Showing posts with label Masoniyya (New World Order). Show all posts
Showing posts with label Masoniyya (New World Order). Show all posts

IS THE THIRD WORLD WAR HERE ALREADY?


*IS THE 3RD WORLD WAR HERE ALREADY?*

China tried to give USA a run for her money.

USA was not happy, she felt threatened because of China's rapid economic growth & rising influence in the world, especially in Asia which has the highest population proportion as compared to other continents.

In retaliation, USA fueled chaos in Hong Kong, but terribly failed as China managed to control the situation, prompting think of USA to think of another method.

Fearing the consequences of escalation & possibility of military action, the USA contemplated a covert strategy that would be used to destabilize China & Iran which seemed to be working on becoming a great influence in the Middle East, hence diverting the attempts to overthrow USA as the world economic super power, or give Russians an advantage.

The CIA revisited its laboratories & came up with a perfect solution (so they thought) which was accepted by the US security Council, since they had a vaccine for the original COVID-19, hence averting threats of a possible boomerang effect.

On the night of a particular day in January 2020,CIA delivered the viruses in Wuhan icy mountain using the undetectable F-35 stealth combat fighter jet. Below Wuhan mountain is China's Aquatic sciences laboratory, serving as a perfect cover,which would make it appear as though China was responsible for the virus.

China, realizing too late that she had been attacked with a biological weapon, took samples of the virus, tested them & discovered that it was impossible to create a viable vaccine within a short period of time due to its characteristic rapid mutation, so what next?

China's scientists & military experts therefore decided to perform a biological twist to the original virus using "Reverse engineering" then decided to send it back to the USA & her allies in Europe, Italy being the worst hit by the metamorphosed virus.

As soon a the first case was recorded in US, they tested & discovered that the virus had been altered & that the intended vaccines couldn't work on the new version, & that is why it is being reported that recovered patients are testing positive again.

This is why POTUS-Trump is fuming & angry that his own creation has come back to haunt the US!

Even so, the USA is hiding the exact number of victims to avert a crisis of panic, rage & an economic shutdown.

It is for this reason again that the USA is trying to buy off anyone who might create a working vaccine (Germany was approached),so that she gets patent rights & prevents China from accessing it.

Now as the virus spreads throughout the world, China, Europe & US scientists are in a race to manufacture a vaccine for the virus, which is what China wanted; To be in the same position with her opponents.

We have always imagined a WW3 which involved bombers flying high in the skies, a lot of nuclear bombs & gunshots renting the air, but modern warfare has dramatically changed all those perceptions.

Today WW3 is happening right before our eyes! What a moment to be alive!🙉🙉🙉

Africa will suffer for no reason, & it will become worst hit! 

However, there is hope in everything, we still believe in hope even when the odds are obviously worrying.

Say a short prayer for our continent my beloved people.❤💕💝
***Copied
Share:

TA'ADDANCIN MASONIYYA 20

TA'ADDANCIN MASONIYYA 20

A Yanzu haka akwai Guraben na'urar tauraron dan Adam (Satellite) na
duniya gaba daya guda Arba'in da Takwas a ORBIT
wadanda Amurka da Kawayen ta suke amfani da su.
Wadannan Satalayitoti na iya karbar Siginoni kuma su
bada Cikakken Bayani ga gurbin Satalayit din da kuma
inda Siginar take.

 A yanzu haka, Guraben da Siginonin
suke Na'urori ne da ake manna su a jikin Tankuna,
Jiragen Yaki da na Sufuri ko kuma a hannu da akanyi
amfani da su don Tabbatar da tsaro dangane da
abubuwan da ke kusa da su. Mataki na gaba da
Masoniyya zata dauka shi ne, a Gabatar da Na'urar da
zata samar da wannan Siginar ga kowane dan Adam. A
Yanzu haka akwai irin wannan Na'urar, itace suka
Sanyawa suna (Electronic Tag) kuma tuni har an fara
amfani da wannan Na'urar a UK.

 Dalilin kirkirar ta kuwa
shi ne, don saboda a san halin da 'Yan gidan yari suke
ciki. Akan Sanyawa masu laifi wannan Na'ura ce a
hannu ko kafa, ta yadda akwai iya inda aka Kayyade
mai da ya je, yana wuce wurin koda da taku daya ne
zata tona shi. Ka kalli film din DISTURBIA don ganin
Misalin irin Na'urar.

 Amfani da wannan Na'ura ga
Direbobin Jirage kuwa tuni har ya zama ruwan dare a
Manchester, Bark Shaw da Norfolk, akwai kuma shirin
ganin an Fadada abin zuwa ga sauran Kasashe nan da
shekaru masu zuwa. A wani rubutu da Jaridar Daily
Telegraph tayi a ranar sha uku ga watan Nuwamba a
Shekara ta alif dubu daya da dari tara da Casa'in da
Bakwai (13-10-2016 November 1997), Jack Straw,
Sakataren gida na Birtaniya a wancan lokacin Ya ce :
''Electronic Tagging dinnan ya samu karbuwa cikin sauri
sosai a 'Yan shekaru kadan, saboda mutane sun Aminta
da shi!! Kaga kenan idan har mutane suna yarda da irin
wadannan abubuwan to fa tamkar suna mika kansu ne
zuwa ga ' Yan Masoniyya, sai dai kuma ba lallai bane
mutum ya iya gujewa irin wannan Sharrin domin
Tuntuni dama sun riga sun gurbata masa zuciya ta
yadda bai da wani zabi face abinda suka Gabatar masa
da shi kuma ba tare da ya sani ba.

 Yakar tunanin
mutane suke yi ta yadda daga baya duk abin da suka zo
da shi sai su karba tare da tunanin ci gaba ne. Sai dai
fa mu sani, duk abinda Masoniyya zata yi, to da Fuska
biyu take yin sa, kuma duk irin abinda ka gani a bayyane, to ka tabbatar cewa akasin sa zaka taras a daya barin.

Zan ci gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com
Share:

TA'ADDANCIN MASONIYYA 19

TA'ADDANCIN MASONIYYA 19

To idan har suna da wadancan bayanan da na fada
akan kusan kowa da kowa, kati daya mai dauke da
dukkan wadannan bayanan da ma wasun su zai basu
wata Muhimmiyar dama wajen sanin yadda zasu juya
mutane yadda suke so a Saukake.. Hakan kuma zai
basu damar tattara duk wani bayani karami da babba
na kowa a cikin kowace irin al'umma.

 Bayanan sune
zasu basu damar Kaddamarwa, Gudanarwa tare da
tafiyar da Miyagun Kudurorin su a cikin al'umma. Sai
dai kuma akwai wani gurbi da dole Yan Masoniyya sai
sun cike shi idan har suna so su sami Nasara. Ta
hanyar yin amfani da Zunzurutun kudi ko kuma ince
Madarar kudi, mutum na iya kaucewa binciken da suke
yi na dan wani lokaci. Saboda babu wata Na'ura da
zata iya gano yadda akayi da ruwan kudi. Kaga kenan
bayanan duk cinikayyar da akayi da wannan kudin sun
gudu musu kenan. Akan hakan, Masoniyya ta dauki
wani mataki wajen ganin ta maye gurbin amfani da
ruwan kudi Izuwa ga tsarin da ya dogara kacokan akan
Sufurin kudi na Na'ura ko kuma ince tsarin da ya
dogara akan amfani da kati (Cards /Electronic
Transfer). Wannan shiri tuni ya fara aiki a UK.

Jadawalin Mondex (The Mondex Scheme) wanda
Bankunan tsakiyar yamma tare da Ma'aikatar Sadarwa
ta Birtaniya suka fitar shi ne farkon alamar tabbatuwar
wannan Simatin kati (Smart Card ). A cikin kowane
Simatin Kati akwai wata 'Yar karamar Na'ura da ake
kira Micro Chip wacce take Kirgawa tare da ajiye duk
wani abu da aka yi da ita, ba wai sai Cinikayyar da
akayi da katin ba kawai, a'a duk wani abu da akayi da
katin. Wannan kati zai iya zama ATM, Katin Mallakar
gida, katin zama dan kasa da dai sauransu. Sai dai
kuma duk da cewa katin Shaidar zama dan kasa ka iya
bada irin wadannan bayanai, ba zai iya gano ko
bayyana inda mutum yake a cikin dan Kankanin lokaci
ba, dole ne sai an bukaci wata irin Na'urar gano
abubuwa, ko kuma ince Mayyar Na'ura (Tracking
Device) da za'a iya sawa don gano duk inda wannan
mutumin yake a fadin duniya.

Duk iya Hayaniyar da
Za'a yi, dole ne wannan Mayyar Na'ura ta zama yar
karama wacce za'a sa a katin ko kuma a Sanyawa
mutum a cikin jikin shi. In aka Sanyawa mutum zata
bada sigina wacce na'urar tauraron dan Adam da ke kasa kasa da
wannan duniyar Tamu zata dauka kuma ta gano inda
wannan sigina take tare da bayyana wanda wannan
sigina take jikin sa. Ko da yake wannan bayani zai
zama tamkar wani shirin fim, wannan shiri ne na
Masoniyya wanda yana nan tafe,kuma duk mai tsawon
rai zai gani da idanunsa.

 Sai dai kuma ga wani misali
Bayyananne, a yanzu an sami wani irin ci gaba ta
yadda idan akace misali yau kana aiki a wani kamfani
ne ko wata Ma'aikata da take biyan Ma'aikatanta ta
Banki, idan wata ta kare kudin naka asusun ka na
Banki zasu wuce kai tsaye, idan ya shiga kai kuma kana
daga zaune a gida zaka iya hawa online kayi Sayayya
da wannan kudi naka dake cikin asusun ba tare da
ka je da kanka ka taba su ba, iya ka kawai da kunyi
ciniki sai su kawo maka kayan har kofar gida kai kuma
sai ka tura musu kudin ta nasu Asusun din.

 To ci gaba
ne ya zo gaskiya, kuma sauki ne ya samu a gare mu, to amma
baka tunanin a cikin irin wannan abubuwan akwai kuma
abinda suke kokarin bullo da shi???

 Zan Ci Gaba In
Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com
Share:

TA'ADDANCIN MASONIYYA 18

TA'ADDANCIN MASONIYYA 18


Aikata Ta'addanci, Yaduwar Laifuka, Tashin Hankali da Jagaliyanci kullum su ake nuna mana a cikin Fina Finai da sauran Kafafen yada bayanai, Rahotanni daga Gwamnati duk sun zama kusan iri daya. Yin hakan kan jawo tausayawa a cikin al'umma tare da bukatar ganin an yi amfani da kowace hanya wajen Murkushe wadannan 'Yan Ta'adda musamman ta hanyar amfani da Na'urorin leken Asiri. A dalilin haka ne yasa Sabbin Na'urori suke ta kara bayyana, kuma nan bada Jimawa ba za'a kai wani mataki da duk wani motsin mutum ana iya sanin shi.

Ra'ayin mutane dai har iyau za'a kara karkatar da shi domin a baiwa 'Yan Masoniyya damar cin karen su babu Babbaka. Samun damar juya mutane ta hanyar ajiye bayanan kowane mutum a wata Babbar Ma'ajiyar bayanai yana nan tafe akan hanya. A yanzu haka akwai wani shiri da ake yi na ganin an tara bayanan mutane irin su bayanan Banki (Banking Details), Lasisin tuki (Driver's Licence), da sauran bayanai Makamantan haka waje daya. A da, duk wadannan bayanai da ma wasun su, suna zaune a wurare daban daban ne a jikin Katuna Mabanbanta, to amma yanzu ana nan ana shirin tara dukkan wadannan bayanai a jikin kati kwaya daya tak!!

Matukar akai hakan, to abinda zai biyo baya shi ne, za'a iya ganin komai game da kowa a cikin rabin minti. A shekara ta alif dubu daya da dari tara da da Casa'in da biyu (1992), Mataimakin kansilan kotun Birtaniya Nicholas Brown Mulkinson ya fadawa kotun cewa idan dai har akace bayanan da 'Yan Sanda suke da shi na Rabano, harkokin Kasuwanci, bayanan lafiya da sauransu za'a tara su waje guda, to ' 'Yancin wannan mutumin fa yana cikin Hadari.

Sai dai kuma Masoniyya Karkashin Gwamnatin da suka kafa kuma suke juyawa tuni suna da Muhimman bayanai akan ka. Sun riga sun san da wa kake magana a waya, inda kake aiki, inda kake Siyayya, abinda kake ci (favorite food kawai), kayan da kake sawa, iya kudin da kake da shi, Kadarar daka Mallaka, Nawa kake samu da dai sauransu. Kuma suna samun wadannan bayanai ne ta hanyar Forms da muke cikawa na hannu da kuma online da kuma bayanan da 'yan leken asirin su ke kai musu. Mafi sauki kuma a yanzu VBN number.

Zan ci gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com
Share:

TA'ADDANCIN MASONIYYA 17

TA'ADDANCIN MASONIYYA 17
A Tarihance, 'Yan Masoniyya sun sha Kirkirar Matsaloli
da tashe tashen Hankula iri iri domin su cimma wata
manufa tasu. Yawaitar Miyagun Kwayoyi a Amurka ya
baiwa Gwamnatin kasar damar yin amfani da Muggan
Makamai da kuma shirye shirye don ganin an cimma
matsaya. Rikita al'amura, daukar Muggan matakai,
amfani da karfin Gwamnati wajen bijiro da bukatar
kariyar kai da kai da kuma na kasa baki daya, Yawaitar
Ta Addanci a cikin al'umma, shaye - shaye da sauran
abubuwa Makamantan haka su ne ke taimakawa
Masoniyya wajen gudanar da aikin ta a Saukake.
Wannan dalili ne ya sa Ta Addanci yayi yawa, da
gangan suke Kirkirar rigima don a tunanin su idan mun
shiga Bala'i, idan suka kawo mana dauki zamu amsa in
yaso daga baya sai su nemi yarjewar mu akan abinda
zai jawo Rushewar mu gaba daya in yaso daga baya
mu zo muna da na sani mara amfani, domin Amsar
taimakon su a irin wannan lokaci dai dai ya ke da ace
ka gudu don kada a harbe ka da bindiga ka fadawa
bom. Ci gaba da ake ta samu a fannin Kimiyyar kere-
kere (Technological Advancement), ita ma wata
Shafaffiyar hanya ce da ta baiwa 'Yan Masoniyya
damar cin karen su babu babbaka, domin hanyar tana
basu damar bibiyar aikin kowane mutum, bincike akan
sa d kuma ajiye bayanan. Bayanai sune makullan su,
iya bayanan da suke da shi dangane da mutum, iya
damar da suke da ita kenan wajen gudanar da aikin su
kai tsaye, kuma wannan bayani ne zai basu damar
Dulmiyar da mutane yadda suke so. Masoniyya tana
kokarin Kirkirar wasu irin al'umma ne wadanda zai
Zamana basu da wani zabi face Abin da aka zabar
musu, in ma kuma har akwai zabin to zabi ne daga
Gurbatacciyar Zuciya. Kirkirarrun abubuwa gasu nan
suna ta takaitar maka da zabin ka, idan kuma kana da
zabin to ta iya Yiwuwa zabi ne da aka cusa maka
Aranka ba tare da ka sani ba, kuma dama so akeyi
wannan zabi naka ya kaika wani mataki, matakin da sai
yadda aka yi da kai. Juya Talakawa tare da Sauran
masu hannu da Shuni ko kuma masu fada aji, yana
nufin juya kowane bangare na rayuwar al'umma ne.
Masoniyya ta san hakan, shi yasa ma take kokarin
ganin ta kama kowane fanni ko bangare na kowane irin
Abu da mutane ke yi. Hatta a Malaman Addini ma
akwai 'Yan Masoniyya. Allah Ya kiyaye mu Ameen. Zan
ci gaba In Shaa Allah

🔰🔰🔰
Haiman Khan Raees @HaimanRaees
08185819176
Haimanraees@gmail.com 
Share:

TA'ADDANCIN MASONIYYA 16

TA'ADDANCIN MASONIYYA 16


Wani Salon Yakin Sunkuru kuma da Masoniyya ke
amfani da shi wajen ganin sun cimma burin su shi ne,
kyale ko barin Ta'addanci ya wanzu a cikin jama'a, a wani lokacin ma harda daukar nauyin TA'ADDANCIN!
Hakan zai Wanzar da tsoro tare da bukatar kariya ta kai
da kai da kuma ta kasa baki daya.

