Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

Showing posts with label Lambun Masoya (Lovers Garden). Show all posts
Showing posts with label Lambun Masoya (Lovers Garden). Show all posts

FALALAR ƘAUNA DON ALLAH

FALALAR KAUNA DON ALLAH
Al-Imamun Nasa’iy da Ibnu Hibban sun ruwaito daga Abu Huraira (Allah ya ƙara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: lallai (a cikin mutane) akwai wasu bayin Allah wadanda ba annabawa ba ne (amma) annabawa da shahidai suna burin su sami irin ladansu. Sai aka ce: su waye su ya Manzon Allah? A faɗa mana su don mu ƙaunace su. Sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: wasu mutane ne waɗanda suka ƙaunaci junansu don hasken Allah ba tare da suna da ‘yan uwantaka ko danganta ba. Fuskokin su suna yin haske (ranar kiyama) akan minbari na haske. Ba sa shiga cikin tashin hankalin da sauran mutane suke shiga. Ba sa shiga cikin baƙin cikin da mutane ke shiga. Sannan sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya karanta fadin Allah (ku saurara! Lallai waliyyan Allah ba sa cikin tsoro kuma ba sa baƙin ciki)”.
Allah ya sa mu dace.

Share:

YAREN SOYAYYA 14


*_💝🌹//YAREN SOYAYYA 014//🌹💝_*

 *_Mawallafi:- Dr Abdulkadir Ismail_*

 
     *e) Rashin Stayawa Akan Wani Abu da Aka Cimma da Juna.* 

     Idan ma`aurata sun cimma wata matsaya akan yin wani abu, ko qaurace wa wani abu, sannan wani ya saba, to wannan daliline da yake sanya ficewa. Idan tana yin wani abu ya hana kuma ta dauki al-qawarin ta daina ya kamata tana sake yi, to to wannan daliline da zai harzuka shi har ya fice. Idan ya yi mata al-qawarin sayo mata ko yi mata wani abu, amma daga baya ya ki, to shi ma wannan yana iya zama dalili wajenta na ficewa daga auren. 

    *f) Rashin Tankwaruwa.*

         Idan fahimtar ma`aurata ta zama; ko dai abu ya yi zama fari sal ko ya zama baqi qirin, to wannan sun rasa tankwaruwa. Abin nufi da tankwaruwa, shi mutum ya fahimci cewa idan abu ba fari ba ne sal, to watakila fari-fari ne, ko kuma ruwan kwaine, ko kuwa kore ne, amma ba ya nuna cewa lallai wannan abin ya zama baqi kuma wuluk. Kuma wani baqin ba wuluk ba ne, baki-baki ne, ko kuma ruwan qasa-qasa ne, ko kore mai duhu ko shudi mai duhu. Ma`ana idan abu bai samu yadda mutum yake so, to ya yi farin ciki cewa an samu, duk da bai cika cif da cif ba. Wannan kuwa *Manzon Allah ﷺ ya umarce mu da ``..Kintaci daidai, mu kusanta...``. [Bukhar: Hadisi na 39, 1/16].* Amma yin abu dari bisa dari wannan ba siffar dan Adam ba ce. Idan aka nemi cewa sai ya yi abu dari bisa dari, kuma idan ba haka aka yi ba bai yi daidai ba, to wannan sababi ne na ficewa daga aure.

   *g) Rashin Cimma Wani Abu Tare.* 

    Mutum a rayuwa yana son idan ya yi wata `yar tafiya, ya ga ya cimma wani abu a tafiyar da ya yi, shi ya sa a aure, mutum yakan so ya ga ya yi gaba a zamantakewarsu da iyali, idan ya rasa wannan sai ya fara tinanin ficewa. Wani yana son ya ga an cimma wata nasara a karatu, wani kuma tana sana`a tana dan samun wani abu ba cima-zaune ba ce. Rashin hakan na sanya korafi tsakanin juna, wanda wannan yake sawa a fice, za ta yi qorafin bai damu da yagama ginin saba, bai damu da ya gyara sana`arsa ba, bai damu da ya samar da wani tsari na karatun `ya`yansa ba. Wani lokacin a matakin kowanansu daidaiku, sannan kuma cimma burin yana kasancewa a matakinsu na gaba daya, haihuwa cimma wani abu ne, tarbiyyar yara ma haka. Shi ya sa a Musulunci ake son su yi sallar dare tare, su yi azumi tare, su zauna tare su tattauna da dai sauransu. Rashin cimma buri a rayuwa dalili ne daga cikin dalilan ficewa daga aure. 

  Wadanda dalilai ne na ficewa daga aure, duk da cewa ana ganinsu qananan dalilai, amma kuma suna da tasiri kwarai wajen ficewa daga aure. Wadanda suke biyo musu su ne manyan dalilai :-

  *a) Izgilanci.* 

     Yi wa juna ba`a da izgilanci a kan wata halitta ko shiga, wannan dalili ne mai qar'fi da yake gaggauta fita daga aure. Kamar ta yi masa izgilanci a kan sanqonsa misali, ko gurguntakarsa, ko wani abu na halittarsa, ko shi ya yi Mata izgilanci kan halittarta, ko wata shiga da ta yi, ko ya nuna wani abu nata ne ya sanya shi nesa da ita, kamar wurin jiki, ko wani abu makamancin haka.

*b) Wulakanci.* 

       Idan aka fara samun wulaqanci tsakanin ma'aurata, to wannan alama ce ta ficewa, wulaqancin na iya kasancewa a kan Mata ko mijin, ko kuma Iyayensa, ko `yan-uwansa. Wani lokaci a kan fahimci kamar wani daga ciki yana jure wulaqanci, amma haqiqanin al`amari shi ne, ya fice daga cikin aure, mai yiwuwa yana hangen wata maslaha ko wani dalili da zai hana shi ficewa bai daya.

*c) Rowa.* 

      Rowa iri biyu (2) ne a zamantakewa, ko dai ya zama rowar abin duniya wanda ake iya gani, ko kuma rowar Qauna da jin mutum a zuciya.... 

*_Zamu dakata anan_*


*_Insha Allah gobe zamu tashi daga wannan mataki na Rowa_*
 

*_Zamuci gaba Insha Allah_*

*✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd*
Share:

YAREN SOYAYYA 13

*💝🌹//YAREN SOYAYYA 013//🌹💝*

 *_Mawallafi:- Dr Abdulkadir Ismail_*

*_CIGABAN - MATAKI NA BIYAR:- FICEWA_*
 
*_D- Yawan Samun Sabani Da Juna Fiye Da Rashinsa._*

      Idan ya zama mijin yana son ayi gabas matar ta je yamma, ko yana son yara su yi wani abu ita kuma ta ji ba ta son haka, ko kuma tana son ta ringa fita shi kuma yana qin haka to wannan alama ce ta samun sabani, kuma yin hakan na nuna alamar ficewa. Idan an tuna a mataki na farko, burin ma`aurata ne su yi abin da wanda suke Qauna yake so, to yayin da aka kai matakin cewa abin da yake so shi ne abin ki a wajen daya bangaren, to wannan an kai kishiyar wancan mataki na farko daga nan kuma an fice.
   Akwai alamu da yawa da za su iya nuna qaramin ficewa bayan wannan, amma wadannan su ne mafi bayyana a zamantakewar aure. Bayan qaramar ficewa akwai babbar ficewa, wanda take biyowa bayan qaramin, shi ne namiji ya saki matarsa, ko kuma ita ta meni khul`i, ko kuma ta bujure ta tafi gida ta ki dawowa. Abubuwan da suke taimakawa wajen kawowa ga wannan mataki suna da yawa, zamu kirgo mafi yawan aukuwa daga cikinsu:-

    *_a- Kwatantawa._*
          Ma`ana kwatantawa miji da wani, ko mutum ya kwatanta matarsa da wata, wannan kwatance ya hada da wajen kyau, ko wajen mu`amala, ko wajen asali, ko wajen dukiya, ko karatu. Allah Bai halicci mutane daidai wa daidai ba, wani ya fi wani, kuma wani bazai taba zama wani ba, amma kuma kowa yana da wani abu da wani bashi da shi, ko an sani ko wannan abun a boye yake. Saboda haka duk mai buqatar dawwamar aure, kada ya kuskura ya kwatanta nasa da na wani, domin wannan wani sababi ne na gaggauta ficewa daga masana`antar aure, da kuma sanya wa kai damuwa a kan abin da ba hakika ba ne.

   Manzon Allah ﷺ yana da mataye da dama, amma kowace daban take, Nana Khadija ba ta yi daidai da Nana Aisha ba, ko wacce tana da na ta abin da ta kebanta da shi. Nana Zainab ba daidai take da Nana Um-Salama ba, kowace tana da abin da takebanta da shi, kuma duk hudun ba su yi kama da juna ba, ballantana a kwatanta su, ko a nemi duk sai sun zama hoto iri daya. 

  *"b- Rashin Qarba._*
          Yayin da mace take son dole sai mijinta ya canja ya zama kamar wani da take tunani, ko shi yana tunanin dole sai ta zama kamar wance, to a wannan lokacin mutum zai tubure ya qi wannan Qoqarin. 
  Abin da yake lallai a kan mace ta karbi mijinta a yanda yake ta zauna da shi a bisa wannan fahimta da ta yi masa, shi ma ya yarda da ita a bisa yadda take ya zauna da ita a hakan.

  *_c- Rashin Gir'mama Juna._*
    Yayin da aka rasa qaddara juna tsakanin ma`aurata, ta han-yar jiz'ga juna, ko rashin ganin darajar juna, to wannan abu ne mai gaggauto da ficewa daga aure. 

  *_d- Rashin Sanya Juna Cikin Al`amura._* 
    Idan ya zamanto namiji yana gudanar da wani abin da ya shafe su baki daya amma ba ruwansa da shawara da ita, to wannan sababi ne na ita ma ta yi hakan kuma wannan zai gaggauto ficewa daga aure. Kamar haka ita ma ya ga tana shawara da wasu sannan ta ba shi labarin abin da za ta aikata, to a wannan yanayin zai fice ya bar mata aure. Idan wani abokin miji ko dan uwansa idan ya zama da shi ake shawarar, saboda tana kishin cewa wannan abu nata ne amma ya zo ya yi kaka-gida a ciki. Haka shi ma idan ya fahimci cewa tana da wasu kayanta ko abubuwanta wanda ba ta taba sanar da shi ba, sai dai ya ji a wani waje to wannan dalili ne na ya fice daga auren.

*_Zamuci gaba Insha Allah_*

*✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd*

Share:

YAREN SOYAYYA 12


*💝🌹//YAREN SOYAYYA 012//🌹💝*

 *_Mawallafi:- Dr Abdulkadir Ismail_*

*_MATAKI NA BIYAR:- FICEWA_*

    Lura da abin da bangaren kyau a rayuwa yana janyo abu mai kyau, kira da baki ko da zuci na abubuwan da ba su day kyau sukan gaggauto zuwansu. *Manzon Allah ya ce:-*

*وَأُحِبُّ الْفَأْلَ الصَّالِحَ*

*_``Ina son kyakykyawar fata (zato, tunani)``._*

     Idan mutum ya yi kyakykyawan fata sai abu ya zo masa irin yadda ya yi zato da Izinin Allah, idan kuwa ya yi mummunar fata sai abu ya zo masa irin yadda ya yi zato. A wannan mataki na ficewa ma`aurata suna gaggauto da halarto da tunanin mummunan abu, sai ya yi ta aukuwa irin yadda suka halarto da shi a zuciyarsu, ko suka furta da bakunansu.

   Kafin isowar wannan mataki abubuwa ne suke tattaruwa daya bayan daya har su sana`anta matsalar da takan janyo ficewa. Saboda haka yana da muhimmanci a lissafo wadannan abubuwan da kuma irin gudunmawar da suke bayarwa wajen gaggauta ko dakile ficewar, aikata su na sanya daya bangaren ya ji cewa lokaci ya yi na ficewa, nisantarsu kuwa yana sanyawa a qauracewa ficewa ko a jinkirta lokacin.

