Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

Showing posts with label Mace Uwar Al'ummah (Women's World). Show all posts
Showing posts with label Mace Uwar Al'ummah (Women's World). Show all posts

AMFANIN SHAZABU GA MACE


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*


_*AMFANIN SHAZABU GA MACE*_

Shidai shazabu yanada amfani sosai musamman matarda bata haihuwa. Shazabu wata itaciya ce mai albarka kuma mai dadin kamshi, duk matarda take son ta samu haihuwa to sai tasamu shazabu mai kyau sosai ta samu zuma itama mai kyau sosai ta hadasu ta rinka sha sannan kuma ta rinka shafawa a gabanta, insha Allahu zata samu haihuwa koda kuwa bata ta6a samuba. Ganyensa kuma yanada karfi sosai wajen fidda Aljanin jikin dan Adam anan take, kuma yana sumarda Aljani. 


WabillahinTaufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*


*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a shiga ta wannan link din* 👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/CzHKa3hRV7DDAAqmz8T1WZ
Share:

MACE MAI MUMMUNAN HALI


🔥GOBARAR ZAMANI
05//

Wallafar:-- Mal. Aliyu Sa'id Gamawa

*Mace Mai Mummunan Hali*

Mace mai mummunan hali, ita ce mai waɗannan halaye: 

- Hauragiya, tsiwa (daga harshe ga mai gida) 

- Kwarmato, mita, gulma, qananan maganganu 

- Ɗora wa miji sai ya sayo abin da ya fi qarfin arzikinsa. 

- Rashin suturta jiki da ganin kai, da sha’awar munanan al’adu. 

- Qaryata mai gida, ko yi masa dariya yayin da ake hira. 

- Yawan yawo da qaurace wa mai gida a shimfiɗa

- Qin yin aikin ibada ko maganganun batsa. 

   Haka dai Malam Rumfa da uwar gidansa suka yi ta irin wannan tattaunawa har zuwa wani lokaci, daga qarshe dai Rahmatu ta ce, Allah ya kai ku lafiya ya dawo da ku lafiya, ya kuma ba ku sa’a. Malam Rumfa ya ce, amin. Don haka jibi da safe za mu tafi in Allah ya kai mu, tafiyar dai za ta ɗauke mu kwanaki goma (10), domin zuwa da dawowa kwana takwas ne (8). Sai dai an ce duk wanda ya yi tafiya ita take da shi, Ba shi ke da ita ba. Ma’ana sai an ga dawowarsa. Suna cikin hira sai Malam Rumfa ya hango wata takarda, ya tambayi Malama Ramatu, sai ta ce, “Jiya malamanmu suka raba mana a makaranta, wai tsaraba ce ta wani taro da suka halarta a can Duniyari a kan kula da lafiyar uwa da yara qanana, da halarcin yi musu rigakafi.” Malam rumfa ya ce, “ Ni a da ban yarda da duk surutun ’yan book da gwamnati a kan rigakafi ba, amma na saurari wani qwararre akan kiwon lafiya da sanin cututtuka, sai na gamsu cewa kusan ma wajibi ne mu kula da kanmu, iyalanmu da yaranmu wajen kiwon lafiya da yin rigakafi ga yara da manya. In muka ci gaba da kasancewa a cikin duhun kai da gujewa duk tsarin da ake kawo mana a kan kula da lafiyamu da ta iyalanmu, to haka za mu zauna har yaranmu su cutu.”

Zamu cigaba Insha Allah

✍️ Ibrahim Muhd Abu muhd

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Share:

DALILIN DA YASA MATAN HAUSAWA KE TSUFA DA ZARAR SUN YI AURE


*Dalilin da ya sanya matan Hausawa ke tsufa da zarar sunyi aure:*

Written by Jamil Usman

- Babbar matsalar mata a zamanin nan ita ce bakar kazanta da rashin kula da jikinsu matukar anyi aure.

- Wannan mummunar dabi'ar kazantar na sa mace ta tsufa tare da ba miji hanyar neman matan banza a waje.

- Dabi'ar kazanta na sa miji ya dinga kyamar matar shi ta yadda baya iya cin abincin da ta girka ballantana a kai ga kwanciyar aure.

Sau da yawa auri saki ya fi ta'azzara tare da yawa a kasar hausawa. Hakazalika ganin karamar yarinya ta tsufa cikin shekara daya ko biyu bayan aure ya zama gama-gari. Yarinya budurwa tana yin aure, haihuwa daya zuwa biyu take yi ta zama wata uwar mata. A lokacin da take tashen budurcinta kuwa, zaka ganta yarinya sharaf mai aji, kwalliya, tsafta ga iya kame jikinta.

Ba wani abu ke tsufar da matan ba da ya wuce kazanta. Mata da yawa bayan sunyi aure su kan yada makaman kwalliya, tsafta, gayu da kame jikinsu. Suna kuwa haihuwa daya, biyu zuwa uku suke tsufa kamar sun haifa mazan nasu. 

Sau da yawa sai ka ga mazan sun fara bibiyar 'yan mata masu tashe ko kuma karuwai a gari. Daga bisani idan ya ga dama sai ya kara aure ko kuma ya saki ta gidan saboda ba zai iya rike mata biyu ba.

Maza masu tarin yawa suna da kyankyami ta yadda basu iya cin abincin kazaman mata marasa gyara jikinsu. 

Namiji mai imani da son matar shi ne yake iya zaunar da mace ya sanar da ita matsalarta don ta gyara. Wani kuwa sai dai ya kyaleta shi kuwa ya nema wa kan shi mafita.

Idan kazantar mace ta kai ta kawo, gashin kanta, fatarta da dukkan jikinta babu mai iya rabarta. 

Mijinta baya iya zuwa kusa da ita ballantana a kai ga auratayya tsakaninsu. Amma abinda zai ba mutane mamaki shine yadda matan ke cin gayu tare da gyara jikinsu matukar zasu fita anguwa.
Wadannan matsalolin na sa mace ta tsufa cikin lokaci kankani kuma yana kashe aure. 

