Skip to main content

Posts

Tambaya Ta 005 A Ina Allaah Ya Ke?

*Tambaya Da Amsa*
.
.
*DAGA DALUBAN ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
.
.
6-11-1438
30-7-2017
.
.
_1---------------Ina Allah yake??
=
_Amsa---------------Allah madaukakin sarki yana sama kuma ya daidaita akan al'arshi, amma iliminsa yagame ko ina****_
=
=
_2-----------------Rukunnan tauhidi guda nawane??
=
_Amsa---------Rukunnan tauhidi guda biyu ne, sune korewa dakuma tabbatarwa****_
=
=
_3---------------Menene Ilimii??
=
_Amsa-------------Ilimi shine mutum ya riski abu wato yasan abu a yadda yake****_
=
=
_4-------------Menene bambanci ilimi da aqida??
=
_Amsa-------------Bambancinsu shine ita aqida bayan ka fahimci abun a yadda yake sekuma ka quudurceshi a zuciyarka****_
=
=
_5----------------Rukunnan musulinci guda nawa ne??_
=
_Amsa-------------Rukunnan musulinci guda 5 ne****_
=
=
_6---------------A lissafo mana rukunnan musulinci dukkansu???_
=
_Amsa---------------1-kalmar shahada 2-Sallah 3-Azumi, 4-Zakka, 5-Hajji****_
=
=
_7----------------Alissa…

Tambaya Ta 006 MIJINANE YAKE ZAGINA NIMA NAKE RAMAWA, MENENE HUKUNCIN HAKAN?

*MIJINANE YAKE ZAGINA NIMA NAKE RAMAWA*       Daga zauren
📕HISNUL-MUSLIM📕       *TAMBAYA*Assalamu Alaikum. Malam miji ne baya kyautatawa matar sa har ma wani lokaci ya zage ta, ita kuma sai ta rama. To meye hukunci wannan auren?
        *AMSA*
wa alaikissalam dan ya zageki bai kamata ki ramaba, kamata yayi kiyi masa nasiha idan nasihar zata kwanto wata fitinar saiki nemi na gaba dashi yayi masa Fada amma bai kyautu mace ta dinga zagin mijinta dan ya zageta baZagin miji ko cutar dashi da harshe, wannan
yana daga cikin manyan laifuka a Musulunci
(wato Kaba'ira).
Manzon Allah (s a w) ya lissafa matan da suke
yin haka acikin Manyan 'yan wuta. (ya Allah ka
tsaremu).  Allah na masani
*ABDUL AZEEZ*
*Masu buqatan shiga Wannan Zaure na hisnul Muslim   suyiwa daya daga cikin wadannan  number  magana ta whatsApp+2348065523065*
*+2348162067271*
    Domin Neman Karin bayani akan wata fatawa sai Ku kira wannan numbar↓
*+2347065588557*
سبانك اللهم وبحمدك، اشهد ان لا اله الا انت استغفرك واتو…

Tambaya Ta 004 YAUSHE AKE YIWA YARO KACIYA ?

*Tambaya*Assalamu alaikum malam, ina tambaya ne akan yiwa yaro kaciya shekara nawa ya kamata ayi masa ?*Amsa*
Wa'alaikum salam,To malam babu wani hadisi ingantacce wanda ya kayyade wani lokaci da za'a yiwa  yaro kaciya, saidai malamai suna cewa: babbar manufar yin kaciya ita ce  katanguwa daga najasar da za ta iya makalewa a al'aura, wannan ya sa ya wajaba a yiwa yaro kaciya dab da balagarsa, saboda idan ya balaga shari'a za ta hau kan shi kuma tsarkinsa ba zai cika ba, in ba'a yi masa kaciyar ba, daga cikin ka'aidojin malamai shine duk abin da wajibi ba zai cika ba sai da shi, to shi ma ya zama wajibi, amma mustahabbi ne ayi masa, tun yana dan karami, saidai wasu malaman sun karhanta yin kaciya ranar 7 \ga haihuwa, saboda akwai kamanceceniya da yahudawa.Allah ne mafi saniDon neman karin bayani duba Fathul-bary 10/349*Dr. Jamilu Zarewa*18/11/2014*ZAUREN📚DARUL-ISLAM📚*

Tambaya Ta 004 Siradi Da Wuta

*_MALAM MINENE GASKIYAR WANNAN MAGANAR?_*
                            *Tambaya:*
Malam wai da gaskene cewar, kowa sai ya dandana wutar lahira, banda Annabi Muhammad (S.A.W.)?
(Daga Dahiru Adam).                                *Amsa*‎
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
A’a cewa akayi "WADDUHA" ba cewa akayi "MUTHEEQUHA" ba.

Watau kowa sai yabi takan wuta sannan ya wuce. Domin Siradi, akan wuta aka dorashi, mutanen da aka yiwa hisabi zuwa Aljanna sai sunbi takan Siradin.

Wanda yake a kan wuta.
Shine (acikin Alkur'ani) akace: "WA-IN-MINKUM-ILLA WARIDUHA KAN-ALARABBUKA HATMAN MAQDIYYA"."وَإِن مِّنكُمْ إِلَّا وَارِدُهَا كَانَ عَلَىٰ رَبِّكَ حَتْمًا مَّقْضِيًّا".
Suratul Maryam.

Amma kuma jin zafinta (wutar) sai wanda Allah ya nufa da yaji zafin nata, sannan yaji zafin. Allah ka tseratar damu daga azabar wuta.

_WALLAHU A'ALAM._

Rubutawa:- Ãbûbäkår Êkâ.Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada ma…

Tambaya Ta 003

*HUKUNCIN MACE TA YI TAFIYA BA TARE DA MUHARRAMI BA*Fatawar Mata fitowa ta 1*TAMBAYA:*
Mene ne hukuncin mace ta yi tafiya ba tare da Muharrami ba?.*AMSA:*
An hana mace ta yi tafiya face tare da Muharrami wanda zai tsare ta kuma ya kare ta daga barnan mabarnata da fasikancin fasikai. Hakika hadisai ingantattu sun zo wanda suke hana mace ta yi tafiya ba tare da Muharrami ba, daga cikin su:An rawaito daga Abdullahi Dan Umar, Radhiyallahu Anhu, ya ce: Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: *_Kada mace ta yi tafiya na kwanaki uku face tare da ita akwai Muharrami_*. Sannan an karbo daga Ibn Sa'id, Radhiyallahu Anhu, Lallai Manzon Allah, Sallallahu' alaihi wa sallama, Ya hana mace ta yi tafiya yini biyu ko darare biyu face tare da mijinta ko Muharraminta. Kuma an karbo daga Abi Hurairah, Radhiyallahu Anhu, daga Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: *_Ba Ya halatta ga mace ta yi tafiya na jini da dare face tare da ita akwai Muharraminta_* Bukhari da …

Tambaya Ta 002 Wa Ya Dace Yayiwa Mace Wankan Gawa?

*WAYE YA DACE YA YI MA MACE WANKAN GAWA?*Fatawowin Mata fitowa ta 2*TAMBAYA:*
Waye ya dace ya yi ma mace wanka idan ta mutu?, kuma shin ya halatta Mace kafira wanda ba Musulma ba ta yi mace Musulma wanka idan ta rasu?. Sannan da shigar da ita Kabari sharadi ne dole sai Makusantanta, ko kuwa kowane Musulmi zai iya shigar da ita kabari?. Akwai wasu mutane shin ya halatta a bar su, su shigar da mace kabarinta?. *AMSA:*
Musantan mace su ne za su yi mata wanka kuma za a yi la'akari da wanda suka fi kusanci daga cikin wanda za su iya kyautata wankan. Kuma ya halatta a wakilta kowace mace wanda za ta iya kyautata wanke ta, koda kuwa ba makusanciyarta ba ce. Haka nan ya halatta miji ya wanke matan shi, ita ta wanke shi. Dangane da Mace kafira ta wanke Musulma, wannan bai halatta ba, domin wanke mamaci ibada ce, kuma Ibadan wanda ba Musulmi ba, bata inganta. Dangane da shigar da mace kabarinta, ya halatta wani daga cikin Musulmi ya shigar da ita koda ba makusancinta ba ne, matukar zai kyau…

Suratul Zil Zila

*☘☘Suratul Zilzila Da Fassararta☘☘*

```🌹بسم الله الرحمن الرحيم🌹

١.اذا زلزلت الارض زلزالها.
1⃣.Idan aka girgiza kasa girgizawa.
٢.واخرجت الارض اثقالها.
2⃣.Kuma Kasa ta fitar da kayanta masu nauyi.
٣.وقال الاءنسن مالها.
3⃣.Sai Mutum yace miye ya sameta???.
٤.يؤمذ تحدث اخبارها.
4⃣.A Ranar zata bada Labarinta.
٥.بان ربك اوحى لها.
5⃣ .Saboda Ubangijinka yayi mata Wahayi.

٦.يومذ يصدر الناس اشتاتا ليرو اعلمهم.
6⃣.A ranar Mutane zasu fito daban-daban domin a Nuna masu Aiyikansu.
٧.فمن يعمل مثقل ذرة خيرا يراه.
7⃣.Toh Duk Wanda ya aikata wani aiki na Alkhairi kwatankwacin kwayar zarra zai ganshi.
٨.و من يعلم مثقل ذرة شرا يراه.
8⃣.Haka ma duk Wanda ya aikata aiki na sharri kwatankwacin kwayar zarra zai ganshi.```

*🌷Rubutawa🌷*

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

+2347039135966

Tambaya Ta 001 Hukuncin Saukewa Mamaci Alqur'ani Bayan Ya Mutu

*_HUNKUNCIN SAUKEWA MAMACI ALQUR'ANI BAYAN YA MUTU_*
                           *Tambaya:*
Assalamu alaikum Wai Malam Meye Hukuncin Saukewa Mamaci Al-qur'ani?
                                *Amsa*
Wa'alaikum assalam. To malamai sun yi sabani akan wannan mas'ala zuwa maganganu guda uku :*1*. Bai halatta ba, saboda ba'a samu wani nassi da yake nuni zuwa haka ba, kuma ita ibada ba'a  yinta sai da nassi na musamman, sannan  kuma mutum ba shi da wani abu sai aikinsa, kamar yadda aya ta 39 da take cikin suratu Najm, take nuni zuwa haka, tun da ba'a samu ba, yin hakan zai zama bidi'a, wannan ita ce maganar farko ta Shafi'i.*2*. Ya  halatta ayi, saboda hadisan da suke nuna cewa mamacin yana iya amfana da abin da mai rai zai masa, kamar hadisan da suka yi umarni da yi masa sallah da nema masa gafara bayan ya mutu, da  yi masa sadaka, wannan shi ne maganar mafi yawan malamai, har wasu marubuta ma sun hakaito ijma'i akan haka, saboda mutane sun jima suna yi…