Showing posts with label Tarihi (History). Show all posts
Showing posts with label Tarihi (History). Show all posts

HIKAYAR ATTAJIRI DA MACIJIYA DA KUMA ABU-IRSI


LABARIN ATTAJIRI DA MACIJIYA DA KUMA ABU-IRSI

(Qissa ce ta tarbiyya domin yara Qanana)

Wata rana wasu ayarin ‘yan kasuwa suka fita domin fatauci zuwa birnin Basrah kudancin Iraqi, can suna cikin tafiya a kan hanyarsu sai suka zo wani dausayi mai koramu da ciyayi masu duhu da kuma wurin wanka da hutawa, to daman iskar da ake yi a wannan lokaci zafi gareta, samun wannan wuri ke da wuya sai wadannan ‘yan kasuwa suka sauka domin su huta su biya wasu bukatun nasu kadan.

Sai daya daga cikinsu ya nufi wurin wata duhuwa ta ganyen da ke fitowa gefen karama inda suke sarke da juna suka hadu suka bada wani yanayi na tanti (dan karamin dakin tafi-da-gidanka), nan take ya shige ciki ya boyewa zafin rana, to saboda sanyin ciki sai ya fara jin gyangyadi yana kama shi, sai kawai ya mike kafa ya kama bacci! Su kuwa abokan tafiyarsa basu san abokinsu yana cikin rumfar ganyayyaki ba yana bacci, ko da suka gama abinda suke sai suka tashi suka daura kaya suka hau rakumansu suka yi gaba zuwa birnin Basrah.

Bayan wasu awanni sai wannan dan kasuwa ya farka daga baccinsa, a tsammanisa wannan ayari suna nan a wurin da suka sauka suna hutawa, sai ya yunqura da nufin ya fita daga cikin wannan tanti na ganye, ai kwatsam sai ga macijiya ta fasa kai a bakin raminta, tun da yake bai taba ganin macijiya mai girmanta ba!

Ko da wannan mutum ya ga macijiyar nan ba zato ba tsammani sai ya ji tsoron tsallakawa ta inda ta tsare masa hanyar fita gashi kuma yanayin sarkakiyar bishiyoyin ba zai yiwu ba ya fita ta wani wuri in banda ta inda ya shiga, ya kama ambaton Allah tare da rokonsa gami da yin tawassuli da soyayyar Annabi (SAW).

Ai yana cikin wannan hali sai kawai ya ga wata dabba mai kama da dila saidai bata kai girman dila ba ana kiranta (Ibnu Irsi), kowa ya san wannan dabba kuwa tana cikin manyan abokan gabar macizai, ai ko da (Ibnu Irsi) ya ga macijiya sai ya tsaya yana kallonta yana nazarin yadda zai yi mata ya kama ta, jim kadan sai ya juya ya koma inda ya fito.

Bacewarsa ke da wuya sai gashi ya dawo tare da dan'uwansa (suka zama biyu) daya ya tsaya daga bangaren dama na kofar tanti, daya kuma ya koma daga bangaren hagu, don haka sai suka kasance daya a wajen kan macijiya dayan kuma a wajen jelarsa, ita kuma macijiyar nan duk bata kula da su ba, (ita dai hankalinta yana kan mutumin nan), duk wannan abu da ake yi mutumin nan yana kallon abin mamaki tare da firgici da idanuwansa!

Lokaci daya suka yi mata dirar mikiya a tare, sai ga kan macijiya a bakin (Ibnu Irsi) jelarta kuma a bakin dayan! Macijiya ta yi yunkurin da duk za ta iya amma bata samu damar guduwa ba, daga nan suka ja ta nesa inda babu wanda zai zo wucewa ya gansu, ko da ganin haka sai wannan tajiri ya fito daga tantin da yake, ya na godiya ga Allah da ya kwace shi daga wannan musibah.

📍📍📍
*WASU DAGA FA’IDOJIN WANNAN QISSA GA YARA:*
▪1. Lalle addu’a makamin mumini ce
▪2. Muhimmancin addu’a a yayin da ka sauka a sabon wuri irin wadda shari'ar Musulunci ta karantar. (a duba littafin Hisnul Muslim) sai a koyawa yara.
▪3. A tare da kowane tsanani akwai sauki.
▪4. Bibiyar halin da dan’uwanka ya ke ciki yana da matukar muhimmanci, domin hakan zai taimaka har ka san irin halin da yake ciki. 

Fassara:
M. Jamilu Nakumbo
16/2/2018

https://t.me/Fisabilillaaah
Share:

TARIHIN RAYUWAR JARUMA LARA DUTTA

TARIHIN RAYUWAR JARUMA # LARA_DUTTA
kamar kowacce larabar tsakiyar mako da muka saba kawo maku shirin mu ,da yake bayani akan jaruman film na bollywood wadanda suka fara harkar film daga 1990s zuwa wannan lokaci ko kuma wadanda tauraruwar su ta haska a wannan zango ,yauma cikin ikon ALLAH mun zo maku dauke da tarihin rayuwar jaruma LARA DUTTA.
An haifi jaruma LARA DUTTA ranar 16/04/1978 takasance jarumar fina finan india wacce take fitowa a bangaren bollywood ,sannan takasance mai sanaar tallata kayan kawa wato (modelling) a turance,kuma jarumar tazamo er india ta biyu data sami nasarar lashe kyautar kyau ta MISS UNIVERSE wacce akayi a qasar CYPRUS shekarar 2000.
tafara fitowa a filmdin ANDAAZ 2003 tareda da jaruma priyanka chopra da kuma AKSHAY KUMAR filmdin yasamu karbuwa sosai a wajen masu kallo (audience) gami da samun yabo daga bakin masu sharhi (critics),sannan da filmdin tasami nasarar lashe kyautar FILMFARE AWARD Ta sabuwar jaruma mafi nuna hazaqa a shekara wato (filmfare award for best female debut),dukda filmdin ANDAAZ shine filmdin ta na farko da yafita amma bashine na farko ba wajen fara aikin jarumar ,A 2002 jarumar tafara amsar (signed ) aikin filmdin ARASATCHI wanda aka shirya da yaren TAMIL ,sai dai filmdin yasami tsaiko wanda baisami fita ba sai a shekarar 2004.
jarumar ta taka rawar fitowa a matsayin KAJAL cikin filmdin ANDAAZ wanda dubban mutane suka yaba da qoqarinta na iya aikin jarumar dukda kuwa shine filmdin ta na farko,abu mafi jan hankali kuwa shine yanayin yadda voice dinta ke fita a filmdin.
Daga nan ba sake ganin jarumar ba a screen sai a waqar AISA JADOO ta filmdin KHAKEE 2004 wnda shine karon farko da jarimar tayi fitowa ta musamman (comeo appearance) a rayuwarta cikin films ,bayan nan ashekarar tafito a fina finai kamar BARDHASHT da kuma AAN MEN AT WORK wadanda duk sunyi faduwar baqar tasa a kasuwancinsu (flop),sannan kuma fina finai kamar INSAN ,elaan gami da JURM basu amsu sosai ba a kasuwancinsu (average) filmdin MASTI shine filmdin jarumar da yafi amsuwa a shekarar.
A wata interview da akayi da jarumar anyi mata tambaya meyasa bata fito cikin filmdin GRAND MASTI ba,wanda shine cigaban filmdin MASTI ta bayyana cewa "nasami offer tayin aikin filmdin amma na bar aikin ne saboda ciwon da yake damun mahaifiyata (illness) a lokacin "
kafin jarumar tafara yin filmdin ANDAAZ sai da tafara fitowa videon waqa da mawaqi ABHIJEET BHATTACHARYA yasaki mesuna TU CHALU HAI RE.
shekarar 2005 zuwa 2010 nan ne lokacin da tauraruwar jarumar tafi haskawa wadda tafito a manyan fina finai kamar kaal,NO ENTRY wanda tafito tare da jarumi salman khan,anil kapoor FARDEEN KHAN,celina jaitly,da kuma ESHA DEOL ,sannan tafito a filmdin DOSTI FREIND FOREVER tareda jarumi BOBBY DEOL ,filmdin bai samu karbuwa sosai ba INDIA amma yazamo fbiggest grosser
TALK SHOW
jarimar ta bayyana cikin wasu SHOW da aka gabatar kamar RANDEZVOUR wanda jaruma SAMI GAREWAL ta gabatar da kuma KOFFE na KARAN JOHAR wanda tagabatar da season one katrina kaif tayi season two,SHOW dinta na qarshe yafito ne a 2010wanda suka tare da mijinta .
EARLY LIFE
An haifeta ranar 16/04/1978 bana tana da shekaru 41 aduniya ,a garin GHAZIABAD dake jihar UTTER PRADESH ,mahaifinta mesuna L K DUTTA yakasance yaren PUNJAB kuma tsohon WING COMMANDO ,sunan mahaifiyata JENNIFER DUTTA,sannan tana da en uwa mata biyu SABRINA da cheryl dutta .
A 1981 suka bar garinsu suka koma BANGLORE anan ne jarumar tafara karatu,ta kammala karatun degree dinta na farko a UNIVERSITY OF MUMBAI wacce takaranci ENGLISH/HINDI.
bayan wadannnan yarukan jarumar tanajin yaren PUNJAB da KANNADA
PAGEANTRY
kyautukan kyawu da jarumar ta lashe a ciki da wajen qasar INDIA .
GLADRAGS MEGAMODEL INDIA 1995 winner .
MISS INTERCONTINENTAL 1997 winner .
FEMINA MISS INDIA 2000 winner
MISS UNIVERSE 2000 winner
PERSONAL LIFE
sunyi soyayya tareda wani abokin yarintarta mesuna KELLY DORJI daga baya kuma suka kama soyayya da wani baturen AMERICAN me buga kwallon BASEBALL ,mesuna DEREK JEFER.
daga karshe a sept 2010 sukayi engaged da wani dan kwallon TENNIS a INDIA mesuna MAHESH BUPHATHI wanda kuma sunyi aure a 16/02/2011,a garin GOA.
ranar daya ga watan august 2011 ta sanar cewa ta sami juna biyu ,wanda ranar 20/01/2012 ta haifi yarinya mesuna SAIRA BUPHATHI
JERIN FINA FINAN JARUMA #LARA_DUTTA
2003 ANDAAZ
mumbai se aaya mera dost
2004 KHAKEE C/A
MASTI
bardhasht
arasatchi TAMIL FILM
AAN men at work
2005 INSAN
ELAN
JURM
KAAL
NO ENTRY
2086 DOSTI freind forever
ZINDA
ALAQ c/a
bhagam bhag
FANAA C/A
2007 jhoom barabar jhoom
PARTNER
OM SHANTI OM C/A
JUMBO
2008 RABNE BANADI JODI C/A
2009 BILLU
do knot disturb
BLUE
2010 HOUSEFUL
2011 CHALU DILLI
DON.2
2013 DAVID
DAVID TAMIL FILM
2015 singh is bling
2016 FITOOR
AZHAR
2018 WELCOME TO NEW YORK
2019 BEECHAM HOUSE

Share:

MANYAN ANNOBAR DA SU KA FARU A TARIHIN MUSULUNCI


MANYAN ANNOBAN DA SUKA FARU A TARIHIN MUSULUNCI. 

Abul Hassan Al-Mada'ini Allah ya masa rahama yake cewa "Manya Manyan Annoba da akayi atarihin musulunci guda biyar ne:-

1. ANNOBAR SHEERAWAIHI; Wanda akayita azamanin manzon Allah shekara ta shida bayan hijira. 
2. ANNOBAR AMAWAAS; Wanda ta faru azamanin sayyidin umar shekara ta sha takwas bayan hijira, Wanda ta kasance akasar shaam, mutum dubu ashirin da biyar (25000) suka mutu adalilinta, acikinta sahabi Abu ubaidata bin jarrah da sahabi mu'azu bin jabal da matansu suka rasa rayukansu. 
3. ANNOBAR JAARIF; Wanda ta faru azamin Ibnuz Zubair shekara ta sittin da tara awatan shawwal, Wanda ta halaka mutane acikin kwana uku, akowane wuni mutum dubu saba'in (70,000) ke mutuwa, awannan lokacin ne yaran sahabi Anas bin Malik guda 83 ko 73 suka mutu, Abdurrahman bin Abi bakrata kuma yaransa 40 suka mutu duka adalilin wannan Annobar. 
4. ANNOBAR FATAYAAT; wannan itace ake kira Annobar yan mata, saboda daga su ta faro, wannan annobar ta faru ashekara ta tamanin da bakwai bayan hijira, azamin Khalifa Abdulmalik bin marwan. 
5. ANNOBAR MUSLIM BIN QUTAIBA; wacce ta faru ashekara ta dari da talatin da daya bayan hijira acikin watan rajab, sannan ta tsananta acikin Ramadan har sai da takai ana irga janaza akowace rana ta mutane dubu (1000), amma kuma sai tayi sauki acikin shawwal, acikin wannan annobane mugeera bin shu'uba ya rasu.
 
شرح صحيح مسلم للنووي ١/١٠٦

NOTE
Akwai wasu annoba da suka faru atarihin musulunci bayan wadannan guda biyar din, kamarsu Annobar guraab, da makamantansu, amma wadannan guda biyar din sune manya kuma wadanda suka jikkata musulmai kamar yadda shi Al-Mada'ini ya fada. 

Ya Allah kar kasa tarihi ya maimaita kansa. Ya Allah ka tausaya mana badan halinmu ba. 

#Annoba
 #Zaurenfisabilillah

https://t.me/Fisabilillaaah
Share:

TASOWAR IBN TAIMIYYAH DA ILIMINSA

*Tasowar Ibnu Taimiyyah da Iliminsa*

 Ibnu Taimiyyah ya tashi a gidan ilimi kamar yadda muka gani. Ya kammala hardar Alqur’ani a cikin quruciya. Sannan ya kula da sanin ilimoman Fiqihu da Hadisi da Tafsiri da Arabiyyah. Ya soma karantarwa da fatawa da rubuta littafai da tattaunawa da malamai Munazara tun bai wuce shekaru ashirin ba. Koda ya cika shekaru talatin an fara yi masa laqabin Mujtahidi kuma “Mai raya Sunnah”. Yana da matuqar wuya a iya sifaita baiwar da Allah ya yi wa Ibnu Taimiyyah ta fuskar ilimi. Masu ba da labarinsa na ganin kasawarsu wajen bayyana irin hikimomin da ke tattare da shi ta wannan haujin. An lisafta malaman da ya gurfana a gabansu don daukar karatu aka tarar sun zarce malamai dari biyu. Akwai kuma littafan da ya karanta su sau da yawa a wurare daban-daban kamar Musnad na Imamu Ahmad. Game da nasa littafai shi kuma, Ibnu Taimiyyah ya wallafa sama da littafai hamsin a fannona daban-daban na addini, banda qananan wallafe-wallafensa da aka tara cikin Majmu’ul Fatawa mai sifili talatin da bakwai. Ya ishi mai karatu misali abin al’ajabi cewa, duk da yake Ibnu Taimiyyah bai wallafa Tafsirin Alqur’ani ba, amma malamai daga bisani sun wallafa shi daga cikin littafansa. Ma’ana an tattara wuraren da ya yi sharhi akan ayoyin Alqur’ani daga cikin littafansa a tsakankanin maganganunsa da kafa hujjojinsa, sai ga shi an samu kusan kammalallen Tafsiri mai Mujalladi hudu. Mujaddadi Ibnu Taimiyyah Muna iya cewa, Allah gwanin sarki ya tashi Ibnu Taimiyyah ne a wani lokaci da buqatar irinsa ta yawaita. Don kuwa a wancan lokaci al’umma tana fama da matsaloli da rikitta da tashin hankula na ciki da na waje. Daga cikin gida musulmi na fama da rabuwar kai, da yawaitar qungiyoyi da yaduwar bidi’ah da raunin ilimin furu’a. Ga kuma lalacin da ya yadu a cikin jama’a da zaluncin sarakuna da kwadayin malamai. Tsibbace-tsibbace da bokanci da duba sun zama gama-gari a cikin al’umma. Daga waje kuma ‘yan mishan sun kai ma musulmi farmaki, ‘yan Shi’ah masu kiran kansu Fadimawa sun hada kai da su. Sannan ga Tattar sun shelanta mummunan fada da musulunci da musulmi a duk in da suke a wancan lokaci. Shaihun musulunci ya fuskanci duka wadannan matsaloli da nufin magance su. Ya kuma samu taimakon Allah matuqa a wajen cimma wannan gurin nasa. Ga shi kuma Allah ya ba shi makamai da ya wuyata a samu wanda ya yi tarayya da shi a dukansu. Mutum ne da aka sifaita shi da kaifin basira da qarfin qwaqwalwa, har wasu ma na ganin bai tava sanin abu ya manta da shi ba. Yana da qarfin tuna ayoyin Alqur’ani da nassosan hadissai da maganganun malamai na kowane fanni. Don haka ya kasance mai kaifin hujja wadda take yanke wuyan abokin gaba nan take. Ga shi kuma jarumi da ba ya tsoron ko-ta-kwana. Don haka ba ya da ja da baya ga abin da ya sa gaba. Sannan yana da kwarjini a idon jama’a da kyawawan dabi’u da suka dada soyar da shi ga mutane. Ga shi mutum mai kishin gaskiya da qoqarin yada ta. Hada da halinsa na gudun duniya da rashin kula da jin dadinta. Irin wannan malami Allah ya dora shi a kan kyakkyawar hanya irin ta Annabawa wane irin canji kake tsammanin al’umma ba za ta ci moriyarsa ba ta hanyarsa? Dan Taimiyyah nan take ya rurrusa aqidun da suka zame ma musulunci tsutsar goro ta hanyar rubuce-rubucensa da wa’azozansa da karantarwarsa. Ya kece raini a wajen wargaza aqidun Yahudawa da na ‘Yan mishan. Ya yi faxa da qungiyoyi mabiyan son zuciya irin mulhidai da zindiqai da ‘yan Shi’ah da waxanda suka wuce wuri a Sufanci. Ya yi kira ga koma ma littafin Allah da Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba tare da ta’assubanci ga wani mutum ko qungiya ko mazhaba ba. Sa’annan ya kira sarakuna da talakawa zuwa ga yaqar kafirai waxanda suka keta hurumin musulmi, musamman dai Tattar. Ya kuma fita ya yi yaqi a matsayin xaya daga cikin sojoji. Tare da haka kuma Ibnu Taimiyyah ya kafa wata makaranta da Allah ya yawaita almajiranta tun daga wancan zamani har zuwa yau, kuma tana ci gaba da bunqasa har a naxe qasa. Wannan makaranta tasa tana mutunta magabatan Sahabbai da Tabi’ai da waxanda suka biyo bayansu, da shugabannin mazhabobi, tana kuma la’akari da ra’ayoyansu da fatawoyinsu baki daya. Tana kuma rinjayar da nassi ingantacce idan ya zo daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a kan maganar kowa kome darajarsa. Wannan makaranta dai tana da daruruwan littafai da dubaiban malamai a cikinta. Dukkaninsu suna jingina kansu ga Sunnah da biyar magabata ba ga shi Ibnu Taimiyyah din ba.

Share:

MADHUBALA: THE TIMELESS BEAUTY AND TRAGEDY 3

MADHUBALA THE TIMELESS BEAUTY AND TRAGEDY (KASHI NA UKU) 

Zuwan film din Dilip kumar na farko wato JWAR BAHTA shine silar haduwar su. A sets na film din jinin su ya hadu, suka saba sosai. A hankali haduwar jini ya koma soyayya,. Abubuwa suka fara daukar salo mai ban sha'awa kai kace sun kusa aure.....ZUWAN NAYA DAUR ya zama sanadiyyar rabuwar su. Sun fito tare a film din NAYA DAUR, amma a yarjejeniyar contract na Madhubala, dole zata dinga fita outdoor shooting, A lokacin mulkin mallaka da mahaifin ta ya saba yi mata ya kuma tashi, yaki yarda da Hakan, Jarumi Dilip kumar ya so yabi raayin masoyiyar sa. Hakan yasa producer na film din B R Chopra ya kai maganar kotu, domin a tilasta musu su yarda da abinda suka rattaba hannu akai game da film din. Kotu ta tilastawa Dilip kumar ya girmama yarjejeniya, hakan yasa tilas ya goyi bayan Producer. Wannan ya janyo sabanin raayi tsakanin Dilip kumar da Madhubala... ITA TABI UMARNIN MAHAIFIN TA, SHI KUMA YABI UMARNIN KOTU... Daga nan Madhubala ta fita daga Film din, Aka musanya ta da jaruma Vyjayanthimala. A gefe guda tuni dama akwai wani sabanin raayi tsakanin Dilip da baban ta, a matsayin ta na wacce family din gaba daya suka dogara a kan ta, kuma Dilip kumar ya sanya sharadin cewa zata daina film bayan sun yi aure, a ganin mahaifin idan ta daina film ta wacce hanya zasu samu abin rufawa kansu asiri? Wani source din ma ya tabbatar da cewa, ATTAULLAH KHAN zai yi amfani da auren su ne wajan cimma wasu bukatun a fagen kasuwancin film kasancewar yana da kamfanin film da yake son rayawa. A ganin sa idan auren ya tabbata, zai iya amfani da su biyun wajan tada kamfanin sa ya zama shahararre. Se su koma karkashin sa, shi ya zama boss nasu. Abin da Dilip kumar ya ke ganin Sam ba zai dauka ba, musamman da yake yana kan number one star a Bollywood a lokacin. Duk wannan suka hadu suka kawo karshen soyayyar,

 Madhubala na yawan kuka a lokacin, saboda masifar son sa da take yi. Sukan yi magana ta telephone, ko za a samu mafita. Kamar yadda yar uwar ta Madhur ta bayyana

Dilip kumar kept saying, ‘Leave your father and I’ll marry you’. She’d say, ‘I’ll marry you but just come home, say sorry and hug him.’He refused, so Madhubala left him. That one ‘sorry’ could have changed her life. It was zid (stubborness and ego) which destroyed their love. My father never asked her to break the engagement or ever demanded an apology from him.

Matsalar ta zame mata biyu, tana fama da karayar zuciya wacce ta sha wahalar soyayya... A cikin wannan halin, tana shooting na wani film mai suna BAHUT DIN HUE cutar ta ta zuciya ta bayyana, ana kiran cutar da VENTRICULAR SEPTAL DEFECT. Cutar da ke bayyanar da huda a zuciyar dan Adam. Ta dinga Amai na jini. An kaita asibiti., likitoci suka bada shawarar ta huta a gado na tsawon wata uku. Se dai maimakon hutun, sae taci gaba da aikin films saboda a ganin ta, hutun wata uku zai sanya films din ta da aka fara shooting su shiga wani hali. A dalilin haka cutar ta cigaba da karuwa

 Issue na rashin lafiyar ta tun yana sirri a cikin family har abu ya fito fili har ta samu wasu failures a box office na dan lokaci, aka sa mata suna BOX OFFICE POISON
Role mafi girma da tayi a career nata A matsayin ANARKALI a film mai suna MUGHAL-E-AZAM ya fara ne a 1953... Bisa matsalar da take ciki reports sun nuna cewa DILIP KUMAR na daga cikin silar da yasa aka zabe ta ta fito a film din. Shooting na MUGHAL-E-AZAM ya dau kimanin shekara tara ana yi, tun bayan rabuwar masoyan, basu kara haduwa se a wajan shooting din. Se dai basa magana har sai inda scene ko dialogue ya hada su. Masana sun bayyana cewa shooting na MUGHAL-E-AZAM ya dan haska irin yanayin soyayyar su a rayuwar gaske. Saboda kamar yadda ANARKALI take kokarin bayyanawa a fili cewa bata son Salim duk da a zuciyar ta tana son sa, haka nan a gurin shooting ta dinga nuna kamar babu son sa a ranta, duk da a cikin zuciyar ta ba haka bane

Scene na karshe, inda matsanancin tsoro da dimuwa ya bayyana karara a fuskar ANARKALI musamman a kwayar idanun ta a yayin da ake ginin kasa a kewaye ta, domin rufe ta har ta mutu a haka.... Ya zama daidai da irin dimuwa da tsoro da take fama da shi a rayuwar gaske saboda tarfata da jikin ta ya fara yi sannu a hankali(wanda ya kalli Mughal-e-Azam zai fahimci me nake nufi) 
 Kafin late 50s, cutar ta tayi tsamari musamman saboda mawuyacin scenes da ta dinga yi a MUGHAL-E-AZAM. Director K Asif bashi masaniyar illar da dogon scenes na film din ya haddasa akan rashin lafiyar ta., tun daga doguwar tsayuwa da tayi a matsayin gunki wacce aka yiwa fenti har ya sa numfashi ke mata wahala, zuwa daurin ta aka dinga mata da ankwa na tsawon lokaci, har ma ta dinga jan wannan ankwar mai nauyi tana zagaye suna daure a jikin ta.... Kanwar ta Madhur ta bayyanawa Filmfare cewa

While shooting for Mughal-e-Azam she was tied with chains and had to walk around with them. That was stressful. By the end of the day her hands would turn blue. She’d even refuse food saying that she had to look anguished and weary for the jail scenes.”

Tayi soyayya ta karshe da kishore kumar, soyayyar da ta kai ga aure... Se dai bayan auren aka rasa inda soyayyar tayi.Ta samu kudi da daukaka, se dai tana bukatar wani a kusa da ita domin samun daidaito a kan al'amuran ta. Kishore kumar shi kuma yana bukatar tallafi na kudi sakamakon bashi da ya tara a kan sa na hukumar karbar haraji masu yawan gaske, har ta kai ga hukumar ta daga gidan sa domin sayarwa. Haduwar sae yaso ya bada ma'ana, se dai bai bayar ba,. A tunanin sa matarsa zata tallafa masa wajan settling na matsalolin kudi da yake fama da su a lokacin, se dai a gefe guda kuma bai san cewa cutar matarsa ta tsananta haka ba. A bisa Hakan ita ma kanta tana bukatar taimako.

 Ba dadewa da auren su ya kai ta London domin a duba lafiyar ta. Se dai bayan gwaje gwaje da bincike akan lafiyar ta, likitocin sun tabbatar da cewa Madhubala ba zata warke ba, kuma zata mutu bayan shekara biyu zuwa uku, kasancewar a lokacin ba a samu maganin warkar da huda ta zuciya ba.. sun yi wa yanayin mutuwar da zata yi hasashe da suna "SLOWLY AND PAINFUL DEATH"

Yar uwar Madhur tace

Due to her ailment, her body would produce extra blood, which would spill out from her nose and mouth. The doctor would come home and extract bottles of blood. She also suffered from pulmonary pressure of the lungs. She coughed all the time. Every four to five hours she had to be given oxygen or else would get breathless

: Wani zai yi tunanin cewa jin irin wannan rashin lafiyar a tare da matar sa zai ajiye komai nasa gefe guda ya tattara hankalin sa gun ta. Se dai sabanin Hakan ne.
 Kamar yadda kanwar ta 
Fada 

"Soon after that Kishore Bhaiyya left her at our home. He said that she was sick and needed care while he had to travel, work, sing and hence wouldn’t be able to give her time,"

Yayin da korafi ya fara karfi daga bangaren family na Madhubala don ganin halin ko in kula da yake nuna mata... kishore kumar ya maida cewa

 "‘I tried my best, I took her to London. But the doctors have said she won’t survive. What’s my fault?”
 Koda yake Madhur bata kalli kishore kumar a matsayin mutum mara kirki ko tausayi saboda barin yar uwar ta da yayi a gadon mutuwar ta ba, se dai a ganin ta tunda ya aure ta da masaniyar halin da take ciki, ya kamata ya kasance da ita har zuwa karshen ta. Ga abin da take fada game da haka

We’re not saying that he was wrong. Aapa was told by the doctors ‘you cannot have sex, you cannot have children’… But yet a woman needs emotional support no matter what. Aapa insisted that she wanted to be with him," "So he bought a flat at Quarter Deck, Carter Road where they stayed for a while. But she’d be alone most of the time. The sea breeze made her sicker. But she had tremendous willpower. She was supposed to live for two years. She went on to live for nine. She’d cry and say
 Mujhe zinda rehna hai, mujhe marna nahin hai, doctor kab ilaaj nikalenge?’ (I want to live; I don’t want to die.When will the doctors find a cure?)”Am sure I'll get operated someday

A kwanakin ta na karshe da jikin ta ya kara tsananta, mahaifin ta ya kira kishore kumar yazo yaga halin da take ciki amma yaki zuwa, saboda yana da event a Kolkata kuma yana tsoron cewa fasa tafiyar tasa zata sa organizers na event din su yi asarar kudi mai yawa. Mahaifin Madhubala cikin takaici yace "YOU'LL NEVER SEE HER AGAIN".......
Ta so ta dawo acting a shekara ta 1966 a inda ta so karasa film din ta CHALAK tare da Raj kapoor, wanda shooting kadan ya rage, amma Sam jikin ta ya kasa jurewa. Dole ta hakura da acting ta juya directing na film. A shekara ta 1969 ta fara directing film din farko mai suna FARZ AUR ISHQ,.. Se dai tun a pre production na film din Allah ya mata rasuwa wanda ya kama ranar 23 February 1969. A saboda haka ba a yi film din ba

Ta rasu kwanaki kadan da cikar ta shekaru talatin da shida(36 years). An binne gawarta a juhu Muslim cemetery dake garin Mumbai. A jikin kabarin ta, an yi alama da rubutu na wasu ayoyin Al qurani mai girma. Se dai a shekara ta 2010 aka share kaburburan su wanda ya hada harda na Muhammad Rafi, parveen babi, Naushad Ali, Talat Mahmud da sauran su...Shekara daya da rasuwar ta, aka maganin warakar cutar da ya zama ajalinta (ventricular septal defect) a inda patient din da aka yiwa theatre ya farfado cikin nasara.

ALHAMDULILLAH

ABDUL KING KHAN AKK

Share:

MADHUBALA: THE TIMELESS BEAUTY AND TRAGEDY 2

MADHUBALA THE TIMELESS BEAUTY AND TRAGEDY (KASHI NA BIYU)

A shekara ta 1942 a Bombay, wani dan kyakkyawan dogon saurayi mai suna ATTAULLAH KHAN wanda kamfanin sarrafa Tobacco dake garin Delhi suka kora daga aiki, ya fara amfani da mafi kyawu a cikin ya'yan sa yar shekara tara wajen samar musu mafita. Sunan yarinyar MUMTAZ JEHAN DEHLAVI wacce aka canzawa suna zuwa MADHUBALA.. An haifi wannan kyakkyawar jaruma a ranar sha hudu ga watan February 1933 wanda yayi daidai da ranar masoya wato VALENTINES DAY. Sunan mahaifiyar ta kuma Ayesha Begum Iyayen sun haifi yara guda goma sha daya, kuma Madhubala itace ta biyar.  

 Tun a yarintar ta, take ganin bakin ciki.Turnuke a cikin talauci, yan uwan ta maza guda biyu, da mata uku duk suka rasa ran su suna yara, babu wanda ya wuce shekara shida a cikin su duka biyar din. Studio mai suna BOMBAY TALKIES, wanda ya kasance mallakin Babbar tauraruwar jaruma DEVIKA RANI suka fara baiwa madhubala aiki a matsayin child artist tun tana yar karamar ta.A lokacin akan kira ta da BABY MUMTAZ. BASANTI shi ya kasance film din ta na farko. Daga nan tayi ayyuka da ɗan dama a matsayin child artist. SE DAI DUK DA HAKA..... TALAUCI YAKI BARIN GIDAN SU. A daidai wannan lokacin ne babbar jaruma ta lokacin wato DEVIKA RANI hankalin ta ya kai ga baiwa guda biyu da BABY MUMTAZ take dauke da su.... KYAU DA KWAKWALWA.. Wannan shine dalilin da ya sa ta shawarci yar BABY MUMTAZ da ta canza sunan ta zuwa MADHUBALA a matsayin sunan da zata yi amfani da shi a kan screen.. Wanda a turance yake nufin "honey belle" A Cewar DEVIKA RANI, duk sanda BABY MUMTAZ tayi murmushi, ta kan yi kama da flower mai rangaji.

Ba dadewa wani masanin ilimin taurari mai suna Kashmirwalle, yayi hasashe a kanta cewa wannan yar yarinyar zata samu daukaka, arziki da suna fiye da tunani.... irin wanda kaf dangin su babu wanda ya taba yin kwatankwacin su, amma zata hadu da bakin cikin rayuwa mai kunshe da rashin dace a soyayya, rashin soyayya a rayuwar aure.... Sannan baza ta Dade a duniya ba. Duk al'amuran nan se da suka kasance a kan ta.

Madhubala ta dawo Mumbai tare da family a inda ta zauna a irin gidajen dake kusa da ruwa. Ana nan kwatsam ranar sha hudu ga watan April 1944.. Madhubala da yan gidan su sun tafi kallon film a theatre aka samu explosion a nahiyar da suke .Gidaje da dama suka ƙone, ciki kuwa har da gidan su Madhubala. Aka yi asarar rayuka. Sanadiyyar haka suka kasance babu gida. Wata classmate dinta ce ta basu gurin zama a gidan su.. Bayan faruwar Hakan da kadan ne ta fara aiki a matsayin jaruma. An ganta a film din director kidar sharma mai suna Neel kamal wanda ta fito da babban jarumi Raj kapoor. A lokacin bata fi shekaru sha hudu ba.... Tun a wannan lokacin, murmushin ta kadai ya kan isar da sakonni da dama. Wa zai manta film dinta MAHAL, wanda ta fito tare da Ashok kumar? Haka nan babu wanda zai manta wakar Aayeega Aanewala. Koda yake jaruma suraiya ce first choice da aka so ta yi MAHAL., amma daga baya Kamal Amrohi ya bata dama....... DAGA NAN FA BATA KARA WAIWAYOWA Ba....... DULARI, BEQASOOR, TARANA, BADAL, acting din ta sun cancanci kallo daga maabota kallon films.( Ko da yake masana sun tabbatar da cewa tsananin kyawn ta ya sanya har ba a kula da talent din ta a fagen acting) .

Kyau, stardom, suka bayyana tare da Madhubala. Masoya suka fara kawo farmaki. Kai kace idan mace ta hada kyau da daukaka to se yadda ta ga damar sarrafa soyayyar ta. A bangaren Madhubala chakwakiya ce. : Maza wajen guda bakwai suka shigo rayuwar Madhubala suka fita suka barta a gadon mutuwar ta. Tun daga masoyin ta na yarinta wanda ta bawa kyautar jan rose flowers a Sanda zata koma Mumbai domin tabbatar da cigaba da wanzuwar soyayyar su, wannan flower ya ajiye har bayan mutuwar ta su ya kai ya ajiye a gefen kabarin ta. 
Director kidar sharma ya so ta a ganin farko, se dai bata so shi ba domin tana ganin ya mata tsufa. Director na film din MAHAL wato kamal Amrohi shi ya biyo baya, sun sha soyayya sosai, sukan yi awannni suna soyayyar su. A Cewar masana, wannan shine lokaci mafi farin ciki a rayuwar ta. Mahaifin ta ma yayi Na'am da soyayyar, a inda yake cewa

Aage chalke ein donho ki shaadi ho jaaye to mujhe koyi aitraaz nahin hai” (I have no objection if they marry each other in the near future.)

Rabuwar su yazo ne saboda Madhubala ta bukaci ya saki matarsa saboda bata so ta yi zaman kishi da wata. Matar kuwa ba wata bace illa jarumar Bollywood MEENA KUMARI. Kamal Amrohi yaki yarda da bukatar ta, yace se dai su zauna tare, Hakan ya jawo sanadiyyar rabuwar su
 Sun hadu da prem nnath a sets na badal bayan ta zama superstar. Alakar tasu bata fi wata shida ba.. Daga nan madhubala ta fara kaurace masa, a Cewar yar uwar ta Madhur, ta kaurace masa ne saboda ya nemi ta bar addinin ta zuwa nasa. Abin da Sam ba zai yiwu ba a gurin ta ba zai yiwu ba.

Apa [Madhubala] first fell in love with Premnath. The relationship lasted six months. It broke on grounds of religion. He asked her to convert and she refused.......... MU HADU A CI GABAN LABARIN

ABDUL KING KHAN AKK

Share:

MADHUBALA: THE TIMELESS BEAUTY AND TRAGEDY 1


" MADHUBALA THE TIMELESS BEAUTY" IDAN ANA MAGANAR KYAU DA TSARIN HALITTA A TARIHIN BOLLYWOOD DA KE AKE KWATANCE....
************************************************************************************************

MADHU, BEAUTY WITH TRAGEDY, ANARKALI OF INDIAN CINEMA, VENUS OF INDIAN CINEMA, THE TIMELESS BEAUTY, MORILYN MONROE OF INDIAN CINEMA duk suna daga cikin sunayen da ake mata lakabi 

... jarumar da industry bata taba ganin kyakkyawa mai cikar hallita kamar ta ba,Jarumar da ake kira BABY MUMTAZ, (lokacin yarinta), .Itace Jarumar da koda wanda suka saba ganin kyawawa ke santi a cikin kalaman su wajen bayyana ta.

A lokacin da shammi kapoor ya fara ido hudu da ita sai da ya dimauce da ganin kyan halittar wannan baiwar Allah. A inda yake cewa

"I was so nervous to work with her that I use to forget my dialogues. When I looked at her, I was lost and tongue-tied. She knew it too, she could see it and she helped me gradually. In no time, I was in love.. I said it then and still maintain i have never seen such beautiful woman, such perfection of face, form and skin. She was almost ethereal"

Masoyin ta Dilip kumar ya taba bayyanawa gidan jarida cewa

"She was extremely popular and I think the only star for whom people thronged outside the gates. Very often when shooting was over, there’d be a vast crowd standing at the gates just to have a look at Madhus beauty. It wasn’t so for anyone else. That was her personal effect on fans. Her personality was so vivacious,"

  Hasashe daga masana kyau da suka ganta a zahiri kuma suke raye har yanzu, sun tabbatar da cewa kaf hotunan ta dake zagayawa a yanar gizo, ko kusa basa nuna ainihin kyan da take da shi
 Madhubala ta taba fitowa a American magazine a 1952 wanda aka yi mata lakabi da "THE BIGGEST STAR IN THE WORLD".... AND SHE IS NOT IN BEVERLY HILLS. lokacin bata fi 19 years ba.

"She was aware of her beauty, a Cewar wani Filmfare editor kuma abokin mahaifin ta mai suna B K karanjia" ... Inda ya kara da cewa

"and because there were so many in love with her, she used to play one against the other. But it was out of innocence rather than shrewd calculation.”

Mace maabociyar saka farar Saari, mai yawan saka kayan adon gashi a kan gashin kanta. Maabociyar mu'amala da Gold da jewelry. Maabociyar raira poems irin na urdu. ta kan dauki yan uwan ta zuwa unguwa a motar ta hillman, Buick ko station wagon. Kullum sanye cikin Abaya, a wajan traffic idan yan sanda suka tsaida ta suka nemi ta bude lullubin ta, ta kan roke su cewa, pls ku barni a haka, in na bude mutane zasu yanyame ni. Rashin ganin ta sosai a baynar mutane ya sanya ta kara tsada, musamman idan wani dalili ya sa fuskar ta bayyana a wuri to se dai addu'a.

    Mahaifin ta baya barin ta zuwa Award function, ko premiere. Bata da kawaye ko abokai, amma bata taba korafi ba saboda tsabar biyayya ga mahaifin ta. Yar uwar ta Madhur take cewa...... ganin yadda mahaifin mu ya rikewa Madhubala wuta komai nata idon sa na kai, sai ake tambayar sa to me yasa ma ka yarda take yin film? Ya bada amsa cewa "yara na goma sha biyu, na rasa 'ya'ya na maza tun suna kanana, da sun rayu da su zasu tallafa mana. In na tsaya kallo, talauci sai ya kashe mu

    Director mai rike da kambun Academy Award, frank Capra da ya kai ziyara Bombay a wani interview da suke yi, kawai ya ganta a cover na magazine, a take yace "OH GOOD GOD!!! WHO IS THIS BEAUTIFUL GIRL, IS SHE AS BEAUTIFUL IN REAL LIFE? A nan fa ya sa a hada shi da mahaifin ta domin neman a bashi ita ya tafi da ita America ta dinga fitowa a manyan Hollywood films kuma a manyan roles, kuma da Hakan ya yiwu cikin sauki tunda tana da mai koya mata turanci... Se dai baban ta bashi da niyyar sakar mata mara daga rikon tsauri da yake mata... A inda ya maida martani cewa... She couldn't eat with forks and knives.

Shashi Kapoor ya taba kiranta “the sexiest woman I've ever seen” inda ya kara da cewa : “

"I recently saw Mughal-e-Azam and she once again succeeded in destroying me totally. It's a fatal attraction, its not just sexiness but that tremendous quality of projecting love." 

     Rayuwar Madhubala na dauke da wasu al'amura,.... Kyau, matsanancin riko daga mahaifi, cutar huda ta zuciya (ventricular septal defect), rashin dace a soyayya, auren da babu armashi, da Mutuwa a gado bayan jinyar na tsawon shekara tara.

    Mafi alhini a bangaren soyayyar ta shine wanda tayi da Dilip kumar, suna son juna, clash of interest da court case ya raba su, raunanniyar zuciyar ta mai dauke da huda, ya kara samun fami. A rayuwar ta, babu dark secret, babu kura a turnuke a cikin cupboard dinta, babu case na shaye shaye ko halin banza da ire iren su. Madhubalar ce kawai se halayyar ta ta kirki, biyayya, da yawan murmushi mai boye zuciyar da ta sha fama da jarrabawa kala kala har ta kai ga sanadiyyar ta.

    Da yawa se ake ganin wannan kyan, daukakar, suna, farin jini, sun zo ne tare da farashi mai matukar tsada wajan biya....... MU HADU A KASHI NA BIYU DAN GANIN KALUBALEN DA TA FUSKANTA A RAYUWA 

ABDUL KING KHAN AKK
Share:

BIKIN VALENTINE: RANAR MASOYA KO RANAR MAGUZAWA?


BIKIN VALENTINE: RANAR MASOYA KO RANAR MAGUZAWA?

BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allaah mai girma da ɗaukaka. Tsira da amincin Allaah su ƙara tabbata ga Manzon Allahu, Annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallam, mutanen gidansa, sahabbansa da ma dukkan wanda ya biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

GABATARWA

Bikin Ranar Masoya, watau Valentine's Day a turance kenan kamar yadda ake kiransa, biki ne da akan yi shagalinsa a kowace ranar 14 ga watan Afrilu, ma'ana dai sau ɗaya ake yinsa a cikin shekara.

Ita dai wannan rana, rana ce wacce miliyoyin mutane daga dukkan sassan duniya suke murnar zagayowarta a kowace shekara. Duk da cewa an ɗauki wannan rana a matsayin ranar murnar tunawa da wani waliyyin kiristoci ne mai suna Valentinus, irin wannan rana a yau ta kasance ana alaƙanta ta ne da bikin soyayya, nishaɗi da kuma jin daɗi a mafi yawancin wurare a duniya. 

A irin wannan rana, masoya a ko'ina a faɗin duniya kan aikawa juna saƙonnin katuka, fulawoyi, kyaututtuka ko wasu abubuwa makamantan haka domin dasawa ko haɓaka alaƙarsu da juna. A ƙarƙashin haka, akan haɗu a bukukuwa da dama da akan tanada domin irin wannan biki a tsakanin samari da 'yan mata ko ma'aurata domin nunawa juna ƙauna, in da hakan ke kaiwa zuwa ga munanan kalamai waɗanda su kuma su ke kaiwa zuwa ga mummunan aiki. Allaah ya tsare mana Imaninmu. 

GA JERIN WASU ABUBUWAN DA A KE YI A RANAR BIKIN VALENTINE. 

*. Sanya jajayen tufafi tare da bayyana tsiraici. 

*. Bayyanar da farinciki da jin daɗi a wannan rana, kamar yadda a ke yi a sauran bukukuwa.

*. Musayar jajayen fulawoyi waɗanda ke alamta soyayya. 

* . Rubuta kalmomin soyayya da amfani da lafuzzan da ke motsar da sha’awa ajikin katin. 

*. Aika da saƙonnin batsa da rashin kamun kai ta hanyar saƙo ko kuma ta hanyar wayar tafi da gidanka.

*. Musayar kyaututtukan da suka haɗa da fulawa da alawa da dai sauransu a tskananin ma’aurata ko samari da 'yan mata. 

*. Aikawa da katin gaisuwa (greeting cards). 

*. A wasu ƙasashen, akan shirya ƙasaitaccen biki inda mata da maza ke cakuɗewa da juna, a yi rawa, a yi shaye-shaye, ayi murna, wani lokaci kuma, a haɗa da masha’a.
 
Sai dai kafin mu tafi da nisa, bari mu ji taƙaitaccen tarihin shi wannan biki a farkon samuwarsa. 


TAƘAITACCEN TARIHIN BIKIN VALENTINE 

Daga ranar 13 ga watan Fabarairu har zuwa ranar 15 na wannan wata, maguzawan ƙasar Rum sun kasance suna yin wani bikin maguzanci da suke kira da Lupercalia. A yayin gudanar da wannan biki, mazajen cikinsu kan yanka akuya ko kare sannan su shafe jikunansu da jinin kuma su riƙa dukan matayen cikinsu da fatun dabbobin da suka yanka nan take ba tare da sun wanke jinin ba. A wannan biki, su kan sha kowane irin kayan maye su dinga yawo a cikin gari tsirara yayinda 'yan matan garin za su zo su jeru domin mazajen su zo su jibge su da fatun dabbobin da suka yanka. 

Dalilin wannan duka kuwa shi ne, matan wancan lokacin sun yarda cewa yi musu wannan duka maganin rashin haihuwa ne kasadin.

Bayan an gama wannan, sai kuma a rubuta sunayen duk 'yan matan garin a saka a cikin tulu ko kofin gilashi. Daga nan sai samarin garin su dinga zuwa suna ɗaukan sunayen. Duk wacce saurayi ya ɗauki sunanta, to shikenan ta zama tashi a wannan biki, wasu kuma sanadin aurensu kenan. A irin wannan rana zina ba laifi ba ne a wurinsu. Wannan biki dai ya fara aukuwa ne tun kimanin ƙarnuka goma sha bakwai da suka gabata 

Sai dai kuma kiristoci na wancan lokacin a Rum ba sa son irin wannan biki domin ya saɓa wa addininsu, hakan ya sa Faparoma Gelasius I (492–496) ya soke wannan biki na Lupercalia. Bayan ya soke wannan biki ne sai ya samar da wani sabon bikin, shi ne bikin tunawa da wani shahidin su mai suna St. Valentine wanda aka kashe a ranar 14th ga watan Fabarairu. 

To amma me ya haɗa wannan biki na kiristanci kuma da bikin ranar masoya? Domin samun wannan amsa, bari mu je ga tarihin shi kanshi Valentine ɗin A taƙaice. 


TAƘAITACCEN TARIHIN SAINT VALENTINE 

Masana sun yi saɓani dangane da wane Valentine ne Paparoma Gelasius I ya ƙaddamar da wannan rana domin tunawa da mutuwarsa. Dalili kuwa shi ne: malaman kiristoci da su ka mutu da dama sunansu Valentine, sai dai akwai guda biyu da suka fita daban waɗanda kuma duk sun mutu ne a ranar 14th ga watan Fabarairu, ko da yake dai ba a shekara ɗaya bane. 

Amma wanda aka fi danganta wannan biki da shi, shi ne Valentine na Rome. Shi dai wannan Valentine ɗin wani malamin addinin kiristanci ne wanda Sarki Claudius II ya sa aka kashe a cikin ta hanyar datse masa kai a cikin ƙarni na uku. 

 Zance mafi ƙarfi dai ya nuna cewa sarki Claudius II, wanda bamaguje ne ya haramtawa sojojin lokacinsa yin aure, saboda a cewarsa, tuzuran sojoji sun fi bayar da abinda ake nema daga sojoji fiye da masu aure. Sai dai duk da wannan doka da sarkin ya kafa, Saint Valentine sai ya ci gaba ɗaurawa sojojin aure a ɓoye, wannan dalili ne ya sa aka kama shi kuma aka kashe shi. Wannan kisa da aka yi masa ne ya sa aka dinga girmama shi a tsakanin 'yan uwansa kiristoci. Shi ma ɗayan Valentine ɗin dai ana tsammanin ya mutu ne a kan wannan dalili. 

Sai dai kafin a kashe Valentine, a yayin da ya ke zaman kaso, ya kamu da son 'yar wanda ya sa aka kama shi. To a cikin kurkukun ne ya rubuta mata wasiƙa tare da bayyana mata irin son da yake mata. A ƙarshen wasiƙar ne ya sa hannunsa da cewa: “from your Valentine” (Ma'ana daga Valentine ɗin ki) wannan shi ne asalin yadda kalmar ta samu zama a cikin bikin masoya na duniya da ake yi a yanzu. 

Wannan jajircewa ta Saint Valentine ya sa Cocin katolika suke girmama shi, har ma coci suka gina a cikin shekarar 350CE a inda ya mutu da kuma ta hanyar bikin ranar Valentine wanda a wancan lokaci biki ne na addininin kiristanci da a koyaushe ake jinjinawa Saint Valentine a matsayin wanda ya yaɗa ƙauna kuma ya ba soyayya muhimmanci a kiristance. 

Hakan yasa da Faparoma Gelasius I ya zo sai ya yamutsa abun ta hanyar daidaita ranar bikin Valentine da kuma bikin Lupercalia domin ya daƙike bikin maguzawan Rum na wancan lokaci. 

Sai dai ungula fa ba ta canja zani ba. Domin kuwa banbancin bukukuwan kawai shi ne su kiristoci suna sanya kaya kuma ba sa dukan mata da ɗanyar fata ne kawai, amma shaye-shaye ba'a daina shi ba, kamar yadda kuma ba'a daina alaƙanta bikin da ranar masoya ba. 

 KO MENENE HAƊIN BIKIN VALENTINE DA HOTON ƊAN YARO MAI FUFFUKE RIƘE DA KWARI DA BAKA? 

Shi wannan yaro da akan ga hotonsa a jikin katukan bikin ranar masoya watau Valentine, a zahirin gaskiya ba yaro bane. Ɗaya ne daga cikin ababen bautar Rumawa da a turance ake kiransa da Cupid. Shi ɗa ne ga abar bautar So da kuma kyau wato Venus. Ya shahara matuƙa a labaran kunne-ya-girmi-kaka inda ake cewa yana harbin mutane da aljannu da kibiyarsa ta so wanda hakan ke sa mutum ya ji kawai nan take ya kamu da son wani. Daga cikin dalilan da suka sa ake sanya shi a jikin katukan saƙonnin bikin Valentine kuwa shi ne, saboda masu aika saƙon suna fatar ya harba kibiyar ta soki zuciyar wanda suka aikawa da saƙon domin ya kamu da son su. Allaah ya kiyaye mu. 

BIKIN RANAR MASOYA A MUSULUNCI.

Manyan malaman Musulunci na wannan zamani kaf sun aminta dangane da haramcinsa, kamar yadda majalisar malaman Saudiyya duk sun haramta wannan biki bisa madogara ta shari'a. Domin Addininmu ya hana mu yin tarayya da kafurai a bukuwan da suka kebanta da su. Baya ga kamanceceniyar da wannan zai haifar ta wannan ɓangare tsakanin musulmi da waɗanda ba musulmi ba, shi wannan biki ta kowace fuska in ka kalle shi yana keta alfarmar shari’ar musulunci ne, bugu da ƙari akwai fasadi mai yawa da wannan biki ya ƙunsa domin kuwa su kansu kiristocin suna ƙorafi da wasu munanan abubuwan da ake aikatawa a irin wannan rana. 

Tunda kuwa hakane, to babu shakka dole mu ƙauracewa wannan biki. 

Saboda faɗin Allaah ta'ala: 

بِسمِ اللَّهِ الرَّحمٰنِ الرَّحيمِ

۞ يا أَيُّهَا الَّذينَ آمَنوا لا تَتَّخِذُوا اليَهودَ وَالنَّصارىٰ أَولِياءَ ۘ بَعضُهُم أَولِياءُ بَعضٍ ۚ وَمَن يَتَوَلَّهُم مِنكُم فَإِنَّهُ مِنهُم ۗ إِنَّ اللَّهَ لا يَهدِي القَومَ الظّالِمينَ


Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku riƙi Yahudu da Nasara majiɓinta. Sashensu majiɓinci ne ga sashe. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, lalle ne shi, yana daga gare su. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai.

(Ma'ida: 51)


لا يَتَّخِذِ المُؤمِنونَ الكافِرينَ أَولِياءَ مِن دونِ المُؤمِنينَ ۖ وَمَن يَفعَل ذٰلِكَ فَلَيسَ مِنَ اللَّهِ في شَيءٍ إِلّا أَن تَتَّقوا مِنهُم تُقاةً ۗ وَيُحَذِّرُكُمُ اللَّهُ نَفسَهُ ۗ وَإِلَى اللَّهِ المَصيرُ


Kada muminai su riƙi kafirai masoya, baicin muminai. Kuma wanda ya yi wannan, to, bai zama a cikin komai ba daga Allah, face fa domin ku yi tsaro daga gare su da 'yar kariya. Kuma Allah yana tsoratar da ku kana. Kuma zuwa ga Allah makoma take.

(Ali Imran: 28)

Kuma manzon Allah Sallallahu alaihi wa sallam yana cewa:
 “Dukkan wanda yayi kamanceceniya da wasu mutane, to yana cikin su”.

Kenan wannan hujja ce ƙarara kan haramcin yin wannan biki. Allaah ya ganar da mu. 


ME YA KAMATA MUSULMI SU YI DANGANE DA RANAR BIKIN VALENTINE? 

1. Da farko dai duk wani musulmin kirki ya kamata ya nuna ƙiyayyarsa ga wannan biki ko tarayya a cikinsa ko halartar wurin da a ke yinsa. 
 2. Ƙauracewa ko bijirewa duk wata ƙofa wacce za ta taimaka wajen ci gaban wannan biki ta kowace fuska. 
 3. Bayyanar da ƙyamar bikin a fili tare da ƙin shiga duk wani abu da ya jiɓince shi. 
 4. Kada ka/ki yi wa kowa murnar ranar kuma ko an maka kada ka amsa, in ma da hali ka zaunar da mutum ka bayyana masa dalilanka na ƙin wannan bikin. 
 5. Yi wa Juna NASIHA dangane da wannan kauce wa irin wannan biki. 

A ƙarshe, ina roƙon Allaah da Ya tsare mu da tssrewarsa, Ya karemu da karewarsa, Ya shiryar da mu daga Shiriyarsa, kuma Ya azurta mu da kyakyawar fahimta. Ya Allaah ka yi mana maganin abinda ya fi ƙarfinmu, Ka yafe mana laifukanmu kuma ka azurta mu da gidan Aljanna.

Aameen Thumma Aamen.

Haiman Raees
08185819176
Haimanraees@gmail.com 
Share:

TARIHIN HAMSHAKIN MATAFIYI IBN BATTUTA Kashi na Uku.

TARIHIN HAMSHAKIN MATAFIYI IBN BATTUTA
Kashi na Uku.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
Bayan Ibn Battuta ya kammala aikin Hajjinsa, sai kuma ya ɗaura harami ya shiga cikin wani ayari mai tafiya kasar Iraqi. Daga can kuma bayan ya huta sai ya wuce zuwa Iran, a inda babu jimawa ya sake tattaro kayansa ya biyo ayarin mahajjata, sai gashi a saudiyya.
Daga nan bai zame ko ina ba sai gabashin afirka, inda yayi kara-kaina, ya zagaya kasashen larabawa ta kudu, sannan ya sake ɓulla kasar saudiyya.
A wannan karon ma bai jimaba, sai yabi tawagar wasu matafiya, kwanci tashi sai gashi a Misira. Ya sauka yayi 'yan kwanaki, sannan ya tashi izuwa kasar syria, a inda babu jimawa ya tsallaka babban teku ya dira a Crimea.
Anan ne kuma tafiyar Ibn Battuta ta mika izuwa yankin Asia, inda ya shiga kasashen Khwarizm, Bukhara da Afghanistan, sannan ya tsallaka tsohuwar daular musulunci data kafu a Delhi ɗin kasar India.
Ibn Battuta ya shafe shekaru biyu a Delhi yana rike da mukamin alkalin alkalai. Daga nan yaji tawaga zata tashi zuwa birnin Sin (China), cikin azama yace zai bita.
Akan hanyarsa ta zuwa china ya sauka a Maldives har ma yayi aikin alkalanci na watanni shidda, sannan ya cigaba izuwa Ceylon, Bengal, Zaitun da Canton, har dai a karshe ya riski china.
Ance a farkon shekara ta 748 hijiriyya, Ibn Battuta ya sake ɗaura ɗamarar komawa kasashen Iran, Iraq da syria, daga bisani kuma sai ya koma saudiyya domin sake gabatar da aikin Hajji.
Bayan ya kammala sai kuma yabi ayarin wasu libiyawa ya riski garin Fezzan mai makotaka da Borno, sannan ba tare da gajiyawa ba kai tsaye yayi haramar tun karar garin Grenada na kasar spain.
Daga can ne kuma sai ya sake ɗaura sirdi, ya dawo yankinmu na afirka, inda kai tsaye ya tunkari birnin Timbuktu na kasar Mali, sannan ya garzaya izuwa garin Gao, daga nan kuma labarnsa ya riske kasarsu Morocco, sai Sultan Abu Inan ya aika masa ya dawo gida.
Bayan Ibn Battuta ya koma gida ne ya labartawa sakataren fadar sarkin kasarsu mai suna Ibn Djozay duk labarin tafiyarsa, wanda shine aka taskance tare da maidashi littafi mai suna RIHLA.
A karshe, Ibn Battuta ya rasu a kasarsa ta haihuwa a shekarar 1368 zuwa 1369.
Littafin Rihla kuwa na ɗaukene da labarin tafiyar Ibn Battuta tun daga sanda yabar garinsu Tangier har sanda ya komo, da yadda yasha wahalar tafiya gami da yadda ya rinka samun arziki yana kuma kyautar dashi ga mabukata.
Haka kuma Ibn Battuta ya bayyana mummunan labarin abin daya auku a gareshi yayin haɗuwarsa da wasu 'yan fashin teku a yankin Turai, waɗanda suka tsareshi tsawon kwanaki takwas tare da kwace dukiyarsa, a karshe da kyar ya kuɓuta daga hannunsu daga shi sai dardumar sallah. Amma kuma bayan ya tsallaka garin Malabar ya nemi mafaka, sai aka naɗa shi alkali mai daraja a garin.
Ibn Battuta ya rinka bada hujja a duk garin daya ziyarta, yana mai faɗin yadda ya samu garin, ko kuma wani muhimmin abu daya auku a lokacin zuwansa.
Misali
Ya faɗa akan zuwansa Kasar saudiyya cewa "Na shafe shekaru biyu ina rayuwa ta tsarki da imani mafi soyuwa ga ubangiji. A koda yaushe ina kusa da ka'aba wajen bautar Allah, da sauran wurare tsarkaka."
Ya faɗa akan zuwan sa Cairo cewa "A garin zaka samu manyan masana da jahilai, zaka samu masu gina gumaka da masu bautar ubangiji, masu zafin zuciya da masu karimci.. Cikar garin da batsewarsa kuwa takai ka misaltata da kaɗawar igiyar teku. Haka kuma duk da garin tsoho ne, amma gine ginen sa na zamani ne".
Ga kuma abin daya faɗa a zuwansa Ceylon "Mutanen cikin birnin mabiya addinin Bhudda ne, amma suna girmama musilmai ta yadda suna basu muhalli da abinci mai daɗi."
Amma game da indiyawa, ya faɗa cewar basa taɓa yin abota da musulmi, ba kuma sa bashi abinci ko abinsha, amma basa cutar dashi yayin da yazo wucewa ta kasarsu.
A Zuwansa Turkey, Ibn Battuta ya faɗa cewa Turkawa suna barin dabɓobinsu suyi kiwo babu mai kula dasu, domin dokarsu akan sata mai tsauri ce.
A cewarsa, idan aka samu mutum da dokin sata a Turkey, za'a tilasta shi ya maida dokin tare da karin dawakai guda tara. Idan kuwa ya gaza yin haka, to ɗansa za'a kwace amaimako.
A game da zuwansa china, Ibn Battuta ya faɗi cewar yasha mamaki matuka musamaman yadda yaga kaji da zakaru a china manya manya. Har ma yace akwai sanda abokinsa ya siyi kaza don suci, amma saboda girmanta sai a tukwane biyu suka dafa ta.
Haka kuma, Ibn Battuta yace ya kayatu sosai da tulin jiragen ruwa dake gaɓoɓin tekunan kasar china. Ya kuma faɗa cewa a kowacce gaɓar teku, akwai mutum dubu goma masu bada kariya, ɗari shidda mayaka ne, ɗari huɗu kuma masu harbi da kibau ne.
Sannan kuma ya faɗa cewar bai taɓa wuce wani gari a china ya dawo shiba face sai ya riski an taskance zanen fuskarsa a garin.
Acewarsa, mutanen kasar nayin haka ga kowanne bako saboda koda zaiyi laifi ya gudu, sai su aika da fuskarsa sassan duniya ta yadda da anganshi za'a kame shi.
Ibn Battuta ya kayatu da kyawun gine ginen garin Constantinopole na kasar egypt. Haka kuma ance ginin cocin Saint Sophia yayi matukar burgeshi, amma yaki yarda ya shiga cikinsa saboda ya lura idan ya shiga tilas ya russunawa gicciye na kiristoci.
Akwai kuma labarin daya bayar mai nuna gudun duniyarsa da rashinsa ga kwaɗayi, wanda yace wata rana suna tare da sarkin ceylon yana cin wasu zaɓaɓɓun Inibai, sai sarkin yake tambayarsa ko ya taɓa ganin inibai masu kyawun waɗannan?
Nan take Ibn Battuta yace tunda yake shige kasashe, bai taɓa ganin inibai kamar suba.
Wannan sai yasa sarkin yaji daɗi, har ma yacewa Ibn Battuta ya kwashe duk iniban ya bar masa su kyauta. Amma sai Ibn Battuta ya kalli abin a matsayin kaskanci, sannan yace da sarkin shifa ba wannan ne damuwar saba, abinda yafi bukata shine yaga sawun kafar Annabi Adamu da akace akwaishi a kasar.
Tabbas Ibn Battuta ya rayu cikin ilimi da imani.
Da fatan Allah yajikansa amin.
Share:

TARIHIN SARKIN MOROCCO MOULAY RASHID ISMA'IL


TARIHIN SARKIN MOROCCO, MOULAY RASHID ISMA'IL.

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
08060869978

An haifi Moulay Ismail Rashid a wajajen shekarar 1646 a birnin Fez na kasar Morocco. Ya gaji mulkin Morocco ne tun yana da shekaru 26 a duniya bayan da ɗan uwansa mai mulki ya faɗo daga kan doki ya mutu.
A wancan lokacin Moulay Ismail ya samu daular Moroco rarrauna saboda yawaitar faɗace-faɗace tsakanin kabilu gami da rikicin sarauta da yayi tsamari a daular. Baya da haka ma, birnin Marrakesh yayi bore ga shugabancinsa, inda mutanen garin suka shiga biyayya ga ɗan amminsa mai suna Ahmad ibn Muhriz.
Don haka da fara mulkinsa, sai ya jagoranci runduna zuwa Marrakesh dake kudancin birninsa, ya faɗawa garin da yaki har kuma yaci nasarar kwace ikonsa, amma sai shugaban boren Ahmad bn Muhriz ya tsere ba tare da an kame shi ba.
Sarki Moulay Ismail na ɗaya daga cikin sarakuna masu karfin iko waɗanda duniya ba zata taɓa mancewa da sunansu ba.
Da fari dai, ya ɗauke cibiyar daularsa daga birnin Fez zuwa Meknes, sannan ya umarci a kawata ganuwar birnin da kawunan sojojin abokan hamayya guda dubu goma.
Ance akalla a kusan shekaru hamsin dayayi yana mulki, ya kashe mutane sama da dubu talatin waɗanda yawancinsu barorinsa ne, ɓata masa rai sukayi kurum, ko kuma ace lalacinsu ne ya isheshi sai yasa a kashe su.
Wasu kuma ya sanya a kashe sune saboda ayyukansu bai gamsar dashi ba. Domin ance shi makarancin littafin alkurani mai girma ne, kuma indai yana bisa doki, yana umartar barori su bishi ɗauke da alkurani a buɗe yana mai karantawa, amma fa da zarar sun aikata abinda ya sosa masa rai sai ya sare kawunansu.
Sarki Moulay Ismail ibn Sharif ya shahara wajen gwabza yakuna da makwabtansa, sannan ya ciri tuta wajen kawata babban birninsa, domin shine sarkin daya umarci ayi gine-gine masu kayatarwa a birnin Meknes, misalin makarantu, masallatai, lambuna da wuraren hutawa da kuma ganuwa ga wannan birni.
Haka kuma yayi gagarumin faɗa da daular Ottoman wadda cibiyarta ke kasar Turkiyya, anan ne har ya samu nasarar 'yantar da kasar Morocco daga karkashin wannn daula.
A shekarar 1981 Sarki Moulay Ismail ya gwabza yaki da turawan Kasar Spain tare da karɓe ikon birnin 'La Mamora' mai ɗauke da tashar teku, inda ya sauyawa birnin suna izuwa al Mahdiya.
A lokacin wannan yaki, wakilin sarkin mai suna Kaid Omar ya faɗawa Sifaniyawan cewa idan suka mika wuya ba zasu bautar dasu ba, wanda hakan ya karfafa musu guiwar dakatar da gwabza yaki bisa tsammanin samun adalci, amma bayan anci nasara, sai Sarkin yaga cewa sam ba zai iya barin sifaniyawa sama da dubu biyu masu ɗauke da kyawawan mataye da kayayyaki masu daraja ba sasakai, sai kawai ya bada umarnin a taso keyarsu zuwa birnin Meknes a matsayin ganimar yaki.
A shekarar 1684 Moulay Ismail ya kwace ikon birnin Tangier wanda a lokacin turawan Portugal ke iko dashi, haka kuma a shekarar 1689 ya sake karɓe ikon wani babban birni mai suna Larache daga hannun turawan sifaniya.
Bunkasar wannan sarki takai yadda sai daya tara rundunar mayaka bakaken fata mai ɗauke da akalla soji dubu goma sha biyar, dasu ya haɗa da nashi wajen yaki ta yadda sai daya karɓe ikon ɗaukacin kasar Morocco daga hannun turawa idan aka ɗauke yankunan Ceuta da Melilla.
Akwai labaru masu nuna gwagwarmayar daya buga da faransawa, tunda ance ya kame wasunsu masu zuwa leken asiri kasarsa tare da mayar dasu bayi, amma wasu na ganin kasancewar a lokacin sarkin Faransa Louis na 14 yana kiyayya da Sipaniyawa, ance akwai zumunta maikyau a tsakaninsa da Sarkin na Meknes.
An kuma ruwaito cewa Sarki Moulay Ismail na Morocco ya taɓa aikewa da jakada mai suna Muhammad Temimin domin nema masa auren gimbiyar Faransa mai suna Marie Anne de Bourbon amma sai taki amincewa, sai dai duk da haka alaka mai kyau taci gaba da ɗorewa a tsakaninsu.
A iya tsawon rayuwar Sarki Moulay Ismaïl, ance ya haifi 'ya'yaye guda 867, maza guda 525 da mataye 342. Ance baya da mataye guda huɗu da yake dasu, akalla yana da kuyangi guda 2,000, kuma an ƙlisssafta cewar a kalla a tsawon shekaru tamanin da yayi a raye, a shekarunsa sama da hamsin bisa karagar mulki akullum yana jima'i sau biyu, ko kuma da mataye guda biyu.
Don haka sunansa ya shiga tarihi a matsayin wanda yafi kowanne namiji yawan haihuwa anan duniya a iya abinda ya fito ga sanin masana zuwa yau.
Bayan rasuwar Moulay Ismaïl a shekarar 1727, rikici ya kara ɓarkewa tsakanin 'ya'yansa bisa wanda zai gajeshi a mulki, daga karshe wani ɗansa Muhammad yayi galaba, tare da ɗorawa akan gine-ginen da mahaifinsa ya soma. Sai dai girgizar kasar data auku a birnin Meknes cikin shekarar 1755 ce ta lahanta kusan ɗaukacin waɗannan gine-gine, daga karshe tilas Sarki Muhammad ya ɗauke cibiyar birnin daga nan inda ya maida ita zuwa birnin Marrakesh.
Macen da tarihi ya kiyaye a matsayin wadda tafi kowacce yawan haihuwa itace Mrs Vassillev ta birnin Moscow, wadda ta rayu tsakanin shekarun 1725 - 1765. Ance tayi nakuda sau 27, sau 16 tana haihuwar tagwaye, ta haifi 'yan uku sau bakwai, ta haifi 'yan huɗu sau huɗu. Jimilla ta haifi 'ya'yaye 69 reras.. (Kimiyya ta tabbatar da haka)
Share:

TARIHIN TSOHON GARIN GANGARA DA YADDA AKA YI GARIN MALUMFASHI YA FITO DAGA GARESHI

TARIHIN TSOHON BIRNIN GANGARA DA YADDA GARIN MALUMFASHI YA FITO DAGA GARESHI.

SADIQ TUKUR GWARZO

Kirarin Garin: Gangara Ta Naturɓe, idan kaji ina kwana bako ne.. Sai dai Nyalli Jam.
Wannan gari tsoho ne, jimawarsa kuma har takai wasu na ganin ya girmewa tsoffin birane misalin Malumfashi, Getso, Baɗari da birnin Kano.
Fulani kabilar Natirawa ne akace suka kafa garin lokaci mai tsawo daya shuɗe, sannan labari na gaskiya ya dusashe dangane da tsohon birnin, ko kuma lokacin kafuwarsa, wanda a yanzu ya zama kufai, amma dai zuwa yanzu an iya gane sashen ganuwar tsohon birnin. Haka kuma marinar garin da tsoffin kukoki nanan a inda tsohuwar rayuwar Natirawan ta auku shekaru ɗaruruwa da suka gabata.
Babban limamin Garin mai suna Mallam Adamu, ya bayyana mana cewar an samo sunan garin 'Gangara' ne daga kalmar 'Gagara', ko kuma ace garin daya Gagara acishi da yaki, domin tunda wannan birni yake babu wani sarki daya taɓa cinsa da yaki.
An samu cewa garin Gangara na usuli shahararre ne, mai zagaye da ganuwa, mai ɗauke da tarin mutane kuma. Mutane na zuwa fatauci daga sassa daban daban na kasar hausa. Har ma ance akwai zamanin da saida gidaje suka cika birnin, har ma wasun suka rinka yin gidaje a bayan ganuwa.
Sannan kasancewar garin na fulani ne, akwai tsohuwar al'adar nan ta sharo da kuma wankan amarya da aka ruwaito tana wakana tsakankanin mazauna birnin, amma dai ance musulunci ya samu karɓuwa tun kafin zuwan Mujaddadi Usmanu ɗan fodio, don haka abubuwa irin na maguzanci basu yawaitaba.
A batun yake-yake, garin Gangara yayi zarra, tunda ance akwai wani K'aton kada mai suna 'Nabogaji' wanda yake cikin wani tafki dake kusa da garin, wanda kuma yake rura kuka yayin da wani bala'i ya tunkaro garin domin sanar da mazauna birnin suyi shiri.
Dukkan maruwaitan tarihin garin Gangara sun haɗu akan cewa babu wanda ya taɓa cinye garin da yaki. Wasu sunce da zarar Nabogaji yayi ruri, sai idanuwan mahara ya rufe, ya zamo basa iya ganin birnin da abinda ke cikinsa. Yayinda wasu ke ganin tsabar jarumtar sadaukan birnin ke basu ikon mayar da keyar mahara baya.
Ance Gangara ta taɓa kaiwa garin Getso hari, taci nasara akan garin, har saida ta kori maza da mata dake garin.
Haka kuma gangara tayi yaki da garuruwan matazu, kurkujan na musawa, da malumfashi a baya-bayan nan, kuma duk ta samu nasara.
Liman Mallam Adamu ya faɗa mana cewar asalin garin malumfashi Gangara ne. Domin kuwa zamani mai tsawo daya wuce, an taɓa yin wata annoba ta ciwon ciki wadda mutanen birnin Gangara suka rinka mutuwa.
Don haka sai mutanen suka tashi izuwa gefensa suka kafa sabon gari, yayinda waɗansu suka fantsama sassan duniya.
To ance daga irin waɗannan mutanen ne wani banatire mai suna Dano (ko Dunu ) ya riski garin malumfashi a lokacin yana jeji. Sai ya sauka sannan ya sari gona domin yaɗan taɓa noma.
Da amfanin gona yazo, sai ya zamana ya samu alheri, don haka ya shiga godiya ga mai sama yana faɗin "Yanzu Na-numfasa"
Daga nan kuma sai labari ya iso garinsu Gangara, inda mutane suka rinka tafiya inda yake da zummar suje suyi noma su samu riba da kuɓuta daga waccan annoba. Don haka sai suma suka rinka cewa "zamu tafi inda Dano yake Munumfasa" watau mu huta daga wannan annobar. Daga baya aka maida sunan garin ya koma 'mulumfashi' ko 'Malumfashi'.
A cewar Liman, babbar hujja akan haka shine unguwar Gangarawa dake garin malumfashi. Wadda babu wata tsohuwar unguwa data girme mata.
Sunan sarautar garin Gangara shune 'ɗan-saka', ance ta samu ne daga wani sarkinta mai sakawa duk waɓda aka yiwa zalunci daga talakawansa. Hak kuma kasancewar sunayen tsoffin sarakunanta sun ɓata, amma dai an samu cewar a baya bayan nan sarakuna irinsu:-
Dan saka Atiku, Dan saka Babba, Dan saka Nani, Dan saka Isiye, Dan saka Bello zarɓe magajin tunkuɗa, ɗan saka sarki ya-musa, ɗan saka yuguda, da ɗan saka muhammadu magajin daɗi duk sun mulketa, sai kuma dagacin dake mulkinta ayau mai suna Magaji Alh Bala ɗan muhammadi majidaɗi.
Koda yake, ance yanzu sarautar ɗansaka ta koma garin Gora bisa tashin tsohom ɗan saka Muhammadu majidaɗi daga Gangara zuwa garin na Gora saboda tsangwamar natirawa, don haka da aka turo ɗansa sai ake masa lakabi da Magaji. Saboda hak yanzu sunan sarautar garin 'Magaji'.
Sannan kuma har gobe mutanen garin Gangara suna fahari da cewar Mujaddadi Shehu Usmanu ya sauka a garin akan hanyarsa ta zuwa kano daga sokoto, harma ya sahale aka soma sallar juma'a a garin, a lokacin da duk yamma da kano daga Rimin Gado, sai malumfashi ake zuwa yin sallar jumu'a...
Zuwa yanzu dai, garin yana nan a kusa da garin Dayi, kuma yana karkashin karamar hukumar malumfashi ne ta jihar katsinan Nigeria.

Share:

TARIHIN JARUMI NANDAMURI KALYAN RAM

An Haifi Jarumi Nandamuri Kalyan Ram a ) 5 ga watan July shekara ta 1978), Yaka sance Jarumin India ne Shi Sannan Kuma Mai daukar Nauyin shiri Wanda akafi Sanin Aikinsa a Masana'antar Telugu cinema .Ďane ga Jarumi Sannan kuma Dan Siyasa Nandamuri Harikrishna , Mahaifiyarsa Lakshmi. Sannan Kuma Jikane ga N. T. Rama Rao, Wanda yaksance shima Jarumi Sannan kuma kwararren dan Siyasa . Sai kuma Jarumi Jr. NTR yaka sance Kani ne ga Jarumi NKR . Sannan yanada Kamfani mallakar Kansa Wanda ya bawa Suna bayan Mutuwar Kakansa Mai Gayayi NTR , An bawa Kamfanin Suna . N.T.R. Arts. Jarumin ya kafta roles a wasu fina finai da ya zama Kwari kamar su Athanokkade, Hare Ram, Pataas, Ism da 118. Sannan kuma yanada Kamfani nasa na VFX company wanda aka bawa Suna da "Advitha Creative Studios",Kamfanin da aka samarda fina finai masu himma kamar su Legend, Nannaku Prematho da Krishnashtami.
An haifi Nandamuri Kalyan Ram a 5 July 1978 Shekarun sa 41 an haifeshi a garin Hyderabad, India a yankinTelangana, India)
Mazaunin: sa Hyderabad, Telangana, India .
Kasar sa ta haihuwa: india.
Inkiyar sa : NKR.
Inda yayi karatu :MS at Illinois Institute of Technology, Chicago, US,BE a Coimbatore .
Aikin sa : Jarumin Film , Mai daukar Nauyin Shiri.
Shekarar da ya Fara Film 1989; 2003–
Matar sa :Swati
Ya'yansa : Sourya Ram da Taraka Advitha
Mahai finsa :Baban shi Harikrishna Nandamuri
Mahaifiyar sa :Lakshmi Nandamuri.
Dan uwan sa na jini: Jr. NTR
Yayar shi : Nandamuri Suhasini.
Kakan shi: N. T. Rama Rao .
Kawun sa :Nandamuri Balakrishna .
Wani Kawunsa kuma :N. Chandrababu Naidu .
Antin shi :Daggubati Purandeswari .
Dan uwan sa :Nara Lokesh .
Dan uwan sa kuma :Nara Rohit .
Wani dan uwan nasa :Taraka Ratna .

Share:

TARIHIN BIRNIN AUYO


Tarihin Tsohon birni 'auyo'.
Daga
Gaddafi Hussain Auyo
08149217486 da
Sadiq Tukur Gwarzo.
Garin Auyo tsohon gari ne, domin kuwa tarihi ya bayyana mana cewa Auyo na ɗaya daga cikin tsoffin birane kuma mashahurai a wannan kasa waɗanda sukayi sharafi har kuma ya zamo suna cin gashin kansu tun tsawon zamani daya gabata.
Haka Kuma birnin Auyo ya jima yana ɗauke da tsarin masarauta wadda sarakuna ke tafiyarwa cikin ka'idoji gami da lura.
Dangane da daɗewar Auyo, tarihi ya bayyana mana cewa ko lokacin da fir'auna Remesis II na zamanin Annabi Musa (A.S) yayi yekuwa tare da gangami daga manyan birane yana mai neman waɗanda suka kware akan sihiri da surkulle, a wannan karawar da tarihi ya ruwaito Firaunan yayi da Annabi Musa A.S, an samu cewa tabbas akwai matune a Auyo, har kuma wasu shahararru akan sihiri daga kasar Auyo sun halarci wancan taron tare kuma da jarraba tsibbace-tsibbacen su a wurin, amma daga bisani da Annabin Allah Musa yayi galaba akan ɗaukacin Masihirtan, ance suna cikin waɗanda suka gaskata Annabi Musa (A.S) kuma sukayi masa mubayi'a.
Har ila yau, akwai zance na gaskiya mai nuna cewar lokacin da tawagar wakilai daga kasar Borno a zamanin wani Sarkinsu da ake kira 'Maidinama' suka tafi birnin Madina domin su karɓo addinin musulunci a wajen Shugaba, Manzon Allah (s.a.w) har kuma suka tarar Manzon Allah yayi wafati sai Sayyadina Abubakar R.A ne ke Halifanci, har da mutanen Auyo acikin tawagar.
A wancan lokacin ance shima Sayyidina Abubakar ɗin yana fama da yakuna, don haka yace su zauna kafin a samu natsuwa, har kuma Allah ya karɓi rayuwar sa. Amma da fara Halifancin Sayyidina Umar R.A sai ya taso da maganar, ya haɗo rundunar sahabbai da littattafai suka taho Borno..
Kasar Auyo ta kasance mai daɗaɗɗen tarihi, domin kuwa anyi imanin cewa duk wasu garuruwa da ake alakantawa da hausa bakwai ko banza bakwai, to kuwa Auyo ta girme su.. A ciki harda Daura, domin dai abisa kiyasi na bincike an gano cewa Auyo tafi shekara dubu biyar da kafuwa.
Ance wani mutum mai suna 'Auya' shine ya kafa garin na Auyo, don haka daga sunan sane aka samo kalmar 'Auyo', kuma shi ɗan kabilar 'Bagirmine' waɗanda akace tun da jimawa suna zaune a arewaccin kasar Sudan.
Kasar Auyo tana da mashahuran malamai masanan addinin musulunci. Tarihi ya bayyana mana cewa daga cikin malaman da sukayi fice a kasar kano akwai da yawansu waɗanda asalinsu Auyakawane.
Garin Auyo yana ɗaya daga cikin garuruwan da anan baya-baya aka haɗe aka samar da masarautar Hadejia. Amma wannan gari sam ba koma baya bane acikin tarihin kasar Hadejia, kasancewarsa tsohon gari wanda ya daɗe da wanzuwa zamuna masu tsawo da suka shuɗe, gashi kuma sanan-nan gari daya tattara mutane masu baiwa iri daban-daban kama daga dakaru da baraden yaki zuwa uwa uba malamai mahardata alqur'ani mai girma.
Auyo ta jima ɗauke da masana masu ilimin taurari dana bugun kasa da masu lakkuna da sauran iliman asararu na tsaron kai da tsaron kasa, haka ma suna da mutane wadanda suka shahara wajen sihiri da surkulle irin na wancan lokacin. Don haka muna iya cewa ita tunjimin gari ne wanda kome mutum yaje nema yana iya samu..
Share:

TARIHIN SARAUNIYA AMINA TA BIRNIN ZAZZAU: MACE MAI KAMAR MAZA

TARIHIN SARAUNIYA AMINA TA BIRNIN ZAZZAU: MACE MAI KAMAR MAZA..
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Amina Sarauniyar Zazzau, ko kuma ace sadaukiyar zazzau wadda akace ta rayu a wajajen shekara ta 1433 zuwa 1610, ɗaya ce daga cikin ‘ya'ya uku da sarkin Zazzau Bakwa Turunku ya haifa. Watau ita Amina ɗin da ƙanwarta mai suna Zariya, sai namijin kaninsu da ake kira Karama.
Ance Amina tayi sarautar Zazzau bayan rasuwar ɗan uwanta Karama wanda ya soma gadar mahaifinsu, a wajajen shekara ta 1509 zuwa 1522, ance kuma shekarunta 13 kacal akan karagar mulki ta rasu. Kuma ita ce mace ta farko da ta mulki masarautar Zazzau, shugaba ta shida a cikin sarakunan haɓe waɗanda sukai mulki bayan Addinin Musulunci ya fara bayyana a ƙasar Zazzau. Har ila yau a cikin jerin sarakunan Zazzau gaba ɗaya ita ce ta 23.
Sarauniya Amina ta shahara matuƙa a ƙasar Hausa da ma yankunan da daular Usmaniyya ta mulka. Ta-yi-ta kaiwa da komowa na yaƙe-yaƙe a wurare da dama. Mulkin Amina ya faɗaɗa tun daga Zariya har zuwa ƙasar Abuja, da kuma can yankin kwararrafawa dake kasar bauchi sai kuma ƙananan garuruwa na kabilun Nufawa da jukun da dama da sarauniya Amina ta karɓe ikonsu waɗanda akace ba masu girma bane, amma ta kafasu a matsayin makarai, watau kamar dai ace wurare ne data ya-da zango kuma suka faɗa karkashin ikonta. Shine har akace tana sanyawa ayi ganuwa don samar da tsaro, ganuwar da ake sanyawa suna 'Ganuwar Amina' (har yanzu akwai wuraren a jihohin kano da katsina).
Da yake Kasar hausa na cikin yamutsin yake-yake tun daga wajajen shekara ta 1200 har zuwa 1700, Kasar zazzau ta zamo cikin halin rashin zama lafiya da makwabtanta a wannan lokaci. Daular Songhai ta kawo mamaya kasar hausa a wannan tsakani, sannan garuruwan kano, katsina da Borno sun zamo manyan abokan gaba ga zazzau. Don haka akace kasar zazzau ta zamo tana matukar bukatar jarumin shugaba a koda wanne lokaci.
Akace akan haka ne Amina ta gaji sarauta. Kuma duk da kasancewar ta mace, ta zamo jaruma abar tsoro ga sadaukai.
Tun tana karama ake ganin alamomin sadaukantaka a tare da ita har girman ta. Don haka lokacin da tahau kan mulki bata samu turjiya daga Sadaukan fadar zazzau ba.
Ance watan Amina ukku akan gadon sarauta ta fara fita yake-yake, inda tarinka cinye garuruwa da yaki tana faɗaɗa masarrautar ta.
A wata fadar ma ance kafin tabar mulki, saida ta tursasa sarakunan Kano da katsina su rinka biyanta Haraji na bayi da goro domin su zauna lafiya. Koda yake wani zancen ya ruwaito cewa Amina ta fuskanci matsananciyar turjiyar yaki daga wani Sarki mai suna Muhammadu Kanejeji, sarkin da Littafin Tarihin kano mai taken 'Kano chronicle' ya ruwaito a matsayin Sarkin Kano na 14 a jerin Sarakunan haɓe. Amma wasu na ganin ta taɓa samun nasarar da har saida ta kori kowa daga birnin kano.
Sai dai bisa wannan, wasu masanan tarihi Mr. J.F Ajayi da Michael Crowder sun sanya rayuwar Amina baya da yadda ake ɗauka duba da yadda littafin tarihin kano ya zayyana cewar tayi sharafi a zamanin sarki Kanajeji, wanda lissafi ya auna cewar ya rayu ne a wuraren shekara ta 1420-1438.
Shi kuma wani masanin tarihin afirka mai suna P.J.M. McEwan ya ruwaito cewa Sarauniya Amina tacinye garuruwan Nufawa dana Kwararrafawa dake yankin ta duka da yaki a lokacin rayuwarta.
Wasu kuma sunce ga dukkan alamu, sai da Amina tafi karfin sarakunan hausa dake mulkin garuruwan kano, Rano, katsina, Daura da Gobir kafin rasuwar ta.
A takaice dai, Babu wani daya taɓa ruwaito cewa Sarauniya Amina ta taɓa aure na din-din-din a rayuwarta, balle ace tabar zuriya bayan rasuwarta. Abinda akace tanayi shine, tana zaɓar sadauki ne idan ta cinye gari da yaki ta (aureshi) kwana dashi, kashegari ta hallaka shi, har wasu sukace a irin haka ta haɗu da wani wanda ya hallaka ta.
Sarauniya Amina tana da jarumta sosai, don haka duk inda zatake yaki itace ke jagorantar rundunar yakin. Kuma zaiyi wahala tayi yaki bataci nasara ba. Wannan ne silar dayasa sunanta ya ɗaukaka a lokacin har wasu ke cewa Amina batayi sarautar zazzau ba, kurum dai Shugabar mayakan zazzau ce wadda sunanta ya kasance maɗaukaki.
Wasu turawa kuwa sun rubuta tarihinta ɗaruruwan shekaru da suka gabata. Har ma ance Shirin fim din Hollywood mai suna 'Xena: The warrior queen' anyi shi akan tane domin ya nuna tarihin ta.
Dangane da batun waje ko kuma garin da Sarauniya Amina ta rasu, a gaskiya babu tabbas, to amma masana tahiri suna kyautata zaton cewa ta rasu ne a can ƙasar Gara, wato ƙasar Igala kenan, wadda ke cikin jihar Kogi a arewacin Najeriya a halin yanzu.
Wasu kuma sukace sam nemar ta akayi aka rasa bayan wani attajiri dayaji labarinta, sai yazo ya nemi kwana da ita, kafin gari ya waye ya sirare yabarta. Ance dagari ya waye sai itama tabar gari, kuma ba'a kara jin duriyar taba. Wannan dalili ne ma ya sa ba a san takamaiman inda kabarinta ya ke ba.
Har ila yau, Wasu sunce kabarinta nacan kasar Bidda, kusa da wani gari nai suna Atagara, wai taje yaki ne ajali ya kamata har aka binneta acan..
Ana mata kirari da 'amina 'yar bakwa ta san rana, mace mai kamar maza kwari ne babu'.
Sai dai har yanzu da akwai bayanai masu sarƙaƙiya da kuma saɓani na masana tarihi a game da rayuwar sarauniya Amina, musamman wajen tabbatar da cewar tayi sarautar zazzau ko kuwa gimbiyar yaki kurum ta zamo ga zazzau ɗin, ba illa yadda wani littafin masarautar zazzau na baya-bayan nan ya rubuta sunayen sarakunan Zazzau tun daga farkon madarautar har zuwa yau ba tare da sanya sunan taba, to amma dai magana mafi rinjaye ita ce, Sarauniya Amina ta taɓa wanzuwa a doron ƙasa, a matsayin jaruma a daular masarautar Zazzau.

Share:

YADDA MULKIN MALLAKA YA KASANCE A NIJERIYA


TARIHI ABIN TUNAWA: Yadda Mulkin Mallaka A Nijeriya Ya Kasance Kafin Bada 'Yancin Kai
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Alhamdullah. Shekaru da dama da suka gabata, yankunan da suka hadu suka bada Kasa mai suna Nijeriya, suna karbar bakuna daga sassa mabambanta na duniya.
A baya-baya nan, wajajen shekara ta 1807, lokacin da masarautar Edu ke kan sharafi, turawa na zuwa yankin domin dillancin bayi izuwa turai. Daga baya kuma sai turawa suka dira a lagos, sannan kamfanin su mai suna Royal Oil company ya wanzu a wajajen Shekara ta 1884 wanda mulkin wasu sassan kasar ya koma karkashin jagorancin George Taubman Goldie mai rike da shugabancin kamfanin kenan, shima kamfanin daga bisani ya gusa inda wasu kamfanonin suka kafu. A takaice dai, daga shekara ta 1900 kafin fara mulkin mallaka, kamfanoni biyu ke mulkar sassan Nigeria guda biyu, watau 'Southern Protectorant Company' a kudu, sai kuma 'Northern protectorant Company' a arewacin kasar, masu kamfanonin sun kasance turawan Ingila, sune kuma jagorori masu kula da siye da siyarwa a yankunan. Suna da sojoji da kayan yaki, tayadda suke amfani da karfinsu wajen maganin duk wata barazana.
An ce a shekarar 1884 ne yayin wata tattaunawa tsakankanin manyan kasashen duniya na wancan lokacin a birnin Berlin na kasar Jamus, akayi kasafin yankunan Afirka don fara gudanar musu da mulkin mallaka. Yankunan Nigeria na kudu da arewa duk sun fada ne a hannun turawan birtaniya, sabanin yankin Niger daya fada a hannun faransa da kuma yankin Cameroon daya fada hannun Jamus.
Kasancewar hakan, sai yasa Ingila tayi shawarar hade yankunan wuri daya. An fara wannan aiki tun a shekarar 1912, amma bai tabbata ba sai a shekarar 1914, a lokacin turawa sun kammala cinye duk wata masarauta kenan dake yankin da yaki. A lokacin kuma, sai aka baiwa tsohon shugaban Mulkin mallaka a Hongkong, Sir Lord Lugard mukamin gwamna janar wanda zai jagoranci mulkin arewaci da kudancin kasar bisa umarnin da zai rinka amsa daga can kasar ta ingila. Hakan na nufin Ingila ta karbe ikon mulki daga hannun kowa, yanzu abinda takeso shi za'ayi a yankin.
An ce babban abin tunawa da Gwamna Lugard a iya zaman da yayi a Lagos yana shugabanci shine kokarinsa na dakatar da cinikin bayi da kuma tabbatar da yankunan sun zamo a hade. Masanan tarihi sun bayyana Lugard da mutum ne tsatstsaura wanda baya jure raini daga bakar fata. Sannan kuma duk da kasancewar sa ya taba rike mukamin gwamnan arewa a baya, ance yafi yiwa kudancin kasar aiki. Dalilin hakan na cikin wani tsari daya kafa bisa sahalewar ingila, cewa kowanne yanki zai rinka samun aikace-aikace ne bisa harajin da suke tarawa. A wancan lokacin ana samun haraji mai yawa daga hada-hadar giya a kudu, amma a arewa giya abar kyama ce saboda musulunci.
Matar Gwamna Lugard mai suna Flora Shaw wadda akace yar jarida ce ta kamfanin 'The Times' ta rinka taimakonsa wajen gudanar da mulki. Itace kuma akace ta lakabawa wannan kasa sunan Nijeriya. (Niger area, watau yankin kogin Niger)
A zamanin mulkin Lugard ne yakin Adubi ya barke a kudancin kasar. Inda kabilar Egba ta yankin yarabawa suka dauki makamai tare da lalata titunan layin dogo (jiragen kasa) da kuma hallaka wasu turawa masu wakiltar ingila dake zama a yankin nasu. Dalilinsu nayin haka shine uzzura musu da akeyi wajen karbar haraji, da kuma tilasta musu bisa yin aiki ga turawa. Kamar misalin layin dogo, duk 'yan kasa turawan ke tursasa yin leburan cinsa cikin zafin rana da kishirwa.
Gwamna Lugard dai bai saurarawa mutanen nan ba. Inda ya taso rundunar soji tazo yankin ta yakesu, kuma taci galaba akansu. Allahu Akbar!
Gwamna Lugard ya rinka turawa Ingila bayanan duk wani abu dayayi a shekara. Wani Kundi mai suna 'Blue Book' a 'Encyclopedia Britannica' ya nuna yadda takardun nasa suka rinka kasancewa. A ra'ayinsa kuma, bai dauki bakar fata mutum kamar baturen ingila ba. Saboda yace bakaken fata nada rauni, idan kabasu fuska rainaka zasuyi. Idan kabasu dama kuma yakar ka zasuyi. Shiyasa ya hana baiwa bakar fata ko ɗaya shugabanci a zamaninsa. Ya kirkiri majalisar zartaswa, amma babu bakar fata wakili koda guda ɗaya, sai dai wata majalisa kurum ta jeka-na-yika daya kafa wadda aka tsulma sarakunan mulki aciki, sukuwa basu da ikon cewa kanzil wajen aiwatar wa, sai dai sujira umarni kurum daga gareshi.
A ranar 8 ga watan Agusta na shekarar 1919 ne Sir Hugh Clifford ya amshi mulki bayan Lugard yayi ritayar aiki. Shikuwa abin tunawa ne ko don kundin tsarin mulki daya sabunta, daga wanda Lugard yayi izuwa sabo wanda ya baiwa 'yan k'asa kafar kirkirar jam'iyyu da kuma kamfanin jarida, da wannan damar Herbert Macaulay yayi amfani wajen kirkirar jam'iyyar siyasa ta farko a kasar nan maisuna 'Nigerian National Democratic Party'. Tare da kirkirar gidan jaridar 'west African Pilot'.
Baya da haka, kundin tsarin mulkin ya tanaji wata majalisar jeka-nayi-ka mai wakilai 46 wadda hudu daga cikinsu yan kasa ne suka zabo su daga yankin lagos da ibadan. Amma fa duk da haka, turawa nanan akan bakansu na cewar babu ruwan yan kasa da tsoma bakin su akan yadda ake mulkarsu. Domin babu bakar fata ko daya a sahun majalisar zartarwar sa, duk turawa ne. Sannan arewacin kasar ya cigaba da zamowa saniyar ware, wanda Gwamnati bata cika kula dashi ba a lokacin.
Ranar 13 ga watan nuwamban 1925 ya zama lojacin fara mulkin Sir Graemi Thompson a matsayin gwamna janar mai shugabantar hadaddiyar Nigeria. Shine wanda akace ya zagaya tun daga ikko har zuwa Borno a mota. Sannan ya samar da karin layukan dogo a sassan kasar, ba illa ma a arewa inda harajin gudanarwar aiyuka yayi karanci, amma ance sai rance akayo daga harajin da kudu ke samarwa wajen aiwatar da aiyukan da arewan ke bukata.
Bayan gushewar sa, sai Sir Donald Charles Cameron ya soma mulki a ranar 17 ga watan yuni na shekarar 1931. Ance Mutum neshi mai daraja bakar fata da son hadin kai. Yayi matukar kokari wajen ilimantar da yan Nigeria ilimin zamani ta hanyar bude makarantu a sassan kasar tare da samar da malamai daga turai. An ma taba jiyoshi yana cewa " Mun zo nan Afirka ne a madadin Kasar Birtaniya domin mu koyar da 'yan Afirkan yadda zasu dogara da kansu. Da zarar wannan muradi ya cika, wajibin mune mu gusa gefe. Hakan kuwa zai dauki tsawon lokaci kafin mu cimmasa, amma kafin nan, dole ne duk abinda zamuyi, muyishi bisa wannan muradin" (Extract ID:4918, Wikipedia-Britannica).
Bayan shi sai Sir Bernand Henry Bourdillon, wanda ya soma mulki a ranar 1 ga watan nuwambar 1935. Shi kuwa ya kamata a tuna dashi ko-dan yadda ya janyo sarakunan arewa masu zaman saniyar ware a gudarwar mulki izuwa cikin mulki. Ya ziyarci manyan sarakunan arewa, ya fada musu cewa ba dai-dai bane rashin tsulma bakunan su a salon gudanar war kasarnan, sannan ya shaida musu irin illar da hakan ke iya samarwa. An ce ya fahimci cewa turawan mulki basu cika kula da arewacin kasar ba saboda dalilai biyu; Na farko, tun sanda Sir Lugard yana mulki ya baiwa ingila shawarar cewa abu ne mai wuya yan arewa su mika kai dari-bisa-dari ga turawan mulki, don haka zaifi kyau a mulki arewa ta hannun sarakunan ta. watau sarakuna na mulkar talakawa, turawa kuma na mulkar sarakuna (sabanin a kudanci da turawan ke mulki kai tsaye ga talakawa). Sannan kuma Lugard din ya fahimci jinin yakibda son shugabanci a jinin al'ummar hausa-fulani, shiyasa yake ganin idan aka basu dama zasu yiwa turawan mulki bore. Abu na biyu kuwa shine karancin harajin dake fitowa a yankin.
Don haka, Sir Bourdillon yayi kokari wajen samar da makarantun zamani a yankin arewa, amma dai manufarsa ta ilimantarwa bata cimmu ba tunda kakannin mu lokacin suna k'in bature da kuma kin duk wani abu daya kawo na sauyi a wancan zamani.
Daga nan sai Sir Arthur Richard ya amshi mulki a shekarar 1943. A lokacin mulkin sane yan kasa (mafi yawa daga kudancin kasar) suka fara kiraye-kirayen abasu 'yancin kai. Hakan ya samu ne saboda an fara wayewa, an samo baiwa wasu kasashen yancin kai, sannan uwa-uba, gwamnan yana da sauki kuma. Shiyasa turawa suke kiran Sir Arthur da lusari, saboda acewar su sanyin sane yasa har aka fara yin wannan ikirari. Abin tunawa a mulkinsa shine ya samar da sabon kundin tsarin mulki a wanda ya raba kasar izuwa sassa uku, gabas, kudu da arewa. A lokacin sane kuma yakin duniya na biyu ya auku, don haka bai samu nutsuwar aiwatar da manyan aiyuka ba.
A shekarar 1948 kuwa Sai sir John Stuart MacPherson ya amshi mulki, wanda ya mukki kasar har izuwa shekara ta 1955. Shima dai ya sabunta kundin tsarin mulki wanda aka sawa suna 'MacPherson constitution'. Koda yake, ance tsarin mulkin baiyiwa wasu dadi ba, hakan yasa Jam'iyyar NCNC ta tattara kudade daga hannun 'yan kasa ta tura ingila akayi kara, daga bisani ingila ta soke kundin. Sannan yayi sassauci wajen sauya sunan wasu yankuna da kadarorin gwamnati daga sunayen da turawa suka sanya wanda yafi musu dadi, izuwa sunayen da yarukan wurin suka fi ganewa. Abinda a turance ake kira 'Africanization'.
Sir James Wilson shine Gwamna janar na karshe a tarihin mulkin mallaka a Nigeria. Ya soma mulki ne a ranar 15 ga watan yuni na shekarar 1955, sannan ya mika mulki a hannun Mr. Nmandi Azikwe, wanda yake shine bakar fata na farko dan Nigeria, daya fara mulkin kasar, a ranar 16 ga watan nuwamba na shekarar 1960.
An ce Sir Robertson bayan komawar sa gida, ya shiga damuwa da takaici bisa yadda 'yan afirka suka rushe duk wani asasin gina kasa da turawa suka kafa musu a iya zaman su a kasashen Afirka suka shiga yake-yake da juna tare da neman yancin kai a tsakanin su. Ya fadi hakan karara a littafin sa mai suna 'Africa in Transition: From direct rule to Independence, wanda aka buga a shekarar 1974. ya kuma fadi cewar 'yan afirka sunyi kusskuren neman 'yanci tun da farko, domin abinda suka sani yanzu (na yake-yake da almundahna) basu sanshiba a baya, shiyasa tun a lokacin suka rinka matsa lambar korar turawa tare da karbar yancin kai, shiyasa kuma muka yanke shawarar basu abinda suke so..
Wannan dai shine takaitaccen zance game da Shugabannin mulkin mallaka a Nigeria.
Da fatan Allah ya albarkaci wannan kasa tamu da zaman lafiya da kuma yalwar arziki. Amin
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
08060869978
Share:

TARIHIN JARUMA JHANVI KAPOOR


_*Tarihin jarumai*_ 


*Takaitaccen tarihin jaruma jhanvi kapoor* 

               _Tare dani_ 

 _*ibrahim so dole Sasha bhai Singh*_ 

An haifi jaruma jhanvi kapoor a 7 march 1997 a Maharashtra dake Mumbai ta kasar india.

Sunan mahaifinta boney kapoor kapoor Wanda ya kasance mai daukar nauyin fina-finai( producer ) ne na masana'antar film ta kasar india wato Bollywood . Sunan mahaifiyarta srivedi wadda itama ta kasance jaruma a masana'antar ta Bollywood .

Kuma ta kasance daliba a makarantar Dharubhai Ambani international school ta garin Mumbai na kasar india. Bayan ta gama ta tafi Lee strasberg Theatre and film Institu Los Angeles, USA domin koyar kafce. Physical Appearance. Jaruma ta fara fitowa a cikin film mai taken Dhadak da akayi shi a shekarar 2018 wacce itace ta fito a matsayin jaruma a cikin film din. Kuma film din anyishine kan soyayya kuma tafito ne tare da mashin jarumin nan kuma kani ga jarumi ( shahid kapoor ) wato ishat kattar, film din anyishine a yaren Hindu kuma mai-maici ne na wani film da akayi shi a shekarar 2016 Marathi film sairat . kuma film din ya kasuwancinsa na worldwide ya karbi kudi kimanin dalar amura 1.1 billion.

A fannin bayanan halitta kamar yadda masana suka bayyana jarumar ta kasance tana da nauyin 50 kg . kuma idonta ya kasance ruwan kasa mai dubu wato ( dark Brown ) kamar yadda masana suka bayyana . kuma kalar gashin yakasance baki ( black ) jarumar yakasance tana yawan ziyartar wajan motsa jiki na gym .

 *A bangaren dangan taka da wanana jarumar take dashi da mutane daban-daban kamar haka :-*

Jaruma jhanvi kapoor ta fito daga Ahalin Hindu Punjabi khatri da suke a Maharashtra Mumbai na kasar india. Jarumar tana da yar'uwa maisuna khushi kapoor . kuma ta yan'uwa kamar haka :- 
Arjun kapoor half-brother da Anshula kapoor half-siblings.
   Jaruma jhanvi kapoor tana da saurayi mai suna Shikhar pahariya da kuma Akshat Rajan sannan sai jarumi ishan kattar Wanda sukafito a cikin film din ta na farko wato Dhadak.

 *Acikin abubuwan da jarumar takeso da wadanda bataso sune kamar haka:-* 

 _A bangaren abinci_.. 
 _Jarumar tanason cin Muttom da abincin Rajastani cuisines , da kuma Italian dishes.


 _A bangaren jaruman da take so, duk da jarumar ta kasance matashiya dole zakuga tanason jarumar da dama a masana'antar ta Bollywood sune kamar haka_ :-_

 _Ga jerin jaruman da jarumar takeso kuma takes on kallon fina-finasu_ :- 

Dilip kumar , salman khan, shahid kapoor, madhubala, waheeda Rahman, nutun, and kareena kapoor khan.

 *A bangaren fina-finan da jarumar take so sune kamar haka* :-

Dilwale dulhaniye le jayenge, Hum dil de chuke sanam . wadanann sune films din da jarumar takeso.

Jarumar fashion designer din da takeso shine manish malhotra. Facts 

Film dinta na farko shine Dhadak da tayishi a 2018 kuma sun fito a tare da ishan kattar Wanda kanine ga jarumi _shahid kapoor_ .

 *Jerin fina-finan jarumar da zasu fita anan gaba.*

 _Gunjan sexena dazai fita a shekarar 2020._

 _Roohi Afza dazai fita a shekarar 2020_ 

 _Ghost stories dazai fita a shekarar 2020._

 _Dostana 2 dazai fita a shekara 2020_

 _*Wadanan sune jerin fina-finan jarumar dazasu fita .*_


 *A bangaren shafukanta na sada zumunta* .

Jhanvi Kapoor (@janhvikapoorr) | Twitter
https://twitter.com › janhvikapoorrJanhvi Kapoor (@janhvikapoor) • Instagram photos and videos
https://www.instagram.com › janhvikapoor


Janhvi Kapoor - Home | Facebook
https://m.facebook.com › ... › Actor
Janhvi Kapoor. 241K likes. Janhvi Kapoor is the daughter of Sridevi, an ageless diva of Indian Cinema. She is the elder daughteSfans_

*Takaitaccen tarihin jarumai ....*_ 


 *Duka-duka anan ne na takaita wannan kafce na tarihin jarumai ...•.......* 

 _*Jinjina ga duk kanin mutanen da suke karfafa mana gwiwa da groups-groups*_ 


 ****🇳🇬 *Sasha bhai singh* 🇮🇳*** 

 *🇳🇬🇳🇬MJL fina-finan india 🇮🇳 🇮🇳* 

 *🇳🇬 muleka india 🇮🇳* 

 *🇮🇳 Indian wale fans of 9ja 🇳🇬* 

 *🇮🇳Bollywood fans 🇮* 🇳

 *🇮🇳🇳🇬Taskar Bollywood Aminchi radio 103.9 fm📻* 

 *🎧Atif aslam of fans 👨‍🎤* 

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••>>
 *Www.Sasha bhai singh.com/facebook* 

 *Www.Sasha bhai Singh.com/Instagram* 

 *Whatsapp.09072875288* 

 *Call :- 07030308254* 

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<
Share:

LABARI NA GASKIYA DANGANE DA KWAZAZZABON 'YAR KWANDO

Labari na gaskiya dangane da Kwazazzabon 'Yar Kwando da kuma saukar Shehu Mujaddadi a K'asar Dugabau.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Hakika Labarin da ake fada dangane da kwazazzabon 'yar kwando gaskiya ne. Ita 'yar kwandon ai aljana ce, watakila tana cikin jinsin fararen aljannu don kuwa bamu samu labarin wani data tab'a cutarwa ba.
Amma dai mutanen Dugabau dake k'asar Kabo ta jihar Kano sun bada shaidar cewa ana yawan had'uwa da Aljanna 'yarkwando a daf da wannan kwazazzabon.
Akwai wanda yace min takan fito da sigar tsohuwa ko Budurwa, har ma zata iya neman wani taimako daga gareka, ko kaganta tana wani uzuri nata, amma dai ba zata yarda kaga fuskar taba.
Ance ta tab'a fitowa wani mutum a siffar tsohuwa, sai tace masa ya taimaka ya tsallakar da ita ta haye ruwa, amma sai mutumin yak'I. Juyawar da zaiyi sai hangota yayi kanta a cikin ruwa, k'afufuwanta suna kad'awa a sama, a haka ta tsallake ruwan.
Wani mutum kuma mai noman rani a daf da wannan kwazazzabo ya shaida min cewa suna yawan ganin abubuwan mamaki dangane da aljanna 'yarkwando. Har yace min ba'a yi musu satar amfanin gona, domin kuwa ita aljanar ke musu gadi, sannan kuma yace gidan ta yana kusa da wani k'aton rimi da aka sare acan kan tudu idan an haye ruwa, ragowar surkukin kuma na d'auke ne da gidajen 'ya'yanta.
Shidai wannan kwazazzabo da ake kira 'kwazazzabon 'yarkwando' a kusa da garin Dugabau din yake, waje ne mai girman gaske dake hayin k'orama, yana da tarihi kuma, domin kuwa anan ne akace Shehu Usmanu Bn Fodio (Allah yajikan sa da rahama) ya taba sauka a sa'ar da yake yak'in Jihadi a k'asar hausa (wajajen 1804).
Marubuci Ibrahim Bala Gwarzo ya ruwaito a littafinsa 'Mazan kwarai' cewa a wannan wuri mai suna kwazazzabon Yarkwando Shehu Usmanu ya sauka ya huta ya kuma k'ara k'arfin rundunar sa. Daga nan ya afkawa masarautar Karaye da yak'i, sannan ya afkawa birnin kano.
Tarihi ya tabbatar mana da cewa Shehu Usmanu Danfodio ya sauka a wannan yanki na Dugabau, tunda akwai masallacin da shehun ya bud'e wanda akace wani mutum mai suna Isyaka ne ya gina shi acikin garin na Dugabau. Kuma sama da shekaru d'ari da tamanin, wannan masallaci ne babba a yankin, saboda an gina shi ya ginu, an kuma k'awata shi da ado dai-dai da wayewar maginan k'asa na wancan zamani.
Na tambayi wani Tsoho akan ko zamu samu wata shaida takamaimiya kamar misalin Littafi Alkur'ani maigirma, takobi ko wani abu wanda ya fito daga shehu mujaddadi a halin saukar sa a wannan yanki wanda kuma zai k'ara tabbatar mana da cewa shehu usmanu ya sauka a wannan guri?.. Sai dai hakan bai samu ba, watakila saboda jimawar zamani ko kuma gushewar Dattijan da suka kiyaye ainihin abinda ya faru a wancan zamanin gwargwadon yadda suka samu labari, amma dai ya tabbatar min da ingancin wannan labari, ya kuma k'aramin da cewa akwai wata Katuwar kuka mai suna 'JARMA' (wadda a yanzu ta fadi da kanta) dake daura da kwazazzabon 'yarkwando, itama ada can jarumai da sarakunan kasar Katsina na sauka a wurinta kafin su riski birnin Kano don kai harin yak'i ko aiwatar da wata buk'ata tasu.
Shikuwa kwazazzabon 'yarkwando, watakila k'oramar dake gudana adaf dashi ke jan ra'ayin matafiya masu shigewa daga k'asar katsina, sokoto da sauran wurare su yada zango a wajen. Tunda wani tsoho ya k'ara min da cewa ada, wajen mad'eba ce, watau ya tab'a zamowa dandali wanda masu sana'ar Su suka kakkafa rumfuna suke kuma dururuwar zuwa don kamun kifi.
Zuwa yanzu dai, Bamu san alak'ar wannan aljana da wadancan matafiya ba, ma'ana, tun a wancan zamanin an san da ita ko kuwa daga baya ne labarinta ya fito?, sannan idan akwaita wanne taimako ko akasarin haka ta basu?, to amma dai ko yanzu mun kara sanin d'aya daga manyan hanyoyin da matafiya kebi daga kano zuwa katsina ko Sokoto ada. Don haka munayiwa Allah godiya domin kuwa hakika ko yanzu mun k'ara Sani..
# SadiqTukurGwarzo


Share:

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive