• This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

Showing posts with label Littatafai (Novels). Show all posts
Showing posts with label Littatafai (Novels). Show all posts

SARKIN SARAKAI BOOK 2. 06

 SARKIN SARAKAI BOOK 2. 06

Al amarin sarki sahibul hairi da aljani
dabarus kuwa sai da suka shafe sa a
hudu
suna tafiya a can kololuwar sama
sannan sahibul hairi ya umarci
dabarus daya sauko kasa ba tare da
wata gardamar komai ba
kuwa sai aljani dabarus ya cika umarni
har suka sauko kasa suka
dira a cikin wani tafkeken jeji mai
dogayen bishiyoyi da manyan
tsaunika da fadamomi da koramai
gimbiya shukura da bawa haluf basu
farfado daga dogon suman
da sukayi ba koda ganin haka
sai hankalin sarki sahibul hairi ya
dugunzuma ya fara jijjigasu don
tsammaninsa sun mutu ne aljani
dabarus ne ya dubi sahibul hairi
yace ya shugabana ka kwantar da
hankalinka ba mutuwa sukayi ba
dogon suma sukayi kaje ka samo ruwa
ka yayyafa musu ni kuma sai
nayi musu fifita da fuka fukaina in muka
yi haka zasu farfado
koda jin wannan shawarar sai sarki
sahibul hairi ya ruga izuwa
cikin wata korama ya tsoma wani
mayafi nasa a ciki sannan ya daw
a guje ya daddana mayafin akan
fuskokin su shi kuwa dabarus sai
ya kamayi musu fifita da fuka fukansa
bayan dakika biyar
da faruwar hakan sai duk su biyun suka
farfado suna masu yin tari
da atishawa koda ganin haka
sai farin ciki ya lullube sarki sahibul
hairi shukura da haluf
suka kama kalle kalle da waige waige
suna masu mamakin yadda aka
yi suka tsinci kansu a cikin wannan daji
koda sarki sahibul
hairi ya fahimci halin da suke ciki sai ya
bushe da dariya yace kuna
mamakin ne bisa yadda kukazo nan?
Shukura ta dubeshi tayi masa
murmushi tace bana mamaki da
al amarinka ya kai jarumi uban jarumai
amma ina so ka gaya mini
abinda ya faru tsakaninka da mijina
shinka kashe shine??
Koda jin wannan tambaya sai sarki
sahibul hairi yayi ajiyar
zuciya sannan yace ai a rayuwata ban
taba haduwa da sadauki
mai tsananin karfi ba kamar mijinki
tabbas in ba don ina da nisan
kwana ba da tuni ya hallakani ina sanar
dake lambo nayi masa kamar na suma
sannan na shammaceshi na dokeshi
daga kan. Daga kan aljani dabarus ni
dai naga sa adda ya fado kasa
kansa ya bugu da wani rusashshen
tubalin gini harma
goshinsa ya fashe jini ya zuba abinda
ban sani ba shine
shin suma yayi ko kuwa mutuwa yayi sa
dda gimbiya shukura
taji wannan batu sai tayi ajiyar zuciya
cikin takaici tace yakai
wannan sarki kayi sani cewa kayi
babban kuskure da baka
tabbatar da mutuwar mijina ba ai kaima
kasan cewa manyan
mazaje basa saurin mutuwa ina
tabbatar maka da cewa
sarki barusa na nan a raye kuma zaiyi
gagarumin shiri
ya biyomu duk inda zamu je ko shakka
babu duk sa adda
muka sake yin arba da shi sai ya sami
nasarar hallakamu
yayinda sahibul hairi yaji wannan batu
sai yayi murmushi
yace yake shukura kiyi sani cewa a
rayuwata ni
,utum ne mai tsananin sa a bisa duk
abinda nasa a gabana
don haka ina tabbatar miki da cewa
komai RINTSI DA
TSANANI sai na cika burina na zama
SARKIN SARAKAI
na duniya lallai sai mun dauko yarinya
alfila a
cikin gidan boka shamzubul azwas
kuma sai na sadu
da sadauki Awaisu ya taimaka mini
mun nemo
wadannan yan mata guda uku wadanda
zan auresu
na sami daukakar dana ke nema
Koda jin wannan batu sai gimbiya
shukura ta jin jinakai
tace tabdijam ashe kuwa kana da
gagarumin aiki
agabanka ina tabbatar maka da cewa
wahalar da
kasha a baya tamkar kaso daya ce
daga dubun wacce
zaka sha a nan gaba yakai wannan
sarki kayi sani
cewa nemo wadannan yan mata uku
dai dai yake da
nemo jaki mai kaho domin babu wanda
yasan inda suk )
saboda sun boye kansu da karfin sihiri
irin na
sadauki awaisu tabbas in ba sadauki
awaisu ba
babu wanda zai iya laluben inda suke
shi kansa
babu tabbacin cewa zai iya gano inda
suke a cikin
karamin lokaci yakai wannan sarki idan
har dukiya
kake bukata da kuma daukaka aiko a
yanzu ka
samesu
domin wannan gatarin sihirin kadai
daka mallaka
ya isa ya baka duk abinda kake bukata
ina tabbatar
maka da cewa idan kaje ka ajiye
wannan gatarin
a cikin gidan sarautarka saika sami
dukiya mai
yawan da tafi cikin RIJIYA GABA DUBU
arba'in
kasancewar kayi babbar bajinta wacce
babu wanda ya
yi ta a wannan zamani don haka dole
ne labarinka
ya bazu ko ina
a cikin duniya mai zai hana yanzu ka
koma kasarka
kaci gaba da sabuwar rayuwa?
Amma ina mai rokonka alfarma guda
daya
Alfarmar kuwa itace ka daure muje
gidan boka
shamzubul azwas mu dauko yarinya
Alfila
ka mallaka min ita
koda jin wannan batu sai sarki sahibul
hairi
ya bushe da dariya sannan ya dubi
gimbiya
shukura yace kai duniya ba gaskiya
wato dai kina
nufin duk wahalar da nasha a baya ta
zamo ke nayi wa kenan
idan na hakura da gatarin sihirin kadai
ke kuma
na baki yarinya Alfila ne zaki sami
wadannan
sirrikan tsafi
guda dari idan kuka samesu kuwa sai
kinfi kowa
arziki da daukaka a duniya shin kin
manta ne
cewa nima matsayin da nake nema
kenan?
Ai so nake nafi dukkan sarakunan
duniya dukiya
mata da daukaka ya kasance ana
kirana da suna
SARKIN SARAKAI
Hakika ba zan taba samun wannan
matsayi ba
face na auri wadannan yan mata uku
kamar
yadda boka hadimul Asur ya yi mini
bayani
ke yanzu na san so kike nayi miki
wahalar banza
ki samu abinda kike nema kin taimakeni
a cikin
gidan sarautar sarki barusa na sami
nasarar dauko
gatarin sihiri nima na ceci rayuwarki
dana
daukoki daga can domin inda na baroki
a can
din sarki barusa ya farfado ya ganki da
tuni kin
zama gawa
guyson naci gaba da cewa
ina mai shawartarki da mu rabu anan ki
tafi can
wani bangare daban na duniya kici
gaba da bina
har mu dauko yarinya Alfila ki iya rabani
da ita muje
zuwa mahaukaci ya hau kura' ai wanda
baiji
bari ba shine yake jin hoho !!!
Sa adda sarki uban sadaukai sarki
sahibul hairi
yazo nan a zancensa sai hankalin
gimbiya
shukura ya dugunzuma
nan take idanunta suka ciko da kwalla
taji
gaba daya ta
tsani kanta kuma ta tsani rayuwar
duniya
gaba daya
domin ta fuskanci cewa zatayi biyu
babu
ma ana bata ga tsuntsu
kuma bata ga tarko... !!!!!!!
.
SHIN SARKI SAHIBUL HAIRI ZAI SAMI
NASARAR SHIGA CIKIN GIDAN BOKA
SHAMZUBUL AZWAS HAR YA DAUKO
YARINYA ALFILA??
.
YAUSHE NE SAHIBUL HAIRI ZAI HADU
DA SADAUKI AWAISU??
.
SHIN IDAN SUN HADU SADAUKI
AWAISU ZAI YARDA SU TAFI NEMAN
YAN MATAN UKU?
.
SHIN SU WAZIRI AKIYANU ZASU SAMI
NASARAR SATO WANNAN DOKI NA
SARKI AMINUL HAS SU KAIWA BOKA
SHUBURUL UZUB?
.
IDAN SUN KAI MASA DOKIN ZAI CIKA
ALKAWARIN YAGAYA MUSU HANYAR
DA ZASU BI SU SAMI NASARAR
HALLAKA AMINUL HAS?
.
YAUSHE NE BURIN SARKI SAHIBUL
HAIRI ZAI CIKA YA ZAMA SARKIN
SARAKAI?
.
SHIN SARKI AMINUL HAS DA
MATARSA SHULAIBA ZASU SAMI IKON
YIN KWANA SITTIN AKAN GADON
SARAUTAR BIRNIN MISRA DON SU
SAMI HAIHUWA?
.
Marubucin littafin yace mu hadu a
SARKIN SARAKAI3
Littafi na uku
don jin karshen wannan kasaitaccen
labariShare:

SARKIN SARAKAI BOOK 2. 05

 SARKIN SARAKAI BOOK 2. 05
LOKACIN DA SAURAN JAMA'A DAKE
CIKIN FADAR SUKAJI FADAR NATA
GIRGIZA KAMAR,
zata rufta cikin kasa sannan karar
haduwar makaman su sarki sahibul
hairi,
ta cika musu dodon kunne sai suka rude
suka firgice aka kama iface iface,
da guje guje domin ba a taba ganin
tashin hankali ba irin wannan,
kafin a jima wannan tashin hankali ya
isa har cikin gari ko ina da ina,
don haka sai gaba daya birnin ya
hargitse kai bama mutane ba hatta,
dabbobin gida da na daji saida suka
firgice suka kama koke koke da,
guje guje tsuntsaye kuwa tashi suka
rinkayi suna barin shekarsu suna kaara
nausawa cikin daji,
