Showing posts with label Kiwon Lafiya (Health Matters). Show all posts
Showing posts with label Kiwon Lafiya (Health Matters). Show all posts

CORONAVIRUS NA SABON ABU BANE


*Mal. Aminu Ibrahim Daurawa*


CORANAVIRUS BA SABON ABU BANE 

An dade ana gamuwa da ibtila'i da jarrabawa a fadin duniya, kwalara da Annoba da yaduwar cutaka ya dade yana addabar duniya, Kuma ana yi masa farrasa iri iri, kowa gwargwadon abinda yake dauke da shi na akida, ko hankali, ko ilmi ko al'ada, ko surkulle. 
Amma mu a mahanda ta addini muna daukar wadananan a matsayin jarrabawa da Jan kunne da Allah yake yiwa mutane domin su saduda, su sallamawa Allah, su yadda wananan duniya akwai me ita, Kuma yana da iko akanta kuma zai Iya tashin ta duk sadda yaga dama.
Domin abubuwan da ake aikatawa a wananan duniya na masha'a sunyi yawa, butulci da kangarewa, da shishigi yayi yawa, wasu ma basu yadda akwai Allah ba, wasu Kuma sun yadda akwai Allah amma sun bashi siffofi irin na mutane, wasu kuma sun yadda da Allah amma sun bijirewa dokokinsa, wasu kuma sun takale shi da fada ta hanyar fada da Annabin sa, da muzantashi, da yiwa addinin sa izgili da baa,
Wasu sun shagala da duniya sun manta da lahira, wasu kuma suna kokarin kwatanta abinda Allah ya yi umarni gwargwadon ikon su.
Wananan duka ba zai hana samun jarrabawa ba daga lokaci zuwa lokaci, Kuma akan kowa da kowa, watakila wani yace to mai yasa abin yake shafar musulmi da mutanan kirki, ba ya tsayawa akan Iya wadanda suka jawo shi, amsa shine ita jarrabawa tana shafar kowa, amma ga mumini sai ya zama shahada da kaffara, ga kafiri sai ta zama azaba da gargadi, ga fasiki Kuma sai ya zama izna da waazi, ga misali na wasu Annoba da aka samu a duniya a tsawon tarihi,
An yi wata Annoba a shekara ta 18 Bayan hijra, 640 miladiyya, lokacin kalifancin S. Umar, a wani yanki na kasar Sham, Mai suna Amwas, wadda ta halakar da mutane kusan dubu 20, daga ciki har da wasu manyan sahabbai kamar Abu Ubaidatu Bn Jarrah da Muazu Dan jabal, 
1, Annoba a akayi a yankin Germany zuwa Rum a shekara ta 165 Har zuwa 180, adadin mutuwa mai yawan gaske .
2 wata Annoba da aka yi a yankin Asiya zuwa Africa a tsakanin shekara ta 541 zuwa 542, wanda aka yi hasarar rayuka Masu yawa.
3, wata mummunar bakar Annoba wacce aka yi a shekara ta 1346, zuwa 1353, wacce ta fara daga turai ta shiga yankin Asiya, Har zuwa Africa, wananan cuta ta yadu ta hanyar kudin cizo har aka yi hasarar rayuka masu tarin yawa , wanda duniya ta girgiza a lokacin.
4. Annobar Landon wacce aka yi ta a shekara ta 1665 zuwa 1666 miladiyya, wacce aka bayar da rahoto cewa mutum sama da dubu dari suka sheka lahira.
5. Wata Annoba a yankin Faransa a shekara ta 1720 wadda ta halaka sama da mutum dabu dari.
6. Wata Annoba da ta barke a yankin Amurka a shekarar 1793, ta kashe sama da mutum dabu 40,
7. Wata cuta mai suna kwalara a shekarar 1820 wacce ta fara daga kudu maso gabashin Asiya ta kashe mutane da dama wadda ta fara daga wani kauye a cikin India har ta kusa gamai duniya.
8. Wata Annobar daga kasar sin a shekara ta 1910 zuwa 1911, ta kashe sama da mutum dubu 60.
9. Sai wacce akayi a Honkon 1968 a tsawon kwana 17 wadda ta kashe kusan miliyan daya. 
10. Sai Cutar HIV mai karya garkuwar jiki wacce ta fara daga 1976, har yau ana fama da ita, Allah kadai yasan yawan wadanda ta kashe zuwa yanzu. 
11. da wacce akayi mata suna zika, wanda ya yadu a Brazil, yana kama Yara ta hanyar cizon sauro, yayi barna a kusan kasashe 68, 2015.
12. Ciwan mashasharar aladu 2009, wanda ya faro daga Mexico ya yadu yayi Barna a duniya har zuwa 2010.
13. Ibola wani ciwo kuma Annoba 2013 ya faro daga wani yanki anan Afrika, farkon tashin sa ya kashe kusan mutum dubu 6.
14. Ga kuma lassa kwanan nan.
15. Ga kuma Coronavirus, Allah kadai yasan me zai faru, amma ko yanzu an dauki darasi, domin wadanda basu yadda da Allah ba sunce a rokeshi ko a sami mafita, abin mamaki ace komai ya tsaya tsak a duniya, gidajan kida da rawa wasanni, Mashaya, 
16. Kuma mutane suna kaura daga yankin Afrika suna zuwa turai, domin gudun talauci, amma yanzu turawa suna gudowa daga turai zuwa Afrika domin gudun Coronavirus,
17. Muyi abubuwa biyar
18. Na daya yadda da kaddara Mai dadi da Mara dadi duk daga Allah ne
19. Mu dauki matakan kare kai yadda jamian kiwan lafiya suke fada
20. Mu dukufa da tuba da istigfari da komawa ga Allah, domin ya yaye mana wananan Annoba, da yawaita zikri da addua. 
21. Duk musulmin da ya mutu yayi shahada,
22. Kada mu shiga inda Annoba take, Kada kuma mu fita daga inda ake yi har sai an tabbatar da bamu dauka ba.
23. Allah ya fidda mu lafiya.
Share:

AKWAI WARAKA TATTARE DA ZUMA


*AKWAI WARAKA TATTARE DA ZUMA 🍯*


Qudan zuma (bee) 🐝 yana sha daga ire-iren ruwa (juices) na furanni da 'ya'yan itace daban daban sai ya samar da zuma (honey) a jikinshi, wanda yake tara shi a cikin kwayoyin kakin zuma (cells of wax). Sai a wasu qarnoni da suka gabata ne mutum ya gane cewa zuma tana fitowa ne daga cikin qudan zuma. Wanda alqur'ani ya tabbatar da hakan tun shekaru dubu ďaya da ďari huďu (1,400years) da suka gabata a wannan ayar 👇 

*”ثُمَّ كُلِى مِن كُلِّ الثَّمَرَٰتِ فَاسلُكِى سُبُلَ رَبِّكِ ذُلُلًا يَخرُجُ مِنۢ بُطُونِهَا شَرَابٌ مُّختَلِفٌ أَلوَٰنُهُۥ فِيهِ شِفَآءٌ لِّلنَّاسِ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَءَايَةً لِّقَومٍ يَتَفَكَّرُونَ“*

*"Sa´an nan ki ci daga dukkan ´ya´yan itãce, sabõda haka ki shiga hanyõyin Ubangijinki, sunã hõrarru." Wani abin shã yanã fita daga cikunanta, mai sãɓãwar launukansa a cikinsa akwai wata WARKEWA ga mutãne. Lalle ne, a cikin wannan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni.”* (Suratun Nahl: 69).
.

Yanzu mun fahimci cewa akwai waraka tattare da zuma kuma tana ďauke da magunguna iri-iri. 'Yan qasar Rasha (Russians) sun yi amfani da zuma a yaqin duniya na biyu (World War II) wajen ďaure ciwukan da suka ji a jikinsu. Ciwon ba zai ru6e ba kuma ba zai zaizaye waje ba. Saboda density na zuma, babu wani fumfuna (fungus) ko bacteria da zai yi tsiro a ciwon. 
.

Mutumin da yake fama da mutuwar wani sashi na jikinshi ana ba shi zuma don magance wannan cutar, 

Zuma tana ďauke da sinadarin sugar (fructose) da vitamin K. 
.

Don haka tabbas alqur'ani ya sanar da mu amfanin zuma, kuma likitoci na wannan zamanin sun tabbatar da hakan. 
.

Allah Ya sa mu dace. 
.

Duba Littafin 👇 
*The Qur'an and Modern Science.*

Rubutawa:
*✍🏾Ayyub Musa Jebi Giwa.*
*(Abul Husnain).*

*🕌Islamic Post WhatsApp.*
Share:

LADUBBAN MUSULUNCI A LOKACIN ANNOBA(CORONAVIRUS)


*LADUBBAN MUSULUNCI DA SUKA SHAFI ANNOBA (CORONA VIRUS)*

*Daga: ✍ Sheikh Basheer Lawal Muhammad Zaria (Abu Sumayyah).*

*1.* Kowa ya kame bakinsa kar wanda yayi magana akan mas'alar sai masana- Ulul Amri( Malamai da Likitoci). 

*2.* Annobar Corona azabace mai gargadi ba abar wasa ba. Saboda haka a kiyaye wasa da ita.

*3.* Tuba cikakkiya zuwaga Allah (At-Taubatun Nasuh) da mayar da haƙƙi ga wanda aka zalunta.

*4.* Yawaita addu'a, istigfari da tasbihi (Allahumma inni auzu bikia minal Juzhami, wal junuuni, wal barasi, wa sayyi'il asƙaam). 

*5.* Kyautatawa Allah zato. Duk abinda ya same mu to akwai hikimar da Allah ya barwa kansa sa ni.

*6.* Haƙuri da rashin raaki, kuyatu da surutai akan mas'alar.

*7.* Katange marasa lafiya don karsu cutar da masu lafiya.

*8.* Sauraron shawarwarin likitoci gameda yadda za ayi mu'amala ga wanda cutar ta bayyana a gareshi.

*9.* Komawa zuwaga malaman addini gameda hukunce-hukuncen shari'ah akan mas'alar. Kamar sallah, gaisawa da mutane, zuwa gaida wanda ya kamu da cutar d.s. 

*10.* Kame baki da rashin yaɗa jita-jita akan mas'alar. Domin yanzu ana cutar da mutane da tsoratar dasu fiye da haƙiƙanin yadda cutar ta ke.

In sha'a Allah za'a ci gaba da bayanai.

*Zauren Sheikh Basheer Lawal Muhammad Zaria Hafizahullah.*
+2348062169629
+2348143646953
Share:

CIWON SANYIN MARA DA AKE SAMU TA HANYAR JIMA'I DA ILLOLINSA GA MAZA


CIWON SANYIN MARA DA AKE SAMU TA HANYAR JIMA'I DA ILLOLINSA GA MAZA

Ciwon sanyi cuta ce da akafi yaɗawa ta hanyar jima'i (STDs/STIs) .ƙwayoyin halittun dake sanya cutar ana yaɗa sune daga wani mutum zuwa wani mutum, ta jini, maniyyi, ruwan farji ko ruwan jiki. Alamomin ciwon sanyi ga maza sun sha banban tsakanin mutane wanda ciwon ya harba. Hakan ya danganta ne da nau'in ƙwayar halittar cutar wacce ta haddasa ciwon da kuma matakin da cutar ta takai a jikin mutum - ma'ana, alamomi ko matakin farko da kamuwar cutar ko alamomi na gaba bayan ta soma jimawa a jikin marar lafiyar. Haka kuma, suma yanayin alamomin sunsha banban ta fuskar tsanani ko sauƙinsu, koma rashin ganin alama ko ɗaya duk da cewa kau akwai cutar a jikin marar lafiyar. Maza da yawa na zargin suna da ciwon sanyi ne kaɗai a lokacinda suka ga wasu alamomi da basu saba gani ba (baƙi) ga al'aurarsu, misali , kamar: feshin ƙananan ƙuraje ko ƙaikayi, ko fitar farin ruwa, jin raɗaɗin zafi daga maraina da sauransu. A taƙaice dai, alamomin ciwon sanyin maza zasu iya ɓuya amma gwaji a asibiti zai iya nuna akwai cutar idan akwaita.

Ciwon sanyi anfi yaɗasa ne ta hanyar jima'i kuma maza na iya harbin mata da ciwon ko kuma su matan masu ɗauke da ciwon su sakawa maza mararsa ciwon. Ciwon yafi yaɗuwa kuma anfi samunsa ga maza masu neman mata ko mata masu bin mazaje. Haka kuma mutum zaya iya kamuwa da ciwon ta wasu hanyoyin na daban daba jima'i ba. Kuma lallai ciwon nada wuyar magani , musamman idan mutum bai samu magani ingantacce ba. Zai iya yin wuyar magancewa saboda rashin samun sahihin magani ko daɗewarsa cikin jiki ba'a magance ba. Sau da yawa zaka ga cewa mutane sukan sha magunguna domin kaiwa ciwon hari da sukar alluran likita amma hakan bai razana ciwon ba sai kaga yana ma mutane jeka-ka-dawo tsawon watanni koma shekaru ba'a samu waraka ba.