 A wani bincike da
aka gudanar, an gano cewa, Kamfanonin dake hada
Miyagun Kwayoyi na daya daga cikin Kamfanonin da
suka fi kowa samun riba a Kasuwance. Kasashen
duniya da dama na nan suna ta fama wajen ganin sun
kawar da Matsalar Safarar kayan maye, kama daga cikin
gida har Izuwa sauran Kasashen ketare domin Safarar
Miyagun Kwayoyi ta addabi mutane.

 Amurka misali,
cike take da Matsalar Safarar Miyagun Kwayoyi da
sauran kayan maye, wannan na daya daga cikin dalilan
da suka sa Ta'addanci iri iri ke afkuwa a Kasar kamar
ba gobe. Saboda ganin goyon baya da kuma daurin
gindi da da Gwamnatin Amurka ta samu a wajen jama'a
don ganin an dau Tsatstsauran Mataki akan wannan
matsala ce yasa Gwamnatin yin amfani da Muggan
Makamai da kuma Miyagun Shirye Shirye don ganin an
Magance wannan Matsala a fili ko a bayyane. Sai dai
kuma Bayyanar wasu abubuwa da suka faru ta bayan
fage sun sa mutane sun fara Daurawa Gwamnatin
alamar Tambaya. Musamman dangane da irin Shirye
Shiryen da Gwamnatin ke yi akan wannan Al'amari.


Kusan kowa Yasan cewa a shekara ta alif dubu daya da
dari tara da sittin (1960) J. Edgar Hoover wanda shi ne
Ciyaman din FBI na wancan lokacin ya bar siye da siyar
da Miyagun Kwayoyi da kayan maye yana ta Wanzuwa
da gangan a tsakanin Bakaken fatar dake zaune a
kasar Amurka domin ayi musu kofar rago wajen dai
daitar da su saboda yawa da kuma karfin da ake ganin
suke Karawa a kullum. A Shekara ta alif dubu daya da
dari tara da tamanin (1980) , lokacin da Kwamunisanci
ya kusan Mamaye tsakiyar Amurka, sai ya Zamana ana
bukatar kudi Haikan domin a samar d Makaman Yakar
'Yan Kwamunisanci, don haka sai CIA suka bar siyar da
Miyagun Kwayoyi da sauran kayan maye sukai ta
Yawaita a cikin Amurka. Ta nan ne suka sami kudin
siyen wadannan Makamai da kuma kera wasun su.

Bayanai daga bakin Sanatan Amurka Jack Bloom
wanda yana daya daga cikin 'Yan Kwamitin bincike
akan wannan Lamarin ya tabbatar da faruwar hakan.

Zan ci gaba In Shaa Allah.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com
Share:

TA'ADDANCIN MASONIYYA 15

TA'ADDANCIN MASONIYYA 15

Misali na gaba kuma dangane da Fina Finan da suke
bayyana shiri da kuma Kudurorin Masoniyya shi ne wani
Fim mai suna "Independence Day", wannan Fim ya
kafa Tarihi iri iri a lokacin da ya fito har sai da ya zama
Fim na bakwai da ya fi kowane Fim kawo kudi a
Masana'antar Fina Finan duniya gaba daya. Wannan Fim yana
dauke da wani Kagaggen labari ne na wasu bakin
haure (Aliens) da suka kawo wa duniyar mu hari, sai dai a
takaice, wannan Fim cike yake da Manufofin
Masoniyya.

A cikin wannan Fim, akwai wani Shashen
Dakarun Sojoji da akewa Lakabi da Area 51, daga
wannan wuri ne ake samar da duk wani shiri na Soji,
kuma anan ne ake samo Maslahar duk wata matsala ko
Damuwa da ta addabi duniya da abinda ke cikin ta. A
Mashigar wannan wuri, ido dayan Masoniyya ne a jiki. A
cikin wannan Fim, an nuna Amurka a matsayin ja gaba
wajen samar da kariya ga kowace kasa da wani hadari
da ya Shafeta. Wannan Tawaga mutum daya ne yake
Jagorantarta, mutum daya Tak!!!

 Bugu da kari, Fim Din
yana daya daga cikin Fina Finai da kuma Shirye Shiryen
gidan Talabijin (Season Films) da ake yi dangane da
bakin Haure da ake cewa zasu zo zasu zo kamar su
Aliens, UFO da kuma harin da ake cewa wai zasu kawo
wa duniyar mutane domin ganin bayan mutane gaba
daya (Ka Kalli wani Fim mai suna WARCRAFT wanda
aka Fassara shi da Hausa aka sa mishi suna YAHUDU
don ganin misalin a bayyane ).

 Irin wadannan Fina Finai
ne ke kara hura wutar Fargaba a cikin zukatan al'umma
tare da Ingiza su wajen Tanadar Makaman Yakin kare
dangi don ayi maganin Matsalar idan ta taso. Wannan
ma daya ce daga cikin Dubunnan hanyoyin da
Masoniyya ke amfani da su wajen ganin sun tabbatar
da wanzuwar gwammati guda daya tak a duniya,kuma a
Karkashin ikon mutum daya jal.

 Masoniyya na amfani
da Hanyoyi da dama wajen Cusawa mutane tsoro a
zukatan su tare da bukatar kariya ta din din din,
wannan kuma bukatace da da take bukatar hadin
guiwar dukkan sauran Shuwagabannin duniya baki daya
domin ganin an kawar da Matsalar da ka iya afkawa
kowa da komai, in ya so daga baya sai su zo su yi
kokarin kawo dauki ko kuma maslaha tare da neman
hadin kai, bayan kuma su suka shiryo tsiyar da Masifar
suka turo muku.

Duk kasar da suka yarda suka bada goyon baya to za su dinga juya su yadda suka ga dama ta hanyar juya shugabannin su. Kasar kuma da taki, za'a ci gaba da gallaza mata tare da bin duk wata hanyar da zasu iya Bi wajen ganin sun jefa kasar cikin BALA'I. Ga Libya nan dai yadda ta Koma yanzu, ita kadai ta ishi kowa misali.
Allaah Ya Tsare mana imaninmu ya rabamu ya rabamu da kafirci.

Zan ci gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com

Share:

TA'ADDANCIN MASONIYYA 14

TA'ADDANCIN MASONIYYA 14

Manufofin Masoniyya da dama da ake yada su ta hanyar Fina Finai da Makamantan su a sauran Kafafen yada bayanai (Mass Media) sun fi isa kai tsaye ga mutane fiye da sauran Hanyoyin. Ta wannan hanya ne suka juyarwa da mutane da dama tunanin su tare da kokarin ganin sun wanzar da tsarin su na gwammati kwaya daya da zata mulki duniya da kuma shugaba daya Tal da zai mulki duniya gaba dayan ta. Fitaccen marubucin nan mai suna Rudyard Kripling wanda shi ma dan Masoniyya ne, ya yi kaurin suna sosai da littafin sa mai suna "The Jungle Book", sannan shi ne ya rubuta wani littafi mai suna "The Man Who Would One Day Be King", wannan littafi ya samu karbuwa sosai inda daga baya aka maida shi Kasurgumin Fim Din Hollywood wanda Sean Connery, Michael Kane da Saed Jaffery suka fito a cikin sa.