domin neman maboya manyan dabbobi
irinsu kura zaki damisa da sauransu,
cikin ramuka da koguna suka ringa
shigewa suna boye kansu,
kai a wannan rana duk dabbar dake
cikin ruwa bata yarda ta leko saman
ruwa ba,
tun sa adda aka fara azababben yakin
tsakanin sarki barusa da sarki sahibul
hairi,
sai bawa haluf ya yanke jiki ya fadi kasa
sumamme saboda tsananin razana,
ko kadan gimbiya shukura bata lura da
halin da haluf ya shiga ba domin,
gaba daya hankalinta na kansu sarki
sahibul hairi sa adda sarki barusa,
ya ga an shafe kusan sa a uku ana
wannan dauki ba dadi amma ko sau
daya,
bai sami nasarar taba jikin sahibul hairi
ba sai ransa ya baci zuciyarsa tayi
bakikirin,
kawai sai yai jifa da takobin hannunsa
yai nuni da hannunsa guda,
izuwa ga sahibul hairi take wadansu
masun tsafi suka fito daga cikin,
hannun nasa kimanin guda dari suka
tafi da gudu kamar an cillosu daga
cikin kasa zasu cake a cikin jikin sarki
sahibul hairi kawai sai shukura ta nuna
masun da yatsantsa guda take suka
tsaya kyam a cikin isa kuma suka kone
kurmus suka ruburbushe, koda ganin
haka sai sarki barusa ya kara fusata
ya juyo kan shukura suka fara musayar
tsafi a tsakaninsu kowa na jefawa
kowa mugayen abubuwa shi kuwa
sahibul hairi sai ya zama dan kallo .
Sai da barusa da shukura suka jefi
junansu da muggan makamai sama da
guda dari
amma dayansu bai sami nasarar
lahanta dan uwansa ba daga nan kuma
sai
suka jefawa juna wata irin iksa mai
karfin tsiya sai gashi suna wujijjiga
juna a sama suna ta katantanwa a cikin
iska a wannan lokaci iskar sarki barusa
tafi ta shukura karfi don haka sai tayi ta
wulwulata da karfin tsiya cikin
kankanin lokaci shukura ta fita daga
cikin hayyacinta kawai sai iskar ta
makata
a jikin gini sannan ta saketa sai ga jini
yana zuba a goshin shukura ta fado
kasa
magashiyan babu alamar tana numfashi
koda ganin abinda ya faru sai
hankalin sarki sahibul hairi ya
dugunzuma shi kuma sarki barusa sai
ya
tuntsure da dariyar farin ciki yace yanzu
na gama da wannan munafukar maci
amana
saura kai karamin alhaki ina mai
shawartarka daka bani wannan gatarin
sihirin
dake hannunka kuma ka durkusa bisa
gwiwoyinka ka tuba gareni muddin
kana son kaci gaba da rayuwa a doron
kasa in ba haka ba kuwa yanzun na
zan yi daga daga da sassan jikinka na
batar dakai yadda har abada babu mai
iya shaida barin jikinka guda
yayinda sarki sahibul hairi yaji wannan
batu sai yayi murmushi irin na manyan
mazaje
wadanda basa karayar zuci yace yakai
tsohon azzalumi kayi sani cewa
babu wani da mai jini a jiki wanda ya isa
ya firgitani walau mutum ko aljan
domin ban san tsoro ba kuma ban san
jada baya ba ina tabbatar maka da
cewa
babu wani bala'i ko wata masifa da ta
isa ta rabani da wannan gatarin sihirin
dake hannuna don haka ina mai
shawartarka daka kauce ka bani hanya
na fice daga cikin fadarka salin alin in
ba haka ba kuwa zaka riski ajalinsa
koda jin wannan batu sai sarki barusa
ya bushe da dariya kawai sai ya
watsawa
sahibul hairi kibiyoyin tsafi da nufin su
cake dukkan jikinsa koda kibiyoyin
suka diro a kan jikin sahibul hairi sai
duk suka narke suka zama jini shikuwa
jikin nasa ko kwarzanewa baiyi ba ko
da ganin haka sai ran sarki barusa ya
baci ya dubi sahibul hairi yace amma
kayi farar dabara daka sha jinin
dodannina
a dakin azaba na karkashin kasa ba
don haka ba da tuni yanzu kibiyoyin
tsafina sun nutse a cikin gangar jikinka
tabbas yanzu ba zan iya hallaka ka ba
da karfin sihiri amma idan ka ci
maganin kaifi da tsini ai bakaci na karfin
damtse ba koda gama fadin haka sai
sarki barusa ya daka tsalle daga kan
aljaninsa ya dira akan aljani dabarus
ya gwabzawa sahibul hairi naushi a
baki saboda karfin naushin saida
sahibul hairi
ya baje a kan aljani dabarus wani irin
gudan jini yai tsartuwa daga cikin
bakinsa sai yai shame shame kamar ya
suma sarki barusa ya raba kafafunsa
akan sahibul hairi kuma ya dunkule
daya hannun nasa da nufin ya yiwa
sahibul hairi fashin albasa aka bazato
ba tsammani sai yaji sahibul hairi
ya gwabza masa naushi a fuskarsa
sarki barusa ya tafi da baya taga taga
kamar zai rikito kasa daga kan aljani
dabarus take idonsa guda ya kumburo
saboda karfin naushin da sahibul hairi
yayi masa amma sai ya sake rugowa
kan sahibul hairi yaci gaba da
tumurmusashi yana naushinsa hannu
da kafa. Cikin zafin nama ba
kakkautawa
tun da sarki sahibul hairi yake fada da
sadaukai
bai taba haduwa da sadaukin daya yi
masa mahaukacin
duka ba irin wannan har saida ta kusa
cewa sahibul hairi baya iya mai da
martani sai dai kokarin
kare duka kai da dukan ma yayi masa
yawa saiya
kasa karewar yanaji yana gani sarki
barusa yayi laga
laga dashi ya hada masa jini da majina
sahibul hairi ya
sake yin wanwar akan aljani dabarus ya
zamo tamkar
gawa sai numfashi yake yi dakyar
hakika barusa ya fi karfin
sahibul hairi
nesa ba kusa ba domin ko tsaywa
sukayi mutum ya dubi
girmansu da kirar sadaukantakarsu
yasan cewa banbancin a bayyane yake
lokacin da sarki barusa ya ga ya sumar
da sahibul
hairi a karo na biyu sai ya sake zuwa
kansa ya tsaya ya sunkuyya
da nufin ya kamo kansa ya karya masa
wuya
koda ya kai hannunsa zai kamo kansa
sai yaga sahibul hairi
ya goce cikin zafin nama yayi dungure
ta karkashin kafafunsa
ya bulla bayansa kafin dabarus ya juya
tuni sahibul hairi ya
naushi bayan barusa da dukkan
karfinsa nan take sarki barusa
ya fado kasa daga kan aljani dabarus
fadowar da zaiyi kuwa
sai ya fado kan wata rusashshiyar
dirkar gini koda buguwar
kansa sai ya sume a wannan lokacine
sahibul hairi ya mike tsaye da kyar ai
kuwa sai ya hango bawa haluf
da gimbiya shukura kwance a sume
cikin tsawa sahibul
hairi ya umarci aljani dabarus daya
dauko gimbiya da bawa
haluf ya fitar dasu daga cikin
wannan fada kafin dakika biyu tuni
aljani dabarus ya cika
wannan umarni tuni sun luluka sama
cikin gajimare
bayan kaamar dakika dari da ashirin da
bacewar su sahibul
hairi sai sarki barusa ya farfado daga
suman da yayi cikin
razana ya mike tsaye zumbur ya kama
dube dube baiga kowa ba
a wajan face wadannan narkeken aljani
nasa zaune waje daya yai
tagumi sarki barusa ya dakawa
aljanin tsawa yace ya kai shumakaru
ina abokan gabata
shumakaru ya risina yace ai tuni
wannan aljani nasu ya kwashesu
yayi sama dasu sun bace a cikin
gajimare cikin tsananin fushi sarki
barusa ya sake dakawa shumakaru
tsawa yace me yasa ka kyalesu suka
gudu shumakaru
ya ce ya shugabana ai bana zartar da
aiki face da umarninka
koda jin wannan batu sai sarki barusa
ya takarkare ya kwarara uban ihi
mai tsananin firgitawa cikin nuna takaici
tamkar ya fashe da kuka
sannan ya sunkwi da kansa kasa yace
yanzu yau ni aka zo har fadata aka cini
da yaki hakika mata
shaidanu ne in ba don shukura taci
amanata ba da babu yadda
za ayi sarki sahibul hairi ya sami
ikon satar gatarin sihirina na sani cewa
yanzu babu inda zasu nufa face gidan
boka shamzubul azwas
don dauko yarinya Alfila abinda zanyi
kawai shine nayi gagarumin
shiri nabi bayansu in yaso sai na labe a
kusa da gidan shamzubul
azwas sai bayan sun gama shan
wahalarsu sun dauko alfila ni kuma na
taresu na kwaceta na hallakasu
koda gama wannan zance sai sarki
barusa ya kama kyalkyala dariyar
mugunta yaci
gaba da yin dariyar kamar ba zai daina
ba nima kuma saina
ci gaba da tayashi wannan dariyar ni
guyson muje zuwa
wannan shine abinda ya faru tsakanin
sarki barusa da sarki
sahibul hairi bayan sahibul hairi ya sami
nasarar dauko gatarin sihiri
Al amarin sarki sahibul hairi da aljani
dabarus kuwa....
Zan Cigaba insha Allah

