Wednesday, 23 January 2019

Fitinar Da Ta Ɓullo Wa Matanmu A Yau

*FITINAR DA TA ƁULLO WA MATANMU A YAU!*
.

Ina farawa da sunan Allah Mai rahama Mai jin 'Kai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin Sarki. Tsira da aminin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta (ﷺ).

Ya 'Yan uwana musulmi, na tsara zan yi wannan rubutu ne ba don komai ba sai don in ankarar da 'Yan uwa musamman mata da iyaye dangane da wata annoba ta lalacewa da ta tunkaro matanmu a yau.

A kokarin kafirai na ganin cewa sun bata tarbiyyar yaran musulmi, sun cire kunya daga jikinsu wadda aka san mata da ita a addinance da al'adance, da kuma kokarinsu na kawar da manufar aure tare da hana auratayyar gaba daya, sun kirkiro wadansu abubuwa (tools) wadanda Mace za ta iya amfani da su don biyan bukatarta (sexual desires) ba tare da ta bukaci namiji ba. Hakika wannan haďarine mai girman gaske, kasancewar zai hana masu yin aure tare da cire masu kunya, kuma uwa ubama zai iya janyo masu matsaloli a jikinsu da kuma fushin Ubangiji.


Daga cikin waďannan abubuwa akwai abin da ake ce ma *Dildo,* shi wannan wani abu ne wanda ake qera shi da roba (rubber) kuma a yi mashi kirar (shape) irin na al'aurar namiji, suna amfani da shi ta hanyar zura shi a gabansu, wanda su kan sanya wani mai (oil) wanda zai ba su damar shigar da shi cikin al'aurarsu, a haka za su yi ta yi har su gamsar da kansu (Cum/ejaculate).

Sannan akwai *Vibrator,* shi kuma wannan akwai wanda ake jona shi da wutar lantarki (electric), akwai kuma wanda ke amfani da battery (manual), suna amfani da shi ta hanyar wasa da al'aurarsu da shi (masturbation), shi ma dai idan mace ta yi amfani da shi tana samun gamsuwa ba tare da ta bukaci namiji ba. Na'udzubillah!

Akwai *Strapon,* shi kuma wannan shi ma yana da kirar al'aurar namiji, Sannan akwai igiya a jikinshi kamar ďamara (belt), mace za ta daura shi a kugunta sai ta dinga yi wa wata macen irin yadda namiji ke yi wa Mace. Innalillahi wa inna ilaihi raaji'un!

Akwai sauran *Sex toys* kala-kala wanda duk an yi su ne saboda wannan manufar. Kuma mafi yawa daga ciki 'yan madigo (lesbians) ne suke amfani da su.

Asali wadannan abubuwa ana amfani da su ne a kasashen yammaci, wato yankin turawa kenan, amma a yanzu na samu labarin cewa wasu gur6atattu a nan kasar (Nigeria) sun fara yo safararsu (ordering) daga kasashen ketare zuwa wannan kasa tamu mai albarka, kuma ma har ya shigo yankin mu na arewa wanda yanki ne na musulmi, da kunnena na ji wata tana ikirarin cewa ta kusa fara yin safarar irin wadannan kayayyaki tunda ta fahimci cewa mazan hausawa ba su iya biya wa matansu bukata ba (Kun ji karya!), wannan abu ya tada min da hankali matuka, shiyasa na za6i in yi wannan rubutu don farkar da 'Yan uwa game da muni da illar wadannan abubuwa.

Amfani da irin wadannan abubuwa be tsaya a kan *'Yan mata* kaďai ba, da yawa a kan samu *Zawarawa* da *Matan aure* ma suna amfani da shi, musamman matan da mazansu ba su iya gamsar da su. Dayawa mata suna daukar wannan dabi'ar ne daga lalatattun Qawaye a gida ko a makaranta, ko ta hanyar shiga dandali (groups/pages) na 'yan maďigo da labaran batsa a yanar gizo, ko ta hanyar kallace-kallace na fina-finan nuna tsiraici (pornographic videos), da cakuduwa da matan Banza.
.

*ILLOLIN IRIN WADANNAN ABUBUWA.*

—Yin amfani da wadannan abubuwa haramun ne, kasancewar ya sa6a wa hanyar da shari'a ta taskance don biyan bukata, wato *aure* tsakanin mace da namiji.

—Sannan wannan abune da zai iya barazana ga lafiyar mace, kasancewar tana shigar da wani abu jikinta sa6anin wanda aka yi gurin don shi.

—Yin amfani da su yana zubar wa mace da budurcinta tun kafin ta yi aure, wannan zai iya sa koda ta yi aure mijinta ya sake ta ko zargi ya shiga tsakaninsu domin ba ta da wani bambanci da bazawara. Kasancewar tsokar da ke rufe da farjinta (hymen) wanda ke da alaka da budurci (chastity/virginity) zai fita daga lokacin da ta fara amfani da irin wadancan abubuwan.

—Yana cire wa mace son aure gaba daya, sai ka ga mace ta manyanta amma ko maganar aure ba ta yi, domin a nata tunanin ai tana samun duk abin da za ta iya nema daga namiji.


—Ga matar aure, zai cire mata sha'awar mijinta, domin za ta ji ba ta iya samun gamsuwa daga mijinta har sai ta yi wancan abin da ta saba.

—Yana janyowa matsala daga kwakwalwa kamar yawan mantuwa, kasancewar akwai ragowar ruwa (sex fluid) wanda ba ya samun fita sai ta hanyar saduwa da namiji, to wannan ragowar yana komawa ya shafi (affecting) din kwakwalwarta (Central Nervour System).

—Baqaqen aljanu (Jinnul ashiq) za su iya shiga jikinta a lokacin da take wannan abin, kuma za su janyo mata matsaloli masu girma a rayuwarta, ko dai su aure ta su hana ta aure da dan adam, ko kuma ko ta yi auren ta ki samun haihuwa ko kwanciyar hankali.

Wadannan wasu kenan daga cikin illolin wadannan abubuwa.
.

*HANYOYIN MAGANCE WANNAN MATSALA*

—Wajibi ne Iyaye su sa ido sosai a kan kaiwa da komowar yaransu, su san abin da suke yi idan sun kaďaitu a ďaki, su dinga yawan duba (searching) na jakarsu domin mafi yawan 'yan mata masu yin wannan yawo da shi a jaka.

Sannan Uwa ta dinga kokari wajen nuna wa 'yarta darajarta da abin da zai kai ga zubar mata da kimarta tare da kai ta ga fada wa cikin fushin Ubangiji.

Uwa ta koya wa 'yarta ayyukan cikin gida domin ta shagaltar da ita da aikace-aikace, wannan zai sa sha'awa ba za ta dinga mata barazana ba.

—Iyaye su ji tsoron Allah su dinga aurar da yaransu daga lokacin da suka balaga matukar sun samu manemi. Kada a bijiro da wani al'amarin duniya kamar gama karatu d.s.

Mazan da ba su iya gamsar da iyalinsu sakamakon wata lalura su ji tsoron Allah su nemi magani.

—Ki kare idanunki daga kallace-kallacen videos da pics na tsiraici ko karatun littafai na batsa.

—Ki Shagaltu da ambaton Allah, karatun Alqur'ani da salloli na nafila da azumin nafila.
.

Sannan daga karshe ina shawartar hukuma da masu fadi a ji da su sa ido a kan masu shigo da irin wadannan kayayyaki, fasa kauri (smuggling) na shinkafa da makamai ba shi kadai bane matsalarmu, makomar tarbiyyar 'ya'yanmu ma abin dubawa ce.
.

Ya Allah Ka shiryar da mu.
.

*✍🏿Ayyub Musa Giwa.*
*(Abul Husnain).*

Daga Zauren
*🕌ISLAMIC POST.*

Ku yi sharing don wasu su amfana ta sanadiyarka!

Tuesday, 22 January 2019

100 DIRECT INSTRUCTIONS BY THE ALMIGHTY ALLAAH IN THE HOLY QURAN FOR MANKIND

100 DIRECT INSTRUCTIONS BY THE ALMIGHTY ALLAH IN THE HOLY QURAN FOR MANKIND
Allah SWT has directly given us 100 instructions through Al Quran :
1. Do not be rude in speech (3:159)
2. Restrain Anger (3:134)
3. Be good to others (4:36)
4. Do not be arrogant (7:13)
5. Forgive others for their mistakes (7:199)
6. Speak to people mildly (20:44)
7. Lower your voice (31:19)
8. Do not ridicule others (49:11)
9. Be dutiful to parents(17:23)
10. Do not say a word of disrespect to parents (17:23)
11. Do not enter parents’ private room without asking permission (24:58)
12. Write down the debt (2:282)
13. Do not follow anyone blindly (2:170)
14. Grant more time to repay if the debtor is in hard time (2:280)
15. Don’t consume interest (2:275)
16. Do not engage in bribery (2:188)
17. Do not break the promise (2:177)
18. Keep the trust (2:283)
19. Do not mix the truth with falsehood (2:42)
20. Judge with justice between people (4:58)
21. Stand out firmly for justice (4:135)
22. Wealth of the dead should be distributed among his family members (4:7)
23. Women also have the right for inheritance (4:7)
24. Do not devour the property of orphans (4:10)
25. Protect orphans (2:220)
26. Do not consume one another’s wealth unjustly (4:29)
27. Try for settlement between people (49:9)
28. Avoid suspicion (49:12)
29. Do not spy and backbite (2:283)
30. Do not spy or backbite (49:12)
31. Spend wealth in charity (57:7)
32. Encourage feeding poor (107:3)
33. Help those in need
by finding them (2:273)
34. Do not spend money extravagantly (17:29)
35. Do not invalidate charity with reminders (2:264)
36. Honor guests (51:26)
37. Order righteousness to people only after practicing it yourself(2:44)
38. Do not commit abuse on the earth (2:60)
39. Do not prevent people from mosques (2:114)
40. Fight only with those who fight you (2:190)
41. Keep the etiquettes of war (2:191)
42. Do not turn back in battle (8:15)
43. No compulsion in religion (2:256)
44. Believe in all prophets (2:285)
45. Do not have sexual intercourse during menstrual period (2:222)
46. Breast feed your children for two complete years (2:233)
47. Do not even approach unlawful sexual intercourse (17:32)
48. Choose rulers by their merit (2:247)
49. Do not burden a person beyond his scope (2:286)
50. Do not become divided (3:103)
51. Think deeply about the wonders and creation of this universe (3:191)
52. Men and Women have equal rewards for their deeds (3:195)
53. Do not marry those in your blood relation (4:23)
54. Family should be led by men (4:34)
55. Do not be miserly (4:37)
56. Do not keep envy (4:54)
57. Do not kill each other (4:92)
58. Do not be an advocate for deceit (4:105)
59. Do not cooperate in sin and aggression (5:2)
60. Cooperate in righteousness (5:2)
61. ’Having majority’ is not a criterion of truth (6:116)
62. Be just (5:8)
63. Punish for crimes in an exemplary way (5:38)
64. Strive against sinful and unlawful acts (5:63)
65. Dead animals, blood, the flesh of swine are prohibited (5:3)
66. Avoid intoxicants and alcohol (5:90)
67. Do not gamble (5:90)
68. Do not insult others’ deities (6:108)
69. Don’t reduce weight or measure to cheat people (6:152)
70. Eat and Drink, But Be Not Excessive (7:31)
71. Wear good cloths during prayer times (7:31)
72. protect and help those who seek protection (9:6)
73. Keep Purity (9:108)
74. Never give up hope of Allah’s Mercy (12:87)
75. Allah will forgive those who have done wrong out of ignorance (16:119)
76. Invitation to God should be with wisdom and good instruction (16:125)
77. No one will bear others’ sins (17:15)
78. Do not kill your children for fear of poverty (17:31)
79. Do not pursue that of which you have no knowledge (17:36)
80. Keep aloof from what is vain (23:3)
81. Do not enter others’ houses without seeking permission (24:27)
82. Allah will provide security for those who believe only in Allah (24:55)
83. Walk on earth in humility (25:63)
84. Do not neglect your portion of this world (28:77)
85. Invoke not any other god along with Allah (28:88)
86. Do not engage in homosexuality (29:29)
87. Enjoin right, forbid wrong (31:17)
88. Do not walk in insolence through the earth (31:18)
89. Women should not display their finery (33:33)
90. Allah forgives all sins (39:53)
91. Do not despair of the mercy of Allah (39:53)
92. Repel evil by good (41:34)
93. Decide on affairs by consultation (42:38)
94. Most noble of you is the most righteous (49:13)
95. No Monasticism in religion (57:27)
96. Those who have knowledge will be given a higher degree by Allah (58:11)
97. Treat non-Muslims in a kind and fair manner (60:8)
98. Save yourself from covetousness (64:16)
99. Seek forgiveness of Allah. He is Forgiving and Merciful (73:20)
100. Do not repel one who asks (93:10)
Let's share with others so we can all benefit from it.
May Allah continue to guide us and make things easy for Us.]

Jahilci Ko Huɗubar Shaiɗan?

JAHILCI KO HUDUBAR SHAIDAN?!

*MALWAHDE ❌❌*

'Yan uwa haqiqa wannan jahilcin da gidadanci da ya bullo mana a wannan zamanin ba qaramar fitina bace ga musulmai.

Wata kalar rawane wai ita MALWAHDE. Asali yahudawa ne suka tsiro da wannan rawar, wata waka ne ake yi da wani yare wadda har yanzu na kasa gane hakikanin fassarar waqar, sai ku ga masu rawar suna faduwa suna tashi. To amma saboda tsabar JAHILCI, GIDADANCI da yake damun wasu daga cikin samarinmu da 'yanmata a wannan lokacin, har an samu wasu na kwaikwayon irin wannan rawar, babban abin takaici ma wai har da mata. Na'udzubillah!

'Yan uwa wallahi mu ji tsoron Allah, ba komai ke damun mu ba sai rashin ilimin addini da son zuciya, na rantse da Allah sam-sam wannan ba waye bane, babu abin da koyi da yahudawa zai jawo mana face halaka da fushin Ubangiji.

Sannan kuma iyaye Wallahi ku ji tsoron Allah! Ku sa ido a kan yaranku domin wallahi za a tambaye ku a kan su domin kiwo ne Allah Ya ba ku!


Ya Allah Ka sa mu fi karfin zukatanmu.

Falalar Yin Sallar Nafila A Gida

FALALAR YIN SALLAR NAFILA A GIDA

Nafila mafi tsada da daukakar daraja a wajan Allah itace wadda akeyinta a gida,kamar yadda mafi yawan nafilolin Annabi s.a.w yana yin sune a gidansa, kadan ne yakeyi a masallaci.

Annabi s.a.w ya kwadaitar da mu akan yawaita nafila a gida yayi hakan a aikace kuma ya fada da dama ga kadan daga cikinsu;-

1-Sallar nafila a gida tafi falala akan wadda akayita a wani guri da daraja ashirin da bakwai.

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Sallar mutum ta nafila a gidansa inda mutane basu ganinsa,tafi sallar nafilar da mutum yayi inda mutane suke ganinsa da daraja ashirin da biyar).
@صححه الألباني في
صحيح الجامع - رقم: (3821)

2-Yin sallar nafila a gida sabawa Yahudawane da Nasara,kuma tana korar shaidhan kuma Mala'ikun sama suna kallon gidan.

Annabi s.a.w yana cewa:
(Ku sanya wani yanki na sallar nafila a gidanku,kada ku sanya gidanku ya zaman maqabarta kamar yadda Yahudawa da Nasara suka riqi gidanjensu a matsayin maqabarta,domin gidan da ake karanta alqurani acikinsa ma'abuta sama "wato mala'iku" suna ganin kamar yadda ma'abuta kasa"wato mutane"suke hangen taurari a sama).
@السلسلة الصحيحة - رقم : (3112) قال الألباني إسناده جيد .
3-Sallar nafila a gida itace mafi alkhairin nafilar bawa kuma Allah yana sanya mata alkhairi.

Manzon Allah s.a.w yace:
(Idan dayanku yagama sallolinsa a masallaci,to ya sanya wani kaso na sallar nafilarsa agidansa, domin Allah ya sanya albarka a sallar ta gida).
صحيح مسلم - رقم: (778)

4-Annabi s.a.w yayi mana umarni da yin sallar nafila agida.

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Kuyi sallar nafila a gidajenku,kada ku bar yin sallar nafila a gidajenku).
@صححه الألباني في صحيح الجامع - رقم: (3786)

Allah ka bamu dama da ikon yin sallar nafila da kyakkyawar niyya da ikhlasy a gidajenmu.

MIYAR OGNO

*👩‍👩‍👧‍👧S.H.D.G STARS*👩‍👩‍👧‍👧


*_(SMASHER,HUBBEEY,DIDEEYLOV&GENTLE)._**14/8/2018.*


*MIYAR OGNO*


*Ingredients:-*


* Nama
* Kifi danye da busasshe
* Ogbono
* Ganda
* Kayan miya
* Man ja
* Maggi da gishiri
* Curry da tafarnuwa
Preparation:
Ki tafasa namarki da gishiri, tafarnuwa, albasa, ki soya man ja amma kadan, ki zuba markadadden kayan miyarki a kai, su ma ba da yawa ba, idan ya soyu sai ki zuba dakakken crayfish kamar cokali biyu, ki zuba busasshen kifinki da kika gyara, ki zuba ruwa a kai, idan ta dahu sai kisa baking powder kadan dan tayi yauki sosai, dama kin sulala danyen kifi kin bare, kin cire kayar, kin gutsuttsura, shi ma sai ki zuba, ki rufe zuwa minti biyar ko goma shike nan kingama miyarki.😋


*MIYAR SHUWAKA*

*Ingredients:-*

* Nama
* Shuwaka
* Busasshen kifi
* Albasa
* Tafarnuwa
* Kayan miya
* Thyme da curry
* Maggi da gishiri
* Man ja
Preparation:
Ki wanke shuwakarki idan ba kya son dacin da yawa, sai ki dinga murje ta kina mutsittsike ta kina tace ruwan da rariya, sai kinyi kamar sau biyar ko sau shida, in kuma kina son dacin sosai sai ki wanke sau biyu ki tafasa namarki da thyme, da albasa da tafarnuwa da gishiri, ki zuba markadadden kayan miyarki da soyayyen man janki a kan tafasasshen namanki, idan ya dahu kamar minti bakwai, sai ki zuba shuwakarki, da gyararren busasshen kifinki, da yankakkiyar albasarki, da maggi, gishiri da curry, ki rufe tayi ta dahuwa, ba'a so tayi ruwa anfi sonta sa kauri.😋~S.H.D.G~*_(SMASHER,HUBBEEY,DIDEEYLOV&GENTLE)._*

Domin Yara

DOMIN YARA
Misalin karfe tara da minti arba'in, na safiyar ranar wata Laraba. Maman Abba na zaune tana wanke-wanken kwanoni, bayan ta gama sharar gida, sai ga danta Abba, dan kimanin shekaru tara da haihuwa, ya dawo daga makarantar firaimari. Yana goye da jakar littattafansa a baya, ya shigo yana kuka.
Mamarsa ta tare shi da sauri, ta zaunar da shi, tana tambayarsa daliln da ya sa yake kuka, ta ce, "Wa ya bugar mini Abbana? ko faduwa ka yi? Na sha fada maka ka daina gudu da yawa."
Abba ya share hawaye ya dubi mahaifiyarsa yana sheshekar kuka ya ce mata, "Bayan almajiran makarantar Malam Dudu, inda muke zuwa karatu da dare, suka tare ni yanzu suna ce mini, wai ni dan wuta ne tunda ina zuwa makarantar boko, Audu yana ta yi mini gwalo yana dariya, shi kuma Bala ya zungure ni."
Mamman Abba ta dafe kirji cikin mamaki, domin dai ta nuna wa danta damuwarta a fili, sa'annan ta ce, "Su Audun da Balan suka buge ka? Ai kuwa ba zan kara ba su abinci ba idan suka zo bara."
Abba ya kara zumbure baki yana cewa, "Kuma kullum in mun taso makaranta sai su yi ta yi mini waka suna cewa, 'Dan makarantar bokoko, ba karatu ba salla, sai yawan zagin malam'."
Maman Abba ta shafa kansa, ta ce, "Kyale su, bari idan Babanka ya dawo in fada masa, ya je ya fada wa Malaminsu, yau sai sun sha kashi. Ba mai kara jan ka cikinsu."
Abba ya yi murmushi ya ce, "Yawwa Mama, a ba su kashi sai sun yi kuka." Ya kwance jakarsa daga bayansa, ya rike ga hannu. Ya kuma duban Mahaifiyarsa ya ce, "Wai Mama da gaske ne Allah ya hana yin boko? Kuma wai duk wanda ya yi karatun boko idan ya mutu sai an sa shi wuta?"
Maman Abba ta yi dariya, ta ce, "A'a, wannan karya ne. Allah bai haramta neman ilimi ba kowane iri ne, muddin dai ba zai raba ka da yin addininka ba. Masu irin wannan ra'ayi, na haramta karatun boko, suna da nasu dalilai, sai dai dalilai ne da suka yi wa bahaguwar fahimta.