   Ficewa a zamantakewar aure kala biyu ne ; akwai qaramin ficewa, shi ne ma`aurata su fara jin cewa lallai ba ruwansu da juna, ko ba sa buqatar juna. Idan mutum ya sami kansa a cikin daya daga cikin wadannan alamomi to lallai ya kai qaramar kofar ficewa daga aure:- 

  *_A:- Ganin Juna Da Kuskure Da Yin Daidai Ba._*

   Babu abu mai tada hankali a zamantakewa kamar haduwa da abokin zama ko abokiyar zama da kullum tinanin sa sai an yi abu daidai dari bisa dari 100%, irin wadannan ba wani abu da mutum zai yi su ga wannan daidai ne. Kullum abin da ya iya shi ne gano wani abu da aka yi ba daidai ba. Gano wani abu na ba daidai ba abu ne mai kyau. Amma duk lokacin da ya koma kuma dalili ne na munana fahimta a kan abokin zama to wannan ya zama matsala.

  *_B- Ma`aurata Su Ringa Kokarai Kin Haduwa Da Juna Sai Da Kyar._*

   Yayin da ma`aurata suke qoqarin kaucewa ganin juna a gida, ta yadda zai iya ficewa lokacin da take barci, ko ya dawo a makare bayan ta yi barci, ko kuma ita ta qi shigowa inda yake in ba shi ya je ba, ko ta kir-kiri fita unguwanni don ta yi nesa da shi, to a wannan lokacin ma`aurata sun fice daga cikin masana`antar aure. Wani lokacin qauracewar juna na faruwa ta han-yar qin yin magana da juna, ko kuma takaita magana a kan neman wani abu kawai ba tare da wata hira da take hada su ba, ko kuma qin neman juna yayin da ya yi tafiya ko qin yin saqon kar ta kwana. Yayin da mai aure ya fara jin cewa yafi jin dadin kasancewa da wasu fiye da abokin zamansa, to wannan alama ce ya fara ficewa daga masana`anta.

  *_C- Qauracewa Haduwa Da Juna A Wajen Taro._*

    Idan ma'aurata suka fara kyamar a gansu da juna a wajen taro ko wani waje na musamman, to wannan alama ce sun fara ficewa. Wani lokacin mace za ta ji ba ta son mijinta ya kaita unguwa gara ta tafi da wasu, ko ta yi tafiyarta ita kadai. Wani lokacin don kada a gan shi tare da ita zai iya neman uzuri na qin kaita unguwa ko halartar wani taro da za a gansu tare. Idan miji ko mata ba ta jin alfahari a ganta tare da mijinta a wani waje to wannan alama ce ta ficewa, domin kamar mutum yana son ya gamu da wani daban wanda ya fi abokin zamansa.

 *_D- Yawan Samun Sabani Da Juna Fiye Da Rashinsa._*

*Insha Allah zamu tsaya anan sabida tsayin wannan Mataki... Insha Allah zamu tashi daganan a rubutun mu nagaba*

*_✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd_*
Share:

YAREN SOYAYYA 11


*💝🌹//YAREN SOYAYYA 011//🌹💝*

*_WALLAFAR:- Dr Abdulkadir Ismail Kano_*


*MATAKI NA BIYAR:- KWATANTAWA*
   Mataki ne mai hatsarin gaske. Mataki ne na korafi, Mataki ne na saurin kosawa, Mataki ne da mutum yake kwatanta rayuwarsa da ta wasu. Allah bai halicci mutane bai daya ba, kowa da irin halinsa kuma kowa da irin yanayin da yake samun kansa, Kuma kowa akwai wani bangare nasa da ba shi da kyau ko dadi. Yayin da ma'aurata suka shiga irin wannan yanayi, sai su koma mataki na farko, ta yadda suke ganin duk wani abu mai kyau, Amma ba na su ba, sai na wasu ma'auratan daban, ganin hakan sai ya bakanta musu rai don zaton cewa su kam ba suyi sa'ar zamantakewar ba.
  Ma’aurata a yawancin lokuta suna iya kokarinsu na boye matsalolin da suke tsakaninsu saboda dalilai da yawa; wani lokaci don nuna burgewa, wani lokaci don bakanta wa Wanda suke ganin kamar ba nasu ba ne, wani lokaci Kuma don gudun abin da zai je ya dawo. Kuma ba sa jin kunyar yin karya, za ka iya Jin namiji Yana cewa: “Ni nafi karfin matata tayi min haka!”. Mace takan iya da'awar cewa: “Ai a gidana sai abin da na fada”. Da dai irin wadannan kalmomi masu nuna su sune ke rike da komai.
   Amma a gaskiyar lamari a mafi yawan lokuta ba haka al’amarin yake ba, hasali ma kishiyar hakan ne yake faruwa, mutum yakan gano haka ne yayin da sabani ya faru tsakaninsu, Kuma aka zo Mai da magana, ko Kuma aka rabu da juna, duk da cewa rashin adalci yakan shiga cikin zantuka bayan rabuwa ko yayin bacin rai. A cikin Hadisi shahararre Hadisin ‘Ummu Zar’in’, don gudun kada matan su yaudari kawunansu sai da suka dauki alkawarin cewa ko wacce gaskiya zata fada game da mijinta.
*”ﻋَﻦْ ﻋَﺎﺋِﺸَﺔَ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ﻗَﺎﻟَﺖْ : ﺟَﻠَﺲَ ﺇِﺣْﺪَﻯ ﻋَﺸْﺮَﺓَ ﺍﻣْﺮَﺃَﺓً ﻓَﺘَﻌَﺎﻫَﺪْﻥَ ﻭَﺗَﻌَﺎﻗَﺪْﻥَ ﺃَﻥْ ﻟَﺎ ﻳَﻜْﺘُﻤْﻦَ ﻣِﻦْ ﺃَﺧْﺒَﺎﺭِ ﺃَﺯْﻭَﺍﺟِﻬِﻦَّ ﺷَﻴْﺌًﺎ.“*
  *_“Nana Aisha (RA) tace: wadansu mata guda goma sha daya suka zauna, sai suka daukarwa kansu alkawari suka yi yarjejeniya akan haka cewa ba zasu boye wani Abu ba na labarin mazajensu (Mai kyau ko Marar kyau).”_*
   Wannan ya sanya malamai suke cewa yawanci idan ba irin wannan alkawari aka samu ba, to labarun da suke fitowa ba lallai su zama gaskiya ba.
   A wannan mataki mace takan hango gidan wata da mijin wata, shima namiji yakan hango gidan wani da matar wani, ba don ya aure ta ba, Amma dai Yana ganin wancan yayi sa’ar mata, shi kuwa bai yi dace ba. A bisa wannan sai ya dora wa kansa ganin bangaren da yafi kyau a rayuwar wasu, haka ita ma sai ta yi ta hango bangaren da yafi haske na rayuwar wani gidan ba tare da sunyi la’akari ko sun kula da daya bangaren ba.
   Mutum zai ji maganganu na kwatantawa tana fitowa daga bakin ma’aurata a Yanayin damuwa da rashin samun irin wannan. Idan yazo yi mata magana, yakan iya cewa: “Ki duba kiga matar wane” “Kibkalli gidan wance”. Dubi yadda Mata suke ado, amma ke gaki nan ballagaza”. Da jumloli masu nuna kwatantawa da wasubko wata. Haka ita ma takan fada: “Tab! kunyi sa’a ni mijina ai sam!”, “Wance ta yi sa’ar miji, mutum mai saukin Kai, Amma ni!!!”.
  A wani salo na yaudarar zuciya, idan mutum yaji irin wadansu zantukan na wani gidan, sai yayi ta farin ciki, Kuma Yana takaicin cewa shi bai sami irin wannan ba. Wannan mataki shine yake daidai da kishiyar matakin Farko, a matakin maganadisu. Kyawawan abubuwan mutum yake kallo ya rufe idonsa wajen ganin maras sa kyau, Amma a wannan matakin sai ya juya lamarin, munanan abubuwan kawai yake duba, ya rufe idonsa daga ganin masu kyawun. Shi yasa suke fadi a waken larabci wanda ake nasabtawa ga Imam Shafi’i cewa:
وعين الرضا عن كل عيب كليلة *** ولكن عين السخط تبدي المساويا
  (Duba da) idon yarda mai kanne dukkan wani laifi ne *** Kamar yadda (kallo da) idon bacin rai mai bayyana dukkan munanan abubuwa ne.
   A matakin Farko, tana kallonsa ne da idon yarda da idon kauna, saboda haka komai idan yayi sai ta fassara shi da ma’anar soyayya. Amma lokacin da rai ya baci, aka zo wannan mataki dukkan abin da zai aikata, to wannan abin aibi ne saboda idon da yake kallon wannan abu cike yake da gaba. idan wani ya kalle ta, ko yayi Mata magana, sai ta ga yayi fushi, sai ta fassara wannan da cewa tsananin kaunarta ne, amma a wannan mataki da wani zai yi mata magana ko ya kalleta, sai ya nuna bacin ransa sai ta fassara yin hakan da yayi da cewa; Yana tuhumarta ne, ko Yana zarginta, ko ya cika zafin kishi ba gaira ba dalili.
  Idan ba ayi hattara ba a wannan kwatanta Kai da wasu a lamarin aure, idan ba a yaba da kokarin juna ba a wannan mataki, idan ba a kalli bangarorin nagarta da kyau na abokin zama ba a wannan mataki, sai tunanin da aka gina shi akan zato da wata rayuwa ta almara tayi rinjaye acikin zuciya. Kuma mutum ya hadu da ciwon zuciya na kunci da ganin kamar shi ya rasa komai na Jin dadi lamarin aure. Idan har ba a magance hakan da wuri ba, ta hanyar mutum ya zauna yayi tunanin da ya kamata, sai ya yanke shawarar ficewa daga dajiyar aure, ta hanyar sulalewa ko yanke igiyar, wannan shine mataki na karshe.
            *_LABARI:_*
   Wata Rana wani miji da matarsa sai suka tafi gidan ajiye dabbabobi (Zoo) sai suka tarar da wani biri da biranya suna ta wasa suna nishadi da juna, abin gwanin ban sha’awa.
  Sai matar wannan Mutumin tace “Subhanallah! Dubi irin wannan soyayya da take tsakanin su” (*Kwatantawa) Mijin bai ce komai ba, sai suka yo shawagi suka zo inda zakuna suke, sai yaga taking zaune can gefe ya dake yayi shiru, ita ma matar acan gefe guda.
  Sai wannan matar ta sake cewa; “Subhanallahi! Dubi irin wannan nisantar juna, ba ko kauna da soyayya a tsakanin su” (*Kwatantawa)
  Nan ma mijin bai ce komai ba, sai ya dubi wata kwalba ta lemo da yake hannunsa ya gama sha, ya cewa matarsa: “Jefa wannan kwalbar cikin kejin da zakin nan yake ciki mu gani, ki nufi samun matarsa da ita”. Z
(*Hakikar lamari)
Sai ta dauka ta jefa, take sai ga Zaki yayi wata irin zabura yayi gurnani don yaje ya Kare matarsa. sai suka koma kejin biran nan. Yace da ita ta jefa kwalban lemonta kan matar birin nan. Tana jefawa sai birin nan ya ruga a guje ya haye bishiya ya bar matarsa don gudun kada kwalbar ta fado masa.
Sai mijin Yace da ita: “Kada ki yaudaru da abin da mutane suke bayyana miki a gaban ki” Birai sun fi zakuna yawa saboda haka sai anyi hattara. Yayin da mutum yake yaro, idan mahaifinsa ya hana shi wani abu, ko ya tilasta shi yin wani abu, sai ya fahimci wannan a lokacin kamar tsana, ko rashin kauna, Amma idan girma yazo masa, sai yayi wa mahaifinsa godiya da addu’a, saboda abin da yayi masa lokacin da yake karami, Kuma wasu suyi da-na-sanin da kaico cewa ba su sami irin wancan takurawar da aka yi wa wasu ba.
*TAKAITACCIYAR SIFFAR WANNAN MATAKI:*
●Rashin ganin kyawun duk abin da abokin zama yake da shi.
● Kwatanta rayuwar da rayuwar wasu ma'auratan ko masoyan.
● Kallon bangaren aibuka ba bangaren kyau da nagarta ba.
● Sanya wa rai damuwa da neman yin shiga rayuwar almara da mafarki.

*_Zamu cigaba Insha Allah_*

*_✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd_*
Share:

YAREN SOYAYYA 15


*_💝🌹//YAREN SOYAYYA 015//🌹💝_*

 *_Mawallafi:- Dr Abdulkadir Ismail_*

*_CIGABAN- MATAKI NA BIYAR:- FICEWA_*

*c) Rowa.*

       Rowa iri biyu ne a zamantakewa, ko dai ya zama rowar abin duniya wanda ake iya gani, ko kuma rowar Qauna da jin mutum a zuciya. Rowar abin duniya yana hadawa da ya kebance kansa da yin wani abu kamar tufafi, ko abinci ko abin hawa, ta yadda yana ganin abokiyar zamansa tana buqata amma ba zai kula ya ba ta ba. Haka ita ma yakan kasance idan ya zama ta fi shi wadata ko kuma tana aiki amma ba za ta iya ba shi komai daga cikin abin take samu ba, ko ta taimake shi alhali yana cikin buqata. Wani lokacin rowar na kasancewa ne na lokacin, ta yadda ba za ta iya shiga wajensa ba, ko ta buga masa waya, to ta yi masa saqon kar-ta-kwana, amma kuma za ta iya daukar lokaci mai tsayi tana hira da kawayenta ko wasu daban, haka shi ma a bangarensa. Kamar yadda rowar zuci take kasancewa ta han-yar rasa tausayi da tarairaya, da jin kusanci da kauna, tare da cewa kuma ana nuna wasu na daban a waje. 
    Wadannan dalilai masu fitar da ma`aurata ne daga cikin gidan aure, kuma masu faruwa ne a cikin al`umma ba tare da ana ba su kulawa da wani Muhimmanci ba. Akwai dalilai wadanda suka fi wadannan girma, kuma sun kasance gingima-gingima masu taimakawa wajen ficewa cikin gaggawa daga aure. Daga ciki akwi:-

*_A) Bashi._*

         Wasu sukan fara zamantakewarsu na aure da bashi, da kokarin burge mace, ko ita ta yi rance na wasu kaya lokacin kulla aure, ta yadda dodon bashin nan zai hana su zaman gida yadda ya kamata, kuma abokin zamansu ya gano cewa lallai wannan abin da ya gani a waje ba haka yake ba a ciki. Duk lokacin da rayuwar aure ta zama mai sauki ba tare da dora wa kai nauyi mai yawa ba, duk lokacin da aure zai fi sauki da al-barka. Bashi damuwa ne a cikin dare, kuma abin kun-yatawa ne da rana, wannan yakan hana mutum ya zauna a gida, ko ita matar ta dora wa mai gidan abin da ya fi kar'finsa, daga nan kullum sai su halarto bangare mafi muni na zamantakewa, su kasa mai da hankali wajen kallon bangaren kwanciyar hankali da kuma kyawun aure.

*_B). Ya`ya._*

       Samun ya`ya ba qaramin ni`ima ba ce a zamantakewar aure, kuma wannan na daya daga cikin dalilan aure a Musulunci. Amma wani lokacin, saboda rashin gudanar da lamari yadda ya kamata, sukan zama sababi na kawo farraka tsakanin ma`aurata...

*_Insha Allah gobe zamu tashi daga wannan mataki na Ya`ya (Yara)_*
 

*_Zamuci gaba Insha Allah_*

*✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd*
Share:

YAREN SOYAYYA 10

*_💝🌹//YAREN SOYAYYA 010//🌹💝_*

*_Wallafar:- Dr Abdulkadir Ismail Kano_*

*_MATAKI NA HUDU:- SABAWA:_*
   Wannan mataki ne da yake biyo bayan matakin hadewar juna. Bayan an zama daya a gida daya, a wajen kwanciya daya, a wajen tunani an zama daya. sai Kuma wannan mataki yazo na sabo, ta yadda dukkanninsu za su fara aikata abin da suka saba yi ne kawai, su fara saba fadin abin da suka saba fada yau da kullum. Ma’ana sabunta lamurra tsakaninsu da yiwa juna bazata da wani abin burgewa zai ja da baya, ya zama abinda suke yiwa juna ya koma kamar wannan nauyi ne a wajibi da mutum yake kokarin saukewa kawai.
Idan a wancan mataki na maganadisu da kokarin fahimtar juna, kullum tunaninsa me zai yi don ya shawo hankalinta, to a wannan matakin babu wannan tunanin acikin kundin karatunsa. Idan a waancan matakai tana tunanin me zata yi na abinci ko ado don tayi masa bazata, to a wannan matakin ba zai ga haka ba, idan a wancan matakin idan ya fita waje kwakwalwarsa na fada masa cewa ya kamata ya sayo wani abu da yake bata sha’awa, to a wannan mataki burinsa shine menene abu na lallai-lallai da ake bukata ya kawo.
Zai iya tashi da safe ya Kai har karfe sha biyu da kayan barci a jikinsa ba tare da ya damu yayi wanka ko ya wanke bakinsa yayi kwalisa ba. Haka ita ma zata iya tashi ba tare da ta shirya ba, har ma ya zama ya zama tana da kayan aikin gida, a lokacin da maigidan yake nan, ba zata fara tunanin wanka ba har sai ta gama aikin gida baki daya, tayi shara, tayi girki. Sai ta fara sabawa da Yanayin da yake ciki, shima ya daina damuwa da Yanayin da take ciki, ko tayi kwalliya ko ta Sanya turare duk Bai damu ba.
Amma wannan bazai hana shi damuwa da kuluwa ba idan ya ga tayi ado zata fita unguwa. Kuma ita ma nan da nan zata tunzura idan taga yayi wata magana cikin tausasa murya, tare da cewa dukkanninsu suna aikata irin wadannan abubuwa suna ganin ba komai bane, tare da cewa dukkansu sukan yi watsi da abubuwan da suke ganin zasu kyautata zamantakewarsu a mataki na daya da na biyu, amma Kuma wannan bai hana su jin zafin abin da ita take yi masa ba, haka shi ma Yana kufula da abin da yake gani tare da ita na rashin kulawa da kanta ko da shi.
Yayin da Ma’aurata suka kawo wannan mataki, a wannan lokacin ne dukkansu sun gina wani tsari na tunani akan junansu. Ya yi wa kansa hukuncin cewa ga abin da zata yi masa, ga irin maganar da zata mayar masa ko ta bashi amsa idan yayi mata wani abu, ga irin Muhimmancin da za ta baiwa abin da ya fada ko rashin muhimmanci. Daga nan sai ya Gina hukunce-hukuncensa kanta a bisa abin da ya gina na fahimtar ta a kansa, Wanda duk hakan ba lallai ya zama haka abin yake ba, amna dai shi ko ita a kan haka suke yin hukunci.
Misali zata fada masa cewa tana so a kaita dubiya marar lafiya karfe hudu na yamma, amma bai zo ba har sai da Magariba ya dawo. Farkon tunaninta shi ne Bai damu da ita ba, shi yasa ya manta da wannan al’amari, da a lokacin da yake son ta ne da Bai manta ba. Shi ma da zai fada Mata cewa zai zo da abokansa Yana son ayi musu wani abu na daban, sai yazo ya tarar ta manta, to fassararsa ita ce, da ma bata dauke shi da muhimmanci ba, shi yasa tayi wasarere da umurnin.
Da zai yi Mata abin da bata zata ba, kamar ya sayo Mata wata atamfa ko wani abu da take tsananin so, sai wannan abin ya kidimata don farin ciki, saboda ita a wannan matakin bata zaton ya damu da ita ballantana yayi Mata irin wannan abu. Haka shima da zai dawo da dare ya tarar tayi masa wani shiri na daban sai ya fara tunanin ko wani abu ne ya faru, ko Kuma tana da wata bukatar da zata tambaye shi yayi Mata, daga nan sai ya Sanya shakka acikin zuciyarsa.
Idan ma’aurata suka zo wannan mataki, shi ne suke Sanya wa kan su wata fahimta ta zama da abokin zamansu. Da yawa zaka ji idan an tambaye ta game da wani abu za ta ce: “Ai na san ba zai yarda ba” Ma’ana ta gamsu da fahimtar da tayi a kansa na cewa ga abin da zai iya yi ga abin ba zai iya ba. Haka shima zai Gina fahimtarsa a kanta. A irin wannan yanayi ne, idan mutum ya gane dan-uwan zamansa, ko dai ya karbi halayyensa kamar yadda yadda yadda, sai yaci maganin zama da shi, ko Kuma ya yi ta damun kansa wajen sai ya canja shi akan abin da bazai canja ba.
A irin wannan matakin ne sukan fara tunanin ko dai zaben tumun dare suka yo, ko Kuma su kudurce cewa yaudararsu aka yi, daga nan sai su shiga mataki na biyu. A tsarin soyayya da suka dauko a matakin Farko babu sharadin cewa lallai sai abokin zamana yayi daidai da irin ra’ayin da nake Kai zan cigaba da zama da shi, Amma da yake tafiya ta fara nisa, sai mutum ya fara tunanin dole sai an canja sannan za a sami gamsuwa.
*_TAKAITACCIYAR SIFFAR WANNAN MATAKI:-_*
● Gina hukunci a kan abin da kowa yake zaton zai yi, ko za a yi masa.
● Yin abu na wajibi kawai, tare da yin ko oho ga abin burgewa ko farantawa.
● Rashin damuwa da ado ko bajinta ga abokin zama.
● Ganin cewa duk an zama daya, babu bukatar wani abu na musamman ga juna.

*_Zamu cigaba Insha Allah_*

*_✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd_*

Share:

YAREN SOYAYYA 09

*💝🌹//YAREN SOYAYYA 009//🌹💝*

*_Wallafar Dr Abdulkadir Ismail Kano_*

*_Domin fahimtar wannan labarin zanso makaranta su koma baya su dan karanta rubutun mu na jiya kamin su karanta labarin-nan_*

              *_Labari:_*
   Sun yi aure irin na saurayi da budurwa, kuma da kaunar juna da mararin juna, da kuma kokarin faranta wa juna. A irin wancan lokacin na da, rediyoyi manya ba a kowane gida suke ba, amma shi Allah Ya bashi iko ya sayo katuwar rediyo kirar Sanyo mai sifika har biyu; hagu da dama, ga gidansa dan karami daidai kana’a. A irin zamantakewa irin ta da, matar nan takan ta shi ta goge ledar dakinta, ta wanke ban daki, ta kai ruwan wanka, kafin ya fito ta ajiye masa abincinsa ta rufe shi da tuma-kasa, ta koma gefe tana kallonsa yana cin abincinsa, kuma tana sauraren ko akwai wani abu da zai bukata.
Wata rana bayan ya tafi neman abincinsa, lokacin ta zarta wata biyu a gidan, sai hali irin na mata ya motsa mata, sai taga bari ta wanke gidan, ta sake jeren kayan kwalla da kumbo da yake cikin dakinta. Ba tare da taimakon kowa ba, ta fito da kayan dakinta, dama a wancan lokacin ba masu yawa bane, sannan ta wanke dakin ta fito ta wanke kwanukanta ta Shanya. A wannan lokacin ne taga ya kamata wannan rediyon nasu ma a wanke, haka kuwa ta sanya sabulu da soso ta wanke wannan rediyo tatas ta kai rana ta shanya.
Yayin da mijin ya dawo bayan rana ta karya, sai yaga gida ya canja, anyi shanya a tsakar gida, cikin farin ciki ta tambaye shi ra’ayinsa, ya kuwa yabawa kokarin ta, yayi murna, tace masa ai har rediyon can sai da na wanke da soso da sabulu, Yace: “A’a! a’ahh!! Har rediyon ma sai da kika wanke?” Ta tabbatar masa ya kara yaba mata. Amma shi a masaniyarsa ya san cewa an tafka kuskure, saboda rediyo bata son ruwa.
     Yamma ta yi aka hada komai aka sake jerawa, aka kunna rediyo, a wannan lokacin ne rediyo ta ce: Ai na kurumce na bebence. Suka yi suka yi don ta yi magana taqi. Shi da ma yasan a-rina, amma dai don ya faranta mata suka yi ta kici-kici don su ji sauti abu ya ci tura. Daga nan sai ya ce: Watakila akwai wani abu da ba mu gane ba, saboda haka an juma zan kai wa Mai gyara ya taba mana. Haka ya fita da rediyo aka gyara. 
   Bayan shekaru da zamantakewarsu ne matar ta gane cewa ashe yana sane bai yi mata inkarin wannan kus-kuren da ta tafka ba, daga baya sai abu ya koma tsokana: ``Miko min soso da sabulu mu wanke rediyon nan`` Sai ya zama abin kakaci tsakaninsu bayan shekaru sun yi nisa. 
   
   Wani zai yi zaton wannan labarin almara ne, amma kuma wanda abin ya faru da shi yana nan a raye, auren na su ya zarta shekaru talatin yanzu haka suna tare.

*_TAKAI-TACCEN SIFFAR WANNAN MATAKI:-_*

   - Marari da Qaddara juna
   - Haduwar juna da sanin hakikanin juna a aikace
    - Kaddara juna da kokarin biya wa juna buqata
    - Bai wa juna uzuri a kan abin da ba daidai ba
    - Qokarin fitowa a sifa mafi kyau a halitta da dabi'a ga juna.

*_MATAKI NA HUDU:- SABAWA_*

*Zamu tsaya daga nan sabida gobe mu tashi daga farkon wannan mataki (Na biyar) zuwa Qar'shen sa Insha Allah*

*_✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd_*

Share:

YAREN SOYAYYA 08


*_💝🌹//YAREN SOYAYYA 008//🌹💝_*

*_Wallafar:- Dr Abdulkadir Ismail Kano_*

*_Mataki na uku: HADEWARJUNA:_*
  
A wannan mataki ne mutum yake yanke shawarar cewa yana son ya kasance da Wanda yake so har abada ta hanyar yin sure. Saboda wannan sinadari na maganadisu da yake tare dasu yana jansu. Da za'ayi kokarin hana su yin wannan aure, sai su fandare, ko su nemi halaka kan su, ko su sami tabin hankali, ko su hadu da mummunan tashin hankali.
   Bayan an zama daya, sun tare a sabuwar shekarsu, sai dukkan su suyi kokarin boywa juna aibin juna, ma’ana bata son ya ganta dagajaja, shima ya zama dan tsaf-tsaf da safe, ya sanya turare, ya goge hakora da safe, zata yi gaggawar tashi don ta danyi shafe-shafe, ya shirya abinci, ta share gida ta kimtsa komai. Shi kuma a bangarensa zai yi iya kokarinsa don ya nuna jarumtakarsa. Da zata nemi a sayo wani abu idan ya fita, to zai kawo, koda kuwa sai yaje yayi rance ne, wani lokaci ma don ya burgeta zai kawo kafin ta tambaya. Yakan iya bada uzuri akan wani abu da yasan ba daidai bane, Saboda kada ya bata mata, kuma har zuwa wannan lokacin mutum yana kokarin ganin daidanta, ya gimtse ido ga duk wani kuskurenta ya bada uzuri akan sa, haka itama take kokarin tayi, tana fassara wani abu da yake mata a matsayin soyayya, da za ta ga ya nuna tsananin kishinsa akan wani idan yana kallonta, sai taji dadi domin a wajenta wannan alamar kauna ce.
   Wannan mataki shine yafi kowane hatsari, bayan an hadu an yi aure, to wadannan sinadarai da suke shawagi tsakanin juna sun zo kusa, kuma an San juna sani na kusa, sannan kuma an ga juna gani na kusa, anyi arba a yanayin da babu kwaskwarima mai yawa, amma duk da haka karfin wannan sinadarai za su ci gaba da aiki gwargwadon karfin su, sannan bayan nan su fara dusashewa, karfin shawaginsu ya fara raguwa.
    Wani lokaci, saboda al’ada da kuma wani tsari na daban sukan bude kwalbar wannan sinadarin har ya sulale da wuri, duk da cewa wannan abu ne da yake bukatar wani bayani na daban mai dan fadi a wani tsari na daban.

*_Labari:-_*

    Sun yi aure irin na saurayi da budurwa, kuma da kaunar juna da mararin juna, da kuma...

*_Zamu cigaba Insha Allah_*

*_✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd_*
Share:

YAREN SOYAYYA 07


*_💝🌹//YAREN SOYAYYA 007//🌹💝_*

*_Mawallafi:- Dr Abdulkadir Ismail Kano_*

   A wannan mataki idon mutum yakan rufe, yaji cewa ya fitinu da Wanda yake so, babu abin da yake so yaji sai zancen wannan, babu abin kallo mafi ban sha’awa kamar wannan, ba ya it's mallakar kansa sai ya tuna zancenta, a mafi yawancin lokaci idan ya tunata sai yaji kawai yayi Murmushi Shi kadai.
Ba’a iya gano aibi a wannan mataki, ba a ganin laifi idan an aikata, an fi kaunar mai kaunarta, takan Kai ga cewa har irin atamfarta idan mutum ya gani sai ya sami farin ciki, akan irin wannan yanayi ne aka sami ruwaya daga Abu Darda’i (RA) Yace:
*_«حُبُّكَ الشَّيْءَ يُصِمُّ وَيُعْمِي»_*
“Son ka da abu sai ya kurumtar da Kai ya makantar da kai”. Ma’ana babu wani abu da zaka ji Mai dadi in ba wannan ba, sannan babu wani abu da za ka gani mai kyau in ba wannan ba. A wannan lokacin ne sai mutum ya ga cewa lallai ya wajaba ya mallaki wannan masoyin nasa ta kowace hanya. ta hanyar addu'a, ta hanyar nuna jarumtaka, ta hanyar burgewa, ta hanyar kamun kafa, ta hanyar yin kyaututtuka, ta hanyar kyautata ado, ta duk abin da ya sani cewa Yana burge daya sashen. Wannan shine matakin Farko, matakin juyawar tilas irin jan maganadisu ga karfe. A irin wannan hali, wasu idan ance su yi Istikhara sai su Ki, su ce: Allah dai ya tabbatar mani kuma ya sanya mani alheri a ciki.
*_Takaitacciyar siffar wannan mataki:_*
- Rufewar ido wajen ganin aibin Wanda ake so.
- Rawar jiki da wajen biye wa son zuciyar Wanda ake so.
- Kaucewar tunani na hankali acikin wannan mataki.
- Alakanta gaba ko kauna ga wannan abin da ake so.
*_Mataki na biyu:- FAHIMTAR JUNA_*
   Bayan matakin maganadisu, sai a fara samun fahimtar juna, ma’ana ya fara gane menene abin da bata so, ko tafi ki. Daga nan sai hirarsu ta tsawaita, ta hanyar rubuta wasika ne, ko ta hanyar yin waya ne, ko Kuma ma yaje da kansa, ba don komai ake haka ba, sai don a Kara game juna sosai. Lokaci zai zo har ya Kai ga mutum ya mai da hankali kwarai da gaske kan Wanda yake so, duk wani zance da za’a yi game da ita, ko ita game da shi, wannan Yana burge shi, Kuma Yana mararin jinsa.
Lamarin yakan bunkasa har a fara kokarin sanin dangin juna. kannenta da yayyenta, har da neman kusanci zuwa gare su, da kokarin sanin mai son sa ko maras sonsa a cikinsu. Duk wannan na yiwuwa ne bayan ya tara labarai akan ta don ya Kara fahimtarta. Shi ya sa idan zai fadi wani abu da ya San abin da take so taji ne sai ya fade shi, Yana sane da abin da ba ta son ji, sai ya nisance shi, haka ita ma. Ba za su iya yin hakan ba, ba don sun sami fahimtar juna ba, ta hanyar labarai da suka tara na junan su a cikin kwakwalensu.
Babban abin da wannan mataki na haduwa yayi fice da shi shine; Kaddara juna, Mutunta juna Wanda takan Kai ga cewa har ma mitum ba zai iya ganin aibi ba, Kuma Yana tsananin kula da abin da yake yi don kaucewa bata wa abokin soyayyarsa. Amma duk da haka wannan matakin yafi matakin farko bayyana al’amura yadda yadda yadda kamata, domin akwai masaniyar labarin juna.
*_Takaitacciyar siffar wannan mataki:_*
- Sanin Kai kawon juna da tara labarai akan Wanda ake so.
- Kaddara juna da bin umurnin da aka bayar.
- Sanin dangin juna, da Kuma sanin mai goyon bayansa ko kishiyar haka acikin dangi da makusanta.
- Jin dadin kasancewa da juna da jin labari Mai kyau akan abin da ake so na juna.

*_Zamu cigaba Insha Allah_*

*_✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd_*
Share:

YAREN SOYAYYA 06

*💝🌹//YAREN SOYAYYA 006//🌹💝*

*_Mawallafi:- Dr Abdulkadir Ismail Kano_*

*_BALAGURON RAYUWAR AURE:_*
   Allah Ya yi tsari a rayuwa cewa babu wani abu da zai dawwama a yanayi guda, komai Yana canjawa daga lokaci zuwa lokaci, Kuma wannan canjin yana nuna cikar kadaitakar ALLAH Wanda baya canjawa Shi kadai, dukkan wani abin halitta mai canjawa ne. ALLAH Ya bayyana halittar mutum da cewa: 
*_( اللَّهُ الَّذِي خَلَقَكُم مِّن ضَعْفٍ ثُمَّ جَعَلَ مِن بَعْدِ ضَعْفٍ قُوَّةً ثُمَّ جَعَلَ مِن بَعْدِ قُوَّةٍ ضَعْفًا وَشَيْبَةً ۚ يَخْلُقُ مَا يَشَاءُ ۖ وَهُوَ الْعَلِيمُ الْقَدِيرُ )*_
*(ALLAH ne Ya halitta ku daga rauni, sa'an nan Ya sanya wani ƙarfi a bayan wani rauni, sa'an nan Ya sanya wani rauni da furfura a bãyan wani ƙarfi, Allah na halitta abin da Ya so, kuma Shĩ ne Masani, Mai ĩkon.) [Rum:54]*
  Wannan tsarin shi yake bin dan-adam aduk rayuwarsa, rauni, sannan bayan rauni a samu karfi, sannan bayan abu yayi karfi rauni ya sake kama shi wani lokaci har ya tsufa ya rududduge. kamar haka rayuwar aure take farawa, da karsashi da marari da doki, sannan al’amura su fara ja da baya, sannan wani lokaci su sane baki daya komai ya zama lami. Kuma wannan itace dabi’ar duk wani abu na duniya. 

