Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

Showing posts with label Others. Show all posts
Showing posts with label Others. Show all posts

SHAWARWARI 7 GA MASU KASUWACI A YANAR GIZO


SHAWARWARI 7 GA MASU KASUWANCI A YANAR GIZO

Akwai wasu shawarwari guda Bakwai da nake ganin in masu kasuwanci a yanar gizo "Online Business" suka bi su In sha Allahu zasu yi kasuwancinsu cikin nasara.

1- Ya zaman to akwai kyakkyawar alaƙa tsakaninka da masu sayen kayanka, kar ya zaman to cewa baka kula da kwastomomi, misali wani zai iya sayen kaya a wajenka amma ba tare da ko lambarshi ka aje a wayarka ba, duk lokacin da kwastoma ɗin nan naka, ya fahimci cewar ko lambarshi baka damu daka aje ba, daga lokacin zai ji a ranshi cewa baka ɗauke shi da muhimmanci ba, ƙila daga nan kasuwancinku ya datse, ko kuma zai dinga kasuwancin da kai ba tare da yana jin daɗin yin kasuwancin da kai ba.

2- Ka kasance kana da Specific time na tallata hajarka a yanar gizo, ba wai Any how kace zaka yi posting ba, wannan zai sa mutananka dake bibiyarka su sa a ran su cewa, ko wall ɗinka suka zo ba zasu tarar da komai ba sai talla, daga lokacin zasu rage karsashin son zuwa duba abinda ka rubuta. 

3- Ka dinga yiwa kwastomominka reply idan sun maka comment koda tsokanarka suka yi, ba wai dole sai sun yi magana kan abinda kayi posting ɗin ba, wani sanadiyyar sakin fuskarka zai iya zuwa ya sayi kayanka.

4- Entertainment ka dinga nishaɗantar da al'ummarka yana jawo mutane a rayuwa, musamman a kasuwanci.

5-Sa Muhawara ko kacici-kacici yana jawowa Business Page ɗinka mutane musamman ka dinga saka 'yar kyauta ko yane.

6- Cimma gaci ga abinda kake son yi, misali sai ince ina son nan da ƙarshen December kowa a Facebook friends ɗina ya san ina sayar da sabulu, ta ya zan yi kowa ya sani? 
Ta hanyar tsara talla mai ɗaukar hankalin jama'a akai-akai.

7-Tagged Audience, Yana taimakawa wajen kasuwanci sosai ba kaɗan ba a yanar gizo, misali in ce ina son Shafina na kasuwanci kafin nan da January 2021 ya kai mutane dubu ko fiye da haka, wannan dole sai na tashi tsaye wajen saka abubuwan da jama'a suke so kafin in samu mutanan da nake buƙata nan da January.

Ku sani yin kasuwanci a yanar gizo ilimi ne mai girma da faɗi, in ka fahimce shi kuma kana yin shi a ilimance ba ƙaramin mamakin yadda zaka dinga sayar da kayanka zaka yi ba. Komai a rayuwa yana son tsari da bin matakan yin sa.

-Zaidu Ibrahim Barmo
CEO/Mujallar Zauren Marubuta.
Share:

WANI SHASHANCI


WANI SHASHANCI DA MUTANEN YANKIN IFRIKIYA SUKA MAIDA SHI BA KOMAI BA:

Idan ɗan ƙasar Faransa bai iya turanci ba, 'yan Afirka sai su girmama shi. 

Idan ɗan Sipaniya bai iya turanci ba, 'yan Afirka sai su girmama shi. 

Yayinda ɗan ƙasar Sin ya zamana bai iya turanci ba, shi ma sai 'yan Afirka su girmama shi. 

Idan ɗan ƙasar Rasha bai iya turanci ba, sai 'yan Afirka su girmama shi. 

Kai ɗan kowace ƙasa daga cikin ƙasashen turai in bai iya turanci ba 'yan Afirka girmama shi suke yi. 

Amma idan ɗan uwansu ɗan Afirka ya zama bai iya turanci ba, sai su maida shi sakarai, daƙiƙi, jahili, soko kuma wawa. 

Wannan shi ne matakin shashanci mafi girma da muke fama da shi a matsayinmu na mutane. Muna amfani da iya turanci wajen gwada baiwa da karamar mutanenmu, har ma da yara ƙanana. 

A makarantunmu, ana sa yara su ji cewa su banzaye ne kuma wawayen da basu da amfani kawai saboda ba su iya magana da harshen da ba su tashi da shi ba a yankunansu. 

Ya ku 'yan Afirka, mu daƙile wannan mummunar ɗabi'ar daga yaɗuwa a ƙwaƙwalenmu da kuma al'ummarmu. Mu koyar da yaranmu harshensu na gado kuma mu bar sauran jama'ar da ke zagaye damu su yi magana da harsunansu cikin 'yanci da aminci ba tare da tsangwama ba. 

Kada mu bawa azzalumai gudunmuwa wajen aikata zalunci akan 'yan uwanmu. 

Idan har ka amfana da wannan saƙo, kana iya turawa wasu domin su amfana, amma a tunanina kowa daga cikin jama'armu yana buƙatar ya ji wannan maganar. 

Na barku lafiya. 


Mu so junanmu, domin junanmu. 

Kyakkywan tunani, kyakkywar rayuwa. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

BAN HAƘURI


BAN HAƘURI

Assalamu alaikum Warahamatullah Wabarakatuhu. 'yan uwa da abokan arziƙi na nesa da na kusa ina muku Barka da warhaka tare da fatan kuna lafiya.

A watannin baya na sanar da cewa masu so in fassara musu waƙoƙi su turo da sunayen waƙoƙin domin in fassara musu in na samu hali. To mutane da dama sun turo nasu, sai dai an yi rashin sa'a na rasa list ɗin, hakan ya sa bani da sunayen a tare da ni. Da haka nake ba kowa haƙuri tare da fatan za a sake turo sunayen waƙoƙin domin na fara shirya sabon list. Amma a daure a rubuta cikakken sunan waƙa da kyau.

Nagode, Allah ya bar zumunci.

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

TAYA KAI MURNA


TAYA KAI MURNA 2

Assalamu alaikum Warahamatullah Wabarakatuhu. Ina mai farin cikin sanar da ku cewa a yau nake taya kaina murna sakamakon na fassara waƙoƙin fina-finan Indiya har guda ɗari biyu. 

Ga sunayen waƙoƙin kamar haka:

 1. Udi Udi Jaye
 2. Vachaadayyo Saami
 3. Yeh Fitoor Mera
 4. Zinda Hai
 5. Tere Sang Yaara
 6. Tu Hi Tu (male)
 7. World Dance Medley
 8. Tay Hai
 9. Teri Meri Kahani
10. Ruk Ja O Dil Deewane
11. Teri Khushboo
12. Zinda 
13. Yaad Aa Raha Hai
14. O Zaalima
15. Kal Ho Na Ho (Title Track)
16. Mar Jaayen
17. Mohenjo Mohenjo Daro
18. Main Yahan Hoon
19. Kaabil Hoon (Title Track)
20. Main Teri Yaadon Mein
21. Main Hoon Don
22. Mere Humsafar
23. Humdard
24. Dhoom Machale Dhoom
25. Aithey Aa
26. Dil To Pagal Hai (Title Track)
27. Ae Dil Hai Mushkil (Title Track)
28. Aap Mujhe Achche Lagne Lage (Title Track)
29. Aaja Mahiya
30. Ishaara
31. Aaraha Hoon Palatke
32. God Allah Aur Bhagwan
33. Mere Naam Tu
34. Muskurane
35. Chinta Ta Ta Chita Chita
36. Hoor
37. Aaj Phir Jeene Ki Tamanna
38. Khuda Haafiz
39. Khel Khel Mein
40. Ek Number
41. Enu Naam Che Raees
42. SubhanAllah
43. Suraj Hua Maddham
44. Saari Saari Raat
45. Saware
46. Selfie Lelere
47. Tum Hi Ho
48. Slow Motion
49. Sanam Re (Title Track) 
50. Sanam Teri Kasam (Title Track)
51. Saanson Ki Mala
52. Sanson Ke
53. Sun Saathiya
54. Tu Milade
55. Sardar Gabbar Singh
56. Selfish
57. Sun Raha hai na tu (Female)
58. India Waale
59. Aankhein Khuli
60. Main Qaidi Number 796
61. Chahun Main Ya Na
62. Chicken Kuk-doo-koo
63. Adhuri Zindagi
64. Ae Zindagi Gale Laga Le
65. Kaho Naa Pyar Hai (Title Track)
66. Kabhi Jo Badal Barse
67. Kheech Meri Photo
68. Chakde India (Title Track)
69. Hawayein
70. Aaj Din Chadheya
71. Tu Hi Junoon
72. Ranga Ranga Rangasthalana
73. Panchadara Bomma Bomma
74. Tere Liye
75. Jab Tak Hai Jaan (Poem
76. Bewaja
77. Badla (Title Track)
78. Jiya Re
79. Kya Khoya
80. Khwahishein
81. Aaya Tere Dar Par
82. Haule Haule
83. Chhapaak (Title Track) 
84. Mehbooba Mehbooba
85. Baatein Yeh Kabhina
86. Mahanati
87. Bole Chudiyan
88. Bhai Bhai
89. Bhula Dena
90. Hasi Bangaye
91. Hum Mar Jayenge
92. Saans
93. Saans (Reprise)
94. Sajan Teri Dulhan
95. Tum Todo Na (Male)
96. Dil Tu Hi Bataa
97. Dhoom Dhaam
98. O Maa meri Maa
99. Jeene Laga Hoon
100. Bande Hain Hum Uske
101. Dil Na Diya
102. Chunar
103. Chand Sifarish
104. Dhingana
105. Aaj Zid
106. Aaj Se Teri
107. Kamli
108. Awari
109. Aaj Unse Milna Hai
110. Hamari Adhuri Kahani
111. Hai Dil Ye Mera
112. Challa
113. Ajab Si
114. Dangal Dangal
115. Dil Diyan Gallan
116. O Saathi
117. O Mere Dil Ke Chain 
118. Pal Pal Dil Ke Paas (Title Song)
119. O Khuda
120. Dandalayya
121. Tu Jo Mila
122. Phir Milenge chalte chalte
123. Piya Aaye Na
124. Prem Ratan Dhan Payo (Title Track)
125. Dil Cheez Tujhe Dedi
126. Teri Meri
127. Pehla Pyaar
128. Tujh Mein Rab Dikhta Hai
129. Tu meri
130. Tu Chale
131. Tujhe Dekha To
132. Rise Of Sultan
133. Tujhe Kitna Chahne Lage
134. Rozana
135. Rang Laal
136. Tu Hai Ki Nahi
137. Tu Chahiye
138. Teri Mitti
139. Shayad
140. Sooraj Dooba Hain Yaaron
141. Satakli
142. Tehra Chehra
143. Saat Samundar Paar
144. Tujhe Kitna Chahein Aur
145. Alizeh
146. Intezari
147. Dil Bechara(Title Track)
148. Bharat Ane Nenu (The Song Of Bharat) 
149. Bholi Si Surat
150. Be Intehaan
151. Bhar Do Jholi Meri
152. Jaana Ve
153. Baaton Ko Teri
154. Jai Jai Shivshankar
155. Bombay Talkies (Title Track)
156. Jiya
157. Dastaan-E-Om Shanti Om
158. Jabra Fan
159. Jeena Jeena
160. Jeete Hain Chal
161. Jaadu Teri Nazar
162. Jeeva Nadhi
163. Janam Janam
164. Jaaneman Jaaneman
165. Jalte Diye
166. Jashn-e-ishqa
167. Aye Khuda
168. Mirchi Mirchi
169. Main Hoon Hero Tera
170. Chaoro (Lori)
171. Aasan Nahi Yahan
172. Guzaarish
173. Meri Aashiqui
174. Milne Hai Mujhse Aayi
175. Chikni Chameli
176. Galliyan
177. Manwa Lage
178. Gerua
179. Agar Main Ka Hoon
180. Agar Tum Saath Ho
181. Channa Mereya 
182. Naina
183. Bandeya
184. Butta Bomma
185. Lo Safar
186. Ziddi Dil
187. The Padman Song
188. Kuch Din
189. Toilet Ek Jugaad
190. Shaitan Ka Saala
191. Tujh Mein Rab Dikhta Hai (Female)
192. Tu Hi Toh Hai
193. Tera Hua
194. Hum Tumse Na Kuchh
195. Tum Hi Aana
196. Tu Meri Zindagi Hai
197. Koi Tumsa Nahin
198. Dheere Dheere Se
199. Rangamma Mangamma
200. Zubi Zubi
Share:

Yi Haƙuri


YI HAƘURI

Daga Phisio Tim YouTube channel video 

Fassarawa

 Jamilu Abdurrahman 


Yi haƙuri!

Barka da zuwa zamanin mutane masu girman kai. Zamanin da mutanensa kan iya yarda su rasa alaƙar da suka yi shekara ɗaya zuwa uku suna ginawa, kawai saboda yi haƙuri!

Zamanin mutanen da mace ta gwammace ta kwashe kayanta daga gidan mijinta ta koma gidan iyayenta a maimakon ta ce: yi haƙuri!

Zamanin da namiji ya gwammace ya rasa iyalinsa matuƙar zai samu jin cewa shi ya fi wani. 

Barka da zuwa zamanin da mutanensa kowa akan dai-dai yake. Zamanin da mutanensa ba sa taɓa yarda sun yi kuskure, zamanin da mutanensa suka san komai. Zamanin da mutanensa su ke ganin cewa sun isa, alhali sun jahilci yadda za su jure zama da juna. 

Zamanin da mutanensa suka gwammace su yi ta gardama na tsawon shekaru a maimakon su furta kalmar yi haƙuri!

Barka da zuwa zamanin da mutanensa suke ɗaura wa wasu laifukansu. Zamanin da mutanensa ke ganin su ke kan dai-dai a koyaushe kuma suke ƙoƙarin yi wa wasu hukunci.

Zamanin da mutanensa ke ganin rashin dai-dai a tattare da wasu kawai banda kawunansu. Zamanin da mutanensa suka gwammace su yi ta gardama a maimakon su ce: yi haƙuri!

Barka da zuwa zamanin da mutanensa ke taƙama da son kai. Zamanin da mutanen cikinsa ke so ko da yaushe mutane su ke basu haƙuri. Zamanin da mutanensa saboda ganin mutuncin kawunansu suka gwammace su ci gaba da rayuwa ba tare da wasu da Allah ya turo musu ba, maimakon su yi sulhu da abokan zaman su. 

Zamanin da mutanen cikinsa suka gwammace su yi baran-baran da abokansu da masu taimakonsu a maimakon su ce yi haƙuri ka manta da aibu na. 

Zamanin mutane masu ji-ji-da-kai. Zamanin da mutanensa ke ganin sun sha ƙarfin su ce: yi haƙuri! 

 Ku saurari labarai ku ji kuma ku ga yadda mutane da dama ke kashe masoyansu, aure ya mutu kuma ahalin da a da yake cike da farinciki yau ya koma mahauta, saboda muna jin cewa bai cancanta ace mu ce yi haƙuri ba

Shin ko za ku iya min wata alfarma ku furta kalmar Yi haƙuri?

Ya kuka ji da kuka furta kalmar?

Shin sunanku ya canja ne? Shin kalar fatarku ko tsayinku sun canja ne? Shin gyaran gashin da kuka yi ko kwalliya sun canja ne? Shin da kuka furta kalmar asusun bankinku ya yi ƙasa ne? Shin jinannakin ku sun rage ne yayin da kuka furta kalmar? Ko kuma kun kamu da Covid19 ne da kuka furta kalmar? 

Hmm, to mai yasa ku ka zaɓi ku rasa wannan kyakkywar budurwar ko saurayin saboda girman kai? Mai yasa ku ka zaɓi ku rasa wannan tarayyar mai ban mamaki, abota da kuma waɗanda ubangiji ya aiko domin su taimake ku a rayuwa? 

Kada ku manta fa shi girman kai rawanin tsiya ne. Wasun mu da dama sun rasa abokan zamansu saboda ya zama mana abu mai wahala mu ce: yi haƙuri! 

Shin ko kun san cewa kalmar yi haƙuri ka iya canja rayuwarku har abada? Kawai ku dinga faɗarta akai-akai, ku yarda da ni babu wani mummunan abu da zai faru. 

A duk sanda kuka furta kalmar sai dai fa a samu sulhu, za a sake samun zaman lafiya da lumana. Abota za ta sake ginuwa yayin da sabbin al'amuran ban mamaki za su ci gaba da wanzuwa.

Ku yi haƙuri, in har wannan saƙon ya saɓa muku. Na zo da salama ne. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 

Share:

MATASA A ƘARNI NA ASHIRIN DA ƊAYA

*MATASA A KARNI NA ASHIRIN DA DAYA.* 

Nabeel Bajoga
12th August, 2020
Ranar Matasa Na Duniya.

Samartaka wani Lokacine na rayuwar Dan Adam Wanda take tsakanin Yarinta zuwa manyanta. Akasarin su Masu shekarun Haifuwa ne tsakanin Shekara 18 zuwa 40.
MATASA sune kashin bayan kowacce Al'umma ta waje Nemo cigaban yanki da samar da zaman lafiya Mai dorewa, Kamar yadda Tsohon Jagoran Siyasa a indiya MAHATMA GANDHI ya fada cewa "matasa su sani kasancewarsu masu nitsuwa cikin al'umma shike tabbatar da zaman lafiyar Wannan al'ummarda suke ciki, sannan suyi taima kekeniya da kwazo cikin hadin kai da zaman lafiya wajen tabbatar da cinma burukan al'ummar da suke zaune"

Matasa sune ginshikin kowace al'umma kamar yadda ake fada sune shuwagabannin Gobe.
Amma kash! Abun takaici da bakin ciki, matasan Wannan karni na ashirin da daya sun kasance akasin sauran matasan dasuka gabata a duniya. Matasan mu a zamanin da muke ciki sun lalatar da kansu, sun jefa kansu cikin hatsari da tagayyarar rayuwa tare da jefa al'ummar da suke ciki, cikin wani hali na fargaba fa rukushewar tarbiya.
A Wannan gaba, zan danyi tsokaci akan hatsarorin da matasan Wannan karni suka tsinci kansu.

1. *SHAYE-SHAYE* 
Matasan mu a Wannan zamani sun jefa kansu cikin mummunan hali na ta'ammuli da kwayoyi masu fitar da hayyaci, Wanda yake Zama illa a rayuwarsu da sakasu cikin tsari da na al'ummar da suke Rayuwa.
Shaye-shaye kan iye cire mutum daga hankalinsa har ya kaiga yin barna ko mugun aiki ga Wanda suke tare, yakan illatar da kwakwalwa zuwa ga rashin tunani, nazari ko banbanta abu Mai kyau da marar kyau, illar ta'ammulu da kyawowi masu bugarwa nada matukar yawan gaske Wanda yakan kaiga haukatar da Masuyi bayan ya jefasu cikin kuncin rayuwa.

2. *BANGAR SIYASA* 
Kasan cewa akasarin matasa sun jefa rayuwarsu cikin hatsari na ta'ammuli da muggan kwayoyi, yasa Wasu daga cikin 'yan siyasar mu suka samu damar yin amfani da matasa wajen bangar siyasa da ta'addacin a lokacin yakin nema zabe domin cinma burukansu na siyasa.
Abun takaici zakaga matasa suna rike makamai a kan tituna suna barazana ga rayuwar al'umma. Hasali ma abun tunani anan shine Wanda yasasu yanada 'yaya da ya killacesu ya samar musu da ingantacciyar Rayuwa, ya turasu sunyi karatun zamani domin suzamo Mutane Masu kima da daraja a idon Al'umma har ma suzo suma sujagoranci wannar Al'ummar.

3. MUMMUNAR ALAKA TSAKANIN JINSUNA.
Haramcecciyar alaka tsakanin samari da Yan mata ta zamo ruwan dare a Wannan zamani, alaka tsakanin jinsi guda biyun a makaranti, guraren taro, wajejen bikukkunan aure, guraren cin abinci dama cikin garuruwa ya zamo alaka na banza, na lalatar da rayuwa, da zubar da mutunci.
Hakan ya ragewa akasarin matasa kima a idon mahukunta, shugabanni dama Al'ummar da suke rayuwa da ita.

4. *LALACEWAR KAFOFIN SADARWA NA ZAMANI* 
 Haƙiƙa kafafen sadarwa na zamani na da matukar amfani a rayuwar Al'umma wajen isar da sakonni, Neman ilimi, kasuwanci, yin nazari da saukaka lamuran rayuwa, Amma Kash! matasan Wannan karni suna amfani da dama da suka samu na kafafen sadarwa na zamani ta mummunar hanya, wajen kallace-kallacen banza da tsiraci, cin mutuncin juna, bata Lokaci wajen yin chatting marar amfani, da rubuce-rubuce na banza da zubar da kima.
Wanda hakan yakan jawo rukushewar tarbiya, rashi ganin girman manya, rashin maida Hankali wajen karatu da fadawa cikin hatsarin lalacecceiyar alaka tsakanin maza da mata.

5. *RASHIN BIN KOYARWAR ADDINAI.* 
 Gujewa da watsi da matasa suka yiwa koyarwa irin ta addinansu shi ya kaisu ga halaka da fadawa cikin mummunar halaye da dabi'u na banza.
Addinin musulunci dama kiristanci yayi hani ga ta'ammuli da muggan kwayoyi, ta'addaci, rashin girmama na gaba, dama alaka marar kyau ga jinsuna biyu, Wanda da matasa sunbi koyarwa da hani irin da addinansu da basu tsinci kansu a wannar mummunar rayuwar ba.
Mafita ga matasa shine komawa ga koyar da tarbiya irin ta addinansu, su maida Hankali ga karatu da niyyan cinma muradu na rayuwa da inganta Al'ummar da suke rayuwa a cikinta ta yanda zasuyi alfahari da kansu kuma Al'umma ma tayi tayi alfahari dasu.
Akwai kalubale babba akan Shugabanni, mahukunta da maluman addinai wajen farfado da tarbiyar matasa da dawo dasu kan turban da zata tsiratar da Al'umma dama kasa baki daya, domin tabbatar da cigaba Mai dorewa.

DIGA KARSHE,
Kamar yadda ake fada Matasa in sun gyaru sune ginshiki kuma kashin bayar kowacce Al'umma, sune Shugabannin gobe, Tabbas hakane! saboda matasa suna da fikira da hangen nesa, suna da manufofi masu kyau ga Al'umma, suna da burin kawo cigaba da nasarori masu dorewa ga kasar da suke. Mafarkin matasa na kawo sauye-sauye na cigaba a Al'umma bai tsaya iya yankin da suke rayuwa ba, yakaiga har duniya baki daya.
Goben ko wacce Al'umma ya danganta ne ga matasansu da kuma irin kwazon da sukeyi wajen tabbatar da zaman lafiya .
A ƙarshe ina Mai bawa 'yan uwana matasa shawara da mudawo kan turban da akasan matasan duniya dashi na tabbatar da zaman lafiya da kawo cigaban Al'umma, Zuwaga Shugabanni da magabata kuma muna Kira a garesu da subawa matasa dama domin su bada nasu gudunmawa da kawo sauye-sauye da zai kai Al'umma tudun na tsira.

NAGODE DA SAMUN DAMAR KARANTAWA!

Usman Muhammad Ali
(Nabeel Bajoga)
Shugaban Kungiyar 
AREWA STUDENTS ORIENTATION FORUM (ASOF) Reshen Jahar Gombe.
Mataimakin Mai Magana da Yawun Kungiyar 
AREWA MEDIA WRITERS
Reshen Jahar Gombe.

Share:

NI MA NA YARDA USTAZAI SUNA DA MATSALA

*NI MA NA YARDA USTAZAI SUNA DA MATSALA.* 

Dr. Aliyu Muh'd Sani

Matsalar da ake fama da ita a yanzu ita ce: su matasa -wadanda ba su wuce matsayin daliban ilimi ba- wadanda suke rubuce - rubuce a Facebook, da sunan Nasiha ko inkarin munkari ko karantarwa, sawa'un da sunan aiki da wani Manhaji na da'awa ko aiki da Manhajin Jarhi da Ta'adeeli, suna mantawa da matsayinsu.

In haka ne to Menene matsayin nasu?

Matsayinsu shi ne matsayin masu Nasiha da inkari a kan abin da ya tabbata kuskure ne a Shari'a. Ma'ana inkari a kan munanan aikyuka.

Amma hukunci a kan mutane, da dora musu sunan Dan Bidi'a, ko kiransa Bakhawarije ba matsayinsu ba ne, ba martabarsu ba ce, ba huruminsu ba ne. Wannan hurumi ne na Malamai wadanda sun kai matsayin su yi ijtihadi, su yanke hukunci da yin fatawa a hukunce-hukuncen Shari'a.

Saboda za ka iya cewa; kama sunan Musulmi ka tsine masa ya saba ma Shari'a. Sukar shugaba a bayyane ko a kan mimbari ya saba ma Shari'a,,, kaza ya saba Manhajin Salaf Ahlus Sunnati wal Jama'a...

Amma cewa; wane dan bidi'a ne, wane Bakhawarije ne, wannan hukunci ne. Yanke hukunci kuwa hurumi ne na manyan Malaman da za su iya ijtihadi su fitar da hukuncin Shari'a.
Saboda haka manyan Malamai ne za su iya yanke hukunci a kan wane da wane ba dalibai ba.

Kuma kar a manta, hatta shi Malamin naka da zai iya yin hukuncin, kar fa ka yi zaton hukuncinsa Nassi ne da bai halasta a saba masa ba, a'a, kawai ijtihadi zai yi, in ya kai ya yi ijtihadin. Idan ya dace yana da lada biyu, idan kuma ya kuskure yana da lada daya, matukar ya ji tsoron Allah a cikin ijtihadin nasa, kuma ya yi aiki da ka'idojin ilimi ingantattu.

Don haka, tun da Malamin ma zai iya yin kuskure, to kenan wani Malamin zai iya yin nasa ijtihadin ya saba masa.

To in haka zai iya faruwa, ta yaya za ka wajabta wa mutane bin hukuncin da Malaminka ya yanke a kan wani malamin?
Ka ce: tun da Malam wane ya ce: Malam wane dan bidi'a ne, ko Bakhawarije ne, to dole kowa sai ya yarda?

To wannan fa a kan hukuncin da Malami ya yanke kenan!
To ina kuma ga hukuncin da ba Malami ne ya yanke ba fa?!
Hukuncin da dalibin ilimi ne ya yanke, ko ma wanda a bisa hakika bai kai a kira shi da dalibin ilimin ba?!
Ya ce: Malam wane Dan Bidi'a ne, ko ya danganta shi ga Khawarijanci?!

Saboda haka kuskure ne ka zo kana kumfar baki, -wai- don wani bai yi irin hukuncin da ka yanke ga wani Malami ba, har ka zo kana tuhumarsa da cewa; yana kare Dan Bidi'a, ko yana kare Bakhawarije.

Wannan ya sa Imamu Ahmad bn Hanbal, Imamu Ahlis Sunnati wal Jama'a ya ce:
إخراج الناس من السنة شديد

"Fitar da mutane daga Sunna ba abu ne mai sauki ba".

Amma a yau an dauki bidi'antarwa, da kora daga Sunna kamar shan ruwan sanyi.

Balle kuma khawarijantarwa, abin da banbancinsa da kafirtawa kadan ne.

Matasa masu rubuce - rubuce da sunan kowane irin Manhaji, ku ji tsoron Allah. Wallahi kun fi bukatar karatu da koyon ilimi da ladabi fiye da komai, balle har ku shiga hurumin da ba naku ba, hurumin yanke hukunci a kan mutane.

Allah ya shirye mu gaba daya.

Share:

ZURFAFA SOYAYYA GA JARUMAN FINA-FINAI


ZURFAFA SOYAYYA GA JARUMAN FINA-FINAI

Bissmillahir Rahmanir Raheem.

Assalamu alaikum Warahmatullah Wabarakatuhu.

'Yan uwa musulmai ina yi mana barka da wannan rana ta juma'a, Allah ya amsa mana ibadunmu kuma ya sada mu da dukkan wani alheri da ke cikin wannan yini, sannan ya kare mu daga dukkan sharrorin da ke cikinsa. Ya Allah ka nuna mana ƙarshen musibar COVID19 a duniya baki ɗaya.

Bayan haka, ba ɓoyayyen abu bane cewa jaruman fina-finai musamman na ƙasar Indiya sun samu karɓuwa sosai a ƙasar Nijeriya, musamman ma a arewacin ƙasar. Dalilin da zai tabbatar maka da hakan shi ne, abu ne mai matuƙar wahala a yau ka samu wani gida a arewacin Nijeriya da babu masoyin fina-finan Indiya a cikin wannan gida. Wannan sai ya haifar da ƙaruwar ƙarfin soyayyar jaruman fina-finan a zukatan jama'a, har ta kai ga mata suna kwaikwayon jarumai mata ta kowace fuska yayin da su ma mazan ke kwaikwayon jaruman ta kowace fuska. A ƙarƙashin haka sai abota, zumunci, barkwanci, soyayya da auratayya ta shigo cikin irin tarayyar da masoya jarumai da kuma harkar Indiya ke yi baki ɗaya.

Amma in da gizo ke saƙar shi ne: masifar da irin soyayyar hauka da indiyawa da mutanen wasu ƙasashe kamar Jamus suke yi wa waɗannan jarumai ne ta tunkaro mu, domin a yau an samu waɗanda har ridda suna yi cikin Kalaman da suke furtawa dangane da jarumansu, sun sani ko ba su sani ba wannan kuma Allah shi ne mafi sani. Hakan yasa ƙiyayya, hamayya, zage-zage, cin mutunci da aibata juna duk sai suka shigo cikin lamarin.

Haba 'yan uwana, ta yaya za mu bari irin wannan ɓaraka ta shigo cikinmu? Me zai sa ba za mu rage irin wannan muguwar soyayya ga waɗannan jaruman ba? Shin laifi ne don mun sassauta soyayyarmu a garesu? Ko kaɗan, hasali ma yin hakan shi ne abin da ya dace. Wani fa yana sane jaruminsa yayi wani abun amma saboda makauniyar soyayya sai ya yi ƙirmijin-ƙememe yace atafau ba haka abin yake ba ayi ta kai ruwa rana da shi, haba aboki baka da aikin yi ne? Haba 'yar uwa baki da abin yi ne? Me zai hana in za mu tattauna mu dinga tattaunawa irin ta hankali a nutse ba tare da cin fuskar juna ba? Na san dai cewa babu wanda zai so ace ga shi ranar ƙiyama sun tashi tare da jaruminsa a gaban Allah, ko ni da nake masoyin SRK ina masa kyakkyawan zato amma wallahi ba zan yarda ace in tashi tare da shi ba ranar alƙiyama. To kuma gashi addini ya tabbatar mana da cewa abin da zai faru kenan ga duk wanda ya mutu yana mai miƙa yana son wasu mutane.

Ashe Kenan akwai buƙatar mu hankalta mu san irin soyayyar da za mu ke yi wa jaruman nan, kuma a ƙoƙarin yin hakan mu tabbatar cewa ba mu ɓata mu'amalarmu da mutanen da muke tare da su ba, domin waɗancan har abada ba za su taɓa maye mana gurbin na nan ba, kuma ba za su taɓa yarda su ɓata da na can saboda mu da ke nan ba (in ma sun san da zamanmu kenan)

Allah ya shiryar da mu hanya madaidaiciya, Aameen Thumma Aameen.

•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman 
•----------•✬(✪)✬•----------•

    +2348185819176

19 June 2020


Share:

ZUWA GA MASOYAN BOLLYWOOD


ZUWA GA MASOYAN BOLLYWOOD

Ina yi muku barka da wannan lokaci, fatan kowa yana cikin ƙoshin lafiya, Allah ya sa haka amin.

Sanin kowa ne dai cewa izuwa yanzu babu wani batu da yafi jan hankalin mutane fiye da maganar mutuwar matashin haziƙin jarumin Bollywood wato Sushant Singh Rajput wanda aka same a rataye a ɗakinsa a ranar Lahadin da ta gabata. To kowa dai ya san cewa wannan ba shi ne karo na farko ba da jarumi ko jarumar fim ta kashe kanta ko ya kashe kansa ba. Amma abin tambayar shi ne: ke yasa wannan ya fi ɗaukar hankali? Me yasa mutane suka fi damuwa da shi? Sannan me yasa shakku game da sahihancin cewa jarumin ne ya kashe kansa ya shiga zukatan mutane tun daga lokacin da aka sanar da mutuwarsa? Waɗannan wasu tambayoyi ne da ya kamata masoyan Bollywood su yi wa kansu.

Sannan, kimanin shekaru biyar da suka gabata, a lokacin ina kan yin wani gagarumin bincike dangane da 'yan Masoniyya na ci karo da wasu bayanai masu ɗimbin yawa waɗanda ko da yake basu da alaƙa da abinda nake bincike akai a wannan lokacin, sun matuƙar tayar min da hankali saboda muninsu. Na so in yi rubutu akansu amma sai na fasa saboda munin al'amarin da kuma kasantuwar cewa a wancan lokacin mutane da yawa suna jin haushina saboda kafewa akan ra'ayina, wannan dalili yasa na yi shiru amma sai na ci gaba da binciken a ɓoye tare da fahimtar lamarin. To, ko da yake yanzu ma ba bayyana abinda na gano zan yi ba, zan so ku sani cewa "jikina yana bani cewa lokacin tona wannan asirin ya ƙarato, kuma mutuwar jarumi Sushant Singh Rajput ita ce sanadi". Don haka, ba lallai ne hasashena ya zama gaskiya ba, amma kada ku yi mamaki idan kuka ji ance kaza da kaza ne tushen afkuwar lamarin, kada ku yi mamaki in ku ka ji an ce jarumanku suna da hannu dumu-dumu a cikin laifi kaza ko ana zarginsu akan laifi kaza da makamantansu.

A ƙarshe ina so ku sani cewa, yadda duk kuke ɗaukar Bollywood ba haka take ba, kuma kowa kuka gani a cikinta shima yana da ɗan guntun kashinsa da be wanku ba, don haka ba za a ji mutuwar sarki a bakina ba, amma in har magana ta fito, to kada ku ce ba mu faɗa muku ba.

Sai anjima.

•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman 
•----------•✬(✪)✬•----------•

    +2348185819176
16th June 2020 
Share:

CATCH THEM YOUNG


Catch them young!!! 
We always hear this words but we never put the meaning into hands
But today i really got the meaning 
A young girl of 4 years reciting quran off hand without a single mistake really got me astonished 
Same thing goes to azkar is as if the whole citadel is on her head
Did you know when she start all this memorization?
During this lockdown period subhanallah She started from suratu naas now she is in suratu buruuj Ma sha Allah with the help of her elder sister and her mum but what amazed most people is that she doesn't know the alphabet yet she memorized all this by heart
Now a challenge to us 
Let's ponder on this what did our children gain in this lockdown period? What positive change happen to our children this period 
Is it that from morning to night they are always watching television hoping to watch the next cartoon they will play or they are busy going from one friend's house to another playing around?  
Lets plan their time for them because they never know the meaning of it now. Let's catch them young
May Allah make our children a righteous muslim and muslimah
And bless those who seeking for such.
 
Fatimah Ademola 
(Umm Attiyah)
28 june 2020
Share:

NIMA NA CE BABU KORONA


*"...NI MA NA CE BABU KORONA"*

✍️ Abdullahi Abubakar Lamido

Da sunan Allah Mai Rahama. 

A yanzu dai duk duniya ana tattaunawa ne a kan yaya rayuwa za ta kasance bayan an fito daga kangin Korona. Kasashe suna ta gina tsare-tsare na mataki-mataki don fita daga takunkumin Hajja Koro a hankali a hankali. Amma a Arewacin Najeriya har yanzu muna tattunawa ne a kan shin ma akwai ta neko babu! Lokacin da za mu kammala wannan cece-kucen, duniya ta tsere ta yi zurfi a cikin sabon shafi. Daga nan kuma wata kila za mu fara tattauna abubuwan da su ne da su ya kamata da a yanzu muna tattaunawa...

Tsoro na shi ne kada kasashe su bude boda a ci gaba da harkokin sifiri, amma kuma a hana dan-kasuwarmu zuwa China ko Dubai ko India ko Ghana sari kaya, a ce dole sai an masa riga-kafi tunda ko wace kasa ta yarda akwai Korona, ta dauki matakin dakileta, alhali Dan Najeriya bai ma yarda akwai ta ba. Wannan dai riga-kafi Wanda alal hakika ba mu yarda da shi ba. Wanda ke yawo a kasashe ya riga ya san irin kallon hadirin kaji, da walakanci da ake yi wa dan-Najeriya a filayen jiragen sama na duniya. Ina tsoron kada sakacinmu ya kara munin wannan....Allah Ya tsare.

A lokacin da al'ummomi suke ta kokarin toshe kofar shigowar Korona kasashensu, mu muna ta maganar cewa ai ba ta kama bakake, ba za ta zo Afirka ba dss. Ko da ta shigo kudancin kasar, mu kuma muna musu dariya muna cewa ai mu Kano muna kaunar Annabi (S.A.W) don haka ba za ta shigo ba, da sauransu. Mun manta a lokacin an fara samunta a Saudiyya...!

Bayan ta shigo Kano, nan kuma tattaunawarmu ita ce ai mutuwar da ake yi babu alaka da ita....Daga mu har shugabanninmu kowa ya koma siyasantar da ita; su sun shagaltu da yaya za su samu kudi da ita, mu kuma muna ta cacar-baki don kare ra'ayin gwanayenmu na siyasa dangane da abubuwan da ke da alaka da ita....!

Toh, yanzu dai mu sani, sauran kasashe da al'ummomi suna ta sama wa kansu mafita game da yadda za su rayu da ita - ka ga dai sun yarda akwai ta, kuma tana da illa, kuma dole a yi nazari kan hanyoyi fita daga kanginta...

A halin yanzu dai ka sani, yanayin duniya gaba daya ya canza. Nau'o'in sana'o'i da kasuwanci da yawa sun tashi daga aiki. Da yawa suna kan hanyar rushewa ta har abada. Hotel-hotel da yawa za su rufe, kasuwancin jiragen sama zai yi matukar karyewa, jami'o'i da yawa na duniya za su talauce, farashin man fetur ya karye, darajar naira sai kara zubewa take yi...

Na san za ka ce ai wannan ba mu ya shafa ba, ya shafi manyan barayi ne (elites) masu hannun jari a hotel da jirage da jami'o'i. Haka ne. Kuma haka ka fada a farkon korona cewa cutar masu kudi ce...Amma kada ka manta, ma'aikatan wadannan wurare duka marasa karfi ne, kuma za su rasa ayyukansu! Za kuma su dawo neman me za su yi. Wata kila tunaninsu ya koma yadda za su bude shago a Kantin Kwari, ku Singa, ko Kurmi ko Tsohuwar Kasuwa a Gombe, kuma idan suka zo sana'arka za su yi, kuma kostomominka za su hara, kuma wata kila sun fi ka sanin dabarun kasuwanci na zamaani...Maana dai mu sani, jiya ba yau ba. 

Diribobi ma su sani, tafiye-tafiye za su ragu! Amma fa sayar data ta internet za ta ci gaba da karuwa....

Kada kuma ka manta, sama da kashi 80 na kudaden shiga na gwamnatin Najeriya daga man fetur yake zuwa. A yanzu kuma bukatar man fetur ta fara zama tarihi....Don haka gwamnati ba za ta iya samun kudin da take raba wa jihohi yadda ta saba ba. Toh! Yaya batun biyan albashi? Sai Allah....! Ka ga ma'aikatan gwamnati su ma kenan sai an canza tunani. Karshe dai gwamnatocin jihohi dole su kara saka ido a kan haraji! Wata sabuwa? Allah Ya kyauta. 

Dan'uwa, ba mugun fata nake yi ba! Sam! Burina shi ne mu yi hangen nesa, mu yi nazarin me ya ke kaiwa ya komo. Abin da nake so da kai, ya dan'uwana, ka nitsu, ka gina tunaninka a kan ilimi da hangen nasa. Ka bibiyi yadda al'amura ke gudana, ka karanci abinda ke kaiwa ya komo a kasar ka, da yadda siyasar duniya da kuma yanayin zazzabin tattalin arzikin duniya zai shafi rayuwarka da ta iyalinka da ta la'ummarka. Wannan kuma shi ne amfanin ilimi da hankali da basira. 

Mafi muhimmanci, ka yi nazarin yadda dukkan wannan sauye-sauye za su yi tasiri ga addininka, da al'adarka da makomar tarbiyyar yaranka....

Yanzu dai, abubuwa da yawa sun koma ta hanyar takanology; wato kimiyya da fasahar zamani. Yau sama da wata biyu kenan kullum sai na yi meeting da mutane daga garuruwa daban-daban; ni ina Gombak a Malaysia, wani yana Kano, wani na America, wani a Ingila, wani a Sokoto, Kai, HAR MA DA DAN BORNO! Kuma duk wannan meeting din muna yin sa a cikin zaure guda kowa yana kallon dan'uwansa yana jin muryarsa!...Kamshin turaren jikinsa ne kawai ba za ka ji ba! Duk wannan kuma fa kowa yana zaune cikin falon gidansa. Wannan shi ake cewa zoom! Kuma shi ake cewa "The New Nomal". Sabuwar Duniya?

Toh ka sani yanzu makarantu ma mafi yawa za su koma zoom! Yanzu haka kasar Malaysia ta sanar cewa daga nan har karshen wannan shekarar karatun Jami'a ya koma ta zoom! Babu batun fita daga gida zuwa aji! Kuma daga yanzu a duniya iyaye za su samu saukin yaransu su yi karantun digiri cikin sauki ba sai sun tafi kasar waje ba, domin jami'ar Malaysia ko ta Ingila ko Uganda ko Saudi Arabia za ta biyo ka da darasi har cikin falonka! Za a sha ingantaccen digiri mai araha...!

Shin ko ka shirya wa wannan sabuwar duniyar! Ko dai har yanzu kana ta yin wakar "Mallam ya ce babu Korona, ni ma na ce babu Korona"?!

Allah Ya taimake mu.

Abdullahi Lamido
Gombak
31/05/20
Share:

GANIN WATA A NIJERIYA


*GANIN WATA A NAJERIYA* 

Wasu sun bayyana cewa sun ga Wata da idanun su, wasu kafafe kuma sun bayyana yadda wasu suka bada rahoto amma aka nuna musu cewa ai lokacin amsar rahotan ya wuce saboda wata kimiyyah na irga da ƙidaya da ake anfani da ita.

Ko shakkah babu tambayoyi sun yawaita matuƙa, daama cikin ruɗani ake na Covid19 da rashin Sallar Juma'a da rashin Sallar idi a wasu jihohin, sai kuma ga wata matsalar, wasu tuni suka yanke hanzari da cewa kawai mai martaba na aiki ne da sanarwar Saudi Arabiya.

Akwai wasu karatuka da short videos wa'inda marigayi Sheikh Albani Zaria Rahimahullah ya warware wa'innan matsalolin filla filla kuma dalla dalla.

Ga su kamar haka;

(https://youtu.be/fz2TAD0gJ3c) a wannan clip din Malam ya yi cikakken bayani dangane da Ganin Wata a musulunci gaba ki ɗaya, wanda in ka saurara zaka fahimci cewa; shin ko meye mafuta gameda halin da ake ciki a yanzu ?

(https://youtu.be/ZEE2aEvnYyY) a wannan clip din kuma Malam ya bayyana hanyoyin tabbatar da ganin Wata ne a musulunci, shin wata ƙasar ake bi ko kuma wasu lissafe lissafe ake bi ko yaya?

(https://youtu.be/ma-Oj1tj7-Y) anan kuma Sheikh Albaniy Rahimahullah ya bayyana mas'alar ganin Wata ɗinne a Najeriyan ce, ya ya matsalar ta fara, ya kuma za'a shawo kanta, a matsayin ka na Ɗan Najeriya ya ya kamata kayi ?

Ina bama ƴan uwa shawarar da suyi ƙoƙari su saurari duka clips ɗinnan guda uku, domin da haka ne zaka cire kanka daga ruɗani da kuma shakku da ka ke ciki, domin ka samu ka bautawa Allah salin-alin.

Allah ya ƙarɓi ibadun mu, Ameen.
 *Abdurrahman Jani*
Share:

BUƊAƊƊIYAR WASIƘA GA MALAM BELLO YABO


*BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA MALAM BELLO YABO*

_Bayaga sallama da salati ga Annabi (s.a.w). Dazu nagama saurarar audio wanda Malam Bello Yabo Sokoto yayi na cin zarafin Malaman Sunnah da suke Kaduna harma da Me girma Gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i Allah ta'ala yakara tsareshi*****_

_Babu shakka wannan sakon danaji beyi kamada abunda za,ace yafito daga wajan Malamin Sunnah ba duk da cewa ga wanda yasan wanene Bello Yabo abun baze bashi wani mamakiba. Amma akwai takaici matuka ace Malamin Sunnah kuma yana magana ba akan abunda ya shafeshiba kuma ba tareda yayi bincikiba domin Annabi (s.a.w) yace:_
*كَفَى بِالْمَرْءِ إِثْمًا أَنْ يُحَدِّثَ بِكُلِّ مَا سَمِعَ"*
*ZUNUBI YA ISHI MUTUM ACE SHI DUK ABUNDA YAJI TOH SEYA BADA LABARI*
       _Sannan Allah ta'ala acikin Littafinsa yace,:_
*يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنْ جَاءَكُمْ فَاسِقٌ بِنَبَأٍ فَتَبَيَّنُوا*
*YAKU WADANDA SUKAYI IMANI IDAN WANI FASIKI YAZO MUKU DA LABARI KUYI BINCIKE*


_Amma kai kawai mutum kanacan cikin garinku kana zaune a sokoto kazo kana bude baki ko kunya bakaji kana karya kana cewa ranekun talata da laraba anbada dama kowacce kasuwa abudeta a jihar kaduna amma ace mutane bazasuyi sallar idi ba. Toh Allah yasani nidai a kaduna nake kuma dan kasuwane ni wanda zeyi wahala ace akwai wata shahararriyar kasuwa a kaduna wacce bansanda zamantaba amma wallahi tun sadda Gwamnatin kaduna ta kafa doka dalilin covid 19 sau dayane nasan anba mutanen kaduna dama suci kasuwa shine ranarda aka fara bude gari akace afita daga karfe 3 na yammacin talata zuwa 12 na daren wata alhamis, toh tun daga wannan ranar idan akwai wanda yace maka an kara bude kasuwanni a kaduna kace nace karyane inkuma ya isa yazo yafadi kasuwarda aka bude. Kasuwar cecenia itace mafi cikar kasuwa a garin kaduna gaba daya kuma rabonda abudeta yau munfi karfin watanni biyu, kasuwa Kawo da Kasuwar Bacci kaje kaga irin yadda ake zuba musu jami'ai idan akace anbude gari amma tayaya mutum da sunan da'awar sunnah zezo yana karya yana cewa an bude dukkan kasuwanni????_

_Cewarda kayi Gwamna El-Rufa'i bayason addini wannan karya kakeyi domin kai ba a kadunan kake bane. Tun zamanin Mulki Ahmad Makarfi a shekarar 2000 ake kashe musulmi babu dalili a kudancin kaduna da yankin Gonin Gora amma tun zuwan Malam El-Rufa'i kaje ka tambaya idan an sake kashe musulmi a wadannan wajaje****_

_Kafin Zuwan El-Rufa'i babu wata ma'aikatar gwamnati a jihar kaduna face seka samu arna sune 70% a wannan ma'aikata duk da cewa musulmine mafi yawan mutane a jihar kaduna amma da zuwan Malam El-Rufa'i shine ya amsowa musulmi 'yancinsu ya gyara tsarin kuma ya daidaitashi*****_

_Alokacin Mulkin Ibrahim Yakowa idan kaje jami'ar Jihar Kaduna Musamman ya kori Shugaban Jami'ar Muhammadu Tanko ya dauko wani katon arne ya maye gurbinsa dashi kuma tundaga sannan shiga jami'ar takewa musulmi wahala kuma inkaje jami'ar babu wani ofishinda babu arne acikinsa hatta tsangayar koyarda harshen larabci a jami'ar kafin Zuwan El-Rufa'i toh sakatariyar wajan arniyace da wando da riga babu hijabi take zuwa kuma wai tsangayace ta ustazai! Da zuwan El-Rufa'i ya kori wancan arnen yadawoda Muhammadu tanko ayanzu kaje kaga irin yadda Musulmai suke samun gurbin karatu a wannan jami'ar wanda Wallahi wallahi nida wani arne da bakinsa yace aisu tunda aka dawo da Muhammadu Tanko yanzu samun gurbi a Kasu yake musu wahala sesun kama kafa da musulmi******_

_Ba zuwa nayi inkare Malam Nasiru ba ko inmasa talla amma duk me hankali da yake jihar kaduna wanda yake fifita Alwazi'ud dini akan Wazi'ud Dab'i kaje ka sameshi kaji meze fada akan Malam Elrufa'i****_

_Amma shi dama jahilin gari matsalar addinifa ba matsalarsa bace duk bemasan wainarda ake toyawa akarkashin kasa da irin yadda Elrufa'i yazamarwa musulmin kaduna gata ba shi jahili kawai abincine agabansa ba sanin halinda addininsa yake ciki ba*****_


_Dakake zagin Malaman kaduna akan sun ajje gemu basuwa gwamna rashin hankaliba toh aisu malaman kaduna masu hankaline ahalus sunnah ne su ba 'yan tamore bane kuma 'yan tayi dadi bane kokuma 'yan taratsi. Domin inaso kabude Usulus Sunnah ta Imam Ahmada Binu Hambal tsakaninka da Allah haka Imam Ahmad yayiwa shugabannin zamaninsa wa'azi???_

_Ibnu taimiya yayi zamani da Tatar wadanda suke yanka musulmi su fedeshi a shanya namansa amma sadda Ibnu Taimiya yabukatu ze yiwa shugaban Tatar Wa'azi tsakaninka da Allah gida yabi shugaban kokuwa Aa daga kan Mimbari ya cillo????_


_Wallahi tallahi inhar Malam Nasiru Azzalumine kamar yadda kake riyawa toh wallahi duk zaluncinsa bekai rabin rabin Hajjaju dan Yusuf Assaqafi ba domin shi Hajjaju Manyan Sahabbai da Tabi'ai yake yankawa amma kata6ajin wani sahabi yahau mimbari yana yiwa Hajjaju mummunar Addu'a?? Toh shin dan Allah kai sunnar taka wacce iri ce????_

_Sannan Mafi yawan malamai suntafi akan cewa yin sallar idi ba dole bane sannan kuma ba,ayin sallar idinma se abayan shugaba kokuma wanda shugaban ya wakilta amma kai tunda kake katabajin anyi sabani akan sallar azahar??? Toh meyasa mukayi hakuri dayin sallar azahar amma ace bazamuyi hakuri da sallar idi ba????_


_Saboda haka malaman kaduna sunabin tafarkin magabatane shine yasa kaji basuyi wani abu na rashin hankaliba amma kuda kuke bin tafarkin 'yan shi'a da khawariju toh sekuje kuyi mukuwa zamuji zamu gani idan mutum zekai labari. Amma tunda Malam Abubakar Gumi yace Karatun Hadisi da aiki dashi shine zaman lafiya toh idan har irinku masu da'awar ilimi zakuyi watsi da hadisi abayan bayanku toh me kuke tsammanin jahilan cikin mabiyanku zasu zama?????_


 _Amma dan Allah inaso Malam Bello yabo yataimaka ya gaya mana sunan kasuwa kwaya daya wadda gwamnati tayarda ake cinta a ranekun talata da laraba a jihar kaduna kamar yadda naji kace dukkan kasuwannin kaduna an yarda abudesu talata da laraba toh inaso kagayamin yaushene aka bada sanarwan budewar kuma wacce kasuwar aka bude???_

_Awata ruwayar wancan hadisin Annabi (s.a.w) cewa yayi:_
*كفى بالمرء كذباً أن يحدِّث بكل ما سمع*
*MUTUM YA ISA ZAMA BABBAN MAKARYACI IDAN YAKASANCE DUK ABUNDA YAJI LABARI SE SHIMA YABADA LABARIN*


✍🏼
```Jameel A Kabo```
_*(ABU ZULAIHAT)*_
25-09-1440
18-05-2020
Share:

DANGANE DA KASHE MUSULMAI DA AKE YI A INDIYA


DANGANE DA KASHE MUSULMAI DA AKE YI A ƘASAR INDIYA

Bissmillahir Rahmanir Raheem.

Assalamu Alaikum warahamatullah Wabarakatuhu. 'Yan uwa barkanmu da Warhaka, fatan kowa yana lafiya.

Izuwa yanzu dai na san kusan kowa da ga cikinku ya samu irin ɓarnar da ake yi wa musulmi a ƙasar India, don haka ba sai na ja doguwar magana a wannan fanni ba.

Fannin da zan ɗanyi tsokaci akai shi ne: Wato ɗabi'a ce ta ƙananan ustazai, ko 'yan bana bakwai, ko gama garin mutane waɗanda su ke da ƙarancin fahimta dangane da abubuwan da ke faru na yau da kullum, idan irin wannan al'amari ya faru za ka ga nan da nan kansu yayi zafi, ƙirjinsu kuma ya ɗau ɗumi. Tabbas ko dabba ce aka taɓa mata nata dole ta ji zafi, kuma dole ta ji cewa tana buƙatar ɗaukar fansa. Ballantana mutane masu hankali, don haka abin da aka yi mana ba mu ji daɗinsa ba, kuma mun yi Allaah wadai da shi. To amma me? Wani mataki ya kamata mu ɗauka?

Na ga rubututtuka da dama na abokai da makusanta akan wannan lamari da kuma na waɗanda babu abinda ya haɗa mu. Wasu sun yi kyau wasu kuma ba'a cewa komai. To a ƙarƙashin wannan, zan so mu fahimci cewa wannan abu da ya faru ba komai bane face ɗaya daga cikin alamomin ƙarshen duniya. Kuma haka abin zai ci gaba da kasancewa har sai alƙawarin Allaah ya tabbata a kanmu. 

To, idan irin wannan abu ya faru ne ya kamata mu yi? Akwai masu tunanin kawai a fito mana a gwabza, to in an ce a gwabza kuna da makaman yaƙar maƙiyanku irin wanda ya fi nasu? Shin cewa aka yi a fito a yi surutu, me surutun zai amfanar da mu? Shin in zai mana amfani ma, su ya kamata ace su yi? Ta wace hanya ya kamata ayi? Kai da kake hawa yanar gizo kana wannan ɓaɓatu feesabilillah matakin da ya kamata ka ɗauka kenan? Shin kai da kake ta zage-zage da aibata dukkan mabiyan sauran addinan da suke da alaƙa da lamarin ka na da hujjar da zaka kare kanka in aka rutsa ka ka yi bayani dangane da abubuwan ɓatanci da ka faɗa a kansu? Shin su jaruman Fina-Finai musulmai da kake cewa sun ƙi fitowa su yi magana, tsakani da Allaah maganar su wane irin canji za ta haifar? Shin wai ma musulmanmu na indiyan sun damu da addinin nasu kamar yadda ya kamata da har za su fito su ɗauki matakin da ya dace? Shin ka san irin halin da su kansu jaruman su ke ciki kuwa da har kake neman jawabi daga gare su?

Shin kamata yayi mu ɗauki hanyar gyara aiyukanmu da halayenmu ko kuma kamata yayi mu fito mu yi hargagi kawai a fito a share mu maganar ta wuce? Shin za mu aminta da cewa mun saɓa wa mahaliccinmu ta hanyar kaucewa umurnin Manzonsa mun ɗauki ƙauna mun danƙawa maƙiyanmu wanda hakan yasa yanzu mu ke fuskantar abinda muka shuka ko kuma za mu fake ne da liƙawa wasu laifin ko da hakan ya dace ko bai dace ba?

Shin za mu ci gaba da zargin juna ne da ganin laifin juna ko kuma za mu shiga taitayinmu ne mu yi yunƙurin gyara baki ɗaya?

Ba Za su daina kashe mu ba, ba za su daina tsanar mu ba, ba za su daina ƙoƙarin ganin bayan mu ba. Amma dukkan su ne su ke yi mana hakan? Shin za mu bar zafin rai da mummunar fahimta ta sa mu tsani waɗanda ba su ji ba basu gani ba ne ko kuma za mu miƙe ne mu koma kan tafarkin da ya dace?

Bani da iko da kowa, bani da ikon dakatar da ta'addanci, amma ina da ikon hana kaina ɗaukan nusarin hukuncin da bai dace ba ga waɗanda ba su cancanta ba a kuma lokacinda bai dace ba.

Allaah ya ƙara tsare mu.

<••••••••••••••••••••••••••••>
      Haiman Raees 
<••••••••••••••••••••••••••••>

        08185819176

Twitter: @HaimanRaees 

Instagram: Haimanraees 

Haimanraees@gmail.com 

Miyan Bhai Ki Daring

Aaraha Hoon! 
Share:

WAIWAYE

WAIWAYE ADON TAFIYA
!
MAULANA SHEHU IBRAHIM NIASSE (R.T.A)
.w
Yana Kwance a Gadon Asibiti a Birnin London Sai Yace Da
IMAAM HASSAN CISSE (R.A); Ya Tayar Dashi Tsaye, Domin
Zai Yi Sallah.
.
Sai IMAM HASSAN (R.A) Ya Kalli SHEHU, Idanuwansa Cike Da
Hawaye Ya Ce: "Haba SHEHU! Ka Bautawa ALLAH Kana Da
quruciya, Ka Bautawa ALLAH Kana Saurayi, Ka Bautawa
ALLAH Kana Dattijo, Me Yasa Baza Kayi Hakuri Ba Ka Bautawa
ALLAH a Kwance, Tunda Kana Cikin Halin Rashin Lafiya".
.
Sai SAYYIDI UMAR FAY (R.A) Ya Kama Hannun Daman
SHEHU, IMAAM HASSAN (R.A) Ya Kama Hannun Hagun
SHEHU, Suka Mikar Dashi Tsaye, SHEHU Ya Juya Ya Kalli
ImamHassan Cikin Matsanancin Rashin Lafiya, Ya Ce
Masa: "Hassan! Ka Kalleni Da Kyau Ka Gani, Kaga Nayi Kama
Da Mutumin Da Zai Bautawa ALLAH(S.W.T) a Kwance?.
.
Wallahi Da SHEHU Ya Tada Sallah, Yace 'ALLAHU AKBAR' Kai
Kace Duk Duniya Ba Mutumin Da Ya Kai Shi Lafiya, Saboda Ya
Fuskanci UBANGIJI (S.W.T).
.
SHI YASA MA SHEHU(R.A) YAKE CEWA: "Na Rantse Da
ALLAH, Rantsuwar Da Babu Kaffara a Cikinta, Duk Mutumin Da
Kaga Yana So Na Wallahi Saboda ALLAH Yake So Na, Haka
Duk Mutumin Da Kaga Yana Qi Na, Wallahi Saboda Soyayyata
Ga ALLAH(S.W.T) Yake Qi Na, DominNi Banda Kowa, Banda
Komai Sai ALLAH", WANNAN GASKIYA NE.
.
BARHAMA SHA NEMAN MABIYA, BARHAMA SHA ZAGIN
MAQIYA. SHI YASA ALLAH(S.W.T) YA WATSA SOYAYYARSA A
CIKIN ZUKATAN
MUMINAI. ALLAH YA QARA MANA QAUNAR SALIHAN BAYI,
YA BAMU ALBARKACINSU AMEEEN.
.

ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ،ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ﺃﺳﻨﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ
Rubuawa ✍✍✍
*​IDRIS SULEMAN UMAR​*

Wallafawa📖🖨
*​FATIMA ABUBAKAR​*

Gabatar wa
*​IDRIS SULEMAN UMAR*

Duk wanda yake bukatar shiga zauran mu na
*INA MAFITA* ko neman karin bayani ko bada shawara ko aiko da tambaya yanememu a ​wannan numbobi​
+2348020582294
+2348036473515

*A aiko da cikakkyan suna kafin tambaya*

​Daga ALKALAMIN​
Idrissulemanumar2294@gmail.com

Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form