Showing posts with label Masoniyya (New World Order). Show all posts
Showing posts with label Masoniyya (New World Order). Show all posts

Monday, 22 July 2019

TA'ADDANCIN MASONIYYA 20

TA'ADDANCIN MASONIYYA 20

A Yanzu haka akwai Guraben na'urar tauraron dan Adam (Satellite) na
duniya gaba daya guda Arba'in da Takwas a ORBIT
wadanda Amurka da Kawayen ta suke amfani da su.
Wadannan Satalayitoti na iya karbar Siginoni kuma su
bada Cikakken Bayani ga gurbin Satalayit din da kuma
inda Siginar take.

 A yanzu haka, Guraben da Siginonin
suke Na'urori ne da ake manna su a jikin Tankuna,
Jiragen Yaki da na Sufuri ko kuma a hannu da akanyi
amfani da su don Tabbatar da tsaro dangane da
abubuwan da ke kusa da su. Mataki na gaba da
Masoniyya zata dauka shi ne, a Gabatar da Na'urar da
zata samar da wannan Siginar ga kowane dan Adam. A
Yanzu haka akwai irin wannan Na'urar, itace suka
Sanyawa suna (Electronic Tag) kuma tuni har an fara
amfani da wannan Na'urar a UK.

 Dalilin kirkirar ta kuwa
shi ne, don saboda a san halin da 'Yan gidan yari suke
ciki. Akan Sanyawa masu laifi wannan Na'ura ce a
hannu ko kafa, ta yadda akwai iya inda aka Kayyade
mai da ya je, yana wuce wurin koda da taku daya ne
zata tona shi. Ka kalli film din DISTURBIA don ganin
Misalin irin Na'urar.

 Amfani da wannan Na'ura ga
Direbobin Jirage kuwa tuni har ya zama ruwan dare a
Manchester, Bark Shaw da Norfolk, akwai kuma shirin
ganin an Fadada abin zuwa ga sauran Kasashe nan da
shekaru masu zuwa. A wani rubutu da Jaridar Daily
Telegraph tayi a ranar sha uku ga watan Nuwamba a
Shekara ta alif dubu daya da dari tara da Casa'in da
Bakwai (13-10-2016 November 1997), Jack Straw,
Sakataren gida na Birtaniya a wancan lokacin Ya ce :
''Electronic Tagging dinnan ya samu karbuwa cikin sauri
sosai a 'Yan shekaru kadan, saboda mutane sun Aminta
da shi!! Kaga kenan idan har mutane suna yarda da irin
wadannan abubuwan to fa tamkar suna mika kansu ne
zuwa ga ' Yan Masoniyya, sai dai kuma ba lallai bane
mutum ya iya gujewa irin wannan Sharrin domin
Tuntuni dama sun riga sun gurbata masa zuciya ta
yadda bai da wani zabi face abinda suka Gabatar masa
da shi kuma ba tare da ya sani ba.

 Yakar tunanin
mutane suke yi ta yadda daga baya duk abin da suka zo
da shi sai su karba tare da tunanin ci gaba ne. Sai dai
fa mu sani, duk abinda Masoniyya zata yi, to da Fuska
biyu take yin sa, kuma duk irin abinda ka gani a bayyane, to ka tabbatar cewa akasin sa zaka taras a daya barin.

Zan ci gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com

TA'ADDANCIN MASONIYYA 19

TA'ADDANCIN MASONIYYA 19

To idan har suna da wadancan bayanan da na fada
akan kusan kowa da kowa, kati daya mai dauke da
dukkan wadannan bayanan da ma wasun su zai basu
wata Muhimmiyar dama wajen sanin yadda zasu juya
mutane yadda suke so a Saukake.. Hakan kuma zai
basu damar tattara duk wani bayani karami da babba
na kowa a cikin kowace irin al'umma.

 Bayanan sune
zasu basu damar Kaddamarwa, Gudanarwa tare da
tafiyar da Miyagun Kudurorin su a cikin al'umma. Sai
dai kuma akwai wani gurbi da dole Yan Masoniyya sai
sun cike shi idan har suna so su sami Nasara. Ta
hanyar yin amfani da Zunzurutun kudi ko kuma ince
Madarar kudi, mutum na iya kaucewa binciken da suke
yi na dan wani lokaci. Saboda babu wata Na'ura da
zata iya gano yadda akayi da ruwan kudi. Kaga kenan
bayanan duk cinikayyar da akayi da wannan kudin sun
gudu musu kenan. Akan hakan, Masoniyya ta dauki
wani mataki wajen ganin ta maye gurbin amfani da
ruwan kudi Izuwa ga tsarin da ya dogara kacokan akan
Sufurin kudi na Na'ura ko kuma ince tsarin da ya
dogara akan amfani da kati (Cards /Electronic
Transfer). Wannan shiri tuni ya fara aiki a UK.

Jadawalin Mondex (The Mondex Scheme) wanda
Bankunan tsakiyar yamma tare da Ma'aikatar Sadarwa
ta Birtaniya suka fitar shi ne farkon alamar tabbatuwar
wannan Simatin kati (Smart Card ). A cikin kowane
Simatin Kati akwai wata 'Yar karamar Na'ura da ake
kira Micro Chip wacce take Kirgawa tare da ajiye duk
wani abu da aka yi da ita, ba wai sai Cinikayyar da
akayi da katin ba kawai, a'a duk wani abu da akayi da
katin. Wannan kati zai iya zama ATM, Katin Mallakar
gida, katin zama dan kasa da dai sauransu. Sai dai
kuma duk da cewa katin Shaidar zama dan kasa ka iya
bada irin wadannan bayanai, ba zai iya gano ko
bayyana inda mutum yake a cikin dan Kankanin lokaci
ba, dole ne sai an bukaci wata irin Na'urar gano
abubuwa, ko kuma ince Mayyar Na'ura (Tracking
Device) da za'a iya sawa don gano duk inda wannan
mutumin yake a fadin duniya.

Duk iya Hayaniyar da
Za'a yi, dole ne wannan Mayyar Na'ura ta zama yar
karama wacce za'a sa a katin ko kuma a Sanyawa
mutum a cikin jikin shi. In aka Sanyawa mutum zata
bada sigina wacce na'urar tauraron dan Adam da ke kasa kasa da
wannan duniyar Tamu zata dauka kuma ta gano inda
wannan sigina take tare da bayyana wanda wannan
sigina take jikin sa. Ko da yake wannan bayani zai
zama tamkar wani shirin fim, wannan shiri ne na
Masoniyya wanda yana nan tafe,kuma duk mai tsawon
rai zai gani da idanunsa.

 Sai dai kuma ga wani misali
Bayyananne, a yanzu an sami wani irin ci gaba ta
yadda idan akace misali yau kana aiki a wani kamfani
ne ko wata Ma'aikata da take biyan Ma'aikatanta ta
Banki, idan wata ta kare kudin naka asusun ka na
Banki zasu wuce kai tsaye, idan ya shiga kai kuma kana
daga zaune a gida zaka iya hawa online kayi Sayayya
da wannan kudi naka dake cikin asusun ba tare da
ka je da kanka ka taba su ba, iya ka kawai da kunyi
ciniki sai su kawo maka kayan har kofar gida kai kuma
sai ka tura musu kudin ta nasu Asusun din.

 To ci gaba
ne ya zo gaskiya, kuma sauki ne ya samu a gare mu, to amma
baka tunanin a cikin irin wannan abubuwan akwai kuma
abinda suke kokarin bullo da shi???

 Zan Ci Gaba In
Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com

TA'ADDANCIN MASONIYYA 18

TA'ADDANCIN MASONIYYA 18


Aikata Ta'addanci, Yaduwar Laifuka, Tashin Hankali da Jagaliyanci kullum su ake nuna mana a cikin Fina Finai da sauran Kafafen yada bayanai, Rahotanni daga Gwamnati duk sun zama kusan iri daya. Yin hakan kan jawo tausayawa a cikin al'umma tare da bukatar ganin an yi amfani da kowace hanya wajen Murkushe wadannan 'Yan Ta'adda musamman ta hanyar amfani da Na'urorin leken Asiri. A dalilin haka ne yasa Sabbin Na'urori suke ta kara bayyana, kuma nan bada Jimawa ba za'a kai wani mataki da duk wani motsin mutum ana iya sanin shi.

Ra'ayin mutane dai har iyau za'a kara karkatar da shi domin a baiwa 'Yan Masoniyya damar cin karen su babu Babbaka. Samun damar juya mutane ta hanyar ajiye bayanan kowane mutum a wata Babbar Ma'ajiyar bayanai yana nan tafe akan hanya. A yanzu haka akwai wani shiri da ake yi na ganin an tara bayanan mutane irin su bayanan Banki (Banking Details), Lasisin tuki (Driver's Licence), da sauran bayanai Makamantan haka waje daya. A da, duk wadannan bayanai da ma wasun su, suna zaune a wurare daban daban ne a jikin Katuna Mabanbanta, to amma yanzu ana nan ana shirin tara dukkan wadannan bayanai a jikin kati kwaya daya tak!!

Matukar akai hakan, to abinda zai biyo baya shi ne, za'a iya ganin komai game da kowa a cikin rabin minti. A shekara ta alif dubu daya da dari tara da da Casa'in da biyu (1992), Mataimakin kansilan kotun Birtaniya Nicholas Brown Mulkinson ya fadawa kotun cewa idan dai har akace bayanan da 'Yan Sanda suke da shi na Rabano, harkokin Kasuwanci, bayanan lafiya da sauransu za'a tara su waje guda, to ' 'Yancin wannan mutumin fa yana cikin Hadari.

Sai dai kuma Masoniyya Karkashin Gwamnatin da suka kafa kuma suke juyawa tuni suna da Muhimman bayanai akan ka. Sun riga sun san da wa kake magana a waya, inda kake aiki, inda kake Siyayya, abinda kake ci (favorite food kawai), kayan da kake sawa, iya kudin da kake da shi, Kadarar daka Mallaka, Nawa kake samu da dai sauransu. Kuma suna samun wadannan bayanai ne ta hanyar Forms da muke cikawa na hannu da kuma online da kuma bayanan da 'yan leken asirin su ke kai musu. Mafi sauki kuma a yanzu VBN number.

Zan ci gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com

TA'ADDANCIN MASONIYYA 17

TA'ADDANCIN MASONIYYA 17
A Tarihance, 'Yan Masoniyya sun sha Kirkirar Matsaloli
da tashe tashen Hankula iri iri domin su cimma wata
manufa tasu. Yawaitar Miyagun Kwayoyi a Amurka ya
baiwa Gwamnatin kasar damar yin amfani da Muggan
Makamai da kuma shirye shirye don ganin an cimma
matsaya. Rikita al'amura, daukar Muggan matakai,
amfani da karfin Gwamnati wajen bijiro da bukatar
kariyar kai da kai da kuma na kasa baki daya, Yawaitar
Ta Addanci a cikin al'umma, shaye - shaye da sauran
abubuwa Makamantan haka su ne ke taimakawa
Masoniyya wajen gudanar da aikin ta a Saukake.
Wannan dalili ne ya sa Ta Addanci yayi yawa, da
gangan suke Kirkirar rigima don a tunanin su idan mun
shiga Bala'i, idan suka kawo mana dauki zamu amsa in
yaso daga baya sai su nemi yarjewar mu akan abinda
zai jawo Rushewar mu gaba daya in yaso daga baya
mu zo muna da na sani mara amfani, domin Amsar
taimakon su a irin wannan lokaci dai dai ya ke da ace
ka gudu don kada a harbe ka da bindiga ka fadawa
bom. Ci gaba da ake ta samu a fannin Kimiyyar kere-
kere (Technological Advancement), ita ma wata
Shafaffiyar hanya ce da ta baiwa 'Yan Masoniyya
damar cin karen su babu babbaka, domin hanyar tana
basu damar bibiyar aikin kowane mutum, bincike akan
sa d kuma ajiye bayanan. Bayanai sune makullan su,
iya bayanan da suke da shi dangane da mutum, iya
damar da suke da ita kenan wajen gudanar da aikin su
kai tsaye, kuma wannan bayani ne zai basu damar
Dulmiyar da mutane yadda suke so. Masoniyya tana
kokarin Kirkirar wasu irin al'umma ne wadanda zai
Zamana basu da wani zabi face Abin da aka zabar
musu, in ma kuma har akwai zabin to zabi ne daga
Gurbatacciyar Zuciya. Kirkirarrun abubuwa gasu nan
suna ta takaitar maka da zabin ka, idan kuma kana da
zabin to ta iya Yiwuwa zabi ne da aka cusa maka
Aranka ba tare da ka sani ba, kuma dama so akeyi
wannan zabi naka ya kaika wani mataki, matakin da sai
yadda aka yi da kai. Juya Talakawa tare da Sauran
masu hannu da Shuni ko kuma masu fada aji, yana
nufin juya kowane bangare na rayuwar al'umma ne.
Masoniyya ta san hakan, shi yasa ma take kokarin
ganin ta kama kowane fanni ko bangare na kowane irin
Abu da mutane ke yi. Hatta a Malaman Addini ma
akwai 'Yan Masoniyya. Allah Ya kiyaye mu Ameen. Zan
ci gaba In Shaa Allah

🔰🔰🔰
Haiman Khan Raees @HaimanRaees
08185819176
Haimanraees@gmail.com 

Saturday, 6 July 2019

TA'ADDANCIN MASONIYYA 16

TA'ADDANCIN MASONIYYA 16


Wani Salon Yakin Sunkuru kuma da Masoniyya ke
amfani da shi wajen ganin sun cimma burin su shi ne,
kyale ko barin Ta'addanci ya wanzu a cikin jama'a, a wani lokacin ma harda daukar nauyin TA'ADDANCIN!
Hakan zai Wanzar da tsoro tare da bukatar kariya ta kai
da kai da kuma ta kasa baki daya.

 A wani bincike da
aka gudanar, an gano cewa, Kamfanonin dake hada
Miyagun Kwayoyi na daya daga cikin Kamfanonin da
suka fi kowa samun riba a Kasuwance. Kasashen
duniya da dama na nan suna ta fama wajen ganin sun
kawar da Matsalar Safarar kayan maye, kama daga cikin
gida har Izuwa sauran Kasashen ketare domin Safarar
Miyagun Kwayoyi ta addabi mutane.

 Amurka misali,
cike take da Matsalar Safarar Miyagun Kwayoyi da
sauran kayan maye, wannan na daya daga cikin dalilan
da suka sa Ta'addanci iri iri ke afkuwa a Kasar kamar
ba gobe. Saboda ganin goyon baya da kuma daurin
gindi da da Gwamnatin Amurka ta samu a wajen jama'a
don ganin an dau Tsatstsauran Mataki akan wannan
matsala ce yasa Gwamnatin yin amfani da Muggan
Makamai da kuma Miyagun Shirye Shirye don ganin an
Magance wannan Matsala a fili ko a bayyane. Sai dai
kuma Bayyanar wasu abubuwa da suka faru ta bayan
fage sun sa mutane sun fara Daurawa Gwamnatin
alamar Tambaya. Musamman dangane da irin Shirye
Shiryen da Gwamnatin ke yi akan wannan Al'amari.


Kusan kowa Yasan cewa a shekara ta alif dubu daya da
dari tara da sittin (1960) J. Edgar Hoover wanda shi ne
Ciyaman din FBI na wancan lokacin ya bar siye da siyar
da Miyagun Kwayoyi da kayan maye yana ta Wanzuwa
da gangan a tsakanin Bakaken fatar dake zaune a
kasar Amurka domin ayi musu kofar rago wajen dai
daitar da su saboda yawa da kuma karfin da ake ganin
suke Karawa a kullum. A Shekara ta alif dubu daya da
dari tara da tamanin (1980) , lokacin da Kwamunisanci
ya kusan Mamaye tsakiyar Amurka, sai ya Zamana ana
bukatar kudi Haikan domin a samar d Makaman Yakar
'Yan Kwamunisanci, don haka sai CIA suka bar siyar da
Miyagun Kwayoyi da sauran kayan maye sukai ta
Yawaita a cikin Amurka. Ta nan ne suka sami kudin
siyen wadannan Makamai da kuma kera wasun su.

Bayanai daga bakin Sanatan Amurka Jack Bloom
wanda yana daya daga cikin 'Yan Kwamitin bincike
akan wannan Lamarin ya tabbatar da faruwar hakan.

Zan ci gaba In Shaa Allah.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com

TA'ADDANCIN MASONIYYA 15

TA'ADDANCIN MASONIYYA 15

Misali na gaba kuma dangane da Fina Finan da suke
bayyana shiri da kuma Kudurorin Masoniyya shi ne wani
Fim mai suna "Independence Day", wannan Fim ya
kafa Tarihi iri iri a lokacin da ya fito har sai da ya zama
Fim na bakwai da ya fi kowane Fim kawo kudi a
Masana'antar Fina Finan duniya gaba daya. Wannan Fim yana
dauke da wani Kagaggen labari ne na wasu bakin
haure (Aliens) da suka kawo wa duniyar mu hari, sai dai a
takaice, wannan Fim cike yake da Manufofin
Masoniyya.

A cikin wannan Fim, akwai wani Shashen
Dakarun Sojoji da akewa Lakabi da Area 51, daga
wannan wuri ne ake samar da duk wani shiri na Soji,
kuma anan ne ake samo Maslahar duk wata matsala ko
Damuwa da ta addabi duniya da abinda ke cikin ta. A
Mashigar wannan wuri, ido dayan Masoniyya ne a jiki. A
cikin wannan Fim, an nuna Amurka a matsayin ja gaba
wajen samar da kariya ga kowace kasa da wani hadari
da ya Shafeta. Wannan Tawaga mutum daya ne yake
Jagorantarta, mutum daya Tak!!!

 Bugu da kari, Fim Din
yana daya daga cikin Fina Finai da kuma Shirye Shiryen
gidan Talabijin (Season Films) da ake yi dangane da
bakin Haure da ake cewa zasu zo zasu zo kamar su
Aliens, UFO da kuma harin da ake cewa wai zasu kawo
wa duniyar mutane domin ganin bayan mutane gaba
daya (Ka Kalli wani Fim mai suna WARCRAFT wanda
aka Fassara shi da Hausa aka sa mishi suna YAHUDU
don ganin misalin a bayyane ).

 Irin wadannan Fina Finai
ne ke kara hura wutar Fargaba a cikin zukatan al'umma
tare da Ingiza su wajen Tanadar Makaman Yakin kare
dangi don ayi maganin Matsalar idan ta taso. Wannan
ma daya ce daga cikin Dubunnan hanyoyin da
Masoniyya ke amfani da su wajen ganin sun tabbatar
da wanzuwar gwammati guda daya tak a duniya,kuma a
Karkashin ikon mutum daya jal.

 Masoniyya na amfani
da Hanyoyi da dama wajen Cusawa mutane tsoro a
zukatan su tare da bukatar kariya ta din din din,
wannan kuma bukatace da da take bukatar hadin
guiwar dukkan sauran Shuwagabannin duniya baki daya
domin ganin an kawar da Matsalar da ka iya afkawa
kowa da komai, in ya so daga baya sai su zo su yi
kokarin kawo dauki ko kuma maslaha tare da neman
hadin kai, bayan kuma su suka shiryo tsiyar da Masifar
suka turo muku.

Duk kasar da suka yarda suka bada goyon baya to za su dinga juya su yadda suka ga dama ta hanyar juya shugabannin su. Kasar kuma da taki, za'a ci gaba da gallaza mata tare da bin duk wata hanyar da zasu iya Bi wajen ganin sun jefa kasar cikin BALA'I. Ga Libya nan dai yadda ta Koma yanzu, ita kadai ta ishi kowa misali.
Allaah Ya Tsare mana imaninmu ya rabamu ya rabamu da kafirci.

Zan ci gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com

TA'ADDANCIN MASONIYYA 14

TA'ADDANCIN MASONIYYA 14

Manufofin Masoniyya da dama da ake yada su ta hanyar Fina Finai da Makamantan su a sauran Kafafen yada bayanai (Mass Media) sun fi isa kai tsaye ga mutane fiye da sauran Hanyoyin. Ta wannan hanya ne suka juyarwa da mutane da dama tunanin su tare da kokarin ganin sun wanzar da tsarin su na gwammati kwaya daya da zata mulki duniya da kuma shugaba daya Tal da zai mulki duniya gaba dayan ta. Fitaccen marubucin nan mai suna Rudyard Kripling wanda shi ma dan Masoniyya ne, ya yi kaurin suna sosai da littafin sa mai suna "The Jungle Book", sannan shi ne ya rubuta wani littafi mai suna "The Man Who Would One Day Be King", wannan littafi ya samu karbuwa sosai inda daga baya aka maida shi Kasurgumin Fim Din Hollywood wanda Sean Connery, Michael Kane da Saed Jaffery suka fito a cikin sa.

Labari ne akan wasu Sojoji guda biyu da sukayi wata doguwar tafiya Izuwa wani gari da ke can kusa da India, akwai rade-radin cewa a wannan garin akwai tarin makudan dukiya da kadarori Mallakin Tsohon Sarki Alexander The Great. Lokacin da suka isa wannan gari, sai mutanen garin wadanda ake kira KAFIRS suka kama su, ana gab da za'a kashe su, sai aka ga wata sarka a wuyan daya daga cikin su wacce take dauke da tambarin ido dayan Masoniyya a jikin ta. Ganin wannan sarka ce yasa dukkan mutanen wannan gari suka maida shi abin Bautar su. Shi kanshi mutumin da farko bai yarda cewa shi Ubangiji bane, amma daga baya, ganin irin yadda suke Girmama shi yasa ya fara tunanin lallai shi ma fa Ubangiji ne.

 Irin wadannan Mugayen Kaba'irori ne ake nuna mana a Fina Finai da dama, sau tari zaka ga mutum ya rufe ido daya ya bar daya, shin ko kasan me hakan yake nufi??? Hakan yana nufin shi Mabiyin Masoniyya ne, idan kuma ba haka to Sun cusa masa irin Ra'ayinsu ne a Zuciyar sa ba tare da ya sani ba ko kuma yana sane so yake yi su jawo shi cikin su.

Abin Takaicin shi ne, da yawan mutane sukan yi irin wadannan alamu na Masoniyya ba take da sun san Ma'anar abinda suke yin ba, sannan akwai kuma masu yi da gangan don neman suna ko wani abu makamancin haka. To wadannan, bani da damar in ce musu 'yan Masoniyya ne su, amma dai tabbas ya kamata musan me muke kallo, kuma me muke barin 'Ya'yan mu suke kallo. Domin Yahudawa Makiyan mu ne, kuma Masoniyya ba abar koyi bace.

Zan Ci gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com