Skip to main content

Posts

Showing posts with the label Tambaya Mabudin Ilimi

TAMBAYA TA 74

*AZUMI GOMA A FARKON ZUL-HIJJA ?*
*Tambaya:*
Assalam alaikum Dan Allah mlm menene ingancin azumi Guda goma da ake awatan zulhijja?
*Amsa:*
Wa alaikum assalam, Hadisi ya tabbata a Sunan Annasa'i: Annabi (s.a.w) ya kasan ce yana azumtar kwanaki Tara na farkon Zul-hijja.                               Ba'a azumtar rana ta goma saboda ita ce ranar sallah, Annabi (s.a.w) ya haramta azumtar ranar sallah a hadisin da babban sahabi Umar ya rawaito.                              Allah ne mafi sani
*Amsawa*✍🏻
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA* 3/8/2016.
Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

TAMBAYA TA 84

📒📗 *TAMBAYA 44* 📗📒
https://darulfikr.com/ra/1042 Don Allah inda macce zatabi mijinta Sallah agida yaya zatayi kabbara Kuma don Allah inason aturomin Attahiyatu complete
*AMSA* Wa alaikumussalaam wa Rahmatullahi wa Barakaatuh. Idan Mace za tayi jam'i da mijin ta ana so ta tsaya a bayan shi be, wannan shine sunnah kuma koyarwan Annabi(SAW), kamar yadda hadisai suka yi nuni akan hakan. Daga cikin su akwai hadisin Anas Bin Malik Allah Ya kara mishi yadda, wanda ya zo cikin Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim da Sunan da Muwadda'u, da sauran su, Anas Allah Ya kara mishi yadda yake cewa kakan shi Mulaikatu ta kira Manzon Allah(SAW) saboda abincin da tayi mishi ya zo gunta ya ci. Bayan ya zo ya ci sannan ya ce ku tashi in yi muku sallah sai Anas ya ce sai na tsaya a kan wata tabarma(shinfida) wadda tayi baki saboda lokaci mai tsawo da aka dauka ana anfani da ita sai na yayyafamata ruwa sai Manzon Allah(SAW) ya shiga gaba ya bamu sallah sai na tsaya ni da wani yaro a bayan Manzon Al…

TAMBAYA TA 82

WANDA YAKE GIDA, ZAI IYA HADA SALLOLI SABODA RUWAN SAMA ? 
Tambaya: Assalamu alaikum. Allah karawa malam ilimi da fahimta. Shin da Allah malam ko mutum zai iya hada sallah shi kadai idan ana ruwa bashi da ikon zuwa masallaci?. Nagode malam.
Amsa:  To dan'uwa malamai sun yi sabani akan wannan mas'alar zuwa maganganu guda biyu : I. Ya halatta ga wanda yake a gida ya hada salloli saboda ruwan sama, tun da ruhusa ce Allah ya bawa mutane, don haka ta shafi kowa da kowa, wannan ita ce maganar Hanabila kamar yadda Mardawy ya ambata a INSAAF 2\340. 2. Bai halatta ga wanda bai je sallar jam'i ba ya hada salloli saboda ruwan sama, saboda an yi sauki ne ga wadanda za su je masallaci don kar su jika jikinsu da ruwa, wannan wahalar kuma babu ita ga wanda ya yi sallah a gida, don haka rahusar ba za ta same shi ba, sannan kuma shari'a ta yi nufin ta kiyaye sallar jam'i shi ya sa ta saukaka wajan hada salloli a ruwan sama,don kar mutane su watse sallar jam'i ta tozarta, wannan ita…

TAMBAYA TA 81

```Assalamu AlaikumMalam tambaya ta itace alokacin da nake haila zan iya kwanciya da alwala. Bissalam```

_*AMSA:*_ *******
ﻭﻋﻠﻴﻜﻢ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ. ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،

Mai haila bazatayi alwala a lokacin da take cikin jinin al'ada ba, kuma koda tayi alwala din, toh alwalar bata inganta ba, saboda jini bai yanke ba, koda ace zatayi wanka a lokacin da jinin bai yanke ba, toh wankan baiyi ba, dole sai jini ya tsaya.
*Al-Hafiz Ibn Hajar* ya kawo zancen *Ibn Daqeeq Al-eid (rahimahullah)* Wanda yace: *Imam Shafi'i* yace yin alwala kafin shiga barci bana matan da suke cikin haila bane, saboda da za'a ce tayi wanka lokacin da jinin bai dauke ba, yin wankan baya tsarkake ta daga jinin dake zuwa, Wanda kuma ba kamar mutumin da ke cikin janaba bane. 
Amma idan jini ya dauke mata kafin tayi wanka saita bukaci yin barci, toh anan ya halasta tayi alwala. _*(Fathul Baari, 1/395)*_
*Imam Nawawi* shima yayi zance makamancin wannan ac…

TAMBAYA TA 80

*The difference between maniy, madhiy and moisture*
Question :  I do not know when that which comes out of a woman is maniy which requires ghusl or it is regular discharge which requires wudoo’. I have tried to find out more than once, but no one gave me a precise answer. Now I am dealing with all discharges as if they are regular and do not require ghusl, and I only do ghusl after intercourse.  I hope that you can explain the difference between them.
Answer
Praise be to Allaah.
What comes out of a woman may be maniy, madhiy or regular discharge, which is called “moisture”. Each of these has its own characteristics and rulings that apply to it. 
1 – *With regard to maniy:* 
1.It is thin and yellow. This is the description that is narrated from the Prophet (peace and blessings of Allaah be upon him): “The water of the man is thick and white, and the water of the woman is thin and yellow.” Narrated by Muslim (311).
It may be white for some women. 
2.It smells like pollen, and the smell of pollen …

TAMBAYA TA 79

*ALAMOMIN KYAKYKYAWAN KARSHE !!*
*Tambaya:* Assalam Alaikum ! Dan Allah me ake nufi da kyakyawan qarshe, akwai wasu sifofin da siga na mutuwa da yake nuna cewa in sha Allah mutum yayi kyakyawan Qarshe??
Amsa Wa alaikum assalam,  Akwai alamomin da yawa da suke nuna kyakykyawan karshe daga ciki akwai:
*1*.Cikawa da Kalmar Shahada, saboda fadin Annabi (SAW) "Duk Wanda maganarsa ta karshe ta zama La'ilaha illallahu zai Shiga aljanna".
*2*.Mutum ya mutu yana aikin alheri kamar sallah Hajji, saboda fadin Annabi SAW " Ana tashin bawa akan abin da ya mutu yana yi".
*3*. Idan mutum ya rasu Daren juma'a ko yininta saboda fadin Annabi SAW "Duk Wanda ya rasu Daren juma'a ko yininta Allah zai kare shi daga azabar Kabari"
*4*. Idan mutum ya yi shahada kamar mace ta mutu wajan haihuwa ko ciwon ciki ko nutsewa a ruwa ko ya mutu a ciwon Kwalara ko kare kansa ko dukiyarsa DSS
*5*.Idan mutum ya rasu yana gumin goshi kamar yadda ya tabbata a hadisin Tirmizi .
Allah ne mafi …

TAMBAYA TA 78

*Tambaya:*

Assalamou alaykum wrhmtllh  Malam brk d wrhk  Ya aiki? Malam macece mijinta yake neman aure ,ama kuma yanata zuwa yana batata a wurin budurwar tasa.tasha ji da kunnenta yana hada mata karya akan abinda batayiba.Malam zata iya rokon Allah akan zalincin karyar da ake mata akan Allah ya lalata lamarin auren nasu? Jxkllh khair .
*Amsa:*

Wa'alaikumussalamu Warahmatullah. 
Allαн(ﷻ) Yana cewa:
*”يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اسْتَعِينُوا بِالصَّبْرِ وَالصَّلَاةِ ۚ إِنَّ اللَّهَ مَعَ الصَّابِرِينَ.“*
Ma'ana: *“Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nemi taimako da haƙuri da salla. Lalle ne, Allah na tãre da mãsu haƙuri.”* [Al-Qur'an 2:153]
'Yar uwata mai daraja! Ina yi maki wasici da ki ji tsoron Allah, kada ki biye wa wasi-wasin shaiďan da 'yan maganganu da za su yi ta kai kawo daga bakin mutane a lokacin da mijinki zai qara aure. 
Wasu za su zo maki da labarin da bai faru ba su faďi maki kawai don su ga sun kore zaman lafiya tsakaninki da mijinki, ki tada hankalinki ki dinga san…