Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

Showing posts with label Ramadan And Eid. Show all posts
Showing posts with label Ramadan And Eid. Show all posts

AZUMIN RANAR ARFA


AZUMIN RANAR ARFA DA FALALARSA

*A-Azumin ranar Arfa*

Yin azumin ranar Arfa yana da falala mai girma kuma sunnane na Manzon Allah s.a.w.
Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ya kasance yana yin Azumin *ranar Tara ga watan Zul-hijjah,da ranar Ashura da kwanaki ukku a kowane wata*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ ﺑﺮﻗﻢ 2106. 

*Falalar Azumin ranar Arfa ga wanda baije aikin Hajji ba*

i-Manzon Allah s.a.w yana cewa;
*(Yin Azumin ranar Arfa yana kankare zunuban shekarar da ta gabata da shekara mai zuwa)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 3805.

ii-Manzon Allah s.a.w yana cewa;
*(Duk wanda yayi Azumin ranar Arfa Allah ya gafarta masa zunubansa na shekara guda biyu,shekarar da ta gabata da wadda ta biyo bayanta)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 6335.

iii-Manzon Allah s.a.w yana cewa;
*(Yin azumin ranar Arfa,ni ina fatan Allah zai kankare zunuban shekarar da ta gabata da shekarar da ta biyo bayanta...........)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 3853.

Allah ne mafi sani.
Share:

WASU DAGA CIKIN HUKUNCE-HUKUNCEN DA SUKA SHAFI RANAR IDI


*WASU DAGA CIKIN HUKUNCE-HUKUNCEN DA SUKA SHAFI RANAR IDI*


*Tambaya*

Assalamu Alaikum, 
Malam ina so sanin hukunce-hukuncen idi 


*Amsa*
Wa'alaikumus salam.

Idi yana da hukunce-hukunce da yawa ga wasu saga ciki:

1. Azumtar ranar idi – ya haramta a azumci ranakun idi guda biyu, saboda hadisin Abu-sa'id Al-kudry, -Allah ya yarda da shi - cewa : "Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana azumtar ranaku biyu – wato ranar karamar sallah da ranar babbar sallah" Muslim ya rawaito

2. Siffar sallar idi- An karbo daga Abu-sa'id -Allah ya yarda da shi – cewa : "Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana fita ranar idin karamar sallah da babbar sallah zuwa filin idi, idan ya fita yana farawa da sallah" Bukari ne ya rawaito
Ana yin ta ne raka'o'i biyu, za'a yi kabbara bakwai a raka'a ta farko, a raka'a ta biyu kuma sai ayi kabbara shida. Abu-dawud 
Idan mamu ya riski limaminsa a tsakiyar kabbarori, to zai yi kabbarar harama ne ya bi shi, ba zai rama abin da kubce masa ba na kabbarori, saboda sunnoni ne ba wajibai ba.

*Dr. Jamilu yusuf Zarewa*

7/8/2013
Share:

HALAYEN MUTANE BAYAN RAMADAN


*Halayen Mutane Bayan Ramadan*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Halayen mutane a bayan Ramadan ya kasu kashi 4.

👉🏻 *Kaso na farko*
Sune wadanda ta sanadiyyar watan Ramadan Imanin su ya karu, suka kara kusanci da mahaliccinsu, suka lizimci aikin da'a tareda kokari wajen nesantar aikin laifuka...... *Madallah da wanda ya fada a wannan kaso*👌🏻

👉🏻 *Kaso na biyu* 
Sune wadanda bayan Ramadan suka koma ruwa wajen lizimtar manyan ayyukan laifuka bayan a cikin Ramadana kuma sun kame basu aikatawa..... *Wadannan sun zama masu bautar Ramadana, Allah ya tsaremu*🤦🏻‍♂

👉🏻 *Kaso na uku*
Sune wadanda suke tsaka tsakiya a bayan watan Ramadana, wani lokacin su aikata ayyukan alkhairan da suka saba aikatawa a watan, wani lokacin kuma sai shaidan ya rinjayesu........ *Tsira da kubutarwa su tabbata ga wannan kaso*🙏🏻

👉🏻 *Kaso na Hudu*
Wadannan sune kaso na karshe wadanda daman basuci ribar watan Ramadana ba haka nan ma bazasuci riba bayansa ba, daman yayi dai dai da fadar Manzon Allah (SAW) da yake cewa: *"da yawa wasu masu azumi basuda ladar azumi sai dai yunwa da kishiri ruwa"*....... *wannan kaso sun tabe kuma sunyi hasara*🙆🏻‍♂

Muna addu'a Allah yasa yadda muka jajirce wajen bautama Allah a cikin Ramadan yasa mu kara jajircewa a bayansa👏🏻
➖➖➖➖➖➖
Domin neman karin bayani kuyi downloading wannan Littafin dake a kasa mai suna *"ماذا بعد رمضان؟"*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
https://t.me/ansarussunnah
Share:

FASTING IN SHAWWAL

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu,
*🌖 MON 02 -SHAWWAL-1441H🌖*
*➡ FASTING IN SHAWWAL ⬅*

 Abu Aiyub Al-Ansari (RAA) narrated that The Messenger of Allah (ﷺ) said:

"Whoever fasts during the month of Ramadan and then follows it with six days of Shawwal will be (rewarded) as if he had fasted the entire year." 

*Related by Muslim.*

وَعَنْ أَبِي أَيُّوبَ اَلْأَنْصَارِيِّ ‏- رضى الله عنه ‏- أَنَّ رَسُولَ اَللَّهِ ‏- صلى الله عليه وسلم ‏-قَالَ: { مَنْ صَامَ رَمَضَانَ, ثُمَّ أَتْبَعَهُ سِتًّا مِنْ شَوَّالٍ كَانَ كَصِيَامِ اَلدَّهْرِ } رَوَاهُ مُسْلِمٌ 1‏ .‏

‏1 ‏- *صحيح.‏ رواه مسلم ( 1164 )‏*.‏

*English reference :*
 Book 5, Hadith 701

*Arabic reference :*
 Book 5, Hadith 681

*🕕 Good Morning 🕕*
*🌖 EID MUBARAK 🌖*

Share:

GAISUWAR SALLAH

🌷 GAISUWAN SALLAH 🌷

Gaisuwan sallah ana yinta ne da kowane lafazi halastacce, lafazin da yafi falala shine *TAQABBALALLAHU MINNA WA MINKUM* domin ita ce aka ruwaito daga sahabbai.

An ruwaito daga Jubair bin Nufair yana cewa; "Sahabban Manzon (SAW) sun kasance idan suka hadu da junansu ranar idi, suna ce musu Taqabbalallahu minna wa minkum". Ibn Hajar ya hassana isnadinsa acikin Fathul baari.

An tambayi Imam Malik (Rahimahullauh) shin akwai laifi mutum ya yace ma dan uwansa bayan sallah idi, Taqabbalallahu minna wa minkum wa gafarallahu lana wa lakum, shi kuma dan uwan ya mayar masa da makamancin hakan?? Sai imam ya amsa da cewa "babu laifi hakan". Almuntaqa sharhul muwadda. 

Shaikhul islam ibn Taimiyyah yace; "Gaisuwa ranar idi, mutum yace ma Ɗan uwansa idan ya hadu dashi bayan sallah Taqabbalallahu minna wa minkum, wa a halahullahu alaika, dama wasun irin wannan gaishe gaishen, an ruwaito su daga wani sashi na sahabban Manzon Allah, sannan wasu daga cikin imamai sun yi rangwame game da aikatashi, kamar imam Ahmad da waninsa, sai dai shi Imam Ahmad yace "Ni bazan fara yiwa kowa ba, amma idan wani yamin zan amsa masa saboda amsa gaisuwa wajibi ne" Amma fara ita wannan gaisuwar babu wata sunnah da tayi umarni da ita kamar yadda bata yi hani da ita ba, wanda yayi yana da magabata akai, wanda ma yaki yi shima yana da magabaci akai". Majmu'ul fatawa.

#Zaurenfisabilillah 

Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah

Share:

KABBARORIN RANAR IDI

#KABBARORIN RANAR IDI 

Ana fara KABARBARIN idin Azumi ne da ranar ta fadi a yinin karshe na Watan Ramadhana, za'a cigaba da yin waɗan nan Kabbarorin har zuwa fitowar LIMAN dan yin sallar IDI. Daukaka murya ga Maza yana cikin girmama Allah kuna raya Sunnar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ne, amma su mata zasu yi Kabbarorin ne ba tare da daukaka murya ba, yin kabbara a fara tare a a jiye tare bidi'a ne, sunnah shine kowa yayi tashi Kabbarorin. 

Allah yana cewa 
(ولتكملوا العدة ولتكبروا الله على ما هداكم ولعلكم تشكرون)

Ma'ana:
*(kuma dõmin ku cika adadin,kuma dõmin ku girmama Allah a kan Yã shiryar da ku, kuma tsammãninku, zã ku gõde)*.

SIGOGIN KABBARORIN SUNE

1-SIGA TA FARKO 
Sigar Abdullahi bn Mas'ud R. A, yana FADAR:-
*_الله أكبر ، الله أكبر ، الله أكبر ، لا إله إلا الله ، والله أكبر ، الله أكبر ، ولله الحمد_*

_ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAH AKBAR, LAA ILAHA ILLALLAH, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WALILLAHIL HAMD_
@مصنف ابن أبي شيبة - ٥٦٣٣

2-SIGA TA BIYU 
*Sigar Abdullahi bn Abbas R.A* Sigar tana cewa:-
*_الله أكبر كبيراً ، الله أكبر كبيراً ، الله أكبر وأجل ، الله أكبر ، ولله الحمد_*

_ALLAHU AKBAR KABIRAN,ALLAHU AKBAR KABIRAN, ALLAHU AKBAR WA'AJAL, ALLAHU AKBAR, WALILLAHIL HAMD_
@مصنف ابن أبي شيبة - ٥٦٤٦.

3-SIGA TA UKU
*Sigar Salmanul Farisy R.A* sigar tana cewa:-
*_الله أكبر ، الله أكبر ، الله أكبر كبيراً_*
_ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR KABEERAN_
@السنن الكبرى - ٣/٣١٦ ] .ALLAH NE MAFI SANI

Share:

KWANAKIN WATAN RAMADAN SUN ƘARE

KWANAKIN WATAN RAMADHAN YA KARE, AMMA HAKKOKIN ALLAH BA SU KARE WA AKANKA SAI RANAR DA YAKININ KA (MUTUWAR KA) TA RISKE KA.

ALLAH Yace'; ka bauta wa UBANGIJIN ka har sai yakini (mutuwa) tazo maka !

ALLAH shine UBANGIJIN watan RAMADHAN, da kuma watan shawwal kuma shine UBANGIJIN dukkan sauran watanni na sheka gaba-daya !

Ka zamto mai tsoron ALLAH cikin dukkanin watanni kuma ka kiyaye addinin ka cikin dukkan rayuwar ka, domin addinin ka shine kan dukkan abunda kake da shi a wurin UBANGIJIN KA tsarkakakke maɗaukaki, kuma riko da addini shine zai tseratar da kai daga wuta, don haka ka kiyaye addinin ka kayi riko da shi cikin dukkanin watanni da kuma lokuta ! 

Muna fara BIBIBIYAR watan watan RAMADHAN ne da godiya ga ALLAH, sai kuma istigfa'ri, sa'annan mu bi ta da farin ciki da falalar ALLAH da ya bamu ikon azumtan ta da kuma tsayuwar ta zuwa karewar ta ! 

Muna farin ciki da wannan ni'imar da ALLAH ya azurta mu ne,
ba wai muna farin ciki bane da karewar ta, muna farin ciki da samun daman mun gama azumtar ta da tsayuwar ta cikin ibadar ALLAH !

GARGADI MAFI GIRMA !
Mu nisanci kuma mu tsoraci yawan wasa da gafala da kuma tozarta ɗa'a ga ALLAH, domin lallai shaiɗan shi mai kwaɗayi ne da ya ɓata mana ayyukan mu, ya kuma goge mana dukkan ayyukan alkhairi da muka aikata !

Sai ya fara raya wa wasu shashin mutane daga cikin mu, idan watan RAMADHAN ya kare to lokacin takura ya kare, ya fita daga kurkuku, sai ya tafi ga shagalar mutane da wasa da gafala, da tozarta sallah da wasun wa'ennan.

Ya yan uwa na kada mu warware sakar da muka sa'ka bayan kai komo da muka yi wajen sa'ka ta !

Muji tsoron ALLAH bayin ALLAH, mu kiyaye abunda muka aikata na alkhairi, mu tuba ga kura kuran mu, ALLAH yana gafartawa wanda ya tuba !

Share:

SHIN ZAN IYA SALLAR IDI A GIDA?


SHIN ZAN IYA SALLAR IDI A GIDA!!!
Haƙiƙa malamai sunyi sabani akan wannan mas'alar zuwa gida biyu:
Na farko: Wanda suke ganin halascin yin hakan wanda sune mafi yawan malamai (Jumhuur) Kamar Imani Malik, Shafi'i da Ahmad Bin Hanbal Allah ya jiƙansu.
Na biyu: masu ganin bai halasta ba kamar Imamu Abu Hanifah.
Ga kaɗan daga maganganun Malamai akan Mas'alar:
Al'Imamul Kharshi (Malikiyyah) yana cewa:
وقال الخرشي (مالكي) : "يستحب لمن فاتته صلاة العيد مع الإمام أن يصليها ، وهل في جماعة , أو أفذاذا ؟ قولان" انتهى باختصار من "شرح الخرشي" (2/104).
Anso ga wanda sallar Idi ta kubuce masa tare da liman da ya sallaceta, amma shin zasu yi jam'i ne ko kuma kowa zai yi nashi ne? Akwai maganganu biyu.
Haka Al'imamul Muzani(Shafi'iyyah) ya naqalto daga Al'imamus Shafi'i cewa:
نقل المزني عن الشافعي رحمه الله في "مختصر الأم" (8/125) : " ويصلي العيدين المنفرد في بيته والمسافر والعبد والمرأة " انتهى .
Mutum zai iya sallatar Idi guda biyu shi kaɗai a gidansa haka ma matafiyi ko bawa ko mace.
Ibnu Qudama (Hanabila) ya fada a cikin littafinsa Almugni:
"وهو مخير ، إن شاء صلاها وحده ، وإن شاء صلاها جماعة" انتهى
An baiwa mutum zaɓi game da sallar idi, in yaso ya sallaceta shi kaɗai ko yayi ta a jam'i. Ma'ana ga wanda ta kuɓuce masa tare da liman.
Haka ma Almardawi (Hanabila) yana cewa a cikin littafinsa Al'insaf:
"وإن فاتته الصلاة (يعني : صلاة العيد) استحب له أن يقضيها على صفتها (أي كما يصليها الإمام)" انتهى
Idan sallah ta kubuce masa, yana nufin sallar idi, anso ya rama ta irin yadda ake yinta tare da liman.
Amma kamar yadda na ambata a farko cewa akwai masu ganin rashin halascin hakan, zan yi ishara zuwa ɗaya daga cikin maganganun su.
Yazo a cikin littafin Addurarul Mukhtar a Hashiyar ibnu Abideen (Hanafi):
وفي الدر المختار مع حاشية ابن عابدين (2/175) (حنفي) : " ولا يصليها وحده إن فاتت مع الإمام "
Ba zai sallaceta (idi) shi kaɗaita ba idan ta kubuce masa tare da liman.
Babban Kwamitin fatawa na ƙasar Saudiyya (اللجنة الدائمة) sun baya fatawar halascin hakan
وجاء في فتاوى اللجنة الدائمة للإفتاء (8/306) : "صلاة العيدين فرض كفاية؛ إذا قام بها من يكفي سقط الإثم عن الباقين .
ومن فاتته وأحب قضاءها استحب له ذلك، فيصليها على صفتها من دون خطبة بعدها، وبهذا قال الإمام مالك والشافعي وأحمد والنخعي وغيرهم من أهل العلم. والأصل في ذلك قوله صلى الله عليه وسلم : (إذا أتيتم الصلاة فامشوا وعليكم السكينة والوقار فما أدركتم فصلوا وما فاتكم فاقضوا) ، وما روي عن أنس رضي الله عنه أنه كان إذا فاتته صلاة العيد مع الإمام جمع أهله ومواليه، ثم قام عبد الله بن أبي عتبة مولاه فيصلي بهم ركعتين، يكبر فيهما. ولمن حضر يوم العيد والإمام يخطب أن يستمع الخطبة ثم يقضي الصلاة بعد ذلك حتى يجمع بين المصلحتين . وبالله التوفيق وصلى الله على نبينا محمد وآله وصحبه وسلم " انتهى .
اللجنة الدائمة للبحوث العلمية والإفتاء
الشيخ عبد العزيز بن عبد الله بن باز ، الشيخ عبد الرزاق عفيفي ، الشيخ عبد الله بن غديان.
والله أعلم .
Ma'ana duk wanda idi ya kubuce masa kuma yana so so ya rama to mustahabbi hakan, wannan shine maganar Imamu Malik, Shafi'i, Ahmad, Nakha'i da wasunsu. Dalili akan hakan shine hadisin idan zaku jewa sallah to kuje a natse, abinda kuka riska ku sallaceshi wanda kuma ya kuɓuce muku ku rama, da kuma abinda aka ruwaito daga Anas ɗan Malik R.A cewa idan Idi ya kuɓuce masa yana tara iyalansa da bayinsa suyi raka'a biyu.
Har ila yau babban Majalisar Malamai na ƙasar Misra dake Azhar sun yi fatawar halascin yin sallar idi a gida musamman a wannan lokaci da muke na bazuwar annobar corona virus. Ga abinda fatawar ke cewa:
"كبار العلماء": يجوز أداء صلاة العيد في البيت.. والخطبة ليست شرطاً
أصدرت هيئة كبار العلماء بالأزهر برئاسة فضيلة الإمام الأكبر أ.د/ أحمد الطيب، شيخ الأزهر الشريف، اليوم الأحد، بيانًا للمسلمين حول العالم بشأن الأحكام المتعلقة بصلاة العيد في ظل استمرار تفشي فيروس "كورونا المستجد"، انطلاقًا من مسئوليتها الشرعية وواجبها الديني.

وقالت الهيئة في بيانها، إنه يجوز أداء صلاة عيد الفطر المبارك في البيوت، بالكيفية التي تُصلى بها صلاة العيد، وذلك لقيام العذر المانع من إقامتها في المسجد أو الخلاء، ويجوز أيضا أن يُصليها الرجل جماعة بأهل بيته، كما يجوز أن يُؤدِّيها المسلم منفردًا، وذلك انطلاقا من أن أعظم مقاصد شريعة الاسلام حفظ النفوس وحمايتها ووقايتها من كل الأخطار والأضرار.
أوضحت الهيئة أنه لا تشترط الخطبة لصلاة العيد، فإن صلى الرجل بأهل بيته فيقتصر على الصلاة دون الخطبة، مؤكدة أنه إذا صلى المسلم صلاة العيد منفردًا أو جماعة بأهله في بيته، فإنه يصليها ركعتين وبالتكبيرات الزوائد، وعدد التكبيرات الزوائد سبع في الركعة الأولى بعد تكبيرة الإحرام، وخمس في الركعة الثانية بعد تكبيرة القيام إلى الركعة الثانية، مضيفة أن وقت صلاة العيد هو وقت صلاة الضحى، يبدأ من بعد شروق الشمس بثلث ساعة ويمتد إلى قبيل أذان الظهر بثلث ساعة، فإن دخل وقت الظهر فلا تصلى؛ لأن وقتها قد فات.

ودعت هيئة كبار العلماء بالأزهر، المسلمين في مشارق الأرض ومغاربها، إلى التضرع إلى الله في هذه الأيام المباركة بالدعاء لرفع ما حل بالإنسانية من البلاء، وأن يُسارعوا لفعل الخيرات والإكثار من الصدقات ومساندة المرضى والمعوزين، تخفيفًا لما حل بهم من آثار هذا الوباء، داعين الله أن يرفع البلاء عن الإنسانية كلها، وأن يحفظ بلادنا والناس جميعًا من هذا الوباء، ومن جميع الأمراض والأسقام.
A takaice sunce ya halasta yin sallar idi a gida irin yadda ake yinta tare da liman, kuma mutum zai iya yi shi kaɗai ko tare da iyalansa, zai yi raka'a biyu tare da ƙarin kabarbari da ake yi. Kabarbari bakwai a raka'ar farko bayan kabbarar harama, da kabarbari biyar a raka'a ta biyu bayan kabbarar miƙewa daga sunada. Kuma ba sharaɗi bane sai anyi khiɗuba, sannan zai yi ta lokacinta wato daga hantsi har zuwa lokacin zawali.
Daga ƙarshe Majalisar tayi kira ga Musulmai a ko ina a duniya da su yawaita addu'oi tare da ƙanƙantar da kansu zuwa ga Allah da neman ya yaye mana wannan hali da muke ciki.

A bisa wannan bayanai nake kira ga yan'uwa musulmi musamman waɗanda suke a jihohi da aka hana tarurruka da ayi a gabatar da wannan ibadar a gidajenmu tunda hakan ya halasta mu roƙi Allah ya yaye mana damuwarmu.
Allah ya taimake mu
Share:

BAYANI GAME DA SALLAR IDI A GIDA SABODA ANNOBAR CORONA


*BAYANI GAME DA SALLAR ĪDI A GIDA SABODA ANNOBAR KORONA*
*✍ Farfesa Sheikh Ahmad Bello Dogarawa*
*Jumu’ah, Ramadān 29, 1441 (22/05/2020)*
*GABATARWA*
Bismillahir Rahmānir Rahīm. Alhamdu lillah. Wassalātu was Salāmu alā Rasūlillah, wa Ālihi wa Ashābihi wa man wālāh.
Bayan haka:
Musulmai na da ranaku biyu da suke yin īdi a cikinsu a kowace shekara: ranar daya ga watan Shawwāl bayan kammala azumin watan Ramadān – īdul fitri (karamar salla) da kuma ranar goma ga watan Zhul Hijjah – īdul adhā (babbar salla). Ranakun īdi na daga alamomi na Allah wadanda Musulmai a ko’ina cikin duniya ke yin bukukuwa da shagulgula don bayyana godiya ga Allah saboda samun nasarar kammala wata babbar ibada, da jaddada ‘yan uwantakar addini, da kuma taya juna murna da farin cikin zagayowar ranakun da Musulunci ya ba muhimmanci. Īdul fitri na biyo bayan kammala azumin watan Ramadān; shi kuma īdul Adhā na biyo bayan nasarar kammala tsayuwar Arfa da mahajjata suka yi wanda ita ce rukunin aikin Hajji mafi girma.
A wannan shekara ta 1441 bayan hijira, wato shekarar 2020 a kalandar Bature, Allah (Madaukaki) Ya kaddara ba za a yi sallar īdi na bayan kammala azumin Ramadān (karamar salla) ba a jahar Kaduna da birnin tarayya Abuja da kuma wasu jahohi na kudu masu yammacin Najeriya saboda tsoron yaduwar annobar Korona. A ranar Talata, 26/09/1441 (19/05/2020), gwamnatin jahar Kaduna ta ba da sanarwar rashin janye dokar dakatar da sallar Jumu’ah da sallolin farilla cikin jam’i, kuma ta bayyana cewa ba za a fita sallar īdi ba, ballantana a yi shagulgulan bikin salla karama, irin yadda aka saba. Tun bayan wannan sanarwa, mutane suka fara yin tambayoyi game da abubuwan da ya kamata su yi, a lokacin sallar īdin bayan azumi.
A cikin wannan ‘yar makāla, in shā Allah, zan yi takaitaccen bayani game da abubuwan da ya kamata kowannenmu ya yi, gwargwadon ikonsa.
*KOMAWA GA ALLAH DA CI GABA DA RIKO DA SABUBBA*
Ba shakka, halin da a ke ciki a Abuja da jahar Kaduna hali ne na damuwa da kuma rashin jin dadi saboda dakatarwar da shugabanni suka yi ga yin sallolin Jumu’ah da sallolin farilla cikin jam’i a masallatai na tsawon lokaci a matsayin daya daga cikin manyan matakan da a ke ganin za su taimaka wajen hana yaduwar cutar Korona a cikin jama’a. Ban da damuwar da a ke ciki ta rashin gudanar da salloli a masallaci, akwai kuma kuncin rayuwa da matsatsi da rashin walwala wadanda dokar zaman gida ta haifar wa mutane da yawa. Bayan wannan, ga tashin hankalin da aka shiga na sanarwar hana fita sallar īdi irin yadda aka saba.
Kasancewar a fahimta ta, wadannan dokoki da aka sanya, da kuma matakai da a ke dauka an gina su ne a kan kokarin tunkude barna da kuma kawo maslaha ga al’umma, duk da cewa ba shi ne abin da mafi yawan mutane ke so ba, akwai bukatar kowannenmu ya natsu, ya mayar da lamari ga Allah, kuma ya bi karantarwar Musulunci wajen mu’amala da irin wannan yanayi da a ke ciki.
Daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata kowane Musulmi ya yi, akwai:
(a) Ci gaba da kankan da kai ga Allah, da tuba gare Shi, da yawaita istigfari da sadaka, da yawaita karatun Alkur’āni da salati ga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), da addu’o’in neman kariyar Allah daga annobar, da kuma rokon yāyewarta da daukakewarta daga al’umma gaba daya.
(b) Yarda da hukuncin da shugabanni suka yanke da kuma karbansa da zuciya daya, da kiyaye dokokin da suka sa, tare da fatan Allah Ya sa hakan ya zama alhairi ga al’umma baki daya. Ba shi daga koyarwar Musulunci zagi ko la’antar shugabanni a cikin irin wadannan mas’aloli da suka shafi makomar al’umma. Haka kuma ba shi daga koyarwar Musulunci yin tawaye ko kira zuwa ga yin bore ga umurnin shugabanni, musamman umurnin da aka gina a kan shawarwarin amintattun kwararrun masana da kuma ijtihādin kokarin tabbatar da maslaha ga al’umma, duk da cewa ana iya samun kuskure a irin wannan ijtihādi.
(c) Kwadayi da kuma kaunar samun cikakken ladan sallolin Jumu’ah da sallolin farilla cikin jam’i da sallar īdi a wajen Allah Madaukaki duk da cewa ba a yi ba, kasancewar ba bisa ganganci ko ganin dama ne aka ki yi ba. Hadisai sun tabbatar da cewa wadanda rashin lafiya ko tafiya (balaguro) ko wasu larurori suka hana su yin ibadodin da suka sāba yi kafin wannan lokaci, ana ba su cikakken lada tamkar sun gudanar da inadodin. Bisa irin wadannan Hadisai, abin da a ke kyautata zato kuma a ke sa rai a wajen Allah (Madaukaki) shi ne a samu cikakken lada duk wadannan ibadodi da ba a samu yinsu ba yadda aka saba saboda wannan larura.
(d) Ci gaba da riko da sabubban da za su taimaka wajen ba da kāriya daga cutar, da kuma dakile yaduwarta, da iznin Allah, bisa shawarwarin da amintattun masana fannin kiwon lafiya su ke bayarwa, tare kuma da yin tawakkali ga Allah.
(e) Taimaka wa mabukata da abubuwan da za su rage masu radadin halin da a ke ciki gwargwadon iko, kuma idan an samu dama, a yi kira ga gwamnati da kungiyoyi da daidaikun mawadata su ma su taimaka gwargwadon iko.
(f) Yin tattali da kintsi da shirin yin sallar īdi a gida, shi kadai ko tare da iyalinsa, kamar yadda aka saba yin sallar.
*HUKUNCIN SALLAR ĪDI*
A wajen mafi yawan malamai, sallar īdi Sunnah ce mai karfi. Wadansu Malamai na ganin cewa mustahabbi ce, a yayin da wasu kuma suka tafi a kan wajabcinta. Salla ce da aka shar’anta ta ga Musulmi, maza da mata. Saboda muhimmancinta, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) har umurni ya bayar game da fita don gabatar da ita, shi kuma a karan kansa, ya lazimce ta tun daga shekarar da aka fara yinta har zuwa lokacin da ya bar duniya. A cikin Hadisin Ummu ‘Atiyyah (Allah Ya yarda da ita) ta ce: “an umurce mu da fitar da ‘yan mata (wadanda suka balaga) da matan aure da ke cikin dakunansu (har da wadanda ke cikin jinin al’ada) zuwa sallar īdi…” [Bukhāri da Muslim suka ruwaito]. Haka kuma, Bukhāri da Muslim sun ruwaito Hadisi cewa Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya umurci macen da ba ta da mayafin da za ta sanya don halartar sallar īdi ta karbi aro wajen wadda ke da safayar mayafi (don dai kowa da kowa ya halarci sallar).
Ana yin sallar īdi ne a filin da aka tanada na musamman, a bayan gari. Wannan shi ne asali. Haka Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da sahabbansa (Allah Ya yarda da su) suka yi. Amma ana iya yin sallar īdi a cikin masallaci ko a gida idan akwai larura ko tsananin bukatar haka.
*ZA A IYA YIN SALLAR ĪDI A GIDA?*
Tabbataccen hukunci a wajen fuqahā’u shi ne idan mutum bai samu sallar īdi ba tare da Liman, saboda ya makara, zai iya yin salla raka’a biyu bisa siffar da a ke gudanar da sallar īdi a wajen. Mata da yara da ba su samu zuwa sallar īdi ba, su ma ana son su yi salla raka’a biyu kamar yadda Liman da sauran jama’a suka yi. Haka kuma, wanda ke nesa da garin da a ke gudanar da sallar īdi, da wanda bai je sallar ba saboda wani uzuri karbabbe ko saboda wata larura, su ma za su yi sallarsu ta īdi a gida; su kadai ko tare da iyalansu. Imāmul Bukhāri ya kulla bābi a kan haka a cikin littafinsa “Al-Jāmi’ As-Sahih”.
Ibn Abī Shaybah da Baihakī sun ruwaito cewa Anas dan Mālik (Allah Ya yarda da shi) ya kasance a gidansa da ke wajen da a ke kira Zāwiyyah kusa da garin Basrah, bai samu zuwa sallar īdi ba, sai ya tattaro iyalansa da barorinsa, ya umurci ‘yantaccen bawansa Abdullah ibn Abi Utbah ya yi masu sallar īdi kamar yadda a ke yinta a cikin gari. Haka kuma Baihaqī ya ruwaito cewa duk lokacin da sallar īdi ta kubuce wa Anas dan Mālik (Allah Ya yarda da shi), yana tara iyalansa su yi sallar īdi kamar yadda Liman yake yi. Bayan wannan, Abdur-Razzāq ya ruwaito cewa an tambayi Abdullah dan Mas’ūd (Allah Ya yarda da shi) game da wanda ya rasa sallar īdi, sai ya bayyana cewa zai sallace ta kamar yadda Liman ya yi.
Bayan Imāmul Bukhāri ya kawo atharin Anas dan Mālik da ya gabata, ya kuma ruwaito daga Ikramah (Allah Ya jikansa) ya ce: “Wadanda ke zaune a bayan gari za su hadu, su yi sallar īdi kamar yadda limamin cikin gari yake yi.” Atā dan Abī Rabah (Allah Ya jikansa) shi ma ya ce: “Wanda ya rasa sallar īdi (tare da Liman), zai yi raka’a biyu (kamar yadda Liman ya yi).” Ban da wannan, Baihaqī ma ya ruwaito daga Muhammad dan Sīrīn, ya ce: “Sun kasance (wato Sahabbai) suna son idan mutum ya rasa sallar īdi, ya samu fili, ya yi salla kamar yadda Liman ke yi.” Haka kuma, Abdur-Razzāq ya ruwaito kwatankwacin wannan hukuncin daga Qatādah da Ma’amar (Allah Ya jikansu), kamar yadda shi ma Ibn Abī Shaybah ya ruwaito daga Al-Hasanul Basrī da Ibrāhim An-Nakh’ī da Hammād (Allah Ya jikansu). Bayan wannan, Abdur-Razzāq da Ibn Abī Shaybah sun ruwaito cewa lokacin da ‘Amr dan Al-Aswad Al-‘Ansī da Mujāhid dan Jabr Al-Makkī suka gudu, suka būya saboda tsoron Hajjāj dan Yūsuf Ath-Thaqafī, sun rika yin sallolin īdi a wajen da suka būya.
A cikin sharhohin da suka yi wa Sahīhul Bukhārī, Ibn Rajab Al-Hanbalī da Ibn Hajar Al-Asqalānī duk sun inganta mafi yawan wadannan āthār da aka ruwaito daga Sahabbai (Allah Ya yarda da su) da Tābi’ai (Allah Ya jikansu) game da halascin yin sallar īdi a gida ga wanda uzuri ya hana shi zuwa. A cikin littafin “Al-Mughnī”, Ibn Qudāmah ya danganta irin wannan fahimtar ga Imām Mālik da Imām Ash-Shāfi’ī da Imām Abū Thaur da Imām Ibnul Munzir (Allah Ya jikansu). Haka kuma, a cikin littafin Al-Insāf, Al-Mardāwī ya danganta irin wannan fajimta ga mazhabar Imām Ahmad ibn Hanbal (Allah Ya jikansa). Sai dai kuma ‘yan mazhabar Hanābilah na da ra’ayin idan mutum zai yi sallar īdi a gida, shi kadai ko tare da iyalinsa, zai iya yin raka’a biyu ko raka’a hudu, kamar yadda Ibn Qudāmah da Al-Mardāwī suka bayyana, sannan suka rinjayar da yinta bisa siffar da Liman ke yinta saboda āthār da aka ruwaito daga Anas dan Mālik (Allah Ya yarda da shi) da Tābi’ai da yawa (Allah Ya jikansu).
Bisa bayanan da suka gabata, za mu fahimci cewa ya halasta a yi sallar īdi a gida saboda uzuri karbabbe ko kuma larura da za su hana a yi sallar a filin da aka saba yi, kamar yadda zai kasance a Abuja da jahar Kaduna da wasu jahohin da ke kudancin Najeriya. A kasar Saudi Arabia da Egypt da wasu kasashe da dama duk ba za a yi sallar īdi a wuraren da aka saba yi ba saboda tsoron yaduwar annobar Korona. Kwamitocin fatawa na kasashen Saudi Arabia da Egypt sun ba da fatawar halascin yin sallar īdi a gida, bisa la’akari da wasu daga cikin dalilan da na ambata a sama.
A nan Najeriya, zuwa yanzu, majalisar malamai ta jahar Kano ta nuna damuwarta game da iznin da gwamnatin jahar ta ba da a kan a fita zuwa sallar īdi duk da yawan karuwar adadin wadanda suka kāmu da cutar Korona a jahar. A mataki na kasa baki daya, Jamā’atu Nasril Islām (JNI) ita ma ta shawarci Musulmi a kan su yi sallar īdi a gida, sannan ta yi kira da babbar murya ga mutanen da ke jahohin da aka ba da damar fitowa yin sallar īdi a kan su bi dukkan tsare-tsaren da aka ce za a yi don dabbaka shawarwarin amintattun kwararrun masana. A yankin kudu maso yamma kuma, hadaddiyar kungiyar al’ummar Musulmai ta kudu maso yamma (Muslim Ummah in the South West of Nigeria – MUSWEN) da kungiyar da ke fafutukar kāre hakkokin Musulmai (Muslim Rights Concern – MURIC) duk sun fitar da sanarwar jawo hankali Musulmin da ke zaune a yankin nasu cewa su yi hakuri, su yi sallar īdi a gida, su kadai ko tare da iyalansu, ka da su je filin īdi ko da kuwa an ba su damar yin haka. Bisa wannan, duk wanda ke zaune a daya daga cikin jahohin da a ka ba da damar zuwa sallar īdi, kuma ya ga shi din bai natsu da shiga cikin daruruwa ko dubban mutanen da za su halarci sallar ba, yana da damar ya yi sallarsa ta īdi a gida.
*YADDA ZA A YI SALLAR ĪDI A GIDA*
Bayani ya gabata cewa siffar sallar īdi a gida iri daya ne da yadda a ke yinta a filin īdi tare da Liman. Huduba ce kawai ta banbanta su. A magana mafi karfi da rinjaye, idan za a yi sallar īdi a gida, ba za a yi huduba ba. Wannan shi ne abin da atharin Anas dan Mālik (Allah Ya yarda da shi) ya nuna kuma shi ne ra’ayin da Imāmul Bukhāri ya karkata gare shi.
A dunkule, ga abubuwan da ya kamata a lura da su dangane da sallar īdi:
(a) Lokacin sallar īdi na farawa ne daga lokacin da nafila ta halasta bayan fitowar rana, kamar yadda Hadisin da Abu Dāwud da Ibn Mājah suka ruwaito ya tabbatar. Lokacinta na fita da zarar rana ta wuce tsakiyar sama, wato lokacin da rana ta yi zawāli.
(b) An so a gaggauta gabatar da ita da zaran lokaci ya yi, musamman idan sallar īdin layya ne. A cikin littafin “Al-Mughnī”, Ibn Qudāmah ya bayyana cewa ba bu sabani tsakananin malamai game da bukatar gaggauta gabatar da salla a ranar layya, da zaran lokaci ya yi.
(c) An so a yi wanka kafin a yi sallar īdi [Baihaqī ya ruwaito Hadisi]; a sanya tufafi mafi kyawu [Tabarānī ya ruwaito Hadisi]; a ci wani abu, musamman dabino, kafin a yi sallar, tunda dai karamar salla ce, bisa Hadisin da Bukhāri da Tirmizi suka ruwaito.
(d) An so a yi kabbarbari tun daga lokacin da aka fara taruwa a wajen da za a yi sallar har zuwa lokacin da wanda zai jagoranci sallar zai iso wajen, bisa Hadisin da Ibn Abī Shaybah ya ruwaito. Wadansu malamai na ganin dacewar a fara yin kabbarbari tun daga lokacin da aka samu labarin tabbatar da ganin watan Shawwāl har zuwa lokacin da za a fara sallar īdi, bisa fahimtar Zaid dan Aslam da Imām Ash-Shāfi’ī (Allah Ya jikansu) game da aya ta 185 cikin suratul Baqarah, kamar yadda ya zo cikin littafin “Al-Awsat” na Ibnul Munzir.
(e) Yadda a ke yin kabbarbarin, kamar yadda Ibn Abī Shaybah da Hākim da Baihaqī suka ruwaito, shi ne mutum ya ce: “Allahu akbar, Allahu akbar, Lā ilāha illallah, Allahu akbar, Allahu akbar, wa lillahil hamd”. Haka kuma, ya tabbata cikin atharin Abdullah dan Mas’ūd (Allah Ya yarda da shi) wanda Ibn Abī Shaybah da Baihaqī suka ruwaito, mutum na iya fadin: “Allahu akbar, Allahu akbar, Allahu akbar, Lā ilāha illallah, wallahu akbar, Allahu akbar, wa lillahil hamd.”
Ga yadda siffar sallar īdi ta ke:
(1) Ba a kiran salla ko yin ikama a wajen sallar īdi. Hadisin ‘Abdullah dan Abbās (Allah Ya yarda da su), da Hadisin Jābir ibn ‘Abdullah (Allah Ya yarda da su) wadanda Bukhāri da Muslim suka ruwaito duk sun tabbatar da cewa ba a yin kiran salla ko ikama a wajen sallar īdi, a zamanin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi).
(2) Sallar īdi raka’a biyu ce kawai; ba a yin nafila kafin a yi sallar, kamar yadda ba a yin nafila bayanta.
(3) Ana fara sallar īdi ce da kabbarar harma tare da niyya. Daga nan sai a yi kabbarbari guda bakwai (bayan kabbarar harma) a raka’ar farko, sannan a yi kabbarbari guda biyar a raka’a ta biyu bayan kabbarar dagowa daga sujuda ta biyu ta raka’ar farko [Abu Dāwud da Ibn Mājah].
(4) An so a karanta surah al-`A’alā a raka’ar farko bayan an karanta fatiha, da surah al-Ghāshiyah a raka’a ta biyu, kamar yadda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana yi. Amma kuma ya tabbata cewa Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yana karanta surar Qāf da al-Qamar wani lokaci [Muslim da Abu Dāwud da Tirmizī]. Idan mutum bai hardace ko daya daga cikin wadannan ba, sai ya karanta surorin da suka saukaka gare shi.
(5) Bayan an kammala salla, ba wata huduba da za a gabatar. Wasu malamai na ganin ba laifi mutum ya dan fadakar da iyalinsa tare da kwadaitar da su a kan ayyulan alhairi da nisantar munanan ayyuka, ba tare da ya yi shi a siffar huduba ba.
*BIKI DA SHAGULGULAN SALLA FA?*
Ya halasta a yi wasa, da bayyanar da farin ciki, da walwala, da anashuwa a ranar īdi, matukar dai ba a ketare iyakokin da Shari’a ta gindaya ba, kuma ya zamanto yin hakan ba zai kai ga saba wa dokar zaman gida da hana cunkoson mutane a waje daya ba. Hadisai da dama da suka hada da wadanda Nasā’ī da Ibn Hibbān suka ruwaito sun tabbatar da halascin haka. Bayan wannan, mata na iya yin kida da waka a ranakun īdi (matukar ba su hada da kalmomin bātsa ko kuma cundanya tsakanin maza da mata ko su yi kida da wakar a gaban maza ba), kamar yadda Hadisin da Ahmad da Bukhāri da Muslim suka ruwaito ya nuna. Idan kuwa bai kubuta daga wadannan matsaloli ba, to ba za a yi ba.
Haka kuma, ya halasta a yi wa juna barka da salla, da addu’ar fatan alhairi, da dacewa, a ranar īdi. A cikin Fathul Bārī, Ibn Hajar ya nakalo daga Jubair ibn Nufair (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “A zamanin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), idan mutane (daga cikin sahabbai) sun hadu da juna (a kan hanya), sukan ce wa juna: ‘Taqabbalallahu minnā wa minka’ (Allah Ya karba mana, mu da kai).”
*GYARA KAYANKA*
Lalle ne mu yi kokarin kiyaye wadannan abubuwa:
(1) Fitar da Zakātul Fitr ga duk wanda ke da iko, kafin a yi sallar īdi a ranar salla ko kuma kwana daya ko kwana biyu kafin ranar salla. Hausawa kan kira ta da suna zakkar fidda kai ko zakkar kono, kasancewarta wajibi ne da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya wajabta fitar da ita a karshen watan azumi, kamar yadda Hadisai ingantattu suka nuna. Zakkar ta wajaba a kan kowane Musulmi; yaro ko babba, mace ko namiji, mai ‘yanci ko bawa. Illa iyaka, mai gida shi ne ke fitar wa yara da mata da bayi da kuma duk wadanda ke karkashinsa, kamar yadda Hadisin da Baihaqī da Ad-Dāra Qutnī suka ruwaito ya tabbatar. Ana fitar da ita ce daga nau’o’in abincin da mutane ke ci. Adadin da a ke fitar wa kowane mutum, shi ne sā’i daya; wato mudun nabiyyi guda hudu. Sunnah ta tabbatar da cewa ana ba da zakkar ce daga nau’o’in abincin da mutane ke ci, ba daga wani abu, madadinsa ba. Hadisin da Bukhāri da Muslim suka ruwaito daga Abu Sa’īd al-Khudri (Allah Ya yarda da shi) da ya yi magana a kan zakatul fitri, da lokacin da suka kasance suna fitar da ita a zamanin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), ya bayyanar da haka karara. Ke nan, ba za a ba da wani abu daban, a maimakon abinci ba. Wannan ya sa mafi yawancin malamai suka ce bai halasta a fitar da kudi ko wani abu ba, a madadin abinci, domin kamar yadda suka ce, zakatul fitri nau’i ne na ibada da aka iyakancewa jinsi, don haka, dole ne a tsaya a kan nassi. Hikimar wannan zakka ta hada da tsarkake mai azumi daga kurakuren da ya yi a lokacin da ya ke azumi, da kuma samar da abinci ga miskinai, kamar yadda Hadisin da Abu Dāwud da Ibn Mājah suka ruwaito ya nuna.
(2) Ba a raya daren īdi da ibada, kasancewar ba bu wani Hadisi ingantacce da ya nuna shar’ancin hana ido barci don yin nafila da karatun Alkur’āni da zikiri a wannan dare. Hadisan da aka ruwaito dangane da falalar raya daren īdi, masu tsananin rauni ne, kamar yadda malaman Hadisi suka tabbatar. Amma mutumin da ya saba tashi cikin dare don yin ibada, zai iya yin ibadarsa a daren īdi, tunda bai kebance ibadar da wannan dare ba.
(3) A yi hattara game da nau’o’in sabon Allah da a ke yi, da sunan bayyana murna, a wannan rana, maimakon gode wa Allah bisa ni’imominSa. Kamata ya yi a gode wa Allah ta hanyar kiyaye dokokinSa, ba kuma a saba maSa ba. Abin takaici, a kan samu wanda bai taba yin zina ko shan taba sigari ko giya ba, amma a wannan rana ta farin ciki zai fara!
*KAMMALAWA*
Ina rokon Allah (Madaukaki) Ya karba mana ibadodinmu kuma Ya sa mu yi sallar īdi lafiya. Allah Ya magance mana wannan annoba ta Korona don mu samu damar komawa cikin masallatanmu, mu ci gaba da ibāda yadda muka saba.
Alhamdu lillah.
DOGARAWA (29/09/1441 - 22/05/2020)
Share:

SALLAR IDI DA HUKUNCINTA 2

_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_

       _*SALLAR IDI DA HUKUNCINTA*_
       ➖➖➖➖➖➖➖➖➖

                 _*FITOWA TA BIYU*_

_Da Sunan *Allah* Mai *Rahma* Mai *Jinqai*_

          ```HUKUNCIN SALLAR IDI```
            ➖➖➖ ➖➖➖➖
_Malamai Sun Tafi Akan Cewa Sallar Idi Wajibi ne. Wannan Shine Zantukan Malaman Mazhabar Hanafiyya Kuma Wannan Shine Zancen *Sheikhul Islam Ibn Taimiyya (rh)*. Sunyi Bayanin Dalilansu na Wajabta Sallar Idi da Cewa: Lallai *Manzon Allah (ﷺ)* Ya Kasance Yana Sallatar Idi Bai Ta6a Fashi ba Har Yabar Duniya._

_Wasu Malaman Kuma Cewa Sukayi Sallar Idi Fard Kifaya ce (Wato Wasu Zasu Iya Daukewa Wasu). Wannan Shine Ra'ayin Mazhabar Hanãbila. Wasu kuma Sun Tafi Akan Cewa Sallar Idi Sunnah Ce Mai Karfi. Wannan Shine Ra'ayin Mazhabin Shafi'iyya da Malikiyya._

     _*HUKUNCIN AZUMI RANAR IDI*_
        ➖➖➖➖➖➖➖➖

_Haramun Ne Musulmi Yayi Azumi Ranar Idin Azumi da Idin Layya da Kuma Kwanaki Ukun Bayan Sallar Idin Layya. Malaman Musulunci Gaba Daya Sun Tafi Akan Haka Saboda Hadisin *Manzon Allah (ﷺ)* da Yake Cewa:_
عن عمر بن الخطاب رصي الله عنه قال: *”ﺳَﻤِﻌْﺖُ ﺭﺳﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋﻠﻴﻪِ ﻭﺳﻠَّﻢَ ﻳﻨﻬﻰ ﻋﻦ ﺻﻮﻡِ ﻫﺬﻳﻦِ ﺍﻟﻴﻮﻣﻴﻦِ، ﺃﻣَّﺎ ﻳﻮﻡُ ﺍﻟﻔﻄﺮِ ﻓَﻔِﻄْﺮُﻛﻢ ﻣﻦ ﺻﻮﻣِﻜُﻢ ﻭﻋﻴﺪٌ ﻟﻠﻤﺴﻠﻤﻴﻦ، ﻭﺃﻣَّﺎ ﻳﻮﻡُ ﺍﻷﺿﺤﻰ ﻓَﻜُﻠﻮﺍ ﻣﻦ ﻟﺤﻮﻡِ ﻧﺴُﻜِﻜﻢ“*

_An Kar6o daga *Umar bn Khaddab (ra)* Yace: *“Naji Manzon Allah (ﷺ) Yana Hana Yin Azumi a Wadannan Ranaku Guda Biyu. Amma Ranar Idin Azumi, Itace Ranar da Zaku Bude Baki daga Azuminku. Ita Kuma Ranar Idin Layya, To Kuci daga Naman Abin Yankanku”*._

     _*LADUBBAN SALLAR IDIN AZUMI*_
    ➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖
_Idin Azumi Ta Kunshi Wasu Ladubba da Hukunce-Hukunce da Suke Bukatar Dukkan Musulmi Ya Kiyayesu Domin Samun Cikakken Lada a wurin Ubangiji. Ladubban Sun Hada da:_

_*1. FITAR DA ZAKKAR FIDDA KAI:* Bayar da Zakkar Fidda Kai Wajibi Ne Akan Dukkan Musulmi Mai Iko. Ana Iya Bayar da Ita a Kowane Lokaci Kafin Ayi Sallar Idi. Zakkar Tana tsarkake Ran Mai Azumi ne ba Dukiyoyin Mutane ba. Hadisi Ya Tabbata *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa:_
عن أﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ، ﻗﺎﻝ: *”ﺇﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﺮﺽَ ﺻﺪﻗﺔَ ﺍﻟﻔﻄﺮِ ﻃُﻬْﺮَﺓً ﻟﻠﺼﺎﺋﻢِ ﻣﻦ ﺍﻟﺮﻓﺚِ ﻭﺍﻟﻠّﻐْﻮِ ﻭﻃُﻌْﻤَﺔً ﻟﻠﻤﺴﺎﻛﻴﻦِ“*

_An Kar6o Daga *Ibn Abbas (ra)* Yace: *“Lallai Manzon Allah (ﷺ) Ya Farlanta Zakkar Fidda Kai Don tsarkake Mai Azumi Daga Alfasha da Munanan Zantuka Kuma Kuma ta Zamo Abinci Ga Miskinai”*._

_*2. KABARBARI RANAR IDI:* Sunnah Ce Yin Kabarbari Ranar Idi. Ana Farayi Ne a Safiyar Ranar Har Zuwa Idar da Sallar Idin. *Allah* Madaukaki Yana Cewa:_
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ: *”ﻭَﻟِﺘُﻜْﻤِﻠُﻮﺍ ﺍﻟْﻌِﺪَّﺓَ ﻭَﻟِﺘُﻜَﺒِّﺮُﻭﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻋَﻠَﻰ ﻣَﺎ ﻫَﺪَﺍﻛُﻢْ ﻭَﻟَﻌَﻠَّﻜُﻢْ ﺗَﺸْﻜُﺮُﻭﻥَ“*

_*“Kuma domin Ku Cika Kwanakin Kuma Ku Girmama Allah Game da Shiriyar da Yayi Muku Lallai Zakuyi Godiya”*._

_*3. CIN WANI ABU KAFIN FITA SALLAH:* Yin Hakan Riko Ne da Sunnar Annabi Mai Girma. Hadisi Ya Tabbata Cewa:_
عن ﺃﻧﺲ ﺑﻦ ﻣﺎﻟﻚ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ : *”ﻛﺎﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻳﻐﺪﻭ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻔﻄﺮ ﺣﺘﻰ ﻳﺄﻛﻞ ﺗﻤﺮﺍﺕ، ﻭﻳﺄﻛﻠﻬﻦ ﻭﺗﺮًﺍ“*

_An Kar6o Daga *Anas bn Malik (ra)* Yace: *“Manzon Allah (ﷺ) Ya Kasance Baya Sammakon Fita Sallar Idin Azumi Har Sai Yaci Dabinai. Kuma Yana Cinsu ne Witri”*._
```{Bukhari}```

_*4. YIN WANKA DA CIN KWALLIYA:* Hakika *Manzon Allah (ﷺ)* da Sahabbansa Sun Kasance Suna Yin Wanka Sannan Suci kwalliya Idan Zasu Tafi Sallar Idi. Hadisi Ya Tabbata Cewa:_
عن ﻣﺎﻟﻚ ﺑﻦ ﻧﺎﻓﻊ قال: *”ﺃﻥ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻛﺎﻥ ﻳﻐﺘﺴﻞ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻔﻄﺮ ﻗﺒﻞ ﺃﻥ ﻳﻐﺪﻭ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻤﺼﻠﻰ}*

_An Kar6o daga *Malik bn Nãfi'u* Yace: *“Lallai Ibn Umar Ya Kasance Yana Yin Wanka Ranar Idin Azumi Gabanin Yayi Sammakon Zuwa Wurin Sallar Idin”*._

_*5. YIN SALLAR IDIN A FILI:* Hukuncin Sallar Idi Sunnah ce. Sallace da Akeyin Raka'oi Biyu Ba'ayi Mata Sunnar Sujjadar Qabliyya ko Ba'adiyya, Kuma Ba'ayi Mata Kiran Sallah Ko Iqamah._

_*6. SAUYA HANYA:* Yana Daga Cikin Ladubban Sallar Idi Sauya Hanya Yayin Dawowa. Ya Zamanto Hanyar da Akabi Yayin Zuwa Sallar daban da Hanyar da Akabi Yayin Dawowa._
عن ﺟﺎﺑﺮ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ، ﻗﺎﻝ : *”ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺇﺫﺍ ﻛﺎﻥ ﻳﻮﻡ ﻋﻴﺪ ﺧﺎﻟﻒ ﺍﻟﻄﺮﻳﻖ“*

_An Kar6o daga *Jabir bn Abdullah (ra)* Yace: *“Manzon Allah (ﷺ) Ya Kasance Duk Ranar Idi Yana Sa6a Hanya”*._

_*7. BAYYANA FARIN CIKI DA ANNASHUWA:* An Kar6o Hadisi dag Uwar Muminai Tana Cewa:_
*{عن ﺃﻡ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ﻗﺎﻟﺖ : " ﺩﺧﻞ ﻋﻠﻲَّ ﺭﺳﻮﻝُ ﺍﻟﻠﻪِ ﺻﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋﻠﻴﻪِ ﻭﺳﻠَّﻢ ﻭﻋِﻨﺪِﻱ ﺟﺎﺭﻳﺘﺎﻥِ، ﺗُﻐَﻨِّﻴﺎﻥِ ﺑِﻐِﻨﺎﺀِ ﺑُﻌﺎﺙَ : ﻓﺎﺿﻄﺠﻊ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻔِﺮﺍﺵِ ﻭﺣﻮَّﻝ ﻭﺟﻬَﻪ، ﻭﺩﺧﻞ ﺃﺑﻮ ﺑﻜﺮٍ ﻓﺎﻧْﺘَﻬَﺮَﻧِﻲ، ﻭﻗﺎﻝ : ﻣِﺰْﻣﺎﺭﺓُ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥِ ﻋِﻨﺪ ﺍﻟﻨﺒﻲِّ ﺻﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋﻠﻴﻪِ ﻭﺳﻠَّﻢ، ﻓﺄﻗﺒﻞ ﻋﻠﻴﻪ ﺭﺳﻮﻝُ ﺍﻟﻠﻪِ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡُ ﻓﻘﺎﻝ : ﺩﻋْﻬُﻤﺎ......}*

_An Kar6o daga *Aisha Uwar Muminai (ra)* Tana Cewa: *Manzon Allah (ﷺ)* Ya Shigo a Wurina Akwai Wasu Yara Mata Guda Biyu Suna Rera Wakar Bu'as, Sai Ya Kishingida Akan Shimfida Ya Juya Fuskarsa. Sai *Abubakar* Ya Shigo Ya Fara Hantara Na Yana Cewa Sarewar Shedan a Wurin *Manzon Allah (ﷺ)!* Sai *Manzon Allah (ﷺ)* Ya Fuskanceshi Yace: *“Ka Rabu Dasu”*.........._

_*8. GAISHE-GAISHE:* Yana Daga Cikin Ladubban Ranar Idi Shine Gaishe Gaishe tsakanin Musulmai da Kuma Ziyartan Juna tare da Gabatar da 'Yan Kyaututtuka._


_Anan Zan Dakata Sai Mun Hadu a Rubuta Na Gaba_

*سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن الإله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك*

_*✍🏼Sulyman Yahya*_
      _{Abu Aysha Almaliky}_

*📞+2347055883010*

*Zaku Iya Bibiyar mu a Shafin Facebook ta Wannan Adireshin👇🏽👇🏽*
https://www.facebook.com/groups/222507361428028/

_*Ko A Telegram ta:*_

https://t.me/joinchat/OOh5_RUljMIixFLQgNCDyg


Share:

TAMBAYA TA 134


ZAN IYA BADA KUDI, A MAIMAIKON ABINCI A ZAKKAR FIDDA-KAI ?

Tambaya
Assalamu alaikum Dr. shin ana iya bada kudi azakatul fitr maimakon kayan abinci ???

Amsa
Wa alaikum assalam, 
Annabi S. A. W ya wajabta zakkar fidda-kai sa'i na dabino ko Sha'ir Kamar yadda ya zo a hadisin Ibnu Umar wanda Muslim ya rawaito a lamba ta (2287).

Abin da Malamai suka fahimta a hadisin da ya gabata shi ne ana fitar da zakkar fiddakai ne daga abin da mutanen garinku suka fi ci kamar Shinkafa Dawa Masara a wajan 'yan Nigeria. 

Fukaha'u sun yi sabani game bada kudi a maimakon abincin da ya zo a hadisi :

1. Umar Dan Abdulaziz da Abuhanifa da Ibnu-taimiyya da Albani da wasu magabata sun tafi akan halaccin bada kudi a maimakon zakkar fiddakai saboda abin da yasa aka shar'anta zakkar fiddakai shi ne: wadatar da talakawa daga barin roko a ranar IDI hakan kuma yana tabbata ta hanyar bada kudi ko kimar abincin. 

2. Ya wajaba a fitar da abincin da mafi rinjaye suke ci, saboda Tun da Annabi SAW ya fadi sunayen abinci, hakan sai ya nuna su yake so a fitar ba kimarsu ba, kamar yadda yake a hadisin Ibnu Umar Wanda ya gabata. 

Zance na biyu ya fi inganci saboda bin sunnar Manzo shi ne daidai, tare da cewa in an samu lalura ta karancin abinci ko kuma talakawa suka nuna sun fi bukatar kudi ya halatta a fitar da kudin ko kimar abincin a maimakonsa, saboda akwai hadisai da suke nuna halaccin amsar kima a babin zakkar dabbobi in SA'I bai samu dabbar da ya kamata ya amsa ba. 

Don neman Karin bayani duba: Al-mabsud 2/156 da kuma Al'istizkaar 9/346 da kuma Al'iktiyarat Alfiqhiyya lil'Albani na Abu-shady shafi na 209-210

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa

13/6/2018
Share:

SALLAR IDI DA HUKUNCINTA 1

_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_

       _*SALLAR IDI DA HUKUNCINTA*_
       ➖➖➖➖➖➖➖➖➖

                 _*FITOWA TA 'DAYA*_

_Da Sunan *Allah* Mai *Rahma* Mai *Jinqai*_

     ```ME AKE NUFI DA SALLAR IDI```
    ➖➖➖ ➖➖➖➖➖➖➖
_*Sallar Idin Azumi* Sallace da Ake Aiwatar da Ita A Farkon Watan Shawwal Bayan Kammala Ibadar Azumin Watan Ramadan Guda Ashirin da Tara (29) Ko Talatin (30). Ana Kiran Wannan Rana da *Idi* Ne Saboda Zagayowa da Takeyi a Kowace Shekara. Kuma Domin Tana Zagayowa da ne da Farin Ciki da Annashuwa Ga Al'ummar Musulmai._

_Addinin Mu Yazo Mana da Bikin Idi Ne Domin Musanyashi da Bukukuwan Idin da Akeyi a Lokacin Jahiliyya, Idin Musulmai Ya Kasance Shi Kadaine Zai Wanzu Kamar Yanda Yazo a Hadisi:_
عن ﺃﻧﺲ ﺑﻦ ﻣﺎﻟﻚ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ : ﺃﻧﻪ ﻗﺎﻝ : *" ﻛﺎﻥ ﻷﻫﻞِ ﺍﻟﺠﺎﻫﻠﻴَّﺔِ ﻳﻮﻣﺎﻥ ﻓﻲ ﻛﻞِّ ﺳﻨﺔٍ ﻳﻠﻌﺒﻮﻥ ﻓﻴﻬﻤﺎ، ﻓﻠﻤَّﺎ ﻗﺪِﻡ ﺍﻟﻨَّﺒﻲُّ ﺻﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠَّﻢ ﺍﻟﻤﺪﻳﻨﺔَ ﻗﺎﻝ : ﻛﺎﻥ ﻟﻜﻢ ﻳﻮﻣﺎﻥ ﺗﻠﻌﺒﻮﻥ ﻓﻴﻬﻤﺎ ﻭﻗﺪ ﺃﺑﺪﻟﻜﻤﺎ ﺍﻟﻠﻪُ ﺑﻬﻤﺎ ﺧﻴﺮًﺍ ﻣﻨﻬﻤﺎ : ﻳﻮﻡُ ﺍﻟﻔﻄﺮ ﻭﻳﻮﻡُ ﺍﻷﺿﺤَﻰ“*

_An Kar6o daga *Anas bn Malik (ra)* Lallai Yace: Mutanen Jahiliyya Sun Kasance Sunada Kwanaki Biyu a Kowace Shekara da Suke Bukukuwansu da Wasani a Cikinsu. A Yayin da Manzon Allah (ﷺ) Ya Iso Madina Sai Yace: *“Kun Kasance Kunada Kwanaki Biyu da Kuke Wasanni a Cikinsu, Hakika Ubangiji Ya Musanya Muku da Mafiya Alkhairinsu: Sune Idin Azumi da Idin Layya”*._

_Yana Daga Cikin Abinda Ke Wajaba Akan Musulmi Ya Bayyana Farin Cikinsa a Wannan Ranaku Tare da Bayar da Kyaututtuka Ga Kananan Yara Don Sanyasu Cikin Nishadi da Annashuwa._

_*Sallar Idin Azumi* Itace Farkon Idin Musulmai Wacce Take Zuwa Kafin Idin Layya. Ana Gudanar da Idin Azumi Ne a Daya Ga Watan Shawwal, Sannan Idin Layya ta Biyo Baya wacce Akeyinta a Goma ga Watan Zul-Hijjah. Ana Kiran Idin Azumi Ne da *Idil Fidr* Saboda Wannan Ranar Itace Rana Ta Farko da Musulmai Suke Cin Abinci da Shan Abinsha da Jima'ai da Rana Bayan Sunyi Wata Daya Cir Ba Tare da Samun Wannan Daman ba. Saboda Hakane Ma *Manzon Allah (ﷺ)* Ya Hana Yin Azumi a Wannan Rana ta Idin Azumi. Hadisi ya Tabbata *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa:_
عن ﺃﺑﻲ ﻋﺒﻴﺪ ﻣﻮﻟﻰ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺑﻦ ﻋﻮﻑ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ : *”ﺷَﻬِﺪﺕُ ﻋﻤﺮُ ﺑﻦَ ﺍﻟﺨﻄَّﺎﺏِ ﻓﻲ ﻳﻮﻡِ ﺍﻟﻨَّﺤﺮِ، ﺑﺪﺃَ ﺑﺎﻟﺼَّﻼﺓِ ﻗﺒﻞَ ﺍﻟﺨﻄﺒﺔِ، ﺛﻢَّ ﻗﺎﻝَ : ﺳَﻤِﻌْﺖُ ﺭﺳﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋﻠﻴﻪِ ﻭﺳﻠَّﻢَ ﻳﻨﻬﻰ ﻋﻦ ﺻﻮﻡِ ﻫﺬﻳﻦِ ﺍﻟﻴﻮﻣﻴﻦِ، ﺃﻣَّﺎ ﻳﻮﻡُ ﺍﻟﻔﻄﺮِ ﻓَﻔِﻄْﺮُﻛﻢ ﻣﻦ ﺻﻮﻣِﻜُﻢ ﻭﻋﻴﺪٌ ﻟﻠﻤﺴﻠﻤﻴﻦ، ﻭﺃﻣَّﺎ ﻳﻮﻡُ ﺍﻷﺿﺤﻰ ﻓَﻜُﻠﻮﺍ ﻣﻦ ﻟﺤﻮﻡِ ﻧﺴُﻜِﻜم“.*

_An Kar6o Daga *Abi-Ubaidah Maula Abdulrahman bn Auf (ra)* Yace: Naga *Umar bn Khaddab (ra)* a Ranar Idin Layya, Ya Fara Yin Sallah Kafin Yayi Khudubah Sannan Yace: *“Naji Manzon Allah (ﷺ) Yana Hana Azumtar Wadannan Ranaku Biyu: Amma Ranar Idin Azumi, Ranace da Zaku Bude Bakin Azuminku, Kuma Idi Ga Musulmai. Amma Ranar Ranar Idin Layya, To Kuci daga Abin Yankanku”*._

            _*LOKACIN SALLAR IDI*_
            ➖➖➖➖➖➖
_Lokacin Sallar Idi Yana Farawa Ne Yayin da Rana ta Dan 'Dago Kadan. Wannan Shine Mazhabin Malikiyya da Hanabila da Shafi'iyya kuma da Hanafiyya._

_Hakika Ya Tabbata A Sunnah Lokacin Sallar Idi Yana Farawa ne Lokacin Hantsi Har Zuwa Lokacin da Rana Tayi Zawali. Abinda Yafi dacewa Shine A Gaggauta Yin Sallar a Idin Layya, Sannan a Jinkirtata a Idin Azumi. Wannan Shine Abinda Jamhur Suka Tafi Akanshi Kuma Shine Zantukan Malaman Malikiyya._


_Anan Zan Dakata Sai Mun Hadu a Rubuta Na Gaba_

*سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن الإله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك*

_*✍🏼Sulyman Yahya*_
      _{Abu Aysha Almaliky}_

*📞+2347055883010*

*Zaku Iya Bibiyar mu a Shafin Facebook ta Wannan Adireshin👇🏽👇🏽*
https://www.facebook.com/groups/222507361428028/

_*Ko A Telegram Ta:*_

https://t.me/joinchat/OOh5_RUljMIixFLQgNCDyg


Share:

TSOKACI KAN ZAKKAR FIDDA KAI


*TSOKACI AKAN ZAKKAR FIDDA KAI*
Abdullahi Dan Abbas (RA) yace: “Manzon Allah (SAW) ya farlanta zakkar fidda kai, Saboda tsarkakewa ne ga mai azumi, daga maganganun da ba su dace ba, kuma abinci ne ga miskinai” 

Abdullahi Dan Umar (RA) kuma cewa ya yi: “Manzon Allah ya yi umurni da zakkan fidda kai ga yaro da babba da Duk wadanda kuke kula da su” (Riwayar Daru Kudniy).

Don haka mai gida Wanda yake da hali zai ba da nasa da na Matansa, yaransa, da duk waɗanda suke ƙarƙashinsa, Sun yi azumi ne ko ba su yi ba, don faranta ran talakawa da miskinai ranar sallah kada su je bara ko roƙo, ana cikin farin ciki su kuma suna baƙin ciki, shi ya sa aka ce a ba su don a faranta mu su rai.

         *ABIN DA ZA A BAYAR:* 
Za a bayar da Sa’i guda ne na kowane mutum Daya, daga dukkan nau’in abin da ake kiransa abinci, ba lallai sai dabino ko Alkama ba, wannan shi ne bayanin da malamai suka tabbatar.

Don haka za a iya bayar da sa’in dawa, gero, masara, shinkafa da garin hatsi, ko na kwaki, matuƙar dai abinci ne babu laifi.

         *LOKACIN FITARWA:* 
Ana bayar da wannan Zakkar ne ana gobe sallah kafin a fita zuwa Masallaci, kamar yadda Hadisin ɗan Umar (RA) ya nuna cewa “Manzon Allah ya yi umarni da bayar da zakkan fidda-kai kafin fitan mutane zuwa masallaci” (Bukhari da Muslim).

          *WANDA ZA A BA WA* 
Za a bawa miskini ne ko faƙiri wanda ba ya da hali, kamar dai yadda Annabi (SAW) ya ambaci lafazin Miskini, to shi ne za a ba shi, ba lallai sai an rarraba ga wadanda aka ambace su a cikin Ayar Zakka ba.

Adda'u Waddawa Social Media 
27/Ramadan/1441
20/May/2020
Share:

TAMBAYA TA 136

YAUSHE AKE FARA KABBARORIN KARAMAR SALLAH??

An tambayi Shaykh Ibnu Uthaymeen Allah ya masa rahama yaushe ne ake fara kabbarorin ranan idi karama, Sannan kuma yaushe ne ake gamawa??

Sai Shaykh ya bada amsa da cewa "Kabbarorin da ake yi ranan idin ƙaramar sallah ana farashi ne daga faɗuwan ranan karshe na watan Ramadhan har zuwa lokacin da liman zai zo domin gabatar da sallar idi".

مجموع الفتاوى ١٦/٢٥٩

ALLAH AKBAR ALLAHU AKBAR LA'ILAHA ILLALLAH, ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR WA LILLAHIL HAMDU

#Zauran ansarussunnah

Telegram: https://t.me/ansarussunnah

Share:

SUNNONI DA LADUBBA GUDA 17 NA RANAR IDI


SUNNONI DA LADUBBA GUDA 17 NA RANAR IDI

*1-Yin ado da kwalliya dan ranar Idi*

Saboda Hadisn Umar bin kaddhaba R.A.
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، 948.

*2-Yin wankan ranar Idi kafin tafiya sallar idi*

Ibn Umar R.A ya kasance baya fita sallar idi har sai yayi wankan idi.
@ﻣﻮﻃﺄ ﻣﺎﻟﻚ، 384.

Sa'id bn Musayyib Allah yayi masa Rahama yana cewa:
*"Manyan sunnonin ranar Idi guda ukku ne tafiya masallacin idi a kasa da cin abinci kafin afita a idin karamar sallah da kamewa daga cin komai sai an dawo a babbar Sallah da yin wankan idi"*
@ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺇﺭﻭﺍﺀ ﺍﻟﻐﻠﻴﻞ‏( 3/104 ‏) ﻭﺇﺳﻨﺎﺩﻩ ﺻﺤﻴﺢ.

*3-Yin sallar idi kafin Huduba*

Manzon Allah s.a.w da Abubakar da Umar sun kasance suna yin Sallar idi kafin Huduba.
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ - ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺼﻼﺓ-ﺗﻔﺮﻳﻊ ﺃﺑﻮﺍﺏ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﺑﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﺣﺪﻳﺚ :972 ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻰ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻰ ﺩﺍﻭﺩ ﺣﺪﻳﺚ ﺭﻗﻢ 1134 0

*4-Haramunne yin Azumi a ranar Idi guda biyu,idan azumi da idin Layya*

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Babu azumi a ranakun idi guda biyu,idin azumi da idin Layya)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ،1197

*5-Cin abinci ko wani abu kafin tafi sallar idin azumi,kuma anfi so aci dabino kuma aci mara sabanin Idan layya ana kamewa ba'acin komai sai an dawo daga Idi*

Manzon Allah s.a.w ya kasance baya tafi sallar idin azumi har sai yaci Dabino kuma yana cin dabinon ne mara.
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، 953.

*6-Yin sallar Idi a musalla shine sunnah wato a bayan gari a wani fili ba masallaci ba*

Manzon Allah s.a.w ya kasance yana fita musallane don yin sallar idi.
@ﺍﻟﻠﺆﻟﺆ ﻭﺍﻟﻤﺮﺟﺎﻥ، 510.

Ibn Umar R.A yana cewa:
*"Manzon Allah s.a.w yana fitane da wuri zuwa musalla dan yin sallar idi...."*
@ﺳﻨﻦ ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ، 1294

*7-Sunnane a fitar da mata da yara zuwa sallar idi,amma matan suyi shiga ta musulinci kuma kada su sanya turaren da kamshensa yake tashi*
@ﺍﻟﻠﺆﻟﺆ ﻭﺍﻟﻤﺮﺟﺎﻥ، 511.

Sayyadina Abubakar R.A yana cewa:
*"Hakkine akan kowace budurwa da macen aure fita zuwa sallar idi"*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ ﻭﺳﻨﺪﻩ ﺻﺤﻴﺢ .

*8-Tafiya masallacin idi kasa idan da ikon hakan*

Manzon Allah s.a.w ya kasance yana tafiya masallacin idi akasa kuma ya dawo akasa.
@ﺣﺴﻦ / ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ ﻟﻸﻟﺒﺎﻧﻲ، 1078 ‏( 1311 )

Aliyu bn Abi Dhalib R.A yana cewa:
*"Yana cikin Sunnah tafiya sallar idi a kasa kuma aci wani abu kafin a fita idi"*.
@ﺣﺴﻦ /ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻟﻸﻟﺒﺎﻧﻲ، 530

*9-Chanza hanyar dawowa ko hanyar zuwa masallacin idi*

Manzon Allah s.a.w ya kasance yana chanza haryar dawowa daga masallacin idi.
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، 986.

Ibn Umar R.A yana cewa:
*"Na koya daga Manzon Allah s.a.w chanza har dawowa daga masallacin idi*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ ﻟﻸﻟﺒﺎﻧﻲ، 254.

*10-Yin kabarbari na ranar Idi*

*_Ana fara kabbarar ne daga Faduwar Ranar karhen ta Ramadhana idan an ga watan Shawwal za'a fara yin kabbarori har zuwa fitowar LIMAN dan yin sallar IDI_*

Imam Sun'ãni yana cewa:
*"Yin kabbar tun daren idi har zuwa fara sallar idi yin hakan sunnane abisa haduwa mafi yawan malamai saboda farrasa fadin Allah Madaukakin sarki*-
*(ﻭَﻟِﺘُﻜَﺒِّﺮُﻭﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻋَﻠَﻰ ﻣَﺎ ﻫَﺪَﺍﻛُﻢْ ﻭَﻟَﻌَﻠَّﻜُﻢْ ﺗَﺸْﻜُﺮُﻭﻥَ )*
@ ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ : 185
@ ﺍﻟﺼﻨﻌﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺳﺒﻞ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﺍﻟﺠﺰﺀ ﺍﻟﺜﺎﻧﻲ : 100-101 .

*11-Sigogin Kabbarorin ranar Idi*
Daga Cikin sigogin da aka samo daga Sahabbai sun hada da;-

Siga ta farko;-
*ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻻ ﺃﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ*
@ﻣﺼﻨﻒ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ، ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ.ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺇﺭﻭﺍﺀ ﺍﻟﻐﻠﻴﻞ ‏( 3/125 ‏)ﻭﺇﺳﻨﺎﺩﻩ ﺻﺤﻴﺢ.

Siga ta biyu;-
* ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ*

Siga ta Ukku;-
* ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ، ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﻭﺃﺟﻞ، ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ ﻫﺪﺍﻧﺎ .
@ﺍﻟﺴﻨﻦ ﺍﻟﻜﺒﺮﻯ ﻟﻠﺒﻴﻬﻘﻲ، ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ . ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺇﺭﻭﺍﺀ ﺍﻟﻐﻠﻴﻞ
‏( 3/125 ‏)ﻭﺳﻨﺪﻩ ﺻﺤﻴﺢ

*12-Sanya Turare dan zuwa sallar idi*

Abdillahi dan Umar R.A ya kasance baya fita sallar idi har sai yayi wanka ya sanya turare.
@ﺃﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﻟﻠﻔﺮﻳﺎﺑﻲ - ﺑﺎﺏ ﻣﺎ ﺭﻭﻱ ﻓﻲ ﺍﻻﻏﺘﺴﺎﻝ ﻟﻠﻔﻄﺮ ﺣﺪﻳﺚ 015

*13-Ba'a sallar nafila kafin sallar idi ko bayanta,kuma ba'a kiran sallah ko iqama*
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺤﻪ - ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﺣﺪﻳﺚ :1517
@ﺃﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﻟﻠﻔﺮﻳﺎﺑﻲ - ﺑﺎﺏ ﻣﺎﺭﻭﻱ ﺃﻧﻪ ﻻ ﺻﻼﺓ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻗﺒﻞ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻭﻻﺑﻌﺪﻫﺎ ﺣﺪﻳﺚ 0143

*14-Yin gaisuwar sallah da fatan Alkhairi da fatan Allah ya maimata mana*

An samu daga aiyukan maganata suna yiwa junansu barka da sallah da fatan alkhairi,daga cikin abinda suke fada akwai;-
*ﺗﻘﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻨﺎ ﻭﻣﻨﻚ*

*15-Yin wasa na al'ada wanda babu sabon Allah acikinsa dan nuna farincin ranar Sallah,sannan mata zasu yi nasu wake da buda kayan kidansu na al'ada wanda babu sabon Allah*
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺤﻪ - ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ - ﺃﺑﻮﺍﺏ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ - ﺑﺎﺏ ﺍﻟﺤﺮﺍﺏ ﻭﺍﻟﺪﺭﻕ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪ - ﺣﺪﻳﺚ :921 ، ﻭﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺤﻪ - ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ - ﺑﺎﺏ ﺍﻟﺮﺧﺼﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻠﻌﺐ ﺍﻟﺬﻱ ﻻ ﻣﻌﺼﻴﺔ ﻓﻴﻪ ﻓﻲ ﺃﻳﺎﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪ - ﺣﺪﻳﺚ 01527:

*16-Cin wani abu daga cikin abinda ka yanka na layya bayan dawowa daga sallar Idi*

Manzon Allah SAW ya kasance baya cin abinci a idin babbar sallah har sai ya dawo daga Masallaci sannan yana fara cine daga wani sashe daga abinda ya yanka na layyarsa.
@ﺯﺍﺩ ﺍﻟﻤﻌﺎﺩ / .144

*17-Girmama ranar Idin layya akan sauran ranaku domin ranace mai girma awajan Allah*

Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Mafi girman ranaku a wajan Allah sune; Ranar Layya da ranar washe garin Layya)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ 

  Allah ne mafi sani

*Ina yiwa dukkan musulmai barka da sallah da fatan alkhair,Allah ya maimata mana*

* ﺗﻘﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻨﺎ ﻭﻣﻨﻚ*
Share:

YIN KABBARORI DA ƘARAMAR SALLAH

YIN KABBARORI DA KARAMAR SALLAH

Yin Kabbarori Sunnah ne mai karfi a Sallar Idi karama(Idul fitr) saboda fadin Allah:

 "وَلِتُكْمِلُوا الْعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُوا اللَّهَ عَلَىٰ مَا هَدَاكُمْ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ"

"...kuma dõmin ku cika adadin, kuma dõmin ku girmama Allah a kan Yã shiryar da ku, kuma tsammãninku, zã ku gõde".

 Lokacin farawa daga ganin watan Shawwal, ma'ana daga faɗuwan ranan karshe na watan Ramadhan, Ibnu Abbas ya ce: "Haqqi ne a kan dukkan musulmi idan sun ga watan Shawwal su yi Kabbara". Lokacin yana karewa ne daga fitowan liman zuwa gabatar da sallah".

Sigan Kabbarorin:

ALLAH AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLALLAH, ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD

#NUURUL ISLAM
Domin samun shirye shiryenmu saiku biyomu ta wadannan hanyoyin

Channel:
https://t.me/nuurul_islam

Telegram:
https://t.me/joinchat/Rgmm4Bxels5dz39qg8gX7Q

Share:

AZUMIN MAI HAILA DA BIƘI


AZUMIN MAI HAILA DA MAI BIƘI

Baya halatta ga mai jinin haila ko na biƙi(haihuwa) ta yi azumi qaulan wahidan, sannan koda ta yi azumin bai yi ba, idan kuwa da gangan ne tayi to dole ta tuba ga Allaah SWT.

Abunda ke kan mai haila ko jinin biƙi in sun sha azumi shine ramuwa.

GA WASU TSOKACI:

A) BAMBANCI TSAKANIN JININ HAILA DANA ISTIHADA(CUTA):
1. Jinin haila yana da duhu wanda yake karkata zuwa ga ruwan ƙasa-ƙasa ko kunkunniya. Shi kuwa jinin istihada sakakke ne mai karkata zuwa ga haske.
2. Jinin haila yana da wari ko ƙarni.
3. Jinin haila yana tunkuɗa yayin fitowar sa, saɓanin na istihada wanda shi bai fiya tunkuɗa ba.
4. Mafi yawan lokuta kafin da kuma lokacin zubar jinin haila akan ji zafi ko ciwo a māra ko kwankwaso ko ciki.

B) ALAMOMIN TSARKI BIYU NE:
1. Zuba ko fitowar farin ruwa wanda mahaifa ke tunkuɗo shi waje bayan jinin haila ya gama zuba.
2. Bushewar gaba(farji), wato ɗaukewa ko yankewar jinin, wanda wasu lokuta akan tabbatar da haka ne idan an saka kyalle a cikin farji, sannan aka cire shi a bushe bayan ɗan lokaci ba tareda jini ba. 

C) SANNAN Ga wani takaitaccen bayani wanda ɗan'uwa malam Abu Uwaisat Zaria ya taɓa yi wanda zai taimakawa mata wurin tantance rikicewar jinin haila da na cuta da kuma tsarki:

1. Ta kiyaye irin launin jinin da ke zuwan ma ta cikin kwanakin hailar ta. 

2. Ta kiyaye yanayin wari ko ƙarnin jinin ta a lokacin al'ada. 

3. Ta kiyaye alamar tsarkin ta. 

Idan ki ka ga tsarkin ki bayan kwanakin hailar ki sun cika, sai kuma wani jinin yazo a cikin wannan watan mai irin launi da ƙarnin jinin hailar ki, sai ki kuma bashi hukuncin jinin haila, a ƙarƙashin haka sai ki sake barin ibadoji har sai kin tsarkaka. Idan kuwa ba shi da waɗannan siffofin to ya zama jinin istihādah(wato jinin ciwo ko rauni), wanda shi baya hana ibada ko mu'amalar aure, sai dai a nema masa magani wurin likitoci.

Dan haka, akan iya yin jinin haila sau biyu ko sau uku ko makamancin haka a wata daya. 

Allaah Yasa mu dace.

Abdullahi Almadeeniy Kagarko.
28/Ramadan/1441
21st May, 2020
Share:

BA A KIRAN SALLAH KO TADA IƘAMA KAFIN SALLAR IDI

BA'A KIRAN SALLAH KO TAYARDA IQAMA KAFIN SALLAR IDI

Ankarbo daga Jabir Bin Sumurah (Allah ya Yarda dashi) yace: " Nayi Sallar Eid (Fitr da Adha) tare da Manzon ALLAH (SAW), ba sau daya ko biyu ba, amma ba tare da Kiran Sallah koh Iqamah ba".

 Saheeh Muslim
Vol2, Hadith2051

Share:

EID SALAH


EID SALAH

Idan har Ranar Eid ta hadu da Jum'ah ( A rana guda ), toh yin Sallar Jum'ah ya zama Sunnah ba Wajibi ba.

Manzon ALLAH (SAW) yace: " Akwai EID guda biyu da zasu hadu a rana guda ( Wato Eid da Jum'ah ), Wanda yaso zai iya Sallar Eid da Jum'ah gaba dayansu, ko kuma yayi Eid sai ya bar Jum'ah, saboda Jum'ah ta zama Sunnah".

Amma saboda Karin Ladah, ka sallah CE su duka (Eid da Jum'ah).

 Sunan Abu Dawood
Vol1, Hadeeth 1073
Share:

MU TUNA DA 'YAN UWANMU MABUƘATA


#Ramadhan

MU TUNA DA ƳAN UWANMU MABUƘATA

A yayin da muke ta shirye shiryen Sallah, ɗinke ɗinken sabbin tufafi, sayen sabbin takalma da jaka, ɗan kunne, sarƙa da kayan ado, hijabai da mayafai da dai sauransu ma kanmu da ƴaƴanmu, TO KAR MU MANTA DA ƳAN UWANMU DA BA SU DA HALIN YIN HAKAN.

Idan da hali su ma a sama masu wanda za su saka suyi fes fes ranar Idi kamar yanda kowa ya ke son kasancewa, idan sababbi ba su samu ba Uwar gida a duba musu cikin waɗanda a ke dasu a gida, a wanke a goge a feshesu da turare a aika musu, haka kai ma Mai gida a duba a cire wa mabuƙata su ma suyi farin ciki, cikin suturun yara ki duba ma wasu mabuƙatan ko marayu da ba su da mai yi musu in ma babu ikon sama musu sababbin.

Haka ku ma ƴan mata da samari, wasu sun tara kaya kamar suyi magana, amma ga sa'anninsu nan wasu ma abokansu ne a na tare amma kun barsu cikin tsimmokara!! 

Abin da yake tsoho a gurinka/ki to wani a gurinsa sabone tas.

Madallah da wanda ya shigar da farin ciki zuciyar dan uwansa.

Telegram:
https://t.me/ansarussunnah
Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form