Share:

SARKIN SARAKAI BOOK 2. 04

 SARKIN SARAKAI BOOK 2. 04

Koda jin wannan tambaya sai boka shuburul uzab ya bushe da dariya sannan yace yakai babban waziri ka sani cewa amsar wannan tambaya tana bukatar a saurareta a cikin nutsuwa ku kuwa yanzu gashi babu nutsuwa a tare daku domin kun gaji ainun kuma kuna bukatar abinci da abin sha don haka zaifi kyau mushiga daga cikin gidana ku zauna ku sami nutsuwa tukunna.
.
Ba tare da wata gardama ba sai su waziri Akiyanu suka bi boka shuburul uzab a baya har izuwa cikin turakarsa da zuwa suka iske an tanadar musu shimfidu da abinci da abin sha irin nasu na sarakai.
Kawai sai boka shuburul uzab ya umarcesu da su zauna su kintsa cikinsu shi kuwa sai ya wuce zuwa wani dakin daban bai fito ba sai bayan sun gama kimtsa cikinsu boka shuburul uzab ya zauna a gefe daya yana mai fuskantarsu boka shuburul uzab yace yaku wadannan manyan baki na sani cewa kuna cikin matsanancin bakin ciki bisa rashin samun nasarar hallaka sarki Aminul has?
.
.
Tabbas ba zaku taba samun nasara ba face kun rabashi da wannan sandar tsafi da takalmin sihiri duk duniya babu wanda zai iya taimaka muku ku sami nasarar rabashi da wadannan abubuwa face mutum biyu.
Na farko shine boka hadimul Asur sai kuma ni din nan ni kuwa ba zan taimaka muku ba face kunyi mini wani abu guda daya.
Cikin matukar mamaki waziri Akiyanu ya dubi boka shuburul uzab yace kai kuwa menene abin da kake son muyi maka.
Boka shuburul uzab yayi murmushi sannan yace ina son ku sato mini dokin nan na sarki Aminul has wanda yai tafiya dashi a can karkashin teku,
domin na ciri wani sinadarin tsafi a jikinsa wanda shi ne zan cika burina na duniya.
Cikin mamaki Akiyanu ya dubi boka shuburul uzab yace to ai wannan doki bashi da wani sihiri a jikinsa,
boka shuburul uzab ya kyalkyale da dariya yace kaine dai baka sani ba ai sakamakon daukan da wannan guntun Aljanin yayi masa yanzu ya sami sirrikan tsafi guda dari ba daya irin na sadauki awaisu.
Akiyanu ya sake tambaya wane ne kuma sadauki Awaise?
Boka shuburul uzab yace sanin wannan bashi da wani mahimmanci a gareku yanzu saiku amsa mini muradina kafin na gaya muku hanyar da zakubi ku raba aminul has da ababan dogaronsa.
Shin kum amince zaku sato mini dokin.
Waziri akiyanu yace kwarai kuwa ai sato wannan doki a garemu abu ne mai sauki tamkar wanke hannu da ruwa,
boka shuburul uzab yayi dariya sannan yace to shi kenan sai ku tashi ku tafi izuwa birni na baku kwana biyu rak ku sato wannan doki ku kawo mini kuna kawo mini shi nayi Alkawarin zan gaya muku yadda zakuyi ku raba aminul has da sandarsa da kuma talakawansa na tsafi don ku sami damar hallakashi.
Koda gama wannan jawabi sai boka shuburul uzab ya lumshe idanunsa ya bace bat daga cikin turakar koda ganin haka sai suma suka hau dawakansa suka nufi birnin misra.
Basu isa cikin gari ba sai da dare ya soma maimakon su rarrabu kowa ya tafi gidansa sai suka sake dunguma gaba daya suka tafi izuwa gidan waziri Akiyanu suka sake sabon zama na musamman don tunanin hanyar da zasu bi su sami nasarar sato wannan doki na sarki Aminul has,
abinda su waziri akiyanu basu sani ba shine boka shuburul uzab yaudararsu zaiyi kawai amma a zahirin gaskiya ba zai iya raba sarki Aminul has da abubuwan nan biyu ba.
Sihirin da yake so ya cire a cikin jikin dokin Aminul has kuwa shine irin sihirin dake jikin yarinya Alfila yar sadauki Awaisu kuma irinsune a jikin wannan sanda da takalmi na aminul has.
Duk abinda wannan guntun Aljanin ya taba da hannayansa sai ya sami wannan sihiri dalilin haka ne dokin Aminul has ya sami wannan sihiri.
++ ++ ++
Acan birnin Askandariyya kuwa lokacin da sarki sahibul hairi yaci gaba da labewa a cikin fadar sarki barusa yana hangen abubuwan dake faruwa kawai sai ya gga wata kyakkyawar mace ta gaban kwatance ta baiyana a gabansa tana mai yi masa murmushi.
Har ya yunkura zai bar wajan ta dakatar dashi tace tsaya na nuna maka hanyar da zaka bi kaje inda gatarin sihiri yake in kuwa kabi wata hanya daban halaka zakayi cikin matukar mamaki da rashin yarda sarki sahibul hairi ya dubeta yace ke kuma wacece kuma saboda me zaki nuna mini inda gatarin sihiri yake alhalin kuna son wannan gatari fiye da komai a cikin birnin nan?
Kyakkyawar tace babu isashshen lokaci da zan iya maka bayani yanzu amma bayan ka sami nasarar dauko gatarin sihirin zanyi maka bayanin komai.
Koda gama fadin haka sai ta jashi izuwa wani sako daban sukaci gaba da tafiya suna ratsa wadansu manyan dakuna har saida suka shige cikin dakuna dari koda suka isa gaban kofa ta dari da daya sai kyakkyawar ta tsaya tace gatarin sihiri na cikin wannan daki a rataye a jikin bango kuma akwai dakaru mutum dubu uku a ciki masu tsaron gatarin wadanda suka kasance karfafa kuma sadaukan gaske yanzu saika shiga cikin dakin ka yaki sadaukan dubu ka karkashesu sannan ka fito na saka a hanyar da zaka fita daga cikin gidan sarautar nan sannan kuma nayi maka jagora izuwa gidan boka shamzubul azwas don dauko yarinya Alfila yar sadaukin duniya Awaisu''. An ya kuwa nima ba zan bisu ba kuwa ganin yadda mace take son raka sarki sahibul hairi?.
Koda jin wannan batu sai sarki sahibul hairi ya cika da tsananin mamakin yadda akayi wannan kyakkyawar budurwa ta san dukkan shirinsa har ya budi baki da nufin ya sake yi mata tambaya sai tace dashi.
Na gaya maka cewa bamu da isashshen lokaci a yanzu wanda zan yi maka bayanin komai don haka kayi sauri kaje ka dauko gatarin sihirin nan.
Koda jin haka sai sarki sahibul hairi ya bude wannan kofa ya kunna kai ciki ba tare da fargabar komai ba yana shiga kuwa ya hango gatarin sihiri a rataye a jikin bango sai sheki da walwali yake tsaitsaye a gaban bangon da aka rataye gatarin wadansu murza murzan kartine majiya karfi su dubu uku kowannansu a tube daga shi sai kamfai.
Kuma duk suna rike da manyan makamai ababan tsoratarwa wani makamin ma tunda sarki sahibul hairi yazo duniya bai taba ganin irinsa ba su dai wadannan karti sun ninka sarki sahibul hairi sau uku a girma da cika ido gaba dayansu kansu daya tamkar tagwaye kai kace mace daya ce ta haifesu rana daya.
Koda kartin sukaga sarki sahibul hairi ya shigo cikin dakin sai suka yi masa kawanya su duka kowannansu ya kama gyara makaminsa shima sarki sahibul hairi sai ya gyara tsayuwarsa a cikin farin kayan karfe yana jiran yaga wanda zai fara afko masa..
Kamar hadin baki sai suka tasammasa gaba daya a lokaci guda ya zamana kowa na kai masa sara da suka shi kuwa sai ya zama tamkar shaidani a tsakiyarsu yayi ta kare kansa yana mayar musu da martani nan fa aka yi ta gumurzu dauki ba dadi da fafatawa tsakanin sarki sahibul hairi da dakaru masu tsaron gatarin sihiri.
Sai da aka shafe sa a biyu a haka subasu barshi ya sami damar isa inda gatarin yake ba shi kuma ya kasa hallaka koda daya daga cikinsu domin idan ya samu sa ar sarar jikinsu ma sai yaga kaamar dutse ya sara babu abinda yake samun su wani abu daya kara firgita sarki sahibul hairi shine ko kadan dakarun basa gajiya kuma basa alamar cewa zasu gaji sarki sahibul hairiya tabbatar da cewa idan akaci gaba da wannan fada a haka zata kai cewa ya gaji sun samu lagonsa
.
Don haka ya zama wajibi a gareshi yayi tunanin mafita ba zato ba tsammani sai dakarun sukaga ya sauya salon fada dabarar da yayi kuwa itace ya fara tsalle tsalle yana taka kawunansu yana karawa gaba a haka suka rinka kaiwa kafafunsa sara amma saboda zafin namansa sai suka kasa cimmasa bare samunsa
.
Kafin su ankara ya daka tsalle ya dira akan gangon da aka rataye gatarin sihiri nan take ya yarda takobin hannunsa ya suri gatarin
duk da cewa gatarin nada matukar nauyi amma sai gashi da hannu daya ma sarki sahibul hairi ke jujjuyashi.
sa adda dakarun sukaga sarki sahibul hairi ya suri gatarin sihiri sai suka sake yin caaa a kansa da nufin su ragargazashi shi kuwa sai yayi amfani da gatarin yaci gaba da saransu wohoho
a wannan lokacine labari ya sha bambam domin duk wanda ya sara da gatarin sai dai kaga ya faskarashi gida biyu.
..
Sarki sahibul hairi yaci gaba da ragargazarsu tamkar mai yanke kabewa kafin a jima yai fata fata da su babu sauran mutum daya a tsaye gabansa koda yaga ya sami wannan nasara sai ya cika da tsananin murna kawai sai ya saba gatarin a kafadarsa ya bude kofar dakin ya fito.
.
A wannan lokaci duk jikinsa yayi kaca kaca da jini hatta fuskarsa kuwa sai da ya cire hular karfen dake kansa sannan ya goge jinin akan idanunsa fitarsa ke da wuya sai yaga wannan kyakkyawar budurwa a tsaye tana jiransa koda ta gasnhi rike da gatarin sihiri sai ta tareshi da farin ciki ta kama hannunsa
.
Faruwar hakan keda wuya sai suka face bat a tare suka bayyana cikin wata babbar turaka wadda akayi matukar kawata da kayan kawa iri iri daga can kuryar kudu an ajiye wani shimfidadden gado na alfarma irin na sarakai kwance akan gadon kuma a lullube cikin mayafi ba wani bane face bawa HALUF yana ta sharar barci tamkar wanda ke dakin matarsa.
.
Nan fa sarki sahibul hairi ya cika da tsananin mamaki domin shi a saninsa ya baro bawa haluf a can bayan gari toyaya akayi ya shigo har ma ya sami jiki yana barci mai nauyi haka.
Koda kyakkyawar budurwar ta fahimci cewa sarki sahibul hairi na mamakin ganin bawansa haluf a cikin wannan turaka sai tayi murmushi sannan ta zauna a gefen gadon tana mai fuskantar sarki sahibul hairi tace dashi.
.
Yakai wannan jarumi uban jarumai ai saika zauna don ka huta sannan na baka amsoshin tambayoyin da kayi mini dazu sarki sahibul hairi ya dubeta cikin kaduwa yace yanzu ni ina na ga lokacin zama alhalin nayi sata a cikin wannan gidan sarautar kuma na tabbatar da cewa da zarar an ankara cewa an dauke wannan gatari dole ne a bazama nemana''
.
Koda jin wannan batu sai kyakkyawar ta dubi sarki sahibul hairi da wani irin kallo mai tattare da alamomin tambaya tace ka kwantar da hankalinka yakai mai birnin Misra ka sani cewa kana tare da wadda tafi kowa sanin sirrin gidan nan.
Gama fadin haka keda wuya sai ta mike tsaye taje kan wani tebul ta dauko tambulan na ruwan inibi tazo Gaban sarki sahibul hairi ta ajiye kofunan ta tsiyaya ruwan inibin a ciki sannan ta dauki kofi guda ta mika masa guda take ta kai kofin bakinta ta fara shan ruwan inibin
ya yinda sarki sahibul hairi yaga ta sha ruwan inibin sai shima ya sha nasa kyakkyawar tayi dariya tace ai nasan cewa in ban shaba kaima ba zaka sha ba domin akwai alamar cewa kana zargi zan iya ha intarka''
.
Sarki sahibul hairi yayi murmushi ya ce ai a duniya idan akwai abinda nake tsoro bai wuce kaidin ya mace ba domin zata iya sawa mutum ya rasa mulkinsa dukiyarsa da rayuwarsa gaba daya.
.
Kyakkyawar tai murmushi tace hakika zancenka dutse ne to amma ina sonka saki jikinka dani domin nai maka alkawarin ba zan cutar dakaiba.sarki sahibul hairi yace to shikenan na gode.
Yanzu kafin ki bani labarin komai ina son ki gaya min yadda akayi bawana haluf ya shigo cikin wannan turaka taki har ya kama barci haka tamkar yana cikin dakinsa 
kyakkyawar na jin wannan tambaya sai tayi murmushi tace na yarda zan baka wannan labari amma dole sai na fara da gabatar da kaina a gareka da farko dai ni sunana gimbiya shukura kuma nice matar sarki barusa mai mulkin wannan birni na Askandariyya.
.
Koda jin wannan batu sai tsoro ya kama sarki sahibul hairi ya mike tsaye daga inda yake zaune ya danja da baya yace ke kuwa menene dalilin da ya sa kika ci amanar mijinki har kika taimaka mini na dauko wannan gatarin nasa na sihiri??
.
Sa adda gimbiya shukura taji wannan tambaya sai ta bushe da mahaukaciyar dariya tace ai cin amanar maci amana ibadane yakai wannan jarumi kayi sani cewa asalin sarautar birnin nan ta mahaifinace amma tun ina cikin mahaifiyata uban sarki barusa ya kashe mahaifina alhalin ya kasance babban amininsa kuma wazirinsa don wai ya gaji dukiyarsa da karagar mulkinsa
A wannan lokaci sarki barusa baifi shekara bakwai ba ni kuwa kamar yadda na gaya maka ko haihuwata ba ayi ba amma mahaifiyata na dauke da cikina wata shida bayan shekara bakwai sai uban sarki barusa ya mutu sakamakon cutar ajali don haka sai barusa ya gajeshi yana da shekara goma sha bakwai a duniya ni kuma a lokacin ina da shekaru goma kacal.
.
Tun kafin sarki barusa ya hau kan karagar mulki ya shaku dani ainun kuma yake nuna min tsananin kauna A zahiri ina nuna masa kauna amma cikin zuciyata na kanji na tsaneshi kamar yadda na tsani mutuwata mahaifiyata ta bani labarin cewar a gaban idanunta mahaifin barusa ya kashe mahaifina ya haye kan karagar mulkinsa amma bai san cewa tana labe tana gani ba
.
Dama mahaifiyar tawa ta lura da cewa baruwa na sona don haka saita rokeni da na yarda na aureshi ko don na samu damar daukar fansar ran mahaifina akansa da wannan manufa a zuciyata na girma na isa aure a lokacin da aka daura mini aure da sarki barusa tsawon shekara shida ina tare dashi bamu samu haihuwa ba kullum sai nayi yunkurin hallakashi amma sai na kasa bisa wannan dalili ne na fake da batun tafiyar neman maganin haihuwa wajen bokaye amma a zahirin gaskiya ba maganin haihuwar nake nema ba 