A cewarsu, boko haramun ne, tunda ana hada maza da mata wuri daya, kuma ana koyar da abin da ya saba wa koyarwar Alkur'ani mai tsarki, kamar yadda ake yin ruwan sama, da yadda duniya da halittu suka samo asali, da duba a kan abin da zai iya faruwa gobe, ko wata mai zuwa, ko ma shekaru masu zuwa.
Masu wannan ra'ayi sun manta cewa sau da yawa kisan kai yakan kawar da rotse. Watau idan sun ce ba za su yi karatun boko ba, saboda ana hada maza da mata wuri daya, me ya sa suke shiga mota maza da
 mata a yamutse? Me ya sa idan suka kai matansu asibiti maza ke duba su? Ina ce ko a Makka, akwai inda maza da mata ke cakudewa wurin aikin hajji. Saboda haka haduwar maza da mata lalura ce, wadda ba za ta hana musulmi yin karatun boko ba. Sauran fannonin da suka saba wa Alkur'ani mai tsarki a karatun boko kuwa, ai ba cewa aka yi dole sai musulmi ya yarda da su ba, karanta su ne dole, domin cin jarabawa, ba yarda da su."
Maman Abba ta takarkare tana ta yi wa danta bayani, kamar mai magana da babban mutum, da ma tuni tana cike da takaicin masu irin wannan ra'ayi. Shi kuwa Abba kallonta kawai yake yi, kamar mai kallon sabuwar mahaukaciya, bai san inda zancenta ya dosa ba. Ita kuwa ta ci gaba da bayaninta, Ba ruwanta da dan nata, ko yana fahimta ko baya fahimta, burinta kawai ta amayar da abin da ya dade yana damunta a rai. "Idan Musulmi ba su yi karatun boko ba, wa zai zama likita a cikinsu? wa zai zama soja? Wa zai zama Dan sanda? Wa zai tuka musu jirgin sama? Wa zai....."
Kafin ta karasa abin da za ta ce, da Abba ya ji ta ambaci jirgin sama, sai ya yi farat ya katse ta da tambaya, "La, Mama da ma sai mutum ya yi boko zai iya tuka jirgin sama?" Maman Abba ta ce, "Kwarai kuwa, sai da ilimin boko ake iya tuka jirgi." Abba ya yi dariya cikin murna ya ce, "Mama idan na gama karatuna, tukin jirgin sama zan yi. Kullum in zan wuce zuwa Makka, zan biyo ta saman gidan nan, in leko da kaina in daga muku hannu, ke da baba. Kuma in bi ta saman makrantar Malam Dudu in leko in yi wa su Audu da Bala gwalo in wuce." Maman Abba ta fashe da dariya, ta ce, "To, Allah ya nuna mana lokacin. Tashi ka dauko abincinka, ka ci ka koma makaranta, ka ga har karfe goma ta kusa yi, kada ka makara a yi maka bulala."
Abba ya shige daki domin cin abinci, ita kuma Maman Abba ta koma wurin wanke-wanke, tana tunani a cikin ranta, "Mhm! Yaro ba mutum ba, sai ya girma. Hakika masu ra'ayin cewa karatun boko haramun ne, suna jawo wa al'ummarsu babbar illa. Idan har muka yi sake 'ya'yanmu suka watsar da neman ilimin zamani, lallai su da jikokinsu, za su zama bayin 'yan kudancin kasar nan, masu neman ilimin zamani ido rufe, ta hanyar mamaye dukkan ma'aikatu, da masana'antu, da madafun ikon kasar nan. Allah ya ganar da su illar wannan ra'ayi nasu." Ta ci gaba da wanke-wankenta.
© Waziri Aku 2013
http://fb.com/waziriaku

Shin Ana Iya Ganin Annabi Ido Da Ido Ba Sai A Mafarki Ba?

*SHIN ANA IYA GANIN ANNABI IDO DA IDO BA SE A MAFARKI BA??!!*
.
Daga zauren
Khulafa'ur-rashiidun".
:
Assalamu alaikum Mlm
  Ina da tambaya da gske ana ganin Annabi ido da ido ko sai a mafarki ko a mafarkin ma baa ganin sa a huta lpy
:     
                ******
:
Wa,alaikumussalam

Ba'a ganin sa ido da ido, amma ana iya ganinsa amafarki, nankuma sekanada ilmin sanin siffarsa "ka karanta shama'ilil muhammadiyya, in sha ALLAHU, idan ka ganshi zaka gane shi"
.
Sedai Qarya ne mutum ko waye shi yazo yace wai ya hadu da Annabi Sallallahu alaihi wasallam ido da ido yabashi wani salati ko wata ibada wadda be baiwa sahabbansa ita ba Wannan kam qarya ne komai girman mutum munce qarya yakeyi tinda har rikici yafaru tsakanin sahabbai Radiyallahu anhum Annabi ko sau daya be ta6a bayyana yace wane shine akan dedai ba wane ba a kan gaskiya yake ba to damme wasu zasuce wai harms sun gashi a zahiri shin kun ta6a ji Aisha (Ra) da aka bunne Annabi Sallallahu alaihi wasallam a dakinta tace yataso ya gayamata wani abun??
.
Shin meyasa Annabi Sallallahu alaihi wasallam be bayyana ya warware matsalar data faru tsakanin Mu'awiya (Ra) Da Imamu Ali (Ra) ba meyasa be bayyana ba?? Kenan Masu qaryan cewa sunga Annabi Sallallahu alaihi wasallam a zahiri qarya suke ba Annabi suka ganiba.
.
Kwanakin nan naga wata fasiqa wai Annabi Sallallahu alaihi wasallam yazo dakinta cikin dare harma yabata Qur'ani kuma wai mujinta be ganshi ba se ita kadai ce ta ganshi abunda muke tambaya wai meyasa idan Annabi Sallallahu alaihi zezo baya zuwa dakin maza sedai mata?? Meyasa baya zuwa da rana se daddare?? Kunga Wannan ai Ikancine da raina hankulan jahilai saboda haka ba'a ganin Annabi Sallallahu alaihi wasallam a Fili ido da ido Amma ana iya mafarki dashi.
.
الله أعلم،
_Dalibin ku kamar kullum_
SANI ILYAS YAKASAI
_(Dan mama-Assalafy)_
========================
*```Date* ```[8-09-1439]Hj {24-05-2018}
  Kuna iya samun mu ta Internet/website http://khulafau.cf
_Masu buqatan Group suyima daya daga cikin Number's innan maga ta whatsApp_
+2349033206238
+2347035269582
+2348063796175
           *```Kuna iya samun mu ta facebook*```
facebook.com/khulafaurrashidun
((سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أشْهَدُ أنْ لَا إِلَهَ إِلاَّ أنْتَ، أسْتَغْفِرُكَ وأَتُوبُ إِلَيْكَ))
〰〰〰〰〰〰〰〰✔
*Wanda yaga gyara, yasanar damu !*

Sinadaran Girki

SINADARAN GIRKI🍲

A wannan post din nawa zaki samu takaitaccen bayani da idea yadda zakiyi anfani da sinadaran girki wato kayanwa kamshi na gida dana waje.

Wani jan hankali da zanyi anan shine,baa zabga spices a abinci,kadan kadan zaki dinga sakawa a girki,kuma kisan spices din da suke going well a kowanne girki,su kansu spices din sai kin san wanne ne yake tafiya da wanne,idan ba haka ba a karshe zaa rasa inda kamshin girkinki ya dosa!

1☀☀CLOVES (Kanunfari):-kanunfari sinadari ne mai matukar dadi a girki,musammam idan kika gano yadda zakiyi anfani dashi,kuma da irin abincin da ya dace ki saka shi..
*Duk lokacin da Zaki tafasa nama ki jepa Dan kanunfari Guda 2 ko uku
*idan zakiyi farfesun nama,kayan ciki,kifi ko kaza,ki tabbata kanunfari yana ciki.
*kanunfari yana dadi sosai a wajen anfani da nama,kuma a farkon girki ake saka shi!

2☀☀BLACK PEPPER(masoro):-masoro yana da dadin kamshi idan kika iya anfani dashi,yadda zakiyi amfani dashi kuwa shine.
*duk lokacin da zakiyi fried rice dinki,ki daka shi tare da tafarnuwa,zakiji banbanci
*ki daka masoro da albasa idan zakiyi miyar yauki,taji daddawa da gyadar miya,zaki ji banbanci!

3☀☀GARLIC(tafarnuwa) :-
Tafarnuwa sinadarin girki ce mai karawa abinci kamshi mai kwantar da hankalin mai chi,akwai hanyoyi da yawa yadda zakiyi anfani da ita..
*hada tafarnuwa da ginger ki saka a soup ko farfesun kayan ciki
*ki hada tafarnuwa da kanunfari ki saka a ruwan miyarki
*idan zakiyi (marinade) ki tabbata kin saka hadin tafarnuwa,ginger da kanunfari,kin hada su wuri daya kin daka su liqwi,ki saka a kaza ko nama..yana matukar dadi a wajen gashi,na nama ko kifi
*zaki iya daka ta ita kadai ki saka a jollof dinki
*amma kada ki soma anfani da ita a miyar yauki,dan kuwa baya dadi.

4☀☀GINGER(citta):- basai nace komai ba game da citta ba saboda duk inda zaayi anfani da kanunfari,masoro toh tabbas citta tana da matsuguni a wurin, ita citta tana da banbancin kamshi da fresh ginger,fresh ginger yafi dadi a lokacin da zakiyi anfani da tafarnuwa,ita kuma citta alokacin da zakiyi anfani da ragowae yen uwanta su masoro da kanunfari.

5☀☀KIMBA:-kimba itama tana cikin kayan kamshin da yawa mutane basu waye daita ba,tana matukar dadi idan zaki hada garin kununki na gero,ki tabbata tana ciki,ko kuma idan markaden kunune na hasara,shima a jefa ta ciki a markado da ita tare da sauran kayan kamshi su citta,kanunfari da masoro

6☀☀NUTMEG(gyadarmiya) :--
Idan ma bakya anfani da nutmeg to ki fara,saboda sinadari ce matukar kamshi a miyar yauki,kuka,kubewa karkashi da sauransu,tafi dadi ida kika hada ta da daddawa da masoro da yer citta kadan kika dakasu liqwi,ki saka a ruwan namanki idan zakiyi miyar yauki,kuma a farkon girki ake anfani ita,saboda idan ta dahu sosai,shine kamshinta zaifito sosai.

7☀☀CINNAMON (girfa):- Ina son girki da cinnamon,akwai na gari akwai kuma na stick,yana matukar dadi a shyi mai kyan kanshi,kuma yana dadi a home made drinks kamar su tamarind drink,milk shakes,ana saka cinnamon a baked foods kamar chocolates cakes,swissrolls,cinnamon rolls ,ana garnishing dashi,ana matukar dadi a soup na kayan ciki da kuma soup din nama.

8☀☀CURRY:- Curry sinadarin girki ne da kowa ya sanshi amma ba lallai yadda yakamat kike anfani dashi ba, hanya mafi kyau yadda zakiyi anfani da curry shine ki sakashi a farkon girkinki da kuma tsakiyar girki,misala idan jollof rice zakiyi ana saka shi a farko wajen bayan kin tsaida ruwan jollof dinki,idanya tafasa,kika zuba shinkafarki,tayi tafasa kamar biyu sai ki qara..

9☀☀THYME:- thyme yawanci anfi anfani da na kanti,amma akwai ganyen sa,wanda shima zaki iya anfani dashi ki saka a nama,kifi ko kaza, ana anfani da ganyen thyme a recipes na dankali yana matukar kawata abinci.

10☀☀POTASH(kanwa):-
Akwai ungurnu,akwai jar kanwa akwai ,bakar kanwa da sauransu,amma anfi anfani da ungurnu da kuma bakar kanwa,duk dai wacce kike anfani da ita,ba lokacin da zakiyi anfani da ita yakamata ki fara kokawar jikata ba,zaki samu robar lemo mai kyau ki wanke kanwarki ki zuba a robar sannan ki zuba ruwa ki cika tap,duk sanda zakiyi anfani da ita daman tana kusa sai tsiyaya a murfin robar ko chokali ki zuba a girkinki.

11☀☀TUMERIC:- wannan indian spices ne ,zaki ganshi yallow shar,kanshinshi bashi da karfi,yana da kyau a girki,domin yana kawata girki da wannan kalar tasa,misali zaki iya saka a farar shinkafa,ki dafa dashi kiyi garnishing da carrots da kume peas,yana kayu sosai,ana saka shi a recipes na dankali,idan zaayi fried chips zakiga yayi kala mai kyau,abin shaawa.

12☀☀PAPRIkA:- yana da dadi sosai a girki, gashi zaki ganshi da jar kala,ana saka shi stew,ana zaka shi a gashi kamar idan zakiyi gashin nama,kifi,kaza da sauransu,zakiga namanki yayi wani jar kala mai kyau,ana saka chi kuma a blend spice,idan zaki hada home made spices dinki

14☀☀CHILL POWDER:- chill combination ne na wasu spice,irinsu chili ,cumin ,oregano,cayyene da sauransu, zaki ji chill powder yana kamshi na musamman,kuma ana anfani da shi a miya da kuma kashin nama

15☀☀ALL SPICES:- all spice sinadarin girki ne mai zaman kansa,wanda da yawa mutane suna zaton wasu combination ne na spice,haka yake round kamae masoro ko kanunfari,yana da dadin kamshi a girki,ana saka shi a dahuwar nama,soup da kuma brown rice,ana saka shi a salad dressing da kuma spice mix.

16☀☀OREGANO:- sinadrin girki ne,zakiji shi da lemony flavor yana going perfectly da garlic da kuma curry a girki.

17☀☀BASIL:-wannan ganye ne wanda yake matukar dadi da kyau a pasta recipes ,kuma ana saka shi a sandwich da burger da sauransu.

18☀☀CILLANTRO/ CORIANDER:- da yawa anacewa cilantro da coriander leaves daya ne,kwai babncin suna ne aka samu, zaki ganshi kamar parsely leaves,sai dai yafi parsely haske,ana saka shi a recipe na nama,kaza,kifi da kuma vegetables.

19☀☀PARSELY:- parsely ganye ne kore shar,mai kyau a girki da kuma dadin kamshi,ana saka shi a minced meat,ko baked food,ana garnishing dashi,kuma ana saka shi a pasta recipe da recipes na dankali,yana kawata girki sosai.

20☀☀CHIVES:- chieves shine lawashin albasa,yana da dadi a nama,ko fate,ko kuma recipes na dambu,yana da kyau a wajen garnish,ana saka shi a recipes na dankali,zaki iya barinshi ya bushe,idan zakiyi wani recipe na flour ki marmasa shi,zai baki kala mai kyau,ko ki marnasashi a bread crumbs shima yana kyau,ko a saka shi a kwai idan zaka soya.

21☀☀MINT LEAVES:- Shine ganyen na'ana'a, dayawa an shayi ake anfani dashi,ana anfani da shi a recipes na drinks,kamar lemon tsamiya,mango drinks,milk shakes da sauransu,kuma yana dadi sosai a girki,ganshinsa yana da karfi,kadan ake saka wa a girki.

22☀☀SPINACH:- Spinach shine allayyahu ana saka shi a miyar agushi,miyar ganye,miyar taushes da sauransu,ana sakashi a alala,fate da kuma jollofs.ana saka shi ne a karshen girki.

23☀☀CUMIN:-sinarin girki zaki ganshi kanar buntun shinkafa, ana saka shi a kayn kamshi spices,kamar idan zakiyi home made spice,spice blend, ana saka shi a stews.

24☀☀CARDAMOM:-cardamon spices ne na indian cuisine,yana da dadin kamshi a girki,ana saka shi tare da su kanunfari ko cinnamon,kuna ana saka shi a baked foods.

25☀☀MEAT TENDARIZER:- sinadarin girki ne da ake sakawa a nama,especially nama mai tauri,zaki fara sakawa a nama yayi wasu yen mintuna sannan ki dora,yana taimakawa sosai namanki ya dahu da wuri.

26☀☀7 SPICES:-wannan combination ne na kayn kamshi,yan matukse dadi a brown rice ,fried spagetti da kuma soups.

SUMMARY LIST:-ga list na spices din ake samu a kantuna masu dadin kamshi da kuma kawata girki akwai na kanmpanin "spice supreme" "ducros" da sauransu

1 Curry
2 Thyme
3 Garlic powder
4 Ginger
5 chicken seasoning
6 fish seasoning
7 chill powder
8 paprika
9 whike oregano
10 meat tendarizer
11 Italian seasoning
12 Ground tumeric
13 parsely flackes
14 barbecue spices
15 ground cinnamon
16 onion powder
17 pizza seasoning
18 French fries seasoning
19 7spices
20 All spices
21 oriental 5-spices
22 ground black pepper
23 vegetable flakes
24 roast beef seasoning
25 Fried rice spices
26 jollof rice spicesSINADARAN GIRKI🍲

A wannan post din nawa zaki samu takaitaccen bayani da idea yadda zakiyi anfani da sinadaran girki wato kayanwa kamshi na gida dana waje.

Wani jan hankali da zanyi anan shine,baa zabga spices a abinci,kadan kadan zaki dinga sakawa a girki,kuma kisan spices din da suke going well a kowanne girki,su kansu spices din sai kin san wanne ne yake tafiya da wanne,idan ba haka ba a karshe zaa rasa inda kamshin girkinki ya dosa!

1☀☀CLOVES (Kanunfari):-kanunfari sinadari ne mai matukar dadi a girki,musammam idan kika gano yadda zakiyi anfani dashi,kuma da irin abincin da ya dace ki saka shi..
*Duk lokacin da Zaki tafasa nama ki jepa Dan kanunfari Guda 2 ko uku
*idan zakiyi farfesun nama,kayan ciki,kifi ko kaza,ki tabbata kanunfari yana ciki.
*kanunfari yana dadi sosai a wajen anfani da nama,kuma a farkon girki ake saka shi!

2☀☀BLACK PEPPER(masoro):-masoro yana da dadin kamshi idan kika iya anfani dashi,yadda zakiyi amfani dashi kuwa shine.
*duk lokacin da zakiyi fried rice dinki,ki daka shi tare da tafarnuwa,zakiji banbanci
*ki daka masoro da albasa idan zakiyi miyar yauki,taji daddawa da gyadar miya,zaki ji banbanci!

3☀☀GARLIC(tafarnuwa) :-
Tafarnuwa sinadarin girki ce mai karawa abinci kamshi mai kwantar da hankalin mai chi,akwai hanyoyi da yawa yadda zakiyi anfani da ita..
*hada tafarnuwa da ginger ki saka a soup ko farfesun kayan ciki
*ki hada tafarnuwa da kanunfari ki saka a ruwan miyarki
*idan zakiyi (marinade) ki tabbata kin saka hadin tafarnuwa,ginger da kanunfari,kin hada su wuri daya kin daka su liqwi,ki saka a kaza ko nama..yana matukar dadi a wajen gashi,na nama ko kifi
*zaki iya daka ta ita kadai ki saka a jollof dinki
*amma kada ki soma anfani da ita a miyar yauki,dan kuwa baya dadi.

4☀☀GINGER(citta):- basai nace komai ba game da citta ba saboda duk inda zaayi anfani da kanunfari,masoro toh tabbas citta tana da matsuguni a wurin, ita citta tana da banbancin kamshi da fresh ginger,fresh ginger yafi dadi a lokacin da zakiyi anfani da tafarnuwa,ita kuma citta alokacin da zakiyi anfani da ragowae yen uwanta su masoro da kanunfari.

5☀☀KIMBA:-kimba itama tana cikin kayan kamshin da yawa mutane basu waye daita ba,tana matukar dadi idan zaki hada garin kununki na gero,ki tabbata tana ciki,ko kuma idan markaden kunune na hasara,shima a jefa ta ciki a markado da ita tare da sauran kayan kamshi su citta,kanunfari da masoro

6☀☀NUTMEG(gyadarmiya) :--
Idan ma bakya anfani da nutmeg to ki fara,saboda sinadari ce matukar kamshi a miyar yauki,kuka,kubewa karkashi da sauransu,tafi dadi ida kika hada ta da daddawa da masoro da yer citta kadan kika dakasu liqwi,ki saka a ruwan namanki idan zakiyi miyar yauki,kuma a farkon girki ake anfani ita,saboda idan ta dahu sosai,shine kamshinta zaifito sosai.

7☀☀CINNAMON (girfa):- Ina son girki da cinnamon,akwai na gari akwai kuma na stick,yana matukar dadi a shyi mai kyan kanshi,kuma yana dadi a home made drinks kamar su tamarind drink,milk shakes,ana saka cinnamon a baked foods kamar chocolates cakes,swissrolls,cinnamon rolls ,ana garnishing dashi,ana matukar dadi a soup na kayan ciki da kuma soup din nama.

8☀☀CURRY:- Curry sinadarin girki ne da kowa ya sanshi amma ba lallai yadda yakamat kike anfani dashi ba, hanya mafi kyau yadda zakiyi anfani da curry shine ki sakashi a farkon girkinki da kuma tsakiyar girki,misala idan jollof rice zakiyi ana saka shi a farko wajen bayan kin tsaida ruwan jollof dinki,idanya tafasa,kika zuba shinkafarki,tayi tafasa kamar biyu sai ki qara..

9☀☀THYME:- thyme yawanci anfi anfani da na kanti,amma akwai ganyen sa,wanda shima zaki iya anfani dashi ki saka a nama,kifi ko kaza, ana anfani da ganyen thyme a recipes na dankali yana matukar kawata abinci.

10☀☀POTASH(kanwa):-
Akwai ungurnu,akwai jar kanwa akwai ,bakar kanwa da sauransu,amma anfi anfani da ungurnu da kuma bakar kanwa,duk dai wacce kike anfani da ita,ba lokacin da zakiyi anfani da ita yakamata ki fara kokawar jikata ba,zaki samu robar lemo mai kyau ki wanke kanwarki ki zuba a robar sannan ki zuba ruwa ki cika tap,duk sanda zakiyi anfani da ita daman tana kusa sai tsiyaya a murfin robar ko chokali ki zuba a girkinki.

11☀☀TUMERIC:- wannan indian spices ne ,zaki ganshi yallow shar,kanshinshi bashi da karfi,yana da kyau a girki,domin yana kawata girki da wannan kalar tasa,misali zaki iya saka a farar shinkafa,ki dafa dashi kiyi garnishing da carrots da kume peas,yana kayu sosai,ana saka shi a recipes na dankali,idan zaayi fried chips zakiga yayi kala mai kyau,abin shaawa.

12☀☀PAPRIkA:- yana da dadi sosai a girki, gashi zaki ganshi da jar kala,ana saka shi stew,ana zaka shi a gashi kamar idan zakiyi gashin nama,kifi,kaza da sauransu,zakiga namanki yayi wani jar kala mai kyau,ana saka chi kuma a blend spice,idan zaki hada home made spices dinki

14☀☀CHILL POWDER:- chill combination ne na wasu spice,irinsu chili ,cumin ,oregano,cayyene da sauransu, zaki ji chill powder yana kamshi na musamman,kuma ana anfani da shi a miya da kuma kashin nama

15☀☀ALL SPICES:- all spice sinadarin girki ne mai zaman kansa,wanda da yawa mutane suna zaton wasu combination ne na spice,haka yake round kamae masoro ko kanunfari,yana da dadin kamshi a girki,ana saka shi a dahuwar nama,soup da kuma brown rice,ana saka shi a salad dressing da kuma spice mix.

16☀☀OREGANO:- sinadrin girki ne,zakiji shi da lemony flavor yana going perfectly da garlic da kuma curry a girki.

17☀☀BASIL:-wannan ganye ne wanda yake matukar dadi da kyau a pasta recipes ,kuma ana saka shi a sandwich da burger da sauransu.

18☀☀CILLANTRO/ CORIANDER:- da yawa anacewa cilantro da coriander leaves daya ne,kwai babncin suna ne aka samu, zaki ganshi kamar parsely leaves,sai dai yafi parsely haske,ana saka shi a recipe na nama,kaza,kifi da kuma vegetables.

19☀☀PARSELY:- parsely ganye ne kore shar,mai kyau a girki da kuma dadin kamshi,ana saka shi a minced meat,ko baked food,ana garnishing dashi,kuma ana saka shi a pasta recipe da recipes na dankali,yana kawata girki sosai.

20☀☀CHIVES:- chieves shine lawashin albasa,yana da dadi a nama,ko fate,ko kuma recipes na dambu,yana da kyau a wajen garnish,ana saka shi a recipes na dankali,zaki iya barinshi ya bushe,idan zakiyi wani recipe na flour ki marmasa shi,zai baki kala mai kyau,ko ki marnasashi a bread crumbs shima yana kyau,ko a saka shi a kwai idan zaka soya.

21☀☀MINT LEAVES:- Shine ganyen na'ana'a, dayawa an shayi ake anfani dashi,ana anfani da shi a recipes na drinks,kamar lemon tsamiya,mango drinks,milk shakes da sauransu,kuma yana dadi sosai a girki,ganshinsa yana da karfi,kadan ake saka wa a girki.

22☀☀SPINACH:- Spinach shine allayyahu ana saka shi a miyar agushi,miyar ganye,miyar taushes da sauransu,ana sakashi a alala,fate da kuma jollofs.ana saka shi ne a karshen girki.

23☀☀CUMIN:-sinarin girki zaki ganshi kanar buntun shinkafa, ana saka shi a kayn kamshi spices,kamar idan zakiyi home made spice,spice blend, ana saka shi a stews.

24☀☀CARDAMOM:-cardamon spices ne na indian cuisine,yana da dadin kamshi a girki,ana saka shi tare da su kanunfari ko cinnamon,kuna ana saka shi a baked foods.

25☀☀MEAT TENDARIZER:- sinadarin girki ne da ake sakawa a nama,especially nama mai tauri,zaki fara sakawa a nama yayi wasu yen mintuna sannan ki dora,yana taimakawa sosai namanki ya dahu da wuri.

26☀☀7 SPICES:-wannan combination ne na kayn kamshi,yan matukse dadi a brown rice ,fried spagetti da kuma soups.

SUMMARY LIST:-ga list na spices din ake samu a kantuna masu dadin kamshi da kuma kawata girki akwai na kanmpanin "spice supreme" "ducros" da sauransu

1 Curry
2 Thyme
3 Garlic powder
4 Ginger
5 chicken seasoning
6 fish seasoning
7 chill powder
8 paprika
9 whike oregano
10 meat tendarizer
11 Italian seasoning
12 Ground tumeric
13 parsely flackes
14 barbecue spices
15 ground cinnamon
16 onion powder
17 pizza seasoning
18 French fries seasoning
19 7spices
20 All spices
21 oriental 5-spices
22 ground black pepper
23 vegetable flakes
24 roast beef seasoning
25 Fried rice spices
26 jollof rice spices

BY ADMIN
Maman humaira
🍎🍇 DUNIYAR KICHEN 🍇🍎

It Is Not Always Easy Being A Teacher

ITS NOT ALWAYS EASY BEING A TEACHER

Teacher: How old is your father?
Kid: He is 6 years.
Teacher: What? How is this possible?
Kid: He became father only when I was born.
(Logic!! Children are quick and always speak their minds.)
_____________________
TEACHER: Maria, go to the map and find North America.
MARIA: Here it is.
TEACHER: Correct. Now, Class, who discovered America?
CLASS: Maria.
_____________________
TEACHER: Habib, how do you spell 'crocodile?'
Habib: K-R-O-K-O-D-I-A-L'
TEACHER: No, that's wrong
Habib: Maybe it is wrong, but you asked me how I spell it.
(I love this child.)
_____________________
TEACHER: Sadeeq, what is the chemical formula for water?
Sadeeq: H I J K L M N O.
TEACHER: What are you talking about?
Sadeeq: Yesterday you said it's H to O.   
______________________
TEACHER: Yusuf, your composition on 'My Dog' is exactly the same as your brother's. Did you copy his?
Yusuf: No, sir; It's the same dog.   
(I want to adopt this kid!!!)
___________________
TEACHER: Ali, what do you call a person who keeps on talking when people are no longer interested?
Ali: A teacher.
______________________________
PASS THIS AROUND AND MAKE SOMEONE LAUGH!
LAUGHTER IS THE SOUL'S MEDICINE!! Tag any teacher you know.😁😁😁😁

Hattara Iyaye Da Mazaje

*Hattara Iyaye da Mazaje*

✍ *Dr.Mansur Sokoto*

Na kalli wani faifan video da ake watsawa na wani karatu mai ban tausayi da ban takaici hade da mamaki. Ba zan iya tura ma kowa shi ba. Amma ina son in yi wata fadakarwa a nan.
- Ya zama wajibi mu kula da yayanmu tun suna kanana; mu koya masu addini. Ina amfanin mutum ya girma yana jahili?
- Mazaje su binciki karatun iyalansu. Allah zai tambayi kowane magidanci akan karatun iyalansa.
- Ba a girma ga yin karatu, ba a tsufa ga neman sanin addini. Don Allah duk wanda ya san akwai bukatar gyaran karatun sallarsa ya/ta nemi malami/malama mai koya masa/mata. A lahira Allah ba ya karbar hanzarin wanda ya ce bai sani ba ko bai iya ba.
- Yan siyasa su daina bayyana wallensu a gaban jama'a ta hanyar kuri da takama da sanin addini alhalin ba su sani ba.
Daga karshe, mu sani, in Allah ya yi uzuri ga mutanen kowane zamani game da jahiltar addini ba zai yi uzuri gare mu ba a wannan zamani saboda hanyoyin karatu sun yawaita sun saukaka kuma sun game duniya.
Allah ya yi muna muwafaqa ya sa mu gyara karatunmu da halayenmu.

YADDA AKE DECORATION ƊIN CAKE

🍴BUDA'S_KITCHEN🍽

Yadda zaki decoration na cake dinki

Dafarko bayan kin gama baking cake dinki
Zaki duba cake dinki kigani gasuwarsa tayi level idan bai yiba zaki saka wuka mai kaifi wadda ba asa mata albasa sai ki yayyanke inda bai daidaitaba.
Idan cake dinki 2 layer ne
Zaki shafa cream dinki akan board din da zakiyi decoration akanshi sai ki dora cake dinki layer na farko....yadai daita sosai sai ki shafa cream din asaman layer na farkon
Sai ki dauko dayn ma ki dora.daganan zaki fara shafa cream dinki ajikin cake dinki da spatula..kina shafawa kina goge spatula din idan kinsu ma zaki iya ajiye ruwan sanyi a bowl kina yi kina wanke spatula din kin kara smooth din cake din nakii..har yayi smooth sosai
..sai kuma kizo wajan zanan adon dakikeso akwai differnt types of nozzles duk wanda kakeso zaka iyayi....
 
CEO @budas_cakes_nd_more

FARA KOYON MULKI DA BAKI KAFIN KA KOYI MULKI DA HANNU

FARA KOYON MULKI DA BAKI KAFIN KA KOYI MULKI DA HANNU

Wata rana wadansu gauraki guda biyu suka gane wani itacen baure a bakin wani rafi. Kullum suka tashi sai su nufi can su hau, su yi ta ci.
Gindin bauren nan kuwa ashe akwai wani kunkuru. Kullum idan gaurakin na cin baure, wadansu ‘ya’yan su kan kucce musu su fado kasa. Da kunkuru ya ga suna fado masa yana ci, sai ya yi tsammani gaurakin nan ke ba shi kyauta, don suna sonsa. Saboda haka, da ya ga alherin ya yi yawa, ran nan sai ya daga kansa ya dubi gauraki, ya ce, “Kai ‘yan’uwana, na gode! Kullum dai na kan ga ‘ya’yan bauren da ku ke sako mini. Abin maku ya yi yawa, wallahi har kunyar godiya na ke yi. Allah dai ya saka da alheri!”
Da gauraki suka ji haka, suka duba suka gan shi, sai suka gane abin da ke aukuwa.
Da har babbar za ta ce masa su ba a kan sonsu bauren ke zuwa gare shi ba, sai karamar ta hana ta. Ta dubi kunkuru ta ce, “Don mun ga kai ba ka iya hawowa, shi ya sa mu da Allah ya ba fiffike mu ke taimakonka. Don dan wannan abu kada ka sa wa kanka wani jin kunya ciki. Allah dai ya bar zumunci.”
Kunkuru ya ce, “Amin! Na ko yi godiya.”
Suka zauna kan haka. Da abu kamar wasa, har ya zama aminci na gaskiya. Gaurakin nan da sun zo da safe, ba abin da su ke fara yi sai sun tambayi kwanan kunkuru tukun. Suka zauna, ba su son abin da ya taba shi, shi kuma ba ya son abin da ya taba su.
Ana nan, bayan kamar wata guda baure ya kare, gauraki suka koma neman kwadi da tana. Bayan kamar wata biyu kuma dan sauran ruwan rafin ya kafe. Wurin ya koma sai ka ce dadai duniya ruwa bai taba zama nan ba.
Da gauraki suka ga haka, sai suka yi shawarar su tashi su sake wuri, don ba su iya zama sai inda ke da danshi-danshi.
Ran nan har za su wuce, sai karamar ta ce, “Ya kamata mu je mu sallami kunkuru, kada ya ga shiru hankalinsa ya tashi, ya yi zaon wani abu ne ya same mu.” Suka tashi, suka tafi wajen kunkuru, suka gaya masa za su yi kaura.
Da kunkuru ya ji haka, sai ya ce, “Af, to, ai ba ku barina, sai mu tafi tare. Abin da ya yi Goje, ai shi ya yi Kaura. Ni ina na ke iya zama inda babu laima?”
Da gauraki suka ji haka, sai suka ce, “Yaya za ka yi ka bi mu, alhali kuwa kai ba ka da fiffike?”
Kunkuru ya ce, “Sai ku dauke ni, in kun ga kwa iya kokarin hakanan.”
Babbar gaurakar ta ce, “Wa ka ke zato cikimmu zai yia daukar kato kamarka? To, ce ma muna iyawa, ina za a kama, ga ka jiki duk kwarya?”
Karamar ta ce, “Bar shi, mu ji tasa, watakila yana da dabara, Kin san an ce mai rai ba ya rasa kokari.”
Kunkuru ya ce, “I, ina kuwa da wata ‘yar gurguwar dabara, in kwa iya. Sai mu sami kara mai karfi kamar zira'i biyu, ni in cije tsakiyar, ku kuma kowace ta kama gefe guda da baki. Kun ga da haka sai ku tashi da ni har inda za ku.”
Babbar ta ce, “Wannan dabarar ban ga za ta yiwu ba ga kamarka, mai surutu.”
Karamar ta ce, “A’a, in ya ce dai ya iya kyalewa, sai sai mu dauke shi.”
Ta tashi, ta tafi ta samo karan dawa mai karfi, ta dauko, ta zo ta ajiye gaban kunkuru. Ta dube shi, ta ce, “To, don Allah in ka kama, ban da yawan magana.”
Kunkuru ya ce, “Haba, wannan ma sai an dankwafe ni kansa, sai ke ce yaro? In yi surutu mana, in ina so!”
Gauraki suka ce, “To, madalla!” Suka kama kara suka tashi da kunkuru yana cije.
Suna cikin tafiya, sai hanya ta dauke su ta bisan kasuwa. Suna kaiwa tsakiyar, sai mutane suka daga kai suka hange su, suka ce “Eho, eho, ku zo ku ga inda gauraki ke daukar kunkuru! Kai jama’a. abin mamaki ba ya karewa nan duniya!”
Da kunkuru ya ji haka, sai ya fusata ya ce, “Kai, Allah ya tsine idandunan nan naku mutane, da ba su iya ganin abu su kyale.”
Bai gama fadin abin da ya ke nufi ba, sai da ya kawo kasa kum.
Gauraki suka wuce abinsu suna bakin ciki, suna cewa “Wanda duk bai iya mulki da bakinsa ba, la
lle yana tare da halaka.”

ƘOSAN ROGO

🍝MrS MuS@'S KiTcHeN
           MuM HeeLaL


           *QOSAN ROGO*
            🥞🥞🥞🥞🥞

Ingredient:
🥞Garin rogo
🥞Attarugu
🥞Albasa
🥞Maggi
🥞Mai
🥞Curry nd thyme           ~Yadda zakiyi~
_Da farko zaki kawo gari saiki zuba a roba ko kwano mai murfi saiki dara ruwa ya tafasa idn yah tafasa saiki juye a cikin garin ki ki rufe saiki bayan miti 5 hka saiki bude ki juya har yah hada jikin sa saiki rufe, saiki koma ki gyara kayan miyarki ki tarugu da albasa Saiki zuba a turmi ki daka idn idn suka daku saiki zuba maggi da sauran kayan dandano ki saiki cigaba da dakawa idn kk daka saiki kawo garin tebarki ki juye a turmin saiki hada ki daka har yah hade da kayan miyar, idn yah hade saiki kwashi ki maida a kwanon saiki rinqa debowa a hannu ki kina fadi dashi kina dan tataba shi da hannu ki guda daya idn kk gama duka saiki sa Mai a wuta ki fara suya idn ya soyu saiki kwashi..aci dadi lpy_ 😋


~BY~
         ✍🏻Admin MrS MuS@ Mb MuM HeeLaL~📲+234 977557005~


🥞🥞🥞🥞🥞🥞🥞🥞

Monday, 21 January 2019

SAƘONNIN BARKA DA SAFIYA 01

Farin Ciki Ba Shi ne Samun Duk Abinda Ranka Ke Bukata Ba, Farin Ciki Shine Samun Wadatar Zuciya Da Haquri Da Abinda Allah Ya Hore Maka... Manzon Allah (S.A.W.) Yace "Yawan Dukiya Ba Shine Arziki Ba, Wadatar Zuciya Shine Babban Arziki"!!!

Barka da safiya

PRINCE AHMAD AND THE FAIRY 13

🏻 *_PRINCE AHMAD AND THE FAIRY_* 🧚🏻‍♀🧚🏻‍♀🧚🏻‍♀

          *Part 13*
 _________/\________

He need but lead the way; I will follow him,' replied Schaibar.
'Brother,' replied Pari Banou, 'it is too late to go to-day, therefore stay till to-morrow morning; and in the meantime, as it is desirable that you should know all that has passed between the Sultan of the Indies and Prince Ahmed since our marriage, I will tell you this evening.'
Next morning, after Schaibar had been informed of all that was proper for him to know, he set out with Prince Ahmed, who was to present him to the sultan. When they arrived at the gates of the capital, the people no sooner saw Schaibar than they ran and hid themselves in their shops and houses, and shut their doors; while others took to their heels, and communicated their fear to all they met, who did not wait to look behind them, but ran too; insomuch that Schaibar and Prince Ahmed, as they went along, found all the streets and squares deserted, till they came to the palace, where the porters, instead of preventing Schaibar from entering, also ran away; so that the prince and he advanced without any obstacle to the council-hall, where the sultan was seated on his throne giving audience. Here likewise the officers, at the approach of Schaibar, abandoned their posts.

Schaibar, carrying his head erect, went fiercely up to the throne, without waiting to be introduced by Prince Ahmed, and accosted the Sultan of the Indies in these words:
'You have asked for me, see, here I am: what do you want with me?'
The sultan, instead of answering, clapt his hands before his eyes, and turned away his head, to avoid the sight of so terrible an object. Schaibar was so much provoked at this uncivil and rude reception, after the Sultan had given him the trouble to come so far, that he instantly lifted up his iron bar, and saying, 'Speak then,' let it fall on his head, and killed him before Prince Ahmed could intercede in his behalf. All that he could do was to prevent his killing the grand vizier, who sat not far from him on his right hand, representing to him that he had always given the sultan his father good advice.

'These are they then,' said Schaibar, 'who gave him bad advice;' and as he pronounced these words, he killed all the other viziers on the right and left, flatterers and favourites of the sultan, who were Prince Ahmed's enemies. Every time he struck, he killed some one or other, and none escaped but they who, not rendered motionless by fear, saved themselves by flight.
When this terrible execution was over, Schaibar came out of the council-hall into the midst of the court-yard with the iron bar on his shoulder, and looking at the grand vizier, who owed his life to Prince Ahmed, he said, 'I know there is a certain sorceress, who is a greater enemy of the prince my brother-in-law than all those base favourites I have chastised; let her be brought to me at once.' The grand vizier immediately sent for her, and as soon as she was brought, Schaibar said, knocking her down with his iron bar, 'Take the reward of thy pernicious counsel, and learn to feign illness again:' and left her dead on the spot.
After this he said, 'This is not enough; I will treat the whole city in the same manner, if they do not immediately acknowledge Prince Ahmed my brother-in-law for their sultan, and Sultan of the Indies.' Then all that were present made the air ring with the repeated acclamations of 'Long life to Sultan Ahmed'; and immediately afterwards he was proclaimed throughout the whole town Schaibar made him be clothed in the royal vestments, installed him on the throne, and after he had made all do homage and fidelity to him, went and fetched his sister Pari Banou, whom he brought with great pomp, and made her acknowledged Sultaness of the Indies.

As for Prince Ali and Princess Nouronnihar, as they had no hand in the conspiracy against Prince Ahmed, nor knew of any such conspiracy, Prince Ahmed assigned them a considerable province, with its capital, where they spent the rest of their lives. Afterwards he sent an officer to Prince Houssain to acquaint him with the change, and to make him an offer of whichever province he liked best; but that prince thought himself so happy in his solitude that he bade the officer return the Sultan his brother thanks for his kindness, assuring him of his submission; and saying that the only favour he desired was leave to live retired in the place he had made choice of for his retreat.

<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________

●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...

PRINCE AHMAD AND THE FAIRY 12

🏻 *_PRINCE AHMAD AND THE FAIRY_* 🧚🏻‍♀🧚🏻‍♀🧚🏻‍♀

          *Part 12*
 _________/\________

'Sir,' replied Prince Ahmed, 'I have no share in the compliment your majesty is pleased to make me; all the honour is due to the fairy my wife; I merely followed her good advice.' The sultan showed outwardly all the demonstrations of joy, but secretly became more and more jealous, retired into an inner apartment, and sent for the magician.
After conferring with her, the sultan next day said to the prince, in the midst of all his courtiers, 'Son, I have one thing more to ask of you; after which, I shall expect nothing more from your obedience, nor your influence with your wife. This request is, to bring me a man not above a foot and a half high, whose beard is thirty feet long, who carries upon his shoulders a bar of iron of five hundredweight which he uses as a quarterstaff, and who can speak.'

Prince Ahmed, who did not believe that there was such a man in the world as his father described, would gladly have excused himself; but the sultan persisted in his demand, and told him that the fairy could do more incredible things.
Next day the prince returned to the subterranean kingdom of Pari Banou, to whom he told his father's new demand, which, he said, he looked upon as more impossible than the first two; 'for,' added he, 'I cannot imagine that there is or can be such a man in the world: either he has a mind to try whether I am silly enough to go and seek him; or if there is such a man, he seeks my ruin. How can he suppose that I should get hold of a man so small, armed as he describes? What arms could I make use of to reduce him to submission?'

'Do not affright yourself, prince,' replied the fairy; 'you ran a risk in fetching the water of the fountain of lions for your father; but there is no danger in finding this man. It is my brother, Schaibar, who is so far from being like me, though we both had the same father, that he is of so violent a nature that nothing can prevent his giving gory marks of his resentment for a slight offence; yet, on the other hand, he is so good as to oblige any one in whatever they desire. He is made exactly as the sultan your father has described him; and he has no other arms than a bar of iron five hundred pounds in weight, without which he never stirs, and which makes him respected. I will send for him, and you shall judge of the truth of what I tell you; and prepare not to be frightened when you see him.'
'What! my queen,' replied Prince Ahmed, 'do you say Schaibar is your brother? Let him be ever so ugly or deformed, I shall love and honour him, and consider him as my nearest relation.'
The fairy ordered a gold chafing-dish to be set with a fire in it under the porch of her palace, with a box of the same metal. Taking some incense out of this, and throwing it into the fire, there arose a thick cloud of smoke.


Some moments after, the fairy said to Prince Ahmed, 'Prince, here comes my brother; do you see him?'
The prince immediately perceived Schaibar, who was but a foot and a half high, coming gravely with his heavy bar on his shoulder; his beard, thirty feet long, supported itself before him, and a pair of thick moustaches were tucked up to his ears, almost covering his face: his eyes were very small, like a pig's, and sunk deep in his head, which was of an enormous size, and on which he wore a pointed cap: besides all this, he had a hump behind and before.
If Prince Ahmed had not known that Schaibar was Pari Banou's brother, he would not have been able to look at him without fear; but knowing beforehand who he was, he waited for him with the fairy, and received him without the least concern.

Schaibar, as he came forward, looked at the prince with an eye that might have chilled his soul in his body, and asked Pari Banou who that man was.
To which she replied: 'He is my husband, brother; his name is Ahmed; he is son to the Sultan of the Indies. The reason why I did not invite you to my wedding was that I was unwilling to divert you from the expedition you were engaged in, and from which I heard with pleasure that you returned victorious; on his account I have taken the liberty now to send for you.'
At these words, Schaibar, looking at Prince Ahmed with a favourable eye, which however diminished neither his fierceness nor his savage look, said, 'Is there anything, sister, in which I can serve him? he has only to speak. It is enough for me that he is your husband.'
'The sultan his father,' replied Pari Banou, 'has a curiosity to see you, and I desire he may be your guide to the Sultan's court.'


To be continued.

<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________

●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...

PRINCE AHMAD AND THE FAIRY 11

🏻 *_PRINCE AHMAD AND THE FAIRY_* 🧚🏻‍♀🧚🏻‍♀🧚🏻‍♀

          *Part 11*
 _________/\________

Prince Ahmed, who had believed that the sultan his father would have been satisfied with so singular and useful a tent as that which he had brought, and that he would not have imposed any new task upon him which might hazard the fairy's displeasure; was thunderstruck at this new request, notwithstanding the assurance she had given him of granting him whatever lay in her power. After a long silence, he said, 'I beg of your majesty to be assured that there is nothing I would not undertake to prolong your life, but I wish it might not be by means of my wife. For this reason I dare not promise to bring the water. All I can do is to assure you I will ask her; but it will be with as great reluctance as when I asked for the tent.'

The next morning Prince Ahmed returned to the fairy Pari Banou, and related to her sincerely and faithfully all that had passed at the sultan his father's court, from the giving of the tent, which he told her he received with the utmost gratitude, to the new request he had charged him to make, and when he had done, he added: 'but, my princess, I only tell you this as a plain account of what passed between me and my father. I leave you to your own discretion to gratify or reject this new desire. It shall be as you please.'
'No, no,' replied the fairy Pari Banou, 'whatever advice the magician can give him (for I see that he hearkens to her), he shall find no fault with you or me. There is a great deal of wickedness in this demand, as you will understand by what I am going to tell you. The fountain of lions is situated in the middle of a court of a great castle, the entrance into which is guarded by four fierce lions, two of which sleep while the other two are awake alternately. But let not that frighten you. I will give you means to pass by them without any danger.'

The fairy Pari Banou was at that time hard at work with her needle; and as she had by her several balls of thread, she took up one, and presenting it to Prince Ahmed, said, 'First take this ball of thread; I will tell you presently the use of it. In the second place, you must have two horses; one you will ride yourself, and the other you will lead, which must be loaded with a sheep cut into four quarters, and killed to-day. In the third place, you must be provided with a bottle, which I will give you, to bring the water in. Set out early to-morrow morning, and when you have passed the iron gate, throw before you the ball of thread, which will roll till it comes to the gates of the castle. When it stops, as the gates will be open, you will see the four lions. The two that are awake will, by their roaring, wake the other two. Be not frightened, but throw each of them a quarter of the sheep, and then clap spurs to your horse, and ride to the fountain. Fill your bottle without alighting, and then return with the same speed. The lions will be so busy eating that they will let you pass.'

Prince Ahmed set out the next morning at the time appointed by the fairy, and followed her directions carefully. When he arrived at the gates of the castle, he distributed the quarters of the sheep among the four lions, and passing through the midst of them with haste, got to the fountain, filled his bottle, and returned as safe and sound as he went. When he was a little distance from the castle gates, he turned round; and perceiving two of the lions coming after him, he drew his sabre, and prepared for defence. But as he went forward, he saw one of them turned off the road, and showed by his head and tail that he did not come to do him any harm, but only to go before him, and that the other stayed behind to follow. He therefore put his sword again into its scabbard. Guarded in this manner he arrived at the capital of the Indies; but the lions never left him till they had conducted him to the gates of the sultan's palace; after which they returned the way they came, though not without frightening all that saw them, who fled or hid themselves, though they walked gently, and showed no signs of fierceness.

A great many officers came to attend the prince while he dismounted, and conducted him to the apartments of the sultan, who was at that time conversing with his favourites. He approached the throne, laid the bottle at the sultan's feet, kissed the rich carpet which covered the footstool, and rising, said, 'I have brought you, sir, the health-giving water which your majesty so much desired to keep in your treasury; but at the same time wish you such health that you may never have occasion to make use of it.'

After the prince had finished speaking, the sultan placed him on his right hand, and then said, 'Son, I am very much obliged to you for this valuable present; also for the great danger you have exposed yourself to upon my account, which I have been informed of by the magician who knows the fountain of lions; but do me the pleasure,' continued he, 'to tell me by what incredible power you have been preserved.'

To be continued.

<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________

●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees 

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees 

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees 
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...

GIBA

*TINATARWA (GIBA)🤐*👉🏼 _*SA'ID BIN ABI RUBAH...>* Yace, angayamana cewa azabar kabari kashi uku neh (3)_
_(1) Saboda Giba. (2)Saboda rashin kiyaye fitsari. (3) Saboda annamimanci._

👉🏼 _*YAHYA BIN UKSUM YA CE:* Mai gulma yafi mai sihiri sharri._

👉🏼 _*HASSANUN BASARY YA CE:* Duk wanda ya kawo maka zancen wani, to ba shakka kai ma zai kai zancen ka wajen wani._

👉🏼 _*MUJAHID DAGA IBN ABBAS YA CE:* Idan ka yi nufin ka ambaci aibun abokinka, to ka fara ambaton aibun kanka._

👉🏼 _*HAFS IBN USMAN YA CE:* Umar Dan Khattab ya ce, kada ku shagaltar da kanku wajen ambaton aibun mutane domin yin hakan musiba ce, ku rika ambaton Allah domin yin hakan rahama neh._

👉🏼 _*QAIS IBN HAZIM YA CE:* Ammar Ibn Ass ya wuce ta gaban wani mushen alfadari sai ya cewa abokansa wallahi dayanku ya cika cikinsa da naman wannan mushen yafi masa alheri akan yaci naman dan uwansa musulmi._

👉🏼 _*AUN IBN ABDULLAHI YA CE:* Ban ta6a son mutumin da ya 6ata lokacinsa akan binciken aibun mutane ba domin bai yi haka ba sai don rafkana da takaicin zuciyarsa wadda ta hana shi shagaltuwa da aibun kansa._

👉🏼 _*BAKAR IBN ABDULLAHI YA CE:* Idan ku ka ga mutum ya shagaltar da kansa da ambaton aibun mutane alhali ya manta da nasa aibun to lallai ku sani cewa anyi masa mummunar tanadi a lahira._

👉🏼 _*AHNAF IBN QAIS YA CE:* Banta6a ambaton aibun wani mutum ba bayan ya tashi daga wajena._

🖋 _Sau da dama za ka ga mun tsaya muna gulmar wasu daga cikin mu wadanda ke aikata wani laifi alhali yin hakan babban laifi ne._
  _Watakila ma yafi laifin wadanda muke gulmarsu domin ita gulma laifi ne guda biyu._

*(1) Ansa6ama Allah (SWT)*
*(2) Ko da ka tuba sai ka nemi yafiyar wanda kayi gulmarsa tukun.*

 _Watakil ma wanda muke yin gulmarsa laifinsa bai kai haka girma ba don haka ya kamata mu lura da kyau sosae akan gulma *(GIBA)*_

SIGOGIN ISTIGHFARI KALA TAKWAS

*_SIGOGIN ISTIGHFARI KALA TAKWAS NE_*

Manzon Allah, tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, yace:
*_(Na rantse da wanda raina Ya ke hannunSa, Allah! Ina neman gafararSa, kuma ina tuba zuwa gare shi,a kowace rana sama da sau saba'in)_*.

Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce:
(Ya ku mutane! Ku tuba zuwa ga Allah. Domin ni ina tuba a kowace rana zuwa gare Shi sau dari).

SIGA TA FARKO
Shugaban Istighfar gaba daya shine:
_ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﻧﺖ ﺭﺑﻲ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ﺧﻠﻘﺘﻨﻲ ﻭﺃﻧﺎ ﻋﺒﺪﻙ ﻭﺃﻧﺎ ﻋﻠﻰ ﻋﻬﺪﻙ ﻭﻭﻋﺪﻙ ﻣﺎ ﺍﺳﺘﻄﻌﺖ ﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺷﺮ ﻣﺎ ﺻﻨﻌﺖ ﺃﺑﻮﺀ ﻟﻚ ﺑﻨﻌﻤﺘﻚ ﻋﻠﻲ ﻭﺃﺑﻮﺀ ﻟﻚ ﺑﺬﻧﺒﻲ ﻓﺎﻏﻔﺮ ﻟﻲ ﻓﺈﻧﻪ ﻻ ﻳﻐﻔﺮ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ_.

*_Allahumma anta rabbee la ilaha illa ant, khalaqtanee wa-ana 'abduk,wa-ana 'ala 'ahdika wawa'adika mas-tata'ata, a'uzu bika min sharri ma sana'atu, abuu-u laka bini imatika alai, wa abuu u bizanbi, faghfir li fa-innahu la yaghfiruz-zunuba illa anta_*.

Manzon Allah (SAW) ya sunnanta mana karanta wannan istighfari sau daya,safe da kuma yamma _Sannan kuma yace:*
*_(Duk wanda ya karanta shi da safe yana mai imani dashi,idan ya mutu kafin yamma, zai shiga aljanna. Kuma idan ka karantata da yamma kana mai imani da hakan, idan ka mutu kafin safiya zaka shiga aljanna in sha Allah)_*
@Sahihul Jami'i.

SIGA TA BIYU
_ﺍﺳﺘﻐﻔﺮ ﺍﻟﻠﻪ_
*_ASTAGH FIRULLAH_*


SIGA TA UKKU
_ﺭﺑﻲ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ_
*_RABBI GHFIRLI_*

SIGA TA HUDU
_ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﻇﻠﻤﺖ ﻧﻔﺴﻲ ﻓﺎﻏﻔﺮ ﻟﻲ ، ﻓﺈﻧﻪ ﻻ ﻳﻐﻔﺮ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ_
*_ALLAHUMMA INNI ZALAMTU NAFSI FAGHFIRLI FA INNAHU LAA YAGHFIRUZ ZUNUBA ILLA ANTA_*.

SIGA TA BIYAR
_ﺭﺏ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ ﻭﺗﺐ ﻋﻠﻲ،ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﺘﻮﺍﺏ ﺍﻟﻐﻔﻮﺭ_
*_RABBI GHFIRLI WA TUB'ALAYYA INNAKA ANTAT TAUWABUL GHAFUR_*

SIGA TA SHIDA
_ﺭﺏ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ ﻭﺗﺐ ﻋﻠﻲ ، ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﺘﻮﺍﺏ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ_
*_RABBIGH FIRLI WA TUB'ALAYYA INNAKA ANTAT TAUWABUR RAHEEM_*


SIGA TA BAKWAI
_ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﻇﻠﻤﺖ ﻧﻔﺴﻲ ﻇﻠﻤﺎ ﻛﺜﻴﺮﺍ ﻭﻻ ﻳﻐﻔﺮ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ، ﻓﺎﻏﻔﺮ ﻟﻲ ﻣﻐﻔﺮﺓ ﻣﻦ ﻋﻨﺪﻙ، ﻭﺍﺭﺣﻤﻨﻲ ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﻐﻔﻮﺭ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ_
*_ALLAHUMMA INNI ZALAMTU NAFSI ZULMAN KATHIRAN WALA YAGHFIRUZ ZUNUBA ILLALLAH, FAGHFIRLI MAGHFIRANTAN MIN INDIKA, WARAHAMNI INNAKA ANTAL GHAFURUR RAHEEM_*.


SIGA TA TAKWAS
_ﺍﺳﺘﻐﻔﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﻫﻮ ﺍﻟﺤﻲ ﺍﻟﻘﻴﻮﻡ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻪ_

*_Astaghfirul lahal lazi la ilaha illa huwal hayyul-qayyum wa atubu ilaih_*

*Ina rokon Allah Ya sanya ni da ku a cikin bayinSa ma su yawaita istighfar, Ya kuma ba mu lada da matsayin da ya ke ba ma masu yawaita istighfar, amiin.*

*Dan Allah a tura wa 'yan uwa dan su amfana da shi.*

Sunday, 20 January 2019

FASSARAR WAƘAR MAIN QAIDI NUMBER 796

Fassarar Waƙar Main Qaidi Number 796

* Sunan Waƙa - Main Qaidi Number 786 (Poem)

* Sunan Fim - Veer-Zaara

* Shekarar Fita - 2004

* Rubutawa - Aditya Chopra

* Sunan Kamfani - Yash Raj Music

* Rerawa - Shah Rukh Khan

* Mai Fassara - Haiman Raees

MATASHIYA

Waɗannan Kalamai da zaku karanta su ne Kalaman da Jarumi Shah Rukh khan ya furta a kotu yayin da Alƙali ya tambaye shi ko yana da abin faɗa. A ciki zaku ji yadda ya bayyana kansa a matsayin sa na Fursuna mai lamba 786 da kuma yadda ya ɗauki duniya. Sannan yayi jawabi dangane da Saamiya wacce ita ce lauyar sa da Ƙasar su ta India da kuma Masoyiyar sa Zaara tare da wasu muhimman abubuwa.


* Main qaidi number 786 jail ki salaakhon se bahar dekhta hoon

NI, Fursuna mai lamba 786, ina kallon Waje daga cikin ɗakina da ke Magarƙama

* Din, mahiney, saalon ko yug mein badalte dekhta hoon

Yayinda Ranaku, Watanni da shekaru suke Canjawa izuwa ƙarnoni

* Is miti se mere bauji ki kheton ki khushbu ati hai

Daga Ƙasar nan da nake, ina iya jiyo ƙamshin gonakin mahaifina

* Yeh dhoop meri matti ki thandi chaas yaad dilati hai

Wannan hasken ranar kuma yana tuna min da irin abincin Mahaifiya ta

* Yeh baarish mere sawaan ke jhoolon ko sang sang lati hai

Wannan ruwan saman kuma yana tafe ne da iskar damina

* Yeh sardi meri lodi ki aag sikh ke jati hai

Wannan lokacin ssnyin kuma yana tuno min wutar da akan kunna a kowane daren Lodi.

* Woh kehta hai yeh tera desh nahi

Sun faɗa mini cewa nan ba ƙasa ta bace

* Phir kyun mere des jaisa lagta hai

To ya aka yi kuma take kama da tawa? (Ƙasar)

* Woh kheta hai mein us jaisa nahi

Sun faɗa mini cewa ni ba irin su bane

* Phir kyun mujh jaisa woh lagta hai

To ya aka yi kuma suke kama da ni?

* Main qaidi number 786 jail ki salaakhon se bahar dekhta hoon

NI, Fursuna mai lamba 786, ina kallon Waje daga cikin ɗakina da ke Magarƙama

* Sapno ke gawn se utri ek nani pari ko dekh ta hoon

Naga wata ƴar aike Yayinda da ta fito daga ƙauyen Mafarkai

* Kehti hai khud ko Saamiya aur mujh ko Veer bulati hai

Ta kirayi kanta da Saamiya sannan ta kirani da Veer

* Hai bilkul begani paar apno si zid woh karti hai

Ita Cikakkiyar baƙuwace a gare ni amma tana faɗa a kaina tamkar dama can ta daɗe da sani na

* Uski sacchi baaton se phir jeene ko maan karta hai

Jin Kalaman ta na gaskiya yasa naji cewa ina sake rayuwa a raye

* Uske kaasmon vado se kuch karne ko maan karta hai

Jin alƙawuranta yasa naji ya kamata inyi wani abu mai nagarta

* Woh kehtay hain ke woh koi nahi hai

Sun faɗa mini cewa ita ba kowa bace a gare ni

* Phir kyun woh mere liye duniya se ladti hai

To me yasa kuma take faɗa da duniya saboda ni?

* Woh kehte hai ke mein us jaisa nahi

Sun faɗa mini cewa ni ba irin ta bane

* Phir kyun mujh jaisi woh lagti hai

To me yasa kuma take kama da ni?

* Main qaidi number 786 jail ki salaakhon se bahar dekhta hoon

NI, Fursuna mai lamba 786, ina kallon Waje daga cikin ɗakina da ke Magarƙama

* Mere gaon ke raango mein lipti ek nayi Zaara ko dekhta hoon

Inda daga cikin kala a cikin Kaloli naga Zaara

* Mere khwabon ko pura karte khud ke khwab bhool chuki hai woh

(Wacce) Saboda ta cika Mafarkaina ta manta da nata (Mafarkan)

* Mere logo ki sewa karte apne logo ko chhod chuki hai woh

(Wacce) saboda yiwa jama'a ta hidima ta bar nata (jama'an)

* Uska daaman aab khushion se bharne ko jee karta hai

Ina ma ace zan iya sake cika mata rayuwarta da dukkan wani farinciki

* Uske leya ek aur zindagi jeene ko jee karta hai

Wa ita, zan so na sake rayuwa a raye

* Woh khete hai ke mera desh uska nahi

Sun faɗa mini cewa nan ba Ƙasar ta bace

* Phir kyun mere ghar woh rehti hai

To me yasa take zaune cikin ahali na?

* Woh kehte hai ke mein us jaisa nahi

Sun faɗa mini cewa ni ba irin ta bane

* Phir kyun mujh jaisi woh lagti hai

To me yasa kuma take kama da ni?

* Main qaidi number 786 jail ki salaakhon se bahar dekhta hoon

NI, Fursuna mai lamba 786, ina kallon Waje daga cikin ɗakina da ke Magarƙama

* Woh khete hai ko woh koi nahi teri

Sun faɗa mini cewa ba mu haɗa komai ba da ita

* Phir kyun woh mere liye duniya se ladti hai

To me yasa kuma take faɗa da duniya saboda ni?

* Woh kehte hai ke mein us jaisa nahi

Sun faɗa mini cewa ni ba irin ta bane

* Phir kyun mujh jaisi woh lagti hai

To me yasa kuma take kama da ni?

* Main qaidi number 786 jail ki salaakhon se bahar dekhta hoon

NI, Fursuna mai lamba 786, ina kallon Waje daga cikin ɗakina da ke Magarƙama


<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________

●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...

GASKIYAR ZANCE 02

*GASKIYAR ZANCE 002 👌*


Cikin daruruwa da dubunnan matan da ake da su a gari, ga su nan birjik iya ganinka, mai yiyuwa ma a gidansu akwai 'yan mata wadanda babu abin da kika fi su, ga classmates dinshi nan birjik wadanda suka yi karatu tare, amma duk da haka ya ketare wadannan matan ya za6o ki domin ki zamo abokiyar rayuwarsa, ya yarda ki zamo uwar 'ya'yansa, ya aje ki a gidansa be gudun ki san dukkan sirrinsa, ya ke fita cikin rana ya yi zufa don ya nemo abin da za ku ci, duk wata fafutuka domin ki ne. To don me ba za ki kasance mai biyayya a gare shi ba.


Mijinki shi ne komai naki, ki kasance mai hakuri da gazawarsa, abin da ya kawo ki amsa ki yi godiya tare da yi masa addu'a da fatan alkhairi, kada ki bai wa kowa damar shiga gidansa sai da izininsa, ki san dukkan abin da yake so, sannan ki san abubuwan da ba ya so don ki kiyaye. Mijinki yana da girman hakki a wajenki fiye da kowa, don haka ki yi kokari ki samu aljannarki ta sanadiyarsa.


Mijinki aljannarki 'yar uwa! Ki nemi ilimin rike abinki, kada ki bari wasu can a waje su rude shi. Sannan ki dinga bibiyan yadda matan Annabi (ﷺ) suka mu'amalance shi.
.
.
Ya Allah Ka hada mu da mata nagari 👏🏼*✍🏿Ayyub Musa Giwa.*
*(Abul Husnain).*


*🕌ISLAMIC POST WHATSAPP.*

GASKIYAR ZANCE 01

*GASKIYAR ZANCE 👌*


Zaune take a gidan iyayenta cikin walwala, lumana da kwanciyar hankali, ba rashin ci babu rashin sha, ba rashin sutura ballantana matsuguni. A koda yaushe tana kallon iyayenta tana kara samun sakewa, tana ganin 'yan uwanta tana samun nishadi, ba ta rasa komai ba na daga kulawa daga wajen iyaye da 'yan uwa, sun ilimantar da ita, sun ba ta tarbiyyar da ya dace gwargwadon iyawarsu. Tun tasowarta ta taso ne a cikin iyayenta da 'yan uwanta, idan ta shiga damuwa za su share mata hawayenta. A lokaci daya ka zo ka kwallafa ranka a kan sai ka aure ta, iyayenta suka yarda suka ba ka ita ba don sun gaji da ita ko don sun rasa abin da za su ci gaba da yi mata hidima ba, ita ma ta amince ta bi ka gidanka ta ci gaba da rayuwa da kai, ta sadaukar da debe kewar iyayenta da 'yan uwanta don saboda ta rayu da kai, ta amince ta zama uwar 'ya'yanka, ta yarda ka san inda babu wanda ya sani a jikinta, ta yarda ta kare rayuwarta a gidanka, ta yarda ta zamo mai hidima a gare ka. Shin wadda ta yi irin wannan sadaukantakar ta cancanci kulawa ne ko wulakanci?!
.
Dan uwa wannan wani description ne na matarka, a koda yaushe ka dinga tunawa da irin halarcin da ta yi maka kafin ka hakaito wani aibinta. Matarka na tsananin bukatar kulawarka, tana son ka, sai dai kuma tana da rauni a wasu wajajen, to me zai hana ka mu'amalance ta da kyautatawa, tausayawa tare da tausasawa? Meyasa za ka yi mata tsawa ko ka zage ta, meyasa iyayenta suka zama abin zagi a wajenka bayan jajircewa da suka yi na rabuwa da wani bangare na jikinsu? Meyasa za ka muzanta mata ta hanyar danne mata wasu hakkokinta? Meyasa ka rabo ta da iyayenta idan ba ka shirya sauraron matsalolinta ba?

Ya kai dan uwa mai daraja! Ka sani, *hakuri* wani laqani ne na cin ma dukkan wata bukata wanda ba a ta6a jaraba shi aka samu faduwa ba. Haquri babban jigo ne na kyautata mu'amala da assasa zaman lafiya, walwala da nishadi tsakanin ma'aurata.

Ka dauki aure ibada, Sannan ka nemi sanin yadda za ka kyautata zamantakewa da iyalinka.

Mace abar tausasawa ce, domin ta kasance wani bangare na jikinmu. Ka yi hakuri da da'ifancinta, ka nuna mata soyayya, ka Qaunace ta kamar a ranar da ka fara ganinta, ka so ta saboda Allah don neman yardarsa....
.

Ya Allah Ka hada mu da abokan zama masu addini da kyawawan dabi'u 👏🏼


Qaninku a har kullum:
*✍🏿Ayyub Musa Giwa.*
*(Abul Husnain).*

*🕌ISLAMIC POST WHATSAPP.*