Alamomin ciwon sanyin maza wanda akafi samu bainar mutane (game gari) :
1. ƙananan ƙuraje akan zakari, ko maraina ko ƙasansu.
2. ƙaikayi akan zakari (kan hular).
3. Fitar farin ruwa daga zakari, mai kalar madara ko ɗorawa, mai kauri ko wanda ya tsinke.
4. Jin zafi wajen yin fitsari.
5. Jin zafi yayin fitar maniyyi.
6. ƙuraje masu ɗurar ruwa da fashewa akan zakari.
7. Jin tsira a jiki ko jin motsi kamar na tsutsa ko kiyashi a jiki.

Alamomi ciwon sanyin maza wanda ba game gari ba:
1. Rauni (gyambo) ga zakari ko maraina.
2. Zafi da kumburin maraina
3. Zafi da kumburi daga kwararo da fitsari da maniyyi suke fitowa daga cikin zakari.
4. Zazzaɓi

Matsalolin jima'i da ciwon sanyi zai iya haddasa ma maza:

1. RASHIN KARFIN MAZAKUTA: Bincike ya nuna cewa cutar ciwon sanyi mai suna da turanci "Chlamydia" (kilamiidiya) zata iya sanya matsalar rashin ƙarfin mazakuta idan ciwon yayi ƙamari ba'a magance shi ba. Cutar maɓannaciya ce da take illa a ɓoye kuma mafi yawanci bata nuna wata alama a zahiri ga mai ɗauke da cutar. Ana samunta bainar mutane da yawa. Rashin ƙarfin mazakuta na nufin matsalar rashin cikakken ƙarfin al’aurar namiji ko raguwar ƙarfin al’aura yayinda aka fara saduwa ko kuma rashin miƙewar al’aura yayinda ake buƙatar fara jima’i. Bugu da ƙari, matsalar na iya zuwa da saurin kawowa/inzali. Rashin ƙarfin maza zai iya saka magidanci cikin damuwa da tawayar jinɗaɗin rayuwarsa ta jima'i, ko jin cewa bai cika mutum namiji ba, ko rashin haifuwa kasancewar bazai iya yima iyalinsa ciki ba saboda rashin miƙewar al'aura. Zuwa asibiti da wuri ko cibiyar lafiya zai iya tsiratar da mai wannan matsala, inshaaAllah.

2 RASHIN HAIFUWA:. Cutar sanyi mai suna "Gonorrhea" (Gonoriya) , kamar dai ƙwayar cutar "Chlamydia", cutace daga halittar "bacteria" kuma zata iya laɓewa a cikin jiki ba tare da wasu alamomi ba. Duk da haka, tana zuwa da alamomi kamar fitar farin ruwa, mai kalar madara daga farkon cutar, daga nan sai ya koma ɗorawa, mai kauri da yawa, wani lokacin harda ɗan jini-jini. Yin fitsari da zafi da yawan yin fitsari, ƙaikayin dubura, zubar jini, murar maƙoshi/maƙogwaro, jan- ido ko ƙananan kuraje, ciwon gaɓoɓi da sauransu. Idan ba'a lura da cutar da wuri ba kuma aka magance ta, zata iya sanya rashin haifuwa ga namiji ko mace.

Nau'in ciwon sanyi (ire-irensu) suna da yawa kuma kowanne iri akwai ƙwayar halittar dake haddasa ciwon da alamominsa da kuma matakan cutar a jikin 'dan adam. Sunayen cututtukan da turanci suna da yawa kamar yawan cututtukan. Cutar sida/ƙanjamau (AIDS/HIV) tana daga cikin manyansu saboda itama anfi yaɗata ta jima'i, kuma sau dayawa itace ke gayyatar sauran cututtuka a jikin 'dan adam.

3) KANKANCEWAR ZAKARI, duk da dai cewa babu wani sahihin bayani a kimiyyance dake nuna cewa ciwon sanyi yana sa azzakarin namiji baligi ya koma ƙarami, akwai rahotanni da yawa daga mutane na ƙorafin cewa sanyi ya sace musu girman zakari. Wannan zance haka yake a zahiri, masu ciwon sanyi sune suka fi lura da damuwa akan ƙanƙancewar alƙalummansu.

Wasu daga cikin cututtukan sanyin da ake samu ta jima'i da ƙwayoyin halittu wanda ke haddasa su (a yaren turanci):

a) CHANCROID (bacteria) , cuta ce wacce ke zuwa da yanayin gyambo wani lokacin tare da ƙululu a hantsa.

b) CRABS (parasite), 'yan ƙananan halittu sosai , yanayin kwalkwata, masu cizo da tsotsar jini mai sanya mugun ƙaiƙayi. Ana samunsu daga gashin mara inda suka maida gidansu, ana kuma iya ɗaukarsu daga gashin gaban wani mutum zuwa na wani lokacin jima'i. Ana kuma iya samunsu ta kayan sawa, gado da sauransu.

c) GENITAL HERPES (virus) , cuta wacce take zuwa da ƙuraje masu ɗurar ruwa a baki ko kan zakari, ƙurajen masu kama dana zazzaɓin dare (fever blisters). Idan ƙurajen suka fashe sai su zama gyambo. Haka kuma za'a iya samun ƙurajen a ɗuwawu, cinyoyi, ko a dubura. Ciwon kai ko baya, ko mura (flu) mai ɗauke da zazzaɓi, ko kaluluwa da raunin jiki/kasala.

d) SYPHILIS (bacteria), anfi samunta wajen 'yan luwaɗi. Tana da matakai bayan shigarta a jiki. Misali, matakin farko (1): fitowar wani irin gyambo (chancre), wannan gyambon shine wajenda cutar ta shiga jikin mutum. Gyambon mai tauri, mai zagaye marar zafi. Wani lokacin abuɗe yake kuma da lema, ko zurfi musamman a hular zakari, wanda zaka ga wurin ya lotsa. Ana samunsa a zakari ko dubura ko leɓe (a baki). Ana kuma iya samun gyambon a ɓoye wani wajen cikin jiki. Mataki na biyu (2): ƙuraje a tafin hannu ko ƙarkashin tafin ƙafa ko wani sashen na jiki. 'Yar mura, zubar gashi, zazzabi marar tsanani, kasala, murar maƙoshi, ciwon kai ko ciwon naman jiki da sauransu. Mataki na gaba: mataki na gaba ko ƙarshe shine wanda cutar zata iya ɓoyewa a jiki, 'buya idan ba'a magance taba, kuma zata iya sanya ƙululun kansa/ciwon daji (tumour), makanta, mutuwar sashen jiki, matsalar ƙwalwa, kurumta, ciwon mantuwa mai tsanani (dimentia). Ana iya magance cutar cikin sauki da idan an lura da ita, da wuri, da yardar Allah.

e) DA SAURANSU, suna da yawa kuma alamomin wani ciwon na kama da na wani ciwon wani lokacin. Don haka bincike a asibiti shine zai nuna nau'in ciwon.

Ciwon sanyi yana da haɗari sosai. Ya zama dole ga mutane su tsaya ga matan su na Sunnah idan har suna son lafiyarsu. Ciwon sanyi yana nan akan hanyar mai neman mata da zinace-zinace, zai cimmasa. Akwai ciwuka masu haɗari sosai kamar AIDS/HIV, wanda zasu iya wargaza iyali. Don haka maison zaman lafiyarsa da rayuwa mai kyau sai yaji tsoron Allah. Wanda kuma Allah Ya jarabta da ciwon bata hanyar zina ba to sai ya nemi magani, haka shima wanda ya tuba ga Allah. Allah Ya bawa Musulmi lafiya.

Domin neman ƙarin bayani ko neman magani/waraka sai a

 kira +234808 402 8794 

 domin neman taimako na musamman daga cibiyar mu ta kiwon lafiya ta Musulunci mai albarka da mutane. Za'a iya tura maka magani ta motar haya, DHL ko speed post (NIPOST) zuwa garin da kake bayan biyan kudin magani ta account din Madinah Isl. Med. (Corporate account). Allah Ya taimaka.
Shafin mu na yanar gizo :
www.madinahislamicmed.blogspot.com
E-mail: madinahislamicmed@gmail.com

Adreshin mu: Sai a ziyarci cibiyar kai tsaye dake garin Katsina, Jihar Katsina, Najeriya-

Adreshin ofis: No. 34 Sabuwar Unguwa Dandagoro, Katsina.

LIKE our Facebook page domin samun bayanan lafiya shigen irin wadannan masu muhimmanci:

https://mobile.facebook.com/MadinahIslamicMedicine
YI DOWNLOADING APPLICATION (MANHAJA) NAMU A PLAY STORE (LIKITAN ISLAMIC CHEMIST) MAI DAUKE DA BAYANAI MASU MUHIMMANCI IRIN WADANNAN NA SAMA:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.andromo.dev679836.app866696
Share:

TATACCEN BAYANI GAME DA CORONAVIRUS


TATACCEN BAYANI A KAN CUTAR SARKEWAR NUMFASHI (CORONA VIRUS) A MAHANGAR MUSULUNCI.

Daga Ash-sheikh Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar lemo.

Babban Malamin addinin musuluncin nan, Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar lemo (Allah Ya kara masa lafiya da albarka) ya ja hankulan al'ummar musulmi dangane da cutar nan ta sarkewar numfashi (Covid 19) da ta addabi duniya a halin yanzu.

Babban Malami ya gabatar da wannan Jawabi ne a Majalisin sa da ya saba gabatar da karatu a dukkan ranakun Laraba, a Masallacin Cibiyar Imamul Bukhari dake Unguwar Rijiyar Zaki a cikin birnin Kano.

Ga bayanin da Babban Malamin ya gabatar a takaice:

Zan yi amfani da wannan dama kafin mu fara karatu domin tunatar da Y'an uwa musulmai a kan yanayin da duniya take ciki a halin yanzu na afkowar cutar nan da ake kira da (Corona Virus).

Mu duba mu gani yadda wannan Ya'r karamar kwayar halitta ta cuta, wacce ko da abin hangen nesa (Microscope) sai an kura ido sosai ake iya ganin ta, amma gashi ta mayar da kowa gida, ta tayar da hankalin duniya, har kasashe masu tinkaho da karfin kimiyya da karfin tattalin arziki, da cigaba, hankulansu ya tashi! Lissafinsu ya birkice,Duk wani abu da suke tunkaho dashi bai iya amfanar dasu komai ba. Wanda wannan lallai shi zai nuna maka karfin ikon Allah, zai nuna maka babu wani wanda ya isa gaba ga Allah.

Mu al'ummar musulmi ga matsayar da ya kamata mu dauka dangane da wannan cuta:

(1) Kallon da musulmi ya kamata su yi wa wannan cuta daban yake da na kafirai, haka a cikin musulmai din ma, mai karanta Alkur'ani da Sunnar Annabi (S.A.W) kallon da zai yi mata daban yake da na wanda ba ya karantasu. Mu musulmi mun yi imani da Kaddara, duk wani abu da ya faru to dama chan Allah Ya san da shi, kuma bai faru ba sai da ganin damar Allah, saboda babu abinda ke gudana a cikin Mulkin Allah sai da izininsa sai da saninsa. (Malamin ya ambaci ayoyin Alkur'ani mai girma a kan haka)

(2) Mu musulmi mun sani cewa ba wannan ne farau ba, ba yanzu aka fara samun irin wannan annoba ba, Allah Ya sha aiko da azabarsa ga al'ummomi da suka gabace mu, saboda sun kangarewa tafarkinSa, sai Allah Ya aika musu da annoba iri daban-daban, misali: mutanen Fir'auna Allah Ya aika musu da annoba iri-iri, kamar annobar ambaliyar ruwa, annobar jini, duk abinda suka bude sai suga ya zama jini, annobar fãra da kwarkwata. A karshe kuma Allah Ya halakar dasu, haka mutanen Annabi Nuhu kafinsu, Allah Ya aiko musu ambaliya ya halakar dasu, haka mutanen Annabi Lud Allah Ya kifar dasu suka halaka baki daya.

(3) Duk da cewa ita wannan al'umma ta Annabi (S.A.W) Allah Yayi alkawarin ba zai tumbuketa Ya halakar da ita baki daya ba, idan da Allah Ya so haka din tabbas zai iya, irin wadannan musibu sun isa shaida a kan haka, to amma Allah sai ya aiko da irin wannan annoba domin jan kunne da kashedi ga bayi. Yayin da annobar tazo kuma bata banbance salihi nagari da na banza, kowa hadawa take dashi, sai dai tana zama Rahama ga Salihai, azaba kuma ga fandararru.

(4) Daga cikin darasin da ya kamata musulmi ya lura dashi a kan sha'anin wannan cuta, mu duba mu gani, a lokacin da Dan adam yake tutiya, yake tunkaho cewa ya mallaki ilimi, ya mallaki karfin tattalin arziki, wasu har suna ganin Allah ma baya yi musu komai, su sun isa, su sune!!! Kwatsam sai ga wata Y'ar karamar halitta daga halittun Allah, wacce ido ma baya iya ganinta saboda tsabar kankantar ta, sai gashi ta baza duniya, ta bazama manyan kasashe, tattalin arziki yana ta rushewa, kowa ya firgita. Lalle wannan ya isa wa'azi! Wannan ya isa shaida akan girman Allah da karfin mulkinSa.