..
Dama nake nema wacce zan iya hallaka sarki a cikin yawona neh na hadu da wani shahararren boka wanda ya sanar dani wai ba zan taba samun damar hallaka sarki barusa ba face na mallaki wadansu sirrikan tsafi guda dari ba daya su kuwa wadannan sirrika suna nan a jikin wata karamar yarinya mai suna alfila
.
Yar wani mashahurin matsafi kuma jarumin gaske ana kiransa da suna awaisu koda naji wannan batu sai na tambayi bokan nace yanzu ya za ayi naje inda wannan yarinya take har na sami sirrikan tsafi daga gareta?
.
Bokan ya kyalkyale da dariya sannan ya murtuke fuska kamar an aiko masa da sakon mutuwa yace ke yarinya baki isa kije inda wannan yarinya take ba domin tana can cikin wani gida dake tsakiyar tekun bahar zallus mallakin sarkin bokayan aljanu na duniya mai suna shamzubul Azwas.
.
Yarinya ke dai baki isa kije wannan wuri ba har ki sami ikon shiga cikin wannan gida amma idan kikayi hakuri nan da wadansu yan shekaru kadan akwai wani jarumin sarki da zaizo birninku neman gatarin sihirin da kuke bautawa idan kika taimaka masa ya mallaki gatarin sihirin za ki iya tafiya tare da shi izuwa tsuburin bahar zallus ku shiga har cikin gidan boka shamzubuk Azwas ku dauko yarinya alfila a sannan ne saiki biya bukatarki ta samun surrikan jikinta''
.
Lokacin da bokan yazo nan a zancensa sai na tambayeshi nace tayaya zan iya cire sirrikan tsafin daga jikin yarinyar?
Koda jin wannan tambaya sai bokan ya bushe da dariya yace ai wannan kuma aikinmu ne na bokaye ba naku ba kedai da kinga kun dauko yarinyar saiki san dabarar da zakiyi ki raaba abokin tafiyar taki da ita ki kawota gareni.
.
Tunda naji wannan batu sai naji hankalina ya dugunzuma naji cewa ko kadan ban yarda da wannan boka ba da ga wannan rana na dada jajircewa wajan neman ilimin tsafi nayi yawo kasa kasa gari gari ina ziyartar bokaye ina yi musu alheri mai yawa suna koya mini tsafi sannu a hankali nima na zama gawurtacciyar bokanya a sirrance ba tare da mijina ya sani ba.
.
Don haka a yanzu ina sanar dakai cewa hadimul asur so yake kawai ka Kawo masa wannan yarinyar don cika burin rayuwarsa amma ba dan ya biya maka bukata ba ni a yanzu nayi maka alkawari indai ka taimaka mini muka dauki alfila na ciri sirrikan tsafinta guda dari ba daya zanyi tsafin da zaka zamo attajirin da babu kamarsa a duniya zaka auri wadannan yan mata uku da babu kamarsu a duniya kuma sunanka da mulkinka zasu shahara ko ina cikin duniya.
Sa adda gimbiya shukura tazo nan a jawabinta sai sarki sahibul hairi yayi shiru ya shiga tunani mai zurfi yana juya al amarin a ransa daga can saiya dago kai ya dubeta yace.
Na gamsu da duk jawabinki kuma na amince zan baki hadin kai domin mu cika burin rayuwarmu yanzu saiki amsa mini tambayar da nayi miki akan yadda akayi bawana yazo cikin turakarki
.
Har ya kama barci mai nauyi akan gadonki na alfarma nan take gimbiya shukura ta kwashe labarin duk abinda ya faru tsakaninta da bawa haluf ta zayyana masa har izuwa sa adda ta yaudareshi da batun zata ceci rayuwarsa da ta maigidansa dalilin da yasa ya bata kansa kenan suka kwanta tare shukura tace maganar gaskiya ban tara da bawa haluf dan na samu haihuwa ba sai don kawai naci mutuncin mijina 
.
Kuma naci amanarsa saboda yadda nasan cewa yana tsananin tsanar bakar fata a rayuwar to yau gashi matarsa da yake matukar so fiye da komai a rayuwarsa ta kwanta da bakin fata kuma bawa.
.
Lokacinda gimbiya shukura tazo nan a zancenta sai takaici da mamaki suka kama sarki sahibul hairi ya jinjina kai yace hakika ku mata ababan tsoro ne domin dafinku da kaidinku yafi na maciji saurin tasiri a jikin dan adam hakika sai yanzu na fuskanci cewa ba karamar ni ima nake ciki ba da banyi aure ba
shukura na jin wannan batu saita bushe da dariya tace haka kuma ba karamar ni ima kayi asara ba domin duk mutumin da bai taba yin aure ba ya rasa kaso tamanin cikin dari na dadin duniya.
.
Zama da su fitina rashinsu kuma asara sarki sahibul hairi ya ce har yanzu dai ban fahimci wannan karatu naki ba abinda nake so dake yanzu mu ajiye wannanzancen komai a gefe daya kawai ki fitar damu daga cikin gidan sarautar nan mu tafi izuwa tsibirin bahar zallus don shiga gidan boka shamzubul azwas mu dauko yarinya alfila gimbiya shukura tayi murmushi tace yanzun nan zan aikata haka amma dai ina mai dada yi maka tuni da cewar ka manta da batun bokanka hadimul asur cewar zai taimakeka idan ka kai masa yarinya alfila tabbas yaudararka zaiyi kawai ya biya tasa bukatar abinda nake so dakai shine ka bani wuka da nama indai muka mallaki alfila tamkar burinmu gaba daya ya cika ne sarki sahibul hairi yayi murmushi yace ai shi kenan na amince da duk abinda kika shirya na baki wuka da nama..
.
A zuciyar sarki sahibul hairi ko kadan bai baiwa gimbiya shukura amana ba don haka duk yadda zaiyi ba zai yadda ta rabashi da alfila ba bayan sun daukota daga gidan boka shamzubul azwas acan karshen zuciyar sarki sahibul hairi sai yaji yana wasu wasu dangane da al amarin boka hadimul asur yaji cewa shima bai yarda da shiba kawai akawai alamun cewa shima akwai wani abinda yake so ya mallaka shiyasa yake son mallakar yarinya alfila
.
Abinda sarki sahibul hairi ya yankewa kansa hukunci shine indai ya sami nasarar dauko yarinya alfila kai tsaye zai tafi da ita zuwa ga mahaifinta sadauki awaisu sannan ya nemi taimakonsa bisa nemo wadannan yan mata uku
.
Sahibul hairi yace a cikin ransa idan idan har sadauki awaisu ya cika dan halak wanda yasan mutunci kuma har idan kaunar da yake yiwa yarsa dari bisa dari ce to lallai ba zaiki taimakonsa ba idan ya sada shi da alfila 
.
Sahibul hairi na cikin yin wannan tunani gimbiya shukura ta runtse idanunta ta fara karanto wadansu dalasimai na tsafi fara hakan keda wuya saiga wata jibgegiyar halitta ta ratso ta cikin saman rufin dakin kamar haske ta fado a gaban shukura wannan halitta ba komai bace face ALJANU DABARUS.
ALjani dabarus na da siffa irin ta bil adama wato yana da hannaye kafafu kirji wuya da kai sai dai kansa rabkeke ne yana da wangamemen baki cike da hakora hancinsa ma wawakeke ne amma idanunsa yan kanana neh ko yaushe jawur suke kamar gauta yana da dogayen kunnuwa wadanda suka kara masa muni fuka fukansa manya ne guda biyu
.
Koda saukar aljani dabaru a gaban gimbiya shukura sai ya rusuna ya kwashi gaisuwa sannan yace ya shubata me kike bukata daga gareni?
Ki sani cewa a shirye nake na sallama rayuwata don faranta miki shukura ta dubi aljani dabarus tace bukatata dakai kawai itace ka daukeni da wannan jarumin ka kaimu can tsibirin bahar zallus inda gidan boka shamzubul azwas yake koda jin wannan batu sai aljani dabarus ya kwalla ihu ya fadi kasa.
Yana birgima da tuba yace kiyi min rai ya shugabata ki yi sani cewa tsakanin mutum ko aljan duk wand aya kusanci gidan boka shamzubul azwas take yake narkewa ya dige ya zama ruwa don haka ina mai rokonki daki sauya min aiki da wata bukatar amma ba wannan ba
.... Koda jin wannan batu sai gimbiya shukura ta dakawa aljanu dabaru tsawa tace kai sha saha sha banza ai ba cewa nayi dole saika kaini har kofar gidan ba zaka iya ajiye mu nesa da gidan koda ya kai tafiyar rabin sa a ce
mu mun san yadda zamu karasa can kai kuwa saika jiramu a baya inda zaka iya tsayawa Aljani dabarus ya saki murmushin murna yace yauwa yanzu naji kan zance wannan ai ba matsala bace saiku hau bayana mu dau hanya
.
Koda jin haka sai shukura ta bude wata akwatu ta dauko wata garkuwa ta zinare ta mikawa sarki sahibul hairi tace ka ruke wannan domin zata maka amfani a gidan boka shamzubul azwas ba tare da gardama da fargabar komai ba yasa hannu ya karbi wannan garkuwar da hannun hadu 
A hannun dama kuwa ya damke gatarin sihiri nan take shukura ta taba kafadar bawa haluf kawai sai ya farka daga barci ya mike zaune zumbur a firgice,
amma da yaga sarki sahibul hairi tsaye a gabansa ruke da gatarin sihiri da bakuwar garkuwa sai murna ya kamashi gimbiya shukura ta dubi sarki sahibul hairi tace ai saika hau kan aljani dabarus ka zauna daga gaba dani da haluf mu zauna a bayanka.
Sarki sahibul hairi yace wannan ba laifi bane nan take kuwa ya hau kan bayan dabarus ya zauna faruwar hakan keda wuya sai haluf da shukura suka yunkura da nufin suma su hau bayan dabarus:
bazato batsammani sai sukaga bangon dakin ya dare gida biyu saiga sarki barbusa ya ratso ta ciki sanye da bakaken kayan yakin nan wadanda sarki sahibul hairi ya gani a gidan karkashin kasa a sakale a jikin bango tare da fararen daya sa da kuma jajaye.
ni kaina bayyanar sarki barusa a wannan lokaci ya razanani kamar ba zan iya ci gaba da typing din ba amma nayi ta maza naci gaba...
Sarki barusa ya dubi gimbiya shukura cikin tsananin bakin ciki idanunsa cike da hawaye yace yake bakar annamimiya maci amana ki sani cewa karyarki tasha karya domin baki isa ki ha inceni ba har ki hada kai da makiyina don a nakastani a rabani da abin dogarona wato gatarin sihiri.
.
Na dauki so da kauna na gaskiya na baki tun muna yara kanana ashe ke ba kaunata kike ba asalima so kike ki hallakani to kin makara domin na gaba yai gaba na baya sai labari ki sani cewa duk hirar da kukayi yanzu tsakanin ki da wannan sarki duk na gani a cikin madubin tsafina don haka naji dalilin da ya sa kike son ki hallakani don ki dauki fansar mutuwar mahaifinki.
.
Haba shukura ni idan kika ce dole a kaina zaki dau fansa bakiyi mini adalci ba domin babu sa hannu na akan mutuwar mahaifinki
asalima sa adda aka kasheshi ina yaro karami ban san abinda yake faruwa ba ba wai ina fadin haka bane donki janye ra ayinki sai donki sani cewa ke kin cika butulu maci amana haka kuma naji da bakinki kina cewa kin kwana da wannan bakin bawa don kawai kici amanata ki tozarta mutuncina tabbas kin sami nasara bisa hakan amma ki sani nima sai na tozartaki irin tozartawar da ba a taba yiwa wata ya mace ba a duniya kuma saina wulakantaki fiye da kima a cikin wannan birni namu na askandariiya yadda duk mai kaunarki idan ya tuno da abinda nai miki sai ya gwammace bai zo duniya ba yanzu a gaban idanunki zan yiwa wannan sarki da bawansa kisan wulakanci irin wanda baki taba gani ba.
.
Duk wannan bayani da sarki barusa ke yi sarki sahibul hairi na zaune akan aljani dabarus ya zuba musu idanu kawai ko gyara zaama baiyi ba maganganun da yake yma jinsu yake kamar tatsuniya ( kunji fa yarda da kai wajan sarki sahibul hairi) ita kuwa gimbiya shukura sa adda taji barusa ya gama jawabinsa sai ta kyalkyale da dariya lokaci guda kuma ta murtuke fuska tace kai barusa dakata kaji ka yi sake dan zaki ya girma ina tabbatar maka da cewa baka isa kayi mini komai ba domin dama na dade ina yin tanadinka.
.
Nima kuma a yanzu ban isa nayi maka komai ba tunda ban mallaki sihirin tsafin da zan iya ganin bayanka ba kafin na tareka mu gwabza yanzu ga dan uwanka nan sarki SAHIBUL HAIRI GAGARA BADAU saiku fara karawa mu gani ko zaka iya dashi ''
koda jin wannan batu sai sarki barusa ya juya ya dubi sarki sahibul hairi ya bushe da dariya sannan kuma ya murtuke fuska kawai sai yaga wata irin walkiya ta fito daga cikin idanun barusa ta bugi jikin sahibul hairi take rigar karfen da yake jikin sahibul hairi ta bace bat barusa ya bushe da dariya a karo na biyu yace yanzu saimu gwabza gaskiya da gaskiya.
.
Kafin sahibul hairi yayi wani yunkuri tuni barusa yayi tsafi saiga wani narkeken aljani nan ya bayyana a gabansa wanda a girma da kwarjini ya ninka Aljani dabarus sau uku.a lokacinne kuma wata katuwar takobi ta bayyana a hannun sarki barusa.
Cikin abinda baifi kiftawar ido ba sarki barusa ya haye kan narkeken aljanin suka afkawa sahibul hairi.
Nanfa aka fara azababben yaki ya zamana cewa sahibul hairi na kaiwa sarki barusa sara da gatarin sihiri shi kuma yana karewa da wannan katuwar takobin yana maida martani
wannan fada dai a sama suke yinsa bisa aljanun biyu cikin isa gimbiya shukura da bawa haluf kuwa sai suka daga kawunansu sama suna kallon abindake faruwa a cikin sararin samaniya.
Al amin ne sunana. Sa adda takobin sarki barusa ta hadu da gatarin sihiri sai kaji wata irin kara mai firgitarwa tamkar saukar aradu sannan kuma sai tartsatsin wuya gami da hayaki sun tashi al amarin da ya janyo girgizar gidan sarautar kenan gaba daya jama ar dake cikin gidan sai da hankalinsu ya dugunzuma saida aka shafe sa a uku ana wannan gumurzu dayansu bai sami nasarar taba jikin daya ba amma tuni sun rugurguza ginin fadar domin a duk sa adda dayansu ya kaiwa daya sara ya goce duk abinda ya sama sai wannan abu ya rabe gida biyu koda kuwa dirkar gini ce shi kansa tartsatsin wutar da ke zuba daga jikin makaman fadan nasu sai da ya haddasa gobara in ba don gimbiya shukura na kashe wutar ba da karfin sihiri da tuni fadar ta kone gaba dayanta. ....
Zan Cigaba Insha Allah

