Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

Showing posts with label Taskar Haiman (Haiman's Archive). Show all posts
Showing posts with label Taskar Haiman (Haiman's Archive). Show all posts

WANI SHASHANCI


WANI SHASHANCI DA MUTANEN YANKIN IFRIKIYA SUKA MAIDA SHI BA KOMAI BA:

Idan ɗan ƙasar Faransa bai iya turanci ba, 'yan Afirka sai su girmama shi. 

Idan ɗan Sipaniya bai iya turanci ba, 'yan Afirka sai su girmama shi. 

Yayinda ɗan ƙasar Sin ya zamana bai iya turanci ba, shi ma sai 'yan Afirka su girmama shi. 

Idan ɗan ƙasar Rasha bai iya turanci ba, sai 'yan Afirka su girmama shi. 

Kai ɗan kowace ƙasa daga cikin ƙasashen turai in bai iya turanci ba 'yan Afirka girmama shi suke yi. 

Amma idan ɗan uwansu ɗan Afirka ya zama bai iya turanci ba, sai su maida shi sakarai, daƙiƙi, jahili, soko kuma wawa. 

Wannan shi ne matakin shashanci mafi girma da muke fama da shi a matsayinmu na mutane. Muna amfani da iya turanci wajen gwada baiwa da karamar mutanenmu, har ma da yara ƙanana. 

A makarantunmu, ana sa yara su ji cewa su banzaye ne kuma wawayen da basu da amfani kawai saboda ba su iya magana da harshen da ba su tashi da shi ba a yankunansu. 

Ya ku 'yan Afirka, mu daƙile wannan mummunar ɗabi'ar daga yaɗuwa a ƙwaƙwalenmu da kuma al'ummarmu. Mu koyar da yaranmu harshensu na gado kuma mu bar sauran jama'ar da ke zagaye damu su yi magana da harsunansu cikin 'yanci da aminci ba tare da tsangwama ba. 

Kada mu bawa azzalumai gudunmuwa wajen aikata zalunci akan 'yan uwanmu. 

Idan har ka amfana da wannan saƙo, kana iya turawa wasu domin su amfana, amma a tunanina kowa daga cikin jama'armu yana buƙatar ya ji wannan maganar. 

Na barku lafiya. 


Mu so junanmu, domin junanmu. 

Kyakkywan tunani, kyakkywar rayuwa. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

WAƘAR ZAIDU IBRAHIM BARMO

ZAIDU IBRAHIM BARMO

Da sunan Rabbana zan fara waƙar Zaidu
Kogin maliya babu mai ganin ƙarshenka. 

Ɗa wurin Ibrahima na layin su Sa'idu
Gwarzonmu a yau muna maka sam-barka. 

Tsira gurin manzonmu wanda ya hana daudu
Kuma shi yazo da sallah yace kar mu yi shirka. 

Kun san mata su ke amfani da tandu
Shi ɗan jibiyawa ko sai dai waraƙa 

In ko rubutu kake so ka je gun Zaidu
Ko ma ba ka iya ba to za ya koya maka. 

Ƙimarsa ta zarce arewa har ta je ga kudu
Watarana duniya ƙwarai za ta yabe ka. 

Maƙiyanka da sun gane ka sai dai su gudu
Murhu da garwashi to wai wa zai taka? 

Masu yi maka hassada suna ruwa kai ko a tudu
Ka yi musu nisa babu mai iya kamo ka. 

Allah kare ka alfarmar Mahamudu 
Ya sa ka zamo a saman maƙiyanka. 

Ana maganar buhu wa ke zancen mudu? 
Kai me gayyar tsiya tafi abinka. 

Ka taka ka rausaya malam Zaidu
A MZM mun sani fa sam ba tamkarka

Allahu ya kiyasheka kamun gafiyar ɓaidu
Ya sa ka zamo cikin ni'ima a kabarinka.

Amin.

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
  08185819176 
Haimanraees@gmail.com

Share:

SHIN NAWA NE KOFIN ƘIYAYYA?

SHIN NAWA NE TSADAR KOFIN ƘIYAYYA? 

Ban taɓa sanin cewa haka yake da tsada ba. Ina so ne in san tsadar ƙiyayya, don haka sai na sauka a wani shagon da ake siyarwa. A matsayinsa na nagartaccen ɗan kasuwa wanda ke neman kwastoma, nan da nan sai mai shagon ya rugo wajena domin jin ko me nake so. Sai na ce masa kofi ɗaya kawai nake so na ƙiyayya, daga nan sai ya yi murmushi kuma ya tambaye ni ko zan iya siya?

 'Shin nawa ne tsadar kofin ƙiyayya? Na tambaye shi. Hmmmmm! Ya kawo wani gwauron numfashi ya sauke sannan ya fara: 

 👉🏼 Da farko dai za ta ɗauke maka duk wata nutsuwa da ke tare da kai. 

 👉🏼 Za ta haifar maka da damuwa iri-iri kuma marasa magani.

 👉🏼 Za ta cinye zuciyarka. 

 👉🏼 Za ka faɗa cikin ƙunci a duk lokacin da ka ga wanda kake ƙin. 

 👉🏼 A duk lokacin da mutane ke taya shi murnar wani abu, kai kuma za ka fara duban dalilan da suka sa kake ganin bai cancanci wannan abun ba. 

 👉🏼 Zai zamana ka suƙe kuma ka gaji da ganin wannan mutumin. 

 👉🏼 A duk lokacin da ya yi dariya kai kuma sai ka yi kuka. 

 👉🏼 A lokacin da mutane ke ƙoƙarin gina rayuwarsu, kai kuma za ka zama kana ta gina masa ramin mugunta ne domin ka kada shi. 

 👉🏼 Tsoron Allah da imani da shi za su fita daga zuciyarka sannan za ka zama dandamalin da shaiɗanu za su dinga taruwa. 

 👉🏼 Za ka fara fuskantar matsalolin lafiya irin su Hawan Jini, ciwon sikari, shanyewar ɓarin jiki, cutar daji, cutar hanta, cutar ƙoda da dai sauransu. Matuƙar dai ka sha daga kofin ƙiyayya to baƙin ciki, riƙo a zuci, rashin yafiya, gaba, fushi, kishi, ƙiyayya da makamantansu duk za su bika. Abu mafi hatsari shi ne babu wani magani da za ka siya ka sha da zai magance maka wannan cutar. 

 👉🏼 Za ka kashe kanka tun gabanin lokacinka ya yi. 

Mai shagon ya ci gaba da zayyano min irin abubuwan da kofi ɗaya na ƙiyayya zai iya ja min in rasa har dai na ce ya dakata haka nan, saboda na fahimci cewa kofin yana da matuƙar TSADA. Na ƙi yarda in biya wannan kofi da tsada haka alhalin ina iya nuna soyayya cikin sauƙi kuma da arha.

Ya ku 'yan uwa, kada ku yarda wani ya ƙwace muku farincikinku ta hanyar siyar ko baku ƙiyayya ku amsa. Ku ƙauracewa gulma, ƙiyayya, fushi da sauransu saboda a mafi yawancin lokuta, abin da ka ji dangane da wani ne ke haifar da ƙiyayya. Kada ka kashe kanka kafin lokacinka ya yi. 


Mu so junanmu, domin junanmu. 

Kyakkywan tunani, kyakkywar rayuwa. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

KAICO!


Kaico!

Bissmillah da sunan ilahi
Wanda ya aiko ɗan Abdullahi
Zan yi batu da tambihi
Bani dama sarkina ilahi.

Mu yaran zamani yau
Ba mu magana ayau
Iyaye na ta fama
Mu kuma muna ta fankama.

Ba mu tsoron ɓaci na ransu
Ba mu yin ladabi garesu
Ba ma biyayya garesu
Amma in buƙata ta tashi mu je wurinsu.

Ra'ayinmu kawai muke bi
Ko mara kyau ne shi za mu bi
Ra'ayinsu ko ba mu bi
Ko da mai kyau ne ba mu bi.

A hakan muke so wai mu ci gaba 
Alhali da uwarmu muke gaba 
Mun ce mu ne za mu shige gaba 
Wai shugabancin ya fi ƙarfin uba. 

To ta yaya ma zamu haske? 
Bayan albarkar mun make? 
Mun aje uwarmu a gefe 
Mun ɓoye ubanmu a shinge. 

Kaico! Wannan lamari da gyara 
Shi ya sa ma har na ɓara 
Ku ka ji ni ina ta ƙara 
Sai ka ce wanda sago ya sara. 

To wallahi mu yi hankali
An ce duniya ɗamarar jangali
Dole sai an bi ta a hankali
Ko kuma mu faɗa baƙin hali.

Allah ka ƙara wa iyaye lafiya
Ka sa mu gama da su lafiya
Mu zamo masu ƙaunar tarbiya
Ga manyanmu mu zam masu biyayya.

Sarki ka shiryar da mu 
Da abokai da ahalinmu 
Da dukkan 'yan danginmu 
Ka sa shiriya a zukatanmu. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

WASU SHAWARWARI DA ZA A IYA BI WAJEN DASAWA YARA KYAWAWAN ƊABI'U


WASU SHAWARWARI DA ZA A IYA BI WAJEN DASAWA YARA KYAWAWAN ƊABI'U. 


1. A yayin da kuka shigo gida, ku gaishe da su ko ma ku rungume su. Hakan zai gina soyayya da darajawa a zukatansu.

2. Ku yi kyakkywar mu'amala da maƙwabtanku kuma kada ku yi munafunci. Kada ku dinga faɗan aibun wasu mutane da kuka haɗu da su kamar direbobi da ma'aikatan kan hanya a gaban su. Saboda yaran nan suna saurare, za su ɗauka kuma za su kwaikwaya. 

3. A duk lokacin da kuka kira mahaifanku, ku ƙarfafawa yaranku gwiwa su ma su yi magana da su. A duk lokacin da za ku kai ziyara gare su, ku tabbata kun je da yaran kuma ku mutunta su a gaban yaran. Saboda irin yadda suka ga kuna girmama iyayenku su ma haka za su girmama ku ko su kula da ku. 

4. Idan za ku kai su makaranta, kada ku kunna musu waƙoƙi ko kaɗe-kaɗe, a madadin hakan, ku basu gajerun labarai masu ƙarfafa gwiwa hakan yana da matuƙar muhimmanci a gare su- Ku yarda da ni! 

5. Ku dinga yi musu tatsuniyoyi, ƙissoshi da tarihin magabata ko kuma karanta musu ko da hadisi guda ɗaya ne a kowace rana. Ba wani lokaci mai tsawo hakan zai ɗauka ba, amma yana da muhimmanci wajen ƙara kusanci da kuma ƙirƙiran tarihin da za a dinga tunawa a tsakanin juna. 

6. Ku gyara gashi, ku wanke haƙora kuma ku sa kaya masu kyau ko da kuwa za ku zauna a gida ne. Saboda yara suna buƙatar su fahimci cewa yin tsafta da shiga ta kamala ba wai kawai sai za a je unguwa ake yi ba. 

7. Kada ku zama masu zagi ko duka ko kuma ƙorafi akan duk wani laifi da yaranku suka yi. Ku zamo masu haƙuri da kauda kai a wasu abubuwan. Yin hakan zai taimaka sosai wajen gina musu ƙarfin gwiwa da kuma sanin ya kamata. 

8. Ku nemi izini kafin ku shiga ɗakinsu. Ba wai kawai ƙwanƙwasawa za ku yi ba, a'a ku nemi izini baki da baki su baku izinin shiga. Suma za su koyi yin hakan yayin shiga ɗakinku ko na wasu. 
 
9. Ku nemi gafara idan ku ka yi wa yaranku laifi, ba su haƙuri da neman gafararsu hanya ce mafi sauƙi ta koya musu bada haƙuri da neman yafiya idan suka yi wa wani ba daidai ba. Sannan hakan zai dasa musu nagarta a zukatansu. 

10. Kada ku zamo masu yawan zolaya ko ci wa yaranku fuska ko da da wasa ne akan wasu zantuka ko ɗabi'u ko mu'amala. Hakan na da ƙona rai, in kuna yi musu hakan, to za su taso da tsana da kuma jin haushinku. 

11. Lallai ne iyaye su zama masu ba wa sirrin 'ya'yansu muhimmanci sosai.

12. Kada ku yi tunanin za su fahimci ko kuma su ɗauki duk abin da kuka faɗa musu nan take, ku zamo masu haƙuri da naci akan abin da kuke koya musu. 

13. Ku dinga yin sallah da addu'o'i tare, ku koya musu yadda ake yi da kanku. 

14. Bayan sallar Asubahi, ku zauna da su ku tambaye su irin abubuwan da suke sa ran yi a wannan yinin. Yaran da ba su da jadawalin abubuwan da za su aikata a kowane yini tabbas za su je su taimaka wa wasu wajen gudanar da nasu aikin ko ba mai kyau bane. Sannan hakan zai taimaka wajen koya musu tsara hanyar gudanar da rayuwarsu. 

15. Ku yawaita rungumar 'ya'yanku, ku yawaita yi musu addu'a da sa musu albarka a kowace safiya. Hakan na gadar da so da ƙauna tare da gadar da albarka a cikin wannan ahalin. 

Ku tuna, wasu iyayen na buƙatar jin irin waɗannan shawarwari, don haka babu laifi don kun tura musu. 

Mu so junanmu, domin junanmu. 

Kyakkywan tunani, kyakkywar rayuwa. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

KUKAN KURCIYA

KUKAN KURCIYA

Da sunan sarkina zan fara
Wannan da shi ne ya yiwo fara
Ya yi kare kana ya yo kura
Ya yi ruwa kuma kana ya yo ƙura
Hikimar Allah sam ba ta da iyaka.

Tsira da aminci gun baban Zahra 
Wannan da cikin annabawa ya yo zarra
Wanda duk wata daraja tuni ya tara
Sahabbai da alaihi duka na tara
Salati gare sa na ke furtawa babu iyaka.

Wai mu yaushe ne za ko mu hankalta
Mu zam nutsuwa da neman mafita
A wayi gari junanmu za mu fifita
Ai ya fi ace kawunanmu muka fifita
Ko ba komai hakan ai zai fishe ka.

Mu kawunanmu kawai muke hange
Ba mu duban wanda yake a jikin shinge
Na ƙoluwa kawai muke hange
Taddo shi kawai muka daddage
Kai mai dogon buri kam kaiconka.

Ƙaddara dai kowa da akwai ta sa
Riga ce da babu mai cire ta sa
Da zamu gane mu daina sa-in-sa
Akan abin da zai zo ne komai nisa
In kuma munƙi za mu wahalta kamar wanda ya sha molanka.

Allah ka tsare mu da na shina
Ka sa mu zamo masu yin murna
Da Duk abin da ka tsara mana
Alfarmar annabinka mijin Nana
Ka sa kar mu zamu cikin masu yin shirka.

Jamilu ne ke waƙar daga nan gefen
Domin isar da saƙo ga 'yan can gefen
Fatana kowa ko ya amfana
Da ɗan abinda na samu a karatuna
Wannan ita ce riba da ba ta da iyaka.

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
  08185819176 
Haimanraees@gmail.com

Share:

RASHIN KUNYA KO ƘARANCIN TAUHIDI?


RASHIN KUNYA KO KARANCIN TAUHIDI???

Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuhu, Barkan mu da warhaka ya 'yan uwa musulmai. Hakika Nazari yana daya daga cikin hanyoyin da akan bi domin samun ilimi kuma a isar dashi. 

A yau ina so ne in yi tsokaci akan wani al'amari wanda ya dade yana ci min tuwo a kwarya. A wannan zamani da muke ciki akwai abubuwa ko kuma ince dabi"u da dama wadanda ake yi da sam basu dace ace musulmai suna yinsu ba, amma kuma anayi, kuma sam ba'a maida hankali kansu ba. Daya daga cikin irin wadan nan dabi'u ne nake so inyi tsokaci akai. Ayau, mafi yawanci matasan mu idan zasu masallaci domin gabatar da Sallah basa tsaftace jikinsu yadda ya kamata, wasu ma basa tsayawa su yi al'walar yadda ya kamata, wani ma
da ya dawo daga wurin aiki dagaje dagaje kawai zai yi alwala bur-bur yaje ya shiga masallaci mutane suna kyamar hada sahu da shi. Wani ma sam baya kula da jikinsa da zaku hada sahu da shi, kai kadai zaka san me kaji saboda warin hammata, warin rana da makamantan su. Amma idan zaice wurin budurwarsa ne tadi ko hira ko zance. Sai kaga yayi wanka, yayi wanki yayi guga an fesa turare an ci gayu. To shin don Allah me ya sa muka fi baiwa 'yan matanmu muhimmanci ta fannin tsafta fiye da wurin ibadar ?? Shin ashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa sallam bai hore mu da yin tsafta a koda yaushe ba? Shin baka.tunanin zaka iya daukar alhakin wadan da zaka hada sahun sallar dasu?? shin kana nufin ita budurwar taka ta fi masallacin muhimman ci ne? Shin Rashin Kunya ne yasa bama tsaftace jikin mu yayin zuwa masallaci amma mun iya cancarewa yayin zuwa tadi ko kuma karancin imani ne? Ya Allah ka bamu ikon yi maka cikakkiyar biyayya ba tare da nuna gajiyawa ba. Ya Allah ka bamu ikon yiwa junan mu adalci. Ya Allah ka sa mu dace kuma ka azurta mu da kyakkyawar fahimta Ameen.


Share:

TAYA KAI MURNA


TAYA KAI MURNA

Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu. 'Yan uwana Makafta kamar yadda kuka sani cewa na saba antayo kafcaccaki iri daban daban a kuma lokuta Mabanbanta, yau kam ba sabon Kafce na kawo muku ba, wannan maƙala ce kawai na yi domin in taya kaina murnar Fassara waƙoƙin Fina Finan India har guda ɗari. Na san ba lallai bane ku ku ga girman abin ko muhimmancinsa, amma a wajena, hakan babban al'amari ne. Hakan yasa nake gayar farinciki a wannan rana, ga jerin waƙoƙin da na fassara nan zan antayo muku. Fatan zaku faɗa min wacce tafi muku daɗi da kuma wacce kuke muradin in fassara muku, hallau kuma dai. Ƙofofin shawari da ƙorafi a buɗe suke. Nagode.

 1. Aaraha Hoon Palatke
 2. Hawayein
 3. Jeene Laga Hoon
 4. Jeena Jeena
 5. Zinda
 6. Mere Humsafar
 7. Suraj Hua Maddham
 8. Tum Hi Ho
 9. Saari Saari Raat
10. Jiya
11. Baaton Ko Teri
12. Saware
13. Jeete Hain Chal
14. Hasi Bangaye
15. Bande Hain Hum Uske
16. Selfie Lelere
17. Tu Milade
18. Teri Khushboo
19. Baatein Yeh Kabhina
20. O Zaalima
21. Sanam Re
22. Sanam Teri Kasam (Title Track) 
23. Dil Na Diya
24. Kal Ho Na Ho (Title Track) 
25. Ajab Si
26. Tehra Chehra
27. Kheech Meri Photo
28. Mere Naam Tu
29. Dangal Dangal 
30. Chakde India (Title Track) 
31. Chicken Kuk-doo-koo
32. Love You Zindagi
33. Alizeh
34. Kamli
35. Tu Chahiye
36. Agar Tum Saath Ho
37. O Saathi
38. Aankhein Khuli
39. Manwa Lage
40. Main Qaidi Number 796
41. Zinda Hai
42. Panchadara Bomma Bomma
43. Guzaarish
44. Ishaara
45. Tu Hi Junoon
46. Dil Tu Hi Bataa
47. Teri Mitti
48. Rang Laal
49. Ranga Ranga Rangasthalana
50. Saanson Ki Mala
51. Prem Ratan Dhan Payo (Title Track) 
52. Dil Diyan Gallan
53. Jaadu Teri Nazar
54. Bhar Do Jholi Meri
55. Bombay Talkies (Title Track) 
56. Kabhi Jo Badal Barse 
57. Slow Motion
58. Tujhe Kitna Chahne Lage
59. Agar Main Ka Hoon
60. Bhula Dena
61. Main Yahan Hoon
62. Main Hoon Hero Tera
63. Jabra Fan
64. Meri Aashiqui
65. Piya Aaye Na
66. Enu Naam Che Raees
67. Laila Main Laila
68. Sanson Ke
69. Bewaja
70. Aasan Nahi Yahan
71. Dhingana
72. Jab Tak Hai Jaan (Poem)
73. Gerua
74. Jeeva Nadhi
75. Janam Janam
76. God Allah Aur Bhagwan
77. Selfish
78. Yeh Fitoor Mera
79. Pehla Pyaar
80. O Khuda
81. Dil Cheez Tujhe Dedi
82. Dhoom Dhaam
83. Badla (Title Song)
84. Sun Saathiya
85. Ek Number
86. Sardar Gabbar Singh
87. Jalte Diye
88. Kaho Naa Pyar Hai (Title Track) 
89. Jaaneman Jaaneman
90. Teri Meri Kahani
91. Ae Dil Hai Mushkil (Title Track)
92. Tujhe Kitna Chahein Aur
93. Sun Raha hai na tu (Female)
94. Milne Hai Mujhse Aayi
95. Tu Hai Ki Nahi
96. Aye Khuda
97. Dandalayya
98. Kya Khoya
99. Jashn-e-ishqa
100. Adhuri Zindagi 

<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring
Share:

SAƘO NA MUSAMMAN ZUWA GA MASOYAN JARUMI SALMAN

SAƘO NA MUSAMMAN ZUWA GA MASOYAN JARUMI SALMAN KHAN

Bismillahir Rahmanir Raheem.

Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu.

Ƴan Uwana Masoyan Jarumi Salman Khan ina muku Barka da warhaka, tare da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya.

A cikin ƴan kwanaki huɗu zuwa huɗu da suka gabata na fuskanci cewa taƙaddama ta ɓalle a tsakanin ku dangane da cewa SHIN SALMAN KHAN YA TAƁA YIN SUMBA A CIKIN FIM?, abin da ya jawo cece kuce sosai inda wani ɓangare mafi girma na Masoyansa suke ƙaryata cewa bai taɓa yi ba, Yayinda wasu ƴan tsiraru su kuma suka dage akan cewa ya taɓa yi ko yana yi da dai Makamantan su. To, a zahiri dai wannan taƙaddamar cikin gida ce, kuma bai kamata in shiga ba kamar yadda kuma bai kamata in koma gefe in yi dariya ba, domin teburin babu ta yadda baya iya juyawa sai dai in Allaah ne bai nufa ba.
Don haka sai na yanke shawarar yin amfani da matsyina na Maƙwabci domin na aiko da wannan saƙon a matsayin shawara ba umurni ba. Domin kuwa bani da iko akan kowa daga cikin ku, kuma yana daga cikin haƙƙin Maƙwabtaka dama in kaga abinda zai cutar da Maƙwafcinka to kayi iya ƙoƙarin ka wajen ganin ka tseratar da shi daga wannan abin cutarwar. Kuma wannan abun ka iya janyo muku zolaya, zargi da kuma zagi daga waɗanda basu san me ake nufi da soyayyar Jarumi ba. 

Dangane da wannan taƙaddama da ake ta yi wadda kowane ɓangare sun kawo hujjoji tare da ƙalubalantar juna da dai sauran abubuwan da suka wakana. Ni ina ganin kamar ita Kalmar Sumba (watau Kiss) ɗin ce ba'a Fahimce ta ba a matakin farko. Ni a tunanina, da za'a fahimci Ma'anar kalmar da kyau, to da komai zai zo da sauƙi domin daga nan babu buƙatar a ja magana indai ba dama da wata Manufa ake yi ba. Hakan yasa na yanke shawarar aiko muku da taƙaitaccen bayani dangane da wannan Maudu'i tare da fatan zai haskakawa waɗanda basu fahimta ba hanyar da waɗanda suka fahimtar suka bi domin su ma su fahimta.

   Menene Sumba (Kiss)?

Sumba shi ne taɓi wanda mutum kan yi da laɓɓansa zuwa ga wani mutum ko kuma wani abu. Sumba ya rabu izuwa kashe-kashe masu yawan gaske, kowanne kuma ya danganta ne da irin al'adun mutanen da ke yankin da wani kaso daga cikin kashe-karshen ya faɗa. 
Misali; a ɗabi'a irin ta Nasarawa, suriki ma kan iya sumbatar surikarsa a fili. Yayinda a wurin Hausawa kuwa, tun gabanin zuwan musulunci, mata da miji ma ba sa iya sumbatar juna su a bainar jama'a. Shi sumba yana aika saƙo ne zuwa ga wanda aka yiwa, kuma kamar yadda ya rabu kashi-kashi, haka ma saƙonnin suka rabu. Daga cikin saƙonnin da sumba ke aikawa akwai irin su So, Ƙauna, Sha'awa, Girmamawa, Gaisuwa, Abota/ƙawance d.s. 

Wani bincike da aka gudanar ya Sumba shi ne aiki na biyu da mutanen Amurka suka fi aikatawa a kullum bayan riƙe hannuwa kuma kaso 85% cikin ɗari na matasa masu shekaru 15 zuwa 16 sun taɓa yin sumba. Sai dai wasu kayan Adabi sun bayyana cewa har yanzu akwai mutane masu yawa waɗanda ba sa yin sumba sam a rayuwar su.

Taƙaitaccen Tarihin Sumba. 
 
Masana a Fannin ilimin halayyar Ɗan Adam sun kasu gida biyu dangane da asalin sumba. Wasu sun ce wai sumba Ɗabi'a ce da kan zo wa mutum a matsayin bazata ko kuma bisa niyya. Yayinda wasu kuma suka ce sumba ya samo asali ne daga ciyarwa irin wacce iyaye mata ke yiwa yaransu ta hanyar tauna abinci su basu ta baki. 
Masani a fannin ilimin halayyar Ɗan Adam kuma ƙwararre a Fannin ilimin sumba wato Vaughn Bryant yace bayanai mafiya daɗewa da aka fara samu dangane da sumba ko wani abu makamancin haka sun fito ne daga Vedas, wasu rubututtuka na Sanskrit waɗanda suke koyar da mabiya Addinin Hinduism, Buddhism da kuma Jainism kimanin shekaru 3,500 da suka gabata. 

Haka kuma an samu sunan leɓe da sumba a cikin tsofaffin rubutattun waƙoƙin Sumeria. Sannan masu bincike a fannin kayan tarihi sun tabbatar da samuwar bayanai da suka bayyana sumba a cikin kayan tarihin da suka haƙo a birnin Misra (Egypt 🇪🇬) . 
Hallau kuma dai an samu wasu muhimman bayanai da suka danganci sumba a cikin Labaran almara na Hindu wato Mahabharata.
Masana waɗanda suka karanci ilimin sumba sun ce yin sumba ya samu haɓaka sosai a duniya tun bayan da Alexander the Great tare da mayaƙansa suka yaƙi wani ɓangare na Punjab da ke arewacin India a 326 BC.

Rumawa (Romans) sun taimaka Matuƙa wajen yaɗa ɗabi'ar sumba a yankunan Yuropiya da kuma arewacin Ifrikiya. Rumawa saboda son yin sumba da suke yi yasa har tattaunawa suke yi dangane da ire-iren sumba a bainar jama'a. Sumba irin wanda ake yi a hannu ko a kumatu shi suke kira da osculum. Wanda ake yi da baki kuma amma laɓɓa a rufe shi suke kira da basium, shi wannan a tsakanin ƴan uwa ake yinsa. Shi kuma Sumbar soyayya shi ake kira da suavium.
An fara karantar Sumba a matsayin gurbin karatu mai zaman kansa ne a cikin ƙarni na goma sha tara, kuma sunan da ake kiran wannan karatu shi ne philematology. Mutane da yawa sun yi karatu a wannan fage, fitattu daga cikin waɗanda suka yi wannan karatu sun haɗa da Cesare Lombroso, Ernest Crawley, Charles Darwin, Edward Burnett Tylor da Elaine Hatfield. 

Rabe-Raben Sumba 
 
Fitaccen masanin sumba wato Kristoffer Nyrop ya bayyana cewa sumba ya kasu izuwa kashi daban-daban. Daga cikin su akwai Sumbar soyayya, Sumbar ƙauna, Sumbar abota, Sumbar girmamawa, Sumbar lumana d.s 
Sai dai kuma yace, rabe-raben sumba yana banbanta daga wuri zuwa wuri dangane da irin al’adun mutanen wurin, hakan yasa na wasu ya fi na wasu yawa. Misali, Faransawa suna da rabe-raben sumba har kashi 20 Yayinda Jamusawa su kuma suke da 30.

* Sumbar Soyayya. 

Duk da cewa sumbatar laɓɓan juna a tsakanin mutane biyu ya riga ya zama ruwan dare a wannan zamani a matsayin alama ta soyayya ko ƙauna, Al'ummomi da yawa basu san da wannan ɗabi'ar ba sai ta hanyar turawan Yuropiya. 
Shi Sumbar soyayya sumba ne wanda masoya suke yiwa junansu a duk lokacin da suka haɗu ko zasu rabu ko kuma lokaci bayan lokaci idan suna tare. Su kan yi Hakane kuma domin nunawa juna soyayyar da suke yiwa junansu. Shi irin wannan sumba akan yi shi baki da baki ne ba tare da Shamaki ba. 

* Sumbar Sha'awa. 

Wannan shi ne irin Sumbar da mutane suke yiwa junansu Yayinda sha'awar su ta motsa ko kuma domin motsa sha'awar. Banbancinsa da Sumbar soyayya shi ne, a mafi yawancin lokutta an fi daɗewa wajen yinsa, sannan an fi tsanantawa. 

* Sumbar Ƙauna 

Shi Sumbar ƙauna ya banbanta da na soyayya wanda masoya ne ke yiwa junansu. Shi wannan Sumbar duk da cewa masoya suna yiwa junansu irin sa, basa yi har sai soyayyarsu ta rikiɗe ta koma ƙauna. Misali ƙarara shi ne irin Sumbar da Mahaifa ke yiwa Ƴaƴansu. Banbancinsa da na soyayya ko sha'awa shi ne, ba'a yinsa don jin daɗi ko samun wata biyan buƙata, kawai ƙaunar ce ke gudana ta cikinsa. 

* Sumbar Abota ko Ƙawance 

Wannan sumba ne da abokai kan yi wa juna haka ma ƙawaye kan yiwa juna. Bugu da ƙari kuma, ahali biyu ma su kan yiwa juna irin sa. Shi wannan sumba yawanci a kumatu ake yinsa, duk da yake dai a kwai wasu yankuna da suke yin baki da baki. Akan yi shi ne domin nuna kulawa a tsakanin abokan ko ƙawayen. 

* Sumbar Girmamawa. 

Tarihi ya nuna cewa, tun tale-tale ana amfani da sumba a matsayin girmamawa ta hanyoyi da dama. Shi irin wannan sumba akan yi shi a ƙafa ko hannu ko a tufafin wanda ake girmamawa. 

* Sumbar da ta shafi Addini. 

Wanna sumba ita ce irin Sumbar da mabiyan addinai ke yiwa abubuwan da suka shafi harkar addinansu, ko kuma a wasu wuraren wa ababen bautar kai tsaye. Shi ma wannan kai tsaye ake ɗaura laɓɓa akan abinda ake sumbatar. 

* Sumbar Lumana ko zaman lafiya. 

Shi wannan Sumbar ana yin sa ne domin Samar da lumana a tsakanin mutane biyu ko tawaga biyu. A can dauri, Mayaƙa ma kan yi irinsa domin nuna tabbacin sulhu a tsakanin su. Hallau dai, sarakuna kan yi irin wannan sumba domin nuna aminci da juna kan zaman lafiya. A wasu wuraren ma shugaba kan tursasawa abokan hamayya sumbatar juna bayan ya shirya su. Shi irin wanna sumba ana yin sa ta leɓe da leɓe, ko a kumatu ko kuma a hannu. 

Ƙarin Bayani Dangane Da Sumba. 
 
Donald Richie ya bayyana cewa a Japan, kamar yadda yake a birnin Sin, sun ɗauki sumba a matsayin alama ce ta sha'awa kawai, kuma yin sa a fili rashin kunya ne. Abin har yayi tsamari ta yadda mutanen birnin Sin suna ɗaukar duk wacce take Sumbatar Namiji a fili kai tsaye a matsayin karuwa. 

A Rayuwar ƙasashen gabashin duniya ta yau, sumba ya danganta ne da irin wuri da kuma mutanen wurin. A yammacin yankin Asiya, sumbatar leɓe a tsakanin maza ko mata alama ce ta gaisuwa da girmamawa, amma a gabashi da kuma kudancin Asiyan, a tsakanin mata ne kawai ake yin hakan, maza basu cika yi ba. 

A Ƙasar Hausa kuwa, sumba a bainar jama'a an ɗauke ta ne a matsayin alama ta rashin Tarbiyya da nuna cewa mutum ya kai ƙololuwar ƙwarewa a rashin kunya. SUMBA A CIKIN FINA-FINAI 

Sumbar soyayya da ya fara bayyana a jikin majigi ya bayyana ne a cikin wani fim ɗin Amurka mara magana mai suna THE KISS a 1896. Sumbar da aka yi a cikin shirin ya ɗauki tsawon daƙiƙa talatin ne wanda hakan ya haifar da gagarumin cece-kuce tare da samun Zafafan kalamai daga masu kare Tarbiyya da ɗa'a na birnin New York. Wani daga cikin masu sharhin Fina-Finai na wancan lokacin ma dai cewa yayi: "wannan abun Allah wadai ne, irin wanda ya cancanci a kira wa ƴan sanda. 
Daga nan ne sai matasa dake kallon irin waɗannan Fina-Finan suka fara kwaikwayon Jaruman soyayya irin su Ronald Colman da Rudolph Valentino. Ƴan Fim mata da yawa a wancan loton sun zama Shahararrun Jarumai ne saboda iya nuna jin daɗin su yayin sumba a cikin Fina-Finai. Daga cikin su akwai Nazimova, Pola Negri, Vilma Bánky da kuma Greta Garbo. 

Sumba irin ta leɓe-da-leɓe ba'a fara yin ta ba a cikin Fina Finan Bollywood har sai zuwa ƙarshen 1990s duk kuwa da cewa ana sane da shi kuma an shirya wa Yinsa tun lokacin da aka kafa Bollywood. 
Wannan kuma ita ma magana ce mai zaman kanta tun da yake bayanai sun nuna cewa sumba ta bunƙasa kuma ta yaɗu ne sosai da sosai a India. Wataƙila hakan yasa tun da aka fara mutane suka amshi abin hannu biyu. Sumba mai tashi ita ce irin Sumbar da ake haurawa zuwa ga wanda ake so, irin wannan sumba ce aka fi yi a cikin Fina-Finan India na farko-farko, kuma har yanzu ana yin sa a cikin Fina Finai. 


A Fina-Finan Japan na farko-farko, nuna Sumba ko wani abu da ya shafi saduwa ko sha'awa abu ne da ke ƙunshe da Jimirɗa Matuƙa. A 1931, wani mai bada umurni ya taɓa yin coge ya sa wata fitowa da ake sumba a ciki har ta shallake masu tace Fina-Finai. Amma ana fara haska shirin a wani gidan haska Fina-Finai da ke Tokyo, nan da nan aka dakatar da shirin kuma aka ƙwamushe fim ɗin.

Dokar Yin Sumba 

Akwai doka mai tsanani a wasu ƙasashen, musamman ƙasashen musulunci. Misali, a Iran duk mutumin da aka kama shi ya Sumbaci wacce ba Muharramarsa ba ko ya taɓa ta, za'a yi masa bulala 100 in bai ci sa'a ba ma sai yayi yari. 
Haka ma a sauran ƙasashen musulunci dokar take. Duk da cewa ya halatta Ma'aurata da muharramai su Sumbaci junansu a fili (musamman a kumatu ga ƴan uwa), sumbatar waɗanda ba muharramai ba ka iya jawo wa mutum abinda bai yi tunani ba. Domin a 2007, gwamnatin Dubai ta ci tara tare da garƙame wasu mutum biyu a kurkuku saboda sun Sumbaci juna tare da yin runguma a bainar jama'a. 


A Ƙasar India, nuna soyayya ko ƙauna ta hanyar runguma ko sumba a bainar jama'a yana matsayin ta'addanci ne kamar yadda yake rubuce a sashi na 294 na Indian Penal Code, 1860 kuma hukuncinsa shi ne garƙamewa a magarƙama har na tsawon wata uku ko tara ko kuma duka biyun. Wannan dokar kuma har yanzu Ƴan Sanda da kotu na amfani da ita wajen ƙwamushe Masoyan da ke irin wannan aiki. Sai dai kuma a wasu sassa na Ƙasar, kotu kan yi watsi da irin wannan cajin. 


To idan mun Fahimci waɗannan bayanai, Tambaya ɗaya ce kawai Ta rage mana. Wannan tambaya kuwa ita ce: WANE IRIN SUMBA NE SALMAN KHAN BAYA YI A FIM? 

Na Barku Lafiya. 

<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring


Share:

NA DAƊE DA FAHIMTAR HAKAN 03

NA DAƊE DA FAHIMTAR HAKAN 03

To abu na gaba kuma shi ne, akwai wasu mutanen da a da suna son wani Jarumi, amma daga baya sai ka same su suna son wancan ɗin amma kuma suna son wani a gefe, wasu kuma sai su watsar da wancan ɗin kacokan su komawa sabon. To me ke jawo faruwar hakan?

Kamar yadda na faɗa a baya, a mafi yawancin lokuta idan Jarumi ya ƙware a fannoni da dama yana kwashewa waɗanda suka ƙware a fannoni kaɗan kasuwa saboda banbancin Ra'ayi. Wasu kuma ƙila Jarumi ko Jarumar da suke so tayi wani abun da bai dace bane sai su dawo daga rakiyar su. Wasu kuma kawai Ƙarewa Jaruman take yi, kamar yadda wani babban Jarumi a da mata suke rubuto mishi wasiƙu da jinin jikin su amma daga Ƙarshe ya mutu a wulaƙance.

To amma kuma akwai wani abu wanda ke kawo irin wannan canji a wajen 'yan kallo, shi ne girma da hankali da kuma tsayuwar Ra'ayi. Sau tari wasu in suna yara sai ka iske sun fi son Fina Finan Jarumi kaza, amma da sun girma sai su canja su komawa wani. Saboda yarinta daban da manyantaka, ƙuruciya daban da girma. Ko da yake ana samun ire-iren waɗanda su har girmansu suna tare da jarumin su (kamar ni kenan), amma basu da yawa gaskiya. Yawancin Masoyan Dilip Kumar da Amitabh Bachchan waɗanda matasa ne ko yara ne a da sun koma son Shah Rukh Khan bayan fitowar sa, yawancin Masoyan govinda da Dev Anan sun komawa Aamir Khan, haka yawancin Masoyan Anil Kapoor da Makamantansu sun komawa Salman Khan. Amma har yanzu akwai waɗanda suna nan suna son su, akwai kuma waɗanda kawai dai suna basu girmansu ne ba wai soyayya ba.

Dama ita rayuwa haka take, in yau kaine gobe wani ne. 

Ina yiwa kowa fatan nasara dangane da Fina Finan Jarumi ko Jarumar sa 

<••••••••••••••••••••••••••••>
       ɧãımãŋ Řâééʂ <••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com


Share:

NA DAƊE DA FAHIMTAR HAKAN 02

NA DAƊE DA FAHIMTAR HAKAN 02

Kamar yadda na faɗa a baya, tabbas kowa na da alaka da jarumin da yake so, ko dai a bayyane ko kuma a sirrance. Akwai mutanen da suke son wasu jarumai kaɗai saboda suna da ban dariya, misali; Johnny Lever, M.S Narayana da kuma Brahmanandam duk sun yi suna a wajen jama'a saboda sun iya bada dariya.

Haka nan kuma, sau tari akan samu wasu gungun mutane kuma waɗanda su kuma Zunzurutun muguntar Jarumi ce ke sa suji suna son shi, ko da kuwa ace su ba mugaye bane a fili. Misali; Amrish Puri, Danny da Prakash Raj duk sun yi ƙaurin suna ta yadda wani ma saboda su Kawai yana iya zuwa ya kalli fim duk da cewa a matsayin azzalumai suke fitowa.

Hallau kuma dai akwai mutanen da su suna son ganin fim ɗin tausayi da shiga mawuyacin hali a rayuwa, to suma suna da irin nasu Jaruman da suke liƙewa.

To kasancewar ita baiwar Allaah tana da yawa, a wasu lokutan sai ka iske Jarumi guda ɗaya ya ƙware a wajen iya abubuwa biyu, uku ko sama da haka waɗanda duk in ya hau yana yin su daidai, hakan ke sa Masoyan waɗannan abubuwan su ji suna sonsa, hakan kuma shi ke sa Aga Jarumi ya tattara masoya da yawa. Misali; Jarumi Hrithik Roshan ya iya rawa, ya iya Kafce kuma ya iya dambe, hakan tasa yana fitowa nan da nan ya samu karɓuwa saboda masu son irin waɗannan abubuwa suna da yawa, kuma a da suna samun su ne kawai a wajen Mabanbantan jarumai yanzu kuma sai gashi sun same su a waje guda.

Misali na gaba kuma shi ne, Shah Rukh Khan. Srk Jarumi ne da maganar gaskiya ba wai don shi ne Jarumi na ba ya iya abubuwa da yawa, ya iya mugunta, ya iya ban tausayi, ya iya ban dariya, ya iya Kafce sannan kuma ya iya soyayya, duniya ma ta san da haka, a taƙaice dai, da wuya a samu wani mutum mai kallon Fina-Finan Indiya da zai ce srk bai taɓa taɓa masa zuciya ba tun da ya fara Fina Finansa, ban ce babu ba, amma da wahala. Kuma wannan dalili yasa Masoyan srk suke da yawa a duniya.

To idan mun fahimci wannan, akwai kuma wasu Jaruman da sun ƙware a wani waje, amma in an je wani wajen ma babu laifi nan ma suna ɗan taɓukawa. Misali; Salman Khan Jarumi ne da ya iya suburbuɗa na gaban kwatance babu ja, kuma ya iya soyayya da Kafce, amma bai iya rawa ba, sai dai kuma hakan baya hana shi taɓuka abin arziki idan ya hau filin rawa, bai iya bada dariya ba, amma da wuya yayi abin ban dariya baka yi dariyar ba.

Zan ci gaba In Shaa Allaah 

<••••••••••••••••••••••••••••>
  ɧãımãŋ Kɧâŋ Řâééʂ <••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com


Share:

NA DAƊE DA FAHIMTAR HAKAN 01

NA DAƊE DA FAHIMTAR HAKAN 01

Masu iya magana na cewa 'Sai hali yazo ɗaya ake abota'. Wannan magana haka take babu tantama. Sai dai ni na ɗauki Darasin wannan maganar ne a wata mahanga ta daban.

Watau na daɗe da fahimtar cewa, mutane suna son Jarumi ne idan ɗayan waɗannan abubuwan da zan lissafo suka yi daidai da nasu.
 1. Hali
 2. Ɗabi'a
 3. Ra'ayi
 4. Salo
 5. Rayuwa

Kamar yadda waccan magana ta nuna, mutum na iya faɗawa soyayyar Jarumi nan take idan halin su yazo ɗaya. Misali; idan halin mutum ne saurin fushi to akwai Yiwuwar zai faɗa soyayyar Jarumi ko jarumar da ke da saurin fushi nan take, haka ma in mai haƙuri ne. 

To haka ma Ɗabi'a, mutane da yawa suna da Ɗabi'ar jin son wanda Ɗabi'ar su tazo ɗaya. Misali, idan Ɗabi'ar mutum ne sanya baƙaƙen kaya, ko shan shayi da safe to akwai Yiwuwar nan take zai iya kamuwa da soyayyar Jarumi ko jarumar da ke da irin wannan Ɗabi'ar.

Hausawa suka ce Ra'ayi Riga, duk wanda yake da tsatstsauran Ra'ayi ko sassauƙan Ra'ayi, to shima nan take zai iya kamuwa da son Jarumi ko jarumar da ke da irin Ra'ayin sa.

Salo wani abu ne da yake bayyana wanene mutum, yaya halinsa da Ɗabi'arsa suke. Idan mutum yana da salon da ya dace da na wani Jarumi ko wata jaruna, to nan take zai iya kamuwa da son wannan jarumin ko jarumar.

Misali; Me yasa Masoyan Jarumi Salman Khan suka fi yawa a India fiye da kowace ƙasa? Saboda mafi yawancin mutanen India salon su, halin su, ɗabi'un su da Ra'ayin su irin nashi ne, don haka duk abin da yayi gani suke yi kamar su ne suka yi ko kuma don su yake yi. Wannan shi ne bayyannen misali da kowa zai iya fahimta.

Sai dai kuma akwai Jaruman da gaskiya kyawun su yasa ake son su, musamman jarumai Mata. Wasu daga cikin su basu da ƙwarewa a harkar Kafce kamar yadda ake tunani, amma saboda kyawun da Allaah Ya basu sai kaga ba'a ganin Kuskuren, wasu mazan ma haka ne abin.

Anan Ƙasar hausa, Jarumai Irin su Sony Deol, Mithun Chakraborty, Prabhas, Charan da Sauran Makamantan su sun sami karɓuwa sosai a wajen matasa saboda sun iya sambaɗa da mazga yadda ya kamata. Yayinda jarumai irin su Shahid, Hrithik, Allu Arjun da sauran su kullum suna samun yabo akan sun iya rawa.

Jaruma Madhubala har yanzu ana yabon kyawun ta, yayinda Madhuri Dixit kuma babu wacce ta kai ta iya rawa. Jaruma Anushka Shetty da Jaruma Kangana Ranaut kowa na yaba musu wajen iya Kafce. Jarumi Aamir khan ma har kiran shi ake yi da sunan ƙwararre, Yayinda Srk kuma duk duniya ta san shi a matsayin sarki ne na masu yin soyayya.

Kenan in kun lura, hankalinmutane yana karkata zuwa ga Jarumi ne idan wani abu da ya dangance su yayi Kamanceceniya da nasu. A taƙaice dai, babu wani masoyin Jarumi ko Jaruma da za'a ce babu wani abu wanda yake yazo ɗaya tsakanin sa da wannan jarumin.

Zan ci gaba In Shaa Allaah.

Amma ku menene Kamanceceniyar dake tsakanin ku da naku Jaruman?

<••••••••••••••••••••••••••••>
  ɧãımãŋ Kɧâŋ Řâééʂ <••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com


Share:

KAN MAI UWA DA WABI


KAN MAI UWA DA WABI


Bismillahir Rahmanir Raheem.

Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu.

Yaku ƴan uwana ina yi mana Barka Da Warhaka. Sannan ina mai neman afuwar duk wanda wannan muƙala tawa zata ɓatawa rai, domin yau kam in shaa Allaah babu sauran ɗaga ƙafa. Haka kuma zan so kuyi min aikin gafara idan kuka ji na saki layi a wasu wuraren, kamawa tayi ne shi yasa. Sannan kowa ya sani, babu batun nuna ɓangaranci yau, Gaskiyar abin da na fahimta zan faɗa ba tare da ɗagawa wani ko wata ƙafa ba, ko da kuwa ni ne da kaina.
 Allaah Ya azurta mu da Kyayyawar fahimta Aameen.

Wato wata Matsala wacce na lura da cewa ana yawan magana a kanta, kuma har wa yau babu wani ci gaba da zan iya cewa an samu akai. Wannan dalili yasa na yanke Shawarar yin bayani akanta tare da kawo mafita a Ƙarshe in shaa Allaah.

Matsalar ita ce,; da zaka tara Mata tun daga ɗaya har zuwa ɗari zaka samu kusan kowacce daga cikin su tana zargin maza da cewa sun faye kallon mata da yawa, matan nan kuwa ko da na aure ne, ko da zawarawa ne, ko da ƴan mata ne, ko da ƙwwilaye ne, ko da Berori ne kuma ko da Tsoffi ne.
A ɓangaren maza kuma, da zaka tara su suma tun daga ɗaya har zuwa ɗari (ciki har dani) mafi yawancin su suna yiwa matan irin kallon da ya wuce na Shari'a, da zarar kayi magana sai su ce ai laifin matan ne saboda irin shigar da suke yi.

A taƙaice dai kowane ɓangare yana zargin ɗan uwansa. Wannan dalili yasa na yanke Shawarar fitowa domin inyi fiɗar bayanai dangane da matsalar da kuma hanyar da nake ganin za'a bi domin a magance wannan matsala.

Da Farko dai zan fara da iyaye na mata. Mata halittu ne masu wuyar Sha'ani, ana son su amma suna da wuyar mu'amala a mafi yawancin Lokaci, sai dai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba. Amma fa, mata sun san cewa Allaah da Manzon Sa Sun yi hani da shigar da bata dace ba yayin fita daga gida a wurare da dama a cikin alƙur'ani da Sunnah, sai dai Kaico! Yawancin iyayen mu mata basa amfani da duk nasihohin da ake musu. Ga ka ɗan daga cikin halayen wasu Iyeye mata dangane da wannan matsala.

*. Wata tana shigar da bata dace bane saboda neman Samari kai tsaye, domin wata gani take yi in ba haka tayi ba bata da hanyar jawo hankalin wani da har zai zo ya neme ta.

*. Wata tana shigar da bata dace bane saboda ta jahilci girman laifin aikata hakan a musulunce.

*. Wata tana aikata hakan ne saboda yahudanci ya riga ya ratsa ta.

*. Wata tana yin Hakane saboda ita tafi ƙarfin kowa, ƴar bariki ce ba mai tsayawa ma yayi mata Nasiha tunda ba ɗauka zata yi ba.

*. Wata dama da gangan take yi don a kalle ta a san cewa ta tara abubuwa saboda wasu DALILAI nata na musamman.

Kaɗan kenan, wasu matan fa kuyi min aikin gafara suna fitowa yawo ba tare da ko ɗan Kamfai ba a jikin su, face doguwar riga kawai ko Hijabi, wanda da zarar iska ta kaɗa, to komai kawai yana waje ne dama. Wani abin mamaki kuma shi ne, yawancin matan nan sukan yi irin shigar da su kansu sun san cewa tabbas in suka fita fa dole sai an kalle su, amma kuma ana kallon nasu sai su koma suna zage-zage da cewa maza karnuka ka ne, ko Mayu ne ko Muzurai ne. To ke kuma fa?

Wata ko Hijabi zata sa sai ta sa shi yadda zata ja hankalin mazaje kanta, kuma da zarar sun kalle ta tace wai Tsinannu ne sun faye shegen Kallo, to ke kuma fa?

Wata fa in tana tafiya har bouncing take yi tana kallon yadda jikinta yake kaɗawa tana alfahari da irin Surar da Allaah yayi mata, ita fa da kanta kenan, amma a haka sai kaji in an bita da kallo tana cewa shegu sun ga kaya, to ke kuma fa?

Maza na dawo kan mu, da yawan maza suna jawa sauran zagi duk kuwa da cewa mu ma ba a taru an zama ɗaya ba. Amma feesabilillah abinda wasu mazan suke yi ko kare bai yi sai dai bunsuru. Wasu mazan fa ko tsohuwa ce In suka bita da kallo sai taji kamar ta faɗi don kunya.

* Idan kuma ƙwaila ce sai kaji ana 'hmm wannan in ta girma za'a yi mace a wajennan.

* In kuma matar aure ce sai kaji ana cewa,' ho ɗan nema wance fa har yanzu da sauran ta. Ko wane fa yayi dace malam, har yanzu ana gurzawa.

* In kuwa ƴan mata ne, haba malam ana magana ma wannan. Sun manta da cewa Addini ya gargaɗesu da cewa su kame ganin su kuma su kasance masu kau da Kawunan su daga irin waɗannan mataye.

Kuma da zarar kai magana sai kaji ance 'ai laifin matan ne, wa yace suyi shigar da bata dace ba? To in sunyi, kai kuma wa yace ka biye musu?
Maza da yawa sun ɗauki Ɗabi'ar kallon matan mutane da ƴan mata kamar wata Sana'ar kirki, shi yasa unguwanni da yawa zaka ga ƴar ƙungiya an zauna kawai ana faman yi da mutane, kaɗan ne suke iya sauke haƙƙin zaman bakin titi.
Kenan idan muka lura da waɗannan bayanai, zamu iya fahimtar cewa kowane ɓangare suna da nasu irin matsalar. To mecece mafita?

Mafita anan ita ce kowa yaji tsoron Allaah Ya tsaya inda aka iyakance shi kada ya ƙetare iyaka. Ke a matsayin ki na mace Musulma wacce ta san mutuncin kanta kiyi iya ƙoƙarin ki wajen ganin kin rufe tsiraicin ki yayin fita, ba ki dinga fita kamar yadda aljifan baya suke fita ba.
Kai kuma a matsayin ka na namiji musulmi wanda ya san mutuncin kan sa, ka yi iya ƙoƙarin ka wajen kare ganin ka daga abin da bai kamata ba.

Sannan kuma dukkanmu mu yi wa junan mu adalci, tunda kowa yana da nashi laifin, me zai hana muyi ƙoƙarin gyara namu kura-kuran a maimakon ci wa juna zarafi da kuma aibata juna? Me zai hana mu dinga yiwa juna Addu'a tare da fatan shiriya a maimakon zagi da tonawa juna asiri?


Ina fatan Zamu ji kuma za mu gyara.
Allaah Ya Shirye mu baki ɗaya, ya Shiryi Zuri'armu. Ya gafarta mana laifukan mu kuma ya ɗora mu akan abinda yake shi ne dai-dai.

Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka wa atubu ilaika. Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  ɧãımãŋ Kɧâŋ Řâééʂ <••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees
Instagram: Haimanraees
Infohaiman999@gmail.com
Share:

FATALWAR SINU 05

""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""
              FATALWAR SINU 05
""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""
              A Short Story
""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""
       FINAL EPISODE

✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
     ʂɬơrყ/wrıɬɛɛŋ   
            ɮʏ✍🏻:

👉🏻© ɧãımãŋ Kɧâŋ Řâééʂ ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹

Na san cewa wasu daga cikin ku zasu ce: ina Haiman! Ai Sam kada ka damu sun zo ne domin su taimake ka daga hannun SINU da mugyambo, blah blah blah! Erm.. Nagode da irin wannan kyakyawan tunani naku a gareni, amma kamar yadda na faɗa muku a baya, rashin sa'ata ya kai maƙura. Ina nan tsaye ina kallon su tare da jiran ganin abinda zai faru, ai kuwa ban daɗe ba ina wannan jira sai naga Shah Rukh Khan ya rikiɗe izuwa Siffar G.ONE Yayinda shi kuma Rajnikanth ya juye izuwa Siffar Chitti. Kafin kace me ke faruwa tuni sun kacame da faɗa. A'a! Kamar wasa fa, kawai sai naga Salman Khan da Surya suma sun koma gefe suna nasu, can kuma sai na hango Aamir Khan da NTR suma sun ja daga suna sambaɗar juna. Nan fa kowa ya fara jan daga da abokin karawarsa. John Abraham da Prabhas suka tari juna, Ram Charan da Tiger Shroff, Allu Arjun da Hrithik Roshan, Vijay da Arjun Rampal, Vidyut da Sanjay Dutt. Haka dai kowane Jarumi da abokin karawarsa, shi Abhishek Bachchan ko me ya kai shi tarar Mahesh Babu oho, zuwa ɗaya Mahesh yayi mai sai gashi yana aman jini. Can gefe kuma naga Anil Kapoor da Ajith Kumar suna tasu fafatawar, Yayinda Govinda da Chiranjeevi suma suka ja daga. Ana haka kuma sai naga wajen ya ƙara yin duhu, kafin in ankara kuma sai ga jarumai Mata suma suna durowa. Nan take suma suka fara nasu artabun, Kangana da Anushka Shetty suka tarbi juna aka fara fafatawa, Katrina da Tamannah suma suka buɗa, Anushka da Samantha suka ja gefe, Kajal kuma sai ta tarbi Priyanka. Haka dai suma suka ware suka dinga ribzar juna kamar tumun dawa.

Nayi Matuƙar mamakin ganin wannan abu da ke faruwa, can daga baya kuma sai na tuna, sama da shekaru uku da suka gabata wani ƙazamin tunani ya taɓa zuwa min a raina har na dinga riyawa ina ma ace Jaruman kudanci da na arewaci za su yi wani gagarumim shiri wanda za'a caskale a cikin sa? To gashi yanzu yana faruwa a gabana ina gani. To tayaya aka yi har SINU yasan da cewa na taɓa yin wannan tunani? Daga nan sai nayi tunanin in raba su mana, don haka sai na nufe su ina mai basu haƙuri, ni gashi baki ya toye babu damar yin magana, garin bada haƙurin ma ni aka mazge ni na faɗi kasa na fasa kai na kasa tashi. Ina nan kwance sai na fara jin ƙaraji, gunji gami da ihun jarumai, da ƙyar dai na lallaɓa a hankali na tashi zaune. Ai kuwa nan take hwnkalina ya ƙara tashi, ba komai ne ya jawo haka ba face ganin cewa duk yawan Jaruman nan mutum huɗu kawai suka rage a filin dagar, sauran daga waɗanda suka mutu sai kuma masu kakarin mutuwa. A ɓangaren maza Jarumi Hrithik Roshan da Prabhas ne kaɗai suka rage a tsaye suma kuma kowanensu ya samu muggann raunuka a jikin sa. A ɓangaren mata kuma Jaruma Anushka Shetty ce tare da Kangana Ranaut suka rage. Nan fa suka yi cirko-cirko kamar zakaru, da alama dai wani sabon faɗa zasu sake yi. Lallai ya zama dole in san abin yi, to me ya kamata in yi? Me zan yi ya jawo hankalin SINU kaina?

Can kuwa sai wata dubara ta faɗo min, don haka sai na yanke Shawarar faɗawa fagen dagar. Na miƙe a sanyaye jiki ba Ƙarfi na nufi wajen matattun domin samun makami, cikin sa'a kuwa sai nayi karo da gawar NTR, hannunsa riƙe da wani ɗan matashin gatari wanda aka yiwa azargiya da wata sarƙa, cikin azama na finciki gatarin tare da yin kan Jaruman ba tare da shakkar komai ba ina zuwa kawai sai na fara kai Sara ta ko'ina da gatarin, bisa sa'a zan ce ko rashin sa'a oho, kai saran da nayi na farko kuwa sai gashi na fille kan Kangana, aifa nan take sai sauran ukun suka yo kaina suka rufe ni da duka. Kafin in ankara, tuni sun haɗa min jini da Majina, daga nan na faɗi matacce ne ma ko sumamme ne ban sani ba.

Bayan wani ɗan lokaci sai na Farfaɗo, bisa mamaki sai na jini na dawo daidai, bakina ya warke sumul kamar ban taɓa jin wani ciwo ba. Nan take kuwa na miƙe tare da nufin kawo ƙarshen wannan lamari ko ta halin ƙaƙa. Miƙewa ta ke da wuya kuwa sai na ga SINU a zaune akan wata jar kujera, yayi kinini da fuskar nan kamar markaɗe yaso gardama. Ko da naga haka sai na buɗi baki nace: "ina sauran Jaruman?" maimakon ya bani amsa, sai ya ƙara fusata, jikin sa ya fara wani tiririn harzuƙa, kafin in ankara kawai sai gani nayi wata irin iska mai Ƙarfi ta tunkaro ni, cikin sauri na duƙa ƙasa iskar ta wuce. Ko da yaga haka sai naga ya miƙe, yanzu za'a yita kenan, na ayyana a raina. Maimakon in yi kanshi, kawai sai na koma gefe na fara antayo duk wani kafcen sa da zan iya tunawa ina lanƙwashe murya tare da kwaikwayon irin abinda ya aikata a cikin kafcen ina kuma ƙarawa kafcen gishiri da magi.
Wannan abu da nayi fa yasa SINU ya haukace ya dinga yaƙushin jikinsa yana ihu da kururuwa yana buga kansa da duk abinda ya samu. Ni kuwa sai na dage da abin da nake yi, nayi ta kaftawa babu ƙaƙƙautawa, shi kuma ya ci gaba da kururuwa gami da ihu. Ana cikin haka kawai sai ji nayi an buge ni ta baya, hakan yasa dole na dakata da kafcen da nake yi sakamakon faɗuwa ƙasa da nayi. Ai kuwa ina daina yin hakan sai SINU ya dawo hayyacin sa, ba tare da yayi wata-wata ba, kawai sai ji nayi an Luma min wata sharɓeɓiyar Wuƙa a cikina, nan fa zafi zogi, raɗaɗi da azaba duk suka lulluɓeni a lokaci guda, ko ganin mutuwa da nayi ne a fili, ko ya akayi ni dai ban sani ba, kawai ji nayi bakina ya furta INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN!

Ina furta wannan kalma kuwa sai nan take na tuna, tun daga lokacin da wannan yaro yazo yayi sallama da ni ban sake furta sunan Allaah ba sai yanzu, duk abinda nake yi kawai na dogara ne da wayau na da dubara ta. Nan take naji kunya ta kamani, amma da na tuna cewa Allaah mai rahama ne, sai kuma naji kwarin gwuiwa ya shige ni. A wannan lokaci har SINU ya ƙara ɗaga Wuƙar nan da nufin ya caka min, cikin sauri kuwa na fara karanta Alƙur'ani mai girma, ban ma san wata sura nake karantawa ba sai da na kai tsakiya tukun na fahimci Ayatul Kursiyu nake karantarwa. Nan take kuwa sai naji SINU ya kwarara ihu kuma ya ɓace, kamar wasa kuma firit! Sai ji nayi na farka, ashe mafarki nake yi, gashi duk na jiƙe da gumi kamar nayi wanka.

Cikin sauri na tashi na ɗauro alwala nazo nayi sallah Raka'a biyu tare da yin Addu'o'in neman tsari da kariya. Amma bacci sai ya gagare ni, nan na fara tunanin yanzu da ace da gaske ne shikenan na tafi Kenan.

DARASIN LABARIN: Yaku 'yan uwa, shin sau nawa muke mantawa da Allaah mu dogara da tunanin mu, sau nawa muke mantawa da yin addu'a tare da neman taimakon Allaah akan lamuran mu? Sau nawa muke dogara da tunanin cewa mun isa ne shi yasa muke ganin daidai a rayuwa mu manta cewa Allaah shi ne Isashe? Sau nawa muke kasa kaiwa Allaah buƙatunmu saboda muna tunanin cewa zamu iya ko ba tare da shi ba? Shin in muka mutu a daidai irin wannan yanayi me zamu cewa Allaah idan muka haɗu da shi?

Ya Allaah Ka shirye mu, Ka sa mu zamo masu dogara da kai a dukkan lamarin mu. Aameen.

In kunne yaji....


<••••••••••••••••••••••••••••>
  ɧãımãŋ Kɧâŋ Řâééʂ <••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees
Instagram: Haimanraees
Infohaiman999@gmail.com

Share:

FATALWAR SINU 04

""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""
              FATALWAR SINU 04
""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""
              A Short Story
""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""
   
                      ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
         ѕtσrч/wríttєn ɮʏ✍🏻:
👉🏻© Hãïmâñ Khãñ Řăééş ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹

Ta yiwu baka san ko baki san wanene Mugymbo ba, amma ni da yake nayi mishi farin sani, kuma nasan me zai iya aikatawa. Nan da nan ban tsaya wani bin diddigi ko neman labari ba sai na arce a matakin gudu na 160m. Wannan arcewa da nayi ne ta sa Mugymbo da Sinu suka fashe da dariya, ina jin ƙarar tafa hannun su amma ban damu ba ni dai kawai gudu nake yi. Ina cikin wannan gudu ne kawai sai naji kamar daga sama wani abu yazo ya gifta a guje ta gabana, kafin in ankara tuni nayi karo da wannan abin. Ƙarfin haɗuwar da muka yi ne tasa nayi baya tare da yin tambul na wuntsula can gefe kamar yadda Rahul yayi a cikin shirin Chennai Express. Na yunƙura na miƙe a hankali saboda na bugu, me zan gani a gabana? Wani ƙaton biri na gani mai Matuƙar munin gaske, ina ganin ma sai ya fi King Kong girma da muni da za'a gwada su. Nan fa muka tsaya muna kallon juna ni da shi ba tare da na iya motsa ko ɗan yatsana ba saboda tsoro. Shi kuma birin ganin yadda na tsaya wani sololo kamar Karen da ke atini yasa shi ya harzuƙa yayi gunji ya bugi ƙirji sannan yayi kururuwa mai ƙarfin gaske!

Dakata! In faɗa muku gaskiya ko In muku ƙarya? Shikenan, na san gaskiya zaku ce don haka babu yadda na iya. Watau saboda tsabar tsoratar da nayi, da na saki wata ƙaƙarfar tusa sai da ta keta min wando sannan ta tayar da wata 'yar ƙaramar ƙura a inda nake tsaye, shi kanshi wannan birin sai da ya toshe hanci saboda mugun warin da ya biyo bayan wannan ƙura, ermmm... Ina nufin tusa. Ganin ya tsaya toshe hanci yasa nayi sauri na bi ta tsakiyar ƙafafunsa na sake arcewa da wani sabon gudun. Ban yi nisa sosai ba naji ƙasa ta fara girgiza tana tsagewa tare da lanƙwame duk abin da ta samu. Nan fa na fara 'yan tsalle-tsale don ganin na kaucewa faɗawa ciki, amma da yake rashin sa'ata ta kai Matuƙa gaya, kwatsam sai gani nayi na zo ƙarshen hanyar da nake gudu a kanta. In na juya baya ga biri na biye da ni, in na ci gaba kuma ga rami, in kuma na ci gaba da tsayuwa Ƙasar wajen zata iya laƙume ni, to ya zan yi? Can sai wata tubara ta faɗo min, tun kafin in canja shawara kawai sai na juya na tsaya Dakyau ina jiran birin ya ƙaraso. Abin ka da dabba bai lura da cewa bayyana fili bane kawai babu komai, sai ya danno da gudu da nufin ya ƙwamushe ni. Ko da yazo dab da ni sai na yi sauri na shige ta osin sa na wuce, ƙarfin gudun da yake yi da kuma nauyin jikinsa suka rinjaye shi yayi cikin wannan rami a sukwane, ni kuma saboda ƙarfin hali kawai sai na bishi cikin ramin. Ni da dubarata ita ce, idan ya faɗa ramin ya mutu ni kuma sai in faɗa kanshi hakan zai taimaka min wajen rage min zafin faɗi. Amma kaico! Ko da na bishi ya zamana muna ta yawo a iska bamu kai ƙasa ba, cikin fushi kawai naga ya juyo tare da kawo min mangari, kafin in yi wani yunƙuri tuni hannun sa mai kama da gungume ya buge ni a ƙafata ta dama. Hakan yasa nayi ta katantanwa da juyi a sama kafin daga baya na faɗo ƙasa Tim! Kamar kayan wanki.

Bana buƙatar a duba ni, nasan cewa ƙafata ta dama ta karye saboda wani azababben zogi da naji tana yi min sakamakon bugun da birin yayi min. Ina nan kwance na kasa tashi sai naji ana tafi daga bayana. Cikin firgici nayi maza na Waiga inda nake jiyo tafin ba tare da na miƙe ba. SINU da Mugyambo na gani tsaye a kaina suna min tafi. Cikin dariyar mugunta Mugyambo ya kalle yace: "yaro Lallai dole in yaba maka domin kayi Kasada mai matuƙar girma, amma kada ka damu dama nafi son sheƙe Jaruman gaske domin hakan ne zai tabbatar da girman izzata". Yana gama faɗar haka sai SINU yayi murmushi sannan ya ce; "gaskiya da ace zaka fara Kafce da anyi babban Jarumi, sai dai ba zaka yi tsawon rai ba balle ma ka kai ga ɗaukar wannan shawara, abokina Bismillah! Cikin dariyar mugunta Mugyambo ya nufo inda nake yana taku ɗaiɗai, ko da ya zo dab da ni sai ya ciwo kwalata ya ɗagani sama, zogin da nake ji a ƙafata yasa ni nayi wani irin nishin wahala. Na buɗe baki na kenan da nufin in gaya masa wata baƙar magana kawai sai ji nayi ya tura min wani abu a bakina. Da fari na ɗauka yaji ya tura min, ashe Garwashin wuta ne ya tura min, nan take harshe na da maƙogwaro na suka ƙone ya zamana hatta kukan da nake yi ma sautinsa ya gaza fitowa waje. Tsabar wahalar da Nasha ce ta sani na sake sakin wata gagarumar tusar wacce hatta shi kanshi Mugyambo sai da ya ja da baya yana cewa Wayyo maƙogwaron sa. Nan fa na kama fagabniya da buge-buge saboda wahala.

Ina cikin wannan hali ne sai naga wajen ya sauya kala, hadari ya haɗu sannan wajen gaba ɗaya ya ɗau cida. Kwatsam kuma sai naga wasu abubuwa kamar Tsuntsaye suna faɗowa daga sama, sai da na tsaya na lura dakyau sannan na fahimci cewa ashe mutane ne. Mutanen sun yi layi biyu ne suna tafiya ba tare da kowa ya cewa ɗan uwansa komai ba. Ko da suka ƙara matsowa kusa sai naji zuciyata ta buga dam! Waɗannan mutane ba wasu bane face Jaruman Fina Finan Indiya gaba ɗayan su. Na arewacin Indiya a damana, na kudanci kuma a hagu. Wanda ke jagorancin na arewacin dai ba kowa bane face Shah Rukh Khan da kansa, yayin da Rajinikanth shi kuma yake jagorantar na kudanci. Nayi Matuƙar mamakin ganin su a wannan wuri, abinda ya fara zuwa min a rai shi ne: suma sun mutu ne ko kuma sun zo ɗaukar fansa ne a kaina?

Zan Ci Gaba In Shaa Allaah
<••••••••••••••••••••••••••••>
  ɧãımãŋ Kɧâŋ Řâééʂ <••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees
Instagram: Haimanraees
Infohaiman999@gmail.com
Share:

FATALWAR SINU 03

*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
              FATALWAR SINU 03
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
              A Short Story
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
   
                      ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
         *ѕtσrч/wríttєn ɮʏ✍🏻:*
👉🏻© *_Hãïmâñ Khãñ Řăééş_* ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹


Yayinda sinu yaji waɗannan tambayoyi nawa, sai yayi wani irin gunji gami da ƙarajin fusata har sai da wani irin farin hayaƙi ya dinga fitowa daga bakin sa, hancin sa da kuma kunnuwan sa. Can kuma sai ya nuna ni da hannu yana mai cewa: kai ɗan bayan gari! Kada ka raina min hankali da waɗannan tambayoyi naka. Hausawan ku basu iya samun Sara ba, a duk lokacin da wata sabuwar Sara ta fito, to ba zasu tsagaita ba har sai sun gallabi jama'a da ita. Tun da aka fara wannan fassarar shikenan na zama abin zolayar kowa, a duk lokacin da kuwa aka zolaye ni ina jin duk abinda ake yi kuma raina yana Matuƙar ɓaci, duba kaga irin tsiyar da ka tsula min a cikin shirin Bunny (Cinnaka) har yanzu ba'a daina zolayata akan sa ba hasali ma dai wannina ɗaya daga cikin dalilan da suka sa na kasa kwanciyar kabarina lami lafiya. Ko da Sinu yazo daidai nan a zancen sa, sai na ce: 'a'aha, shin ashe dama binne ka aka yi ba ƙona ka aka yi ba? Wannan tambaya tawa ba ƙaramin harzuƙa shi tayi ba, don haka cikin fushi ya ce dani: "Ya isa! Wannan Iskaranbarancin naka ya isa Hakanan, bana buƙatar wani bayani daga gareka, yanzu zan fara gana maka muggan azabobin da na tanada kafin daga baya in sheƙe ka kowa ya huta.

Ko da naji wannan batu nasa, sai dariya ta ƙwace min hakan tasa yayi shiru kawai yana Kalllo na Yayinda baƙin ciki ya ƙume shi. Da naga alamar ya nutsu sai na ce da shi: "ka yi min afuwa bisa dariyar da nayi babu yadda na iya ne, amma twmbayoyina basu Ƙare ba. Shin ta yaya aka yi ma har ka iya magana da harshen Hausa? Ta yaya akayi ka san da wanzuwar masu fassara a Ƙasata? Ta yaya kai da kake FATALWA zaka iya azabtar da wanda yake raye?
 Sannan kuma menene shirin ka a kaina da kuma sauran masu fassara da harkar Indiya baki ɗaya a Ƙasar Hausa? Erm... Kada ka yi min mummunar fahimta, kawai dai ina so in samu cikakken bayani ne dangane da dalilin da yasa kake son kashe ni bayan ka azabtar da ni. Hakan zai taimaka min wajen mutuwa cikin kwanciyar hankali". Yayin da yaji na sake antayo masa waɗannan tambayoyi haka, sai ya sake kurɓar barasa sannan ya yi murmushi. Kamar daga sama kuma sai ga wata kyakyawar kujera fara tas ta bayyana a gaban sa, zaman sa ke da wuya kuma sai ga wani farin teburi ya bayyana a hannun daman sa,ga kwalaben giya nan iri-iri an jera. Ya ɗauko wata kwalba guda wacce aka rubuta STAR LARGER BEAR a jikinta ya buɗe Ya kwankwaɗe ta kai tsaye sannan ya ajiye kwalbar. Ajiye kwalbar ke da wuya sai kayan jikinsa suka koma farare tas. Ya sake yin wani mummunan murmushi a gareni sannan ya fara magana da cewa: "Duk da cewa ba zan so ka mutu cikin lumana da kwanciyar hankali ba, amma Haƙiƙa kayi tambaya mai buƙatar amsa, domin kai da zaka mutu wani amfani ko rashin amfani amsar zata yi maka? Amma manta da wannan, amsar tambayar ka ta farko mai sauƙi ce, duk wanda ya mutu yana iya fahimtar kowane irin yare a duniya kuma yana iya magana da kowane yare. Amsar tambayar ka ta biyu kuma ita ce, na san da wanzuwar masu fassara a Ƙasar Hausa ne bisa irin yawan ambaton sunana da ake yi a yankin, sannan a matsayina na fatalwa ina da wani SIHIRI da zan iya aiki da shi a kan duk wanda naga dama. Shiri na kuwa a kan ka tare da sauran masu fassara da harkar India baki ɗaya shi ne, da fari dai tukun zan ganawa kowannen ku azaba mai raɗaɗi sannan daga baya in sheƙe ku kowa ya huta.

Don haka, a matsayin ka na mutum na farko da zai fara fuskantar wannan Waƙi'a, zan baiwa wani babban aminina damar gana maka azaba kafin in amsa daga inda ya tsaya. Har na buɗe baki zan tambaye shi wanene wannan abokin nasa kawai sai gani nayi wata ƙofa ta bayyana. Daga cikin ƙofar kuma sai ga wani mutumi ya bayyana. Bayyanar wannan mutumi yasa na kiɗime fiye da ganin Sinu. Mai yiwuwa ku iya cewa "haba Haiman, wannan ai yawa ne" , amma ina dole ce ta saka ni na kiɗime. Domin ba kowa na gani ba face babban azzalumin da duniya kaf ta yarda da cewa shi azzalumi ne. Wannan kuwa ba kowa bane face Amrish Puri, watau Mugyambo mugun boss.


Zan Ci Gaba In Shaa Allaah

<••••••••••••••••••••••••••••>
  ɧãımãŋ Kɧâŋ Řâééʂ <••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees
Instagram: Haimanraees
Infohaiman999@gmail.com
Share:

MURNAR SALLAH KAMAR ALGAITA

MURNAR SALLAH KAMAR ALGAITA

A wannan rana ta sallah na riga nayi baran-baran da tuwo sa Rangyam, hakan yasa ake kirana da ƊAN TAWAYE! Amma da yake ina sambaɗar taliya kamar yadda nake sambaɗan cin-cin, hakan Yasa ake kirana da Mai FUSKA BIYU. Tsakanina da naman Kaji akwai soyayya mai ƙarfin gaske, hakan yasa ake kirana da SARKIN SOYAYYA! Watau in dai soyayyen nama ne, da zarar mun haɗu to fa shi ya kaɗe kenan, hakan yasa na zama HATSABIBI a gare shi.

Kada ku taɓa damuwa da irin surutun da zaku ji Akuyoyi suna yi a kaina, tsabar cinye namansu da nake yi ne yasa suke kirana da AZZALUMI. Shi kuwa naman sa komai taurin sa hakanan zan yi amfani da IZZAR MULKI wajen ganin na taune shi ba tare da jinkiri ba. A taƙaice dai abokai, duk masu tsoron taurin nama ni kawai ina ɗaukar su ne a matsayin HAMAGAWA! Ko da yake nasan in suka zama HORARRU zasu iya tafi da kowane gagararren nama, amma domin cimma wannan mataki nasan cewa dole sai sun je makarantar NINJAN KISA tukunna. Domin Ita wannan makaranta tayi ƙaurin suna wajen sauya halayyar mutane, hakan ya faru ne tun bayan da ta canja DOLAYE UKU suka koma 'YAN UKU sannan suka rankaya HANYAR MADARAS domin zuwa shagalin bikin salla tare da MACASKALI.

To kun ga saboda haka, a wannan Sallar naga cewa ya kamata nima in ɗan yiwa wasu kaji KISAN GILLA domin samun Nishaɗi irin na BABBAN YARO tunda nima dai JIKINA DA JINI. Kun san cewa NAMIJIN ZAKI baya tsoron DAMISA, amma tun bayan da na zamewa tunkiyoyi MAI TAƁARGAZA sai duk suka koma kirana da SHUGABA saboda sun fahimci cewa YAƘI DA RASHIN ADALCI yana buƙatar MAI GASKIYA, su kuma basu da shi. Saboda haka, in dai a fagen ɗiban girki ne, to ni ake yi wa laƙabi da MAI SUBURBUƊA. Na riga n zamewa agawagi Inuwar mutuwa don har ma kiran suke da MAI ADDA. Tsabar shiƙar da nake yiwa raguna a kowace sallah in tazo ne yasa tuni aka ƙaƙaba min sunan MASHEƘI

MAZGA, MAKIRCI, haɗa TARKO ko yin amfani da barazanar kaini GIDAN KURKUKU ba zasu hanani amsa sunana na MASHAHURI a fagen shan jar miya ba. Wai don a hanani shan miyar yasa fa suka cika mata BARKONO, basu san cewa ni tuni na shiga cikin CAKWALKWALIN CAKWAKIYAr daɗi ba bana ma ko jin zafin. Sai dama an ce MAKASHIN MAZA... Kun dai gane domin kuwa a wancan sallar na kasa rabewa tsakanin SIYASA DA AƘIDA har sai da JAMI'IN TSARO ya kawo min ɗauki, a wannan lokaci kuwa tuni na daɗe da ɗaukar fasahar BOTORAMI. Na dai gane kuskure na tunda BABBAN YAYA yayi min Nasiha don haka babu ni babu MAKAUNIYAR SOYAYYA, shi yasa a wannan Sallar na kauda kaina daga SOYAYYAR BEBAYE ko MAKAHON SO, na tsaya kawai a matsayin ƊAN BASAJA.

Dama can AKASI, aka samu na zama UBAN DABA LAMBA ƊAYA a soyayya saboda KADDARA ta riga fata, amma in zaka ji shawarata aboki, kada ka sake ka yi budurwa ranar sallah in kuwa ba haka ba to zaka shiga cikin TAWAGAR MAƘARYATA ba tare da ka ankara ba kuma daga baya azo ayi ta binka da SABABI! kai ni dai na gwammace in zama MAI MAZGA a wajen nama kamar yadda na zama MAI ZAFIN HANNU a wajen loma. Kai gara ma in zama MADAKIN ƘATTI ko SARKIN ASKA a fagen feɗe dabbobi daga fatun su. Don haka kowa ya saka ZOBEN SIHIRI, ya ɗauki MASHI don shirin TAFIYAR AJALI in yaso komai ta fanjama FANJAM. Amma kuyi hattara sa SANGAMI, GARUJE, TAƘADARI da kuma SOJA domin suna iya antayewa da ku zuwa BIRNIN TSAFI.

Nidai na Zama ZAKIN ZAKUNA mai cinye namuka.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  ɧãımãŋ Kɧâŋ Řâééʂ  <••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter:  @HaimanRaees
Instagram: Haimanraees
Infohaiman999@gmail.com

Share:

FUSATACCIYAR MACE

FUSATACCIYAR MACE

Fusatacciyar Mace haɗari ce matuƙa

Tana Da matuƙar ban haushi

Ga ta da mugun kishi

Tana Da Taurin Kai

Kuma ga Wuyar Sha'ani

Tana iya kisa ko Lahanta Komai

Ba Za Ta huta ba, bare tai murna

Ba Ta iya magana haka ma tunani

Ba hutu balle cin abinci

Ta fi Zaki haɗari

Ta fi Maciji Dafi

Ta fi Fatalwa ban tsoro

Ta fi Aljani Shu'umanci

Hattara dai da Fusatacciyar Mace!


<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com


Share:

HABA YALLAƁAI!

HABA YALLABAI!
YALLABAI YANZU KO KUNYA BAKA JI ACE KA DAUKO 'YAR MUTANE DAGA GIDANSU AMMA ABINCIN DA ZATA CI SAI TAYI AIKATAU ZATA SAMU BAYAN KUMA KAI GA KUDI NAN RAM A KUGUNKA KA BOYE? YANZU KANA GANIN HAKAN YA DACE? KO KANA DAGA CIKIN IRIN MAZAJEN NAN NE MASU CEWA: ''RABU DA KAFIRA, INJE IN SHA WUYAR NEMAN KUDI ITA KUMA TANA GIDA TANA WALAWA, TO BARNI DA ITA, MIYAR KUKA MA KADAI TA ISHI BAHILAR MATAN NAN''. YANZU IRIN HAKA FISABILILLAHI YA DACE? KAI IN AKAYIWA KANWARKA HAKA ZAKA JI DADI? GASKIYA MAZA ADINGA KIYAYE HAKKIN MATAYE WANDA YA RATAYA A WUYANKU KUMAMATAN ADINGA KIYAYEWA DOMIN AKAWAI RANAR TSAYUWA WALLAHI!
YALLABAI DA FATAN KAJI!

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com

Share:

DARUSSAN RAYUWA DAGA JARUMI SHAH RUKH KHAN 02

DARUSSAN RAYUWA DAGA JARUMI SHAH RUKH KHAN

Kashi Na ɗaya 01

Fitowa Ta Biyu 02

Daga Haiman Khan Raees

Bismillahir Rahmanir Raheem.

Barkan Mu da Warhaka.


 7. GIRMAN KAI RAWANIN TSIYA:

 Jarumi Shah Rukh Khan yana daga cikin Jaruman Indiya da suka fi saura sauƙin kai da iya mu'amala. Bugu da ƙari SRK bashi da girman kan tsayawa a nuna mishi abinda bai sani ba ko bai iya ba ko da kuwa ace wanda zai koya masa abin nan yana ƙasa da shi ne sosai. Domin mun ga hakan a fili Yayinda ake ɗaukan fim ɗin Zero inda ƴar cikin sa mai suna Suhana ta zo tana koya masa wasu al'amura dangane da aikin fim ɗin.

8. ƊAN UWA RABIN JIKI:

Mutane da yawa basu san cewa Jarumi Shah Rukh Khan yana da wata ƴar uwa ba, amma a zahiri yana da ita. Su biyu mahaifiyar su ta haifa. Bayan mutuwar iyayen su wannan ƴar uwa tasa ta faɗa cikin mawuyacin hali na rashin lafiya wanda wasu da dama ma sun yi tunanin mutuwa zata yi, amma hakan bai sa ɗan uwanta ya guje ta ba. Hasali ma, mafi yawancin ayyukan da ya karɓa a farko-farkon fitowar sa, ya karɓe su ne kawai domin ya samu abinda zai ci da kansa da iyalan sa da kuma nemawa ƴar Uwar sa lafiya.

9. ALLAAH NA TAIMAKON MAI TAIMAKO:

 Shah Rukh Khan ya kasance ɗaya daga cikin Jaruman da suka fi kowa tausayin Talakawa da waɗanda Iftila'i ya faɗawa. Yana taimakawa mutane a duk inda ya samu damar taimakawa, ko da yake baya son baiyanawa, amma duniya ta sani, domin har lambar yabo ya samu akan hakan.

10. A SAI DA RAI A NEMO SUNA:

 Jarumi Shah Rukh Khan Haƙiƙa ya cancanci a kira shi da suna ƊAN KASADA, domin kuwa yayi abinda a Tarihin Masana'antar Fina Finan India kusan in ka cire Jarumi Amitabh Bachchan, to za'a iya cewa ba'a taɓa samun jarumin da yayi kamar sa ba. Ba komai ne ba wannan abu ba face karɓar wasu ayyuka wanda jarumai da yawa suka gujewa domin tsoron zasu iya karya musu alƙadarin su a harkar Fina-Finai. Bisa sa'a kuwa sai gashi ya hau su kuma ya tsallake rijiya da baya. Kamar yadda jarumin yakan faɗa, "tari Aradu da ka, in ka yi Nasara zaka ji daɗi in kuma baka yi ba zaka ƙara ilimi".

11. DATTIJO:

Haƙiƙa Alamomin Dattijantaka sun bayyana a tattare da Jarumi Shah Rukh Khan. Domin kuwa banbancin tsoho da Dattijo abu ne mai muhimmanci da ya kamata mu sani. Tsoho shi ne wanda ya tsufa sakamakon shekarun sa sunyi nisa, amma zuciyar sa tana cike da yarinta. Dattijo kuwa shi ne tsohon da ya tsufa a shekaru, kuma ya tsufa a hankali da tunani. Jarumi Shah Rukh Khan yayi aure, kuma ya haihu, sannan shekaru sun ja kuma yasan da hakan. Sanin kowa ne cewa jarumin yana da kyakkyawan tarihi da ke bayyana cewa bai taɓa yaudara ko cin zarafin wata Jaruma ba, bai taɓa ha'intar wani abokin aikin sa ba kuma bai da mugunta. Sannan hankali da nutsuwar sa ne suka sa ake gayyatar sa zuwa taruka domin ya gabatar da jawabai. Bugu da ƙari yana daga cikin Jaruman da suka fi saura kula da yaransu musamman ta fuskar karatu da kuma ɗa'a.

12. BAYAN WUYA SAI DAƊI:

 Iyeyen Jarumi Shah Rukh Khan har Suka mutu basu mallaki gidan kansu ba, a gidan haya su ke. Asali ma, akwai lokacin da aka wayi gari sun gaza biyan kuɗin hayar gidan da suke zaune har aka watso musu kayan su waje. Amma a yau Jarumi Shah Rukh Khan yana da katafaren gida na gani na faɗa. Bugu da ƙari, gidan jarumin ya samu damar shiga cikin jerin gidajen da ko da nan gaba Gwamnatin India ta yanke Shawarar yin rusau domin gyara tsarin gine-ginen Ƙasar, to su ba za'a taɓa su ba. Lallai Allaah Shi ne mai yin yadda ya so.

13. GIDA BIYU MAGANIN GOBARA:

 Kasancewar Jarumin yana da ilimi a harkar kasuwanci da iya tallata haja, kamfanoni da dama sun sha ɗaukar sa a Matsayin mai tallata musu hajojin su. Hakanan kuma jarumin yana da Kamfanin shirya Fina-Finai mai suna Red Chillies Entertainment wanda a yanzu haka babu kamar su a kaf Bollywood wajen VFX. Har ila yau kuma dai, jarumin yana da kaso mafi tsoka a cikin kungiyar ƙwallon Cricket ɗin nan mai suna Kolkata Knight Riders. Kenan yau ko da ta Allaah ta kasance ya daina fim, to yana da abin yi.

14. KWALLIYA TA BIYA KUƊIN SABULU:

Tabbas Jajircewar wannan Jarumi ta jawo mishi suna da ɗaukaka mai tarin yawa a rayuwar sa. Domin a daidai lokacin da na ke wannan rubutu, alƙaluma sun bayyana cewa jarumin yana da lambobin yabo a ƙalla guda ɗari biyu da Casa'in da biyu (292). Lallai wannan ko ba'a faɗa maka ba kasan cewa banza bata kai zomo kasuwaA nan zan ɗan dakata dangane da Darussan rayuwar wannan Jarumi ba don sun Ƙare ba, sai dai don kada abin yayi yawa. In Shaa Allaahu Ta'ala a fitowa ta gaba zamu taɓa Darussan da ke tattare ne da wasu daga cikin finafinan sa.

Nagode.

Zan Ci Gaba In Shaa Allaah
<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com

Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form