*_Kamar yanda Manzon ALLAH (ﷺ) ya bayyana mana acikin Hadisi:_*
*”حَقٌّ عَلَى اللَّهِ أَنْ لاَ يَرْتَفِعَ شَيْءٌ مِنَ الدُّنْيَا إِلَّا وَضَعَهُ “*
  *_“Alkawarin ALLAH ne cewa; Babu wani abu na duniya da zai daukaka sai ALLAH ya dawo dashi kasa.”_*
  A bisa wannan fahimta, Malamai masana halayyar dan-adam, da Kuma lura da lamura sun bayyana matakai na haduwar mutum da matarsa, tun Yana alakar tana jaririya har ta girma har Kuma ta tsufa kamar haka:
*_Matakin Farko:- MAGANADISU-*
   Da larabci sukan kira shi da *_(مرحلة الانجذاب)_*, da turanci *(Infatuation Stage)*, wannan mataki yakan zamo kamar yadda mayen karfe yake janyo karfe, matukar sunyi arbu, to sai ya janyu zuwa gare shi. Maganadisunsa zai fizge shi, ba tare da yayi la’akari ba, ba tare da ya shirya ba, kwatsam sai ya ji shi ya kamu. shiyasa ake cewa: Ciwon soyayya ya kama shi, ya fada cikin kogin soyayya, soyayya ta fizge shi, ya kamu, da dai sauran kalmomi da ake amfani dasu. irin haka zaka ji a harshe kamar larabci sai ace: *(وقع في الحب، شغفه الحب*) da sauran su, a turanci ace: *_(Falling in Love)_* ma’ana dai mutum fadawa yayi, idan kuwa akace mutum ya fada, to ma’ana bai shirya ba, an debe tsammani, Bai yi zaton abin zai bayu zuwa ga hakan ba.
  Soyayya wata kalma ce da masana suka ce tana da fadin gaske, tana da zurfin gaske Wanda hakan ya Sanya tana da wahalar fahimta ko iyakancewa acikin wadansu kalmomi. Wannan ne ma ya Sanya suka ce babu wani malami da ya taba yin ta’arifin soyayya Kuma yaci nasarar iya bayyana ta ba tare da wani tasgaro ba.
  Ita soyayya wani abu ne da mutum yakan ji a zuciyarsa na Yana son ya fadada kansa, ya Kara buda kansa ya Kara yawaita kansa ta hanyar kamfato wani zuwa gare shi. Yayin da mutum yake son wata ko wata take son wani, kamar tana so ne ta fadada kanta don ta karu ta habaka, Kuma har ta wanzu tsawon lokaci.
  A irin wannan yanayi ne zaka samu nau’in soyayya iri-iri, kamar shakuwa, domin rabuwa wani nau’i ne na rage fadadar mutum, zaka samu tsoro akan wani abu kamar 'Da, saboda shima wani bangare ne na fadadar mutum, haka kishi akan Mata ko mace akan mijinta, saboda kaucewa tuntube da wani zai yi don ya yafi ce shi, da misalai irin wannan. Wannan yake bayyana cewa akwai bambanci tsakanin fadawa cikin soyayya, ko kamuwa da soyayya da Kuma ita soyayyar kanta, domin a yayin da mutum yake kokarin fadada shi da kansa ne yake hobbasa, Kuma ya Sanya himma, Amma faduwa kuwa bashi yake yi ba, samun kansa yake yi a ciki. 

*A bayanai masu zuwa za mu yi kokarin bayyana wannan bambanci.*

*_Zamuci gaba Insha Allah_*

*_✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd_*

Share:

YAREN SOYAYYA 05


*💝🌹//YAREN SOYAYYA 005//🌹💝*

 *_Mawallafi:- Dr Abdulkadir Ismail_*

 *_9- Kare Al`umma Daga Lalacewa Da Sakwarkwarcewa_*
  Rashin aure na janyo yaduwar alfasha, yaduwar alfasha na sanya samar da `ya`ya da ake Haifa ba tare da tabbatatun Iyaye ba. Idan yaro ya zamo bai san mahaifinsa ba, yakan taso ne cikin matsalar rayuwa, kuma uwar ta sa takan kasance cikin matsananciyar wahala wajen kula da shi, da kokarin faranta masa.
  A qasar Iran a yau akwai tattaunawa mai zafi tsakanin masu ganin a ci gaba da barin Mut'ah na gudana da kuma masu ganin cewa dole a tsayar haka. Dalilin masu ganin lallai dole a tsayar da yin Mut'ar ya hada da; yaduwar yara da ake kiran`ya`yan titi, wadanda ba su dangantuwa da kowa. Hakan ya sanya su sun tsunduma cikin aikata muggan laifuka masu hatsarin gaske, kamar kisa da sata da fesa sinadarin Acid a fuskar mata masu fitowa da ado, da kashe mata masu zaman kansu. Sannan barin Mut'ar ya qara sanya mazaje suna iya fita waje su biya buqatarsu ba a wajen matansu ba, kuma sakin aure ya yawaita, kuma idan aka yi sakin, mace sai ta shiga harkar Mut'ah gadan-gadan don ta iya ci da kanta.
  Rashin samun nasaba tsakanin da da wanda ya yi dalilin samuwarsa yana haifar da rugujewar tsarin iyali da zamantakewa, ya yanke alaqa tsakanin `yan uwa ta yadda dangi ba za su yarda da dan da ba a san ubansa ba, yana je fa yaro cikin mummunar tarbiyya, ya batar da nasabar mutum, kuma yana sanyawa a baiwa wani haqqin da bai cancanta ba wajen gado, wadannan da ma wasu dalilan duk sabubba ne na sukurkucewar al`umma baki daya, kuma wannan kadai na tabbatar da muhimmancin sanin manufar aure a Musulunci.

*_10- Kare Al`umma Daga Cututtuka Masu Fatattakar Zamantakewar Al`ummah_*
   A yau bai zama abu boyayye ba cewa cututtuka masu kacalcala al`umma suna yaduwa kamar wutar daji, cuta mai karya garkuwar jiki (AIDS) cutar ciwon sanyi, cutar neman kananan yara, cutar jinsi daya da sauransu suna ta yaduwa saboda mutane suna son su biya buqatarsu wadda Allah ya halitta musu ba ta han-yar aure ba. Yin aure na kare al`umma baki daya daga wannan annoba da take yaduwa ta cututtuka, tabbaci ne na kashedin da Manzon Allah ﷺ yayi mana inda ya ce:-

”خَمْسُ خِصَالٍ يَا مَعْشَرَالْمُهَاجِرِينَ أَنْ تَنْزِلَ بِكُمُ أَعُوذُ بِاللَّهِ أَنْ تُدْرِكُوهُنَّ: لَمْ تَظْهَرِ الْفَاحِشَةُ فِي قَوْمٍ قَطُّ حَتَّى يُعْلٌنُوا إِلَّا فَشَا فِيهِمُ الطَّعُونُ والأَوْجَاعُ الَّتِي لَمْ تَكُنْ فَشَتْ فِي أَسْلَافِهِمْ.“

  ``Ya ku taron Muhajirai (wadanda suka yi hijira)! Abubuwa biyar idan aka jarrabe ku da su, kuma suka sauko muku- ina neman Allah ya tsare kada ku riske su: alfasha ba za ta taba bayyana ba cikin wata jama'a har su bayyana ta sai cututtuka wadanda a da ba asansu ba sun bayyana a cikinsu....``.
   Abin fahimta a wannan gaba shi ne:- mutum ya zauna ya yi karatun ta nutsu a kan dalilin da ya sa zai yi aure, kuma ya sanya wannan burin basa a gaba don qoqarin cimma wannan burin, irin yadda mutum yake neman kudi ko karatu ya fadi ko ya rasa a wani lokacin, umma wannan ba ya sanya shi ya ce ya fasa, sai dai ya qara kaimi da gyara kus-kure. Wani manufarsa za ta iya zama gaba dayan abin da aka ambata ne da kari wani kuma wani bangare ne daga cikin abin da aka ambata, amma dai a fahimci cewa aure a Musulunci ba kawai ta-more ba ba ne, a,a akwai manufofi masu tarin yawa a ciki wadan da sukan zama linzami daga kaucewa daga kan hanya ta daidai.
   Wadannan manufofi na aure da Musulunci ya tsara, dukkansu masu muhimmancin ne, da ace don soyayya kadai ake yin aure da kuwa an tozarta abubuwa da dama, daga ciki idan mutum ya ga cewa shi ba ya jin soyayya a cikin zuciyarsa, sai ya sanya qafarsa ya fice daga cikin gidan aure, ya bar yara da aka haifa a tozarce. Sai kuma ta fita ko ya je ta qara aure, ta qara rasa soyayya sai ta sake ficewa ta sake tozarta yara don kawai biyan buqatar zuciyarta. Wannan dalilin ne ya wajabta wa mutum a matsayinsa na Musulmi ya san cewa aure na da manufofi dama ba lallai soyayya kadai ba, kuma ya yi iya qoqarinsa don kare wannan manufar don samar da al`umma ta gari.

*_Zamu cigaba Insha Allah_*

*_✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd_*
Share:

YAREN SOYAYYA 04


*💝🌹//YAREN SOYAYYA 004//🌹💝*

 *_Mawallafi:- Dr Abdulkadir Ismail_*

*_4- Dawwamar Da Wanzuwar"Yan Adam a Bayan Qasa_*
   Allah Ya sanya dan Adam halifa a bayan wannan kasa, kuma Ya umarce shi da ya raya ita wannan qasa ya haramta masa yin duk wani abu da zai kawo barna a ban qasa, saboda yin haka zai cutar da dan Adam, duk kuwa abin da zai cutar da `Yan Adam haramun ne aikata shi. Babbar cuta ga dan Adam ita ce a rasar da shi, a kashe koh a tauye shi, kashe dan Adam guda daya kamar kashe dukkan mutane ne baki daya, haka ma raya shi. Wannan yake nuna haramcin wani abu da zai janyo raguwar `yan Adam da kuma wajibcin bin hanyar yaduwa `yan Adam. 

*_5-Daukar Nauyin Mace A Matsayinta Na Uwa Ko `Ya_*
    Mace takan zama uwa ko mata ko `ya ko `yar uwa, duk wannan kashe-kashe daukar nauyinsu wani abu ne da Musulunci ya ba shi Muhimmancin kwarai da gaske. Uwa ita ce wanda ta fi kowa, cancantar a kyautata mata a duk rayuwa, mata kuwa ladan kula da ita ya gabata a Hadisi, `ya mace kuwa idan har sun kai biyu, to Manzon Allah ya ce:-

« مَنْ عَالَ جَارِتَيْنِ حَتَّى تَبْلُغَا جَاءَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ أَنَا وَهُوَ.» وَضَمَّ أَصَابِعَهُ.

 ``Duk wanda ya dauki nauyin kula da `ya`ya mata guda biyu har suka girma, to zai zo ranar alkiyama ni da shi kamar haka`` Manzon Allah ya gwama tsakanin `yan yatsunsa biyu manuniya da ta tsakiya. 
   Su ma `yan uwa mata ladan kulawa da su ba qarami ba ne, har sahabbai sukan bar auren wanda zuciyarsu take so don su kula da `yan uwansu mata.

 عَنْ جَابِرٍ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ هَلَكَ أَبِي وَتَرَكَ سَبْعَ بَنَاتٍ أَوْ تِسْعَ بَنَاتٍ فَتَزَوَّجَتْ امْرَأَةً ثَيِّبَا فَقَالَ لِي رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ تَزَوَّجْتَ يَا جَابِرُ فَقُلْتُ نَعَمْ فَقَالَ بِكْرَا أَمْ ثَيِّبًا قُلْتُ بَلْ ثَيِّبًا قَالَ فَهَلَّا جَارِيَةً تُلَاعِبُهَا وَتُلَاعِبُكَ وَتُضَاحِكُهَاوَتُضَاحِكُكَ قَالَ فَقُلْتُ لَهُ إِنَّ عَبْدَ اللَّهِ هَلَكَ وَتَرَكَ بَنَاتٍ وَإِنِّي كَرِهْتُ أَنْ أَجِيئَتُهُنَّ بِمِثْلِهِنَّ فَتَزَوَّجْتُ امْرَأَةً تَقُومُ عَلَيْهِنًَ وَتُصْلِحُهُنَّ فَقَالَ بَارَكَ اللَّهُ لَكَ أَوْ قَالَ خَيْرَا.

  An karbo daga Jabir dan Abdullahi (R.A) ya ce:- Mahaifina ya rasu ya bar `ya`ya mata bakwai ~ Ko cewa ya yi tara- sai na Auri bazawara, sai Annabi ya ce da Ni:- ``Jabir ka yi aure ne ? Sai na ce: Na'am. Sai ya ce: ``Budurwa ko bazawara?`` Sai na ce: A,a bazawara ce. Sai ya ce: ``Me yasa ba ka auri budurwa ba da za ta yi ma wasa ka yi mata wasa, ka ba ta dariya ita ma ta sa ka dariya``. Sai na ce: Haqiqa (mahaifina) Abdullahi ya rasu ya bar `yan mata, sai na ji ba na son in auro musu budurwa kamarsu, sai ya auri bazawara da za ta kula da su ta gyara al`amuransu. Sai Manzon Allah ya ce: Allah Ya sanya maka al-barka``.

*_6- Samun Kwanciyar Hankali Da Rahama_*
    Mutumin da Allah Ya azurta shi da abubuwa na duniya mace ko namiji, ba zai sami kwanciyar hankali ba idan ba shi da mata ko ba ta da miji, wannan dalili ya sa Musulunci ya kwadaitar da yin aure don samun kwanciyar hankali da nutsuwar zuci. Allah ya fada a cikin littafinsa cewa:-

( ... أَنْ خَلَقَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَاجًا لِّتَسْكُنُوا إِلَيْهَا وَجَعَلَ بَيْنَكُم مَّوَدَّةً وَرَحْمَةً ۚ )

  ``Ya halitta muku matanku daga kanku don ku nutsu zuwa gare su, Ya kuma sanya soyayya da tausayi a tsakaninku...`` {Rum:21}.

*Kuma Manzon Allah ya ce:*
‏« ﺃَﺭْﺑَﻊٌ ﻣِﻦَ ﺍﻟﺴَّﻌَﺎﺩَﺓِ : ﺍﻟْﻤَﺮْﺃَﺓُ ﺍﻟﺼَّﺎﻟِﺤَﺔُ »

  ``Abu hudu suna daga cikin kwanciyar hankali da jin dadi; salihar mace....``. 
   Samun nutsuwa da kwanciyar hankali da soyayya wata manufa ce ta aure tabbatacciya a Musulunci wanda mutum ya kamata ya sanya a cikin manufofin yin aur.

*_7- Rabauta Da Ni'imar `Ya`ya_*
     `Ya`ya ni`ima ce babba a rayuwar dan Adam, ba ga dan Adam kadai ba, Allah Ya nuna mana ishara har ga dabbobi yadda suke himmatuwa ba himmar wasa ba wajen kare `ya`yansu da kuma nuna musu qauna, wannan ya tabbatar mana da cewa samun `ya`ya da kulawa da su wata ni'ima ce babba ba wanda yake fahimtar haka sosai sai wanda ya rasa `ya`yan. Ba kasafai akan samun mutum ya zama daidai ba a hankalce idan ya zamo Allah bai ba shi haihuwa ba, ba qaramin gibi ake samu a cikin zuciyar wanda Allah bai taba ba shi haihuwa ba. Musulunci ya sanya yin aure ne don a tabbatar da samuwar daidaito da kuma cike wannan gibi na rashin da.
  Mutumin da ya zamanto bai san mahaifinsa ba, ko ake shakkarsa, ko kuma an san shi amma ba ta han-yar aure aka same shi ba, yana rayuwa ne daidai da matacce, ko kuma ya zama matsala ga al`umma saboda gabar da zai ringa yi da saura al-umma. 

*_8- Samar Da Musulmin Gida Ta Han-yar Iyalie_*
   Musulmin gida, wata al-umma ce ta ginu daga daidaikun mutane har suka zama jama'a suka zama al-umma. Tubalan ginin wannan al-umma su ne Musulman gidaje da suka tattaru suka tada katangar wannan gini na al-ummar Musulmi. Kowane Musulmi tubali ne a cikin wannan ginin, kuma ana buqatar tubalin ya zama mai nagarta da qarko. Idan mutum ya tarbiyyantar da gidansa tarbiyya ta Musulunci sahihiya to wannan gini sai ya yi kwari ya zama nagartacce, idan kuma tarbiyyar iyali ta samu tazgaro to lallai wannan gini ba zai yi qarko ba, sai al`ummar Musulmi su nakasa. 
  Daga manufar aure a Musulunci shi nesamar da tubali ingantacce wanda za`a hada a tada ginin al`ummar Musulmi.

*_Zamuci gaba Insha Allah_*

*_✍️Ibrahim Muhammad Abu Muh'd_*
Share:

YAREN SOYAYYA 03

*_💝🌹//YAREN SOYAYYA 003//🌹💝_*

*_Wallafawa:- Dr Abdulkadir Ismail Kano_*

   *_MANUFAR YIN AURE A MUSULUNCI_*

  Idan mun gano cewa lallai a cikin zamantakewar aure wani abu ne da yake tasiri a farkon auren, bayan nan kuma ya yi kasa, to ya kamata kuma mu kula da cewa mu Musulmi ba wannan ne kadai abin la`akari a wajenmu ba, Musulunci ya sanya mana manufofi tabbatattu wadan da zasu sanya mu mu riqe aure har zuwa lokacin da zamu bar wannan duniyar, kuma saninsu da riqo da su ya zama wani kalubale ne ga dukkan Musulmi.
  Dan Adam mai hankali yana yin abu ne da manufa, mutum marar manufa a cikin lamarinsa daidai yake da mutumin da ya fito da safe daga gidan sa amma bai san inda za shi ba, irin wannan mutumin duk inda iska ta kada shi nan zai yi. A Musulunci mutum yakan sami lada ne gwargwadon irin niyyarsa, kuma daidai da dace da ya yi na samun dacewa da manufar addinin Musulunci.
  Ana yin aure ne a Musulunce saboda dalilai da dama, kuma sanya wadannan dalilai a gaba su ne sukan zamo sitiyari na rayuwar aure, kuma su taimaka wa mutum shanye duk wata damuwa da zai iya gamuwa da ita saboda sanin muhimmancin manufar da ta sa shi ya yi auren. Daga cikin manufofin akwai:- 

  *1- Yin Biyayya Ga Umar'nin Allah (s.w.a) Da Manzons (ﷺ).*

   Allah Mai girma da buwaya Ya yi umar'ni da a yi aure kuma Manzon Allah ﷺ ya qara bayyana wannan lamari qarara. Allah Yana cewa:-

( وَأَنْكِحُوا الْأَيَامَى مِنْكُمْ )

  Ma`ana:- (Kuma ku aurar da marasa aure mata daga cikinku) *_(Nur:32)_*

  Kuma Manzon Allah ﷺ ya ce:- 
« يَا مَعْشَرَ الشَّبَابِ مَنِ اسْتَطَاعَ مِنْكُمُ الْبَاءَةَ فَلْيَتَزَوَّجْ ...»

  ``Ya ku taron samari! Duk wanda yake da ikon yin aure to ya yi...``
  
  Wadannan Umar'nin daga Allah (s.w.a) da Manzonsa ﷺ sun isa abin zaburarwa ga duk wani Musulmi mai koqarin biyayya ga Allah, kuma sanin cewa aure bautar Ubangiji ne, zai sauqaqa wa mutum duk wani radadi da zai ji a ciki bayan ya gamu da abin da baya so a lokacin da ya yi aure, kuma wannan zai zame masa waqar gindi na yin haquri da matsalolin aure da zai fuskanta. 

*2- Neman Lada A Cikin Aure*

   A tsarin rayuwa ta Musulmi, yakan yi dakon sanin wani abu da Allah yake so, kuma yake ba da lada a kansa don ya aikata shi. Aure na daga cikin abubuwa a Musulunci wanda ba kasafai za a iya samun abin da ya fi shi kawo lada mai gwabi kamarsa ba. Idan mutum ya sadu da matarsa, ko mace ta sadu da mijinta akwai lada mai girma a ciki,
 Manzon Allah ﷺ ya ce:-
 
  « وَفىِ بُضْعِ أَحَدُكُمْ صَدَقَةٌ »

  ``A cikin saduwar da za ku yi da (Iyalanku) akwai lada``

  Manufa idan mutum ya sadu da iyalinsa to a wannan abin da ya yi, bayan ya ji dadi, ya debe sha'awarsa, kuma Allah kuma zai ba shi lada. 
  Manzon Allah ﷺ ya ce:- 
 
« وَلَسْتَ بِنَافِقٍ نَفَقَةً تَبْتَغِي بِهَا وَجْهَ اللَّهِ إِلاَّ آجَرَكَ اللَّهُ بِهَا حَتَّى اللُّقْمَةَ تَجْعَلُهَا فِي امْرَأَتِكَ »

   ``Babu wani abu da za ka ciyar kana neman yardar Allah, sai Allah Ya ba ka lada a ciki, har lomar da za ka sanya a bakin matarka``. 

   Ma'ana idan mutum ya kawo abinci da iyalinsa suka ci, to wannan akwai lada a ciki. A dunkule yin aure da wannan manufar wani babban Abu ne a Musulunci.

*3- Kare Kai Daga Fadawa Cikin Alfasha da Mataimakanta*

  Allah (s.w.a.) Ya umarci muminai maza da mata da su rufe idanuwansu daga kallon mata wadanda ba nasu ba, wannan yana nuna haramcin kallon matar da ba muharrama ba ga mutum ko mijin da ba muharrami ba ga mace. Tabbatar da bin wannan umar'ni yana da wahala kwarai da gaske idan ba ga wanda ya zamo yana da aure ba, wannan ne ya sa Manzon Allah ﷺ ya sifanta yin aure da cewa:-
« فَإِنَّهُ أَغَضُّ لِلْبَصَرِ وَأَحْصَنُ لِلْفَرْجِ »

   ``(Yin aure) shi ne ya fi kare ido (daga kalle -kallen haram) kuma ya fi kare farji (daga fadawa cikin alfasha)``. 
   Ko da mutum ya yi azumi, ko ya nisanci inda mata suke, wannan bai kai kamar mutum ya yi aure ba wajen kare kai daga fadawa cikin alfasha, kuma Hadisin Jabir dan Abdullahi (R.A) yana qara fito da wannan lamari quru-quru.
   عَنْ جَابِرٍ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَأَى امْرَأَةً فَأَتَى امْرَأَتَهُ زَيْنَبَ وَهْيَ تَمْعَسُ مَنِيئَةً لَهَا فَقَضَ حَاجَتَهُ ثُمَّ خَرَجَ إِلَى أَصْحَابِهِ فَقَالَ: « إنَّ الْمَرْأَةَ تُقْبِلُ فِي صُورَةِ شَيْطَانٍ وَتُدْبِرُ فِي صُورَةِ شَيْطَانٍ، فَإِذَا أَبْصَرَ أَحَدُكُمُ امْرَأَةً فَلْيَأْتِ أَهْلَهُ فَإِنَّ ذَالِكَ يُرَدُّ مَا فِى نَفْسِهِ »

  Daga Jabir dan Abdullahi (R.A), cewa Manzon Allah ﷺ ya ga wata mata, sai ya tafi wajen Zainab matarsa a lokacin da take jeme wata fata tata, sai ya biya buqatarsa da ita, sannan ya fito wajen sahabbansa ya ce:- ``Haqiqa mace tana fuskantowa ne da surar shedan , tana kuma ba da baya da surar shedan, idan wani daga cikinku ya ga wata mace (ta ba shi sha'awa) to ya tafi wajen iyalansa domin wannan zai kare shi daga abin da ya ji a cikin zuciyarsa``.

*_Zamu cigaba Insha Allah_*

*_✍️Ibrahim Muhammad Abu Muh'd_*

Share:

YAREN SOYAYYA 02


*💝🌹//YAREN SOYAYYA 002//🌹💝*

*_Wallafar:- Dr Abdulkadir Ismail Kano_*

*_MANUFAR WANNAN DAN LITTAFIN_*

_Manufar wannan littafin shine:-_
  • Fahimtar da ma'aurata wasu halayyar da ke tare da su, amma yawanci ba su sansu ba
  • Bayyana hanyoyin da suka kamata a bi don wanzar da zamantakewar aure, da kuma kaucewa rashin fahimtar juna
  • Ilimantar da ma'aurata da Iyayensu bambance-bambancen da ke tsakanin daidaikun mutane, don samar da fahimta ta kwarai ba maimaita abin da wani ya yi ba
   • Nuna cewa kowane Mutum akwai abin da Allah ya sanya masa shi ne abin da yake so ko ya fi so, ko kuma qi ko ya fi qi.

*_MUHIMMANCIN WANNAN RUBUTU_*
   Idan muka yi la'akari da yawan aure da aka yi a wannan zamanin, da fahimtar mutane wayen raya Sunnar Manzon Allah ﷺ a wannan bangare, da kuma samun matsaloli da ake yi a cikin wannan aure, da yawan koke daga duk bangarori; maza da mata a kan zamantakewaa, lallai hakan zai wajabta a sake duba don bada gudunmawa wajen takaita damuwa, da kawar da matsala, da bin hanyoyin da zasu sanya aure ya zama waje na sa'ida da hutu da jin dadi, nesa da abin da ake bayyana wa mutane a fina-finai, da kuma kafofin yada labarai na nuna ai shi dama aure matsala yake dauke da ita. 
  Daga cikin muhimmancin wannan talifi shi ne; bayyanawa ma'aurata masu buqatar gyara zamantakewarsu, kan cewa lallai aure na gyaruwa koh bayan an samu matsala, kuma ana iya sauyawa sama bisa kasa, daga ba daidai ba zuwa daidai, wanda hakan takene na addininmu na cewa duk bar'na tana gyaruwa.
    Abinda zai qara sanya wannan talifi ya zama mai muhimmanci shi ne, kasancewar Iyaye da kakanni sun yi nesa da 'ya`ya, ko kuma suna shakkarsu, sabida `ya`yan sun yi karatun boko, sai suke zaton sun fi Iyayensu sani, amma kuma alal haqiqa, sun jahilci yadda zaman aure yake, kuma su iyayen ba su day kar'fin gwiwa su gaya musu abin da haqiqanin aure yake buqata, ko yake dauke dashi.
  Aure sunna ce ta Manzon Allah ﷺ , wanda ba ya son aure haqiqa ya nuna rashin sonsa ga abin da Manzon Allah ﷺ yake so. Wannan dan littafi yana koqari ne don nusar da mai karatu kan cewa:- 
  • Soyayya jigo ne a cikin aure a musulunci, kuma abu ne da ya wajaba a karfafi samuwarsa da karuwarsa 
  • Ko wane dan Adam akwai irin abin da Allah Ya sanya masa so a cikin wannan duniya. Mutum a dan wannan talifi, zai fahimci shi me ya fi so, sannan kuma yaya zai gane abin da abokin zamansa ya fi so.
  • Gano cewa yawancin sabani yana faruwa ne, ba don babu soyayya ba, amma saboda an kasa gane abin da yake janyo matsalar da take kawo sabani tsakanin ma'aurata 
  • Muhimmancin wannan talifi yana da alaqa ne da bayyana hanyoyi mafiya sauki da mutum zai bi ya mallake zuciyar abokin zamansa, sannan shi kuma ya sami rayuwa mai am-fani da sa`ada.

*_MUHIMMANCIN DAWWAMAR SOYAYYA A ZAMAN TAKEWAR AURE A MUSULUNCI_*
  
   Dukkan wani aiki da mutum yake yi ya kasu ne gida uku (3) ; ko dai ya zama yana yin aiki tare da cewa yana sane kuma da ganin damarsa, ko kuwa dai ya zama yana yin aikin ne ba tare da ya sani ba kuma babu ganin damansa, ko kuma wani ya sanya shi tilas ya yi wannan aikin ko ba tare da yana so ba. Aiki da mutum zai yi da saninsa ana kiran wannan da 
  A. "Iradiyya" ma'ana mutum yana sane, kuma radin kansa yaso ya yi wannan aikin, kamar soyayya ko kiyayya ko dukan wani, ko neman ilimi da sauransu.
  B. "Dabi`iyya" wanda shi mutum yana yinsu ba tare da ya yi la'akari da hakan ba , kamar yadda idan iska ta zo, mutum zai motsa giransa, ko kuma idan ya dirgo daga wani daki kasa zai yi ba zai iya yin sama ba, ko kuma jariri da yake kama nonon babarsa ba tare da yana da wannan ilimin ba, kamar yadda mutum yake furzar da abin da ba ya so idan ya shiga bakinsa.
  C. "Kasriyya" wato wani ya sanya mutum dole ya yi wannan aiki, kamar a dura wa mutum ruwa ko giya dole ya sha saboda an fi kar'finsa, ko a yi kokarin halaka dansa ko matarsa don ya yi wani abu ko wani abu da ya yi kama da haka.

  Aiki na farko mutum na yi ne don dayan abu biyu (2); ko dai don ya janyo wa kansa maslaha, ko kuma don ya ture wani abu da zai cutar da shi. Da wannan mutum ya bambanta da sauran halittu, saboda Allah Ya ba shi hankali na gane abin da zai cutar dashi, da kuma abin da zai amfanar da shi, kuma soyayya abu ne da kan janyo wa mutum jin dadi da annashuwa, shi ya sa dan Adam yake zabansa, kuma kishiyarta `kiyayya` na janyo damuwa da kunci da rashin jin dadi, saboda haka dan Adam yake gudun kiyayya, har ya tafi yaki saboda kawar da wannan kiyayyar.
  Shi kuwa Musulmi ya ginu ne a kan tabbatar da maslaha da kuma kawar da bar'na da cuta da qunci. Saboda haka Musulunci ya yi umar'ni da a gina aure a bisa soyayya da qauna, kuma a gujewa aure a kan kiyayya da cutarwa. Amma wani lokacin idon 👁️ dan Adam kan rufe a kan abin da yake so, tare da cewa akwai barna mai girma a ciki gare shi, kuma yakan iya kin wani abu alhali kuwa akwai maslaha mai yawa a gare shi, a wannan lokacin ne ya wajaba a nemi taimakon Allah, da shawarwarin kwararru da kuma dawowa cikin hayyaci yayin yin soyayya ko kiyayya. 

  Allah Yana cewa:- 

 كُتِبَ عَلَيْكُمُ الْقِتَالُ وَهُوَ كُرْهٌ لَّكُمْ وَعَسَىٰ أَن تَكْرَهُوا شَيْئًا وَهُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ وَعَسَىٰ أَن تُحِبُّوا شَيْئًا وَهُوَ شَرٌّ لَّكُمْ وَاللَّهُ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ

  "Mai yiwuwa ku qi wani abu alhali kuwa alheri ne a gare ku, mai yiwuwa ku so wani abin alhali kuwa sharri ne a gare ku, Allah ne masani alhali kuwa ba ku sani ba" (Baqara: 216)
  
  A bisa wannan aka ruwaito daga Manzon Allah ﷺ 

 عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَبَّاس قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ” أَلاَ أُخْبِرُكُمْ بِنِسَائِكُمْ مِنْ أَهْلِ الْجَنَّةِ الْوَدُودُ، اَلْعَؤُدُ عَلَى زَوْجِهَا، اَلَّتِي إِذَا آذَتْ أَوْ أُوذِيَتْ، جَاءَتْ حَتَّى تَأْخُذَ بَيْدَ زَوْجِهَا، ثُمَّ يَقُولُ وَاللَّهِ لاَ أَذُوقُ حَتَّى تَرْضَى.“

  Daga Abdullahi dan Abbas (R.A) ya ce: Manzon Allah ﷺ ya ce: "Shin ba na baku labarin matayenku `yan al-jannah ba? Ita ce mai qaunar mijinta kuma take yin duk abin da zai kaunace ta, mai haihuwa, mai ba da haquri ga mijinta idan sun bata, ita ce wadda idan ta cutar da wani ko aka cuce ta, sai ta riqe hannun mijinta ta ce: Wallahi yau ba ni ba barci har sai ka yi haquri". 
  A bangaren maza kuwa Manzon Allah ﷺ sai ya bayyana su ma`yan al-jannah: 
  ﻋَﻦْ اﺑْﻦِ مَسْعُودٍ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: أَلاَ أُخْبِرُكُمْ بِمَنْ تُحَرَّمُ عَلَيْهِ النَّارُ، بَلَى يَا رَسُولَ اللَّهِ، قَالَ: عَلَى كُلِّ هَيِّنٍ، لَيِّنٍ، قَرِيبٍ، سَهْلٍ.
  An karbo daga Abdullahi dan Mas'ud (R.A) daga Manzon Allah ﷺ ya ce: "Ba na baku labarin wanda wuta za ta haramta a gare shi ba?". (Sahabbai) suka ce: Muna so Ya Manzon Allah ﷺ sai ya ce: "Ta haramta ga dukkan wani mai sauqin (lamari) mai taushin (hali) na kusa ba murdadde ba".
  Hadisan nan guda biyu, suna tabbatar mana da wasu sifofi na bai daya da ya kamata a sifantu da su a zaman aure, domin tabbatar da manufar Musulunci a kan lamarin aure, da kuma samar da al'umma ta gari Musulma, sannan kuma a kawar da duk wata cutuwa, a kuma tabbatar da dukkan alheri.

*_Zamuci gaba Insha Allah_*

*_✍️ Ibrahim Muhammad Abu muh'd_*
Share:

YAREN SOYAYYA 1


*💝🌹YAREN SOYAYYAH🌹💝 // 01*
 .
Rubutawa: Dr. Abdulkadir Ismail

          *_SHIMFIDA_*
Godiya gaba dayanta Allah ne ya cancance ta, muna gode masa muna neman gafararsa, kuma muna neman taimakonsa. Dacensa da shariyarsa da yardan sa su ne babban rabo, tabar barewar'sa da rashin taimako daga gare shi ita ce babbar hasara. Salati da sallama ga masoyinsa, abin Qaunar mu annabi Muhammad, ya shiryar damu zuwa ga han-yar tsira, ya isar da sako kamar yadda Allah ya umarce shi, ya koma ga Ubangijinsa bayan ya isar da amanar da aka daura masa, Allah yayi dadin tsira da aminci da sallama gare shi da iyalansa da sahabbansa da duk wanda sukabi tafarkinsa har izuwa ranar Qar'she.
.
Aure shi ne ginshikin Samar da zuri'a tagari a addinin musulunci, kuma wan-zuwarsa al'amari ne da wannan addinin, ta hanyoyi daban-daban ya lazimta a kula da shi, lalacewarsa abin ki ne kyama matukar ba lalura bace Mai kar'fin gaske ta wajabta hakan ba. Manzon Allah ya yi umar'ni da a auri mace wadda ake qauna, kuma take tarairayar mutum da kauna. Anas dan Malik yace:
يٱمرنا بالباءة، وينهانا عن التبتل نهيًا شديدًا ويقول: تزوجوا الودود الولود". 
Manzon Allah ﷺ ya kasnce yana umartar'mu da yin aure, kuma yana hana mu hani mai tsanani ga kin yin aure, kuma yana cewa: "Ku auri ( Mata ) masu son ku kuma masu haihuwa". Ma'anar "Wadud" ita ce wanda take son mutum kuma take yin abin da zata janyo hankalinsa ya so ta.
.
Mafi yawancin lokuta aure yana kasancewa ne a bisa soyayyah, wani lokacin ma'aurata sukan iya baje turjiyar da a kan samu daga wajen magabatansu wadanda ba lallai su kasance cikin farin ciki da haduwar ba, wani lokacin turjiyar masoyan kan sanya a yi baran-baran tsakanin iyaye da `ya`ya. Amma kwatsam! Ba tare da an dauki shekaru ba, sai a ga auren yana reto, ko ya sane, ko yana neman tabar-barewa ma baki daya, ko ma an rabu ta hanyar saki, kuma ba tare da wannan soyayyar da aka yi a farko ta iya tabuka wani gudunmawa wajen ceto auren ba .
.
Wannan yakan sa mutane da yawa su yawaita tambayar cewa: me ke faruwa ga soyayya ne bayan an yi aure? Ko dama soyayyar ba ta Allah da Annabi ba ce?
  Ko kuwa ma asalin soyayya da ake fada duk zancen kawai ne ba shi da wani tushe ballantana makama?
  Idan kuwa haka ne, to meyasa Manzon Allah ﷺ Zai yi umarni da a yi aure da soyayyah?
Kuma me yasa har ya raba auren wata da ta nuna cewa tilas aka yi mata da wanda ba ta so?
.
Ko kuwa asiri ake yi dan samar da soyayyah, kuma yake karyewa bayan an yi aure?
  Ko kuwa akwai dai wani abu da ya boyu ga masoyan wanda idonsu yake rufewa a kansa lokacin neman aure, amma sai su ga ya canja bayan yin auren?
  Ko kuwa rashin dawwamar soyayya abu ne da yake cikin jinin hausawa da wadan da suke kewaye da su, ba haka abun yake ba a sauran kabilu na duniya?
.
Wannan dan littafi zai yi kokari ne ya bayyana abin da yake faruwa na rashin gane al'amura yadda ya kamata, tsakanin masoya bayan sun yi aure, zai tattauna wannan al-amari ne ta mahangar shari'ah tare da yin la`akari da masana ilimin halayyar dan Adam suka bayyana game da dabi'ar mutum.   
  Sannan kuma ya yi bayanin wasu matakai da suke dawwamar da soyayyah bayan aure, su kawo fahimtar juna, da janyo hankalin juna don sanya marari ga juna. 
.
  Shi wannan littafi ba wani sabon abu zai kawo ba wanda Malamai da masana ba su yi magana a kansa ba, amma dai zai rattabo shi ne ta wani tsari da watakila mai karatu bai san haka suke kasancewa ba, wani lokacin masana halayyar dan Adam da za a dauko daga cikin abubuwan da Allah ya sanar da su ba lallai su zama Musulmi ba, amma dai Allah cikin baiwarsa yana sanar da wanda ya so abin da ya so, aikin mumini a nan shi ne ya yi amfani da hikima duk inda ya same ta kamar yadda aka ce: 

"الحكمة صالة المؤمن يٱخذها إذا وحدها"

"Hikima abu ne na mumini da ya bata, duk inda yaga abin sa sai ya dauka". 
.
  Muna rokon Allah cikin ludufinsa ya sanya dace a cikin wannan rubutu, kuma ya mikar da karkata a duk inda za ta zo, ya kuma yi budi da fatahi a cikin abin da za a rubuta, domin idan bai ba da dama ba, babu wani abu da zai wakana.
Share:

YAUDARA A SOYAYYA

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_YAUDARA A SOYAYYA_*

Abun dai ruwan dare ne, ba ga mazan ko matan ba.

Kowane 6angare na maza da mata suna ta6a waccan halayya ta yaudara a soyayya kuma suna fuskantar hakan daga abokan zamansu.

To amma shin wai mene ne yake kawo yaudara a soyayya? Mece ce ma ma’anar kalmar yaudara?

Yaudara ita ce, hali na 6oye gaskiya da niyyar cuta ko zambatar wani.

A lokuta da yawa maza su ke sakin jiki har mata su yaudare su, ko kuma su mata suke sakankancewa har maza su yaudare su a soyayya. Ina ganin za ku yarda da ni idan na ce.

A dukkan lokacin da ka ji yaudara to da akwai rashin so da tausayi.

*_MAZA:_*

A sau da yawan lokuta namiji kan makance a kan soyayya har idanuwansa su rufe a kan haka, ya gaza gane macen da ta ke son shi dan abun hannunsa, ko ta ke kula shi kawai saboda rage dare, ko dan wani abu da ta ke nema a wajensa, ko macen da ta ke kula shi ba dan tana son shi ba, sai dan kawai ya matsanta mata akan ta so shi, da macen da ta ke son shi kawai dan tana jin dad’in kalamansa ko jin dad’in hira da shi amma ba dan tana son shi ba, har ta kai daga baya da zarar ta samu wani da take so ko ta gama cimma burinta a gare shi sai ta guje shi. Sai ka ji daga bisani ana mayar da yawu kan cewa ai wance ta yaudare ni, bayan kuma da ma can babu son gaskiya a tsakani.

Domin gujewa fad’awa irin wannan halin, tun da fari akwai bu’katar ka san wasu alamomi da ganinsu zai tabbatar maka da cewa tabbas wance tana sonka da gaskiya. Amma duk da haka sai ka yi taka-tsantsan.

*_MATA:_*

Ke ma akwai bu’katar dukkan wanda ya zo miki da batun soyayya, ki tsaya ki nutsu ki tantance masoyinki na gaskiya, domin gujewa fad’awa tarkon samarin shaho (‘yan-yaudara)

Akwai wani zai zo ne yana son ki kawai dan ya yi alfahari da cewa ke budurwarsa ce. Wani kuma zai yi ‘ko’karin neman hanyar da zai bi ya yaudare ki ne dan ya lalata miki rayuwa. Wani zai zo wajenki dan ya rage dare ne kawai. D.s.

Da yawan ‘yan yaudara, za su iya kashe miki ko nawa ne, har ma su yi wa waninki hidima, dan bu’katarsu ta biya a kanki. Sun iya kalamai masu dad’i amma na yaudara.

Maza ‘yan yaudara suna da wahalar ganewa a wajen mata, wani zai iya zubar miki da hawaye, wai dan duk ki yarda ya na son ki da gaskiya, zai iya siyo miki duk abun da kike so, zai iya baki duk abun da kika bu’kata daga wajensa matu’katar bu’katarsa za ta biya a kanki.

Domin gujewa hakan ya kamata kike lura da irin kalaman da yawanci ke futa daga bakinsu, kike tace na gaskiya da kuma na ‘karya. Karda *SO* ya rufe miki ido ki gaza tabbatarwa da zuciyarki wane yaudararki kawai yake son yi, bayan kin gano hakan ko alamun hakan sun bayyana ‘karara a zahiri, saboda gudun yin da-na-sani daga baya. Wanka da gari dai ba ya maganin yunwa.


Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*

Share:

NAU'IKAN SOYAYYA


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_NAU' IKAN SOYAYYA_*

*1-SOYAYYA DON SHA’AWA:* A wani lokaci mace kan ga namiji ko kuma namiji ya ga mace, sai d’aya daga cikinsu ya ga wani abu a jikin d’ayan har ya ja hankalinsa ya ba shi sha’awa, ya ji yana son wannan mutum saboda wannan abu. To irin wannan ba soyayya bace sha’awa ce da zarar d’aya daga ciki ya biya bu’katar tashi sai a fara neman hanyar rabuwa da juna.

*2-SOYAYYA DON ABUN DUNIYA:* Irin wannan soyayya Ita ce wadda ake yi don kud’i, ko dan kyau ko dan wani ‘kyale-‘kyalen duniya. Ita ma irin wannan soyayya ba ta cika nisa ba, da zarar abun da ake yin soyayyar dan shi ya gushe, sai a fara shirye-shiryen nesanta da juna.

*3-SOYAYYA TA HAK’IK’A KO GASKIYA:* Irin wannan soyayya ita ce wadda ake amfani da hankali da tinani wajen kafa ta. Duk soyayyar da ba a gina ta a kan sha’awa ko wani abun duniya, ko wani mugun nufi ba, to wannan soyayya ta gaskiya ce. Kuma ita ce irin soyayyar da take d’orewa wadda ba ta yankewa har abada.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*
Share:

MENENE SO?


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Menene So?_*

Shi dai so ya kasu kashi-kashi a takaice, shi ne zuciya ta ji tana son wani abu, hakan na iya faruwa ta hanyar jin jin labarin mutum, sauraron muryarsa ko kuma ganinsa a zahiri. A irin wannan yanayi dan’adam yake tsintar kansa da shaukin son kasancewa tare da abin da ya kamu da sonsa.

Allah (SWT) shi ke da ikon sanyawa dan’adam soyayya wani a zuicya, shi ya sa wasu lokuta da dama, idan aka kamu da so ba a iya rabuwa, domin ba yin mutum ba ne, yin Allah ne.

Soyayya Shi ma ya kasu kashi-kashi sai dai in yi bayani a takaice tun da na gaban zamu rika tattaunawa a kai.
A wata ma’anar, Soyayya na nufin isar, watau yin sa a aikace musamman idan wanda ake so ya amince. Da zarar haka ta faru, shi ke an wannan So din ya koma soyayya. Ba a yin soyayya dole sai zukata biyu sun aminta juna, idan ta kasance bangare daya ne kawai yake fama da so, dan’uwansa bai damu ba, to wannan ba soyayya ba ce.
Soyayya ba ta cika dole sai bangarori biyu sun damu da juna, ta hanyar kyautatawa, kulawa da kuma begen ganin juna ko jin muryoyin juna.
Shakuwa
Shakuwa na da dangantaka ko na ce alaka da soyayya, domin duk wanda ya ce soyayya dole a samu *SHAKUWA* a cikinta. Ba lallai ne duk wanda ya shaku da wani to dole sai sun yi soyayya ba. 

Sai dai wata shakuwar takan koma soyayya dalilin kulawa da juna tsakanin saurayi da budurwa.

Amma soyayya sam ba ta yiwuwa matuka babu shakuwa, domin ita tamkar wani sinadari ne yake kai zuciyoyi dausayin da za su fara tunanin ba za su iya rayuwa ba tare da juna ba.

A takaice, Shakuwa tana nufin kasancewa tare da abinda ake so na tsawon lokaci ba tare da an gundiri juna ba.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*
Share:

SOYAYYAR ZAMANI 1

*DA'AWA WOMEN GROUP* 🎤🎤🎤
💞 *SOYAYYAR ZAMANI {1}* 💞


Dan taqaitaccen rubutu akan halin da samari da yan mata suka tsinci kansu da sunan *soyayya.* 

Allah ya kawo mu wani *zamani* da sai dai ace innalilahi wa'inna ilaihir raji'un, yanda samari da yan mata suke holewa san ransu da sunan soyayya abin yayi muni. 

A zahirin gaskiya a yanxu yanda mutuwar aure da rigingimu tsakanin ma'aurata suke qara yawaita... wani aurenma ko wata baya qarasawa sai ace an rabu.
to irin wannan auren meye amfaninsa, ina qaunar? ina soyayyar da akeyi kamar za a cinye juna? duk ta tafi a banxa kenan?

Wannan yana faruwa ne sakamakon tun kafin auren an gama debe albarkarsa an gama sabawa Allah da take dokokinsa, an qulla alaqar ba don Allah ba, an ginata ba akan doron gaskiya ba, sai kuma uwa uba an gama taba jikin juna tas tun kafin auren,duk wadan nan su suke haduwa suke haifar da matsaloli bayan aure. 

Sai dai galibin mutanen da hakan take faruwa dasu basu fahimtar ai ga abin da suka aikata kafin aure wanda shine silar jefasu halin qaqani kayi a rayuwar aurensu. 

 Abin mamakin be wuce yanda alaqar saurayi da budurwa ta zamo tamkar ta ma'aurata ba a wannan xamanin sai dai yan kadan da Allah ya tseratar.

 ire iren wadannan abuwan da suke faruwa tsakanin saurayi da budurwa na *tabe taben jikin juna* kafin aure shine mafi akasarin abinda yake debewa aure *albarka* a yanxu, da zaka ga kafin aure saurayi ba inda bai taba a jikin budurwarsa ba ita ma haka, kuma wai duk da sunan iya soyayya da wayewa, waiyazubillah.... 

wadannan abubuwa su aka dauka *soyayya* a yanxu, shine wayewa da har wadanda ba sa yin hakan ake daukansu kidahumai wadanda basu waye ba, indai kuwa wannan shine wayewa gwanda kai zamanka baka waye ba dan yafi sauqi

Abu mafi muni shine sai kaga saurayi yazo ya dauki budurwa a mota su tafi sharholiyarsu da sunan wai shaqatawa, ita kuwa dama kwadayi, san abin duniya da rudin shaidan ya gama rufe mata ido saboda tasan in ta bishi za ta samu wani abu a hannunsa. 

wasu kuwa ma a qofar gidansu yarinyar suke tsiyarsu, dan rashin kunya, kaga saurayi da budurwa manne da juna... sai anyi magana, yace,ai ba (sex) bane, menene dan n riqe hannunta! mene ne dan nayi mata (kiss)! mene ne dan na taba jikinta, a tunaninsu duk wadannan abubuwan ba laifi bane sun manta da *Allah madaukakin sarki haka yace kada ku sake ku kusanci zina.* 

dan uwa /yar uwa shin kuwa kunsan girman laifin da kuke aikatawa? kunsan zunubin da kuke tarawa kanku yana da girman gaske? amma baku dauke shi a bakin komai ba.

Allah da manzonsa sun haramta kuma sunyi hani kan abinda kuke aikatawa...ga wasu daga cikin hujjojin da suke haramta hakan daga alqur'ani da sunna.

mu hadu a rubutu na gaba insha Allahu zakuji ayoyi da hadisan da suka haramtawa namiji/mace su taba wanda bamuharraminsa ba. 
✍ *Habeebatus Sunnah* 

07036335308
Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form