Share:

SARKIN SARAKAI BOOK 2. 03

 SARKIN SARAKAI BOOK 2. 03

Sarki sahibul hairi ya ci gaba da cewa 
yauwa fari kalace ta adalci da nuna alamun tausayi don haka su zansa ba tare da fargabar komai ba sai ya dauki fararen kayan ya sanya a jikinsa tsaf
wohoho duk wanda yaga sarki sahibul hairi a cikin wannan shiga ta fafaren kayan yaki dole ne ya bashi sha awa kuma ya bashi tsoro saboda sunyi masa kyau matuka kuma sun kara bayyana kwarjininsa a fili
.
Gama sa tufafin ke da wuya sai yaga wata kofar ta bayyana a jikin bango kai tsaye ya nufi kofar ya shiga cikinta sai gashi yana ratsawa ta cikin wadansu kofofi wannan na bin wannan tun yana irga kofofin har sai da ya gaji ya daina nan fa sarki sahibul hairi yayi ta ganin abubuwan tsoro iri iri da abubuwan mamaki kala kala amma duk inda yazo sai yaga ya wuce lafiya ba tare da wani abu ya same shi ba mamaki ya turnuke sarki sahibul hairi
.
Abin da bai sani ba shine duk wanda yasa wadannan fararen kaya na yaki babu wani mahaluki walau mutum ko aljan da zai iya ganinsa kai hatta tsuntsaye da dabbobi ma bazasu iya ganinsa ba face mutum daya kwal a duniya ba wani bane face sarki barusa mai birnin Askandariyya
.
Sai da sarki sahibul hairi ya wuce kofofi dubu tara da dari tara sannan ya iso gaban wata matattakalar kasa koda ganin wannan matattakalar sai murna ta kama sahibul hairi
kai tsaye ya khau kanta ya kama tafiya har ya iso karshenta inda yaga wata kofar koda ya bude kofar saiya hango cikin fadar sarki barusa ga jama a nan a cike an kewaye sarki barusa ana fadanci
.
A lokacin wani mai baiwa sarki labari na zaune a gabansa yana ta sharara labari mai ban dariya sarki barusa na ta kyakyatawa saboda karfin dariyar tasa ma kiris ya rage bai fado kasa ba daga kan karagar mulkinsa cikin sauri sarki sahibul hairi ya fito daga cikin dakin ya kulle kofar ba tare da kowa ya ganshi ba sannan ya kama labe labe yana tunanin hanyar da ya kamata yabi yaje inda aka ajiye gatarin sihirin inda matsalar take shi bai san a ina aka ajiye gatarin sihirin ba haka dai ya ci gaba da labewa a cikin wani sako mai duhu yana tunani a lokacin da hadimai da dakarun gidan sarautar ke kai komo wasu mata gabansa suke wucewa amma basu ganshi ba.
**
wannan shine abinda ya faru ga sarki sahibul hairi bayan ya sha bakar wahala a cikin gidan halaka wanda ke karkashin kasa a masarautar sarki barusa
++
++ ++ ++ ++
ACAN BIRNIN MISRA KUWA kashe gari da sassafe fada ta cika makil da jama a tare da dukkan fadawan sarki kowa ya zuba idanu yana jiran fitowar sabon sarki wato mai rikon karaga AMINUL HAS.
don aga yadda zai tafiyar da nasa tsarin mulkin ana cikin wannan haline aka hango shi a tafe shi kadai a bayansa kafarsa sanye da wadansu tsofaffin takalma wadanda saboda tsufa har sun fara lalacewa sannan kuma yana rike da wata tsohuwar sanda itama duk ta fara farfashewa rigar dake jikinsa ma ba wata mai kyau bace rigace irin wadda kowanne irin talaka zai iya sawa
.
Koda ganain Aminul has a cikin wannan shiga sai su waziri suka shiga duban junansu suka fara dariyar farin ciki jama ar gari kuwa sai suka cika da dumbin mamaki suka kurawa aminul has idanu a lokacin da jama a suka dare suka bashi hanya ya nufi kan karagar mulki dama a wannan lokaci kowa a tsaitsaye yake har saida aminul has ya zauna a kan karaga sannan fadawa suka zazzauna a mazaunansu suma mutanan gari sai kowa ya nemi wuri ya zauna take fadar tayi tsit kamar mutuwa ta gifta
.
Cikin nutsuwa sarki aminul has ya mike tsaye ya dubi jama arsa cikin fara a da walwala yace yaku jama ar birnin misra kuyi sani cewa adalin sarkinku wato sarki sahibul hairi wanda yai tafiya bai tafi ba yana nan
.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama kowa da kowa fadar ta sake rude wa da hayaniyar jama ah koda ganin haka sai Aminul has ya daga hannu aka yi tsit sannan yace nasan kun shiga rudani bisa jin abinda na fada yanzu to amma abin da na ke nufi anan shine sarki ya tafi amma ni wakilinsa ne duk irin mulkin da yasaba yi akansa zanci gaba ba zan sauya komai ba
.
Ban yarda mai mulki ko wani attajiri ya zalunci talaka ba duk mutumin da yayi laifi za a hukuntashi kamar yadda za a hukunta kowa da kowa.
Sa adda jama a sukaji wannan batu sai suka barke da shewa suna tafi kowa ka dubi fuskarsa sai kaga ta cika da annuri amma ban da ragowar fadawa su waziri Akiyanu wadanda suka murtuke fuskokinsa sai muzurai suke kamar zasu fashe da kuka don bakin ciki musamman waziri Akiyanu ji yayi kamar ya tashi yaje ya soke aminul has da takobi yayi juyin mulki nan take
.
Sarki aminul has yaci gaba da bayani yana mai tabbatar da cewa za aci gaba da yiwa jama a adalci da kuma taimakon marasa shi haka dai yayi ta bayanai har ma yana kirkiro sababbin abubuwa don farantawa talakawa haka dai taro ya watse kowa yana farin ciki aminul has ya mike tsaye ya shiga cikin gidan sarauta inda ya wuce kai tsaye izuwa cikin turakar sarki sahibul hairi.
Da shigarsa cikin turakar sai ya iske matarsa shulaiba zaune a gefen gadon taci ado fuskarta cike da annuri ya yinda ta dago kai suka dubi juna sai kowannansu ya Kama murmushi saboda tsananin farin ciki aminul has ya matsa gareta ya zauna daf da ita sannan ya ajiye sandarsa akan gadon a gefe daya koda ya sunkuya da nufin ya cire takalman kafarsa sai tayi wuf ta tare hannayansa tace A kul ka cire wadannan takalma lallai dasu zaka yi barci akan wannan gado mai Albarka.
Yayinda Aminul has yaji wannan batu sai yayi murmushi yace ki gafarceni yake abar kaunata hakika na sha afa da dokokin da kika shimfida mini bisa wadannan takalma da kuma wannan sandar amma ba komai bane ya haddasa hakan ba face tsananin farin ciki kasancewar yau ne zamu shafe dare daya daga cikin dare sittin na farin ciki akan wannan gado na sarauta 
.
Yayinda shulaiba taji wannan batu sai tayi dariya sannan ta mike tsaye taje ta rufe kofar turakar ta kuma kashe gaba dayan fitilun dake cikin turakar dakin yayi duhu matuka yadda ko tafin hannu mutum ya daga ba zai iya ganiba.
++ ++ ++
Al amarin waziri Akiyanu kuwa sai suka kasa tashi daga filin fadar saboda tsabar bakin ciki ya zamana cewa kowa ya watse an barsu a zaune su kadai a cikin fadar har dare ya raba basu koma gidajensu ba sai da suka tabbatar da cewa babu kowa a cikin fadar sai su kadai a lokacin ma masu gadin kofar fadar sunrufe kofa sannan suka fara tattaunawa akan yadda zasu ga bayan sarki Aminul has.
Waziri akiyanu ne ya fara magana yace yaku yan uwana yan majalisa kun gani kuma kunji abubuwan da babban makiyinmu ya fada lallai ya zama wajibi muyi saurin kawai dashi in ba haka ba kuwa gaba dayanmu zamu wulakanta sai mun kaskanta a idon talakawa saimun talauce mun zama abin tausayi
.
Yayinda yan majalisa sukaji wannan batu na Akiyanu sai duk sukayi shiri aka rasa wanda zai ce kala daga can sai tsoho kilzam yayi gyaran murya yace yakai waziri Akiyanu kayi sani cewa dolene a dawo kan maganata ta farko wato dolene mu yiwa aminul has juyin mulki a dare daya idan ba hali kawai muje mu kashe shi yanzu yanzu a cikin wannan dare
.
Waziri Akiyanu yayi murmushi yace kai kuwa dadina dakai kenan ka cika gaggawa na yarda da shawararka cewa mu sa a kashe shi a cikin darennan amma ba mu da kanmu za muyi wannan aiki ba domin aikin ne mai hadari manufa ta anan inda bamuci nasara ba asirinmu zai tonu a hallaka mu amma idan wasu muka sa sukayi wannan aiki kome za ayi musu ba zasu fadi cewa mune muka sasu ba
.
Abinda za ayi kawai shine yanzu idan muka bar nan zan tura a kirawo mini manyan yarana amintattu bakwai wadanda zasuyi wannan aiki a gobe da daddare ina tabbatar muku da cewar sai dai a wayi gari sarki ya mutu kun san kuwa yana mutuwa nine zan hau karaga kasa ta zama tamu
.
Koda jin wannan batu sai gaba dayansu suka bushe da dariyar mugunta dariyar da suke ce masu gadin kofar fadar suka jiyo suka fahimci cewa akwai mutane a ciki dan haka sai suka rugo da gudu suka bude kofar suka haska fitilu koda sukayi arba dasu waziri akiyanu sai suka zube kasa suka kwashi gaisuwa nan dai su waziri Akiyanu suka tarwatse kowa ya tafi gidansa cikin farin cikin muguntar da suka kulla.
.
Lokacin da waziri Akiyanu ya isa gida sai ya tsaya cikin wani babban falonsa inda ya saba ganawa da jama arsa ya zauna nan take ya kira wani bawanda mai suna JAMASI ya umarceshi daya hau doki a cikin wannan dare ya tafi izuwa gidajen wadansu barade su uku musabu, Akaifu da samar yace ya gaya musu cewa suzo yanzu yanzu yana son ganinsu a gidansa cikin rawar jiki jamusi ya fita daga cikin falon ya tafi cika umarni
.
waziri akiyanu na nan zaune a falonsa har tsawon kusan rabin sa a sai ga musabu da akaifu da samar sun bayyana kamar wadanda aka jefosu daga sama cikin biyayya su duka suka zube kasa gaban waziri Akiyanu suka kwashi gaisuwa.
Su dai wadannan barade uku sune manyan mayakan birnin misra wadanda sarki sahibul hairi ke takama dasu domin duk sa adda zai bita yaki sune suke take masa baya kasancewar waziri akiyanu mai dukiyane saiya dinga siye zuciyoyinsu da abin duniya ya zamana cewa yana yi musu kyauta da alheri mai yawa fiye da tunaninsu su kansu sun dade suna mamakin dalilin da yasa yake musu wannan alheri bisa dalilin haka ne suke matukar yi masa biyayya duk abinda ya umarcesu dayi ba zasu ketara ba A zahirin gaskiya ba wani abu bane yasa yake musu alheri ba face tanadin irin wannan rana wacce ya san cewa ko ba dade ko bajima zatazo amfaninsu zai taso.
.
Bayan su barde musabu sun gama kwasar gaisuwa ga waziri akiyanu sai ya dubesu cikin murmushi da girmamawa ya yi musu izinin zama akan kujeru na alfarma ba tare da gardamar komai ba kuwa suka zauna cikin nutsuwa ya sake dubansu yace yaku wadannan zaratan jarumai kuma dirkokin misra ina mai mika godiyata gareku da kuka amsa wannan gayyata tawa ta bazata kuma a cikin wannan dare na san zakuyi mamaki matuka to amma idan kuka dubi sabon yanayin da muka shiga na mulkin kasar nan bai kamata kuyi mamaki ba ku duka kun sani cewa sarkinmu yayi gagarumar tafiya mai tsananin hadari da kowa ya san ba zai taba dawowa ba hakane ko ba hakaba!?
.
Gaba dayansu ukun suka amsa da cewa wannan haka ne gaskiya kam Waziri Akiyanu yayi murmushi sannan yaci gaba da cewa a halin yanzu galadima Aminul has ne sarkinmu maimakon ace nine na hau karagar mulkin.
Ina tabbatar muku da cewa idan yaci gaba da mulkinmu ba zan iya ci gaba da muku alherin da na saba yi muku ba domin kuwa zan talauce na zama fakiri..
Abinda nake so daku shine ku bani hadin kai mu kawar da gwamnatin Aminul has mu kafa tamu idan har mukayi nasarar hakan nayi muku alkawarin zan sanyaku a cikin manyan yan majalisata kuma na baku dukiya mai yawa irin wacce baku taba mallaka ba a rayuwarku idan aka sami akasi akan wannan aiki to kada ku kuskura ku fada sunana domin kun san illar da hakan zata iya haifarwa ina mai dada tabbatar muku da cewa dani da sauran yan majalisa duk bakinmu daya muna da goyon bayansu dari bisa dari
.
Lokacinda su barde musabu suka ji wannan jawabi daga bakin waziri sai duk suka bushe da dariya a lokaci guda kamar hadin baki Al amarin da ya bashi mamaki kenan
musabu ya dubi Akiyanu cikin nutsuwa yace ya shugabana kayi sani cewa yadda muka yarda da kanmu ko sarki sahibul hairi kace mu yiwa juyin mulki zamu iya bare galadima Aminul has wanda bashi da jarumtaka kuma bashi da karfin sihiri na kare kansa muna tabbatar maka da cewa cire silin gashi daga cikin tandun mai yafi wannan aiki wuya a daren gobe zamu je har cikin turakar sarki mu kashe shi salin alin ba tare da kowa ya ganmu ba hatta iyalansa kuwa
.
Cikin mamaki waziri akiyanu ya dubi musabu yace tayaya zaku iya wannan aiki alhalin ciki da wajen gidan sarautar a zagaye yake da dakaru masu tsaro dare da rana
musabu ya sake yin dariya shi kadai a karo na biyu yace ai kowa akan aikinsa sarki ne wannan aikinmu ne ba naka ba.
Don haka ka kyalemu muyi aikinmu kawai sai dai akwai wani hanzari ba gudu ba'
waziri akiyanu ya zazzaro ido yace wanne hanzari ne daku?
Musabu yace duk da cewa wannan aiki mai sauki ne a wajanmu amma hadarinsa na da matukar yawa dalilina anan shine koda bayan ka zama sarki ne idan bisa tsautsayi wani ya ganmu a sa adda muke wannan aiki tofa sai sirrinmu ya tonu har abada jama aba zasuga kimarmu ba da mutuncinmu ba sbd haka ba zamu fara wannan aiki ba face ka bamu dukiya mai yawan gaske ta kimanin rakuma dari dari da shanu hamsin hamsin da kuma gonakai goma goma
.
Koda jin wannan batu sai waziri ya bushe da dariyar farin ciki har da tafa hannaye sannan yace gobe da safe zan dankawa kowannenku wannan dukiya a hannunsa idan aka wayi gari na samu labari cewa galadima ya mutu zam kara muku rubi uku na wannan dukiya yayinda su barde musabu sukaji wannan lafazi sai suka cika da murna nan take suka yiwa waziri sallama suka tafi.
Kamar yadda waziri akiyanu ya yi alkawari haka al amarin ya kasance wato kashe gari da safe ya sake turawa aka kirasu baradan uku ya basu wannan dukiya su kuwa suka tafi suka zauna suna ta shirye shiryen yadda zasu sami nasara bisa wannan gagarumin aiki dake gabansu
.
Lokacin da dare ya fara rabawa sai musabu Akaifu da samar sukayi wata irin shiga ta bad da kama gaba dayansu bakaken kaya suka sa sama da kasa suka fufe fuskokinsu da babaken rawani ya zamana cewa idanunsu kadai ake gani hatta kufen takubbansu da kakalminsu bakake ne bayan sun gama wannan kimtsi sai suka nufi gidan sarautar yayinda suka isa daf da gidan sai suka hada hannayansu waje guda sukayi kawanya faruwar hakan keda wuya sai ga wata guguwa ta zagayesu guguwar ta suresu a sama ta rika yin katantanwa dasu nan take suka rikide suka zama guguwar ta bace dasu bat !!
A can cikin gidan sarauta kuwa yaune dare na biyu ga sarki Aminul has tare da matarsa da samun wannan kwanciya yin barci a gadon sarauta tun a farkon darensuka yi barci suna ta shara mafarkai masu dadin gaske shulaiba na cikin yin mafarki ne ta farka daga bacci kawai sai taji bawali ya kamata don haka saita sauko daga kan gadon ta shiga kewaye ta bar Aminul has a kwance bisa gadon yana ta shara barci abinsa
.
Shigarta cikin kewayen keda wuya sai ga guguwa ta bayyana tana mai kewaye gadon karfin guguwar yasa gashin kan Aminul has ya kama tashi sama maimakon ya farka daga barci sai ya kara gyara kwanciya saboda jin dadin iskar guguwar da ke kadawa nan take kuma sai guguwar ta rikide ta zama su musabu suna zagaye da gadon kowannansu na rike da takobi ya dagata sama tsininta na kallon kasa
.
Lokaci guda suka dubu juna kawai sai suka yunkura da nufin su tsire cikin sarki aminul has da takubbansu bisa mamaki sai sukaji an ruke hannayansu tamau a sama sun kasa saukesu kasa nan fa suka ci gaba da kokarin sauke hannayen amma sai abu ya gagara sai da suka jarraba soke cikin shi sau uku amma suka kasa bisa dole suka hakura suka rikide izuwa guguwa suka bace bat faruwar hakan keda wuya saiga shulaiba ta fito daga cikin kewayen duk abinda ya faru bata sani ba koda ta hau gadon da nufin ta kwanta sai taga gashin kan Aminul has duk ya tarwatse kuma matashin kai ya fado masa mamaki ya kama ta amma dataga cewa Aminul has ya sauya wuri daga inda ya ke kwance saita yi tsammanin cewa garin mirgin murgin Ne ya jeho matashin kan kasa har gashin kansa ya barbaje kawai saitayi kwanciyarta taci gaba da barcinta
Al amarinsu barade kuwa lokacinda suka zama guguwa suka bace bat sai suka bayyana a can nesa da gidan sarautar su ukun suka dubi juna cikin matukar mamaki da razani masabu yace yaya akayi aminul has ya sami tsari da sihiri.
Akaifu yai ajiyar numfashi yace ni dai a tunanina kafin sarki sahibul hairi ya bar gida ya taimaka masa samar yace sam sam ba haka bane shin kun mantane cewa sarki sahibul hairi ya taba gaya mana cewa babu wani mahaluki da zai taba yin amfani da irin sirrikan tsafinsa 
ai duk yadda akayi ya sami wannan tsari ne daga wajan wani mutum daban kun san cewa tun da ya zama sarki dole ne shima ya mike tsaye ya nemi tsari musabu yace to yanzu menene abin da zai fishshemu?
.
Akaifu yace bamu da abinyi face muje mu sanar da waziri akiyanu duk abinda ya faru kuma mu bukaci ya bamu dama ta biyu in ba haka ba kuwa kun san cewa duk dukiyar da ya bamu karbeta zaiyi.
Ai kan wannan shawara baradan suka rabu kow aya tafi izuwa gidansa
Kashe gari da safe tun kafin alfijir ya keto su musabu sukaje wajan waziri akiyanu suka zayyane masa duk abinda ya faru sa adda sukaje hallahaka aminul Has
koda jin wannan batu sai bakin ciki ya turnuke Akiyanu zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone har saida kallar takaici ta fado masa cikin tsananin fishi ya dubi su musabu yace ku tashi kuje na bamu dama ta biyu lallai kuyi tunanin duk hanyar da zaku bi kuga bayan wannan mutum kafin nan kafin kwana bakwai in ba haka ba kuwa duk dukiyar da na baku sai kun dawo mun da ita.
Cikin sanyin jiki da tsananin damuwa su musabu suka mike tsaye suka tafi sai da su musabu suka shafe kwana uku suna tunanin hanyar da zasu bi su hallaka sarki Aminul has amma basu sami mafita ba a rana ta ukuce da yammaci suka tsinci dami a kala a wannan lokaci suna zaune su ukun a can bayan gari suna tattauna wa matsalar kawai sai suka hango sarki Aminul has tare da mai dakinsa da kuma dakaru kimanin mutum dari kacal sun fito ran gadi.
Da yake suna labe ne a bayan wani dutse babu wanda ya hangosu har tawagar sarki ta wuce bayan wucewar sune musabu ya dubesu yace.
Yauwa ga tsuntsu daga sama gasashshe yanzu menen abinyi Akaifu yai ajiyar zuciya yace ai ba hawan ba saukar kun sani dai cewa koda munyi gaba da gaba da sarki ba zamu iya hallakashi ba tunda mun jarraba mun gani
duk su ukun sukayi shiru suka shiga tunani mai zurfi daga can sai dabara ta fadowa samar yace ku bani dama na san abinda zanyi Ni kadai zanje na aiwatar da wannan aiki bana bukatar taimakonku.
.
Hm cikin matukar mamaki musabu ya dubesu yace haba samar tayaya zaka iya yin aikin da mu uku ya gagaremu samar yace ai ka san ance kowanne mutum da irin tasa hikimar kuma ai ita hikima baiwace don haka saiku kyaleni na jarraba sa ata
musabu ya dubi Akaifu yace yaka gani Akaifu yace aiba a kwacewa yaro garma mu bashi dama mu gani
koda jin wannan batu sai samar yayi girgiza ya bace bat su kuwa sai suka ci gaba da labewa a bayan dutsen suna jiran dawowar samar.
.
Lokacin da tawagar sarki aminul has sukayi nisa da bayan gari sukayi nisa da bayan gari sukayi nisa a cikindaji sai suka yada zango a bakin wata koramar koramar mai kyawun ruwa garai garai nan take aka kafawa sarki tanki aka sauke kayansa aka zuba a ciki
.
A rayuwar Aminul has babu abinda yake sha awa sama da harbin tsuntsaye dan haka ana sauka a bakin wannan korama sai yaga tsuntsaye iri iri suna ta shawagi a cikin dajin nan take yasa aka dauko masa kwari da baka ya fara kaiwa tsuntsaye hari bisa sa a kuwa sai yaga yana harbo tsuntsayen suna fadowa kasa ana debewa ana tarawa a cikin wani babban kwando Al amarin da ya jefashi cikin farin ciki kenan yaji zuciyarsa tayi fari ana cikin wannan hali ne samar ya baiyana a wajan ba tare da kowa ya ganshi ba cikin sanda ya isa inda dokin sarki ke daure.
Ba tare da kowa ya ganshi ba sai ya fiddo bakar ciyawa ya baiwa dokin ya cinye koda fruwar haka sai samar ya bace .
Sarki aminul has yaci gaba da harbo tsuntsaye cikin farin ciki da nishadi har sai da ya harbo guda dari a sannan gajiya ta riskeshi ya bada umarnin a tashi a tafi gida nan da nan kowa ya haye kan dokinsa aka juya da baya don a koma cikin gari koda fara tafiyar sai kawai aka ga dokin sarki yai turjiya yana mai dag kafafuwansa sama yana haniniya tamkar ya ga wani abin tsoro da ya firgitashi.
.
Kafin a yi wani yunkuri tuni dokin ya juya da baya sarki na kansa ya zabura da gudu ya nausa cikin dawa cikin tsananin tashin hankali dakaru sukabi bayansa a sukwane don su tsayar da dokin.
Ita kuwa gimbiya shulaiba kida taga abinda ya faru da mijinta sai ta sulale ta fado daga kan dokinta a sume saboda tsananin razana.
Guyson ke magana
dakaru da dokin sarki aka kasa tsere suna ta kokarin cimmasa amma abu ya gagara domin na gaba yai gaba na baya sai labari.
Aminul has yayi ta jan linzamin dokin don ya tsaya amma kamar ma kara masa gudu yake yi don haka sai ya rungumi kaddara ya zuba ido yaga inda...Ya zuba ido yaga inda dokin zai kaishi dokin yaci gaba da azababben gudu ya zamana cewa ya baiwa dakarun tazara mai yawan gaske babu yadda za ayi su cimmasa babu abinda zai baiwa mutum mamaki face yadda dokin yake ratsawa ta cikin kwazazzabai da kayoyi ba tare da wata damuwa ba rami kuwa komai girmansa yana yin tsalle ya haye shi 
.
A iya sanin Aminul has bai taba ganin doki mai tsananin karfin gudu ba kamar wannan doki amma abin da ya bashi mamaki shne ya mallaki wannan doki fiye da shekaru ashirin kuma babu wanda ya taba hawansa face shi kadai yaya akayi wannan doki ya zama maguji haka alhalin bai taba yin tseren gudu da shi ba dokin yaci gaba da gudu irin gudun da idan aminul has yace zaiyi gangancin dira daga kansa sai iya hallaka kansa.
.
Haka dai dokin yai ta tsala gudu har ya iso bakin teku suka lume a cikinsa su biyun a dai dai wannan lokacin dakarun suka iso wajan bakin tekun sukaja tunga cikin thanzari wadanda suka iya ninkaya suka sauka kasa daga kan dawakansu suka fada cikin tekun suka hau lalube.
Saida aka shafe sa a uku suna lalube a cikin tekun amma ba a ga sarki da dokinsa ba bisa dole aka hakura aka fito daga cikin tekun aka juya da baya,
.
Lokacin da labari ya riski gimbiya shulaiba cewa da sarki da dokinsa sun lume a cikin teku an nemesu sama da kasa an rasa sai ta fashe da kuka da kyar kuyanginta suka dauketa suka dorata akan doki aka tafi da ita gida,
.
Nan da nan labari ya cika gari cewa sarki da dokinsa sun hallaka a can bayan gari cikin teku nan fa hankalin jama a ya dugunzuma aka kama kuka cikin kankanin lokaci fada ta cika makil da jama a ana ta koke koke da zullumi cikin tsananin bakin ciki ba komai ne yasa jama ar gari suke wannan bakin ciki ba face sanin cewa yanzu fa mulkine zai koma hannun waziri akiyanu idan kuwa mulkin ya koma hannunsa talakawa sun shiga uku babu wadanda zasuji dadi face masu mulki da tajirai.
Lokacin da labari ya riski waziri akiyanu da mukarrabansa cewa sarki ya hallaka a cikin teku sai farin ciki ya lullubesu sukaji kamar su zuba ruwa akasa su sha tun kafin su iso fada suka fara rabawa makada da mawaka dukiya suka shiga aikinsu kafin a jima kuwa tuni su waziri Akiyanu sun hallara a fadar don kaddamar da bakin nadin sarautarsa kafin ya hau karagar ne makada da mawaka wuka yi ta cashewa bayan nan sai waziri akiyanu ya mike yayi bayanin tsautsayin da ya sami sarki Aminul has har ma ya matso hawayan karya yana mai nuna bakin cikinsa duk da ya san cewa jama a sun san cewa murna yake da faruwar tsautsayin
.
Bayan ya gama jawabin sai ya tafi izuwa kan karagar mulkin don ya zauna ba zato ba tsammani sai aka jiyo sukuwar doki gaba daya jama ar dake fadar suka waigo suka dubi bakin kofa saiga sarki Aminul has bisa wannan dokin a sukwane
.
Da shi da dokin duk a jike suke sharkaf da ruwa Al amarin da ya jefa kowa a cikin mamaki kenan shi kuwa waziri akiyanu sai ya kasa zama a kan karagar mulkin ya kame kamar gunki sbd tsananin mamaki da jin kunya,
Da shi da mukarraban nasa duk sai ido ya raina fata sarki Aminul has yazo har gaban karagar mulkin fuskarsa cike da annuri da zuwa sai yaja tunga ya sauko daga kan dokinsa ya nufi kan karagar
.
Waziri akiyanu ya matsa gefe daya ya bashi hanya
a wannan lokaci gimbiya shulaiba na can cikin turakarta tana shara kukan bakin ciki tana cikin hakanne wata kuyanga tazo ta tabbatar mata da cewa ai ga sarki can ya dawo a cikin koshin lafiya koda jin wannan batu sai ta mike zumbur ta ruga izuwa fada da zuwanta bakin kofar fada saita hango Aminul has a zaune bisa karagar mulki jama a na kewaye da shi suna tayashi murnan tsira da rayuwarsa
.
Kawai sai ta tsaya a bakin kofar ta na ta kyalkyala dariyar farin ciki bayan sarki Aminul has ya gama karbar jajen murna sai ya mike tsaye ya fuskanci jama a yace'
yaku jamar wannan birni na misra na fuskanci cewa kunyi matukar mamaki da kuka ga na dawo gareku a raye?
Hakika akwai alajabi a cikin wannan al amari don haka akwai bukatar nayi muku bayanin yadda akai na kubuta da rayuwata
da farko lokacin da dokina ya zabura dani ya kama gudun tsiya dani sai hankalina ya dugunzuma ainun domin nine nayi kiwon dokin tun yana karami kuma ko sau daya ban taba jarraba yin gudu dashi ba haka kuma babu wanda ya taba hawa dokin in baniba
.
Ko da naga na kasa sarrafa wannan dokin don na tsai dashi sai na rungumi kaddara na zuba ido kawai naga inda zai kaini ban ankara ba sai gani nayi ya afak dani cikin teku kafin nayi wani yunkuri dani dashi mun lume izuwa karkashin tekun
ba zato ba tsammani kuma sai naga munci gaba da tafiya a karkashin ruwa tamkar akan doron kasa muke ba a ruwa ba nan ne fa na dada cika da mamaki ainun.
Haka dai dokin nawa yayi ta tafiya dani a karkashin teku har tsawon sa a biyar kawai sai naga ya juyo da baya cikin tsananin gudu fiye da na farko tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya nan da nan muka iso bakin gabar tekun muka fito waje fitarmu keda wuya ..Sai dokin ya tsugunna kasa ya kama kumallo nan take ya amayar da wata irin bakar ciyawa duk wannan abu da ya faru hannu na na rike da wannan sanda ta hannuna shi kuwa takalmin nan dake kafata bai bar jikina ba kwatsam sai naga wani danguntun Aljani ya bayyana a gabana wanda baifi na kifeshi da kwando ba.
Aljanin yayi sujjada a gareni yace an gaisheka ya wakilin adalin sarki ka kwantar da hankalin ka ka sani cewa indai kana tare da wannan sanda ta hannunka da kuma wannan takalmi na kafarka babu wani tsautsayi da zai sameka
.
Koda naji wannan batu sai na cika da mamaki nace kai kuma waye yaya akayi kasan wannan al amari?
Koda jin wannan tambaya sai aljanin ya bushe da dariya yace ni sunana MAKANUL URUD kuma na kasance mai tsaron wanda duk yake tare da wannan sanda da takalmin in baka mance ba asalin wadannan abubuwa biyu na mahaifin matarka ne wato Abu hakim a wajansa ta gajesu
.
Labarin wadannan sanda da wannan takalmi mai tsawon gaske ne koda zamu kwana bakwai a nan ba zan iya gama jawabi ba ina sanar dakai cewa makiyanka ne suka ciyar da wannan doki naka wata ciyawar sihiri don ya haukace yaje ya hallakar da kai lokacin da ya afka dakai cikin tekunne na biyoku cini na aza dokin a kaina naci gaba da tafiya daku kuma na dinga zuko iskar numfashi daga can saman tekun ina feso muku kuna shaka.
Hm kaji Aikin sihiri .
Wannan shine iyakar bayanin da zan iya yi maka a yanzu sai kuma idan ka sake ganina a karo na biyu koda gama fadin haka sai aljanin ya bace bat bacewarsa keda wuya sai na tashi dokina tsaye na haye kansa na taho nan fada.
Nima yanzu da wannan kalami nake muku sallama don haka na sallami kowa ya tafi izuwa gida a sanar da sauran jama a wadanda basu san hallarataba cewa ina nan a raye ban mutu ba
nan take fada ta watse jama a suka tafi izuwa gidajensu suna masu farin ciki 
Al amarinsu waziri Akiyanu kuwa batun bakin ciki a cikin zuciyoyinsu ba sai an fada ba domin yadda sukaga rana haka suka ga dare a wannan rana
kashe gari da sassafe sukayi shiri su takwas suka tafi izuwa wani kauye da ake kira BAHUS a sirrance don ziyarar wani maketacin boka wanda ake kira da SHUBURUL UZAB
.
boka shuburul uzab ya shahara a cikin yankin kasar misra harma ana ganin cewa in banda boka HADIMUL ASUR babu wand aya fishi ilimin tsafi
da rana tsaka su waziri suka isa gidan boka shuburul uzab inda suka iske shi tsaye a kofar gidansa ya kura musu idanu yana mamaki koda suka matso daf dashi sai ya dubesu ya tuntsure da dariya yace..
Lale marhaban da manyan baki wadanda na dade ina jiran zuwansu a irin wannan rana........
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama su waziri Akiyanu suka sauko daga kan dawakansu cikin sanyin jiki gaba dayansu suka risina suka kwashi gaisuwa sannan waziri ya dubi boka shuburul uzab cikin nutsuwa yace.
Yakai wannan boka mai daraja kai kuwa menene dalilin da yasa kace ka dade kana jiran zuwanmu gareka?
Idan har kana son mu ziyarceka me yasa tuntuni baka aika mana muzo ba?
Zan Cigaba Insha Allah

Share:

SARKIN SARAKAI BOOK 2. 02

SARKIN SARAKAI BOOK 2. 02
Koda sarki sahibul hairi ya fuskanci manufar wannan macijiyar sai yayi ta zulle da goce goce yana kaimata duka da hannu da kafa gami da kai ma ta sara ita kuwa ta dinga fyada masa jelarta kafin wani lokaci duk su biyun sunji jiki haka dai aka cigaba da wannan gumurzun har izuwa tsawon wata sa'a gudan Ana cikin hakane sarki sahibul hairi ya shammaci macijiyar nan ya soki idonta guda da tsinin takobinsa faruwar hakan keda wuya sai ruwan idon ya fashe yace tus! Kamar an fasa kwan jimina saiko ruwan jini yata kwarara tamkar teku ta balle ammam saboda naci saida macijiyar taci gaba da kokarin hadiye shi Abinda sahibul hairi ya lura dashi shine kanda wannan ido ke jiki bashi da kuzari kamar sauran kawunan koda ya lura da haka sai yaci gaba da fas a sauran kawunan na jikin sauran kawunan dama a jikin kowanne kan idanuwa biyune idan sarki sahibul hairi ya sami nasarar fasa idanuwa biyu saikaga wannan kai ya daina tasiri ya fadi kasa ya jabe tamkar jikakken tsumma yayinda sarki sahibul hairi yaga ya samo lagon macijiyar saiyaci gaba da fasa mata idanu har saida yafasa gaba daya idanun nan take macijiyar ta baje kasa matacciya jini kuwa ya rinka fita a jikinta saida ya kusan shanye sahibul hairi yazo masa iya kirji kaikace a cikin kogi aka tsomashi A sannanne shima ya langabe a jikin garu ya kama nishin gajiya koda ya dubi jikinsa sai yaga ko ina yai burdin burdin wato jini ya taru masa sakamakon dukan da macijiyar nan ta ringa yi masa tana fyada shi da kasa da kawunanta da jelarta saida sarki sahibul hairi ya kwana ya yini yana jinyar jikinsa a cikin wannan daki na muguwar macijiyar sannan ya sami kwarin jikinsa naman macijiyar ne ya zamo abincinsa a iya tsawon wannan lokaci bayan ya dawo cikin hayyacinsa sosai kuma ya gama jinyar jikinsa sai ya tunkari kofa ta gaba wato daki na hudu kamar yadda ya banke kofa ta uku haka ya banke kofa ta hudu kawai ya kunna kai ciki shi dai wannan daki na hudu ya sha ban ban da sauran dakunan uku da ya wuce domin shi ya kasance mai tsananin tsawo da babu alamar karshe sannan kuma babu wada taccen haske a cikinsa daga shigar sahibul hairi cikin wannan daki sai ya dinga jiyo wani irin gurnani mai ban tsoro irin wanda bai taba ji ba a rayuwarsa koda jin wannan gurnani sai sarki sahibul hairi ya tsaya chak yana waige waige da nazarin gurnanin kawai sai sahibul hairi ya daga takobinsa sama ya riketa da hannu biyu yaci gaba da tafiya abinsa a hankali yana mai ci gaba da waige waige da dube dubensa kwatsam sai ya tsinci kansa a tsakiyar wani makeken fili wanda bashi da duhu ko kadan kuma babu alamar wata kofa da za a fita isowarsa wannan wuri sai hanyar daya biyo ta shafe ya zamana cewa babu batun komawa da baya babu gaba sahibul hairi ya gyara tsayuwarsa yana wulkila idanuwansa izuwa kowanne bango yana jiran duk abinda zai baiyana gareshi bazato ba tsammani sai ya ga wadansu irin gabza gabzan dodanni suna ta fitowa ta cikin gango tamkar haske suna yi masa kawanya Adadin dodannin yakai dari biyar kuma kowannensu yana rike da zabgegiyar makami kai koda guda daya daga cikinsu aka turo birnin Misra zai iya tarwatsa birnin gaba daya wasu da majaujawa ce mai kula kulan tsini wanda girman makaman kadai yafina bil adama bare kuma su kansu don haka lokacin da dodannin sukayi masa kawanya sai ya zamo dan mitsitsi a tsakiyarsu don dayansu ma zai iya tatsileshi da kafa daya babu abinda zai firgita mutum face irin munin fuskokin dodannin don idan mutum ya cika kura musu idanu zuciyarsa zata iya tashi kumallo bayan dodannin sun gama yiwa sarki sahibul hairi kawanya sai suka kama karkada makamansu suna jujjuyasu koda ganin haka sai shima sarki sahibul hairi ya kama wasa takobin hannunsa yana jujjuyata .
Lokaci guda dodannin suka kawo masa wawan duka da sara da makamansu cikin zafin nama sarki sahibul hairi ya daka tsalle sama har saida ya tabo rufin saman dakin koda makaman dodannin suka bugi kasa sai suka haifar da wawakeken rami tamkar rijiyar da karti hamsin suka kwana suna hakwa A sama sarki sahibul hairi ya fara saran dodannin amma sai yaji kamar karfe yake sara don har tartsatsin wutane ke tashi nan fa dodannin sukayi ta kai masa sara da suka yana zukewa kuma shima bai fasa saran su ba tuni hankalin sarki sahibul hairi ya dugunzuma domin ya san cewa idan aka jima ana wannan artabu gajiya zaiyi in kuma ya gaji take dodannin zasu gama dashi Lokacinda dodannin sukaga sarki sahibul hairi na wahalar dasu ya zame musu alakakai sai suka fara wani irin sabon gurnani mai tsananin kara wanda ka iya sa kunnan mutum ya dode ba shiri sarki sahibul hairi ya yagi rigar jikinsa ya nannadata a kansa wato ya rufe kunnuwansa yaci gaba da artabu amma dukda haka saida kunnuwansa sukayi dum ! Kamar an zuba masa ruwa a ciki ana cikin wannan gumurzu ne daya daga cikin dodannin ya yagi kirjin sarki sahibul hairi da faratan hannunsa guda uku.. . 
Take wajan ya dare tamkar an sareshi da takobi uku a lokaci guda har saida jini yai tartsatsu sarki sahibul hairi ya kwarar uban ihi saboda tsananin jin zafin da yayi ya fado kasa magashiyan . Koda ganin haka sai dodannin sukayi ca a kansa gaba daya da mugun nifi kowannansu ya zaro faratan hannunsa da nufin su yi tsire da gangar jikinsa cikin tsananin zafin nama sarki sahibul hairi yayi katantanwa a tsakiyarsu yana filfila takobinsa ya fice fit ta karkashin kafafuwansu . 
Lokacinda suka kawo masa suka da faratanne bisa tsaursayi wani daga cikinsu ya caki wani da farce a tsakiyar kai take wanda aka caka aka kansa ya huje saiga jini yai tsira sama take ya sulale kasa matacce . Wani kuma da ya soki wani a hannu sai ya tsinke masa hannu koda sarki sahibul hairi ya fahimci abinda ya faru sai yayi wata irin yar dungure a kasa ya mirgina sau goma a cikin dakika daya ya suri guntulallen hannun dodon da ya guntule ya mai dashi makaminsa .
Ai kuwa sai fada ya sauya salo domin da farcen hannun dodannin ya dinga yiwa dodannin barna wato yayi ta saran jikinsu jini na zuba amma saboda naci da taurin kai saikaga sunyi girgiza sun ci gaba da kokarin hallakashi babu abinda zai burge mmutum kuma ya bashi mamaki face yadda sarki sahibul hairi ke yin wannan yaki cikin matukar karfin hali da juriya domin tuni jiri ya fara dibarsa sakamakon jinin dake zuba a kirjinsa amma duk da haka yaki yarda ya fadi kasa kuma bai fasa ci gaba da ragargaza su ba abindake tayar masa da hankali shine basa mutuwa . 
Saida aka shafe sa a ana wannan artabu ya kasa kashe dodannin su kuma sun kasa hallakashi amma kuma suma sun fara nakasa shi domin sun yayyankeshi da kaifin faratansu gaba daya jikinsa yai fata fata da jini kamar yadda nasu yayi A wannan lokacin ne sarki sahibul hairi da dodannin suka kamalayi kamar wadanda suka sha giya suka bugu Wohoho hakika idan namiji ya cika namiji baya faduwa kasa banza sai dai ayi ragas sai da ya rage saura kiris ayi mutuwar kasko sai sarki sahibul hairi ya sami nasarar sukar tsakiyar kan daya daga cikinsu nan take kuwa dodon ya sulale kasa matacce .
Koda ganin haka sai sahibul hairi ya tabbatar da cewa ruhin dodannin a tsakiyar kansu yake nan fa ya ringa tsalle a kansu kamar dan biri cikin zafin nama tamkar walkiya yana ta soka musu farcen a tsakiyar kawunansu sai gashi dodannin suna sulalewa kasa matattu tamkar ana sassabe a gona cikin abinda bai wuce dakika dari da sittin ba gaba daya dodannin suka zama gawa . Koda ya gama kashe dodannin sai shima ya sulale kasa sumamme sarki sahibul hairi bai farfado ba sai bayan sa'a biyu farkawarsa keda wuya sai yaji kirjinsa na yi masa azababben zugi da radadi koda ya dubi kirjin yaga wannan lafcecen yanka guda uku sai hankalinsa ya dugunzuma domin ya tabbatar da cewa wannan rauni zai iya zama sanadin ajalinsa don har yanzu jini na zuba a jikin rauninnan fa ya fara tunanin hanyar da zaibi ya yiwa kansa magani yana cikin hakan ne wata dabara ta fado masa da jan ciki ya rarrafa yaje kan gawar dodo guda ya cisgi gashin kansa sili uku sannan ya dauki guntulallen hannun dodon ya sa a bakinsa ya fisgi farce guda sannan yayi amfani da wani farcen ya yanke wannan farcen da ya cisge har saida ya mayar dashi dan siriri kamar allura . Da wannan allura da kuma silin gashin dodon ya dinke raunin dake kirjinsa guda uku bayan ya kammala dinke raunikan ne ya jingina bayansa a jikin bango yai shiru yana hutawa da tunani tabbas yanzu dai ya san cewa ba zai iya shiga cikin daki na biyar ba face ya zauna yayi jinyar raninsa a kalla kwana bakwai . 
Abin tambayar anan ya za ayi ya rayu har tsawon kwana bakwai a cikin wannan daki baci basha? Kai idan ma akwai abinci da sha ai gawan dodannin ma idan ta rube warinta kadai ya isa ya kashe shi wai shin ma masifu nawa ne suka rage a gabansa kafin ya samu ya fita daga cikin wannan wuri na karkashin kasa? 
Koda yazo nan a tunaninsa sai zuciyarsa ta karaya nadama ta sake zo masa a karo na biyu ya fara sabon tunani . Lokacin da sarki sahibul hairi yayi tunani har tunanin ya ishe shi sai yace da kansa kai wannan banzan ba zai fishsheni da komai ba abinda zai fishsheni kawai shine na yi tunanin hanyar da zan iya rayuwa a cikin wannan daki har tsawon kwana bakwai . Sarki sahibul hairi ya shiga sabon tunani ai kuwa bai dade ba yana wannan tunani sai dabara ta fado masa cikin karfin hali ya mike tsaye yana kama gawarwakin dodannin yana zuba su cikin ramin nan da suka yi sakamakon kawo masa sara da makamansu sai bayan ya zuba fiye da rabin gawar a ciki ya fuskanci cewar ramin ba zai cinye dukkanin gawar ba bisa dole ya sake fito da gawarwakin ya shiga aikin daddatsa gawarwakin gutsun gutsun sai dai ya yi sa a biyar yana wannan aiki sannan ya gama daddatsa su duka.
Daya gama sai ya kwashi kadan daga cikin sassan jikin dodannin ya ajiye gefe guda kuma ya saro kofaton dodo guda biyu ya ajiye da yai haka sai ya dure gangar jikin dodannin duka a cikin ramin sannan ya kama bako kasa yana watsawa cikin ramin har saida ya binne wannan sassan jiki duka a cikin ramin . A sannan ne fa ya gaji likis kuma ya jike sharkaf da gumi kamar an tsamoshi daga kogi saida ya huta tsawon rabin sa a sannan ya sake mikewa yaje gaban kofaton dodon da ya ajiye ya tsugunna kawai sai ya maida kofaton kyastu ya dinga goga daya akan daya har izuwa tsawon lokaci sannan yayi sa a wuta ta kama a jikin naman dodon daya hada waje daya . Kawai sai ya kurawa wutar da naman idanu har saida naman ya babbake gaba daya kawai sai ya kama cin naman dodon yana ci yana zubar da hawaye ba komai ne ya haddasa wannan hawaye ba face tsananin rashin dadin naman dodon da kuma tsananin takaicin da ya tsinci kansa a ciki ya tuna cewa shifa sarki ne guda amma yau gashi ya tsinci kansa a cikin wannan mugun hali har ma yaci danyen naman zaki kuma yaci naman dodo haka dai sarki sahibul hairi yaci gaba da cin wannan naman cikin matukar juriya har saida yaji cikinsa ya cika yana gamawa kuma sai yaji kishirwa ta addabeshi a sannan ne fa ya gane kuskurensa domin ko kadan baiyi tunanin hanyar da zai magance kishi ba . Bisa dole ya kama kwankwadar jinin dodannin nan da ya malala a kasa cikin dakin nan ma saida ya sha ya ishe shi sannan ya bingire kasa cikin jini ya kama barcin dole Allah sarki ita masifa ba a samata rana ita kuwa kazar wahala indai mutum ya yankota to sai ya fige abarsa . 
HAKa dai sarki sahibul hairi yaci gaba da rayuwa a cikin wannan daki na hudu har izuwa tsawon kwana bakwai ya zamana cewa bashi da abinci sai wannan babbakakken naman dodon daya tanada ruwan shanshi kuwa wannan jini ne nasu har saida jinin ya daskare amma bai daina shansa ba ahaka duk da cewa jinin yana wari da karni mai tayar da zuciya . A ranar kwana na bakwai ne sarki sahibul hairi yaji kwarin jikinsa kuma wannan rauni na kirjinsa ya kame nan take sarki sahibul hairi ya mike tsaye ya sungumi gatari daya daga cikin na dodannin nan da ya kashe shi kansa saida ya hada karfinsa waje guda sannan ya iya daga gatarin sama . Nan fa ya shiga saran bango domin ya samarwa da kansa hanya ta fita bai gushe ba yana saran bangon har saida yayi sa a uku ta shude sannan ya sami nasarar fasa garun kofa ta samu kawai sai ya yarda gatarin ya kunna kai cikin daki na biyar . Shidai wannan daki na biyar ya bambanta sosai da sauran dakunan hudun da ya wuce a cikinsu domin ko kadan babu duhu a cikinsa a haskake yake fayau kamar rana babu komai a cikin dakin face wasu manyan akwatuna guda bakwai wadanda aka rufesu ruf da wani irin murjejen kwado mai kaurin gaske kafin mutum ya iya sareshi sai ya jike sharkaf da gumi . 
Koda sarki sahibul hairi yayi arba da wadannan akwatunan sai yayi tsaki yace '' To meye gamina da wadanna akwatuna Ai ni hanya kawai nake nema da zan fita daga cikin karkashin kasar nan '' koda gama wannan furuci sai ya koma da baya izuwa wannan daki na hudu ya dauko gatarin nan ya dawo ya kama saran bangon daki na biyar din don ya sami hanya koda ya fara saran bangon sai yaji kamar karfe yake sara koda ya kara kaimi sai bakin gatarin ya kama dakushewa al amarin da ya dugunzuma hankalinsa kenan amma saboda naci bai fasa sara ba har saida ya gaji likis yaga babu alamar nasara sannan yayi jifa da gatarin ya tsugunna a kasa cikin alamun bakin ciki da karayar zuciya . Ya kurawa wadannan akwatunan bakwai idanu ya shiga tunani'' to wai in banda abinka ai gatarin sihiri kazo nema babu mamaki ma yana cikin daya daga cikin akwatunan nan don haka me zai hana ka jarraba bubbude su ka gani '' . Wata zuciyar kuma sai tace kai kada ka bude akwatin nan domin wata kila wasu masifunne aka tanada a ciki haka dai sahibul hairi yayi ta tunani iri iri ya kasa yanke hukunci daga can sai ya mike tsaye yaje ya kwankwasa akwatin farko baiji alamar akwai wani abu a ciki ba . Ya kara kunnansa a jikin akwatin nanma yaji shiru babu alamar wani motsi a ciki kawai sai ya mike tsaye yaje ya dauko gatarin nan ya kama saran kwadon makullin akwatin ta farko aikuwa bai dade ba yana saran ya bincineshi . Sarki sahibul hairi ya sunkuya ya cire kubar sannan ya daga murfin akwatin dagowar ke da wuya sai yaji wasu abubuwa kaman kwari sun yi fitar burgu daga cikin wannan akwatin sun doki fuskarsa saboda karfin dukan saida yayi sama ya gwaru da rufin saman dakin ya fado kasa a galabaice . Ba wasu abubuwa bane suka fito daga cikin wannan akwatu face wasu yan kananan aljanu wadanda girmansu bai wuce na fara ba Adadinsu yakai miliyan daya su duka suna wata irin kara mara dadin ji . Kafin sarki sahibul hairi yayi wani yunkuri tuni sun sureshi sunyi sama dashi suka rinka gwarashi a jikin bango basu saukeshi ba saida sukaga sun farfasa masa kai da jiki ya suma . 
Bayan sun sauke shi ya rikito kasa sai suka rinka curewa waje guda da kadan kadan kafin su gama curewa sai sarki sahibul hairi ya farfado koda ya gama kyallara idanunsa ya hango wadannan kananan aljanu suna curewa a waje guda ba tare da sanin abinda suke shirin yi masa ba sai hankalinsa ya dugunzuma tabbas ya san cewa ba zai iya yin fada da wadannan aljanun ba kawai sai ya yunkura cikin zafin nama ya dauki . Akwatin da suka fito daga ciki ya kifa a kansu ta rufe su fuf to amma ya rufe daki ya kulle da barawo domin akwai ragowar kimanin guda dubu da bai rufe dasu ba duk da cewa ya zauna akan akwatin sai da suka ringa girgiza suna kokarin jefar dashi daga kanta don su fito waje shikuwa sai ya yi amfani da dukkan karfinsa wajen danne akwatin yayinda ragowar aljanun suka ga an danne yan uwansu a cikin akwatin sai suka tasamma sarki sahibul hairi suna kai masa cizo da yakushi nan fa sarki sahibul hairi ya raba karfinsa da hankalinsa gida biyu . 
Ya zamana cewayana yaki da wadannan aljanu dubu kuma yanaci gaba da kokarin danne wannan akwatin wadda ya zauna a kanta. Sudai wadannan aljanu suna da fuka fukai don haka shawagi sukeyi kawai akan sarki sahibul hairi suna kai masa hari tako ina shi kuwa ya wanzu yana kai musu sara cikin zafin nama da takobinsa takobin bata iya yi musu komai amma karfin dukan da yake shine yake kadar dasu su fadi kasa. Ana cikin wannan dauki ba dadi ne daya daga cikin aljanun ya sami nasarar kafa hakoransa akan kafar sarki sahibul hairi aikuwa koda ya ciza sai ya finciko. Sai ga gudan tsokar nama a bakinsa tsananin zafi da zugin da sarki sahibul hairi yaji ne yasa ya kwala kara mai karfin tsiya. Wadda ta firgita aljanun suka ja da baya a dai dai wannan lokaci ne ya lura da cewa aljanun da ya danne a cikin akwatin da yake kai sun daina motsi koda ya sunkuya kansa sai yaga jini na malalowa waje. Cikin sauri ya daga akwatin sai yaga ashe gaba daya aljanun sun mutu. Ba wani abu bane ya kashe wadannan aljanun face rashin iskar da zasu shaka numfashi A farko kafin sarki sahibul hairi ya bude wannan akwati a saman murfinta akwai hudoji masu yawa wadanda koda mutum ya leka ta cikinsu ba zai iya hango abin dake ciki ba sirrin ruhin wadannan aljanu shine ko yaya suka daina shakar iska a duniya sai jikinsu ya kama daddarewa shi yasa da aka kullesu a cikin wannan akwatin aka hurhuda samanta. . Sa adda sarki sahibul hairi ya kifesu da akwatin a kasa ba sa shakar numfashi shiyasa suka mutu lokacin da sauran aljanun guda dubu sukaga gaba daya yan uwansu sun mutu sai suka harzuka suka sake afakawa sark sahibul hairi da nufin su hallakashi farat daya shi kuwa sai yaci gaba da makesu da wannan takobi tasa.amma duk wanda ya fadi kasa sai ya sake tasowa tamkar babu abinda ya sameshi sai da aka shafe sa a hudu ana wannan gumurzu in banda rauni na farko da aka yiwa sarki sahibul hairi a kafa babu abinda ya sameshi amma kuma gajiya ta fara riskarsa . Su kuwa wadannan aljanun kamar ma a sannane suka fara fafatawa koda sarki sahibul hairi ya fuskanci cewa idan fa akaci gaba da wannan fada izuwa wani lokaci zasu hallakashi sai ya sauya shawara cikin zafin nama ya suri wannan akwatin ya ruke a hannunsa duk aljanin da ya make a sama suka fado kasa kafin su yunkura su sake tasowa sai ya kifesu da wannan akwati ya take akwatin da kafarsa guda yana mai ci gaba da saran sauran ba zai daga akwatin ba har saiyaga jini na fitowa daga karkashinta a haka a haka har sarki sahibul hairi ya samu da kyar da sidin goshi ya karar da wadannan aljanun duka . Nan fa ya tsugunna kasa yana numfashi sama sama cikin karfin hali ya yagi rigarsa ya daure wannan rauni dake kafadara don tsaida jinin sannan ya kurawa ragowar akwatunan shida idanu yana shawara a cikin zuciyarsa akan ya budesu ko kuwa kada ya bude. Wata zuciyar tace dashi ''ya za ayi kaci gaba da bude wadannan akwatuna alhali baka san masifar dake cikinsu ba''. 
Wata zuciyar tace dashi kuma' ++ to idan baka bude akwatunan ba me zakayi tunda baka da wani zabi wand ayafi hakan''. Koda gama wannan tunani sai ya mike tsaye yaje kan akwati ta biyu ya dauki gatarin nan ya kuma saran kwadon sannu a hankali ya bincine kwadon yasa hannu ya zareshi ya daga murgin akwatin sama faruwar hakan keda wuya saiga wata katuwar kunama ta fito daga ciki tunda sarki sahibul hairi yazo duniya bai taba gainin kunama mai girma kamarta ba . Koda kunamar tayi arba da shi sai ta tasammasa tana wurkila kafafuwanta guda goma sha biyu masu fitar da dafi ga kuma kaifin farata. Sarki sahibul hairi ya kama ja da baya ita kuma taci gaba da binsa har sai da ya kure a jikin bango. Nan fa suka fara mugun artabu ya zamana cewa tana kawo masa suka da kafafuwanta ta ko ina shi kuma yana kare kansa gami da kai mata suka amma duk inda ya soka a jikinta sai yaji kamar dutse ya soka ko kwarzanewa bata yi Al amarin da ya dugunzuma hankalinsa kenan. Ya tabbatar da cewa bashi da wata sauran dabara face yayi iya yinsa inda karfinsa ya kare shi kenan haka dai aka ci gaba da fafatawa kunamar ta kasa hallaka sarki sahibul hairi shima ya kasa cutar da ita har izuwa tsawon lokaci ana cikin hakane kunamar tayi masa wata irin mahaukaciyar sura tayi sama dashi ta makashi a jikin bango ya fado kasa . Cikin tsananin galabaita harma yaji ba zai iya tashi ba koda ganin haka sai kunamar ta taho gareshi cikin tafiyar kasaita da nufin ta caka masa kafafunta shida ta zuba masa dafi... ... . 
Koda ta iso daf da shi ta daga kafafuwan nata sama zata cakeshi sai ya yunkura cikin zafin nama ya daka tsalle ya haye samanta kawai sai ya kama naushin idanunta da hannunsa guda ita kuwa ta rinka kawo masa suka da kafafunta yana kadasu da takobinsa nan fa suka yi ta wutsil wutsil da mirgin mirgin ya zamana cewa ta kasa cafkoshi shi kuma ya kasa burma idanunta . Koda ganin wanki hula zai kaishi dare sai ya fusata ya dunkule hannunsa ya tattaro karfinsa duka ya gabzawa kunamar mahaukacin naushi a ido take kwayar idon ta fashe hannunsa ya lume a cikin idon tamkar an zura guga a rijiya saiga jini na bulbulowa nan fa kunamar ta kama tamagungun. . Cikin hanzari sarki sahibul hairi yya daka tsalle ya dira a kasa daga kanta kunamar taci gaba da birgima a kasa tana wani irin gurnani da kakarin mutuwa tun tana motsi sai data sandare komai na jikinta ya daina aiki. . 
A sannan ne hankalin sarki sahibul hairi ya dawo jikinsa ya kawo gwauron numfashi ya ajiye ya kurawa gawar kunamar idanu jim kadan sai kuma ya dubi akwati ta uku ya fara tunanin budeta sarki sahibul hairi ya mike tsaye yaje kan akwatin. . Har ya sunkuya zai dauki gatari ya sare makullin sai ya fasa kawai sai ya dauki gatarin ya wuce izuwa kan akwatin kashe ya kama saranta koda ya balle makullin ya budeta sai yaga wani irin haske ya fito daga cikinta ta bugi jikin bango take zanen kofar ya fitar da kansa sai ga wata kofa ta bayyana kuma ta bude kanta wanda ta cikinta ne za a iya shiga cikin daki na shida sarki sahibul hairi ya kurawa kofar idanu cikin tsananin mamaki yace '' Oh! Na yankewa kaina wahala yanzu inda na bude sauran akwatunan can da yanzu ina cikin masifa. . Gama fadin hakan keda wuya ya yarda gatarin dake hannunsa ya dauki takobin ya kunna kai cikin wannan kofa ta shiga da shigarsa kofar sai ya tsinci kansa a cikin wata wangamemiyar fada wadda aka kawatata ainun da abubuwan ban sha awa komai dake cikin fadar an sassakashi ne da dutsen lu'u lu'u don haka fadar ta haskake da sheki da walwali . Sarki sahibul hairi yaci gaba da tafiya a cikin fadar yana wuce wadansu gumaka wadanda aka yi su cikin siffofin dukkanin sarakunan da suka mulki birnin Askandariyya sarki sahibul hairi yaci gaba da tafiya a cikin fadar nan yana kallon abubuwan al ajabi iri iri ba tare da ya taba komai ba . Kwatsam sai ya hango wani karamin baho na zinare a tsakiyarsa an kera wani kyakkyawan dawisu na karfe ruwa na diga daga cikin bakin dawisun yana zuba a cikin bahon har ya dan taru mamaki ya kama sarki sahibul hairi bisa yadda makerin wannan dawisu da bahon yayi basira wajan sassakasu . Abinda yafi bashi mamaki shine ta ina wannan ruwa yake shiga cikin jikin dawisun har yake digowa kasa ta cikin bakinsa sarki sahibul hairi ya zagaye bahon yaga babu ta inda ake zuba ruwan sai ya dada cika da mamaki kawai sai sha awar dawisun ta debeshi ya dafa kansa faruwar hakan keda wuya sai wadansu kibiyoyi suka rinka cillo kansu ta ko ina zasu soke sarki sahibul hairi. Cikin zafin nama ya rinka karkade kibiyoyin amma sai yaga kibiyoyin sunki karewa saboda haka sai ya zabura ya kama gudu a cikin katon dakin yana gudu yana karkade kibiyoyin ta gaba ta baya. Hakika in ba don sarki sahibul hairi ya kasance mai tsananin zafin nama ba da tuni sama da kibiyoyi dari sun cake a jikinsa duk da zafin namansa sai da kibiyoyi uku suka cakeshi. Har ya fada bayan wani gunki ya labe kibiyar farko a cinya ta cakeshi ta biyu a bayansa wajan kuibin kafadar hagu ta uku kuwa a hannunsa na dama. Cikin tsananin galabaita ya fadi sharam!! A bayan gunkin a sannan ne kuma kibiyoyin suka daina cillo kansu daga inda suke fitowa cikin tsananin dauriya sarki sahibul hairi ya zare kibiyar dake jikin hannunsa jini yai tsartuwa yana mai rusa ihu saboda tsabar zafi da zugi A haka ya zare kibiya ta biyu da ta uku sannan kuma ya daure inda kibiyoyin suka cakeshi da tsumman rigarsa dan tsaida jini gama yin hakan ke da wuya sai yaji jiri ya debeshi nan take ya sulale kasa sumamme. . 
Sarki sahibul hairi bai farfado ba sai bayan rabin sa a yana bude idanu ya tsinci kansa anan inda yake. Wato a bayan wannan gunki kawai sai ya mike tsaye da kyar yaci gaba da tafiya a cikin katuwar fadar saida yayi doguwar tafiya sannan ya kure karshenta ba tare da ya sake shiga wani hadarin ba kawai saiyaga wadansu kayan yaki kala uku na karfe a rataye a jikin bango. . Daya bakine daya fari daya kuma ja kowannensu rigane da wando da hula kuma da takalmi har da takobi sarki sahibul hairi ya kurawa kayan yakin idanu yana shawarar wanda ya kamata ya dauka ya sanya a jikinsa da ya dubi bakaken kayan da farko sai yace.. Kai shifa bakin abu duk inda yake ba abin sha awa bane kuma kalace mai nuna mugunta don haka bazansa bakin ba. Ya dubi jajayen yace. Shikuma jan abu ai kalace ta ban tsoro mai nuna alamun tashin hankali don haka bazansa jaba. Ya dubi farin yace. Yauwa fari kalace ta adalci da nuna alamun tausayi don haka zu sansa..... . yaudai zakusha karatu .......
Zan Cigaba Insha Allah

Share:

Popular Posts

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...

Blog Archive

Recent Posts

Unordered List

 • Lorem ipsum dolor sit amet, consectetuer adipiscing elit.
 • Aliquam tincidunt mauris eu risus.
 • Vestibulum auctor dapibus neque.

Sample Text

Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipisicing elit, sed do eiusmod tempor incididunt ut labore et dolore magna aliqua.

Ut enim ad minim veniam, quis nostrud exercitation test link ullamco laboris nisi ut aliquip ex ea commodo consequat.

Pages

Theme Support

Need our help to upload or customize this blogger template? Contact me with details about the theme customization you need.