Abin mamakin kuwa shine yadda suke komawa mata masu kula da jikinsu bayan sun koma gidan iyayensu. Daga nan wani ya dauka ya aura bai san matsalar kazanta ba ce ta hana ta zaman gidan mijin.

Gareku mata,a dage da gyara jiki da tsafta komai yawan yara. Tsakanin kazanta da tsafta mintoci kadan ne ko sa'o'in kadan. Sa'a uku kacal zasu isa mace ta gyara jikinta da dakinta tare da yaranta. Kuiya da lalaci kuwa basu barin wasu matan, kamar yadda jaridar Leadership Hausa ta ruwaito.
Share:

YADDA AKE HAƊIN RUWAN RAKE DOMIN ƘARIN NI'IMA


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Yadda Ake Hadin Ruwan Rake Don Samun Ni'ima Da Nishadi Lokacin Saduwa_*

Zaki nemi kayan hadin kamar haka;
* Ruwan rake
* Kankana
* Garin kanunfari
* Zuma
*Bayani;* Zaki samu ruwan rakenki mai kyau sai ki kawo yankakken kananarki sai ki sa a blenda ki zuba ruwan raken nan a cikin blenda ki markada sai ki zuba garin kanunfari idan ya jiku sai ki tace ki zuba zuma ki dunga sha.


WabillahinTaufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*


*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a shiga ta wannan link din* 👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/CzHKa3hRV7DDAAqmz8T1WZ
Share:

IDAN KIN GYARU...


*🌴IDAN KIN GYÃRU🌴*
                *To dukkan al’umma*
                                 *🌴TÃ GYÃRU🌴*

*Laifi na sittin ɗaya (61): Karya murya da rangwaɗa ga maza waɗanda ba muharramai ba:*

👉🏼 Yin ƙasa-ƙasa da murya da rangwaɗa ga maza waɗanda suke ba muharramai ba hakan haramun ne, kuma ana yawan yin hakan musamman idan ana waya!

📚 Allah (SWT) yana faɗa game da mãtan babban gida iyãyen muminai cikin Suratul Ahzãb ãya ta(32) cewa: ((Yã mãtan Annabi! Ba ku zama kamar kõwa ba daga mãtã, idan kunyi taƙawa, sabõda haka, kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cuta a cikin zuciyarsa ya yi tammani, kuma ku faɗi magana ta alheri)).

👉🏼 Wannan fa an faɗã ne ga mãtan Annabi (SAW)! To, ina kuma ga wasu mãtan da ba su kaisu a tsoron Allah ba!kuma ba su kaisu matsayi a duniya da lãhira ba!

✍🏼 Sannan kuma ki sani ya ke ‘yar uwa karya murya hanya ce da take kaiwa ga zina!

📚 Allah (SWT) yana faɗa cikin Suratul Isrã’ ãya ta (32) cewa: ((Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã munãna ga zama hanya)).

📚 Kuma Allah (SWT) yana faɗa cikin Suratut Nur ãya ta (30-31) cewa: ((Ka ce wa muminai maza su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjojinsu. Wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da suke sanã’antãwa().

📚 Kuma ka ce wa muminai mãtã su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjojinsu, kuma kada su bayyana ƙawarsu face abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su doka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu…)).

Kasance da mu a Facebook 👇🏼
-https://www.facebook.com/102613724899406?referrer=whatsapp

Ko a Telegram 👇🏼
https://t.me/AbbaLHassan

*📝Abba Lawan Hassan {Abu Aysha}.*
Share:

GUDUNMUWAR ILIMIN 'YA'YA MATA GA YANKIN AREWA 2

Arewa students orientation Forum!!!


"GUDUNMUWAR ILIMIN 'YA'YA MATA GA YANKIN AREWA"


Kashi na biyu(2)

•Tarihin Ilimin 'Ya'ya Mata a Nigeria

•Tarihin Ilimin' Ya'ya Mata a Yankin Arewa.

Fatima Umar Muhammad
Arewastf@gmail.com
_______________________________________________________

✔️Tarihin Ilimin 'Ya'ya mata a Nigeria.


Kafin nayi bayani akan gudunmuwar Ilimin 'ya'ya mata ga yankin Arewa akwai bukatar mu kalli shi karan kanshi tarihin Ilimin 'ya'ya matan dan ya haska mana ta yadda zamu fahimci gudunmuwar.

Ilimin 'ya'ya mata a Nigeria zamu iya cewa ya fara ne tun a Shekarar 1920 inda a lokacin muke da makarantun Primary Dana Secondary guda 25, Kuma uku ne kacal suke na mata zallah, sauran kuma duk na maza ne, a Shekarar 1949 Makarantun da aka warewa mata suka kai guda 8, a yayin da 49 suke na maza, kana, a Shekarar 1960 aka kara samarwa da matan makarantu guda 6, sai ya zama jimillar makarantun mata a wannan lokacin sun kai 14.
Duka Wadannan Makarantun suna karkashin kulawar Kungiyoyin Mishan ne (Missionaries Organization) da kuma turawan mulkin mallaka na Ingila (England Colonial Masters).

Bayan da Nijeriya ta samu 'yancin kai (Independence) a Shekarar 1960, gwamnatin tarayya ta bude Jami'o'i 5 da suka hada da:
1• Jami'ar Nsukka (1960)
2• Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria (1962)
3• Jami'ar Ile-ife (1962)
4• Jami'ar Legas (1962)
5• Jami'ar Ibadan (Wadda aka fara kafa ta tun a Shekarar 1948).

✔️Tarihin Ilimin 'Ya'ya mata a Yankin Arewa

Nijeriya kasa ce da ke da mabiya addinai daban daban, (Secular State) manyan cikin su su ne: Musulunci da kiristanci, wanda dadaddun addinai ne a Nijeriya.
Kuma tun daga wannan lokaci ake samun hanyoyin ilmantar da jama'a.
Alal misali: tun a karni na 14, (14th Century) lokacin da musulunci ya shigo arewacin kasar (Northern Region) ake koyar da jama'a harshen larabci ta yadda zasu iya karatun al-qur'ani da sauran ilimomin addinin Musulunci (Islamic Educations).

Wannan ya nuna cewa Ilimin Arabia (Arabic/Islamic Education) ya riga ilmin boko (Western Education) shigowa Najeriya.

A shekarar 1934 a lokacin Sarkin Kano Abdullahi Bayero aka fara gina makarantar koyon harshen larabci (Arabic School) a Kano, inda ake koyar da shari'ar musulunci (Islamic Law) da kuma yaren turanci (English Language) da lissafi (Mathematics).
Makarantar ta bunkasa sosai inda a yau ita ne ta rikide ta zama Jami'ar Bayero (Bayero University, Kano).
An kiyasce cewa a shekarar 1914 akwai makarantun
Arabiyya kimanin dubu ashirin da biyar (25,000) a fadin arewacin Najeriya.

✔️ILIMIN BOKO✔️

Ilimin Boko (Western Education) ya shigo Nijeriya ne lokacin da kungiyoyin mishan suka shiga kasar a tsakanin shekarar 1842 zuwa 1914.
Tun daga wannan lokacin aka gina makarantu ana daukar yara domin a basu ilimin bokon.

Suna koyar da darrusa 4 da suka hadar da: 
-karatu (Reading Skills)
-Rubutu (Writing Skills)
-Lissafi (Arithmetic) da
-Kiristanci (Christian Religious).
Sannan akan horar dasu ta yadda zasu samu aikin yi
kamar: Koyarwa (Teaching) wa'azi a masalattai da coci-coci (Preaching) da tafinta (Intermediary).
Sai dai Ilimin bokon bai samu karbuwa a arewacin Najeriya ba sosai a wancan lokacin, sakamakon tasirin da ilimin addinin musulunci yayi ga mutanen yankin, kuma su kayi amannar cewa Ilimin bokon zai gurbata masu addinin su.
Duk da dai tarihi ya nuna cewa da karfin tsiya aka rika kama mutane ana kaisu makarantun bokon da Kuma bayi (Slaveries) da ake turawa suna yin bokon.
Idan ana maganar ilimin 'ya'ya mata a arewacin Najeriya Kamar yadda muka fada a sama,tarihi ya nuna cewa an
fuskanci manya-manyan kalubale da suka hana a bai wa mata damar neman ilimin boko, wanda namijin ma ba'a bashi damar neman Ilimin ba bare kuma mace. Kai bama ilimin boko ba har na Addini mata basu samu damar neman sa ba yadda ya kamata, har takai ana yi masu take da cewa “Sabbi saukar Mata” Wato da sun kai Suratul-A'ala Shikenan sun bar karatu da neman ilimi. A wancan lokacin an fi mayar da hankali ne kawai wajen ganin an aurar dasu da zarar sun fara tasawa.
Kalilan ne suka samu damar kammala makarantar firamare ko sakandire, yayin da tsirarru suka je jami'a,amma suma yawanci daga dakin aurensu.


NB. Asof bata kar6ar kudin kowa gun wani ko Kuma a turamaku wani links. 

02/02/2020.
Share:

NEMAN RA'AYIN BAZAWARA KAFIN A AURAR DA ITA


*NEMAN RA'AYIN BAZAWARA KAFIN A AURAR DA ITA.*
.

Sheikh Solih bin Fauzan Al-Fauzan ya faďi a cikin littafinsa na
تنبيهات على أحكام تختص بالمؤمنات:

Bazawara kuwa ba a aurar da ita sai da izininta, kuma izininta shi ne ta fada da bakinta, sa6anin budurwa da aka sanya shirunta ya zama izininta. Ibnu Kudamah ya ce a cikin Al-Mugni (6/493):

Ba mu san wani sabani ba tsakanin malamai cewa izinin bazawara shi ne magana da bakinta, saboda hadisin da ya zo; kuma saboda harshe shi ne mai fadar abin da ke cikin zuciya, kuma da shi ake lura a ko ina aka ce a nemi izini.
.
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyya, Allah Ya ji kansa, ya ce a cikin Majmu'ul Fatawa (32/39-40):

Mace bai kamata wani ya aurar da ita ba ba tare da izininta ba, kamar yadda Annabi (ﷺ) ya yi umarni. Idan ta qi, to ba za a tilasta ta ta yi aure ba, sai dai yarinya karama (da ba ta kai munzalin balaga ba); ita ubanta yana da damar ya aurar da ita. Ita babu izini a gare ta. Amma bazawara wadda ta balaga, be halatta a aurar da ita ba tare da izininta ba; bai halatta ba ga uba, ko ga waninsa. Wannan kuwa ijma'in musulmi ne. Hakanan budurwa da ta balaga bai halatta ga wani in ba uba ko kaka ba, ya aurar da ita ba da izininta ba. Shi ma wannan ijma'in musulmi ne. Amma uba da kaka, su ya kamata gare su su nemi izininta. Kuma malamai sun yi sabani shin neman izinin nata gare su wajibi ne, ko Mustahabbi ne? Ingantacciyar magana ita ce cewa wajibi ne. Kuma wajibi ne ga waliyin mace ya ji tsoron Allah wajen wanda zai aurar da ita gare shi. Kuma lallai ya duba mijin shin ya dace da matsayinta ko bai dace ba; domin an sa shi ne ya aurar da ita don maslaharta, ba don maslahar kansa ba.
.

Wannan shi ne matsayar shari'a game da aurar da mace bazawara. Allah Ya sa mu dace.
.

*📚Irshadul Ummah.*
WhatsApp: 08166650256.
Share:

YADDA AKE GYARAN NONO IDAN ZA A YAYE YARO

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*


*_Yadda Ake Gyaran Nono Idan Za'a Yaye Yaro_*

Zaki nemi kayan hadi kamar haka;
* Garin farar shinkafa
* Garin alkama
* Garin habbatus sauda 
* Garin ayaba (platain)
* Gyada mai malfa (mai zabo)
* Aya
* Zuma
* Madara
*Bayani;* Zaki samu dukkan garinki sai ki hada da aya da gyada sai ki markada sai ki tace sai ki dora ruwan akan wuta sai ki zuba zuma da madara sai ki dama har yayi kauri sai ki dunga sha, safe da yamma, zaki yi wannan hadin in kina saura sati biyu kiyi yaye.


Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*


*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a shiga ta wannan link din* 👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/CzHKa3hRV7DDAAqmz8T1WZ


Share:

HAƊIN MADARA MAI SA NISHAƊI


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Yadda Ake Hadin Madara Mai Sa Mace Nishadi Lokacin Saduwa_*

Zaki nemi kayan hadi kamar haka;
* Madarar ruwa ko na shanu
* Abarba 1 
* Sugar 
* Flavour (na abarba)
*Bayani;* Zaki fere abarbanki, ki yanka, ki zuba a blanda ki markada, Idan yayi sai ki tace ki zuba abu mai kyau, ki zuba madara da yawa sai ki sa sugar da flavour, sai ki juya sosai, anan sai ki dandana, idan yayi ki sa a firinji yayi sanyi, sai ki dunga sha.Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*
Share:

GYARAN NONO DON ƘARA KYAU DA KINTSUWA

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*


*_Yadda Ake Gyara Nono Don Kara Kyau Da Kintsuwa_*

Zaki samu kayan hadi kamar haka;
* Albasa 
* Zuma
* Garin gero
* Madara peak
*Bayani;* Zaki samu albasa ki yankata sannan ki
dafata har sai ruwan yayi baki, sai ki sauke ki zuba zuma ludayi daya da garin gero ludayi
daya, sannan ki xuba madara paek sai ki dunga sha da dumi, na tsawon kwana goma sha tara (19).


Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*

Share:

BUDURCI NA 29

_*======BUDURCI NA=====*_

*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*

*Fitowa ta daya=*{29}

*Tambayar Yammata* 

1=Slm Malam Barka da war haka ina godiya da fada karwa da kake mana kuma muna Karuwa Sosai tambaya na Malam shine ina da Saurayi muna so yayya dashi kuma gaskiya ina sonshi Amma yace inde ina san shi dole na bari yarika taba jikina idan muna zan ce nikuma malam Ina tsoron sabawa Allah kuma gaskiya ina son shi banaso narasa shi to malam ya zanyi? Ina fatan za'a amsa min baza'a shareniba, Nagode.

2=Salamu alaika dafatan Malam yana cikin koshin lafiya Allah yasa haka Amin
Ni dalibace da cikin miftahul ilim malam ni mace ne mai yawan sha'awa kuma gashi mahaifina yaki yi min aure wai se na gama karatu gashi har nakai 34 years banyi aureba kuma inason auren gashi duk Samari na babana ya koresu bawan da yake zuwa gurina yanzu, toh Malam ko ya hallatta narika biya wa kaina bukata ta sha'awa Dan gudun karna fada cikin zina?

Kuma Dan Allah Malam ayiwa iyayen mu wa'azi suna aurar damu kafin mutsufa agida Dan Allah Malam ate maka.

3=Salam malan inada tambaya kamar haka toh Malam mu mata ya zamu gane Shima wan nan namijin baitaba Neman mataba kafin aurensa ko su maza Basu da wata sheda da ake gane su?

4=As'salamu Alaikum Warahmatullah
Malam Allah yasaka da Alkhairi gaskiya muna Jin dadin wan nan Darasi kuma Malam ga tambaya ta Shin ya mace zata gane wan nan namijin nagarine kuma aure yazo ba yaudara ba?

5=aslm malan ina wuni da fatan kana lafiya Dan Allah Malam ko ya hallatta mace taga mutum kamar de wani namiji haka taji tana son shi ta gayamasa ko ta aika agaya masa tana son shi,
Tambaya ta biyu ko akwai wasu wanda kasani mutanen kirki wanda suke son aure kamar bazawara ko budurwa?
Nagode Malam Allah yabaka abinda kakeso na Alkhaiyri duniya da lahira Amin,

Wadan nan sune kadan daga cikin irin tamyoyin da nake samu yau da gobe daga gurin yammata dama wasun su danjin amsa>>>

_*Muhadu agaba insha Allah,*_

*GABATARWA Miftahul ilmi*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248

Share:

BUDURCI NA 28

_*======BUDURCI NA=====*_

*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*

*Fitowa ta daya=*{28}

*Samari ko matasa,*

Inada budurwa kuma Munda de da ita har mun shaqu Sosai Amma sheidan yayi galaba akanmu musan juna awaje kuma bamuyi aureba har tasamu ciki gashi kuma ni inaso nayi aure Amma bazan iya aurarrta ba saboda batada tarbiyya toh yaya zanyi ?

Aslm mlm ya kake dafatan kana lpy ina daga cikin wanda ya ke bi biyan karatunka mlm ina da budurwa mun shaku sosae akalla munkai shekara 8 da ita kuma tana sona ina sonta sosae saodai soyayyan da takemin yasa harga tace min in sumbaceta amma naki itakuma ta sumbacen yanxu abunda nake gayamaka mlm har ciki nayi mata kuma wlh ha yanxu inasonta amma saitaba da aurenta ga wani bayan sallah za ayi toh yanxu mlm tana da haqqi akaina sanan nadaina kusantar ta yanxu wace hanya zanbi na gyara rayuwata?

*Amsa*

Toh Dan Uwa yakamata kasani duk duniya ayanxu Babu wanda yadace ya aureta sama dakai dalili kuwa shine tare kuka Aikata laifin kuma Tare kuka tuba kuma kafi kowa sanin halinta idan har ta tuba da gaske kasani idan ma bata tuba ba kasani kuma Kaine namiji kai zaka Kula da ita san nan zaka bata duk wani goyon baya da gudunmawa Dan tazama takwarai inde da gaske kun tuban,

San kasani ita nutsuwa Allah ne k bada ita idan har kun tuba dagaske tuba tabba taccen tuba toh Allah zai sa Albarka cikin auren Ku kuma yabaku cikakkiyar nutsuwa domin dama laifin shi kuka yiwa kuma kun tuba Dan haka zai kawar muku da duk wani shakku ko zargi tsakanin Ku ,

Kasani Karuwa tana tuba kuma Allah ya karba tubanta yabata miji kuma yasan da karuwace Amma se yamanta da wan nan aikin ta na baya saboda aikin Alkhayrin ta nayanxu,

Idan kuma kace bazaka aureta ba toh kasani zata iya fadawa cikin gararin rayuwa kuma Kaine Sila tayu ta fada Aikata karuwanci kuma kana da kaso mai tsoka Dan haka kacika aikin ka na Alkhayri da ka dauko yanxu,

*Amsa ta biyu*

Yadda zaka gyara rayuwarka shine katuba Kabar sabon kuma kayira istigfar akan wanda kayi abaya kuma tunda tasamu wanda zai aureta Shikenan kafita harkarta karka sake dawowa har abada insha Allah rayuwaku zata yi kyau,

 _*Muhadu agaba insha Allah,*_


_*GABATARWA Miftahul ilmi*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248

Share:

BUDURCI NA 27


_*======BUDURCI NA=====*_

*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*

*Fitowa ta daya=*{27}

Alhamdu-lillah hamdan kasiran 

Godiya ta tabbata ga *Allah* (Subhanahu wata'ala) daya bamu ikon kammala wan nan Darasi mai taken *budurcina abin alfahrina*
Muna rokon Allah da yasa abinda muka karanta ciki na kwarai Allah yabamu ikon Aikata shi wanda yake bana kwarai ba Allah yabamu ikon kaucewa daga Aikata shi,

Bashakka wan nan Darasi akwai abin lura aciki daya kama daga kan iyaye da ya yaye da kuma matasa maza da mata, wan nan Darasi lalle yataba kowane Ban gare na Al'umma sede fatan Allah yabamu ikon gyarawa,

Kasan cewar duk lokacin da akasa wani Darasi da ya shafi rayuwar Al'umma zakaji mutane suna aiko da tambayoyi ta kowane bangare iyaye da yammata da kuma Samari ,
Toh saboda karanci lokaci da kuma yawan tambayoyi zan amsawa ko wane bangare tambaya daya,

*Zan fara takan Samari*
 suna tambaya ne kan ya za'a yi sugane cewa wan nan budurwar mace ce kamila wadda ta amsa sunanta budurwa lokacin da zasuyi aure?

Abinda suke nufi shine bata taba saduwa da waniba kafin aurenta nafari,

Toh wan nan amsace mai sauki kuma Saukin fahimta idan kana so kasan wan wan nan yarinya bata taba saduwa da waniba toh koma kanka kabinciki kanka tsakanin ka da Allah baka taba saduwa da wata Budurwa ba wadda ba ita zaka auraba?

Idan har baka taba ba toh ka kwantar da hankalinka Allah bazai baka wadda wani yasadu da itaba saboda hukuncin *aljazã'u min jinsil amal*
Kowane aiki yanada Saka mako idan ko ka tabayi kadena Amma ba tuba kayiba toh yanxu katuba kanemi gafarar Allah zai yafema maka kuma yabaka tagari,
Saboda duk lefin da mutum ya Aikata komai dadewar sa da yatuba Allah zai yafe masa duk girman laifi,

Idan ko kana cikin yine yanxu haka toh ba'a yiwa Allah wayo kana lalata matan wasu kace kai baza'a lalata takaba kaima ka yaudari kanka, abinda za'a yi shine yanxu katuba kuma tuba tabba tacce wanda bazaka koma Aikata Wan nan sabonba ,
Saboda fadin Allah duk wanda yaji tsoron Allah toh Allah zai bashi mafita kenan zai baka mata tagari sharadin shine kaji tsoron Allah katuba kadena,

_*Muhadu agaba insha Allah,*_


_*GABATARWA Miftahul ilmi*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Share:

BUDURCI NA 26

_*======BUDURCI NA=====*_

*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*

*Fitowa ta daya=*{26}


_*BUDURCI NA WUCCIN GADI*_

 *(ARTIFICIAL VIRGINITY HYMEN)*

Da akwai Wani Budurci na Wucin Gadi da Ya Shigo Nigeria tun Kusan Shekarar 2015, ta Inda Idan Macce ta Rasa Budurcin ta a Waje Idan zatayi aure sai ta saye shi ta sanya (ta yanda Za a yiwa Mijin Basaja),
 kuma Alhamdulillahi Mun fad'akar a wancen lokaci game da Wannan Budurci.

Sai dai kuma yanzu abin ya k'ara ha6aka ta In da Suke da Web Site Wanda Idan Mace tana buk'atar Wannan Budurci zasu Iya samunta duk In da take a Nigeria su kai mata shi tare da koyar da Ita yanda ake amfani da shi

*HYMEN*
a turance wata fatace datake gaban mata dab da cervix, a hausance tana daukan sunan *BUDURCI,* 
kuma rashin (wannan fatar shine rashin budurci).

Fatar bata da karfi sosai domin ruwa kan iya wucewa ta cikinta, wannan fatar tana dauke Da kananan hanyoyi na jini, shiyasa fashewa ko tsagewarta kansa jini ya fita.

Mafi akasari wannan fata kan tsage ne idan daya daga cikin wadannan abubuwa ukku 3 suka faru ga mace,

1. Idan an sadu da mace
(wanda ake kira copulation a turance)

2. Wajen neman fitar da sha'awa da wani abu mai karfi ko yatsa *(vaginalinsertion*
             or
*mastubation)*

3.Yawan tsalle ko hawa mashin, keke, doki ko jaki Duk sukan iya fashe wannan fatar.

Kasancewa mafi yawan Maza kanyi amfani da fashewar wannan fata da fitar jini wajen gwada budurcin 'Ya mace don tabbatarwa bata ta6a saduwa da ko wani namiji ba,

Sai turawa suka zauna sukayi nazarin yin Jabun wannan Fatar 
*(mai suna Artificial Virginity Hymen)*

 domin matan da suka rasa budurci kafin Aure

Shi wannan
FAKE HYMEN roba ce da akayita da sinadare masu narkewa dazai dace da jikin mutum *(prosthetic in nature)*
yanda idan macen da ta rasa budurcinta tasa shi zai zauna daidai gurbin ta,

 sannan da zarar ta sadu da angonta wani jan sinadari zai fashe daga cikin *Artificial Virginity Hymen* din mai kama da jini,
toh dazarar ango yaga haka sai ya zaci matar sa budurwa ya aureta,

Babu shakkah akwai abubuwanda ya kamata mata su kula da su game da wannan Fake *Hymen* din.

Kasancewar bayan saduwa fake hymen zai iya fitowa, in kuma bai fito ba zai iya narkewa a cikin gaban mace, 
don haka zai iya kawo matsalolin lafiya ga macen datayi amfani dashi

Haka zalika jan ruwan da wannan FAKE HYMEN din ke fitarwa mai kama da jini,
shima zai iya canza ka'idar tsaftar gaban mace, saboda cikinsa akwai *(chemicals)*
masu dauke da kalar JA, don haka wannan abin zai iya kawo matsaloli kamar haka:

Yana canza yanayin sinadaran dake kiyaye al'aurar Macce daga kamuwa da cutukka. Yana iya kawo cutar
*(cancer of vagina)*
 Yana toshe mahaifa akasa samun haihuwa Yana canza tsarin hailar mace (ta yanda hailar zata rikice.

Sannan dadin-dad'awa wannan fake Hymen din Yana kawo rashin haihuwa *(infertility)*
ga mazan da sukayi amfani da wacce ta sanya shi.

Don haka yana da matuk'ar kyau matayenmu su guji yin Amfani da Wannan Fake Hymen din.

Sannan Yana da Kyau Malamai su tashi tsaye Wajen Yin fad'akarwa akan Cewa,
Rashin Ganin Jini a lokacin Saduwa da Mace da Angonta ba shike nuna ta yi amfani da wani a waje ba

Sannan Muma Maza Mu san Cewa,
Ganin Jini a daren Farko bashi ke Nuna Cewa Macce ba 'yar Iska bace, Domin Mu samu matayen mu hankalinsu ya kwanta kar su kai kawunansu ga Halaka.

Mu san Cewa, Tsallaka Rami ko Hawa Keke,
ko Hawa babur kad'ai na iya Farke wannan Hymen din, don ba dole sai Macce ta sadu da Namiji ne kadai hanyar Rasa Budurcin ta ba.

Kai Hatta dogon Numfashi Mai Karfi Idan macce tayi Shi Zai iya sanya tayi hasarar wannan Budurcin, a likitance ma an gano cewa, akwai matan da basu da ma shi kwata kwata. Don haka mu tashi tsaye domin yak'ar wayannan yahudawa da suke yak'ar mu a b'oye.

Mai Aikata Alkheri Yafi Alkheri Alkheri a Cikin Al'ummah.

Allah Ka shiryar damu
_*Muhadu agaba insha Allah,*_


_*GABATARWA Miftahul ilmi*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248

Share:

BUDURCI NA 9

_*======BUDURCI NA=====*_

*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*

Fitowa ta daya=*{9}*

Sai kuma wata tambayar tayaya mace zata gane tana bude wato budurcin ta ya kau?

Wannan kuma zamu duba bayanai da masana sukayi akan budurcin mace kamar yanda wani marubuci dan kasar india ke cewa alamomi hudu sune suke nuna gaban mace ya bude koda na miji be sadu da itaba,

1=akwai fitar iska me kamada tusa ta gabanta,

2=yatsar mace ta tsakiya wato ta kusada manuniya ta shiga gabanta ba tareda taji zafiba,

3=mace ta tsuguna babu wando amma taji iska yana shiga jikinta,

4=mace taga jini tareda zafi kuma ba lokacin al’adaba misali ko tana tsallaka wani abu makamancin haka,

Muhadu agaba insha Allah,
Rubutawa✍🏼
Dr. Auwal Azare

*GABATARWA Miftahul ilmi*

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248

Share:

BUDURCI NA 25

_*======BUDURCI NA=====*_

*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*

*Fitowa ta daya=*{25}

Maganar gaskiya Samari ko mazan wan zamanin sunfi kowa laifi cikin wan nan lamari saboda sude iyaye sunyi iya lakarinsu na bawa yayansu tarbiyya haka suma yaran suna kokari wajen Kare kansu zuwa ga fadawa han nun mayaudaran Samari Amma kash se ayi rashin sa'a su tsinci kansu a hannun wadan nan mayaudaran,
 
Zakaga wanima ba yaro bane yagirma wanda ba'a sa ran samun wasa ko wata karamar magana daga gareshi Amma seka sameshi da zuciya irin tayara da yaudarar yammata,

Sukuma saboda suna saurin aminci da yarda da wanda suke so ga kuma karamin tunani ga kuma kwadayin abin duniya se yakasance duk tarbiyyar da tasamu agidan su wan yazo ya rusata lokaci daya kafin ka Ankara ya gama da ita ya lalata mata rayuwa kuma yagudu ya barta,

Zaka gansu suna da ladabi da nutsuwa idan sunje gaban iyayen yarinya- ga zakin baki da iya magana wanda duk yarinyar da sukasa agaba toh sede Allah ya kwaceta,

Toh daga nan ne idan yarinya tafarga komai ya kure mata yanzu aure takeso toh seta fara tunanin koma waye yazo Ade rufawa juna asiri bayan ta makara,
Toh idan tasamu mijin aure seta tuna yanxufa ita ba budurwa bace kuma bata taba aureba, toh yaza'ayi kar mijin yagane ita ba budurwa bace awan nan lokacin hankalinta zai tashi matuqar tashi tafara neman maganin dawo da Budurcin wanda kuma hakan bazai taba yiwuwa ba,

Wasuma suje gurin bakaye ko miyagun malamai wai abasu wani hadi da zaisa mijin bazai gane su ba budurwa ye bane,
Wan yasa takai ga mata suna Amfani da wani abu ko wani sinadari ko roba wadda take maye musu gurbin budurcin na dan wani lokaci batareda tunanin yin hakan ha'intar mijine kuma cutar da lafiyarsune ba.

_*Muhadu agaba insha Allah,*_


_*GABATARWA Miftahul ilmi*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248

Share:

BUDURCI NA 24


_*======BUDURCI NA=====*_

*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*

*Fitowa ta daya=*{24}

Abin mamaki da takaici ne kaga yarinya mai hankali da tarbiyya agidan su kaga tana Kula irin wadan mazan wadanda burin sulalata rayuwar yarinya subar ta da cizon yatsa kuma kaga har suna alfahari da yin hakan kai kadauka ba mace bace ta haifesu ko ta renesu,

A irin wan nan halin ne zakaga mutum mai mutunci da kima yaga yarin yana sonta da aure Amma saboda bashi da irin wan nan dabi'a sekaga tajuya masa baya wai shi bai waye ba saboda baya kai hannunsa jikin ta tana ganin shi bagidajene ko kuma tace ai shi ustazune ita kuma holewa take da bukata,

Daga nan idan akayi rashin sa'a sheidan yayi nasara akansa shikenan se ya biye mata suyi ta lalatar su awaje suko iyaye Basu saniba,

Wallahi akwai wanda ya min da tambaya wai yanada budurwa kuma sun shaku Sosai har takai ga yayi mata ciki awaje Amma anzubar da cikin toh yan sun tuba kuma ita tace lalle shi takeso ta aura shikuma yana ganin bai kamata ya auri yar iskaba wadda ta bayar da kanta gareshi tun awaje Dan haka shi yanaso ya auri mace tagarine,

Tam bayarsa shine wai yanxu idan yaki aurenta yayi laifi a gurin Allah?
Alokacin naji arainã inama yana kusa Dani ne ba awaya yake min wan tambayar ba naji kamar innemi inda yake nasa akamashi Amma sena tuna ai yace yatuba kuma tuba yana goge duk wani zunubi da bawa ya Aikata matuqar ba shirka yamutu akaiba,

Amma Dan Allah kujifa shi yalalata mata rayuwa kuma yanzu yanaso yasamu mafaka a shari'a yagudu yabarta ko wayakeso ya aureta?

Niko na ta qar Qare nabashi amsa de de ta tambayar sa dakuma nuna masa irin muni aikin da yayi da cin amanar Allah da manzon sa da iyayen yarinyar da yayan da zata Haifa da danginta da sauran musulmi da musulunci,

*Ya Allah muna rokon ka da ka Kare mana mutuncin Dana iyalenmu da sauran Al'ummar musulmi kasa Mufi karfin sheidan*

_*Allahumma Ameen yãhayyu-yãQayyum*_
🤲🏼🤲🏼🤲🏼

_*Muhadu agaba insha Allah,*_


_*GABATARWA Miftahul ilmi*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Share:

BUDURCI NA 23

_*======BUDURCI NA=====*_

*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*

*Fitowa ta daya=*{23}

Yãku iyaye muji tsoron Allah musani fa sufa yaya Amanace Allah yabamu kuma ba makawa zai tambaye mu akansu idan mun sauke nauyin dake kanmu munrike amanar mun tsira idan ko mukayi sakaci muka barta talalace toh Wallahi mun halaka, yana da kyau musani yadda muke da haqqi akan su suyi mana biyayya haka suma suna da haqqi dole mu kyautata musu mu inganta rayuwarsu mukula da tarbisu,

Toh lalle matan wan nan zamanin dayawa daga cikin su sune ke lalata kansu da kansu tun gabannin suje gidan mijin su, bashakka nace yammatan yanxu suna kwakkwarar gudunmawa waje bata rayuwarsu awaje kafin suje gidan aure,

Dalili akan haka zakaga yarinya takai she karun aure kuma tanada lafiyar da zata iya yin aure Amma sekaganta Babu tsa yayyen namiji da zai aureta, sabo ta dauki buri ta dorawa kanta wai ita lalle se me gida da mota koma de wani ham shaki ko Masha huri wanda kowa ya sanshi agari, lokacin da Namiji mai mutunci da kima yaganta yaji yana sonta da aure toh alokacin ita kuma zata daura damarar cin mutunci da wulakanci gareshi saboda kawai yaganta yanaso bashi da ko sisi,

Toh ta haka wasu Samari marasa mutunci da tsoron Allah zasuzo gurin ta suyita kashe mata kudi ita da iya yenta kowa na murna ai wance tasamu miji tayi arxikin shiko gogan naka yanada wata boyayyar manufa aranshi yanata lallabata har seta saki jiki dashi tanaganin sun zama daya seta sakar masa jiki yayi duk abinda yaga dama da ita,

 daga nan seki ga yafara canxa wa yafara Jan kafa yau yazo gobe shiru idan kin kira shi yace wani uzurine,

 Dagan nan se ya Dena daukar wayar ki ke da kanki zaki yankewa kanki hukunci Wan nan fa yadena Sona ke ma kingane, 
da kin matsa masa yace shifa bazai iya auren yar iskaba,

 bayan kuma duk Samari masu mutunci sun manta dake sunyi aurensu kuma suna zaune lafiya da matansu,
ga kuma shekarun ki sunfara ja dan kin Wace ashirin da biyar .

_*Muhadu agaba insha Allah,*_


_*GABATARWA Miftahul ilmi*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248

Share:

BUDURCI NA 22


_*======BUDURCI NA=====*_

*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*

*Fitowa ta daya=*{22}

Kamar yadda mukace iyaye suna bada gudunmawa wajen lalacewar tarbiyya yaransu, San nan mukace suma yammata suna da nasu gudunmawa wajen bata rayuwar su awaje tun kafin suje gidan mazajensu,

Toh koshakka babu Samari suma nada tasu gudunmawa kuma mai tasirin gaske wanda kusa tafi ta dukkan iyaye da yayan wajen lalata tarbiyya,

1=dalili akan iyaye yakamata duk wata uwa ko wani Uba yasan cewa akwai haqqin da Allah ya Dora musu akansu na yayan su wajen Kula da tarbiyar su da lafiyar su da duk wasu bukatu nasu, kash Amma ba duka iyayene suka san hakaba,

Su sun dauka kawai suhaifi yara subasu abinci da sutura da sasu makaranta shikenan sun sauke duk wani nauyi ko haqqin dake kansu bawani saura ko kadan,

Lalle duk iyaye idan yaransu suna Jin yunwa hankalin su yana tashi se sunga sun ne momusu abinci sunci san nan hankalinsu yakwanta haka idan yaran basuda sutura tufafi zakaga iyaye sun tashi tsaye wajen nemuwa yaran su tufafi har se sunga sun tufatu san nan su Sami gurin zama,

Haka idan yaran basa zuwa makaranta zasuyi duk yadda zasuyi wajen sunkaisu makaranta san su sudawo gida suyi bacci,
San nan idan yaran ba lafiya zasu biya ko nawane kudin magani Dan de yaran su Sami lafiya san su iyayen suji dadi aransu,

Yãku iyaye Allah yasaka muku da Alkhayri yakarbi wan nan aiki naku yasu muku cikin mizani yasa Ku amfana dashi tun aduniya,

Amma tambaya ta daya itace Dan Allah kun taba tunanin cewa yayanku sunada wata bukata wadda Allah ya haliccesu akanta daku kanku kuma bazaku iya biya musu itaba bazakuma suiya gaya muku itaba?
Kutuna yadda kukejin taku bukatar idan ta motsa muku yakukeji toh sumafa mutane ne kuma suna da wan nan bukatar da kuke da ita wata kilama tasu tafi taku Amma se kukace A'a

Ya kuke gani idan ba'a samu tsoron Allah azuciyarsu ba Kokuma sheidan yayi musu busa acin zuciya?

_*Muhadu agaba insha Allah,*_


_*GABATARWA Miftahul ilmi*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Share:

BUDURCI NA 21


_*======BUDURCI NA=====*_

*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*

*Fitowa ta daya=*{21}

Azahirin gaskiya iyaye suna taka muhimmiyar rawa wajen kawar da Budurcin yayan su mata, Kode ahalin rashin sanin Addini ko Kokuma ahalin rashin gogewa arayuwa koma muce wasu ahalin san duniya da rudin sheidan,

Zakqga yarinya ta isa aure kuma ta nuna tana son auren san nan tasamu wanda zai aureta Amma iyayenta se sukafe kai da fata su bazasu Aurar da itaba yanxu wai se tayi karatun boko koda kuwa wanda zai aureta yanada halin Kula da ita dede gwar gwado 

Sekaji iyaye nacewa ai idan yamutu ko yasaketa tana da madafa da zata kula da kanta sabo shi uban yagaji da Kula da ita so yake tazama itace mai Kula da kanta, yamanta cewa Shima dayake daukan nauyin nata bashi ya halicceta ba kuma arzikinta ba'a hannunsa yakeba,

Wasu iyayen kuma Dan kwadayin abinda yar tasu take kawo wane yasa bayason tayi aure saboda tunaninsa in tayi aure bazata ci gaba da bashi wan nan *darham* dinba,
Sun manta da cewa tun kafi su haifeta suna ci suna Sha suna sa sutura kuma ma sune suka reneta da babun nasu har ta girma san nan kuma suka manta wanda ya kula dasu da ita tun kafin tasan kanta,

Wasu iyayen kuma Basu da halin hidimane da zasuyi wajen bikin dan haka sun dorawa kansu abinda bazasu iyaba sunce dole se sunyi, akan haka gara sufasa Aurar da yar tasu komai zatayi tayi sude se sun samu abinda sukeso,
Iyaye muji tsoron Allah musani fa akwai Ranar da Ido zai Rena fata kuma wallahi tabbas setazo ko mun shirya ko bamu shirya ba,

Wasu kuma yammatan ne da kansu suke lalata rayuwarsu awaje kafin suje gidan aure wanda hakan ke hanasu samun nutsuwa acikin gidan mijin, Wanda dayawa daga cikin yammata ba aure sukeso suyiba ko ince ba kwanciyar hankali suke nema ba sunfi son gurin da zasu huta ba ibada ba Amma bazaka gane ba se kaje Neman auren su baka da sisi san nan zaka fahimta,

*Akwai hujja mai Karfi kan haka,*

_*Muhadu agaba insha Allah,*_


_*GABATARWA Miftahul ilmi*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form