Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

Showing posts with label Rubutattun Wakoki (Poems). Show all posts
Showing posts with label Rubutattun Wakoki (Poems). Show all posts

WAƘAR BAKANDAMIYAWAƘAR BAKANDAMIYA

Da sunan sarki rabbana mai duniya
Al-kaliƙu wanda ya yo duniya
Ya yi ƙorama har da teku na maliya
Al-maliku kai ke mulkin duka duniya
Sunanka ne farkon faɗi kowace safiya
Kuma kai nake kira da yamma sakaliya.

Na yi yabo gurin Annabi Muhammadu
Da ya fi kowa bauta Annabi Hamidu
Ma'aikin Allah Sahibinmu Mahmudu 
Shalelen Ubangijina ya Ahmadu 
Allah ka ninka salatai a wurin Ahidu 
Manzonmu sha-kundum Mahmudu.

Waƙa ce zan rera wa Bakandamiya
Shafin yanar gizon ga na duniya
Da ya zamo abin son mutanen Ifirikiyya
Kuma sha ziyartar mutanen Nijeriya
Yau shafin ya shiga dukkan nahiya
Fatanmu ya zamo na ɗaya duka duniya.

Matattarar fasaha ce Bakandamiya
Tsangayar marubuta ce Bakandamiya
Sulkumin manazarta ce Bakandamiya
Kajar ɗalibai ce Bakandamiya
Shirinyar Facebook ce Bakandamiya
Kinin Google ce Bakandamiya.

Akwai malumma a shafin Bakandamiya
Mafakar ɗalibai ce Bakandamiya
Muna sada zumunci a Bakandamiya
Muna koyon ilimi a Bakandamiya
Akwai fa nishaɗi a shafin Bakandamiya
Komai an taskace kamar Wikipedia

Jama'a na yi kiranku maza ku garzaya
Shafin al'ajabin nan maza ku antaya 
Ko gida ko ofis ko akan hanya 
Kuna iya buɗe shafin Bakandamiya 
Sauƙi ne ya zo wa Hausawan duniya
Fatan alheri na ke yi wa Bakandamiya. 


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
  08185819176 
Haimanraees@gmail.com

Share:

RUBUTACCIYAR WAƘAR TARNAƘIWAƘAR AMINU LADAN ABUBAKAR ALAN WAƘA 

Tarnaki

Tarnaƙi hana miƙa 3x

Majaujawa sai cillawa
Sasari kuma ɗaurewa
Tarnaƙi mai zargewa
Takunkumi mai shaƙewa
Tarko mai kamawa
Turaku ko na ɗaurewa
Sarƙa rikicin gangan ƙasar uwa da uba nawa
Tarnaƙi hana miƙewa
Sasari hana rugawa
Garƙami wandon ƙarfe masaka ba ya zaunawa. 


Tarnaƙi hana miƙewa
Sasari hana rugawa
Garƙami wandon ƙarfe a saka ba a zauna ba.

Ubangiji masanin gaibu da baɗini da faken kowa 
Adalin sarki rabbu da yai hanin cutar kowa 
Mai huwacewar mulki daidai da halayyar kowa 
Na taho da buƙatata tsare ni kadda amin arwa, tsare ni kadda a min arwa. 

Ɗan Aminatu tsanina da so da koyin halaye
Mai gidan asahabati da ahal baiti da sufaye
Mai ɗabi'u kyawawa gami da tsarkin halaye 
Nai riƙo da abin ƙauna abin yabon sarari har ɓoye, sarari har ɓoye. 

Kama zuwa daga 'yancin kai zuwa a yau ban kore ba
Ina batun ilimi namu hallanzu dai ba mu ƙosa ba 
Da tattalin arzurƙanmu zuwa a yau ba mu kama ba 
Bare a kai ga ginin birane har yanzu ba mu wuce ƙauye ba 
A shekara hamsin baya magani ba mu samar ba 
A shekaru hamsin har yau ko Keke Napep ba mui ba 
Industry ba ta zauna ba 
Ruwa na sha ba mu samar ba 
Da laturun ba ta zauna ba 
Ga agric ba mu kama ba
Ga ilimi ba a samu ba
Rayuwa ta ƙabilanci, rikicin addinanci ba inda ba mu yi asasi ba. 