(5) Mu musulmi mu sani cewa babu abinda zai yaye mana wannan annoba illa kadai mu koma ga Allah, mu guji dukkan abubuwanda ke janyo Allah Yayi haka ga al'umma, kamar manyan laifuka, Zinace-Zinace, Zalunci, Barna a bayan kasa.

(6) Mu sani cewa komawa ga Allah shine matakin farko domin magance wannan annoba, duk wani abu da ba wannan ba ciko ne, amma komawa ga Allah shi ne Jigo. Mu koma ga Allah da yin addu'oi da yin istigfari.

(7) Mu sani cewa lalle babu wata musiba da wuce a jarrabeka a cikin addininka, yau gashi ana ta rufe masallatai, ana hana fitowa sallar Jam'i, har sallar juma'a da yawa daga kasashe sun bayarda sanarwa a dakata sakamakon wannan cuta. Lalle wannan abun tsoro ne! Kamar Allah Yayi fushi da mutane ne yace: Ku fita ku bar min dakuna na (Masallatai) tunda barnar ku a bayan kasa tayi yawa. Babbar musiba ce a rabaka da dakin Allah, a ce babu Umarah, babu Dawafi, babu sallar jam'i, lalle babu musibar da tafi musiba a cikin addini. Tabbas Allah Yana fushi da mutane, Ya zama wajibi mu koma mu tuba ga Allah.

(8) Musulunci ya yarda da tsarin killace marasu lafiya, da kuma tsarin kare kai daga cututtuka, musulunci shi ya fara zuwa da irin wannan tsari. (Malamin ya ambaci Hadisi a kan haka) amma kuma a musulunci munyi imani da cewa zama da mai cuta ba shi ke janyo kamuwa da cuta ba har sai idan Allah Ya hukunta haka, cuta a karan-kanta bata da ikon shiga tayi tasiri a cikin mutum sai da ganin damar Allah. ita cutar sababi ce, sababi kuwa baya aiki a karan-kansa sai idan Allah Ya kaddara, mu duba mu gani, wuta a al'adarta tana kona mutum, amma Annabi Ibrahim da aka jefa shi a wuta sai Allah Ya sa wutar taki kona shi, mu duba ruwa yana dulmiyar da mutum, amma sai Allah Ya sa Annabi Musa da mutanensa suka taka saman ruwa suka wuce ba tare da sun dulmiya ba, saboda haka ko da abu sababi ne, Allah Yana iya zare sababiyyar yaki yin aiki. A musulunci mun sani cewa duk abinda ya sameka ba zai kubuce maka ba, duk kuma abinda ya kubuce maka ba mai samunka bane. Kamar yadda Annabi (S.A.W) Ya fadawa Abdullahi Dan Abbas.

(9) irin wannan annobar an sha yinta a baya, a lokacin Sahabbai an samu annoba da tayi sanadiyyar rasuwar wasu daga cikin Sahabbai, kamar: Mu'az bin Jabal, da Abu Ubaida bin Aljarrah da sauran su, wannan ya faru a shekara ta (18) bayan Hijra. 

Haka nan akwai annobar da aka tabayi inda tayi sanadiyyar mutuwar Y'ayan Anas bin Malik kusan mutum saba'in (70), da Ya'yan sahabi Abu Bakrata kusan Mutum arba'in (40). 

(10) Na daga cikin abinda zai magance irin wannan annoba, gujewa aikata Zalunci, danne hakkin mai hakki, wajibi ne shugabanni su riki yin adalci su guji yin zalunci, domin zalunci sababi ne afkawa irin wannan masifa.

A karshe Malamin yayi addu'a mai ratsa zukata, inda Ya roki Allah da Ya yaye mana wannan masifa ba don halinmu ba, Allah Ya dube mu da Rahamarsa da Ludufinsa ya kawo mana agaji.

Wadannan bayanai an tatattaro su ne a takaice daga jawabin babban Malamin, mai bukatar cikakken jawabin sai ya nemi karatun littafin (Alwabilussayyib) darasi na 149.

Mai rubutu:
Musa Muhammad Dankwano.
Secretary, Dr. Muhd Sani Umar R/lemo Academic Forum.

Allah Ka sakawa Malam da alheri, Ka kare duniya daga sharrin wannan cuta Amin
Share:

HAIHUWA A SAUƘAƘE IN SHAA ALLAAH


'HAIHUWA ASAUƘAƘE' Daga bakin SHEIKH MALAM YAHAYA ISHAQ. 

RAGE YAWAN LAULAYI:- Babu wani magani dayake hana laulayi gabaɗaya face sai sai asami sauƙin hakan. Da Farko za'a sami BAƘIN ZOƁO, KANUNFARI, GARIN CITTA kaɗan, HABBATUSSAUDA, Sai a tafasasu, atace, ruwan sai asa Zuma, ta rinka sha kaɗan kaɗan..... Wannan zai rage mata yawan kasala da amai. 
  GA MACEN DA TAKE YAWAN JIN TASHIN ZUCIYA BAYAN TACI ABINCI :- Ta sami CITTA kaɗan ɗanya, saita rinka ɗan taunawa tana tsotse ruwan. InshaAllah wannan zai kashemata wannan tashin zuciyar. 

YAYIN DA CIKIN MACE YAKAI WATA 3 KO 4:- Anaso ta yawaita cin AYABA, Sannan ta kiyaye waɗannan abubuwan::-
1. Ta daina zama kanta Babu ɗankwali ko hula, Dominkuwa alokacinne shaiɗanun Aljanu ke barazanar shiga jikinta, donsu cutar da abinda ke cikinta. 

2.Ta daina zama a tsakar gida jikinta abuɗe. 

3. Ta daina zama aiki goshin magariba, duk abinda take da zarar ankira sallar magariba ta dakatar koda kuwa lokacin bata Sallahne, duk da zaiyi wiya kasami irin hakan, Amma akwai wasu matan masu irin hakan. To saita bari bayan magariba sai tacigaba da aikinta. 

4. Ta kiyayi kallon kaɗe-kaɗe, raye-raye da waƙoƙin zamani. 

5. Ta kiyayi wasannin banza da irin raye-rayen zamani da wasu abubuwan da matan banza sukeyi. 

6. Ta rinka tsabtace jikinta da ɗakin da take, tanasa karatun Al-Qur'ani mai girma. 
7. Ta cire hotunan dake liƙe/rataye/kafe acikin ɗakinta. 

LOKACIN DA CIKIN MACE YAKAI WATA 6::- Anaso tayi amfani da LUBBAZZAKAR, KANUNFARI, NA'A-NA'A, DA GANYEN ZAITUN, ta rinka tafasasu tanasha ;sukansu malaman tsubbu cewa sukai matar data saba shan waɗannan abubuwan a cikinta da ɗanta, to Insha Allah zata haifi yaro/yarinya ya zama haziƙi, Sannan ita kanta zai amfaneta, kuma shannasu zai zamto yana wankemata zakin jikinta, ɗan da zata haifa zaizo lafiya. Ƙalau. 

LOKACIN DA CIKIN MACE YAKAI WATA 7 KO WATA 9 (Duk ana iya haihuwa).  
   ABUBUWAN DAYA KAMATA ATANADA KUSA DA ITA SUNE:::-ZAM ZAM, HIJIRATUL MARYAM wanda akafi sanida(HANNU), DABINO, RAIHAN Wato (ƊAƊƊOYA) Suna da matukar muhimmanci. Kuma suna taimakawa wajen samin sauƙin haihuwa. Akwai matar da take naƙuda 1week, wata 5days, wata kuma tana daukar tsawon lokaci, Abinda akafiso a al'adunmu na hausa, shine mace ta haihu da kanta, amma da yawa Turawa ko Larabawa sai asami mace tai haihuwa 10 amma duka dazarar ta fara naƙuda sai akaita asibiti amata CS aciro ɗan. Su hakan al'adarsuce. 

ALOKACIN DA MACE TA FARA NAKUDA AKWAI WASU ADDU'OI DAYAKAMATA TARIƘAYI(inzata iya) DA KUMA MAGUNGUNAN DA MUSULUNCI YACE TAYI AMFANI DASU KAMAR HAKA. 

   ƁANGARAN ADDU'OI ::-Kisami Zam-Zam, sai asami kwano mai tsafta ajuye ruwan aciki, Sai a karanta waɗannan ayoyi masu zuwa ƙafa bakwai-bakwai(7)

1. Ayar ƙarshe ta cikin 'Suratul Yusuf' wato:(LAQAD KANA FIIQASASIHIM IBRATUN LI'ULEE ALALBABI MA KANA HADEETHAN YUFTARA WA LAKIN TASDEEQA ALLATHEE BAYNA YADAYHI WATAFSEELAKULLI SHAY'IN WA HUDAN WARAHMATAN LIQAWMIN YAWMIN NUNA(7) Sannan za'a karanta 

2.Ayar karshe ta cikin SURATUL AHQAf. Afara daga KA ANNAHUM.. HAR ƘARSHENTA Wato ::-(KA ANNAHUM YAWMA YA RAWNAMAA YU'ADUNA LAM YALBATHU ILLASSA'ATAN MINNAHARIN BALAGHUN FA HAL YUHLAKU ILLA ALQAWMU ALFASIQUUN. kafa(7). 

3. Ayar ƙarshe ta cikin SURATUL NAZI'AT wato(KA'ANNAHUM YAWMA YARAWNAHA LAM YALBATHUU ILLA'ASHIYATAN AWDUHAHA. kafa(7). 
  Sanna inzata iya lokacin da tafara najin nakudar tayi AlWALA, sannan inzata iya saita rinka karanta wannan addu'ar:- ALLAHUMMA LAASSAHALA ILLAMA JA'ALTAHU SAHALA WA'ANTA, TAJ'ALA KUB IZAHI SAHALA.  


ƁANGARAN MAGANI::- Asami HIJIRATUL MARYAM (Hannu) a jikashi aruwa minti kaɗan inyayi sai abata tasha.
  Sannan ana amfani da RAIHAN(Ɗaɗɗoya) itama jiƙata akeyi sai asha. Dukkan waɗannan abubuwan suna taimakawa sosai.  
""Kuma InshaAllah yanda kikasan zare gashi acikin mai haka zata haihu lafiya". 

BAYAN MACE TA HAIHU:-
1. Wata tana samin matsalar ɓallewar jini, to ta sami DABINO mai bauri, wannan sunnace mai ƙarfi tunda NANA MARYAM tayi amfani dashi. Saiki sami DABINO mai bauri saikici, jini bazai ballemikiba InshaAllah. Ko kuma ki sami NONON RAQUMI kisha, jini bazai ɓallemikiba InshaAllah.  

2. Wata tana samin irin kumburin cikinnan, saikaga cikinta ya girma sosai, :Tota sami NA'A-NA'A da KANUNFARI saita tafasa tasaha. Wannan zai hana miki wannan kumburin cikin. 

MIJINKI BAYANAN KIN HAIHU YAZAKI:! Kina haihuwa aka yankewa yaro/yarinya cibiya aka mai wanka, abinda yakamata kiyi shine::Ki daukeshi da kanki, ki abinda Manzon Allah (SAW) yayi lokacin da NANA FAƊIMA wato Ɗiyar annabinmu Muh'd (SAW) saiya umarci su NANA ZAINAB dasu ɗaukoshi, bayan an miƙo masa jaririn saiya karantamasa AYATUL QURSIYYU, Ya kuma karantamasa AYata 54 acikin SURATUL AL-ARAF wato(INNA RABBUKUMULLAHULLAZII KALAQASSAMAWATII WAL ARDI FII SITTATI AYYAMI THUMMASTAWA ALAL ARSHI........... har izuwa ƙarshen ayar. 
 Idan bazaki'iyaba ki karanta AYATUL QURSIYYU kawai
2.saikimai kiran sallah akunnensa na dama
3. Tada Hiƙama akunnensa na hagu... Amma awata ruwayar ance kiran sallah kawai yaymasa akunnensa na dama, wata ruwayar kuma ance Annabinmu (SAW) yayimasa akunnensa na dama dakuma na hagun. Wallah a'alamu. 
4. Saiki ambaci sunansa kice Sunanka...... Misali kice Sunanka Muhammad basai ranar sunaba, saiki tauna DABINO saikiɗan buɗe bakinsa saikisamai, abinda akafiso kenan yaro yafaraci arayuwarsa kenan, sannan sai ki samasa Albarka. Sannan kullum kirinƙa yiwa ɗanki addu'oin kariya. Wato kice U IZUKUMA BI KALMATILLAHI TAMMAT, MIN KULLI SHAIƊANUN WA HAMMAH, WA KULLI AYNIN LAMMAH. Saiki tofa ki safe jikin ɗanki dashi.
Share:

ILLOLIN CIWON SANYI (INFECTION)

ILOLIN CIWON SANYI(TOILET INFECTION)

 

Bayan haka nazabi yin wannan bayaninne ganin Kusan yawanci mata na fama da wannan cuta ta infection yazama ruwan dare yanzu ga mata harda mazan.

Infection Kala kalane amma Wanda yafi damun mata yanzu shine yeast infection.

Yakamata mace ta kula da kanta sosai da kuma tsaftace jikinta da mahallinta Dan ganin ta kubuta daga wannan cutar

 

*ILLOLIN INFECTION GA MATA*
1: Rashin aihuwa domin yana haifar da kuraje abakin mahaifa da haka har ya toshe mahaifar

2: yawan ciwon Mara Mai tsanani.

3: rikicewar Al'ada da.
ya kuma maida jinin Al'adar tazama baqiqqirin.

4: fitan farin ruwa Mai wari da kaikayi.

5:Jin zafi Yayi saduwa kokuma bayan saduwa adinga ganin jini na fitowa.

6: yanasa yawan barin ciki.
7: yakan sa mace ta dinga jin Abu na motsi acikinta alhalin ba cikine garetaba.

8 : yakan maida gaban mace ta qanqance Sannan ya dinga jin zugi ta cikin al'auranta.

9: yana tafiyar da ni'imar mace kwata-kwata kuma ya hanata jin sha'awa.

10 : yanasa yawan zubar jini Ko ruwa ko wani Abu dusa dusa kaman awara.

*ILLOLIN INFECTION GA MAZA.*
1: qanqancewa Al'aura 
2 Rashin sha'awa.
3: saurin Yin inzali.
4: yawan fitan ruwa 
Da sauran su 
5: yana stinkar da maniyi ta yanda bazata iya Yin amfani ba.

 

*ABUBUWANDA KE KAWO INFECTION*
1: Rashin sanya pant
2: barin always ajiki ya Dade alokacin Al'ada (musamman ultra pads Yakamata mata su kiyaye amfani da shi). 
Inzaki lura alokacinda jini ya jima a kan pad seya canza Kala yakoma Kore amaimakon ja to chemicals dinda ke cikine ke sa haka haka kuma zai tafi har cikin mahaifa se a kiyaye.

3: Barin pant Mai datti ajiki Anason Mace akalla ta canza pant sau biyu arana.

4: Saka pant a jiqe.

5: yawan tsarki da ruwan sanyi Ko Mai zafi sosai 
Rashin aski.

6:Wasa da gaba.

7:yawan cin danyen Albasa.

8: Yin amfani da magungunan mata /maza. Mara inganci.

9: Dade akan Masai

10:Saduwa da Mai cutar

11: zama akan Masai Ko toilet immediate lokacin da aka bude ( anfison inhar toilet a rufe ne in anbude kar a tsugunna atake Adan barshi tukun.

 

*SHARADI*
anason Mai magance wannan ciwon akalla ta dau watanni 3 zuwa 6 tana magani nanne zata warke kwata-kwata sannan 
Yazama mijinta Shima zaiyi wannan maganin kokuma ya Dena saduwa da ita har seta Fara samun sauqi musamman ga Wanda nata ke sata kuraje Ko zuban jini da fidda farin ruwa mai wari. Amma inta samu sauki zasu iya saduwa amma ana ci gaba da maganin har watannin su cika.

Shiyasa zakuga yawanci abinda ke hana mutum warkewa kenan ba'a maganceshi ya warke kwata kwata se anyi magani in andan Fara sauqi abari bayan wasu lokutan kuma yadawo kokuma ita mace ta magance nata na mijin bai warkeba dole in an sadu cuta tadawo. Kokuma Nata ya warke amma na Dayan bai warkeba ga wayanda suke su biyu ga mijinsu kenan Ko fiye da haka . Se asan yanda za'abi Dan ganin kowa ya maganceshi.


yanadaga cikin abinda yasa infection ya ke yawaita.

Sannan Akwai wani infection Wanda jinjul Ashiq ke sawa mace musamman macen da ke mafarkin ansadu da ita. To inhar ta bi wayannan hanyoyin da kuma lokutan amma baka warkeba to seta nemi maganin Jinjul Ashiq.

Share:

MAGNIN TASHIN ZUCIYA

MAGANIN TASHIN ZUCIYA

 

ZUCIYA:Wani sashe ne daga cikin jikin halittu imma mutum,aljan ko dabbobi.Zuciya Na taka muhimmiyar rawa a cikin rayuwar halittu,hakan yasa idan ta samu matsala kuma zasu shiga mummunar matsala.

 

TASHIN ZUCIYA
Mafiya yawan mutane suna fama da matsalar tashin zuciya hakan ya ankarar dani akan nemo mgn wannan matsalar ga masu fama da ita.
Mai fama da wannan matsalar zai samu:

*lemun tsami (lemon)
*ruwan ruman
*kaninfari
*ruwan albasa
*ruwan tsamiya
Za'a hadesu guri daya a dinga sha.Allah yasa mu dace

 

 MAGANIN TASHIN ZUCIYA

 

ZUCIYA:Wani sashe ne daga cikin jikin halittu imma mutum,aljan ko dabbobi.Zuciya Na taka muhimmiyar rawa a cikin rayuwar halittu,hakan yasa idan ta samu matsala kuma zasu shiga mummunar matsala.

 

TASHIN ZUCIYA
Mafiya yawan mutane suna fama da matsalar tashin zuciya hakan ya ankarar dani akan nemo mgn wannan matsalar ga masu fama da ita.
Mai fama da wannan matsalar zai samu:

*lemun tsami (lemon)
*ruwan ruman
*kaninfari
*ruwan albasa
*ruwan tsamiya
Za'a hadesu guri daya a dinga sha.Allah yasa mu dace

 

 

Share:

AMFANIN BISHIYOYI GA ƊAN ADAM


1. ASAWAKI
Asawaki yana maganin mashashara, ciwon kai, asma, tsutsar ciki, da mugun tari.

Related image

2. KUKKUKI
Kukkuki yana maganin tari, majina, da mashashara.

3. KAMOMOWA
Kamomowa tana maganin chizon maciji da jimuwa.

4. GWAIWAR RAKUMI)
Gwaiwar rakumi yana maganin jimuwa, ciwon ido da ciwon ciki.

5. DUKKI
Dukki yana maganin amosanin kashi, ciwon kai da rashin haifuwa, kurajen zafi, ciwon hauka, tsutsar ciki, rashin karfi da kullewar jini.

6. KURNA
Kurna tana maganin cizon maciji.

7. GORIBA
Goriba tana maganin fitsarin jini.

8. GIGINYA
Giginya tana maganin ciwon haure, ciwon huka, kuma tana kara karfin maza.

9. ZOGALA
Zogala tana maganin ciwon amosanin kashi, kurajen zufa, ciwon kai da gudawa.

Related image

10. TSADA
Tsada tana maganin ciwon kai, ciwon haure, mashashara, rashin kashi (Bushewar ciki) ciwon ido da ciwon kunne.

11. SHARANNAB
Saharannabi yana maganin mashashara.

12. BAGARUWA
Bagaruwa tana maganin majina, ciwon haure, tana karin namiji.

13. AKWARA
Akwara tana maganin sanyin gaba, ciwon ciki, zawo, yoyon jini, bushewar ciki, da karin maza ko mata.

14. NAMIJIN BAGARUWA
Namijin bagaruwa yana maganin zazzabi, kumburi da ciwon fata.

15. GWAIBA
Gwaiba tana maganin zawo.

Image result for GUAVA TREE png

16. LALLE
Lalle yana maganin hawan jini, sanyi.

Image result for HENNA TREE png

17. TUWON BIRI
Tuwun biri yana maganin kuraje, da shawara.

18. DOGON YARO
Dogon yaro (Darbejiya) yana maganin ciwon ido, hawan jini, da ciwon dasashi.


Share:

AMFANIN SABARA GA ƊAN ADAM


AMFANIN SABARA GA DAN ADAM.

 

Ganyen sabara nataka muhimmanchi sosai arayuwar dan adan kawai rashin sanine da mafi yawanchin mutanenmu basuyiba domin hausawa nacewa magani agonar yaro amma ga kadan daga cikin amfanin sabara ga dan adam.

 

-A kasar Hausa, mata su kan yi amfani da ganyen sabara a sanda suka haihu, inda suke dake ganyen ta su yi kunun gero suna sha dan kara yawan ruwan nono da kuma inganta lafiyar ciki.

-Ana amfani da garin ganyen sabara dan warkarda ciwon daji waton cancer a Turance.

-Ganyen sabara na maganin kumburin jiki da kaikayin jiki.

-Ganyen sabara na maganin kurajen kazzuwa da kurajen fiska masu kaikayi da kuma zafin jiki dama na ciki.

-Ganyen sabara na magance tarin asima da kuma tarin tibi.

-A kan gauraya garin ganyen sabara da garin bawon bagaruwa dan a yi maganin kuna a jiki.

-A kan hada wasu ganyayyakin itatuwa da ganyen sabara a tafasa ko a dake a maida su gari dan a iya warkar da basir, gudawa, cututtukan ciki, farfadiya, ciwon gabobin jiki, hawan jini, kuturta da dai sauransu.

-A kan yi amfani da danyen ganyen sabara dana nunu sai a tafasa macen dake jego sai ta rinka surace da ruwan hakan zai ba ta lafiya da karfin kassan jiki da kuma rage kumburin jiki ko na kafafuwa dama jin ciwo a bayan haifuwa.

-Macen dake shayarwa za ta iya fake shan kunun sabara dan ta tsabtace nononta dama kara yawan ruwan mamma.

-A kan tafasa saiwar sabara sai a tace ruwan a sha da safe kamin a ci abinci dan kashe tsutsar ciki.

-Ana tafasa saiwar sabara da kuma kirya sai a rinka zama a cikin ruwan dan magance basir maisa kaikayin dubura da kuraje ga dubura kai har da basir mai tsiro.

-Ana amfani da sabara dan magance kurajen da suka yi lailayi a cikin baki ko harshe.

– Ana shan cokali daya karami misalin 5ml na garin sabara a cikin nono sai a sha a sanda ake fama da dan kanoma.

-A nasu tsarin maganin gargajiyan, Sudan su kan yi amfani da ganyen sabara su yi maganin ciwon suga.

-Sabara na maganin amosanin kai da kuma iskan dake ma yawo a cikin jiki kamar tana.

-Ana tauna danyen ganyen sabara a hadiye ruwan dan magance kuraje a cikin wuya ko ciwon makogwaro da jin zafin hadiyar yawu. Wannan faida tasamo asali daga khalifa herbal medicine and marriage councelling.

 

SIRRIN RIKE MIJI

 

Ina budurwar da ko bazawara ko maccen da taji ta tsufa tana son aji ta dawo budurwa yar shekara 18 tana son taji far jin ta zai zai ya matse gashi gaban ta ya bude tana son dawo da martabarta domin gyaran farjin dinki batareda kinshiga cikin komaiba koyin tsuguno acikin komai ba

Kinemi wadannan abubuwan insha Allah zaki dace


1-Garin sansamin aduwa
2-Garin yayan bagaruwa
3-
Zuma sahihiya ta ainihi wacca batada hadin komai

Zaki hadasu gu daya kidinga shan cokali daya da safe dakuma dare kamin ki kwanta dakusan 15minutes ki kara

Suna wanke mahaifa sannan mahadar HQ naki ta ciki yakan Shiga tacikinsa ya wankesa tass tayarda idan maigidanki ya kusance ki zairasa shin awane matsayi zai ajiyeki azuciyarsa macen da ta kammala jego ma zata iya amfani da wannan hadin Allah ya taimaka mana ameen
Share:

YADDA MATA ZA SU RABU DA INFECTION HAR ABADA


YADDA MATA ZAA RABU DA INFECTION KWATAKWATA INSHA ALLAH   
kamfanin khalifa herbal medicine and marriage councelling munyi binciken cewa kashi tisiin bisa dari na mata na fama da wannan matsala kuma muna samon complain sosai akan wannan lalura saboda haka muka yanke shawarar taimaka yanuwa mata da yadda muke hada magungunan wannan matsalar indai akabita to insha Allah zaa rabu da infection kwata kwata da ikon Allah ga hanyoyin kamar haka.   
1- A samu Saiwar Garafuni da Sassaken Magarya, sai a tafasa, idan ya dan huce sai mace ta dinga kama ruwa da shi. Kullum sau daya. Yana maganin budewa da kaikayi. 
2- A samu Garafuni da Sassaken Sanya sai a tafasa, mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma. Ya na fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari. 
3- A samu Furen Tumfafiya, sai a shanya ya bushe, a daka a dinga zubawa a cikin Nono a na sha. Ya na magance matsalar ruwan infection. 
4- A samu Lalle da Ganyen Magarya da Kanumfari, a hada waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya dan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma. Yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba. 
5- A samu Kabewa a dafa ta, bayan an dafa sai a tsame daga ruwa a jajjagata ko a birga, a zuba Madara ko Nono sannan a sa Zuma a sha. Wannan yana mganin rashin sha’awa da bushewa da rashin gamsuwa.   
6- A dafa Zogale, idan ya dahu sai a murje shi ko a dama, a tace, a yi lemon juice da shi. Yana maganin fitar farin ruwa mai wari da cushewar mara kuma ya na kara ni’ima. 
7- A samu Dan-Tamburawa da Albabunaj a tafasa a zuba Man Hulba a ciki. Sai ta dan tsuguna tururin ya dinga shigarta. Idan ya dan huce kuma sai ta shiga ciki ta zauna. Zai magance mata kaikayi da kuraje kuma ya na sa matsewa. 
8- A samu Farar Albasa da Kanumfari da Citta da Malmo da Barkono da Raihatul Hubbi, sai ta da ke su ta yi yaji ta dinga cin abinci da shi. Ya na saukar da ni’ima da magance duk matasalolin sanyi. 
9- A samu Sabulun Zaitun da Sabulun Habba sai a daka su. A samu ganyen Magarya da Garin Bagaruwa a daka a tankade. Sai a zuba akan sabulan da aka daka sannan a kwaba da Ma’ul Khal, a zuba Man Tafarnuwa da Farin Almiski. Sai mace ta dinga kama ruwa da shi kullum sau daya. Da ruwan dumi amma ake tsarki da shi. Wannan Sabulu ya na maganin kuraje da kaikayi da fitar wari. 
10- A samu Man Zaitun da Man Habba da Man Tafarnuwa da Man Kanumfari sai a hade su waje daya. Mace ta dinga shan cokali daya kullum kafin ta karya. Ya na wanke dattin mara kuma ya na samar da ni’ima   
11- A samu Ciyawar Kashe-Zaki da Farin Magani sai ta hada waje daya ta dinga jika rabin karamin cokali ta na sha. Sannan ta dinga shan Man Zaitun Cokali daya kullum kafin ta karya. Wannan ya na maganin dattin mara da wanke daudar mahaifa. 
12- A bare tafarnuwa, idan za ki kwanta bacci sai ki dauki sala daya ki yi matsi dashi, ana son idan mace za ta yi wannan hadin to miji ya daga mata kafa wato kada ya kusance ta, Da safe sai ta tafasa garin hulba ta zauna a ciki zata yi hakan har tsawon kwana uku. 
13- Ki hada hulba da bagaruwa guri daya, ki dafa idan ruwan ya sha iska sai ki zauna a ciki, kuma ki samu man habbatussauda ki yi matsi da shi.    
SAKA ME GIDA SUMBATU

 

kisamu totuwar rake me tsafta ki busar da ita saki hada da
miski da kanunfari saiki hadasu waje daya ki dakasu ki
samu garwashin wuta kina zuba garin kadan aciki kina
tsuguno kibar hayakin ya ratsa gabanki sosai kisamu kamar
5minutes wannan hadin yana karawa mace dandanon jima i
sosai musammamn idan kin kasance me ni ima

GYARA GABANKI

 

ga wani sirri shikuma amfaninsa zaisa gabanki yaciko ma
ana mararki ta cika da ni ima sosai
sassaken baure sassaken gamji gishirin gallo dan kumasau
sai minannas sannan saiki samu hanta tattasai
yanda ake hadawa shine zaki saka hanta akan wuta sannan
ki saka sassaken da dan kumasau cokali daya gishirin gallo
rabin cokali ki saka tattasai sai minannas shima rabin
cokali sannan ki dafa sosai amma zaki iya saka kayan miya
duk yanda yakamta bayan ya dafu ki cinye gaba daya
wannan zakiyi mamakinsa idan kika hadashSAKA MEGIDA SUMBATU

wannan hadin bashida wahala amma kuma yana aiki 100%
kisamu sautar zogale sauyar kankana kununfari dukkansu
ki dafasu bayan sundafu saiki tace ruwan sannan kisamu
mazar kwaila da zuma ki saka sannan kimayar dasu kan
wuta sannan kibari ya dafu saiki juye kinasha safe da
yamma
2/ko kuma kisamu lemon zaki kamar guda biyu ko uku ki
matsesu akofi saiki zuba madara peak guda biyu ki saka a
freg yayi sanyi kisha
 

 

GYARAN GASHI

Ga hanyarda zakibi ki gyara gashin kanki cikin sauki
kisamu garin hulba ki zuba acikin ruwan lalle ki dafa ya
dafu sosai sannan saiki saukeshi kibarshi yayi sanyi sannan
ki samun sabulun h/sauda ki wanke kayin dashi sannan
saiki samu wadannan mayikan

 

1/man zaitun
2/man kwakwa
3/man alayyadi
4/man h/sauda
5/man sim sim
6/zautun lauz

duk wadannan mayikan zaki hadasu waje daya sannan kina
shafawa akai kisamu kamar wata guda ko fiye da haka...
Insha allahu gashinki zaiyi tsayi yayi laushi yayi bak

SHA YANZU MAGANI YANZU

 

idan kinaso lokaci daya ki jike da ni ima agabanki ki samu
kankana me yashi ki fereta kiyi mata kofa sannan ki daka
kanun fari ki zuba aciki saiki daka dabino bayan kin cire
kwallon shima ki zuba saiki samu kwallon kwakwa ki fasa ki
zuba ruwan aciki sannan ki rufe wannan kankanar kibarta
ta kwana idan kari ya waye saiki dauko ki shanye gaba
daya sannan ki cinye wannan kwakwar uwar gida wannan
hadin keda kanki zaki gane kin hadu


SIRRIN KARAWA MACE SHA AWA

akwai mata da yawa wanda zaka samu matan aurene
amma suna fama da karancin sha awa hasalima suna jima
ine bawai don dadiba sai dan raya sunnar manzan allah
(saw) amma ga wata faida wacce idan kikayi amfani dasu
zakiyi sha awar jima i sosai
kisamu danyen zogale ki markadashi saiki tace wannan
ruwan ki zuba masa kanunfari da zuma kinasha safe da
yammaMAGANIN RAKE TUMBI&KIBA

mutane da dama basusan yanda ake amfani da zogale
wajen rage kiba ko tumbiba yanda za ayi shine asamu
ganyensa a tafasa arinka shan ruwan kullum insha allahu
za ayi mamaki allah yasa adace


KARAWA MACE NI IMA

 

ki samu ganyen ugu ki matse ruwan a kofi ki fasa kwai
guda daya ki gauraya sosai acikin ruwan gwanda saiki
samu garin madara cokali biyu ki zuba sannan ki zuba
zuma cokali uku saiki samu lemun tsami ki matse rabinsa
saboda kada yayi karni ki gauraya sosai saiki shanye
kisamu kwan uku kina wannan duk bushewar gabanki
zakiga ni ima

INGANTACCEN MATSI

idan kinaso kimatse farjinki koda kin haufu farjinji zai dawo
kamar budurwa yar shekara16
Da farko kisamu lallenki me kyau ki kwabashi da zuma
farar saka ki hada ki matse farjinki dashi sannan kisamu
man zaitun da beby oil kidauko auduga kina dangwalowa
kina digawa acikin farjinki kuma kada kina tsarki da ruwan
sanyi kirinkayi da ruwan dumi musamman idan kinyi jima I
kuma kina tafasa bagaruwa kina tsarki da ruwan farjinki zai
kumburo ya burge me gidanki
Kokuma kisamu lalle gabaruwa ganyen magarya alimun
dan kadan domin idan yayi yawa akwai matsala saiki tafasa
saiki juye awajenda zaki iya shiga ki zauna acikin ruwan
kisamu minti20 saiki fita koda sau daya kikayi farjinki zai
matse musamman idan kin taba haifuwa zakiga yanda
farjinki zai matse kamar baki taba haifuwaba uwar gida a
gwada wannan
allah yasa adace


SIRRIN MATSI

Ga wani sirri wanda akasari larabawane suke amfani dashi

(1)kisamu kwallo mangoro
(2)Turaren miski
(3)Zuma
(4)Bawon ruman ga yanda ake hadashi shi wannan kwallon
mangoron dan cikin zaki cire ki shanyasu tareda bawon
ruman bayan sun bushe saiki takasu ki kwabashi da zuma
da turaren miski saiki rinka matsi dashi idan ya jima kadan
saiki wanke wannan zai saka gabanki ya matse yanda
kikasan budurwa kuma zaiyi santsi sannan kuma zai rinka
kamshi
Uwargida ki gwada wannan

 

AMFANIN KANKANA

uwargida kisamu kankana ki gyarta ki cire kwallayenta ki
samu dabino ki saka sannan ki markada kisamu zuma
cokali uku ki zuba sai madara da ruwa ki zuba kisaka a
furej yayi sanyi kisha saiki dauko bawon kankanar ki busar
dashi bayan kinyi wanka saiki turara farjinki dashi

 

KARIN NI IMA

Zaki samu ridi ki surfa ki dakashi sai kuma aya itama
kidaka amma saikin soya ayar sannan kihada da garin
cukwi kirinka saka cokali kamar3 acikin madara peak
kinasha wannan ya inganta yana karawa mace ni ima
sosai..
daga mana


KARIN NI IMA

Zaki iya yin shayin kara karfin sha awa da ni ima yanda
zakiyi shine kisamu sassaken baure ki dakashi saiki daka
kanunfari ki hada da lefton kinasha zakiyi mamaki
musamman idan ke matar aurece...


RAGE TUMBI

Mata da maza masu kato tumbi wanda yake hanasu dadin
saduwa sasu iya amfanida da KHAL TUFFA azuba aruwan
dumi arinkasha sau2 safe da yamma allah yasa adace...


YANDA ZAKI ZAMA MAI NI IMA KAMAR KORAMA

 

Kisamu sassaken baure ki dafashi sai bayan ya dafu sai ki juye ruwan sai kisamu bazar kwaila da zuma da kanunfari
da citta ki zuba aciki ki tafasa kirinka sha safe da yamma
hmm..zaki zama cakwala dadi..


KARIN MANIYI*

Wasu mazan suna fama da rashi maniyi amma ku gwada
wannan kasamu albasa guda biyu a yan yankasu a soya sai
bayan ta soyu sai ka kawo kwai ka zuba amma kada ka bari
ya soyu ka sauke kaci idan kana haka in sha allahu za kayi
mamaki..

 

SAKA ME GIDA KUKAN DADI

 

Ki samu totuwar raken da kika mai tsafta saiki barshi ya
bushe kisamu gabaruwa guda3 da almuski da kanufari ki
hadasu waje daya kirinka tsuguno kuma kirinka goga zaitun
awajen zakiga yanda mai gida zaiyi..

 


SIRRIN RIDI

Kisamu ridi mai kyau ki wankeshi ki nikashi ya koma gari ki
barshi ya bure kirinka sha da nonon zai miki amfani wajen
jima I da maganin dattin ma haifa...


KARIN GIRMAN NONO

wasu matan wanda daga sunyi haifuwa daya zakaga
nononsu ya zuba wannan yana saka me gida yayi miki
kishiya h/sauda hulba alkama gyada ridi danyar shinkafa
da busassen karas duk ki dakasu waje daya kina sha da
madara peak Awa2 kafin barci da kuma Awa2 bayan
barci...

 

KAMMALA JININ HAILA KIDAWO DAI DAI*

 

Kisamu zuma da garin tagargaje da almuski bayan kin
gama wanakan tsarki saiki debo garin tagargajen ki dama
acikin ruwa ki wanke gabanki dashi saiki dangwalo zuma ki
rinka sakawa acikin farjinki sai ki bari idan dare yayi saiki
dauko farin almuski ki kara shafawa acikin farjinki sannan
ki jira dare yayi zakiga yanda mai gida zaiyi...

 

BAKYA IYA GAMSARDA MIJINKI

Kisamu furen tunfafiya da yayan zogale da gero ki dakasu
lukui sannan kirinka sha da fresh madara daga ranar zaki
fara gamsarda mijinki har sai ya g

 

MATSI DA SANTSI

 

Idan kinaso mijinki yarinka jinki lutsulutsu kisamu lalle mai
kyau ki kwabashi ki hada da zuma ki saka farjinki sai ki
samu man zaitun da beby oil ki dauko auduga ki rinka
dangwalowa kina sakawa a farjinki wannan shine asalin
matsi mai saka mai gida kyauta bayan haka sai kisamu
kankana ki markadata ki hada da madara peak wannan
shine zaki zama mai dadin jima i..

 

RAGE GIRMAN NONO*

Ganyen lemun
zaqi Buhuru sudaniya.Ki hada ki
dakasu ki dinga shafawa a nonon ze
ragu amma ki rage shan madara
Ki dinga soya hanta da kitsen akuya
kina ci zasu ragu kuma bazasuyi girma ba.

 

SAURIN KAWOWA MANIYI*

Maza da dama suna bukatar jimawa awajen jima I amma
hakan baya samuwa saboda daga sunfara jima I zasuyi
riles amma ka gwada wannan kasamu garin h/sauda cokali
daya
Sai kasamu kwai guda uku sannan ka hadasu ka soya kada
ka bari ya soyu sosai insha allah za adace..ZAFI LOKACIN JIMA I

Rashin ni ima afarjin mace shiyake kawo mata jin zafi
lokacin jima I shi kansa mijin zafi yakeji to ki gwada
wannan kigani ki samu gero ki surfa ki hada da bazar
kwaila da kanunfari da man shanu ki saka ruwa ki dora
akan wuta ya dafu sosai saiki tace ruwan kisha.,hm lallai
ranar tun kafin dare zaki fara nason ruwa..

 

KI KARAWA KANKI DADI*

Kisamu dan bashana da gyadar mata da yayan kankana da
fara biya rana da yayan zogale da bazar kwaila ki hadasu
waje daya ki dakasu kirinka sha da madarar shanu zakiga
yanda me gida zaiyi...

 

SAURIN KWANCIYAR NONO

Kina budurwa kinaso kada nononki ya zuba kafin aurenki ki
daina saka damanmu kaya kuma babu brz ko kirinka tsalle
da sauransu kuma ki daina kwanciya rub da ciki ko kirinka daga zani sama kina damesu kuma rashin shan kayan marmari da rashin saka brz suma suna kawo saurin zubewar nono.

 

YANDA ZAKI KARAWA KANKI DUWAWU*

 

Tabbas maza suna bukatar mace ne kugu saboda yana
basu sha awa musamman awajen jima I to amma ga yanda
zakiyi kirinka shan kankana da latas (salak) kabeji zannan kirinka zama kusa da mijinki sanna idan kuna jima I yarinka shafawa ki.
Share:

ƘARFIN GABAN NAMIJI


KARFIN GABAN NAMIJI

Idan maigida yana da matsala wajen karfin gaba ma'ana karfina mazakuta wajan kwanciya jima'i ya nemi.

garin habbatus-sauda cokali 1

kwai guda uku ko biyu

Ana so kina zuba garin habbatus-sauda a cikin ruwan kwai.

kina gauraya wa so sai kina soyawa Amma fa karki Bari ya soyu so sai kina yi masa yana ci ko wane lokacin.

sannan yana da kyau ka yawaita cin kayan itatuwa ba maiko ba.

・ cocumber
・ zuma
・ ayaba
・ kankana
・ da sauran su.
 

MAGANIN BASIR

duk mutumin da yake shan wahala a bayan gida sabo da

basir wani ma sai ya zubda hawaye a samu.

Man zaitun

Garin habbatus-sauda.

kwaba wa 'Yan nan abubuwa sai a turashi a cikin duburar sa yana yin haka kamar kwana biyar ko goma.
Share:

RIGA-KAFIN CUTAR CORONAVIRUS

*RIGA-KAFIN CHUTAR CORONA VIRUS.* _(IN SHA ALLAHU)_

Binciken likitocin zamani har yanzu bai gano maganin wannan CHUTA ba. Sai dai binciken likitocin musulunci ya tabbatar da cewar wannan chutar bata iya tasiri aduk inda tafarnuwa take. 

Don haka Cibiyar Zauren Fiqhu ke bada shawara ga 'yan uwa musulmai musamman mazauna Jihohin da aka tabbatar da bullar wannan chutar cewa ku rika yawan amfani da tafarnuwa acikin girke-girkenku. 

Sannan ku nemo Kwayoyin tafarnuwar ku yankata Qanana ku rika hadiyarta kamar yadda ake hadiyar maganin asibiti. Da zarar ka hadiyi tafarnuwa acikin kankanin lokaci zata bi duk sassan jikinka ta yaqi chututtuka kuma tayi maka garkuwa. 

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (03/07/1441 28/02/2020).
Share:

MATSALOLIN CIWON SANYI GA MATA


ALAMOMIN CIWON SANYIN MARA NA MATA 

SANYIN MATA WANDA AKE YAƊAWA TA JIMA'I

 

Waɗansu daga cikin alamomin ciwon sanyin mata da ake samu ta hanyar saduwa da namiji ko mace mai ɗauke da ciwon : (STD/STI):

 

1. Fitar ruwa daga farji, ruwa mai kauri ko silili, kalar madara ko koren ruwa daga farji.

2. Kuraje masu ɗurar ruwa da fashewa a farji , musamman wurinda pant ya rufe.

3. Feshin ƙananan ƙuraje a farji ko cikin farji

4. Raɗaɗin zafi a lokacin yin fitsari

5. Jin zafi cikin farji lokacin jima'i

6. Zubar jinin al'ada mai yawa ko zuwan jinin al'ada mai wasa, wato akan lokacinda ya saba zuwa ba

7. Ciwon mara

8. Zazzaɓi

9 . Ciwon kai

10. Murar maƙoshi/maƙogwaro

11. Kasala/raunin jiki

12. Zubar jini lokacin saduwa

13. Dakushewar sha'awa, ko rashin sha'awa ko ɗaukewar ni'ima

14. Bushewar farji

15. Ƙaiƙayin farji

16. Warin farji (ɗoyi) mai ƙarfi

17. Kumburin farji da yin jawur

18. Gudawa

18. Ko rashin ganin wata alama daga cikin wadannan alamomin da muka bayyana a sama.

 

A can baya munyi bayanin ciwon sanyin mata na "toilet infection" (vaginitiies: Yeast infection & Bacterial vaginosis) wanda cutar sanyin mara ce wacce ba'a yaɗata ta hanyar jima'i - wato sanyin mara wanda mace bazata iya harbin mijinta da cutar ba, wanda akafi samu daga "toilet" (bandaki/bayan gari). Duk da haka , munyi bayanin wata nau'in cutar sanyi guda 1 (Trichomoniasis) a cikin waɗancan bayanan da suka gabata, wacce cuta ce da mace ka iya sakawa mijinta ciwon (STD). A wannan karon kuwa zamu yi bayani ne kaɗai akan ciwon sanyin mata wanda akafi samunsa ko yaɗawa ta hanyar jima'i (STD/STI).

 

Ciwon sanyi cuta ce da akafi yaɗawa ta hanyar jima'i, wato ta hanyar saduwa da mai dauke da ciwon, shiyasa ake kiran dangin cututtukan da turanci da suna SEXUALLY TRANSMITTED DISEASES/ SEXUALLY INFECTIONS (STDs/STIs), wato CUTUTTUKAN DA AKE YAƊAWA TA HANYAR JIMA'I.

 

Ciwon sanyi anfi yaɗasa ne ta hanyar jima'i kuma maza na iya harbin mata da ciwon ko kuma su matan masu ɗauke da ciwon su sakawa maza mararsa ciwon. Ciwon yafi yaɗuwa kuma anfi samunsa ga maza masu neman mata ko mata masu bin mazaje.

 

Haka kuma za'a iya samun cututtukan sanyi ta wata hanyar daba jima'i ba, kamar ta hanyar bada jini ga marar lafiya - jinin mai ɗauke da cutar sanyi daga wani mutum, ko haɗuwar jikin wani da wani - fata-da-fata ; wato idan fata mai ɗauke da cutar ta fashe zata iya harbin fatar wani mutum mai lafiya da cutar, ta jini ko ruwan jiki dake a jikin fatar mai cutar zuwa fatar wanda baya da cutar - wato idan akwai kafa buɗaɗɗiya komin ƙaƙantarta zuwa cikin hanyoyin jinin wanda baya da ciwon a fata zai iya samun cutar, misali ta hanyar sunbata (kissing) ko tsotsar al'aurar mai ciwon (oral sex), ko ta hanyar saka kayan sawar wata (pant) mai ɗauke da kwayar cutar mai rai, ko ta hanyar amfani da reza (razor blade) wanda wani yayi amfani da ita, rezar mai ɗauke da kwayar cutar mai rai, da kuma wasu hanyoyin na daban. Ataƙaice, ƙwayoyin halittun dake sanya cutar ana yaɗa sune daga wani mutum zuwa wani mutum, ta jini, maniyyi, ruwan farji ko ruwan jiki.

 

Alamomin ciwon sanyi ga mata sun sha banban tsakanin mata wanda ciwon ya harba. Hakan ya danganta ne da nau'in ƙwayar halittar cutar wacce ta haddasa ciwon da kuma matakin da cutar ta takai a jikin mace - ma'ana, alamomi ko matakin farko da kamuwar cutar ko alamomi na gaba bayan ta soma jimawa a jikin marar lafiyar. Haka kuma, suma yanayin alamomin sunsha banban ta fuskar tsanani ko sauƙinsu, koma rashin ganin alama ko ɗaya duk da cewa kau akwai cutar a jikin mace. A taƙaice dai, alamomin ciwon sanyin zasu iya ɓuya amma gwaji a asibiti zai iya nuna akwai cutar ko akasin haka.

 

Alamomin ciwon sanyi na " toilet infection " na iya kama da alamomin cutar sanyi da ake samu ta jima'i (STD/STI). Saidai banbancin shine hanyoyin samun cututtukan , kuma cutar sanyin "toilet infection" tafi saukin magancewa; ita kuwa cutar sanyin da ake yaɗawa ta jima'i (STD) nada wuyar magani da naci, musamman saboda wasu na'uin cutar daga kwayar cutar "virus" ne (kamar "syphillis" da "genital herpes"). Gwaji a asibiti shine zai iya nuna na'uin cutar da maganin da ya dace, imma "toilet infection" ko kuma cutar sanyin jima'i wacce tafi muni da wuyar magani.

 

MATSALOLIN DA CIWON SANYIN ZAI IYA HADDASAWA MACE:

 

a) RASHIN SAMUN JUNA-BIYU/ HAIHUWA: Cutar sanyi mai suna "Gonorrhea" (Gonoriya) , ƙwayar cuta ce daga halittar "bacteria" kuma zata iya laɓewa a cikin jiki ba tare da wasu alamomi ba. Itace mafi tsohuwar cutar sanyin da akafi sani. Gonoriya bata cika nuna alamun taba a jikin mace, musamman a matakin farko na shigarta cikin jiki, ba kamar ga maza ba wanda alamomin kan bayyana gare su . Mata da yawa basu san ma suna dauke da cutar ba a jikinsu. Duk da haka, tana iya zuwa da alamomi kamar fitar ruwa daga farji ko ɗan koren ruwa, mai kalar madara daga farkon cutar, yin fitsari da zafi da yawan yin fitsari, yawan zubar jinin al'adah, murar maƙoshi/maƙogwaro, jin zafi a farji yayin jima'i, da sauransu. Idan ba'a lura da cutar da wuri ba kuma aka magance ta, zata iya sanya rashin haifuwa ga mace ko namji. Tana shafar wani hangaren mahaifa da yi masa dameji, sai mace ta kasa samun juna-biyu.

 

Haka kuma itama cutar "Chlamydia" (kilamidiya), wacce kwayar halittar "bacteria" ke haddasata , na daga cikin game garin cutar sanyi wacce ke hana mace ɗaukar ciki. Hakan yafi faruwa idan mace nada cutar na tsawon lokaci ko kuma ta samu cutar wasu lokutta na rayuwarta da dama. Idan an gano cutar kuma an magance ta da wuri zai rage illa ga mahaifar mace a gaba. Cutar "Chlamydia" maɓannaciya ce da take illa a ɓoye kuma mafi yawanci bata nuna wata alama a zahiri ga mai ɗauke da cutar. Ana samunta bainar mata da yawa fiye da maza. Mafi yawanci bata nuna wata alama sai haddasa rashin haihuwa.

 

b) RASHIN JIN DADIN JIMA'I , ƊAUKEWAR NI'IMA , KO DAKUSHEWAR SHA'AWA KOMA RASHINTA

Sanyin gaba mai zuwa da 'yan 'kananan kuraje cikin farji , na sanya mace taji zafi wajen jima'i yayinda zakari ke kai-kawo cikin farji, wanda sau da yawa masu kurajen basu ma san suna da kurajen ba cikin al'aura, saidai suce suna jin zafi lokacin saduwa. Kurajen suna fashewa saboda da gugar zakari, sai wurin ya zama rauni. Hakan nasa mata tsoron jima'i da ganinsa abin azabtarwa gare su mai maimakon abin jin dadi. Sau tari basu san abinda ya haddasa zafin ba, wanda kuma mai yiwuwa ciwon sanyi. Ciwon sanyi na iya dakushe sha'awar mace ko namiji. Ciwon sanyi na iya haddasa bushewar gaba (vaginal dryness) wanda alamunsa shine daukewar ni'ima da 'kaikayin gaba. Idan gaba ya bushe zaiyi wahala mace da miji suji dadin jima'i in banda zafi.

Wasu daga cikin cututtukan sanyin da ake samu ta jima'i da ƙwayoyin halittu wanda ke haddasa su (a yaren turanci):

 

a) CHANCROID (bacteria) , cuta ce wacce ke zuwa da yanayin gyambo wani lokacin tare da ƙululu a hantsa.

b) CRABS (parasite), 'yan ƙananan halittu sosai , yanayin kwalkwata, masu cizo da tsotsar jini mai sanya mugun ƙaiƙayi. Ana samunsu daga gashin mara inda suka maida gidansu, ana kuma iya ɗaukarsu daga gashin gaban wani mutum zuwa na wani lokacin jima'i. Ana kuma iya samunsu ta kayan sawa, gado da sauransu.

c) GENITAL HERPES (virus) , cuta wacce take zuwa da ƙuraje masu ɗurar ruwa a baki ko kan zakari, ƙurajen masu kama dana zazzaɓin dare (fever blisters). Idan ƙurajen suka fashe sai su zama gyambo. Haka kuma za'a iya samun ƙurajen a ɗuwawu, cinyoyi, ko a dubura. Ciwon kai ko baya, ko mura (flu) mai ɗauke da zazzaɓi, ko kaluluwa da raunin jiki/kasala.

 

d) SYPHILIS (bacteria), anfi samunta wajen 'yan luwaɗi. Tana da matakai bayan shigarta a jiki. Misali, matakin farko (1): fitowar wani irin gyambo (chancre), wannan gyambon shine wajenda cutar ta shiga jikin mutum. Gyambon mai tauri, mai zagaye marar zafi. Wani lokacin abuɗe yake kuma da lema, ko zurfi musamman a hular zakari, wanda zaka ga wurin ya lotsa. Ana samunsa a zakari ko dubura ko leɓe (a baki). Ana kuma iya samun gyambon a ɓoye wani wajen cikin jiki. Mataki na biyu (2): ƙuraje a tafin hannu ko ƙarkashin tafin ƙafa ko wani sashen na jiki. 'Yar mura, zubar gashi, zazzabi marar tsanani, kasala, murar maƙoshi, ciwon kai ko ciwon naman jiki da sauransu. Mataki na gaba: mataki na gaba ko ƙarshe shine wanda cutar zata iya ɓoyewa a jiki, 'buya idan ba'a magance taba, kuma zata iya sanya ƙululun kansa/ciwon daji (tumour), makanta, mutuwar sashen jiki, matsalar ƙwalwa, kurumta, ciwon mantuwa mai tsanani (dimentia). Ana iya magance cutar cikin sauki da idan an lura da ita, da wuri, da yardar Allah.

 

e) TRICHOMONIASIS (parasitic organism) , cutar sanyi maisa warin farji, mace zata iya harbin mijinta da cutar ko mijin ga matar. Idan ya kasance miji nada wata mata ko yana neman matan waje masu cutar ko kuma macen ta taba saduwa da wani mutum mai cutar daya samo cutar daga wata mace, to akwai yiwuwar ma'aurata su samu cutar. Mazaje ba kaso suke sanin suna da cutar ba kasancewar alamomin cutar basu cika bayyana ga maza ba. Yawanci sai idan ciwon ya kama matan su suna cikin neman magani a asibiti suke gano suna da cutar. Wasu daga cikin alamomin cutar ga mata: zubar ruwa mai launin kore-da-dorawa - mai kumfa da wari, zafi wajen yin fitsari, rashin jin dadi wajen jima'i. Wannan cuta tana da hadari ga mace mai juna-biyu da abinda ke cikinta

 

f) DA SAURANSU, suna da yawa kuma alamomin wani ciwon na kama da na wani ciwon wani lokacin. Don haka bincike a asibiti shine zai nuna nau'in ciwon.

Ciwon sanyi anfi yaɗasa ne ta hanyar jima'i kuma maza na iya harbin mata da ciwon ko kuma su matan masu ɗauke da ciwon su sakawa maza mararsa ciwon. Ciwon yafi yaɗuwa kuma anfi samunsa ga maza masu neman mata ko mata masu bin mazaje. Haka kuma mutum zaya iya kamuwa da ciwon ta wasu hanyoyin na daban daba jima'i ba. Kuma lallai ciwon nada wuyar magani , musamman idan mutum bai samu magani ingantacce ba. Zai iya yin wuyar magancewa saboda rashin samun sahihin magani ko daɗewarsa cikin jiki ba'a magance ba. Sau da yawa zaka ga cewa mutane sukan sha magunguna domin kaiwa ciwon hari da sukar alluran likita amma hakan bai razana ciwon ba sai kaga yana wa mutane jeka-ka-dawo tsawon watanni koma shekaru da dama ba'a samu waraka ba.
Share:

ALAMOMIN BUƊAƊƊEN FARJI


ALAMOMIN BUƊAƊƊEN FARJI

 

Yanayin halittar farji tamkar robar danƙo ce wacce zata iya buɗewa idan aka yi mata talala, haka kuma zata iya komawa ta haɗe, wato ta tsuke bayan buɗewa. Tsokokin bangon farji masu motsi ne kuma zasu iya tsukewa ko buɗewa idan mace tayi yunkurin tayi hakan, wato idan ta motsa su ko matse su ta ciki. Buɗaɗɗen farji (loose vagina) ko buɗewar farji (vaginal looseness) wani yanayi ne dake shafar mata da yawa musamman lokacin juna biyu da kuma bayan haihuwa inda farji ke canza yanayin halittarsa ya ƙara girma, wato ya zama buɗaɗɗen wuri kasancewar naman dake zagaye da farji mai yiwa zakari zobe lokacin jima'i ya saki , tsokokin sun saki basu iya damƙar zakari yanda ya kamata lokacin saduwa.

 

 

Kamar dai yanayin halittar fatar jikin mutum, wasu mutanen fatarsu nada tauri kamar roba marar sauƙin budewa idan aka jata, wasu kuma fatarsu nada laushi da sauƙin yin talala idan aka jata, kusan haka itama halittar gaban mace take. Wurin haihuwa jinjiri na fitowa ne ta farji inda wurin ke buɗewa sosai domin jinjiri ya fito. Bayan wani lokaci da haihuwa farji na komawa ya tsuke . Duk da haka , farji ba zai taɓa komawa ba kamar yanda yake ada ko kamar na macen da bata taɓa haihuwa ba (ko budurwa) , koda kau anbi hanyoyin magani , farji zai zamanto ya ƙara girma kaɗan ko da yawa.

 

Yawan haihuwar mace, budewar gaba saboda tiyatar likita/ƙarin kofa a lokacin haihuwa (tear) da yawan yin jima'i yau da gobe, na daga cikin dalilan dake haddasa budewar gaban mace. Idan buɗewar farji tayi yawa yana zama kalubabale ga ma'aurata. Zaya iya zama matsala a rayuwarsu ta jima'i . Saboda wannan yanayi na sanya raguwar ɗanɗanon jima'i ga mace da mijinta koma ya hana macen jin ƙoluluwar daɗi (orgasm) lokacin saduwa. Dalilin faruwar haka shine , farji baya matse/riƙe zakari da kyau,

 

ta yanda za'a samu ɗanɗanon gugar fata-da-fata tsakanin ma'aurata biyu wanda jin wannan guga shine zai kai ma'auratan biyu ga gamsuwa mai ƙarfi a lokacin jima'i. Bugu da ƙari, wannan matsala na iya saka mace cikin damuwa da jin cewa bata amsa sunanta na cikakkiyar mace ba saboda bata jin dadin saduwa kuma bata iya gamsar da mijinta da kyau. Hakan kuma zai iya sanya maigidan ya ƙara wani aure domin biyan buƙatarsa. Hakika gamsuwar aure itace saduwa mai daɗi tsakanin ma'aurata da zata samar da soyayya da zaman lafiya mai ɗaurewa. Matsatstsen gaba (tight vagina) bakin gwargwado, yanayi ne mai kyau da zai iya ƙarawa mace gishirin soyayya mai ƙarfi tsakaninta da mijinta.

 

YAYA ZA'AI KI GANE CEWA KO KINA DA BUƊAƊƊEN GABA?

 

1. Mafi yawan mata masu fama da matsalar buɗaɗɗen gaba na fama da matsalar rashin riƙe fitsari , wato ɗigar fitsari. Digar fitsarin zata iya faruwa a lokacinda kika ɗauki wani abu mai nauyi, ko lokacinda kika yi dariya, tari, ko atishawa. Wannan alamace cewa mace nada budadden gaba.Yawan shekaru, yawan haihuwa , yawan jima'i, tiyatar likita (ƙarin kofa) ko wani rauni a gaban mace, ko tsayawar al'ada (menopause) saboda karancin sinadarin "estrogen" na iya sanya raunin tsokokin farji wanda daga ƙarshe zai iya haddasa buɗewar tsokokin bangon farji masu matse zakari .

 

2. Hanya ta biyu da zaki iya sanin ko kina da gaba mai faɗi itace: ki saka ɗan yatsanki guda (manuni) cikin gabanki sa'annan kiyi ƙoƙarin matse dan yatsan da tsokokin farjinki. Idan har ki gwada yin hakan kuma ya zamanto baki iya jin kina matse dan yatsan da farji to zaya iya zama kina da babban wuri. Bugu da ƙari, idan kika saka yatsa 2 ko 3, misali manuninki da kuma yatsan tsakiyar hannnunki (mafi tsawo) , kuma baki ji wata alamar bangon farjinki yana matse yatsun ba to yiwuwar itace kina da buddden farji.

 

3. Idan ya zamanto yana da wuya kamin kiji ƙololuwar dadi (orgasm)/kawowa lokacin saduwa. Yana iya yiwuwa alamar budadden gaba ne. Haka kuma, raguwar jin dadi ba kamar daba shima na iya zama alamar.

 

4. Idan ya zamanto mace tana wasa da gabanta domin biyan buƙatarta kuma tafi sha'awar ta saka wani babban abu a gabanta akan ƙarami - wato bata jin dadin ƙaramin abu idan ta saka a farji sai babba. Shima alamace cewa mace nada girman farji. A baya munyi bayani da tsoratarwa akan wasa da gaba. Yana da illa ga lafiya da rayuwar auren 'ya mace. Don haka sai a kiyaye.

 

5. Idan ya zamanto kina shan wahala kamin ki gamsar da mai gidanki wajen jima'i ba kamar daba.

 

6. Idan ya zamanto sai kin matse ko haɗe cinyoyin ki biyu sosai sa'annan kike jin dadin jima'i da maigidanki. Wannan ma yana iya zama alamar budadden gaba. Duk da dai cewa wani lokacin yana iya zamantowa mijin ne keda ƙaramar al'aura. Amma idan kamin haihuwarki babu wannan matsalar sai daga baya to sai ki zargi budewar gaba.

 

7. Idan ya zamanto kina jin ƙarar fitar iska daga farjinki lokacin da maigidanki yake saduwa dake , iskan kamar fitar "tusa" amma ba tusa bace (fanny farting) kuma babu wari. Iskan yana shiga yana fitowa lokacinda maigida yake kaikawo. Wannan alamace kina da budadden farji.

 

MINENE HANYOYIN TSUKE FARJI ?

 

Akwai hanyoyi da dama na matse gaba musamman bayan haihuwa wanda sun hada da hanyoyin magani, motsa jiki (exercise), tiyatar likita domin rage girman farji da sauransu. Wasu hanyoyin nada illa ga lafiya , wasu kuma hanyoyin basa da wata matsala ko hadari kamar dai yanda likitoci ke bayani. Wasu daga cikin hanyoyin:

 

1. Motsa jiki , hanyoyin motsa jiki na zamani domin matse gaban mace suna da yawa (such as kegel exercises) da sunaye. Motsa jikin ya shafi horo da mace zata iya bawa jikinta domin ya zamanto tsokokin gabanta masu motsi sun kara ƙarfi da tsukewa. Misali, wata kwararriyar likita a India Dr. Sangeeta Gomes ( Consultant Obstetrician and Gynaecologist) , ta nuna cewa mace zata iya inganta tsukewar gabanta idan tana yin motsa jikin dauke numfashi (breathing exercises). Zaki dauke numfashinki na tsawon 'yan daƙiƙoƙi (seconds) kadan sannan ki tsuke (tsokokin) farjinki matakam na tsawon wani lokaci a lokacinda kike mai dauke numfashin.

 

Za kiyi hakan a kowace rana, sau 10 ko 15. Zaki iya yin hakan a kicin lokacinda kike aiki, a ofis, a tsaye ko a zaune , a ko ina kuma a ko wane wuri bata tare da ma wani yasan abinda kike yi ba. Sa'annan zaki yawaita cin Ƴaƴan itatatuwa (kayan marmari) da abincin ganye (vegetables). Wannan ko shakka babu zai taimakawa mace wajen matse gaba domin gyara aurenta. Wani nau'in motsa jikin kuma shine ake cema "Kegel exercise". Toh yaya ake yinshi? Dr. Gomes ta nuna cewa idan kina yin fitsari sai ki tsaida fitar fitsarin, wato ki riƙe fitarin, ki danne sa na tsawon daƙiƙoƙi 10 , wato ki ƙirga 1 zuwa 10 sa'annan ki saki fitsarin a hankali a hankali. Zaki iya yin hakan sau 2 ko 3 a rana idan za kiyi fitsari. Shima wannan nau'in motsa jikin na tsuke gaban mace.

 

2. Hanya ta biyu shine wanke gaba da ruwan sanyi mai ƙankara. Yana taimakawa wajen matse gaba amma sai an hada da motsa jikin da muka yi bayani. Wannan yana daga cikin hanyoyin da Dr. Gomes ta zayyana. Amma zaifi dacewa ace sai mace ta gama wankan jegonta na kwana 40 kwatakwata sa'annan tayi amfani da ruwan sanyin , wato bayan ta koma "normal". Saɓanin yanda al'adar Bahaushe tayi imani dashi cewa ruwan sanyi na lalata gaban mace ,wasu likitocin a wasu al'adun na ganin yana matse gaba.

 

3. Yin amfani da aluf (alum). Aluf yana matse gaba sosai sai dai likitoci na tsoratarwa akan yin hakan saboda da sinadarin kemikal ne.

 

4. Yin tiyatar likita domin rage budewar farji. Wannan ma hanya ce ta zamani amma ana tsoratarwa akan yin hakan saboda wasu dalilan lafiya.

 

5. Yunƙurin tsuke gaba a lokacin saduwa, wato ki matse farjinki ta ciki lokacinda mijinki yake kaikawo. Zaki yawaita yunƙuri domin tsuke gabanki domin mijinki yaji alamun ana riƙe masa al'aura tamkar zobe zagayen gabansa. Idan mace na yawaita yin da haka to zai zama ɗabi'arta kuma nan gaba ba zata san ma tanayin hakan ba saboda ta riga ta horar da jikinta, kuma hakan zai inganta jin daɗin mijinta sosai. Allah Ya taimaka.

 

6. Da sauransu.
Share:

MAGNIN INFECTION


SIRRIN MATA, WOMEN ONLY GROUP 

   Maganin infection 

          Wannan maganin infection ne wanda xaki dinga tsarki da shi in kin dafa kina kama ruwa d shi d dan dumi, 'yar uwa ki gwada d yaddar Allah xaki samu Lpy ki nemi infection ki rasa
   Hulba
   Kanin fari 
   'Yayan xogale
   Malmo 
   Tafar nuwa 
   Bagaruwan mata
   Habbatussauda 
   Alum
    Lalle
    Ganyen magarya
Domin neman Karin bayani xaki iya nemana ta Wannan number 09064258831 
     By admin xahra m Sulaiman
💖SANYI MAI SANYA FITAR RUWA DA KAIKAYI KO KURAJE💞

A nemi hulba ,man tafarnuwa, man Shanu,yayankabewa,a daka a hada a Kwana a wajen daya a dinga sakawa acikin shayi ana sha ko a abinci.


💖KA'ARI NI'IMA💞
Ki nemi ridin ki daka ki tankade ki nemi madara ta ruwa ki hada ki gauraya kisha👍

👍💖SAKA ME GIDA SUMBTU💞

Kisamu totuwar rake me tsafta ki busar da iya sauki hada da miski da kanunfari sauki hadasu waje daya ki dakasu ki samu garwashin wuta kina xuba garin kadan kina tsuguno kibar hayaki ya ratsa gabanki sosai kisamu kamar 5minutes wannan hadin yana karawa mace dandanon jima'i sosai musamman idan kin kasance me ni'ima.


Share:

GYARAN FARJI

😎 Sirrinmu 😎😎

💞GYARA FARJI 💞
Ki nemi man tafarnuwa
Man habba
Miski farin 

Ki kwaba su wajen daya kina inserting a FARJINKI yana Kore infection yasa wajen kamshi, yayi tighting dinki ya kuma sa wajen yayi laushi da taushi😃


💖MAGANIN KAIKAYIN GABA💖
A nemi hulba a dafa snn idan ya dan huce a xauna acIkI at least 30 mint,snn a Debi Wanda aka dafa a sa tsamiya a sha.

💞GYARAN NONO💞
Gero 
Alkama
Jar masara 
Farar shinkafa

💖sai ki gyara ki hadasu ,ki wanke ki shanyasu a rana su bushe,sai ki soya sama sama,sai ki juye ki kai nika gaba daya,sai ki dinga diban cokali daya da Rabi kina sha da nono ko yoghurt mai kyauta,zaki yi mmk ydd zai canxa.

2💞 ko kuma kisami garin garin hulba ki tafasa sai ki rinka gasa su,idan kin gama sai ki sami man hulban ki shafa musu, wacce xatai yaye xata rinka sha two weeks bf n after tayi yayen.Share:

AMFANIN DABINO A JIKIN ƊAN ADAM


AMFANIN DABINO A JIKIN DAN ADAM

Dabino na da tsohon tarihin da wasu 'ya'yan bishiyan ba su da shi, ba wai yanzu ba ko tun a da can mutane sukan dauke shi a matsayin abinci, za kuma a iya cewa yana gaban duk wani dan itace, masamman sabo da sukarin da ya tattara a cikinsa, wannan zakin ya shafi busasshe da danye wanda ya nuna. Wata malama mai zurfin ilimi a bangaren kayayyakin abinci a Juddah, wato Prof. Waddaha Mohammed na cewa, Cin kwayan dabino guda goma mai nauyin 100g zai iya ba mutum wasu abubuwa na amfani ga lafiya jiki. Haka ma hukumar kula lafiya ta Amurka ta bayar da shawara ga matasa da cewa, wanda ya ke cin dabino zai sami duk abin da ya ke bukata na Magnesium, Manganese, Copper, zai sami kusan abin da yake bukata na rabin sinadaran Potassium da calcium. Ana kimanta zakin sukarin da dabinon ya tattara wajen kashi 78-70 cikin dari na abubuwan da dabinon ya kumsa, kuma wannan sukarin na dabino nan take ya ke narkewa a cikin jini sabanin sauran 'ya'yan bishiya. A nan ne za mu ga hikimar muslunci ta sanya dabino ya zama abin farko da mai azumi zai fara ci, wannan don a dawo masa da abubuwan bukatar da ya rasa ne cikin gaggawa, Allah Mai girma ne a dukkan lamarinsa. Ba wannan kadai ba akwai ma 75g na carbohydrate, 63g na sukari, 8g na Dietary fiber, 0.4g na Fat, 2.5g na Protein, 21g na ruwa,0.262 mg na Manganese, 1.32 na minerals. 

 Abin da Prof. Waddaha ta ce shi ne bushasshen dabino ya qumshi: Carbohydrate 79.6%, Fat 2.5%, Water 33%, Minerals 1.32%, Dietary fiber 10%, sai Vitamins A, B1, B2 da C, kamar yadda ya kuma ya kumshi abubuwa da dan dama, a takaice in ka duma dabino shi kadai ya isa ya zama abincin da zai gina jiki in ba don tsoron a yi masa cin koshi ba. Bincike ya nuna cewa dabino ya kumshi sanadaran; Minerals da Calcium, da Protein, da Fat, da Lime, da Coramine, da Dietry fiber, da Phosphor, da da Chlorine, Manganese, da Potassium, da Copper, da Vitamin C, da kuma Magnesium. Da wannan ne za mu gane cewa dabino ya kumshi manya-manyan abubuwa na abinci, wadanda za su gina jiki da jijiya, suma bayyana wa mutum matasantarsa ko da kuwa ya dan kwana biyu, da za a haga dabino da madara tabbas abinci ne mai kyawun gaske, masamman ga wanda yake da matsalar ciki. Masana kimiyya na cewa, abubuwan gina jiki da su ke cikin danino na daidai ne da na wani nau'i na nama, ko ribi uku na kifi. Kuma ya kan amfanar da masu cutar fatarar jini, da wasu cututtuka da suka shafi kirji kamar yadda ake kwaba shi a dafa a rika sha daidai gwargwadon yadda aka nunawa mutum. Dabino na amfanar da kananan yara, da matasa, da 'yan wasa, da ma'aikata, da ramammu, da kuma mata masu ciki.

 

Share:

SHAYE-SHAYE A TSAKANIN MATAN HAUSAWA

SHAYE SHAYE A TSAKANIN MATAN HAUSAWA. 

Yawaitar ta'ammali da kayayyakin gusar da hankali da mata ke yi a yanzu, na daya daga cikin manyan matsalolin da al'ummar Hausawa ke fuskanta.
Yara mata da shekarunsu suka kama daga 18-45 ne suka fi aikata wannan mummunar dabi'a. Akwai dalilai masu yawa da ake ganin sune musabbabin haddasawa matan Hausawa tsunduma cikin wannan mummunar hanya ta shaye-shaye. Daga cikin wadannan dalilai akwai:
Rashin aure
Tsantsar damuwa
Auren dole
Damuwar da auren ke haifarwa. 

Wannan dabi'a ta shaye-shaye a tsakanin matan Hausawa, a iya cewa bak'uwar aba ce, wadda a 'yan shekarun da suka gabata sam ba a santa ba, akwai tabbacin cewa kwanan nan ta kutso kai cikin al'ummar ta Hausawa, sakamakon su ne suka fi kowa matsalolin aure a tsakankanin takwarorinsu wato k'abilun Yoruba, Igbo, Kanuri da kuma Fulani.
Duk da kasancewar matsalar shaye-shayen mata ta zamo ruwan dare game duniya, sakamakon babu wata al'umma a yanzu da za ta bigi k'irji ta ce ta tsira daga wannan mummunar dabi'a, sai dai ace wata ta fi wata.

WANE DALILAI NE SUKA FI SA MATAN HAUSAWA SHAYE-SHAYE? 
Shaye-shaye na nufin shan dukkan wani abu da zai iya jawo buguwa, ko daukewar barci, ko karin wani karfi na musamman ko gusar da hankali. Jaridar Vanguard News ce ta rawaito hakan a wani gangamin wayar da kan matasa da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta k'asa (NDLEA) ta gabatar a jami'ar Bwari a watan March na wannan shekarar. 

Wani bincike da Medlineplus ta k'asar Amurka ta gabatar, ya nuna cewa binciken National institute on drug abuse ta k'asar Amurka ya baiyana cewa, shaye-shayen magunguna ba bisa ka'ida ba, babban tarnak'i ne ga lafiyar kowacce al'umma. Miliyoyin mutane suna rasa rayukansu, ko su kamu da cututtuka masu yawan gaske.

Dalilai da yawa ne dai ake ganin su ne suka sanya mata tsunduma cikin harkokin shaye-shaye. Daga cikin manyan dalilan akwai:

RASHIN YIN AURE A KAN LOKACI
Sanannen abu ne yadda Hausawa suka dauki aure, hasali ma aure shi ne abu mafi muhimmanci a bahaushiyar al'ada.
Rashin samun mijin aure a lokacin da mace ta kai minzalin yin auren na zama babban sanadin haifar da shaye-shaye ga mata. Wannan matsala ce babba da ke tunzura rayuwar 'yan mata su fara ta'ammuli da kayan gusar da hankali. Damuwar da al'uma kama daga iyaye, 'yan uwa, kawaye da sauran jama'a da suke d'orawa macen da bata yi aure ba na saka matan su fara amfani da kayan gusar da hankali. Haka kuma mata da yawa da ba su da aure kuma ba sa so su fada cikin harkokin zinace-zinace, su kan yi amfani da magungunan gusar da hankali domin ya taimaka mu su wajen rage sha'awar maza da za su iya ji. Shan kayan maye na ba su damar mancewa da kuma tsai da duk wani yanayi da za su iya ji a jikinsu.

DAMUWA
Tsantsar damuwa sakamakon rashin wani abu na jefa mata cikin shaye-shaye. A wannan rukuni an fi samun matan aure a ciki, wadanda yawanci ba sa samun kulawar da ya kamata daga wajen mazajensu, wato ba su da lokacin yin hira da su ko jin wasu matsalolinsu. Hakan ya kan tunzura matan su fara shan kayayyakin da za su gusar musu da hankali, domin su samu damar mance kaso da yawa na matsalolin da suka addabi rayuwarsu.

GASA/KWAIKWAYO

Jinsin mata a dabi'ance jinsi ne ma su gasa da kwaikwayo, wato hanya ce mai sauki na samun yawaitar mata ma su shaye-shaye, sakamakon wata ta ga wata kawarta ko makociyarta ta na yi. A nan akwai buqatar bayar da kulawa ta musamman ga mata da sa ido koyaushe akan hanyoyin da mata ke bi don gudanar da rayuwarsu.

NAU'O'IN KAYAN MAYE DA MATA SUKA FI AMFANI DA SU
Mata ba su cika amfani da kwayoyi ba, sai dai magunguna na ruwa wato syrup. Wadannan magunguna sun hada da: Emzolyn
Benelyn
Coplin
Codin, da kuma wasu kad'an da su kan yi amfani da tabar wiwi da k'wayoyi kamar su Tramol da sauransu.

ILLOLIN DA SHAYE-SHAYE YAKE YIWA JIKIN MACE
Daga cikin manyan matsalolin da shaye-shaye ke haifarwa ga mata sun had'a da:

HANA HAIHUWA
Mata ma su shaye-shaye na fuskantar barazanar rashin haihuwa, domin kuwa ya na raunata mahaifarsu yarda ko da ma ciki ya shiga ba ya iya zama. 

HAIHUWAR YARA MARA SA LAFIYA
Akwai barazanar haihuwar yara marasa koshin lafiya, idan ma har an samu haihuwar kenan, ana haifar yara da wani nak'asu a jikinsu ko kwakwalwarsu.

RAUNANA GARKUWAR JIKI
Shaye-shaye na matukar raunana garkuwar jikin mace, da hana su kuzari ta hanyar haddasa musu cututtuka iri-iri.

RAGE DARAJA A CIKIN AL'UMA
Shaye-shaye na rage darajar mace a cikin al'uma, ya na sawa a gujeta a kyamaceta. Idan budurwa ce yana hanawa a aureta, idan kuma mai aure ce yana jawo rabuwar aure. 

RASHIN SON KUSANTAR NAMIJI
Matan da suke shaye-shaye ya na rage mu su sha'awa, ya na sa su ji ba sa so maza su taba su ko su kusancesu da gaske. Ya na hana garkuwar jikinsu karbar duk wani sako da namiji zai aika gareta. 

SAUYAWAR GABOBIN JIKI
Ana gane mata ma su shaye-shaye ta hanyar kankancewar idanuwansu da canzawar launin idon, labbansu na bushewa kuma hakoransu na lalacewa har ma su rube wani lokacin. Ya na sa rama da bushewar jiki, yana saukar da gashin mace, ya lalata kyakkyawar surarta. 

YAWAN RASHIN LAFIYA
Matan da suke shan kayan maye su na da yawan laulayi, ko yaushe cikin ciwo suke, sabo da sun riga sun raunata garkuwar jikinsu. K'ashinsu kuma yana rage k'wari, dan haka akwai yiwuwar saukin samun karaya a k'ashinsu. 

A karshe zuwa ga duk wanda abin ya shafa, akwai bukatar d'aukar kowane irin mataki da ake ganin ya dace, domin yak'ar wannan mummunar d'abi'a da ta kutso kai cikin al'umarmu.

Aysha Bilkisu Umar 
8/6/18.

Share:

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive