Showing posts with label Tambaya Mabudin Ilimi. Show all posts
Showing posts with label Tambaya Mabudin Ilimi. Show all posts

SHIN AKWAI ZAKKA A CIKIN ALBASHI?


*_SHIN AKWAI ZAKKA A CIKIN ALBASHI?_*


                       *Tambaya*
Malam yaya zakkar ma'aikaci ya kamata ta zamo? Domin wasu ma'aikatu sukan bada alawus a dunkule wanda ya isa zakkah to amma wasu sukanyi gini ko sayen filaye ko gonaki da kudin kafin shekara ta zagayo sun kare 


                           *Amsa*
To dan'uwa, hukuncin wannan albashi zai fara ne daga lokacin da ya shiga mulkinsa, don haka mutukar ba su shekara ba, to babu zakka a ciki, domin ba kawai samun nisabI ne ya ke wajabta zakka ba, dole sai an samu zagayowar shekara daga lokacin da kudin su ka shiga mulkinsa, don haka duk albashin da ya kai zakka, kuma aka ajjiye shi ya shekara to ya wajaba a fitar masa da zakka, amma mutukar shekara ba ta zagayo masa ba, to zakka ba ta wajaba ba akan wanda ya mallake shi.

staidai yana daga cikin dabarun da sharia ta haramta, mutum ya yi abin da zai sarayar masa da wajibi da gangan, don haka mutukar ya sayi filayan ne da nufin kaucewa fitar da zakka, to tabbas ya sabawa Allah.

Allah ne mafi sani

14/5/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Share:

MIJINA YANA SADUWA DA NI A RANAR GIRKIN KISHIYA TA

*_MIJINA YANA SADUWA DA NI A RANAR GIRKIN KISHIYATA?_*


                        *Tambaya:*
Asslmu alaikum Mun kasance mu biyu awajen mijinmu, Sai ya kasance yar'uwata bata iya gamsar dashi, to ko ranar girkinta yakan shigo ya tara dani da rana ko da daddare, Tambaya anan shi ne malam shi hakan ya halasta?
Kuma idan na mishi magana ya daina zuwa baya ji, ba gidan mu daya ba, Dan Allah hukuncin hakan da mafita?


                              *Amsa:*
Wa'alaikum assalam, Ya wajaba ya nemi izininta, tun da hakkinta ne, in har ta sarayar ya halatta ya sadu da ke a ranar kwananki da kwananta.

Saboda lokacin da Nana Saudah ta tsufa ta ji tsoron kada Annabi ﷺ ya sake ta, ta dauki kwananta ta bawa Nana A'isha,kamar yadda Bukhari ya rawaito. Bayan haka Annabi ﷺ yana yin kwana dai-dai a dakunan matansa guda bakwai, ita kuma Nana Aisha yana mata kwana biyu, Saudat kuwa ba ya kwana da ita, saboda ta sarayar da hakkınta.

Ya wajaba mai gida ya guji dukkan abin da zai kawo matsala da fitintinu a tsakanin iyalansa, adalci yana tabbatar da zaman lafiya.

Allah ne mafi sani.

11/7/1437
19/4/2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Share:

SHIN MUSULMI ZAI IYA YIN SALLAH A COCI?


MUSULMI ZAI IYA SALLAH A COCI ! ! *Tambaya:* Assalamu alaikum, Malam Shin ya halatta musulmai su yi sallah a coci kamar ranar juma'a ? *Amsa:* Wa alaikum assalam, da yawa daga malamai sun tafi akan haramcin hakan ko kuma karhanci saboda coci ba ta rabuwa da hotuna, kuma mala'iku ba sa shiga dakin da yake akwai hotuna ko kare a ciki, kamar yadda ya zo a Sahihil Bukhari. Ibnu Khudaamah ya rawaito halaccin sallah a coci mutukar tana da tsafta daga Umar dan Abdulaziz da Auza'i, da wasu jiga-jigan magabata, ya Kafa hujja da cewa: Annabi s.a.w. ya yi umarni da mutum ya yi sallah duk inda ta riske shi, kamar yadda ya yi bayanin hakan a Al-Mugni 1/407. Zance mafi inganci, In har akwai lalura ta rashin wurin sallah ya halatta musulmi ya yi sallah a coci kamar su rasa inda za su yi jumaa, kamar yadda Abu Musa Al-ash'ary ya yi sallah a wata Coci mai suna Nahya a Damashka, hakan ya zo a Musannaf a hadisi mai lamba ta: 4871, in babu kuma to haramun ne. Allah ne mafi sani. *Amsawa:* 16/10/2016 *DR Jamilu Zarewa*

Share:

TAMBAYAR SAKI BA TARE DA WANI LAIFI BA


TAMBAYAR SAKI BA TARE DA WANI LAIFI BA.


Annabi Muhammad S.A.W yana cewa duk Matar da ta tambayi Mijinta Saki ba tare da Wani Laifi ba, toh haramun ne gareta taji kamshin Aljannah, kuma Allah na fushi da ita Mala'ikun Allah Wanda basu Sabon Allah suna tsine mata. Duba cikin (Tirmizy 1199, Da Abu Dawud 2209).

Wannan Hadisan suna karantar damu cewa Allah ne yace ayi Saki, amma fah duk Ranan da ke Mace kika budi bakin ki kikacema Mijin ki ya sake ki ba tare da wani Hujjah mai karfi Wanda Shari'a ta yadda dashi in kin fada ya Sake ki hakan yayi daidai ba, ko kuma ba tare da wani Laifi ba. Haka kawai sharrin shedan da kuma sharrin kawaye ko kuma sharrin abokan zaman ki suka zuga ki ke kuma kika yadda da shawaran su har kika budi baki kika cema Mijin ki ya sake ki yau ke kin gaji da zama dashi. Toh Manzon Allah yace Allah ya Haramta miki jin Kamshin Aljannah, kuma Allah na Fushi dake ah Wannan lokacin, kuma Mala'iku nata tsine miki. Fushin Allah barai bar kanki ba tsinuwan Mala'iku barai kare kanki ba, har sai kin bama Mijin ki Hakuri akan abinda kika furta kuskure kikayi ya yafe miki kafin nan ki samu sawa ba. Allah ya tsare mu Ameeen.


Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah 
WhatsApp Group.

Muhammad Tukur Jalingo
Domin Shiga Wannan Group Mai Tarin Albarka Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Ta Wannan Number
08164223447.
This Group Is Only For Women.
Share:

SALLAR ƘASARU

SALLAR KASARU SALLAR KASARU.

Assalamu Alaikum Malam Dan Allah Inason amin bayani akan Sallar Kasaru. Allah yakara basira Nagode.


Wa'alaikis Salam.
Amsa:Sallar Kasaru Sallah ne Wanda Akeyinta a lokacin da kikayi Tafiya diga garin da kike zuwa wani Gari. Indai misali za'a zo gidan Ku a tambayeki ina kike ko ina kika tafi ne? ace ai kinyi tafiya ne, bawai kinje unguwa ba. To zakiyi kasaru. Kuma in tafiyar yakai km46 anayin Kasaru. Manzon Allah saw yayi Kasaru, Kasaru Sauki ne ga musulmai masuyin Sallah daman shi Addinin Allah a koda yauce mai sauki ne saidai in bakisan yaya zakiyi shi ba sai kiga akwai wahala. In kinyi Kasaru a yayin da kike tafiyar ki kin samu lada, kuma kinyi koyi da Ma aikin Allah ne.

Amma fa ba ko wani tafiya ne zakiyi Mai kasaru ba. In tafiyar nan baishafi na Allah a ciki ba barakiyi kasaru ba. Misali wasu in zasuje party ko fashi ko wani aikin Alfasha a wani Gari babu kasaru a Kansu ko sunyi kasaru a hanya to su tabbata Sallar su bai cika ba Suketa kawai. Sannan Kasarun kwana nawa akeyinta? Akwai Sabanin maluma akan iya kwana kin da akeyi na kasaru. Na farko akwai malaman da suka tafi akan cewa indai kinyi kwana 4 ko 5 a garin da kikaje. To kasaru ya sauka a kanki zaki ci gaba da cika Sallah. Akwai Masu cewa in kinyi kwanaki 15, ko 18 a garin to Kasaru ya sauka a kanki zaki cika Sallar ki. Akwai kuma masu cewa iya kwanakin da duk zaki a wajen duk zakiyi tayin Kasaru ne har ki dawo garin da kike kafin nan Kasaru zai sauka a kanki. To Wallahu Alamu. Amma mun tafi akan in kin yi kwana ki 4 ko biyar ko 15, indai Wannan kwana kin sun cika kuma baki dawo ba. To ki cika Sallar ki shine zance mafi inganci.

Sallar Karasu diga lokacin da kikayi niyyar barin garin da kike zuwa garin da zakije zaki dauki niyyar duk Sallar da ya same ki a hanya zakiyi Kasaru, Sallar Azahar zaki mai dashi Raka'a 2 ne, Sallar La'asar shima zakiyi Raka'a 2, Magariba zaki kawo su dukka 3, Isha'i zakiyi 2 ne, Asubahi zaki kawo su dukka 2. Ba'a rage sallar Asubahi da magariba da sunayin Kasaru. Sannan indai zaki bi Sallar Jam'i ne, misali kinji Ana Sallah a wani Masallaci sai kikace bari ki bi su. To anan zaki ajiye Kasarun ki, zaki cika sallar ki kaman yadda zasu cika nasu. Kuma kada kice ke bara ki bi Jam'i ba sai kin bari sun idar da nasu kema kice zaki naki dabam saboda ke kina Kasaru, kin sabawa koyarwa ta Sunnar Annabi Saw, zaki bi su a lokacin kuma zakiyi Sallar ne kaman yadda zasuyi nasu. ba Kasaru ba. Ka da kaman Misali zaki bisu Sallar Azahar ke kice Kasaru kikeyi bari ki bi su Sallah, lokacin da Liman yayi zaman tahiya na farko sai suka tashi ke kuma kina zaune kina jiran su, su ciko sauran biyun kuyi Sallama tare in kinyi haka kin Sabawa Annabi. Indai zaki bi Sallar ma zauna Gari to zaki cika Sallar ki. Amma in ke kadai zakiyi Sallar ki to zaki yi Kasaru ne. Inda misali kene zakiyi Liman shi, kaman yadda maza sukeyi kuma tare da ma zauna garin toh nan kan zakiyi Kasaru. In yaso kina Sallama sai su kuma su tashi su cika Sallar Su. Wallahu Tala Wa'ala Wa Alam.

Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah
WhatsApp Group.

Muhammad Tukur Jalingo
Domin Shiga Wannan Group Mai Tarin Albarka Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Ta Wannan Number
08164223447.
This Group Is Only For Women.

Share:

HATTARA DA SA ƘARAMAR RIGA IN ZAKA YI SALLAH


TAMBAYA TAMBAYA TAMBAYA 

MATASA AYI HATTARA DA SA 'DAN GUNTUN RIGA DA SUNAN ZAKA YI SALLAH. 

Assalamu Alaikum Malam Ga Tambayana Kamar Haka. Me Hukuncin Mutumin Da Sa 'Dan Guntun Riga Yana Cikin Sallah Sai Iska Ya Daga Rigan a Lokacin Da Yayi Ruku'u Har Bayan Shi Ya Bayyana, Kunkumin Shi Na Waje. Nagode. 

                AMSA
Waalaikas Salaam: Sallar Shi Ya Baci Ya Chanja Riga Sannan Ya Sake Yin Wani Sallah. Domin Inda Ya Bayyana a Bayan Shi Yana Daga Cikin Al'auran Shi, Kenan Yana Sallah Al'auran Shi A Waje. Bi Ma'ana Yana Sallah Ne a Cikin Sirara. Kuma Ba'a Bautama Allah Mutum Yana Cikin Siraishi Har Sai Ya Suturce Jikin Shi daga Sama Har Kasa, Ya Sa Kaya Na Kamala Kayan da Zai Rufe Dukkanin Al'auran Shi. Idan Ka Duba Cikin (Darirul Saleh ila Mazabil Malikiyya) Sallar Shi Ya Lalace Kuma Zai Sake Yin Wani Sabo. Daga Lokacin da Ya Bayyana Al'auran Shi a Lokacin da Rigar Shi Ya Dagu to Daga Lokacin ne Ya Dace Ya Yanke Wannan Sallar ya Je Ya Nemi Dogon Riga Wanda Zai Rufe Mai Al'auran Shi Ya Sa Ya Zo Yayi Sallar Shi. Amma Indai Yana Yin Sallar a Haka Baida Sallah. Sannan Ya Cutar Da Mutanen da Suke Sahun Bayan Shi in Yana Sahun Gaba ne, Domin Yana Bude Musu Al'auran Shi Suna Gani Wanda Yin Hakan Haramun ne. 

Matasa Don Allah Idan Zakuyi Sallah Kasan Cewa Ka Sanya Kayan Da Koda Kayi Ruku'u Ne Bayan Ka Barai Bayyana a Lokacin da Kake Yin Sallar Ba. Wannan Shine Sallah Mai Kalama. Amma indai zaka Sa Dan Guntun Riga wai Kai Gaye Kake Yi. To Kasani Cewa Kana Yin Sallar Da Allah Baya Karban Shi. Idan Ka ji Waazin An Ce Ma Yin Haka Yana Bata Sallah Kai Kuma Kayi Girman Kai Kaki Ka Daina Sawa Kullum a Haka Kake Yin Sallar ka Baka Da Sallah, Sannan Kasani Fa Laifin ka Yafi Na Wanda Da Bai Sani Ba, Allah Barai Kama ka Da Laifin da Da Can baka San Shi Ba, Wanda Kayi ilmi a Kanshi Kaki Dainawa Shine Allah Zai Kama dashi, Tunda Yanzu Kasani Kuma Kaji an Fada Sai Kaki Dainawa da Sunan Gaye Kake Yi. Azabar Allah Na Jiran Ka. Wajibi ne mu Gyara. Allah Yasa mu Gyara Sanya SUTURAR Mu Amiin. 
Dafatan Ka Gane??? 

Wallahu Alamu. 

Daga Zauren Muslim Woman Mata Zallah 
WhatsApp Group. 

MUHAMMAD TUKUR JALINGO 
Domin Shiga Wannan Group Ki Turo Mana Da Cikakken Sallama Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Kai Tsaye Ta WhatsApp Number Namu Kamar Haka 
08164223447. 
This Group Is Only For Woman Please.
Share:

TAIMAKON MABUƘACI YA FI KA KOMA HWJJI BAYAN ZUWAN FARKO


TAIMAKON MABUKACI YA FI KA KOMA AIKIN HAJJI BAYAN ZUWANKA NA FARKO!


_Mutum ya bayar da dukiyarsa ga wanda bashi ya tauye masa don ya biya bashin, ko ya bayar da ita ga Matalauci, ko wanda iyalai suka yi masa nauyi don ya kula da iyalinsa, ko ya ba mai rainon maraya don ya yaye masa wahala, ya fi alkhairi fiye da mutum ya tafi aikin Hajji sau dari bayan zuwansa na farko._

_Domin hakika cusa farin ciki cikin Zuciyar musulmi da taimakon wanda ke cikin kunci da yaye wahalar Mabukaci da taimakon mara karfi ya fi Hajji dubu bayan na farilla._

_Allah Ya bamu ikon taimakawa mabukata._

_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_

_Daga Zauren_
_*🕌Islamic Post WhatsApp.*_

_Domin kasancewa tare da mu a group din *Islamic Post WhatsApp* sai a turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *08166650256.*_

Wassalamu alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.
Share:

HUKUNCIN ISKAR DA KE FITA DAGA GABAN MACE


Tambaya
:
Mene ne hukuncin Iskar da ke fita ta Farjin Mace Shin tana karya alwala ko a'a??
:
Amsa:
:
Malamai Ma'abota Ilimi sunyi Saɓani Dangane da hukunci akan Iskar dake fita ta gaban Mace, Mazhabin Hanafiyya da Malikiyya Sun tafi ne a kan cewa dukkan wani abu da zai fita ta gaban Namiji ko kuma ta gaban Mace wanda kuma asali abisa al'ada ba tanan ba ne hanyar fitarsa, wato kamar irin iskar da take fita ta farjin Mata a waɗan su lokuta ko kuma tsakuwa ko tsutsa ta fita ta wajen Malamai sukace irin wannan ba ya warware alwala, domin wannan Iskar ba daidai take da Tusa ba, Sannan sukace ba a samu wani Nassi afili Ƙarara da yake nuna cewa wannan Iskar tana warware alwala, domin Mαnzon Allαh(ﷺ) cewa yayi:
:
"لا وضوء إلا من صوت أو ريح"
(رواه الترمذي)
MA'ANA:
Ba a sake alwala Sai dai idan anji Sautin (fitar tusa) ko kuma anji warin (tusar):
:
Amma Mazhabin Shafi'iyya da Hanabila Sukace dukkan wani abu da zai iya fita ta Farjin Mace ko Zakarin Namiji koda kuwa a bisa al'ada ba hanyar fitarsa bace kamar irin wannan Iskar ko wani abun da yake Nadiran (abinda ba a saba gani yana fita ta wajen ba) sukace dukkan waɗannan abubuwa suna warware alwala, Sannan ita kuma iskar dake fita ta Farjin Mace sunyi kiyasin ta ne da tusar dake fita ta dubura, sukace tunda dai tusa tana karya alwala to duk hukuncinsu yazama Ɗaya da na tusa kenan, danhaka dole a sake alwala.
:
Amma zance mafi inganci shine dukkan wata iska da zata iya fitowa daga gaban Mace to bata warware alwala, amma inda ta fita ne daga duburarta to ko Shakka babu alwala ta warware domin dukkan Malamai Sunyi ijmā'i akan cewa tusar dake fita ta dubura tana karya alwala danhaka dole sai an sake wata kenan, Sai dai wasu daga cikin Malamai sukace idan Mace taji wannan iska ta fito daga Farjinta to abu mafikyau shine ta sake alwala don ta kubuta daga cikin Sabanin da Malamai sukayi
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
              Daga Zaυren
             Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Share:

BANBANCI TSAKANIN RIBA DA RIIBA


*_BAMBANCI TSAKANIN RIIBA DA RIBA_*


                          *Tambaya*
Don Allah ina da tambaya: wai ma ye riba a musulunci? kuma idan mutum ya siyi abu nera 5 ya halatta ya saida akan nera 8?


                             *Amsa*
To malama riba ta kasu kashi biyu:

1. Akwai ribar jinkiri, kamar ka ba mutum bashin naira hamsin, ka nemi ya dawo maka da naira sittin, ko kuma idan ka bawa mutum bashi, ya yi jinkirin biya, ka ninninka masa kudin da ka ba shi, irin ribar da ake amsa a banki, za ta shiga cikin wannan bangaren.

2. Ribar fi-fiko, kamar yanzu, ki bada naira 1100 tsofafi, a ba ki naira 1000 sababbi, ko kuma ki bayar da shinkafa 'yar gwamnati kwano uku, a ba ki shinkafa ta gida kwano hudu.

Duka wadannan nau'oin guda biyu Allah ya haramta su, kuma ya kwashe musu albarka. Amma idan mutum ya sayi abu naira 5, ya sayar naira 8, wannan ba'a kiran shi riba a musulunci, saboda yana daga cikin riibar da Allah ya halatta, saidai ana so idan mutum yana siyar da kaya ya saukaka, Annabi ﷺ yana cewa: "Rahamar Allah ta tabbata ga mutumin da idan zai siyar da kaya yake rangwame", kamar yadda ya zo a hadisin Bhukari mai lamba ta: 2076

Allah ne mafi sani.

28/08/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Share:

HOTON MU NA YAU: MATAMBAYI BA YA ƁATAShare:

RULING ON SELLING GOODS THAT ARE NOT AVAILABLERULING ON SELLING GOODS THAT ARE NOT AVAILABLE
Question:
Malam, concerning e-business: A picture of goods will be shown to a person and the person will choose the product he likes and pays for it, They (Business men) will add some amount before they give the person the product when it arrives (From abroad), They do so because the goods are not available here and most of them do not have enough capital to order the goods, They make order with the money given by their customers. 

Answer: 
Waalaykumussalam, Such business is prohibited, because it is selling of what is not available to the seller.
Hakim Bn Hizam asked the prophet (PBUH): A person will ask him about goods that he does not have in store, thereafter they will make bargain, then he will go to the market and buy it and give it to the buyer, the prophet PBUH told him that: "Do not sell what you do not have in store" as narrated by Abu Dawud, Tirmidhi, Nasa'i, Ibn Majah and Imam Ahmad.

Islam prohibits such business because it lacks certainty, dishonest person can easily defraud the buyer and the shown goods may not be exactly found in the market. 

 Any business transaction that will cause confusion among Muslims is prohibited. Whoever stands firm on the commands of Allah, He will enrich him unexpectedly as He says in Surah Attalaq. 

Allah knows best.

Dr Jamilu Yusuf Zarewa 
27/10/2019

Share:

ZAMA DA MUGUN MIJI

*TAMBAYA TA 147*

ZAMAN DA MIJI MAI MUGUN HALI:

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah.

Wai ta yi kusan shekaru ashirin da aure, amma a kullum ba ta cikin kwanciyar hankali saboda:-
Mijinta mai munanan halaye ne: Ga dai duka, ga yawan zargi, ga ƙaryar tsiya, ga ƙulla sharri, ga kuma neman mata!
Ko Islamiyya ya hana ta zuwa saboda zargin cewa, wai malaman suna neman matan auren jama’a!
Har da mahaifinta ma ya zarge ta, haka da sauran maƙawabta, sannan kuma da ɗanta na-cikinta mai shekaru sha-shida!
Ta kai shi ƙara wurin iyayensa amma sai suka goya masa baya! Da ta kai wurin iyayenta kuma sai ya yi musu sharri wai sun tozarta shi, don haka ba ya ganin girmansu!
Daga baya da ta ce za ta bar gidansa sai ya yi ta ba ta haƙuri, tare da alƙawarin cewa idan ya sake zargin ta, to daga ranar ya yarda ta bar gidansa. 
Daga baya kuma ya sake yi har sau biyu! A nan ne ya yi alƙawarin cewa: Idan ya sake to a bakin aurensa. Kuma ya sake yi ɗin!!
Da ta kai ƙara wurin manya, shi ne aka tabbatar masa cewa igiyoyin aurensa guda biyu sun tsunke, yanzu saura guda ɗaya, don haka ya kula kar ya sake maimaitawa. Amma kuma ya sake maimaitawa har sau ba iyaka!
Tambayarta: Wai yaya matsayin aurensu? Kuma wace shawara za a ba ta? 

AMSA A147:

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Abin da na lura da shi dai, kamar tun farko ba su bi umurnin da Shari’a ta yi ba ne na yin kyakkyawan bincike tun kafin su fara nema, kuma har a ƙulla auren. Wannan kuwa yana daga cikin manyan musabbabin dukkan matsaloli da yawancin gidajen aure suke fama da su a yau. Amma dai wannan nata ya yi tsanani matuƙa. 

Shawarar da zan iya ba ta a nan ita ce: Ta tafi wurin wani alƙalin musulunci mai adalci, ko wata ƙungiyar musulunci mai ƙarfi kamar ta hisbah, ta kai musu wannan bayanin. Su za su iya gayyatan wannan mijin, su bincike shi har su tabbatar da gaskiyar waɗannan bayanan, daga nan kuma sai su ɗauki matakan da suka dace.

Har matsayin auren nasu ma za ta samu bayanai gamsassu daga wurinsu, idan dai aka zauna da malamai masana, kuma masu tsoron Allaah.

Allaah Ta’aala ya samar mata da mafita, kuma ya sa a dace.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
30/09/2019
12: 08am.

Majlisin sunnah
08164363661


Share:

SHIN ZAN IYA TSARKI DA RUWAN ZAMZAM?


SHIN ZAN IYA YIN TSARKI DA RUWAN ZAMZAM ?
*Tambaya
Assalamu alaikum Malam wani ya tambaye ni, shin zai iya yin tsarki da ruwan zamzam, saboda ya ji an ce yana kara karfin mazakuta, to gaskiya malam ban sani ba, shi ne na ce bari na tambayi Fukaha'u ?
*Amsa
Wa alaikum assalam To dan'uwa ruwan zamzam ruwa ne mai albarka, kamar yadda ya zo a hadisi cewa : Waraka ne ga cututtuka, Suyudi ya kyautata shi a Jami'ussagir, duba Faidhu Alkadeer 3/489.
Saidai duk da haka ya halatta ayi tsarki da shi a zance mafi inganci , saboda ba'a samu dalilin da ya hana hakan ba, ga shi kuma daga cikin ka'idojin malamai duk abin da ba'a samu nassin hani akansa ba a cikin mu'amalolin mutane, to ya halatta.
Sannan sahabbai sun yi tsarki da ruwan da ya bubbugo daga hannun Annabi s.a.w. , ruwan zamzam kuma ba zai fi wannan ruwan daraja ba.
Don neman Karin bayani duba : Hashiyatu Ibnu-abiidin 1\180 da kuma Insaf 1\27.
Allah ne mafi sani
*Amsawa*
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
18\9\2015.
Share:

SHEKARA TA 11 DA YIN AURE AMMA BANDA NI'IMA


SHEKARATA 11 DA AURE BANA JIN NI'IMA??!
:
Daga zauren
Kulafa'ur rashidun
:
Salamun alaikum Nice naje wajan wata maibada magani nayi Mata bayanin abunda kedamuna cewa nayi maganin infection wato ciwon sanyi Kala kala amma bansamu saukiba Kuma tindanayi aure shekara 11 haka nake koda yaushe abushe Kuma bana jinwani kaikayi KO fitar far in ruwa KO kuraje aa bushewa ce kadai saitace aljannune inbari takirawo aljanunta sai ingayamasu sai naceto sukazo nagamasu saisukace tabbas akwai jinsinsu at are Dani sukabani magani nadwo gida amma hankalina bai kwanta DA mgnarsuba .shine nake tambaya menene hukuncina Kuma in akwai shawarwari game dahakan dan Allah abani .nagode
:
              ******
:
Wa,alaikumussalam
Dafarko dai kinje waje. Boka Wanda kuma zuwa wajen su haramunne da bakin Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace: duk wanda yaje wajen boka baza'a kar6i sallar sa ta kwana arba'in (40) ba idan kuma kika gazgata maganar daya fada to kin kafirta. Yanzu abunda yakamace ki shine ki tuba zuwa ga ubangijin halittu insha ALLAHU ze gafarta miki.
.
Dangane da matsalan ki, kuma akwai na halitta akwai na matsala !
.
Sannan wannan bayanan da kikayi
 babu alamun 
 infection aciki. Matsalace ta rashin ni'ima shikuma ansha karanta shi awannan zauren
.
 *Amma ga maganin kaman haka*⤵
.
1: kisamu man hulba zallah seki zuba acikin madara peak ko kuma madaran shanu mai kyau inya rage kaman awa daya ki kwanta seki sha shi amma ba'ason ki kwanta alokacin da kinasha seya dan jima. 

1: ki nemi gero ki surfa shi seki hada da sassaken baure ki Dora kan wuta ki tafasashi sosai inya nuna seki sauke ki tace seki maida ruwan kan wuta ki sa kanunfari, man shanu, mazarkwaila da Zuma seki sake maidashi kan wuta inya nuna zakiji yana qamshi seki sauke kisa samu peak milk gwangwani daya ki juye aciki seki shashi kaman da yamma. Ki dinga yin haka wannan hana saurin magance wannan matsalar da izinin Allah insha Allah .
.
Sannan Ki yawaita shan kankana da cin danyen dabino amma fa ba danye sosai ba.
.
Inkika bi wayannan hanyoyin insha Allah zaki samu waraka. Kuma haquri akeyi kan magani bawai sau daya akeyi abari ba balle ke da kika jima seki dinga yi harse kin warke kuma da yardar Allah in kina yi zaki dinga ganin canji.
.
Allah yasa mudace 
.
➡ Jamila Dahiru Muhsinat Datti
========================
*```Date* ```[1-09-1439]Hj {17-05-2018} 
  Kuna iya samun mu ta Internet/website http://khulafau.cf
_Masu buqatan Group suyima daya daga cikin Number's innan maga ta whatsApp_
+2349033206238
+2347035269582
+2348063796175
           *```Kuna iya samun mu ta facebook*```
facebook.com/khulafaurrashidun
((سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أشْهَدُ أنْ لَا إِلَهَ إِلاَّ أنْتَ، أسْتَغْفِرُكَ وأَتُوبُ إِلَيْكَ))
〰〰〰〰〰〰〰〰✔
*Wanda yaga gyara, yasanar damu !*
Share:

ZAN IYA BIN LIMAN YAYIN IƘAMA?


*_ZAN IYA BI-BIYAR LADANI LOKACIN DA YAKE TADA IKAMA?_*


                        *Tambaya:*
Assalamu alaikum, ina fata malam yana lafiya, bayan haka malam don Allah inada tambaya kamar haka..menene hukuncin maimaita ikama awajen mamu ayayin tada sallah???


                            *Amsa*
To dan'uwa akwai hadisin da yake nuni da cewa: ana bi-biyar ladani lokacin da yake ikama, saidai hadisin bai inganta ba, wasu malaman hadisin sun raunana shi, don haka ba za'a iya gina hukunci akansa ba. Saidai akwai malamai da yawa da suke ganin za'a bi-biyi mai ikama saboda Annabi ﷺ ya kira tad a sunan kiran sallah a cikin hadisin Bukhari mai lamba ta: 601, don haka za ta dau hukuncinta. 

Zance mafi inganci shi ne: ba za'a bi-biyi mai ikama ba, saboda ibada tana bukatar dalili tabbatacce. Kasancewar Annabi ﷺ ya kira Ikama da kiran sallah da suna daya, ba ya nuna hukuncinsu daya ne, saboda idan abubuwa biyu suka hadu ana iya kiransu da sunan daya daga ciki, kamar yadda ake cewa Wata da rana: watanni biyu. 

Don neman karın bayani duba: Almajmu'u na Nawawy 4/122 da kuma Likaa'u babi Almaftuh na Ibnu uthaimin: 219. 

Allah ne mafi sani

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Share:

SHIN YA HALATTA ARNIYA TA YIWA MUSULMA KITSO


*SHIN YA HALATTA ARNIYA TA YIWA MUSULMA KITSO ?*


*Tambaya*

Assalamu alaikum, shin ya halatta Arniyya ta yiwa musulma Kitso ?


*Amsa*

Wa'alaikumus salam 
Ya halatta macen da ba musulma ba ta yiwa musulma kitso, saboda a zancen mafi inganci, al'aurar mace ga 'yar'uwarta mace, shi ne daga guiwa zuwa cibiya, babu bambanci tsakanin kafira da musulma a cikin haka, domin a zamanin Annabi s.a.w. Yahudawa mata suna shiga gidan Annabi s.a.w., kuma ba'a samu suna yin shiga ta musamman ba idan suka ga za su shigo, saidai in kafirar tana da wani sharri da ake jin tsoro, to wannan mace za ta iya suturta daga ita, sannan kuma mutukar akwai musulma to ita ta fi dacewa ayi hulda da ita .

ALLAH NE MA FI SANI

*Amsawa*✍🏻

*DR JAMILU YUSUF ZAREWA*

5/1/2014
Share:

TSINTUWAR DA AKE YIN CIGIYA


*TSINTUWAR DA AKE YIMA CIGIYA ?*
   
*Tambaya:* 
                                                                                                       Assalamu alaikum malam wani bawan Allah ne ya tsinci Naira: #500#, a wurin kuma bai ga wadanda zai yi wa cikiya ba... Ya ya kamata yayi da kudin tsintuwar ?, suna ajiye yanzu haka kusan wata daya .  

*Amsa:*
                                                                                                                                                                                    Wa alakum assalam To dan'uwa idan mutum ya yi tsintuwa ya wajaba a gare shi ya yi cigiya har tsawon shekara guda, idan bai samu mai ita ba, daga nan zai iya amfani da ita, amma in mai ita ya zo daga baya zai biya shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 5761. Amma idan abin da ya tsinta dan kadan ne ba shi da yawa, to ya halatta ya yi amfani da shi ko da bai yi cigiya ba, saboda abin da aka rawaito cewa : Annabi s.a.w. ya ga wani dabino akan hanya, sai ya ce : In ban da ına tsoron na sadaka ne da na ci. Muslim ya rawaito a lamba ta:2527, sai hadişin ya nuna dan karamin abu ba ya bukatar cigiya.  

Malamai şun yi sabani wajan iyakance tsintuwar da ba ta bukatar cigiya, wasu sun ce za'a koma al'adar mutane, duk abin da mutane şuke ganinsa ba a bakin komai ba, to in an tsince shi ba ya bukatar cigiya, Ibnu Khudama ya hakaito daga Imamu Malik cewa: bai wajaba mutum ya yi cigiyar abin da bai Kai a yanke hannu saboda shi ba, wato daya bisa hudun dinari, haka nan sayyadina Aliyu ya tsinci dinare daya ya yi amfani da ita ba tare da yayi cigiya ba. Abin da ya gabata yana nuna cewa: mutukar ba ka samu mai Naira (5,00) din da ka tsinta ba a kusa da Kai, ya halatta ka yi amfani da ita ba tare da cigiya ba, tun ba kudi ne mai yawa ba, kuma mai ita ba zai kwallafa rai Akanta ba. Don neman karin bayani duba : Al-mugni 6/351.
                                                                 Allah ne mafi Sani

*Amsawa* ✍🏻    

 *DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
             
1/11/2015
Share:

BIN JAM'IN ISHA'I DA NIYYAR MAGARIBA

*BIN JAM'IN ISHA'I DA NIYYAN MAGRIBA !!*

*Tambaya*

Assalamu Alaikum, nine nazo masallaci natarar imam yana sallar isha'i nikuma banyi magriba ba shin zan iya binshi da niyyar magriba? Kuma yaya zanyi da sallama tunda adadin raka'o'in ba dayaba? 

*Amsa*


   Eh ya halatta kabishi in yayi raka'o'i 3 kazauna kayi tahiyya kasallame sai katashi dawuri kabishi a raka'ar karshen da niyyar shine raka'arka ta farko a isha'i in yasallame sai kakawo cikin ukun, 
   irin wannan amsar SHEIKH BN BAAZ yabayar yayinda akayi masa irin tambayarnan gawanda yazo yatarar ana hada sallar magrib da isha'i don ruwan sama kuma dayazon an idarda Magrib ana kan isha'i kuma yakara dacewa= inma raka'a daya na isha'in ya subuce musa sai yssami 3 sai yayi sallama tareda imam su amatsayin isha'i shi kuma amatsayin Magrib, inma yasami isha'in kasada raka'o'i 3 shi kuma da niyyar biyan magrib yabisu in sunyi sallama sai yakawo cikotonda zai cikeshi raka'a 3 na magrib nasa, BN BAAZ yace= wannan shine mafi ingancin maganganu biyu na Malamai, dubi👉🏼
(مجموع فتاوى ومقالات الشيخ ابن باز ١٢/٢٩٥)
ALLAHU A'ALAM. 

*via : Sheikh Abubakar BN Mustafa Biu*
  23/Al-muharram/1441
    23/September/2018

*Daga ZAUREN ISLAMIC SUNNAH*

08035408319

Share:

IDAN KWANAKIN KAFFARA SUKA FAƊO A RANAR IDI

IDON KWANAKIN KAFFARAR KISA SUKA RATSO A RANAR IDI, MENE NE HUKUNCI?


Tambaya:

Assalamu Alaikum. Allah ya karama rayuwa albarka. Malam don Allah a taimakamin da amsar tambayarnan.
Mutumin da yake azumin kaffarar mutuwa ya zaiyi da ranar sallah. Shin zai aje azumin na ranar ne koko zai wuce kawai da azumin shi. Allah ya bada ikon amsawa.

*Amsa:*

Wa alaikum assalam, Amin Allah ya amsa adduarka.
Malamai sun yi sabani game da azumin kaffara idan ya ratso ranar idi zuwa maganganu guda biyu :
1. Ba za'a tsaya ba saboda ranar idi za'a cigaba da azumin saboda aya ta (92) a suratun Nisa'i ta shardanta yin azumin kaffarar Kisa a jere, dakatawa saboda idi kuma zai Kore wannan sharadin, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai.
2. Ya wajaba ya sha azumi a ranar idi, saboda yin AZUMI haramun ne a wannan ranar kamar yadda hadisin Umar dan khaddabi ya tabbatar, wannan yasa ba shi da laifi idan ya sha tun da Sharia ta yi masa izni.
Zance mafi inganci shi ne na Biyu, saboda idan hani da umarni suka ci karo da juna ana gabatar da hani, saboda haka mai kaffarar Kisa zai sha saboda Idi ko tafiya ko haila.Allah ne mafi sani.
Don neman Karin bayani duba: Al-Muntaka min Fataawa Alfauzaan 1/152


*Dr. Jamilu Zarewa*
31/08/2017.

Kukasance Damu a shafin mu na Facebook ta wannan link dake kasa👇🏿👇🏿👇🏿
http://www.facebook.com/Islamicsunnah . Ga masu Sha'awar shiga group din ISLAMIC SUNNAH a whatsapp saisu aiko da suna da state ta wannan number +2348060618481

Share:

INA FAMA DA ƘARANCIN NI'IMA DA BUSHEWA

*INA FAMA DA QARANCIN NI'IMA DA BUSHEWA???!*
:
Daga zauren
Kulafa'ur rashidun
:
Assalamu alaikum matsalata itace karancin ni'ima ina yawan bushewa wanda dachan bahaka nakekeba ataimakeni da yanda zansamu mafita?
:
              ******
:
Walaikumussalam.... 

Kisamu aya danye, dabino, ganyen zogale danye, kwa-kwa, kankana, nonon rakumi da mazarkwaila .

Ki hada su duka banda mazarkwaila da nonon rakumi sekiyi blending nasu ki tace seki zuba nonon rakumi da mazarkwaila aciki ki gauraya shi seki sha. Insha ALLAH zakiyi mamakin sauyi cikin qanqanin lokaci
.
ALLAH yasa mu dace
.
➡ Jamila Dahiru Muhammad 
_(Muhsinat Datti)_
========================
*```Date* ```[8-09-1439]Hj {24-05-2018} 
  Kuna iya samun mu ta Internet/website http://khulafau.cf
_Masu buqatan Group suyima daya daga cikin Number's innan maga ta whatsApp_
+2349033206238
+2347035269582
+2348063796175
           *```Kuna iya samun mu ta facebook*```
facebook.com/khulafaurrashidun
((سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أشْهَدُ أنْ لَا إِلَهَ إِلاَّ أنْتَ، أسْتَغْفِرُكَ وأَتُوبُ إِلَيْكَ))
〰〰〰〰〰〰〰〰✔
*Wanda yaga gyara, yasanar damu !*

Share:

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...