Ƙasar da ba ta da jirgin kanta ɗiyanta na zazzagawa
Ƙasar da ba ta asusun kanta ɗiyanta ke da kuɗin cashewa 
Ƙasar da babu zani a jikinta ɗiyanta ke da zanin ɗaurawa 
Mutum guda a cikin 'ya'yanta dubu ɗari da ta haifawa 
Ya tattare arzurƙanta yana rawa da bazar kowa 
Suna kiɗa da bazar kowa 
Wai ma'aikata aka samarwa ko 'yan yasa muka samarwa? 
Wai 'yan ceto muka zaɓowa ko cuta muka ɗaukowa? 
Wai ɗalibai muka yayewa ko ɓeraye muka yayewa? 
Ƙasar babata, ƙasar abbana, Nijeriya ta. 


Share:

RUBUTACCIYAR WAƘAR BURI UKU A DUNIYAWAƘAR AMINU LADAN ABUBAKAR ALAN WAƘA TARE DA FATI NIJAR 
Buri Uku A Duniya

Sarƙaƙiya guda uku
Tai sansani a zuciya
Buri uku a duniya
Buri uku a duniya. 

Sarƙaƙiya guda uku
Tai sansani a zuciya
Buri uku a duniya
Buri uku a duniya. 

Daure masoyi daure daure
Ka san lago na zuciya
Ka san abin buƙatar ruhi
Sarƙa ta sarƙe zuciya
Ni na yi durƙuson
Gwiwoyi kuka ka bi idaniya
Tanyo nake buƙata gunka
Buri uku a duniya
Na zo da mazubin ƙoƙona
Buri uku a duniya
Buri uku a duniya
Buri uku a duniya. 

Ma-dama rayuwa na nan
Ruhi fa za ya wazaya
Ma-dama zuciya na nan
Buri fa za ya antaya
Ga rai da lafiya na nan
Tilas jiki ya hau ƙaya
Tsumma maƙunshe cuta na nan 
Sarƙaƙiya ƙarangiya 
Buri fa yai wa ruhi zobe 
Sarƙa ta ɗaure zuciya 
Buri uku a duniya 
Buri uku a duniya. 

Buri uku a duniya
Sun zam mini ƙarangiya
Sautin bugu na zuciya
Ya sa jiki galauniya
Sarƙaƙiya ƙarangiya
Buri uku a duniya
Burin cikinta zuciya
Na kasa buɗe zuciya
Ɗa zai ɓace a ragaya
Ceto jiki da zuciya.

Ruhi duka da zuciya
Fansa gareki gimbiya
Na gamsu babu karaya
Zan baki duka zuciya
Komai da ke a duniya 
Nau'in dukkansu dukiya 
Tarin kuɗi da dukiya 
Garken awaki saniya
Fansa gareki gimbiya
Burinki dukka duniya 
Share:

WAƘAR ZAIDU IBRAHIM BARMO

ZAIDU IBRAHIM BARMO

Da sunan Rabbana zan fara waƙar Zaidu
Kogin maliya babu mai ganin ƙarshenka. 

Ɗa wurin Ibrahima na layin su Sa'idu
Gwarzonmu a yau muna maka sam-barka. 

Tsira gurin manzonmu wanda ya hana daudu
Kuma shi yazo da sallah yace kar mu yi shirka. 

Kun san mata su ke amfani da tandu
Shi ɗan jibiyawa ko sai dai waraƙa 

In ko rubutu kake so ka je gun Zaidu
Ko ma ba ka iya ba to za ya koya maka. 

Ƙimarsa ta zarce arewa har ta je ga kudu
Watarana duniya ƙwarai za ta yabe ka. 

Maƙiyanka da sun gane ka sai dai su gudu
Murhu da garwashi to wai wa zai taka? 

Masu yi maka hassada suna ruwa kai ko a tudu
Ka yi musu nisa babu mai iya kamo ka. 

Allah kare ka alfarmar Mahamudu 
Ya sa ka zamo a saman maƙiyanka. 

Ana maganar buhu wa ke zancen mudu? 
Kai me gayyar tsiya tafi abinka. 

Ka taka ka rausaya malam Zaidu
A MZM mun sani fa sam ba tamkarka

Allahu ya kiyasheka kamun gafiyar ɓaidu
Ya sa ka zamo cikin ni'ima a kabarinka.

Amin.

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
  08185819176 
Haimanraees@gmail.com

Share:

RUBUTACCIYAR WAƘAR GUGAN ƘARFE


WAƘAR AMINU LADAN ABUBAKAR ALAN WAƘA 


Gugan Ƙarfe

Masu fagabniya a gari
Jure kwaramniya bidiri
Balle ma ta taƙadari
Ɗanduƙusuru mai bidiri
Masu kamar yabo a gari
Ga su kamar suna zikiri
Baƙin halinsu ƙona gari
Ya sattaru Al-ƙadiri
Tsare mu baƙin shirin ja'iri
Kamar na ashana ƙona gari.

