Skip to main content

Posts

Showing posts with the label Mace Uwar Al'ummah (Women's World)

TSAFTAR CIKIN ƊAKIN KWANA

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Tsaftar Cikin Dakin Kwana:_* 
Dakin kwana dole ne mu kula da gyaranshi fiye da ko’ina a cikin gida, domin nanne wurin da Maidiga yake samun cikakken nutsuwa da hutawa da samun kwanciyar hankali da dai sauransu. Saboda haka dole ne mu riqa kula da gyaranshi qwarai da gaske, da kuma qoqarin qawatashi da duk abinda Allah ya hore, da qoqarin sanya turare da abubuwa masu sa qamshi a kowannen lokaci musamman lokacin kwanciya. In har Allah ya hore yana da kyau ayi amfani da turare na ruwa ko na hayaqi kala daban-daban, kina iya amfani da kala hudu ko biyar a lokaci daya kowannen ki sa shi a bangare daban. Misali na zanin gado daban, na filo daban, idan filon yafi daya kowanne ki sa masa nashi daban, na labule daban, na tsakar daki daban, na kujeru daban dss. Hakan zai bada wani irin qamshi mai tada hakalin Maigida ya rasa wanne irin qamshi ne wannan kuma daga ina yake fitowa !!!
Wabillahi Taufiq.
Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdull…

FAHIMTAR MATUƘAR SHA'AWAR 'YA MACE

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Fahimtar Matukan Sha’awar ’Ya Mace:_*
Wani abun da ke kawo matsala cikin ibadar auren ma’aurata shi ne karancin ilmin yanayin sha’awar juna. Kamar yadda halittar mace da namiji ta bambanta, to haka halayyarsu, hankalinsu da kuma sha’awarsu. Shi namiji Allah SWT Ya inganta ma’aikatar hankalinsa, Ya ba shi karfin basira da aiki da hankali sama da wanda Ya ba ‘ya mace, ita kuma ‘ya mace, Allah Ya inganta ma’aikatar hankalinta da shau’uka masu tsananin karfi da inaganci, sama da na da namiji. In muka lura da irin yanayin zamantakewar dan Adam, sai mu ga kowannen mu an ba shi abu mafi cancanta da shi a halin zaman rayuwar duniya. Maza su ne masu rike gida da al’umma gaba daya, dole suna bukatar kaifin hankali da basira wajen zartar da ayyukansu. Ita kuma mace, in so da kauna da tausayi ba su cika zuciyarta ba, ya za a yi har ta iya yin hakurin daukar ciki, raino ta kuma yaye ‘ya’yanta har a samu cikar al’umma? Yanayin halittarmu yanayin sha’awarmu; da namiji hankali…

KI YI ADO DA KWALLIYA SABODA MIJINKI

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_KI YI ADO DA KWALLIYA SABODA MIJIN KI_*
Ki kasan ce kamar wata kyakyawar fulawa ma abociyar kyau da daukar hankali tare da kyakyawan kanshi ga mijin ki Ki fuskance shi da mafi dadin kamshi da mafi kyawun tufafi
Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yace: “Mumini bai amfana da komai ba bayan kiyaye dokokin ubangiji mafi alkhairi gare shi sama da mace ta gari, idan ya kalle ta zata faranta masa rai”
Nana Aisha ta ce: mata ku kwadaitu da yin kwalliya ga mazajen ku Idan kina da miji kike so kiyi masa magana toh kiyi ta a mafi kyawun yadda take
Umamatu bintul Haris tana yiwa yar ta nasiha yayin auren ta tace: Kar idon sa ya ga mummunan abu daga gare ki Kar hanchin sa yaji kanshi daga gare ki sai mafi dadi
Abdullahi bn Ja’afar yana yiwa yar sa nasiha yayin auren ta Kwalliya ta zama dole a gare ki Ki sani kuma hakika mafi kyawun kwalliya shine kwalli Kuma mafi kyawun turare shine ruwa (yana nufin ki sance mai yin wanka a koda yaushe, saboda idan babu wanka toh kwalliya da tu…

MUN ZO WANI LOKACI DA MATA SAM BA SA JIN KUNYA

*_MUNZO WANI LOKACI WANDA MATA SAM BASA YIN KUNYA!_*
بسم الله الرحمن الرحيم.
_▪Subhanallah! Astagfirullah 😔 Allah ka gafartamana ka Shiryar damu_
▪Yanzu mun zo wani zamani wanda akasarin 'yan matan mu basa jin kunya kuma basa yinta ko kadan! Mace bata jin kunyar yin hira da samarin da ba ta sani ba. Ta nan media abun ma yafi muni sosai a instagram ne ko facebook ko a wasu shafukan sada zumunta irinsu whatsapp, twitter, snap chat da sauransu, basa jin kunyar yin bidiyo chart da samari ko su kira su ko suyi musanyar hotuna wasu ma hotun nan batsa da fitsara.
▪Wasu ma a jahilcinsu suna tunanin cewa babu wani laifi wurin hira da maza, sai ma suka ce, idan bamuyi magana da samari ba, ta yaya zamu sami mijin aure? Ta yaya zamu gane cewa suna son mu?
▪Mace yarinya budurwa zaka sameta da tarin samari a media, kuma sam bata jin kunya daga kalamanta, mu'amalarta, halayyarta, dabi'unta, domin kuwa haka zaka ga tana sakin zance da sakin jiki a hurinsu. Itace tura hotunanta, yi musu video …

DANCING FOR NY HUSBAND 1

*DANCING FOR MY HUSBAND*

RUBUTU NA 0️⃣1️⃣

_✍️Wannan itace sabuwar shegantakar da shigo cikin wannan al'ummar ta musulmi_
إنا لله وإنا إليه راجعون!!!😔

Yan uwana Musulmai, idan muka kalli irin rayuwar da muke yi a yanzu zamu ga ta sha bambam da ta baya saboda fitintinu sun mana yawa, mune cikin yawan yaƙe-yaƙe, kashe-kashe, tsanantawa a wajen rayuwa, da kuma rashin adalci na shuwagabanni, tsadar rayuwa, tashe tashe hankula, kidnapping, fashi, sata, rashin albarka acikin rayuwa da makamantansu wanda hakan yay ta haifar da tambayoyi da yawa daga wajen mutane kan cewa: *_Mai Ya Kawo Wannan Musifun? Musamman mu anan arewacin Nigeria!?_*
*Mai muka yi muka cancanci wannan? Ina muka dosa ne acikin rayuwar nan? Kuma mene ne za mu yi don hana faruwar wannan alamura?*
Yayin da masu hankalin cikinmu suka zurfafa tunani da tantance abinda ya haufar mana da wadannan fituntinu se suke kokarin gano amsar wadannan tambayoyi.👇

shin muna yin rayuwarmu ne ta fuskar bin maganar Allah - (Alqur’ani) - da kum…

YADDA AKE HAƊIN DABINO

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Yadda Ake Hadin Dabino_*
Wannan yana da matukar mahimmanci ga ya mace domin yana gyara ma mata jiki kuma yana saukar mata da ni'ima ko da ta kasance gabanta a bushe yake zai taimaka mata.
Zaki nemi wadannan abubuwan kamar haka;
* Dabino * Zuma  * Tatacciyar madara * Kanunfari *Bayani;* Ki nika kanunfari ko kidaka ya daku sosai, sannan ki zuba busasshen dabino ki cigaba da dakawa sai ya daku sosai sannan ki samu tatacciyar madarar ki zuba cokali uku na wannan garin dabino da kanunfari a ciki sai ki sha.
Ki dunga sha lokaci lokaci zaki sha mamaki da yardan Allah.
Wabillahi Taufiq.
Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*

ALAMOMIN TSARKIN MAI JININ HAILA

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Alamomin Tsarkin Mai Jinin Haila_*
* Bushewar abinda akasa gaba.
* Wani ruwa ne fari kuma mara kauri yana zuwa a karshen haila, amma wannan yafi samun wanda ta dade tana haila, amma an fi so ta dan jira kadan har taga bushewar abin da tasa a gaba.
Amma wanda yanzu ta fara jinin hailan an fi so tayi amfani da bushewar abin da akasa a gaba.
*_Lokutan Duba Tsarkin Haila_*
= Ana so mace ta duba jinin ta yayi da tazo kwanciya da dare sai ta duba idan taga alamar tsarki, sai ta kwana da shirin wanka.
= Ana so mace ta duba alamar tsarkin ta kafin fitowan alfijir idan tayi tsarki kawai sai tayi wanka ta cigaba da ibadunda suka haukanta.
Wabillahi Taufia.
Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*