Sai Munyi Amfani Da Wani Instrument Domin Mugane Misalin Microscopic Anatomy Sune Kamar:- Cells ( Cytology ) Dakuma Tissue ( Histology ).
Ku daka cemu A Program Na Gaba
DAGA NAKU :- YUSUF MUHAMMAD

Share:

ILIMIN PHP

(PHP) Hypertex Preprocessor
(Programming Language) kashi na (2)

Daga Salisu Abdulrazak Saheel

PHP programing Language ne da yakeda matiqar muhimmanci wajen gudanar da ayyukanmu na yau da kullum sannan kuma ya shahara sosai wajen yawan amfani dashi da akeyi..
 Sannan yana daya daga cikin Scripting language (Severside)
Abinda ake nufi da server side shine yaren yana mu'amala tsakanin "Server da Browser".
PHP programing language ne wanda ake amfani dashi wajen Developing Website, shine (Backend) na Creating Website wato ba kamar "HTML" and "CSS" da suke (Frontend) ba.
Ana amfani da yaren PHP wajen gina Backend na Website, 
Yaren PHP yanada matukar sauki sannan kuma idan ka iya shi zaiyi wahala ka rasa ayyukan da zaka gudanar sbd la'akari da cewar kaso 80% na Website din duniya da yaren PHP aka hada su..
PHP bai tsaya nan ba zaka iya hada abubuwa da yawa dashi bawai sai website kadai ba kamar yadda wasu suke tunani..
www.tizag.com zai taimaka maka wajen koyo PHP..

Whatssp Only: 08137350232


Share:

NA'URA MAI ƘWAƘWALWA 01

Na'ura Mai kwa-Kwalwa;
       Kashi Na Daya. 

Yadda Ake Hada Android Da Computer Ta Zama Modem;

Daga Salisu Abdulrazak Saheel 


Mutane da yawa suna tambayata da kirana a waya cewa tayaya zasu hada wayansu Techno Android da Computer a matsayin modem suyi browsing da ita
Allah yabani sa'a nasamu wasu hanyoyi guda biyu wanda zaka iya hada ta da computer sune kamar haka: WiFi da USB Cable..😀

Yadda zaka hada techno android da computer ta WiFi hotspot.
Idan kana buqatar hadata da computer ta WiFi, sai kabi wadannan matakan:
1. Kaje Settings> Wireless & Networks> Tethering & Portable Hotspot.
2. Sai ka duba Portable WiFi Hotspot, sai kabude shi.
3. Bayan wasu yan dakiku WiFi Network din zai bayyana akan wayar daga sama.
4. Sannan se kaje Portable WiFi Hotspot Settings> sannan kayi configure din WiFi hotspot.
Wato wurin (blank space) dukansu ka cikesu, Username da Password.

<Network SSID = Kasa abinda kaga dama, kamar sunanka ko inkiyarka haka.

<Security == WPA2 PSK.
<Password naka ya kasance guda takwas zuwa sama.

Idan kabude shi yana dauke da sunan kamfani, sai kabashi naka kasa mashi password yadda kana hadawa zaifara, amma fa idan kabude kabarshi kara zube, kukuma baka bude WiFi din ba to bazaiyi Connect ba, zaita cewa a sanya Password.
Kabarshi a bude karka rufe, sannan kayi search nasa idan ya kamo sai ka danna connect shikenan sai kafara Browsing..😀😍

✍️Salisu Abdulrazak Saheel 
 08137350232
@ASOF2020 Whatsapp 08038485677


Share:

TSANGAYAR KIMIYYA DA FASAHA

Special courses

Tsangayar kimiyya

Facultyn yan nigeria inji wani professor. Kashi biyu cikin ukun daliban qasarnan suna karatu ne a wannan tsangayar.tsangaya ce mai farin jini hakan baya rasa nasaba da karkasuwan ta da kuma yadda dole rayuwa a cikin duniyar nan yake da matsananciyar buqatar kwarewa a fannonin ta.
Tsangayar kimiyya a zamance ana kasa ta zuwa kashi kamar haka:

1-pure science
2-Physical science
3-life science
4-classical science
5-medical science

Duk da wasu na qarawa da social science sai dai haqiqanin gskya social science ba zallar kimiyya bane cikin sa. Bari mu kalle su d'aya bayan d'aya

1-PURE SCIENCE.
Dukkan wani fanni dake qarqashin tsangayar kimiyya to ancire shine daga nan shiya sa ake kiran shi pure science b'angarorin shi sun had'a

Biological science
Chemistry/pure and applied chemistry
Physics/pure and applied physics
Mathematical science

Kai tsaye kana iya cewa wayannan sune tsangayar kimiyya don in babu su to babu kowa ne fanni a science

2-Physical science
Wasu sashe ne aka cire qarashin pure science da suka shafi zallan abin da ya shafi physical aspect daga ciki akwai

Physics and electricity
Industrial chemistry
Geology
Computer science ETC

Wasu jami'oin na qara
Geography da
Astronomy a qarqashin yayin da wasu kuma suke kaisu Social science domin su ba zallar science bane.
Shima computer science wasu na aje shi a social science.

3-Life science
Ilimin kimiyyar daya shafi halittu masu rayuwa sun shafi

Botany
Zoology
Marine biology etc

4-Classical sciences
Sabin fannonin kimiyya da duniya ke tafiya dasu da yawa daga cikin matsalolin kimiyya musamman abin da yashafi harkar (lafiya da cututtuka,noma,hade haden magani etc) ana saka ran way'annan fannoni zasu kawo hanyoyin magance su.

Microbiology
Biotechnology

5-Medical sciences

Dukkan wani sashe daya shafi harkar lafiya to yana qarqashin nan

Sai dai qarqashin bangaren kimiyyar lafiya akwai wasu sashe da su ake kiran su para medical courses suma suna tsangayar harkar likitanci sun had'a da

Physiology
Biochemistry
Anatomy

Wadanda su kamar uwaye ne a dukkan wani medical course.
Daga cikin kwasa kwasan kimiyyar lafiya sun had'a da=

MBBS
Nursing
Pharmacy
Dental
Medical lab.sci.
Physiotherapy
Radiography
Veterinary Med.
Optometry
E.T.C


NB dan haka a matsayin ka na sabon dalibi ko mai niyan karantar kimiyya sai ka nutsu ka duba a cikin fannonin nan wannene kake sha'awar karanta sannan karka manta dukkan way'annan kashe kashe munyi ne dan ka fahimci idan ina neman course kaza sai ban samu ba dan marking dina bai kai ba ko kuma jami'ar da na nema basa yin wannan Course din sai ka duba wanda yake da alaqa dashi ka zaba
 misali =kana neman BIOTECHNOLOGY baka samu ba sai ka nemi MICROBIOLOGY

Ko kuma kana neman ZOOLOGY baka samu ba sai ka gwada neman BOTANY

Ko kana neman MBBS baka samu ba sai ka nemi wani course daza ka iya samu a cikin medical courses din

Sau da dama rashin chanjawa zuwa wanda zaka iya samu ko zaban wanda kake da requirement na saka jami'a ta dauke ka gaba daya ta chanja maka faculty .


M.A IBRAHIM
ABU MUBEENAH
08141919945

Share:

HUMAN ANATOMY 2

#HUMAN-ANATOMY KASHI NA BIYU
A Wane Makaranta Ne Ake Karatun Anatomy ?
Kamar Yadda Take A Najeria A Kwai Makarantu Dayawa Wanda Suke Yin ANATOMY Wanda Kuma Course Din Yasamu Complete Accreditation ( Ma'ana An Bawa Makarantar Damar Yin Course Din Daga NUC ( Nigerian University Commission)
JAMI'OIN DASUKE YIN ANATOMY A NIGERIA
1. AHMADU BELLO UNIVERSITY ( A B U ) ZARIA
2. UNIVERSITY OF CALABAR ( UNICAL) CROSS RIVER
3. BAYERO UNIVERSITY ( B U K ) KANO
4. FEDERAL UNIVERSITY DUTSE ( F U D ) JIGAWA
5. YOBE STATE UNIVERSITY DAMATURU ( YSU) YOBE
6. UNIVERSITY OF ABUJA ( UNIABUJA) FCT
7. UNIVERSITY OF JOS ( UNIJOS ) PLATEAU
8. UNIVERSITY OF ILLORIN ( UNIILLORIN ) KWARA
9. UNIVERSITY OF MAIDUGURI ( UNIMAID ) BORNO
10. UNIVERSITY OF PORT HARCOURT ( UNIPORT ) RIVERS
11. AMBROSE ALLI UNIVERSITY ( AAU ) EDO
12. CHUKWUEMEKA ODEMEGWU OJUKWU UNIVERSITY ( COOU ) ANAMBRA
13. BABCOCK UNIVERSITY ( B U ) OGUN
14. BENUE STATE UNIVERSITY MAKURDI ( BSU ) BENUE
15. DELTA STATE UNIVERSITY ABRAKA ( DELSU ) DELTA
16. EBONYI STATE UNIVERSITY, ABAKALIKI ( EBSU ) EBONYI
17. ENUGU STATE UNIVERSITY OF SCIENCE AND TECHNOLOGY ( ESUT ) ENUGU
18.NNAMDI AZIKIWE UNIVERSITY ( UNIZIK ) ANAMBRA
19. BAUCHI STATE UNIVERSITY ( BASUG ) BAUCHI
20. OLABISI OLABANJO UNIVERSITY ( OOU ) 
21. OSUN STATE UNIVERSITY ( UNIOSUN ) OSUN
22. MADONNA UNIVERSITY,OKIJA ( MOU ) ANAMBRA
23. AFEBABALOLA UNIVERSITY ( ABUAD ) EKITI
24. LADOKE AKINTOLA UNIVERSITY, OSOGBO OYO
25. FEDERAL UNIVERSITY NDUFE ( FUNAI ) EBONYI 
26. UNIVERSITY OF MEDICAL SCIENCE ( UNIMED ) ONDI
27. GREGORY UNIVERSITY UTURU ( GUU ) ABIA
28. IGBINEDION UNIVERSITY , OKADA ( IUO ) EDO
29. BOWEN UNIVERSITY ( BU ) OSUN
30. BINGHAM UNIVERSITY ( BU ) NASARAWA 
DAGA NAKU. YUSUF MUHAMMAD


Share:

#HUMAN-ANATOMY

Meyakamata Kasani Dangane Da Human Anatomy?

HUMAN ANATOMY :- Na Nufi Wani Karatune Na Sassan Jikin Dan Adam, Dabbobi Da Kuma Sauran Halittitu, Anatomy Wani Bangarene Na Biology Wanda Ya Ta'allaka Akan Sassan Jikin Dan Adam Dakuma Rabe Rabensu.

 Ko Kuma 
HUMAN ANATOMY:- Na Nufin Karatun Jikin dan Adam Kama Da Ga Jijiyoyi Wanda ake Kira { Vains} Zuwa Sassan Jiki Wanda Ake Kira { Organ} Har IzuwaTsari Wanda Shine ake Kira { System }

Shima Dai Karatun Sassan Jikin Dan Adam Wato ANATOMY Yazama Dole Dalibin Science Ne Kawai Zaikaranchi Wannan Bangaren Saboda Wannan Karatun Shi Ake Kira Da Hantsi Leka Gidan Kowa A Bangaren Karatun Lafiya, Saboda Duk Wani Bangare Nakaratun Lafiya Dole Ne A Wannan Bangaren Kasamu Chewa Akwai Anatomy Kaman Kashi 60% bisa 100% Saboda Wannan Shi Zai Bawa Ma Aikachin Lafiya Damar Sanin Ya Yanayin Mutum yake Kuma Daga Ina Matsalar Sa Take.

Shima Dai Anatomy kamar Sauran Kwasa Kwasai Ana Iya Karantarsane Ta Hanya Biyu, Hanya Ta Farko Ita Che Wanda Aka Kira UTME Wato Shiga Jami'a Kai Tsaye Bayan Gama Karatun Sikandire, Sai Kuma Hanya Tabiyu Wato DE { Direct Entry } Ita Kuma Wannan Hanya Ita Che Bayan Mutum Yagama Sakandire Kuma Yashiga Wata Makaranta Datake Gaba Da Sikandire Misali Kamar NCE, Diploma, Amma Dai Shi Wannan Karatun Mafi Yawanchi Amfi Badashine Ga Daliban Da Suka Yi JAMB Ne. 

ABUBUWAN DA AKE BUKATA KAFIN KARANTAR SHI WANNAN KARATUN
Ga Dalibin Da Zai Karanta Wannan Karatun Ta Hanyar JAMB: Dole Ne Mutum Yazama Yanada Five Credit A Science Course Wanda Suka Hada Da Biology, Chemistry, Physic, English, Mathematics Sannan Kuma Yazama Yachika Ka'idar Maki Da Makarantar daya nema Ta Fidda.

A WANE FACULTY AKE KARANTAR ANATOMY?

Shide ANATOMY Ana Karantar Sane A Faculty Na Basic Medical Science A Wata Makarantar , Yayinda A Wata kuma Ake Karantar Sa A Faculty Na Medical, Pharmaceutical & Health Sciences.

Daga Naku: YUSUF MUHAMMAD

@ASOF2020 Whatsapp 08038485677
Share:

NA'URA MAI ƘWAƘWALWA 03

"Na'ura Mai Kwakwalwa"
Kashi Na Uku

"GUI = (General User Interface).

Daga Salisu Abdulrazak Saheel

" GUI wato General User Interface
 A takaice shine abin da yake baiwa Programmer damar karbar bayanai daga mutanen da suke amfani da manhajar shi, kamar yanzu da muke amfani da Facebook to duk wani bayani da muke tattaunawa koma dai menene to "GUI" yana kaiwa Zukerberg wanda ya kirkiri Facebook din bayanan, bari na baku wani misali: idan zamu hada manhajar Scanning din ciwon ido dolene muna bukatar "I/O" wato (Inputs & outputs) to kunga a bangaren "Input" muna bukatar wani bangaren da zai dauki photon idon wannan mutumin ko kuma ace an dauki photon zamu samu wani waje da za iya saka photon ta wajen kaga wannan zabin yake baiwa likita damar saka photon ido ko kuma daukar photon kai tsaye wannan shine "INPUT" din mu..😀
tunda mun shigar da bayanai sauran ita manhajar (Software) ta sarrafa bayanan sannan ta fitar da sakamako wannan Result din shine "OUTPUT" kunga kenan mun hada I/O Interface..😀
A takaice dai "I/O" sune suke hadewa su bada "GUI"

Zamu iya daukar "GUI" kamar "Apps" amma dai "Module" ne wanda wasu mutane suka kirkira domin sauqaqa mana aiki wajen karbar bayani daga "Users" (masu aiki da wannar software din)
a cikin su akwai: 
1. Tkinter
2. wxPython
3. JPython
Da sauransu..
Amma dai wadannan guda "3" sune mafi shahara musamman "Tkinter" mutane sunfi aiki dashi
"Tkinter" yanada Input guda: "19" wadanda sune kamar haka: 
1. Button
2. Canvas
3. Checkbutton
4. Entry
5. Frame
6. Label
7. Listbox
8. Menubutton
9. Menu
10. Message
11. Radiobutton
12. Scale
13. Scrollbar
14. Text
15. Toplevel
16. Spinbox
17. PanedWindow
18. LabelFrame
19. tkMessageBox
Idan kukayi la'akari da wadannan "Interface" din ina tunanin zasu taimaka maku wajen hada kowanne kalan manhaja kake so cikin sauki sbd babu wanda ba zaku iya sarrafawa ba a cikin su..

Whatssp Only: 08137350232
@ASOF2020 Whatsapp 08038485677

Share:

NA'URA MAI ƘWAƘWALWA 02


Na'ura Mai kwa-kwalwa
      Kashi Na Biyu

(Python) Programming Language.

Daga Salisu Abdulrazak Saheel

Python programming language ne da muke abubuwa da dama dashi sai dai yanada wahala idan baka maida hankali ba sosai idan kuma ka maida hankali to lallai yanada sauqi, zaka iya amfani dashi wajen gina website dinka..
Ga kadan daga cikin bayani akan Python (Programming Language)

Gaskiya dokokin Python sunada dan wahala musamman idan mutum bai maida hankali sosai ba akanshi...
saboda a programming akwai abinda ake cewa (White Space) toh gaskiya a Python babu wannan abun kuma ana kiranshi da (Indentifiers) a yaren Python saboda ana amfani da space da kuma paragraph (sakin layi) wajen baiwa yaren umarni, 
abinda nake nufi da hakan shine misali idan ka cikin rubuta module ko block to idan kayi sakin layi hakan yana nufin kagama da wannan block din kenan
haka kuma indentifiers
misali mu dauki wannan code din
if 5 > 2:
 print("Five is greater than two!")
if 5 > 2:
print("Five is greater than two!")
if 5 > 2:
print("Five is greater than two!")
if 5 > 2:
  print("Five is greater than two!")
if 5 > 2:
   print("Five is greater than two!")
a cikin wannan misalan dana baka akwai block guda 2 da zasu baka error wajen printing shin ko zaka iya fadamin me yasa?

Ok bari nayi maku bayani da farko nayi amfani da "if statement" wajen gwada tsakanin "2" da "5" wanne yafi wani girma idan "5" yafi "2" shin zai nuna min cewar "5" is greater than "2" ...?
Misali idan ka yi code dinka kamar haka:
if 5 > 2:
print("5 is greater than 2")
Wannan code din zai baka error saboda if da print suna kan layi guda (the same line of code) idan kana coding da computer zaka fahimci abinda nake nufi..
Misali ka lura da code din yanzu zan saka space kafin na saka print
if 5 > 5:
 print("5 is greater than 2")
Ka luraSaheel
Ba space (tazara) kafin na rubuta print..

08137350232.. Whatssp Only.
@ASOF2020 Whatsapp 08038485677
Share:

SHIN MENENE KIMIYYA DA FASAHA?

•Shin menen kimiya da fusaha ma ita karan kanta?

Mutane da yawa suna kasa fahimtar Zuwa Abu guda biyu ne ya hadu ya zama daya ko nace ya bada ma'ana daya.

Toh ilimin kimiyya da fusaha ilimi ne na zamani da ya kunshi bincike a fannukan ilimi daban daban akan dukkan halittun da Allah yayi doron kasa.

 A yau muna cikin rayuwa ne wanda komai mun daura shi akan bincike, Muna bincika menene wannan ko wancan abun?

Yaya yake kuma a wani mataki ake amfani dashi?

Idan mun tattara wannan bayani sai kuma mu watsa wannan bincike a duniya domin mutane su san gaskiyan binciken da akayi Mu a fannin mu na information technology Mun bada muhimmanci akan bayani,
Bayan an samu bayanin sai kuma mu san hanyar da za a yada wannan bayanin....


-Malam Aminu Lawal Husain, Kenan, Shahararren Malami a Jami'ar Tarayya ta Dutse.

A Tattaunawarsa Da Kungiyar Arewa Student's Orientation Forum (ASOF)
A Bangaren ilimin kimiyya Da Fusaha.

Zamu Cigaba da Kawo Muku Firar Mu Dashi.

@ASOF2020 Whatsapp 08038485677

Share:

TWEAKING 01


"Tweaking" (1)

Daga: Salisu Abdulrazak Saheel

Bayani akan "Tweeking": idan akace "Tweeking" shine kamar canjawa, wato canja wani abu zuwa wani abu daban, Misali: Canja "Imei" na wayar "Android", idan akace " Imei " to sune wasu lambobi guda 15 wanda ake kiransu da serial number wanda kowace waya tanada nata lambobin wanda ake ganinsu ta hanyar danna *#06# dan haka kowa ya danna a wayarsa domin ya ganewa idonsa..😀
To da zarar kundanna zakuga lambobi guda 15 to wannan sune "Imei" kuma su ake kira da Serial Number, kuma kowace waya tanada nata lambobin sannan sunada matiqar amfani a waya domin idan babusu a waya to waya kwata-kwata network dinta zai dauke babu damar yin kira ko browsing da sauransu.
To wani lokaci wannan numbobin suna yawan gogewa a wayar android sai kaga wayarka kwata-kwata takiyin kira ko browsing kuma gashi da service sai ka kasa gane matsalan har sai ka kai wajen masu gyara to da ace zaka danna *#06# zakaga wannan lambobin ne suka goge.
To Amma Alhamdulillah insha Allah indai kuna biye da "Arewa Students Orientation Forum" zaku koyi yadda zaku canja wasu lambobin.

Bayan haka kuma wasu lokutta zakuji anata maganar "MB" ko "GB" masu yawa wanda zakuji har sayar da sim din akeyi a kasuwa kokuma kuji ance akwai wata sabuwar waya tafito wanda idan kasiyeta ka aika (sending) sunan wayar zuwa wasu lambobi zaka samu wata garabasa ta data mai yawa da sauran ire iren wadannan to duk anayinsu ne ta hanyar "Tweaking" Misali: Misali abinda yasa ake samun Mb ta hanyar Tweak shine akwai sabbin wayoyi masu tsada wanda zakuga an rubuta a jikin kwalin wayar kan cewa idan kasiya wannan wayar kasanya Sim dinka zaka samu wani Mb mai yawa, to sai kuma wayoyin sunyi tsada babu dama kasamu wannan Mb data din kanaji kana gani sai dai ka haqura to ana hakane sai kimiyya ta gano ai abinda yasa ake samun wannan Mb mai yawa irin a wannan sabbin wayoyin saboda "Imei Number" din ne, inda ace zaka iya sawa wayarka irin wannan "Imei" to kaima zaka iya samun wannan Mb din..😀😍
To a haka ne sai "Programmers su Abokina Biggiey" suka kirkiri wani Application mai suna "Mobile Uncle Tools" ko "MTK-Engineering" da sauransu.
Wanda da wannan apps din zaka iya canjawa wayarka "Imei Number" dinta kaima kasamu Data Mb.
Sai kuma irin wayoyin da zakuji ance tana zuwa da kyautar Data. Misali: Kamar Techno P5 tana zuwa da kyautar 2GB idan ka dora layin Airtel ka aika (Sending) Data zuwa 141, haka Infinix tana zuwa da kyautar 1GB a layin MTN idan ka aika Ifinix zuwa 131, wayoyi da dama suna zuwa da irin wannan kyautar to idan kasamu "Imei number" din wannan wayar da take zuwa da wadannan kyautar to idan kasanya wa wayarka sannan ka aika wannan saqon da ake turawa kaima zaka samu wannan Mb din.
Misali: kanada waya Gionee P4 ko P5 to zaka canja mata "Imei number" dinta zuwa na Techno C8 ko na Airtel ko na Blackberry haka zalika suma na Techno din zaka iya canja "Imei number" nasu zuwa na kowane waya.

Amma fa canja "Imei number" din anaso ace wayarka takai Version 4 zuwa sama idan kuma baikai Version 4 ba to wani lokaci "Imei Number" din baya canjuwa.

Wannan shine takaitaccen bayani akan "Tweeking".

Mu hadu kashi na 2.

Whatssp only: 08137350232
Share:

ILIMIN PSYCHOLOGY


Saikoloji(Psychology)
Abubuwan Da Darasin Yakunsa:
1-Ma'anar Saikoloji

2-Ma'anar Idukeshinal Saikoloji(Educational Psychology)

6-Kammalawa

EDUCATIONAL PSYCHOLOGY

•Menene Ilimin Karatun Halayyar Dan Adam❓

•Taya Masana wannan fannin(Psychologist) suka dauki kalmar ta Psycholo❓

•Menene alakar Psychology da Education❓
Ku, Kasance Tare da Arewa Student's Orientation Forum! 

Menene Saikoloji(Psychology)❓ 

Kalmar Saikoloji Ansamota ne Daga Yaren girkawa(Greek) Kuma ta kasu gida biyu: ('psyche‘da 'Logos) 
Kalmar 'Psyche' tana Nufin Ruhi ‘soul’ da ‘Logos’ tana Nufin ‘science’ a yaren girkawa, Bisa Wadannan Ma'anonin An Bayyana Saikoloji a Matsayin kimiyyar Ruhi/Rai.


Wasu Masana Saikoloji (Psychologist) Na baya Bayan Nan Sun yi Bayanin Saikoloji a Matsayin
Wani ilimi Dayake Taka muhimiyar Rawa; "a, yanayin Kai komo Na Ruhi, (Nature) Asalin Ruhi, (Origin) Dakuma kaddarar Ruhin Dan Adam"

 Sai dai Kuma Shi Ruhi ko Rai Wani Abune (Metaphysical)
Ba'a iya ganin sa ko a taba Shi Kuma Baza'a iya Aiwatar da gwajin Masana kimiyya ba Akan sa.(Ruhi)


A Karni Na 18(18th) Masana sun Fahimci Saikoloji a Matsayin 'kimiyyar abunda yashafi tunanin Dan Adam' (Mental) 
Kokuma Tunanin Dayake Cikin kwakwalwa (Mind).

William James (1892) yayi bayanin Saikoloji; a Matsayin "kimiyyar Kai komo Na kwakwalwa wajen Yin Tunani Dakuma karbar Abubuwa" (So, Ko kuma ki) 

B.F. Skinner, Shahararren Masanin Saikoloji ya Fassara Saikoloji da
“kimiyyar Halayya da kwarewar Dan Adam, wajen Sarrafa abubuwa a, Cikin Ransa. 

A Takaice dai ilimin Saikoloji ilimi ne Dayake Bibiyar Halayyar Dan Adam a kimiyyance ko a ilimance, tun daga zuwa ko kafin Zuwan Dan Adam Duniya(Zero Years to Death) Har Zuwa ga Barin sa Duniyar.

Misali; A, Saikoloji Za'a Fahimci Halayyar, jarirai(Infants), Za'a Fahimci Halayyar Matasa, Manyan Mutane Dakuma Tsoffi, da ma Banbance-banbancen Dai Dai kun Mutane (individuals differences) 

✅Menene alaka tsakanin Ilimjn Psychology da Kuma Education❓

Mun dai fahimci Menene shi kanshi Saikoloji (Psychology) a Yanzu Zamu Fara Fahimtar Shima Education Menene?


•Educational Psychology;

Idan Muka Duba Kalmar Educational+ Psychology, Zamu Ga Saikoloji din Damuka sanshi ne, ko Mukayi Bayanin sa a Baya, Kuma aka kara hada shi da Education; Hakan Yana Nuna Sunada wata Alaka ta ilimi.

Bari Mufara Sanin Ma'anar Education Sai mu hada Ma'anar sa Da ta Saikoloji, yanda, Mu Zamu Fahimci Alakarsu Da Juna.

Kalmar Education; Asalin Kalmar a cirota ne daga 'Latin' 'educare' ko 'educatio'
Wanda a turance Kuma ana kiranta da educate a karni na 16 (16th)

Ma'anar Kalmar Education Da Hausa Muna Cewa "ilimi"

Kalmar Education Kokuma ilimi Da Hausa yana Nufin "Hanya ce ta Saukaka Koyo, ko Samun kwarewa da Dabaru ko Halayya, Dakuma Imani da Wani Abu ko yadda, da kudurcewa a Zuciya. 

A fannin koyarwa Kuma akwai wasu salailai ko Dabaru Da'ake bi Wajen koyar da ilimi shi kanshi: daga cikin su akwai dabarar Koyarwar bayar da Labari, Tattaunawa, Dakuma Bincike. D.s.

A Takaice Duba Abubuwan Biyu(Psychology Da Education)
Suna tare da Juna Basa Rabuwa, Domin ilimi yana tare Da tunani Kokuma abunda Rai/Ruhi Yaso Kokuma Yakeso, Hakanan Shima ilimi ba'a ganin sa ko a taba shi.

Shin ilimin Psychology, Shine Yake Qunshe Da ilimi (Education) Kokuma ilimi(Education) Shine Yake Kunshe Da Psychology?

A Dunkule idan Mukace ilimi Ko Education, Mun Game Komai; Dukkannin Wani ilimi Yana Ciki.

Amman Psychology Kuwa, a, Dunkule Wani ilimi Ne Na Halayyar Dan Adam, a kowanne Matakin Rayuwar sa(Jinjiri, Matashi, babban Mutum, Dattijo, Mace da Namiji, Dss.)

Duk Dahaka ilimin Psychology Yanada Alaka Da kowanne ilimi, Domin kowanne ilimi yanada Alaka Da Tunanin Dan Adam Dakuma abunda Yake Cikin Ran Dan Adam,
Idan Kuwa Hakane tako Wacce Fuska ilimin, kimiyyar Sanin Halayyar Dan Adam (psychology) ba'a Raba Shi Da ilimi Gamamme(Education)

*Kammalaw;*

A Taqaice Bazaka Raba Saikoloji Da Idukashen Ba;
Education Yana chanja Halayyar Dan Adam ne, ta kyawawan Hanyoyi, Dakuma Shiryar da, Dan Adam ko Luratar dashi Abubuwan Rayuwa Masu Muhimmanci, a Zamantakewa.
Saikoloji(Psychology) Kuma Karatun ilimin, kimiyyar Halayyar Dan Adam ne.

Mu Hadu a Darasi Nabiyu, Domin Cigaba Da bayani akan Educational Psychology.

@ASOF2020 Whatsapp 08038485677
Share:

BACCIN DOKI A TSAYE

BACCIN DOKI A TSAYE

Daga: Zakariyya Shu'aib Adam

Doki dabba ne mai ƙarfi da kyawu. Masu sarauta da dukiya ne suka fi anfani dashi. Saɓanin jaki da raƙumi, doki bai cika aikace aikace na wahala ba. Yafi kuzari da karsashi a wurin hawan sallah (Durbar festival), sukuwa (Horse race) da kuma wasan ƙwallon doki (Polo). Doki yana da tsafta shi yasa bai cika kwanciya a wuri mai dauɗa ba. A mafi yawan lokuta, baya fita kiwo sai dai a kawo masa abinci turkensa.

Shekaran jiya, ni da abokina mun wuce wani doki yana barci a tsaye. Abokina yayi mamakin wannan ɗabi'a matuƙa. Sanin cewa ni ɗalibi ne a Tsangayar likitancin dabbobi tasa ya jefo tambaya gareni. Me yasa doki ke da wannan ɗabi'a? Ba shi kaɗai ba, na san da yawan mutane (har da wasu daga cikin masu karanta wannan rubutu) sun taɓa ganin doki na barci a tsaye kuma za su so jin hikimar hakan.

Doki dabba ne mai nauyin gaske. Idan ka kwatanta girman jikinsa da ƙafafunsa, za ka riski cewa ƙafafun ba za su iya ɗaukar nauyin jikin na tsawon lokaci ba tare da hutu ba. Wannan tasa Allah (SWT) yayi wani masarrafi da ake kira
STAY APPARATUS a ƙafafunsa na gaba da na baya (Fore and hind limbs). Wannan tsari na stay apparatus, shi ke ba doki damar tsayuwa na tsawon lokaci tare da bacci ba tare da ya faɗi ba.

STAY APPARATUS yana nufin haɗuwar tsoka (Muscles), tendons da ligaments waɗanda ke ɗaure (locking) gaɓɓan ƙafafun doki (limb joints). Wannan masarrafi yana taimakawa doki wurin sauke nauyin jikinsa ga ƙafafu uku yayinda yake hutawa da guda. Bayan ya huta da ƙafa gudan, sai ya kuma sauke nauyin ga wasu ƙafafun uku ya huta da wata ƙafar guda.

'STAY APPARATUS' ya ƙunshi ababe kamar haka:

(1) Suspensory apparatus (irinsu superficial da deep digital flexor tendon, proximal da distal check ligament haɗi da sesamoidean ligament).

(2) Tsokoki irinsu Biceps brachii, Triceps brachii da kuma Extensor carpi radialis.

(3) Stifle-locking mechanism, hock, patella tendon da patella ligaments.

[Ayi haƙuri da waɗansu kalmomi da na kasa fassara su zuwa Hausa. Hakazalika, ban faɗaɗa bayanin Mechanism na stay apparatus ba saboda rubutun zai tsawaita kuma fahimtar abin zai yi wuya ga wanda ba ɗalibin likitanci dabbobi ba.]

Allah shine mafi sani.
Share:

A VERY INFORMATIVE AND EDUCATING MESSAGE

*#Very very _informative_ and _educating_ message!📱📲 📱*


*Please dial *_#61#_ on your phone to know if your phone number(s)/line(s) is(are) being _monitored!_*

*If _"call forwarding"_ appears; that confirms that that phone number/line is being _monitored!_*

*Therefore, do dial _##21#_ to remove the _"monitoring device"_ from that phone number/line!*

*_Please do so for_ ALL _your phone numbers/lines!_*


*KINDLY _SHARE, SPREAD, SEND and FORWARD_ THIS VALUABLE INFORMATION _FAR and WIDE!👀_*
👉🏾📱📲📱♻🌍♻📱📲📱👈🏾


Share:

HOW TO TRANSFER FROM YOUR BANK ACCOUNT (ALL BANKS)

How to transfer from your bank account. (All banks)
1. Access Bank:
----*901#
2. EcoBank:
----*326#
3. Fidelity Bank:
----*770#
4. FCMB:
---- * 389 * 214#
5. First Bank
----*894#
6. GTB:
----*737#
7. Heritage Bank:
---- * 322 * 030#
8. Keystone Bank:
---- * 322 * 082#
9. Skye Bank:
---- * 389 * 076*1#
10. Stanbic IBTC:
----*909#
11. Sterling Bank:
----*822#
12. UBA:
---- * 389 * 033*1#
13. Unity Bank:
---- * 322 * 215#
14. Zenith Bank:
----*966#
15. Diamond Bank
---- * 710 * 555#
To know your BVN, dial
---- * 565 * 0#.
Share the information with friends and loved ones.

Share:

THE IMPORTANCE OF IMEI

IMEI
Please dial *#06# on ur phone.The lengthy number that appears on what looks like a Barcode,is called ur phone's IMEI Number With this number, your last/ current location can be traced even if the sim card had been removed from ur phone.
Give ur IMEI NUMBER to family and friends so that when u disappear without an explanation and ur phone is off or rings unanswered, they can make the case easy for the police by providing them with this number which can then be used to track ur movements.
Young girls are being abducted for porn videos
That is why we are having a high rate of missing girls suddenly. Human trafficking is real let's unite to fight it.
NB: Please send this message to all your friends and family on WhatsApp contacts and WhatsApp groups before it's too late

Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form