Jure kwaramniya gugan ƙarfe kwana alif da ɗari, Allah in ya yarda da kai ba mai iya saka a garari.

A yau ƙoƙon bara na taho gurin mai juya al'amari
Kashe mani gobarar kogi da ta fi ta zahiri bidiri
Wuta daga bahari kogi kasan da akwai shirin garari
Idan ka tsaya mani wuturi
To bani shirin ganin bidiri.

Muhammadu sahibul bushra da ke horo da ai haƙuri
Naziru na gargaɗin da kake da ribar masu yin haƙuri
Muna roƙon gwani wuturi
Ya ƙara dubu-dubun zikiri
Gurin Musbahu cinye-gari
Muhammadu sahibul bashari.

Akwai su gwani akwai nagwanaye akwai agwanaye duk a gari
Akwai 'yan bani ni na iya akwai 'yan mu muke a gari
Akwai 'yan mu da mu aka fara sannan mu muke da gari
Akwai 'yan mu muke fa da gado ba mu bari a karɓi gari.

Allah in ya yarda da kai ba mai iya saka a garari, jure kwaramniya gugan ƙarfe kwana alif da ɗari.

Akwai 'yan ba mu sha kuma ba mu bari wasu ma su sha a gari
Su jaɓa da an sako baki a yau kwalara ta watsu gari
Da masu shirin gada ta zare suna tarko na mai haɗari
Da an kai walƙiya sun zam kamar sun sha ruwan tsari.

Suna da faran-faran a kama suna da wutsilniyar badari
Ga zulwajahaini guntsi-baza kullum aikinsa zaga gari
Yana hana mai zuma talla, yana tallar maɗi a gari
Gari ya watstsake kure yana kiwo tsaka ta gari.

Akwai su ƙuda mazan kwaɗayi halak da raham yana marari
Da yaki-halak da yaki-haram yake burga kamar mazari
Ina ranar sanin ilimi na hauni da dama ai nazari
Kamar jaki da littattafai cikin akumare ba nazari.

Akwai su biri uban ɓarna gata a birai fa taƙadari
Akwai su dila uban wayo da sari ka noƙe ba tare
Akwai kura da kan rago cikin babbansu al'amari
Umurun almushtabiha sai dai dafa'i na yin zikiri.

Akwai riga ta malanta da kan sawa a zare kwari
Da kambun baki al'ainu da yasan ƙage duk sihiri
Hawayena a kunduƙuƙi ina roƙonka Al-ƙadiri
Tsare mu balahirar maƙiya mayar masu dukkanin ƙuduri.

Waɗansu wutar ciki tamkar an bai maye riƙon jinjiri 
Waɗansu ko handama tamkar loma aka bai wa almajiri 
Suna hannu-baka-hannu-ƙwarya tamkar su cinye gari 
Idon su da kunnuwa a rufe summum-buƙumum cikin garari. 

Jure kwaramniya gugan ƙarfe kwana alif da ɗari, Allah in ya yarda da kai ba mai iya saka a garari.
Share:

KAICO!


Kaico!

Bissmillah da sunan ilahi
Wanda ya aiko ɗan Abdullahi
Zan yi batu da tambihi
Bani dama sarkina ilahi.

Mu yaran zamani yau
Ba mu magana ayau
Iyaye na ta fama
Mu kuma muna ta fankama.

Ba mu tsoron ɓaci na ransu
Ba mu yin ladabi garesu
Ba ma biyayya garesu
Amma in buƙata ta tashi mu je wurinsu.

Ra'ayinmu kawai muke bi
Ko mara kyau ne shi za mu bi
Ra'ayinsu ko ba mu bi
Ko da mai kyau ne ba mu bi.

A hakan muke so wai mu ci gaba 
Alhali da uwarmu muke gaba 
Mun ce mu ne za mu shige gaba 
Wai shugabancin ya fi ƙarfin uba. 

To ta yaya ma zamu haske? 
Bayan albarkar mun make? 
Mun aje uwarmu a gefe 
Mun ɓoye ubanmu a shinge. 

Kaico! Wannan lamari da gyara 
Shi ya sa ma har na ɓara 
Ku ka ji ni ina ta ƙara 
Sai ka ce wanda sago ya sara. 

To wallahi mu yi hankali
An ce duniya ɗamarar jangali
Dole sai an bi ta a hankali
Ko kuma mu faɗa baƙin hali.

Allah ka ƙara wa iyaye lafiya
Ka sa mu gama da su lafiya
Mu zamo masu ƙaunar tarbiya
Ga manyanmu mu zam masu biyayya.

Sarki ka shiryar da mu 
Da abokai da ahalinmu 
Da dukkan 'yan danginmu 
Ka sa shiriya a zukatanmu. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

KUKAN KURCIYA

KUKAN KURCIYA

Da sunan sarkina zan fara
Wannan da shi ne ya yiwo fara
Ya yi kare kana ya yo kura
Ya yi ruwa kuma kana ya yo ƙura
Hikimar Allah sam ba ta da iyaka.

Tsira da aminci gun baban Zahra 
Wannan da cikin annabawa ya yo zarra
Wanda duk wata daraja tuni ya tara
Sahabbai da alaihi duka na tara
Salati gare sa na ke furtawa babu iyaka.

Wai mu yaushe ne za ko mu hankalta
Mu zam nutsuwa da neman mafita
A wayi gari junanmu za mu fifita
Ai ya fi ace kawunanmu muka fifita
Ko ba komai hakan ai zai fishe ka.

Mu kawunanmu kawai muke hange
Ba mu duban wanda yake a jikin shinge
Na ƙoluwa kawai muke hange
Taddo shi kawai muka daddage
Kai mai dogon buri kam kaiconka.

Ƙaddara dai kowa da akwai ta sa
Riga ce da babu mai cire ta sa
Da zamu gane mu daina sa-in-sa
Akan abin da zai zo ne komai nisa
In kuma munƙi za mu wahalta kamar wanda ya sha molanka.

Allah ka tsare mu da na shina
Ka sa mu zamo masu yin murna
Da Duk abin da ka tsara mana
Alfarmar annabinka mijin Nana
Ka sa kar mu zamu cikin masu yin shirka.

Jamilu ne ke waƙar daga nan gefen
Domin isar da saƙo ga 'yan can gefen
Fatana kowa ko ya amfana
Da ɗan abinda na samu a karatuna
Wannan ita ce riba da ba ta da iyaka.

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
  08185819176 
Haimanraees@gmail.com

Share:

HAPPY BIRTHDAY SHAH RUKH KHAN


Happy Birthday Shah Rukh Khan 

Da fari sai na sa Rabbana da yai kowa 
Shi ya yi Albasa da wake ya yi mai kowa 
Tsira, aminci gun sahibi fa son kowa 
Wannan da saƙonsa a yau yana ga duk kowa 
Wannan da darajarsa ta shafe ta kowa 
Wannan da ba ya ƙyashin ya bai kowa 
Wannan da ruhinsa ya shafe na duk kowa 
Ubangijina, baiti a yau zan tsara, fatan ka sa ya amsu gun kowa. 

Ka yi murna da shagalinka gwanina. 
Ka more jin daɗin duniyarka Sarkina 
Ka ɗaure ɗamarar ka zam kawai gwanina 
Ka tunkari aikinka babu batun wani kwana 
Ka kece raininka don ka fi ƙarfin su sarkina 
Ko an ƙi ko an so dai kana gaban arna 
Ko ba a sonka yau dai kana gaban ɓauna 
Shah Rukh gwanina, ka rabu da tunanuka, ka sanya Allah a cikin rai da addu'a. 

In banda ƙaunar gaskiya da bata Ƙarewa
Ya Zana bika da son nan da ba ya ragewa 
Ya Zana gina gida wanda bashi rushewa 
Ya Zana tara Kalaman da basu Ƙarewa 
Ya Zana dasa itacen da bashi bushewa 
Ya Zana shimfiɗa wundin da ba shi yagewa 
Ya Zana ɗaura majanyin da bashi suncewa 
Shah Rukh gwanina da zaka ɗan ji uzurina, da ka canja akala kafin a gicciye kwana. 

In banda burin zuciya da ke Mankantarwa 
Shah Rukh gwanina ya zarce duk gwanin kowa 
Aikin gwanina ya zarce na gwanin kowa 
Gami da baiwa duk ta wuce ta gwanin kowa 
Sauti, kalamai duk sun wuce na gwanin kowa 
Daidai da muryar sa ta fi hasashen kowa 
Hatta fahimtarsa ta fi ta gwanin kowa 
Shah Rukh gwanina da zaka ɗan ji uzurina, wallahi da anyi ruwa da tsakiyar rani. 

Kalma dubu na aje tanadi na waƙena 
Gami da sauti dubbai daban-daban guna
Don tanadi da tsumin fitowa a watarana 
Sannan in kaucewa tunanuka da ke bina 
In ɓadda sawayena ga masu nemana 
Sun ɗauki rayuwa mai tabbata gidan kwana
Gida ga mai burin rayuwa cikin ƙuna
Shah Rukh gwanina Allahu ya kiyaye ka. 

Mutum guda jiran biliyan Shah Rukh gwani gwarzo 
Ɗaya tamkar miliyan Shah Rukh ka zamo kadarko 
Sha-kundum kake ƙwarewarka ta zarce ko'ina 
Bango kake a jikinka Bollywood ta jingina 
Gaba dai mijin Gauri baban Aryan da Suhana 
Mai Raees da fan da Main Hoon Na 
Taka sannu matakalar ɗan Johar da Aditya 
Shah Rukh gwanina, girmanka ya mamaye ko'ina. 

Na zama bawan ƙauna da bata Ƙarewa
Ina haƙa ya na mai rijiya da babu ruwa
Ina ta tihu zuciya tana ta nutsewa
Ina ta bautar ƙaunarka kuma ba ƙiwa
Ina biyewa muryarka ina wayewa
Giya ta so ta sanya ina ta yin shewa
Hatta tunani da sani da ke a ƙwaƙwalwa
Shah Rukh gwanina da ka fahimci uzuri na, da ka yi ɗauki da ruwan kashe ƙuna.

Ubangijina ka taimaki Shah Rukh da taimakonka 
Ubangijina ka agaji Shah Rukh da agajinka 
Ubangijina ka tallafi Shah Rukh da tallafinka 
Ubangijina ka tsare shi da tsarewarka. 
Ubangijina sa hannunka mu ke nema.

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

HAPPY BIRTHDAY AKKI


🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻AKSHAY KUMAR FANS NIGERIA 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻


HAPPY BIRTHDAY AKKI

Na gaida gwani na gwanaye wajen aiki ka wuce jaki, 
Namijin duniya kake sha-kundum kai ne tafki.

Majaujawar nasara kuke ji wannan shi ne Akki,
Balbela da farinta kun san ba ta biɗar wanki.

Gwarzon maza sannu da ƙara shekaru nawa,
Tabbas ka yi mun gani kuma dole mu yo tafawa.

Ka yi haƙuri ya zam nasara yau kai ke shanawa,
Zakaranka ya riƙa yau ga waƙa yana rerawa.

Happy birthday day muke ma domin yau ce ranar ka,
Kuma jajircewa har yau babu wanda ya kamo ka.

Mun yi murna muna ƙara domin muna ƙaunarka,
Aikinka ai na musamman ne shi yasa muke daɗa bibiyarka.

Maƙiya sun sha haushi kai kuma kullum sai tashi
Kai ne iska da ba ta biɗar fuffuke domin tashi.

Maƙiyinka fa kowaye sai mu ce a kamo shi,
Mu danne ɗan nema mu shafe mai ido da toshshi!

Happy birthday sir

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

💫 *AKKIANS NA ALFAHARI DA KU* 💫

Share:

HRITHIK ROSHAN

HRITHIK ROSHAN

Gwani na gwanaye ne Hrithik
Ba Ya tsoron Mazan Fama. 

Idan sun zo gabansa fa dole ne su yi cik
Sarki na rawa ko da a ruwa kuma ba lema. 

Mai lambobin yabo ku duba gasu nan birjik
Agwanaye kuwa sai fafitika ake ana nema. 

Ko da birnin Landan kake na san da zaman Hrithik
Labarin gwanintarsa ya shiga har in da na lema.

Idan zance na kafce ne Ɗan Roshan babu mai I ma
Idan ko fage na dambe ne anan sai dai a sara ma. 

Ina kuke masu so na rawa kuzo ku ga mazari goga
Rijiya ta rawa lallai mun gane kai ke da guga. 

Duggu kake ka zamo dakalin mada
Don ko a kafce ka wuce ɗan wada. 

Gurin kyawu a nemo ka
A ƙyale batun su hankaka. 

Gyan ɗa dama an ce ya biyo mahaifi nai
To gashi ko shi har ya ma zarce mahaifi nai. 

Baya rigima da kowa ko da an shige masa ne
Yana da haƙuri da naci ina ma a ce musulmi me ne?

Allahu ka ceci bawanka kasa shi ya gano dai-dai
Ya karɓi shahadarka ya zam bawa akan dai-dai.

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com


Share:

TSOHON NAJADU


TSOHON NAJADU

Mahesh Bhatt ko ku ce Ja'iri 

Uban a wajen haɗa bidiri. 

Rashin haƙuri kamar an ba maye jiran Jinjiri. 

Haɗama kuwa kamar an miƙa loma ga al'majiri. 

Kure ya bi yana ta ɓarna a gari. 

Ga shi biri uban ɓarna kuma yana yawo a cikin gari

Allah shirye shi don Zatinka ko ma samu sauƙi na al'amari.

Babu ɗuyarsa ba na wani a gunsa abin hawa ya gani.

Jaki kenan da littafai cikin akumari babu sani.

Shekaru sun ja amma son zuciya ya hana shi gani.

Wannan tsoho da ban mamaki yake domin ba shi da tunani.

Allah shirya shi don ƙudura taka ya zamo a cikin masu imani.


©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

MAHESH BHATT


MAHESH BHATT

Dattijon biri kafi samari ɓarna. 

Dujal kake jagoran duka arna. 

Cinye duka akan kira ka da ɓauna. 

Tsohon najadu mai ƙwaƙule-ƙwaƙule. 

Kaza kake mai shegen tone-tone.

Ƙaton burgu mai lalube-lalube. 

Mai budurwar zuciya da yawan neme-neme. 

Mai dogon wuya da yawan leƙe-leƙe. 

Kai ga dokin-lada mai yawan hange-hange. 

Kura cinye du da yawan lashe-lashe. 

Sai ƙaton ciki kamar taiki a kwance. 

Allah dai Allah dai ka raba mu ɗan tukwane.

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

GANTALALLIYA


GANTALALLIYA

Da sunan Allah madaukaki nake waƙar Gantalalliya
Allah Rahmanu, Arrahimu mai ikon duka duniya
Ina roƙonka da ka ba musulmai juriya 
Akan irin waƙi'ar da muke fuskanta a duniya 
Albarkacin baban Fati Muhammadu mai son gaskiya. 

A yau zan yo raddi gurin Kangana Wahalalliya
Jaɓa mai dogon baki Jemammiya
Kin taɓo mu ne don haka dole mu yi miki tirjiya
Kuma kin ɗauko hanya ta ɓata Wahalalliya 
Tabbas yanzu kin tabbata ke ce Wawiya. 

A cikin azamarki na son ganin kin zamo Shahararriya 
Kin zamo kunama wacce bata da sabo ko ɗaya 
Kin ci zarafin kowa kuma kin ɓata rawarki gaba ɗaya 
Hakan yasa ayau ki ka zamo gantalalliya
Baki nan ba ki can ko ina gudunki ake yi Mujiya. 

Allah ga baiwarka ta taɓo Addinin gaskiya 
Idan tana da niyyar tuba ka sa ta samu shiriya 
Idon bata da shi ka sa ta zamo Watsatstsiya 
A bita a layi ko'ina ana ga bushiya 
Kuma cikin gaggawa ka sa ta zamo taɓaɓɓiya. 


©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

TAMBAƊAƊIYA


TAMBAƊAƊIYA

• Har yanzu ina nan ina zance kan Mujiya. 
• Kangana ko kuce Firgitacciya. 
• Mai sukar Addininmu ita ce la'ananniya. 
• Ga ta 'yar ƙyamas kama an ɗaura zane ga Muciya. 
• Kin yi asara yar bayan gari Makauniya. 

• Maras hankali kai kuce mata Mahaukaciya. 
• 'Yar bala'i ku kira ta Masifaffiya.
• Ja'ira mai ja'irci 'yar jagaliya.
• Allah ya watsa lamarinki ki zamo Tambaɗaɗɗiya. 
• 'Yar maye mai shisshigi Makakkiya. 

• Shagiɗaɗɗiya mara kunya Karkatacciya. 
• Sai zare ido kamar ana yi wa Mujiya tsargiya. 
• Jemammiya, 'yar bishiya Lanƙwasashiya. 
• Allahu kasa wanga baiwa taka ta gane gaskiya. 
• Ta shiryu ta dawo hanyar Muhammadu mai son gaskiya. 

• Ta daina ƙwafa da makirci ta gane gaskiya. 
• In kuma ba ta da rabo ka sa ta zamo Wulaƙantacciya. 
• A koma gudun ta tun da ta zamo Annamimiya. 
• A wayi gari ta yo mushe ta zamo Sheƙaƙƙiya. 
• Busashiya, mara tsari Wahalalliya. 

• Jamilu ne na Kaduna ke waƙar raddi a gurin Watsatstsiya. 
• Ɗan Abdurrahman na Gadan nan mai bawa musulunci Kariya. 
• Makafcin zamani mai rattabe da ƙafiya. 
• jariri marubuta, neman ƙarin sani bai ɗaya 
• Ina muku sallama, Allah ya ƙare mu da lafiya. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

NAYANTHARA

NAYANTHARA 


Sarauniyar Kudanci Nayanthara
Samun kamar tabbas sai an tona
A can kudanci ta tabbata ba ki da tsara
Ko a cikin mafarki zan so ki zam amarya guna
Da ke ake yi tun da har yau Nayanthara
Wa ke ta zomo idan ana batun su ɓauna
Ni ke na hango a sama babu gadara
Idanuwanki kan sa shauƙi a raina
Balo-balon so a zuciyata tuni kin hura 
Wuta ta bege a ruhina tuni kin kunna 
Goron ɗaurin auren mu na gani ashe tuni kin ɓara 
Ko za ki zaneni na yarda ki zamo mata gunaaa... 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 


Share:

WAƘAR GODIYA

WAƘAR GODIYA

Bismillah da sunan sarki Rabbani
Ilahu ubangijin da ya ƙage ni
Salati a gunsa manzo a gare ni
Aminullah wanda ya zo mana da addini
A yau murna nake kamar gimbiya ce ta aure ni
Saboda abin faharin da ya same ni
Mujallar Zauren Marubuta ta hore ni
Daga ƙarshe gashi kuma yau ta yaye ni
Nagode da karramawar da akai a gareni
Allahu yasa ku cika da imani
Ya taimaka muku kamar yadda kuka taimake ni
Ya yi muku gata kamar yadda ku kai a gare ni
Malamina Zaidu gwarzon zamani
Abubakar Imam ɗin wannan zamani
Allahu ya kare ka daga duk wani abu mai muni
Ka tashi ƙiyama fuskarka ta na annuri
Allahu ya saka da alheri
Ya kare ka daga dukkan wani mai sharri
Jamilu ne ko ko kace jariri
Na marubuta wanda ba ya inkari. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 

Share:

ANUSHKA SHETTY


ANUSHKA SHETTY

In ka ji taken manya ai daban da na yara
In ka ji sautin manya ai daban da yara
In ka ga tafiyar manya ka san ta zarce ta yara
In ka ga fitowar manya ta zarce a kai bara. 

Ga zakkar matan kudu Anushka ta
Kin yi gaba kin zarce su a fada ta
Ga ta gaban-gishin Prabhas Anushka ta
Ko ba a so da kin zo dole a sassauta.

Devasena ba kya tsoron a fafata 
Ga kirarin mace ɗaya kama da dubu Anushka ta 
Kai kauce ga jaruma ta ku bubbuɗa 
Babban daushe wane goro wajen gatsa. 

Babbar bishiya kin zarce a daddatsa 
Ɗanyen gwal ta yaya zai yo tsatsa? 
Karsana ba ki ramewa ko kullum za a yi tatsa 
Bayan bushiya ko mahaukaci bai takawa. 

Gaba dai gaba dai Anushka 'yar lele 
Kyakkywa ce an sani ko ba ta sa lalle ba 
Ko babu ado mata dole su yo Shayi 
Masu kyan ma a gabanki zama suke kamar 'yan tayi. 

Ga nasarori gareta fa ta tattara 
Dama an ce da safe ake kamun fara 
Na yi jinjina ga Sarauniya 
Ni ne Jamilu katibin Sarauniya 

Na yi rattabe kuma zan ƙara ga Sarauniya 
Fatan watarana zaki zo nan Nijeriya 
Kuma in kin zo zaki ganni ya Sarauniya 
Ko ba komai in na ganki zan samu nutsuwar zuciya. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 


Share:

DAGA ZUCIYATA 4


DAGA ZUCIYATA 04

Ko na yi ko kuma ban yo ba
Za ace ban yi dai-dai ba
Komai na yi wai na yi ƙwaɓa
Komai na yi wai ban caɓa ba
Sai kace ni ne na auri asara.

Nima fa ɗa na Adam ne
Nima fa ina da idanu ne
Nima ina fa da hanci ne
Nima ina fa da ai kunne
Nima ina da duk abin da kowa yake taƙama da shi.

Kamar yadda kake son kanka
Haka nima nake son kaina 
Kamar yadda kike son kanki
Haka nima nake son kaina
Kamar kowa ni ma ina son kaina.

Kana so kai ka ji daɗi
Kina so ke ki ji daɗi
Ku sha madara mai garɗi
Da ɗanɗanon duk wani daɗi
To menene yasa ni ban cancanci hakan ba?

In har ma laifi ne na yi
Me ya sa za ku kyare ni?
Madadin ku nusar da ni
Shi ne sai kuma ku tsane ni
To menene ribar hakan don Allah?

Iyaye duk ku yi nazari 
Shugabanni ku yi nazari 
Malamai ku yi nazari 
Manyanmu duk ku yi nazari 
Shin matsalar ta ina take a sassan mu? 

In Allah ya maka ni'ima 
Burinka ka guji al'umma 
In Allah ya jarrabe ka 
Sai ka nufo gun Al'umma 
Ta yaya ita al'ummar za ta ci gaba?

Ka ce ni wai yaro ne 
Aikin ga wai na manya ne 
Manya a cikin dukka mutane 
Wai ni na gaza in gane 
Bayan kuma kullum duniya ni ake cuta. 

Ku sani Allah na nan
Ku sani tsufa na nan
Ku sani mutuwa na nan
Ku sani lahira na nan
Ku sani ranar tsayuwa ita ma na nan.

Rabbana ka yafe mu 
Rabbana ka kare mu 
Rabbana ka shirye mu 
Rabbana ka cece mu 
Rabbana ka kawo mana ɗauki da gaggawa. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 
Share:

MADHURI DIXIT NENE


MADHURI DIXIT NENE

Madhuri Dixit Nene
Duka kin bi su da ɗai-ɗai
Kin buge su fa lallai
Duka kin barsu da tsalle
Ke ce kike kan dai-dai
Madhuri Dixit Nene.

Maƙiyan Madhuri Dixit Nene
Ku tattaro su da ɗai-ɗai
Mu kai su bayan bene
Mu yi musu aikin uj-mai-mai
Mu barsu can su ci ƙosai.

Madhuri Dixit Nene
Ki furta komenene
Zan yi shi komenene
Dominki zan yi ki gane
Gwanar rawa Madhuri Dixit Nene.

Madhuri ba ki da rowa
Madhuri na son kowa
Madhuri gwana ce ta rawa
A kafce ba ta da ƙwawa
Kai sai Madhuri Dixit Nene!

Mai zagin Madhuri Dixit Nene
Ku cakumo fitinanne
Ku kai ga bango ko manne
Ku bashi bulala ne
Ya gane ikon Madhuri Dixit nene.

Sarauniyar rawa uwar gidan Nene
Ni ne Jamilu ki gane
Ko da kina kan bene
Ni zan yabe ki Nene
Saboda son da nake miki Madhuri Dixit Nene!

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 
Share:

PRIYANKA CHOPRA


PRIYANKA CHOPRA

Gaisheki Jaruma Priyanka
Babu kokwanto wuyarki ta isa yanka 
Giwa kike kin fi gaban karnuka 
Daddawa kike kece me gyara miyar kuka 
Hasken rana kike abin biɗa gun shuka 
Alfaharin Bollywood kike jaruma Priyanka 
Ke mata suke shayi yau ba ki da tamka 
Amaryar ɗan Jonas yau gare ki nake baituka. 

Ke ce abin girmamawar mutanen kudu 
Ke ce abar alfaharin mutanen arewa 
Ke ce abar son jama'ar gabasawa 
Ke ce mai sanyaya ruhin jama'ar yammawa 
Sarauniyar Bollywood babu mai tankawa 
In ta fito dole mata su yiyo rusunawa
Ko ba sa so dole su yo gaisuwar girmamawa
Jinjinar ban girma nake a gareki Priyanka.

Kyakkywa ce ita jaruma Priyanka
Attajira ce ita jaruma Priyanka
Shahararriya ce ita jaruma Priyanka
Kuma gwana ce ita jaruma Priyanka
Ta riga ta karɓu a Indiya Priyanka 
Ta yi ƙauri na suna a Amurka
Ko ba ka sonta ka san ta ƙware Priyanka 
Hakan ya sa a yau nake waƙe wacce ba ta da tamka. 

Ni ne Jamilun nan na Kaduna 
Al-katib da ke a Kaduna 
Salon aiki ne yau na nuna 
A cikin saƙon wake daga guna. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
    +2348185819176

Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form