Labari ne akan wasu Sojoji guda biyu da sukayi wata doguwar tafiya Izuwa wani gari da ke can kusa da India, akwai rade-radin cewa a wannan garin akwai tarin makudan dukiya da kadarori Mallakin Tsohon Sarki Alexander The Great. Lokacin da suka isa wannan gari, sai mutanen garin wadanda ake kira KAFIRS suka kama su, ana gab da za'a kashe su, sai aka ga wata sarka a wuyan daya daga cikin su wacce take dauke da tambarin ido dayan Masoniyya a jikin ta. Ganin wannan sarka ce yasa dukkan mutanen wannan gari suka maida shi abin Bautar su. Shi kanshi mutumin da farko bai yarda cewa shi Ubangiji bane, amma daga baya, ganin irin yadda suke Girmama shi yasa ya fara tunanin lallai shi ma fa Ubangiji ne.

 Irin wadannan Mugayen Kaba'irori ne ake nuna mana a Fina Finai da dama, sau tari zaka ga mutum ya rufe ido daya ya bar daya, shin ko kasan me hakan yake nufi??? Hakan yana nufin shi Mabiyin Masoniyya ne, idan kuma ba haka to Sun cusa masa irin Ra'ayinsu ne a Zuciyar sa ba tare da ya sani ba ko kuma yana sane so yake yi su jawo shi cikin su.

Abin Takaicin shi ne, da yawan mutane sukan yi irin wadannan alamu na Masoniyya ba take da sun san Ma'anar abinda suke yin ba, sannan akwai kuma masu yi da gangan don neman suna ko wani abu makamancin haka. To wadannan, bani da damar in ce musu 'yan Masoniyya ne su, amma dai tabbas ya kamata musan me muke kallo, kuma me muke barin 'Ya'yan mu suke kallo. Domin Yahudawa Makiyan mu ne, kuma Masoniyya ba abar koyi bace.

Zan Ci gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com

Share:

TA'ADDANCIN MASONIYYA 13

TA'ADDANCIN MASONIYYA 13

Gaba ki dayan duniyar nishadi (Entertainment world)
cike take fam da Hujjojin bayyana da kuma kasantuwar Masoniyya a cikin duniyar nan. Kodai a
boye ko kuma a bayyane, tsarin su, akidar su da kuma
kudurorin su ake Bayyanawa.

 Manufofin Masoniyya ana
bayyana su musamman a cikin Fina Finan da muke
kallo yau da kullum, daga kana nan Fina Finai zuwa
Manya su, kai har ma da "Cartoons"! Masoniyya bata
bar kowace kafa ba wajen yada manufar ta da
kudurorin ta na samar da Gwammnati guda daya da
zata mulki duniya gaba dayan ta. Matt Growning, shi ne
mutumin da ya kirkiri daya daga cikin Manya Manyan
wasan Dodanni (Cartoons) na duniya gaba daya. Shi
ma dan Masoniyya ne kuma ya ce yana da wasu
"Tunanuka" da kuma Ra'ayoyi da yake son Bayyanawa
mutane, sai dai yana so ya bayyana su ne ta yadda
jama'a zasu karbe su kuma su amince da su cikin
ruwan sanyi. Hanyar da wannan mutumin ya bi kuwa
don ganin ya cimma burin sa itace, kirkirar wani wasan
Dodanni mai suna "The Simpsons", to abin tambaya
anan shi ne, me wannan shirin yake koya mana ne tare
da iyalan mu?? Akwai darussa da dama da aka shirya a
cikin sa irin su : Karya, Rashin Kunya, Fitsara, raina
iyaye da Shuwagabanni, Katsalandan a cikin abin da bai
shafe ka ba, kangara da rashin mutunci sune hanyar
zama wani a cikin al'umma, sannan Jahilci da
Tumasanci abubuwa ne masu ban sha'awa, yayin da
karatu da neman ilimi a kowane fanni ya zama
kauyanci wanda ba'a yayin sa.

 Irin wadannan Mugayen
darussa ne ake shirya mana a cikin Irin wadannan Fina
Finan kuma muke barin 'Ya 'Yan mu suke kallo ba tare
da yin nazari akan su ba. Da za muyi duba Dakyau ga
yanayin rayuwar matasan mu a yanzu da kuma yadda
rayuwar su take, na tabbatar da cewa kusan kowa zai
iya fahimtar me nake nufi. Sai dai kuma abinda zai fi
tayar maka da hankali shi ne wani kalami da aka fada a
wata fitowa na shi wannan wasan Dodanni inda Homer
Simpson ya ci karo da 'yan kungiyar Stone Cutters ko
kuma ince Freemasons, lokacin da ya shiga wannan
kungiya, sai Suka ga wani hatimi a jikin sa, ganin
wannan hatimi ne ya sa Suka nada shi shugaban su,
domin an ce musu wai duk wanda yake da wannan
hatimi a jikin sa, shi ne zai jagorance su Izuwa ga
Nasara. Bayan samun wannan matsayin ne sai shi
Homer Simpson ya fara tunanin shi ma fa yanzu
Ubangiji ne. SUBHANALLAH!

Wasu da dama zasu dauki
wannan magana da cewa ai ba komai bane face Abin
Bandariya da Nishadi, amma tasirin sa a zukatan masu
kallo, musamman yara ya wuce hakan.

Zan ci gaba In
Shaa Allah

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com

Share:

TA'ADDANCIN MASONIYYA 12

TA'ADDANCIN MASONIYYA 12

Wani karin misali kuma shi ne, akwai wata Shararriyar
Waka wacce Fitacciyar kungiyar Mawakan Amurkan
nan da ake kira da "The Eagles" suka yi wacce suka
Sanyawa suna "Hotel California", idan akayi amfani da
Back Tracking wajen Sauraron wannan Waka, ita ma a
cikin ta akwai Shaidanun Sakonni masu dauke da
Miyagun dafi wadanda za'a iya jin su a fili.

Alal Misali ana
iya jin "Oh Yeah Satan" (Hakane Shaidan/Kwarai
Shaidan) to irin wadannan wakoki ne fa muke ji yanzu,
anya kuwa hakan zai haifar mana da DA mai ido kuwa?

To sai dai kuma ba anan kawai zancen ya tsaya ba, ita
kanta wannan Waka tana dauke da wani labari ne mai
zaman kanshi, Carlifonia da suke fada a cikin wannan
Wakar ba Otal bane, wani babban gari ne daga cikin
Biranen kasar Amurka. A wannan wuri ne Hedikwatar
wani babban Coci ta fara wanzuwa, sai dai shi wannan
Coci ba I irin Cocin da muka sani anan bane, Coci ne
da ake kira da "The Church Of Satan" (Wato Cocin
Shaidan).

 Anthony Stanzor Lavey (zan kawo muku
Cikakken Tarihin sa Watarana in shaa Allah) shi ne
shugaba na farko a wannan Cocin, kuma shi ne ya kafa
Cocin. Bugu da kari, shi wannan mutumin Wato Lavey,
shi ne ya rubuta wani littafi mai suna "The Satanic
Bible" (Baibul din Shaidan) sannan kuma ya dabbaka
Bautar Shaidan din. Manya Manyan mutane tun daga
masu rike da Madafun iko, Mawaka, 'Yan Fim (na
Turai), Makada da dai sauransu Suna zuwa wannan
Cocin domin su gudanar da addinin su na Bautar
Shaidan.

 Wasu daga cikin' yan gani kashe nin addinin
ma har yada shi suke yi domin neman mabiya. Daya
daga cikin mabiya wannan addini mai suna Mick
Jagger, wanda shi ne kuma jagoran kungiyar "The
Rolling Stones" ya taba rubuta wata Waka mai suna
"Sympathy For The Devil" (wato Tausayawa ga Shaidan ),
a cikin wannan Waka ce ya ke bayyana cewa wai an
Yankewa Shaidan danyen hukuncin da bai kamata ba.
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN!!! Ina fatar
tabewa, lalacewa da la'ana ta tabbata akan wadannan
'yan iska.

A takaice dai, kungiyar da ta taso tun da
farko a matsayin dakarun addinin Kiristanci, itace
yanzu ta koma kungiyar kazamu masu bin kazamin
addini wanda yake tababa, jayayya da kuma hamayya
da shi kanshi Kiristancin. Allah na ke roko da ya kare
mu daga Sharrin wadannan mutane Ameen.

Zan Ci gaba In Shaa Allah
<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com

Share:

TA'ADDANCIN MASONIYYA 11

TA'ADDANCIN MASONIYYA 11

Anan zan so in fara da yin wata Tambaya mai matukar
Muhimmanci, shin me ya hada Michael Jackson da
Aliester Crowley???

 Gamayya tsakanin Mawaka da 'yan
Masoniyya ba anan kawai ta tsaya ba, mafi Yawancin
wakoki, Fina Finai da kuma Litattafan da suke fitarwa,
suna dauke da Shaidanun Sakonni wadanda mu kuma
kullum kwasar su mu ke yi.

 "Back Tracking" wani salo
ne na ajiye Sakonni da akayi rikodi zuwa odiyo. Su kan
ajiye irin wadannan Sakonni da kuma bayanai ne a cikin
Wakokin su ta yadda in dai mutum ba ta baya ya kunna
wakar ba (kamar zai yi tariya kenan a rediyo mai
rikodi ) to ba zai taba fahimtar sakon ba ba.

Idan mutum
ya kunna su ta dai dai zai ji Waka ce kawai take tafiya,
amma da zarar ya kunna wakar ta baya, to anan ne fa
labarin zai sha banban. Sai dai kuma duk da cewa mai
saurare ba zai fahimci me ake cewa ba, ita Zuciya
saboda hikimar dake cikin halittar ta tana iya gane irin
wannan sakon kuma ta ajiye shi a cikin ta.

Sannan shi
Irin wannan sakon Yana iya Gurbatawa mai Sauraron
sa tunanin sa kuma ya lalata masa Zuciya. Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam Kuma ya ce Idan
Zuciya ta baci to dukkan jiki ya baci, idan kuma Zuciya
ta gyaru to dukkan jiki ya gyaru ", to su Zukatan
mutane suke so su dinga Lalatawa.

 Wannan na daya
daga cikin irin salon da Masoniyya ke amfani da shi
wajen yakar tunanin Jama'a tare da cusa musu akidar
Masoniyya a Zukatan su. A takaice dai, shi wannan
Back Tracking din tamkar wankin Kwakwalwa yake yi,
kuma zai iya canjawa mutum yanayin tsarin Rayuwar
sa ma ba tare da ya ankara ba.

Bari in baku misali,
Shararriyar Mawakiyar nan mai suna Madonna ta taba
yin wata Waka mai suna " Like a Prayer" (kamar
addu'a ), sai dai a wannan Waka ba addu'a ake yi ga
Ubangiji ba face Shaidan. Idan akayi amfani da Back
Tracking (wato aka kunna wakar ta baya), kalmomi irin
su "Oh hear us Satan" (Ya Shaidan ka saurare mu) ana
iya jin su a fili.

Sannan ido dayan da Masoniyya ke
amfani da shi a hanyoyi da dama ya sha fitowa a cikin
bidiyoyin Wakokin Madonna. Madonna kuma ta sake
fitowa a wani bidiyon inda take tsaye akan wani rubutu
yayin da ido dayan ya bayyana a goshin ta, bincike mai
zurfi da akayi dangane da wannan rubutu dai ya nuna cewa rubutun Arabiyya ne (Harshen Alqur'ani).

 Wannan Kadan ne daga cikin cin Fuskar da suke yiwa Musulunci, amma a hakane wasun mu suka dauke su a matsayin ababen nunawa Soyayya.
Allaah Ya Kyauta.

Zan Ci Gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com

Share:

TA'ADDANCIN MASONIYYA 10

TA'ADDANCIN MASONIYYA 10

Har ila yau, kungiyar Masoniyya tana amfani da kafar
nishadi (Entertainment industry) domin jawo mutane
Izuwa ga tunani irin nasu. Ko dai a boye ko kuma a
bayyane, kullum yada akidar su suke yi. Hanyoyin da
'yan Masoniyya suke amfani da su wajen Dulmiyar da
mutane suna da yawa, amma manufar su guda ce.
Manufar kuwa ita ce ya Zamana kowa ya bi bayan su
domin Shiryawa zuwan Dujal. 

Wadannan mutane a
kullum suna nan suna ta kokarin ganin sun dasawa
mutane tunani, akida da kuma ra'ayi irin nasu a cikin
zukatan su ta yadda mutum a hankali tunanin sa
zai rika canjawa izuwa ga gurbataccen tunani irin na su
ba tare da ya fahimci hakan ba.

Wasu mutane da dama suna karyata bayyanar waɗannan mutane da kuma kungiyar su, sai dai kuma Alamomin bayyanar su
a duniyar Nishadi (Entertainment World) a bayyane
suke karara. Daya daga cikin Manyan makaɗan kasan Turai Wolf
Gang Amadeus shi ma dan Masoniyya ne, kuma shi ne
ya shirya wani sauti mai dankaren dadi wanda
Masoniyya suke amfani da shi a matsayin taken su. 

Ya tsara wannan sauti ne akan wani labari da aka samo
daga Misra tun a Zamanin Jahiliyya, labarin kunne ya
girmi kaka ne akan Avyus da Cyrus da kuma irin al'adun
da ake Gabatarwa na Addinin Bautar Gumaka da kuma
tsafi irin na Kabala, daya daga ciki Manya Manyan
Ginshikan kafuwar Masoniyya.

 Daga cikin wannan bakin
addini na Zamanin Jahiliyya ne aka samo Tambarin ido
daya wanda Masoniyya ke amfani da shi. Shaidun
wanzuwar Masoniyya a cikin duniyar Nishadi ana iya
samun su a cikin Wakoki da kuma Fina Finai na
wannan zamani da muke ciki waɗanda anan gaba zan yi sharhi akan su sosai in shaa Allaah. 

Michael Jackson shi ne
Mawakin da har yanzu ba'a taba yin kamar sa ba a
kasar Amurka, shi ne kuma Mawakin da ya fitar da
kundin Wakokin da har yanzu ba'a sami wanda ya fishi
kawo kudi ba a harkar Kasuwancin Wakokin duniya
gaba daya, to shi ma yana da alaka da 'yan Masoniyya.

Da zaka duba Ainahin bangon kundin Wakokin sa mai
suna "Dangerous" zaka ga abubuwan ban mamaki. Da
farko dai akwai Hoton ido dayan Masoniyya a jiki, sai
kuma Hoton wani Takadiri kuma fitaccen kafiri sannan
kuma Gawurtaccen Matsafi mai suna Aliester Crowley
(zan kawo muku Cikakken Tarihin sa Watarana in shaa
Allah), shi wannan mutumin dan Masoniyya ne daga
baya kuma ya koma Bautar Shaidan. Kuma shi ne ya
rubuta wani littafi mai suna "The New Law Of Man"
Wanda a cikin sa aka rubuta cewa, wai a karshen
Duniya wannan littafi shi ne zai maye gurbin Kur'ani
(A'uzubillah). Allah wadai da irin wadannan mutane da
ma sauran masu biye musu.

Zan ci gaba In Shaa Allah.

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Hãïmâñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees 

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees 

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees 
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*


Share:

TA'ADDANCIN MASONIYYA 09

TA'ADDANCIN MASONIYYA 09

Yayin da 'yan Masoniyya suka fahimci wannan al'amri,
sai suka sake kulla wani gagarumin tuggu wanda irin
sa bai taba wanzuwa a ban kasa ba, wannan tuggun
kuwa shi ne hana mutane' Yancin yin tunanin da ya
dace suyi.

Don ganin sun cirewa mutane 'Yancin yin
tunanin da ya kamata, sai Masoniyya ta kafa wata irin
katuwar Katangar KARFE tsakanin mutane da kuma
tunanin da ya kamata ace shi suke yi ta yadda kalilan
din mutane ne ke iya Ratsawa ta cikin wannan
katanga. Ita kuwa wannan katanga an sana'anta ta ne
ta hanya tattaro duk wasu hanyoyin rayuwar dan Adam
gaba daya. Kuma Makaman da suke Yakar mutane da
su suna nan a cikin gidajen mu suna Nishadantar da
mu da iyalan mu.

 Wadannan Makamai da su ne ake
amfani wajen Yakar tunanin mutane ba tare da sun
ankara ba, kuma wadannan Makamai su ne suke
canjawa mutane tunanin su a hankali Izuwa ga tunani
irin na Masoniyya ba tare da sun ankara ba. A wannan
Zamanin da mu ke ciki yanzu, mutane da yawa suna
Banzatar da lokutan rayuwar su ta hanyar rudu da
kuma ci gaban da zamani ya kawo, Talabijin, Sinima,
waya, Kwamfuta, yanar gizo, wasanni, Fina Finai, kade
kade, raye raye da wake wake sun zama wani bangare
na rayuwar mutanen wannan zamani namu.

 Dukkan
wadannan abubuwa suna dauke da wasu jiga jigan
bayanai da kuma Sakonni wadanda mafi Yawancin su
Gurbatattu ne, irin wadannan Sakonni na batanci da
shaidana a hankali suke samun wurin zama a zukatan
mutum, kodai cikin rashin sani ko kuma da gangan. Ta
hakane suke Cusawa Mutane sabbin dabi'u da munanan
halaye Iri daban daban, daga cikin abubuwan da suke
koyawa mutane ta wannan hanya ko kafa shi ne "yadda
ya kamata ace duniyar ta kasance" ko kuma yadda ya kamata ace rayuwar ita kanta ta kasance a bisa tsari da
tunani irin nasu.

 Irin wadannan munanan akidu da kuma
halaye su ake yadawa kullum a cikin wadannan kafafe.
A takaice dai, kafar yada labarai wa al'umma (mass
media) ita ce babbar hanyar da 'yan Masoniyya ke
amfani da ita wajen yada akidun su, dabi'un su, halayen
su da kuma burin su. Kenan idan har wannan kungiyar
tana da damar juya irin wadannan al'amura, to ba abun
mamaki bane don sun sami damar jawo dubban mutane
Izuwa ga wannan tsari na su, wato sabon tsarin duniya.

Wannan itace hanyar da Masoniyya ke bi don ganin sun dulmiyar da mutane izuwa ga sabon Allaah mafi girma wato kafirci. Don haka lallai ne mu kiyaye da irin abubuwan da muke mu'amala da su, kuma mu dinga kyakkyawan nazari akan irin wadannan abubuwan don KAUCEWA fadawa tarkon 'Yan Masoniyya.


Zan ci gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Hãïmâñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*

🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*

Share:

TA'ADDANCIN MASONIYYA 08

TA'ADDANCIN MASONIYYA 08

A haka Masoniyya tayi ta juya tunanin mutane da
yanayin su Izuwa fushi, kamar dai Faransawa, fushi sai
ya koma fada, amma a wannan karon basu bari Suka
sami matsala ba, irin artabun da suka sha da Napoleon
a Yurop ya koya musu darasi, don haka suka sa dokar
duk wani shugaba da zai fito daga cikin 'yan adawa to
dole ne ya bi DOKOKIN Masoniyya, hanya mafi sauki da
za'a tabbatar da an sami damar yin hakan ita ce, a
tabbatar da cewa shi kanshi shugaban dan Masoniyya
ne, kuma ba wani shugaba bane ya Jagoranci wannan yakin
neman' Yanci daga Birtaniya a Wancan lokaci ba face
George Washington.

 A Ranar hudu ga watan Yuli na
shekarar alif dubu daya da dari bakwai da saba'in da
shida (4th July 1776) Ne aka tabbatar da niyyar neman
'Ƴancin kan Amurka, yayin da a Ranar sha bakwai ga watan
oktoba shekara ta alif dubu daya da dari bakwai da
tamanin da daya (17th October 1781) kuma aka sami
galaba akan Birtaniya in da suka Mikawa Amurka' Yancin ta.

A wannan rana ce kasar 'yan Masoniyya ta farko ta kafu a duniya, kasar da zata wakilci
Masoniyanci ta kowace fuska. Alamomin wanzuwar
Masoniyya a kasar Amurka Bayyanannu ne, a jikin dalar
Amurka, akwai Hoton George Washington, shugaban
kasa dan Masoniyya na farko a duniya kenan, tare da
tambarin Masoniyya wanda ake kira "ido daya mai ganin
komai", (The All Seeing One Eye).

Tarihi ya nuna cewa,
dulmiyar da mutane izuwa ga bata, canjawa mutane
tunani tare da wasa da hankulan su, musamman ta
fagen siyasa, su ne Manyan abubuwan da 'yan
Masoniyya suke amfani da su wajen Mallakar duk kasar
da suka dira akan ta.

Da zarar sun kama ' yan siyasa,
attajirai da sauran Manyan kasar, sai kaga dare daya
kawai DOKOKIN wannan kasa ta canja izuwa ga tsari
da Tafarki irin na Masoniyya. To amma tunda hana jiki
ba yana nufin hana zuciya ba ne, sai Masoniyya ta
fahimci cewa burin su na son ganin sun mulki duniya
gaba dayan ta ya ta'allaka ne akan jawo dukkan
mutane daga kowane sashe na duniya izuwa ga tsarin
su.

A tunanin su idan suka yi hakan, Shikenan sun
kashe duk wata dama da wani ko wasu za su iya samu
wajen yin jayayya da su. Wannan dalili ne ya sa 'yan
Masoniyya suka bude kofar su ga kowa ga kowane irin
mutum daga kowane irin addini.


Zan ci gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Hãïmâñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐
*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*

Share:

TA'ADDANCIN MASONIYYA 07

TA'ADDANCIN MASONIYYA 07


Nathan Rothschild shi ne shugaban Bankuna na
wancan lokacin, amma saboda Kasancewar su
Yahudawa, sai ya Zamana ana nuna musu Banbanci.

Nathan sai yayi Amfani da wannan dama wajen hada
kan Jama'ar sa, inda ya yarda cewa zai baiwa Yurop
rancen kudi amma bisa Sharadin za'a dinga daukar
Yahudawa da Muhimmanci kamar sauran 'yan Yuropiya,
kuma za'a basu dama Suyi Kasuwanci irin wanda suke
so. Idan' yan Masoniyya suka ki yarda, kudin za su
koma wajen Napoleon. Ganin cewa ba su da wani zabi
face su Amince, sai suka sanya hannu a takardar
Yarjejeniyar hakan.

A wannan shekara ce sojojin Birtaniya,
Dutch da na Rasha suka dira a Waterloo dake kasar
Belgium inda suka hadu da dakarun Napoleon kuma
suka ci su da yaki. A wannan lokaci ne aka kama
Napoleon, dawowar da bai yi ba kenan. A karshe dai
Faransa ta koma Karkashin Mulkin Masoniyya.

 Duk da cewa Malaman Tarihi basu yi wani Cikakken Bayani
dangane da sa hannun Masoniyya wajen samun 'Yancin
kan Faransa ba, su' yan Masoniyyar sai da suka fito da
kan su suka bayyana irin rawar da suka taka wajen yin
hakan. A shekara ta alif dubu daya da dari tara da
hudu (1904), wani Dan Masoniyya mai suna Mac
Vadora Sambo ya furta wasu kalamai a bainar
jama'a inda ya ce "Masoniyya ta yi aiki tukuru ta
Boyayyiya kuma Jajurtacciyar hanya wajen haifar da
yakin neman 'Yancin kan Faransa, hakan yasa duk
muka yarda cewa Masoniyya tare da samun damar
Kaddamar da wannan Fafutikar ta neman' Yancin kai
tare da yarda da ni da aka yi, ya tabbatar da cewa kun
aminta da ni cewa, Masoniyya ce Ginshikin samun
'Yancin kan Faransa",!!!


A lokacin da iyayen Amurkawan yanzu
suka yada zango a dutsen play mouth, ba wai kala-kalan mutane daban daban kawai suka debo tare da su
ba, har dabi'un Masoniyya ma sun debo. Irin Zaluncin
da iyayen Amurkawan suka guda daga Yurop, sai ga shi
anan ma sun same shi a Karkashin Mulkin Birtaniya.

Domin su sami damar Mulkin wannan sabon wuri, sai
'yan Masoniyya suka yi amfani da irin tuggun da suka
Kullawa Faransawa. Duk da cewa Masarautar Birtaniya
tana Karkashin ikon Masoniyya ne, yakin neman' Yancin
Amurka ya zama dole ne ga 'yan Masoniyya, kuma
wadanda suke wannan yaki zaratan Azzalumai ne
wadanda zasu iya yin komai domin ganin biyan Bukatun su.

Zan ci gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Hãïmâñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*

Share:

TA'ADDANCIN MASONIYYA 06

TA'ADDANCIN MASONIYYA 06

Gurbatattun 'Yan Siyasar da Masoniyya ta tanada kuma
sai suka dinga yada Akidar Masoniyya ta ko ina. Manya
Manyan Lojinan Masoniyya (Masonic Lodges) kuma sai
aka bude su ga Sojojin Faransa, Manyan kasar da
Janarori duk aka dulmiyar da su Izuwa ga Gurbataccen
tunani irin na Masoniyya.

 Lokacin da Masoniyya ta ga
cewa ta kama 'Yan Siyasa, Attajirai da kuma Yawancin
mutanen Faransa a Karkashin ikon ta, sai ta fara
kaddamar da Mummunar Manufar ta.

A Ranar sha hudu
ga watan Yuli shekara ta alif dubu daya da dari bakwai
da Tamanin da Tara (14th July 1789), wasu mutane da
ba'a san ko su waye ba, suka afka gidan yarin Basteel
dake Farisa (Paris). Wannan al'amari ne fa ya tadawa
mutane hankali, akai ta Surutai iri iri Musamman akan
irin raunin Mulkin Masarautar Farisa. Sai dai fushin 'yan
kasar bai samu gushewa ba har sai a shekara ta alif
dubu daya da dari Bakwai da casa'in da uku (1793).

A Ranar Ashirin da daya ga watan Janairu na wannan
Shekarar ce aka sarewa Sarki Louis XV kai a bainar
Jama'a, hakan ne ya kawo karshen Mulkin Gargajiya a
kasar Faransa. Daga nan ne kuma aka sake share
sabuwar hanyar da zata taimakawa Masoniyya wajen
cimma burin ta a Yurop. Bayan faruwar hakan,
Masoniyya gani take tamkar ta gama samun Ragamar
Mulkin kasar Faransa. Sai dai abinda ya biyo baya wani
al'amari ne da yayi matukar girgiza su sannan kuma ya
tayar musu da hankali.

 Wani Matashin Soja da ake kira
Napoleon Bonaparte ne ya taso da nufin mulkar
Faransa ko ta halin kaka. Amma Maimakon ya biyo ta
hannun Masoniyya, kawai sai ya kaddamar da kan shi a
matsayin sabon Sarkin Faransa.
Bayan an tafka yaki ne
daga karshe dai aka matsawa Napoleon har sai da ya
arce daga kan Karagar sa a shekara ta alif dubu daya
da dari takwas da goma sha hudu inda ya gudu Tsibirin
Corcica.

Shekara daya da faruwar hakan, sai ga
Napoleon ya sake bayyana a Farisa yana Tara sabbin
Mayaka domin sake Tunkarar Yurop. To anan fa sai
'yan Masoniyya hankalin su ya tashi, domin kasar
Birtaniya tare da Kawayen ta ba zasu iya jure fada da
Napoleon na tsawon wani lokaci ba face sai sun afka
cikin Matsanancin Talauci.

Zan ci gaba In Shaa Allaah.


<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Hãïmâñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*

Share:

TA'ADDANCIN MASONIYYA 05

TA'ADDANCIN MASONIYYA 05

Wannan sabon suna da kuma sabon tsarin da suka zo
da shi, shi ne ya baiwa Membobin kungiyar cin karen
su babu babbaka ya kuma kara musu kima a idon
duniya. Memba na farko da ya fara bayyana kan sa shi
ne Fredrick Yariman Wales (Fredrick The Prince Of
Wales), daga cikin Membobin su na baya kuma akwai
irin su Prince Philip mai Mulkin Edinborough har zuwa
kan Sarauniyar Ingila ta biyu (Elizabeth II), ita ma
babbar mai lura da Al'amuran kungiyar ce.

 Sai dai kuma, ta bayan fage, 'Yan Masoniyya suna da damar
yin tsafe tsafe, sihiri da Siddabaru.' Yan Masoniyya ba
wai mulkar kasar Birtaniya bane kawai a gaban su. Ina!
Burin su yana da matukar fadi da kuma girma.
A Shekarun da suka biyo bayan Bayyanar su munga
yadda yaki ya barke a tsakanin kasashe da dama da
Amurka. Sai dai duk wadannan abubuwan ba wai
Faruwa suke yi saboda ragwanta ko Sakacin al'umma
ba, a'a wannan ba komai bane face tuggu irin na 'yan
Masoniyya, Mutane ne' yan kalilan amma su ne ke
shirya tashin hankalin da ka iya addabar duniya baki
daya.

Duk wannan artabu zai faru ne daga kasar da
suka tsere daga cikin ta a Shekarun baya, daga nan
kuma Izuwa ga duniya baki daya.
A karni na sha
takwas (18th Century), Yawan cin Mutanen Kasar
Faransa suna fama da Talauci da kuma Karan cin
kayan Masarufi, yayin da Shugabanni da Attajiran su
kuma suke sheke ayar su tare da Almubazzaranci da
dukiya yadda ran su yake so. A Wancan lokacin, akwai
tazara sosai tsakanin mai kudi da Talakan Faransa.
Faruwar hakan ne ya baiwa 'yan Masoniyya damar
shirya wata gadar zare wacce zata canja kasar
Faransa, Canji na har abada. Masoniyya tayi amfani da
fushi da kuma qiyayyar dake tsakanin Jama'ar kasar
Faransa wajen rikita musu tunani. Kamfanonin Jaridu
kuma suka dinga zuga mutane wajen ganin an kau da
Mulkin Gargajiya (na Masarautu) a kuma kafa Siyasar
Dimokuradiyya ta hanyar 'Yanci, Cancanta da kuma
Kwarewa. Tarin Dukiyar da Masoniyya ta tara kuma sai
aka dinga amfani da ita wajen canja Akalalar Siyasar
Faransa tare da Cusawa Shugabanni ra'ayi da kuma
tunani irin na Masoniyanci.

Zan ci gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Hãïmâñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176


*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*

Share:

TA'ADDANCIN MASONIYYA 04

TA'ADDANCIN MASONIYYA 04


A shekara ta Alif dubu daya da dari uku da goma sha
hudu (1314), wannan kungiyar Mayaka ta 'Yan Tampula
(Knights Templers) sai suka hada hannu da Sarki
Robert The Bruce tare da Mayakan sa suka nufi
Ballack Burn domin su gwabza da Mayakan Ingila.

Idanun Sarki Robert sun ga abin mamaki a wannan
yaki, inda zaratan Jaruman Ingila har guda dubu
ASHIRIN da biyar (25,000 men) suka sha kashin tsiya a
hannun mutane dubu shida da doriya. A karshe dai,
kasar Scotland ta samu 'Yancin kai. To tun daga nan
ne fa sai wannan kungiyar Mayaka ta dawowa da kanta
martabar da aka santa da shi a baya ta yadda ba za'a
taba iya karya ta ba, kuma suka sha alwashin ba za'a
kara samun galaba a kansu ba. Sun kuma sha alwashin
su zasu koma juya kasar yadda suke so ta hanyar juya
Sarakunan kasar a tafin hannun su. Sai dai kuma idan
har suna so su cimma wannan buri, to dole ne acikin
biyu ayi daya : ko dai su mutu ko kuma sunan su ya
mutu.

Wadannan Mayaka dai sun samu wajen zama a
Rovelin Chapel na kasar Scotland wanda ya zama
shaidar wanzuwar su a Yankin Birtaniya har Izuwa
wannan lokaci da muke ciki.
A shekara ta Alif dubu
daya da dari shida da uku (1603), mutuwar Sarauniya
Elizabeth ta Farko (Queen Elizabeth I) ya jawo wa Ingila
zama ba tare da Magaji ko Magajiya ba. A bisa dacewa
da Cancanta, Sarki James na biyar (King James V) na
Scotland ya zama Sarkin Ingila a wancan lokacin. Yin
hakan ya sa Scotland da Ingila suka hade wuri daya
suka samar da sabuwar Masarauta. A dalilin hakan, sai
karfin wannan kungiya ya kara habaka ta yadda cikin
sauki suka kama zuciyar Birtaniya. Saboda kwarewa da
suka yi a fannin Munafurci da iya ladabin Kunama, sai
da wannan kungiya ta share sama da shekaru dari tana
aiwatar da Aiyukan ta a Sirrance.

A hankali suka dinga
bacewa daga bakin mutane har ya zamana da qyar ma
ake iya tuna sunan su. Sai dai kuma duk tsawon
wannan lokacin sunyi bakam ne suna ta kutsawa cikin
kowane sako da lungu na kasar.
A shekara ta Alif dubu
daya da dari bakwai da goma sha bakwai (1717),sai ga
shi sun sake bayyana a Yuropiya. Yanzu sun kara yawa
da kuma karfi, kuma a shirye suke su kawo sabon
tsarin samun 'yanci wa kansu daga halin da suka shiga
a baya,tare da samun Cikakken ikon yin hakan daga
Madafan Iko da sauran masu fada a ji na kasar Ingila.

Anan ne suka Laqabawa kansu wani sabon suna, sunan
da kusan kowa ya san shi sai dai ba kowa ya Fahimce
shi ba. Wannan sabon suna shi ne THE FREEMASONS!!
('Yantattun Magina (duniya).
'Yan Masoniyya kenan a
Kungiyance.


Zan ci gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Hãïmâñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*

Share:

TA'ADDANCIN MASONIYYA 03

TA'ADDANCIN MASONIYYA 03

A Jerusalem, a hankali a hankali sai wadannan Mayaka
suka fara ja da baya daga koyarwar addinin Kiristanci,
in da suka koyi dabi'un Kabala, daya daga cikin manya
manyan Sashen tsafe tsafen zamanin Jahiliyya, tare da
yadda ake gudanar da tsafin da kuma yi masa hadaya
(da mutane).

Yahudawa sun koyi wannan tsafin ne
daga Bokayen Misra a lokacin cinikin bayi na zamanin
Sarki Fir’auna, daga baya kuma sai suka daukaka shi Izuwa Babila (Babylon) a zamanin Navakanazar.
A shekara ta Alif dubu daya da dari uku da bakwai
(1307), Sarki Philip na kasar Faransa yasa aka damqe
su bisa zargin su da ake yi da laifin kin yarda da
Almasihu, Luwadi, bautawa gumaka da kuma aikata
tsafe tsafe. A shekara ta Alif dubu daya da dari uku da
goma sha hudu (1314) Fafaroma Claymont na biyar
(Pope Claymont V) ya bayyana cewa duk mazaunan
wadannan Mayaka suna tababa da koyarwar addinin
Kiristanci, sannan ya sa aka kwace dukiyoyin su da
kuma Kadarorin su gaba daya. Shugaban su na wancan
Lokacin mai suna Chek The Moley kuma aka kamo shi
aka qona shi da ranshi a bainar jama'a.
Daga nan
Kungiyar ta Tarwatse. Sai dai kuma a lokacin da ake
tunanin an rushe su gaba daya, ashe ba anan gizo ke
saqar ba, domin wasu daga cikin su sun sami isa ga
tudun mun tsira, inda Suka sami mafaka da kuma
abokan Harkalla, sai dai ba a Faransa wannan dama ta
samu a gare su ba, a wata kasar ce daban wacce a
wancan lokacin ta ke matukar bukatar 'Yancin kai daga
turawan Ingila, wato Scotland.

A tunanin mutane da
dama, burin samun - Yancin kan Scotland ya rushe ne
a Sanadiyyar mutuwar William Wallace, amma ga Sarkin
Scotland na wancan lokacin, Robert The Bruce,
wanzuwar wadannan Mayaka a kasar sa ya samar
masa da wani babban Makami da zai taimaka masa
wajen cimma burin sa. Irin sanin Makama da dabarun
yaki da suke da shi sakamakon artabu da suka sha yi a
baya yasa suka zama zaratan Jarumai a fagen yaki fiye
da duk Mayakan da aka hada su da su.

Zan ci gaba In Shaa Allah


<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Hãïmâñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*

Share:

TA'ADDANCIN MASONIYYA 02

TA'ADDANCIN MASONIYYA 02

Wadannan mutane sun sami sa'ar dulmiyar da mutane
da dama Izuwa ga gurbataccen tunani irin na su.

 Su wadannan mutane suna da qafa a kowane lungu, sako,
kwana Da kuma kowane irin kwararo na rayuwar mutane
a ko ina a cikin fadin duniyar nan.
Duk wani waje da
ake gudanar da wani muhimmin al'amari, to ka tabbatar
cewa suna da jami'ai a wajen. Sannan daga bayan fage
ne suka samu damar bullo da wata sabuwar dokar
siyasa, sabuwar dokar Kasuwanci kuma sabuwar dokar
Addini.

Babban muradin su shi ne su mamaye duniya,
ya zamana kowa su ya ke bi, kuma zasu iya yin KOMAI
don ganin burin su ya Cika.
Tsohon Shugaban kasar
Amurka, biri mai muguwar barna ya taba bayyana cewa
: "wannan shiri da kuke gani ba wai na karamar kasa
ba ce kawai, tunani ne mai fadin gaske, sabon tsarin
duniya", (New World Order).
Yanzu ashe har wani ya
isa ya kawo wani tsari da ya fi na Allah??? Sam bai
Yiwuwa.


Sai dai kuma, asalin wannan shiri na sabon
tsarin duniya (New World Order) ko kuma in ce sabuwar
dokar duniya da ake son kafawa, ba daga fadar Amurka
abin ya soma ba. Asalin shi ya fara ne tun daga wani
katafaren yaki da aka yi a shekara ta alif dubu daya da
casa'in da biyar (1095) a Cleremont da ke kasar
Faransa.

A karni na sha daya (11th Century), Kasar
Yuropiya tana karkashin shugabancin wani babban Coci
ne wanda ya sami babban matsuguni a zukatan dubban
jama'a. Irin wannan karfin mabiya da suka samu ne ya
sa Fafaroma Erwind na biyu (Pope Erwind II) ya samu
damar kaddamar da yaki akan musulman wancan
lokacin domin ya kwato Jerusalem.
A Sanadiyyar
wannan yaki ne aka yiwa matayen Musulmai da yawa
Fyade, sannan aka hallaka su, aka karkashe yara da
tsofaffi har sai da ta kai cewa jinin dake kwaranya a
kasa gab yake da ya kawo guiwoyin dawakan dake filin
yakin.

 Ana cikin wannan yanayi na hatsaniya ne, sai
wata kungiyar Mayaka ta bayyana, Mayakan da suka
kware wurin iya yaki, Mayakan da zasu iya bin kowace Hanya
don ganin burin su ya cika komai runtsi da tsananin
dake cikin yin hakan.
Bayan shekaru ASHIRIN da karbe
Jerusalem daga hannun Musulmai, sai jagorancin
wannan wuri ya fada hannun wadannan Takadiran
Mayaka masu zaman Zuhudi da ake kiran su da 'The
Knights Of The Temple Of Solomon' (wato Mayakan
Majami'ar Salamon) ko kuma 'Knight Templers' kawai
(wato Mayakan Majami'a).
Ni kuma sai na kira su da
suna 'Yan Tampula'.

Zan ci gaba In Shaa Allaah.


<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Hãïmâñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*

Share:

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive