Barka da zuwa Bankin Bayanai

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

A INA YA KAMATA NA YI RIJISTAR JAMB? 08

💯 AREWA STUDENTS ORIENTATION FORUM 💯


  A INA YA KAMATA NAYI RIJISTAR JAMB ?


   
    Kashi Na Takwas


  A Koƙarin wannan Program na bayyanawa Dalibai Amintattun Guraren da Hukumar Jamb ta Yarje musu domin zuwa su gudanar da rijistar Jarrabawarsu ta Jamb, wato Approved Cbt Centres, dasuke a Fadin Jihohin Arewacin Najeriya guda Goma Sha Tara, Dakuma Babban Birnin Tarayya Abuja,


   Bisa Alfarmar Faisal Jibril, Insha'Allahu a yau zamu Dora program dinne da Cbt Centres din da hukumar Jamb ta Amince dasu a Jihar Niger, tareda Adireshin kowacce Cbt Centre.


   Jihar Niger dai tanada Cbt Cbt Centres guda Goma Sha Bakwai,


   Gasu Kamar haka:


1• Air-Max Computer Institute, Beside St. Theresa Catholic Church, Madalla, Niger State

2• Bishop James Yisa Memorial School CBT Centre, Kwamba, Suleja, Niger State

3• Brilliant Impact International Academy CBT Centre, Plot 1, 2 &3 Brilliant Impact Street, Angwan-Boro Gauraka, Tafa L.G.A. Niger State

4• FH Investment Limited CBT Centre, Uphill rest house estate, kobwa,Kuta, Niger State

5• Federal Polytechnic, ICT Hall, Doko Road, Bida, Niger State

6•Federal Univeristy of Tech, E -exam Centre 3, Main Campus, Gidan Kwano, Minna, Niger State

7• Federal University Of Tech, Electronic Test Centre, Gidan Kwano Campus, Minna, Niger State

8• Federal University of Technology, E-Exam Centre 2, Main Campus, Gidan Kwano, Minna,Niger State

9• IBRAHIM BABANGIDA UNIV. LAPAI, E-LIBRARY CBT CENTRE, NIGER STATE

10• JAMB Zonal Office, CBT Centre, 3 Arms Zone, Maitumbi, JAMB Office, Minna, Niger State

11• JAMB/NCC CBT Centre, 3 Arms Zone, Maitumbi, Beside JAMB Office, Minna, Niger State

12• NIGER STATE POLYTECHNIC, BIDA CAMPUS (CABS), DOKO ROAD, NEAR FEDERAL POLYTECHNIC, BIDA, NIGER STATE.

13• Niger State College of Agriculture CBT Centre, Beside Railway Station, Mokwa, Niger State

14• Niger State Polytechnic, Zungeru-Bida Road, Zungeru, Niger State

15• Niger state College of Education, CBT Centre, Minna, Niger State

16• Sani Bello College ICT Centre

17• Spectrum Computer Centre, Beside Pinnacle Petrol Station, Opposite Polosa Junction, RafinSanyi, Suleja.


  Wadancan 🖕 Cbt Centres din da muka lissafo a sama, Sune Cbt Centres din da hukumar Jamb ta Amince dasu yanzu haka, a Jihar Niger.

   ∆ Yanada Kyau Dalibi yasani cewar yin rijista a wani gurin da ba Cbt Centre ba, Kan Iya haifar Masa da Matsala a lokacin Jarrabawarsa, dan haka yanada Kyau a kiyaye.


   A Kashi na Tara na wannan Program din, zamuzo muku dauke da Approved Cbt Centres, na Jiha ta Gaba, a cikin Jerin Jihohin da muke dasu a Fadin Arewacin Najeriya.


  NB: Kusani Cewar wannan CBT Centres ne da JAMB ta Tabbatar dasu a 2021, Adadin nasu zai Iya Raguwa ko Kuma Karuwa, anan gaba.


     MUNGODE


Daga Ofishin Secretary General


Marubuci: MIFTAHU AHMAD PANDA (PRO ASOF ONLINE JAMB ORIENTATION COMMITTEE).


    Tare da Taimakon:

FAISAL JIBRIL.


@ ASOF 2021


(08039411956 / 08088119753).

Share:

KU NISANCI ABUBUWAN BAKWAI MASU HALAKARWA

_*KU NISANCI ABUBUWA BAKWAI MASU HALAKARWA*_
        
_Hadisi Ya Tabbata Daga *Abi-Hurairah (ra)* Yana Cewa *Manzon Allah (ﷺ)* Yace:_

ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ : ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ : *”ﺍﺟﺘﻨﺒﻮﺍ ﺍﻟﺴﺒﻊ ﺍﻟﻤﻮﺑﻘﺎﺕ“*، ﻗﺎﻟﻮﺍ : ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻣﺎ ﻫﻦ؟ ﻗﺎﻝ : *”ﺍﻟﺸﺮﻙ ﺑﺎﻟﻠﻪ، ﻭﺍﻟﺴﺤﺮ، ﻭﻗﺘﻞ ﺍﻟﻨﻔﺲ ﺍﻟﺘﻲ ﺣﺮَّﻡ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻻ ﺑﺎﻟﺤﻖ، ﻭﺃﻛﻞ ﺍﻟﺮﺑﺎ، ﻭﺃﻛﻞ ﻣﺎﻝ ﺍﻟﻴﺘﻴﻢ، ﻭﺍﻟﺘﻮﻟﻲ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺰﺣﻒ، ﻭﻗﺬﻑ ﺍﻟﻤﺤﺼﻨﺎﺕ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﺎﺕ ﺍﻟﻐﺎﻓﻼﺕ“* 
```{ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ: ٢٦١٥}```

_An Kar6o Daga *Abi-Hurairah (ra)*, Daga *Annabi (ﷺ)* Yace: *“Ku Nisanci Abubuwa Guda Bakwai Masu Halakarwa”.* Sai (Sahabbai) Sukace Wadanne Abubuwa ne? Sai Yace: 
1-“Hada Allah da Wani a Cikin Bauta,
2-da Yin Sihiri, 
3-da Kashe Ran da Allah ya Haramta (Sai da Dalili Na Shari'a),
4- Da Cin Riba, 
5- da Cin Dukiyar Maraya,
6_Da Guduwa a Fagen Dãgã, 
7_da Yiwa Mata Muminai Katangaggu Kazafi”.

```{Bukhari Ya Ruwaitoshi: 2615}```

Share:

ƊAGA HANNU A MAƘABARTA YAYIN ADDU'A GA MATATTU*DAGA HANNU A MAKABARTA YAYIN ADDU'A GA MATATTU ! ! !*

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum Tanbaya malam.Malam meye hukuncin mutun in yamutu in an kaishi makabarta wasu suke daga hannu suna addua sai su shafa su tafi, nama wani malami tambaya ya ce ba daidai ba ne, ni kuma tunanina daga hunnun ayi addua shine mafi rinjaye, malam menene gaskiya ? 

*AMSA*👇

Wa alaikum assalam To dan'uwa ya tabbata a hadisin Muslim mai lamba ta : 974 cewa : Annabi s.a.w. ya ziyarci makabartar Baki'a ya kuma daga hannu har sau uku yayin addu'a ga mamatanta" 
Hadisin da ya gabata yana nuna mustabbancin daga hannu yayin addu'a ga mamaci a makabarta.
Nawawy yana cewa Akwai hadisai da yawa wadanda suka zo akan daga hannu yayin addu'a, don haka duk wanda ya iyakance wuraren da Annabi s.a.w. ya daga hannaye, ya yi mummunan kuskure" Almajmu'u 3\489.
Saidai malamai suna cewa : yin addu'ar jama'a da murya daya a makabarta na daga cikin bidi'o'in da ba su da asali.

Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Share:

ZAKKAR MAI BASHI*ZAKKAR MAI BASHI:* 

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

*TAMBAYA*❓

 _As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah_ .

Manomin da 2/3 na kuɗin nomansa bashi ne ya ciwo, wai yaushe zai cire zakkah: Kafin ko bayan ya biya bashin ne?

 *AMSA*👇

 _Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh_ .

(1) Al-Imaam Al-Baihaqiy ya ruwaito (7857) da irin isnadin Al-Bukhaariy (#7337) daga Sahabi As-Saa’ib Bn Yazeed _(Radiyal Laahu Anhu)_ cewa: Shi ya ji Uthmaan Bn Affaan _(Radiyal Laahu Anhu)_ yana huɗuba a kan mimbarin Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam),_ yana cewa: Wannan watan fitar da zakkarku ne. Sannan kuma ya ce:

فَمَنْ كَانَ مِنْكُمْ عَلَيْهِ دَيْنٌ فَلْيَقْضِ دِينَهُ ، حَتَّى تَخْلُصَ أَمْوَالَكُمْ ، فَتَؤَدُّوا مِنْهَا الزَّكَاةَ
Don haka, duk wanda akwai bashi a kansa to ya biya bashinsa, har sai dukiyoyinku su kuɓuta, to sai ku cire zakkar daga cikinsu.

Wannan ya nuna: A wurin Khalifah Uthmaan Bn Affaan da waɗanda suke tare da shi daga cikin Sahabbai _(Radiyal Laahu Anhum)_ da Tabi’ai _(Rahimahumul Laah):_ Sai a bayan an cire bashi ne sannan ake cire zakkah.

(2) Sannan kuma Al-Imaam Al-Baihaqiy ya sake riwaitowa (7858) da ingantaccen isnadi daga Jaabir Bn Zaidin, daga Ibn Abbaas da Ibn Umar _(Radiyal Laahu Anhum)_ game da mutumin da ya ciwo bashi kuma ya kashe shi duk a kan gyara ’ya’yan itacen gonarsa da kuma iyalin gidansa. Shi ne Ibn Umar _(Radiyal Laahu Anhumaa)_ ya ce:

يَبْدَأُ بِمَا اسْتَقْرَضَ فَيَقْضِيهِ وَيُزَكِّى مَا بَقِىَ 
Sai ya fara da bashin da ya ciwo ya biya shi, sannan ya fitar da zakkar abin da ya rage.

Watau dukkan bashin da ya kashe a kan gonar da iyalinsa.

Shi kuma Ibn Abbaas _(Radiyal Laahu Anhumaa)_ cewa ya yi:

يَقْضِى مَا أَنْفَقَ عَلَى الثَّمَرَةِ ، ثُمَّ يُزَكِّى مَا بَقِىَ
Sai ya biya bashin da ya kashe a kan gonar, sannan ya fitar da zakkar sauran da ya ragu.

Watau ban da ɓangaren bashin da ya kashe a kan iyalinsa.

Amma idan ya kashe dukkan bashin a kan gonar ce har ma ya ƙaro kamar sulusi (1/3) daga aljihunsa, kamar yadda ya zo a cikin wannan tambayar, sai amsar ta zama:

Daga buhuna ɗari biyar (500) ko ɗari bakwai (700) da ya samu a gonar sai ya fara da ware adadin buhunan da farashinsu ya yi daidai da yawan bashin da ke kansa, sauran buhunan kuma sai ya raba su gida goma ya bayar da kashi ɗaya (1/10), idan da ruwan damina ne aka shayar masa da gonar. Ko kuma kashi ɗaya cikin ashirin (1/20), idan da ban-ruwa ne ya shayar da ita.

Allaah ya ƙara mana fahimta.

 _Wal Laahu A’lam._ 

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Share:

YADDA AKE WARWARE MATSALOLIN RAYUWA*_YADDA AKE WARWARE MATSALOLIN RAYUWA_*

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum Dafatan Malam ya tashi lafiya,.wata 'yar uwa ce take son Karin bayani a kan wani lamari wato ya kasance tana da aminiya sai take gaya mata matsalolnta sai ta hadata da wani Dan uwanta malami akan zai bata addu'oi, sai tace tana so kuma ya mata istihara sai su kaje sai ya yi istharan, a lokacin ya mata bayani kamar yadda tayi wa kawarta bayani har ya karbi kudin da za’a yanka kaza saboda za’a karanta suratul yasin. Malam sai yabata rubutu yace ta sayi tumbin shanu ta dafa da rubutun. Ta kuma yi amfani da kifiya ta naci daidai ta roki Allah ya kareta daga sharrin makiya, so daga baya tai ta tambaya aka ce taguji irin wadannan malaman, har tazo ta karyata abin. To mal ya matsayinta yake?

   *AMSA*👇

Wa'alaikum assalam Akwai alamun da suke alamin ba mai ilimi bane, don haka Ina bata Shawarar da ta rabuda shi don kar ta fada cikin halaka. Ana iya samun waraka daga matsaloli ta hanyar yawaita istigfari da tuba zuwa ga Allah da mayar da hakkokin da ba na ka ba, da yawaita sadaka, da nisantar cin mutuncin mutane, da yawaita addu'o'i, saboda addu'a tana tunkude bala'i, taimakawa mutane da yaye musu bakin ciki na daga cikin abubuwan da suke warware mushkiloli, Annabi (S.A.W). Idan abubuwa suka dame shi yana ta shi izuwa sallah kamar yadda Abu-dawud ya rawaito shi kuma Albani ya inganta shi a hadisi mai lamba ta: 4171> Gano ainihin matsala da shawartar masana wadanda suka goge a rayuwa yana taimakawa wajan warware wasu matsalolin, mutukar shawarar da suka bayar bata sabawa ka'idojin sharia ba, ana iya samun mafita in aka bita. 

Allah shine mafi Sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Share:

WARNIN AGAINST THE LURES OF SHAIƊANبسم الله الرحمن الرحيم

السلام عليكم ورحمه الله وبركاته.

WARNING AGAINST THE LURES OF SHAYTAN....

Allah warns the Children of Adam against Iblis and his followers, by explaining about his ancient enmity for the father of mankind, Adam peace be upon him. Iblis plotted to have Adam expelled from Paradise, which is the dwelling of comfort, to the dwelling of hardship and fatigue (this life) and caused him to have his private part uncovered, after it had been hidden from him. This, indeed, is indicative of deep hatred (from Shaytan towards Adam and mankind). Allah said in a similar Ayah,

(Will you then take him (Iblis) and his offspring as protectors and helpers rather than Me, while they are enemies to you What an evil is the exchange for the wrongdoers.) ﴿18:50﴾.

(28. And when they commit a Fahishah, they say: "We found our fathers doing it, and Allah has commanded it for us.'' Say: "Nay, Allah never commands Fahishah. Do you say about Allah what you know not'') (29. Say: "My Lord has commanded justice and that you should face Him only, in every Masjid and invoke Him only, making your religion sincere to Him. As He brought you (into being) in the beginning, so shall you be brought into being again.'') (30. A group He has guided, and a group deserved to be in error; (because) surely, they took the Shayatin as supporters instead of Allah, and think that they are guided.)


 *THE TRUE RELIGION IS ISLAMIC MONOTHEISM* ...
Share:

THE COMMAND TO STAND AT NIGHTبسم الله الرحمن الرحيم

السلام عليكم ورحمه الله وبركاته


 *THE COMMAND TO STAND AT NIGHT* (in Prayer)


Allah commands His Messenger to cease being wrapped up, and this means to be covered during the night. He commands him to get up and stand in prayer to His Lord. This is as Allah says,

(Their sides forsake their beds, to invoke their Lord in fear and hope, and they spend out of what We have bestowed on them.) (32:16) Thus, the Prophet did as Allah ordered him, by standing for prayer at night. This was obligatory upon him alone, as Allah said,

(And in some parts of the night offer the Salah with it (the Qur'an), as an additional prayer for you. It may be that your Lord will raise you to Maqam Mahmud.) (17:79) Here Allah explains how much prayer he should perform. Allah says,

(O you wrapped up! Stand all night, except a little.) Ibn `Abbas, Ad-Dahhak and As-Suddi all said,

(O you wrapped up!) "This means, O you who are asleep.'' Qatadah said, "The one who is wrapped up in his garments.'' Concerning Allah's statement,

(Half of it) means, instead of the whole night.

(A little less than that, or a little more.) meaning, `We have commanded you to stand in prayer for half of the night, either a little more than it or a little less. There is no hardship on you concerning that (slight increase or decrease).


 *THE SUNNAH OF ISLAMIC MONOTHEISM* ...
Share:

HADITH OF THE DAY 5TH APRIL 2021

.
On the authority of Abu Sa'id al-Khudri (may Allah be pleased with him), who said that the Messenger of Allah (ﷺ) said: Paradise and Hell-fire disputed together, and Hell-fire said: In me are the mighty and the haughty. Paradise said: In me are the weak and the poor. So Allah judged between them, [saying]: You are Paradise, My mercy; through you I show mercy to those I wish. And you are Hell-fire, My punishment; through you I punish those I wish, and it is incumbent upon Me that each of you shall have its fill. It was related by Muslim (also by al-Bukhari and at-Tirmidhi). 


40 Hadith Qudsi
(40 Hadith Qudsi)
Arabic/English book reference : Hadith 39 *THE SUNNAH OF ISLAMIC MONOTHEISM*
Share:

WOMEN AND FOOD

        *Women and Food [Man Talk]*

It is reported that _Al-Aḥnaf b. Qays –_ Allāh have mercy on him – said:

*_Stay away from mentioning women and food in our gatherings, for I hate a man to constantly describe his private parts and his stomach. It is an aspect of higher conduct and religiousness that a man [sometimes] leaves eating food while he desires it._*

_Abū Bakr Al-Daynūrī, Al-Mujālasah wa Jawāhir Al-‘Ilm 3:44, 45_


https://www.sayingsofthesalaf.net/women-and-food-man-talk/Share:

WAHAYIN SHAIƊAN


WAHAYIN SHAIDAN.
[ Sheik Ibrahim Disina ]

Wannan itace makarantar shedan, Ga fatawoyin da almajiransa suka gabatar masa tare da abinda ya cusa musu na jayayya Don kange mutane daga daukar gaskiya:

Almajirai : Shin yaushe ya kamata a tsaida gemu ??

Shedan: Ana tsaida gemu ne in an tsufa, domin kar ka tsayar da shi ka kasa bashi hakkinsa.

Almajirai: Shin dole Mata su sanya Lullubi?

Shaidan: Ai dayawa masu sanyawar suna fakewa da shi suyi barna, Tsoron Allah Ai a Zuciya ya ke ba a Hijabi ba, In sun matsa da bayanai Ku sanya Please call me, ko Half Sunnah.

Almajirai : Yaya za a samu nasara kan Masu Da'awah.

Shaidan: Ku cire musu yi Don Allah, ku sanya musu son burge Jama'a, Ku rabasu da yawaita Ibada Sannan Ku cusa musu son Duniya, in kuka ci nasara makamansu na yakar rundunata zai yi rauni.

Almajirai: Shin yabon manzon Allah da kida halal ne??

Shedan: Kwarai da gaske, An rawaito a rarraunan Hadisin karya cewa lokacin Hijira an taryeshi da kida tare da 'yammata suna rawa suna juyi, Wannan salon yana daurin sanya nishadi.

Almajirai: Wanda ya bar tufarsa ta wuce idon sau ba don girma kai ba yayi laifi?

Shedan: Tsoron Allah ai a zuciya ya ke ba wai a tufa ba, Annabi yace Abubakar ba ya cikin masu girman kai, In ka sanya tazarce ne kadai za ka fito dan Birni, domin irin Wannan shiga ta kan sanya a yi maka kallon dan tsanani.

Almajirai: Menene matsayin wanda yake satar kudin Gwamnati amma yana sadaka?

Shedan: In baku sata ba 'yan kudu za su sata!!
Kuma ai sadaka tana tsarkake Dukiya! sannan ai taimakawa Jama'ar ake yi. Ki gina Masallatai Ku taimakawa kungiyoyin addini laifukan za su karanta.

Almajirai: In muka isar da sakon sai aka kawo mana wasu hujjoji yaya zamu yi??

Shedan: Ku kalato rubabbun dalilai, ku kaucewa gaskiya, Ku tuhumcesu da kin Manzon Allah, Ku ce musu 'yan tsanani, Ku jajirce kan matsayinku sannan kuyi tawilin gangan, ku tuhumcesu da wasu karerayi
sannan ku jirani in karo muku Hujja.
Allah yace cikin Qur'ani

"Shaidan ya kan yi wahayi zuwa ga Mutanensa don suyi jayayya da ku"

.
Allah ka kare mu daga sharrin shaidan

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=1928795747269415&id=100004170251164&sfnsn=scwspwa
Share:

WHO ARE THE SALAF?| Who are the Salaf and the obligation to follow them | Written by: Muhammad Ali Mazari

Salaf in Arabic means predecessor, and In Islamic terminology it refers to the first three best generations of Muslims titled Sahābah, Tabieen (students of the Sahabah) and the Tabi al-Tabieen (followers of the students). Whom the Prophet ﷺ has declared the best (Sahih al-Bukhari 6429), has ordered us to follow them on the beliefs and Methadology they agreed upon (Tirmidhi 2165, Sahih), has said the Soundness of the entire Ummah meaning in religious understanding, beliefs and Methadology is within them (Sunan An Nasa'i 4191, Sahih), and said that the saved sect will be the one who is upon their beliefs (Tirmidhi 2641, classed as Hasan by Al Iraaqi, as Suyuti and Al Albani) and Prophet Muhammad ﷺ has established himself as the leader of the Salaf in Sahih al-Bukhari 6285, and Allah has said, He is pleased with them in the Quran 9:100, promised them with forgiveness in 9:117 and has threatened those who follow a path other than the path of the Salaf with the fire in 4:115. 

So for us, following the Salaf in their beliefs and Methadology and interpretation of the book and the Sunnah has indeed been obligated. And Allah knows best.
Share:

LET'S LIVE TOGETHER IN PEACE


LET'S LIVE TOGETHER, IN PEACE 

Ibrahim and Habeebah were both doctor couples. They worked together in a big hospital owned by the couple, IMMACULATE MEDICAL HOME. Ibrahim was a surgeon while Habeebah was a gynecologist. The hospital was actually a mahr given to Habeebah by Ibrahim. And he even had to relocate from Abuja to Lagos to grant his bride's wishes.

Ibrahim was Hausa-Fulani while Habeebah was Yoruba. Ibrahim was from a wealthy family while Habeebah came from a poor family. The couple met through Jamilah, Ibrahim's sister. They met on the wedding day of Jamilah. And it was an instant connection as Ibrahim liked Habeebah immediately.

He proposed marriage to her through his sister, Jamilah. Habeebah was afraid. She wasn't ready to go into the world of discrimination. She thought a social gap existed between the rich and the poor. She thought the rich would never dine with the poor. She thought rejecting the proposal would be knowing her place to avoid humiliation. Aside from this reason, she had so many other reasons.

She was a relative-less girl who couldn't trace her background. She thought marrying from the big wig in the society would expose her birth deficiency which she'd kept from public glare all the years. She thought marrying from de creme la de creme in the society would only bring her nothing but headache. She grew up with so much contempt from her own biological mother, she wouldn't love to delve into a marriage that she perceived would be filled with contempt and discrimination.

Another reason she ran away from Ibrahim's proposal was because of her unlettered mom. Her mom couldn't converse with the simplest English word. She feared there would be barriers in communication if she married Ibrahim who was Hausa. How would her mom communicate with her in-laws? How would she introduce her mom to her in-laws and there wouldn't be any form of connection from the go, due to language barriers? She wouldn't want that, hence, she ran as fast as her leg could carry her. She also feared that she might be a misfit for Ibrahim and his family. She feared there might be hullabaloo on her wedding day when media outlets from all corners of the country would grace the occasion and introduce Ibrahim as the son of a serving senator, how would her own family be introduced? She thought it would be better for her to know her place.

She had so many reasons for rejecting Ibrahim's proposal. And part of it was her past. While she was abandoned and neglected by her mother, she was accepted by another family. All the love she was denied was given to her by Adam and his grandfather. She thought it was too good to be real. She couldn't believe life could have a meaning. She couldn't believe life could be so sweet. But then, this newly found love was slipping away from her hands again. She wanted to retain this love, come what may. She wanted to have this love forever, no matter what it would cost her. Then she made a huge mistake. A mistake which hunted her till her path crossed with Ibrahim. And this mistake was part of what made her flee when Ibrahim proposed to her. When the past came hunting, the present would be filled with agony and melancholy.

Destiny eventually took its cause. What God had willed, no one could stop. They did get married. Ibrahim slaughtered her fears. He eliminated her worries. He accepted her wholeheartedly. She was relative-less, so what? She had a past, so what? She was from a poor home, so what? She wasn't even from his tribe, so what. True love exists. True love can be unconditional. True love conquers all. Where there is love, every other thing does not matter.

Ibrahim was a God sent. He turned her mournings into a bright morning star. He was everything to her. He stood by her when challenges crept into her world. He held her hands and assured her of a brighter ray. He was the shoulder that erected her neck so firmly. He was the rock she rested her back on without faltering. He was a knight in shining armour. He was the father she never had. The brother she never had. The love she never experienced. He gave her pure and unblemished love.
_______

Fast forward to this day, they had seven children together. The first gift Allah gave them came in three. They had triplet boys. Followed by twin girls and then twin boys.

A beautiful Sunday evening, the couple had a break from work. Ibrahim had a guest, his Hausa-Fulani childhood friend. Habeebah was preparing a delicacy in the kitchen.

Ibrahim and his friend were watching the news. Habeebah came out of the kitchen, she served them Amala and efo riro with orange juice. She sat beside her husband.

"Join us dear." Ibrahim said to Habeebah.

"No, darling, I'm full. Enjoy your food with your friend." Habeebah replied with smiles.

On the news, the Sasha ethnic clash was being broadcasted. 'The Yoruba and the Hausa clash in Sasha market in Ibadan. Lots of lives and properties were lost,' The news said.

Ibrahim's friend fumed with anger.

"See the way the Yorubas are killing our people. This is not fair at all. Our people too should retaliate by killing the Yorubas in the north." Bashir, Ibrahim's friend said while the couple exclaimed.

"What!" Ibrahim and Habeebah said in one voice.

"Yes now. Our people too should retaliate by killing the Yorubas in the north, you heard me right. That's the best revenge we can have." Bashir said in anger.

"Wow! What a submission! Those Yorubas in the north that would be killed, are they the ones that killed our people here in the southwest?" Ibrahim asked.

"Who cares. Those Hausas that were killed as well, were they the ones that committed the atrocities that were levied against the Hausa-fulanis that prompted this unjust killing?" Bashir asked. 

"That's it. And if the unjust killings continue, so many innocent lives would be lost. There would be blood baths on the land which could lead to war. The prophet (PBUH) warned us against taking innocent souls in a number of Hadiths. 'whoever kills a soul unless for a soul or for corruption [done] in the land - it is as if he had slain mankind entirely. And whoever saves one - it is as if he had saved mankind entirely.' Ibrahim quoted from the hadith of the prophet (saw) while Bashir was mute. He was still angry.

Ibrahim continued.

"The prophet warned us against tribalism and unjust killings in numerous hadith 'And do not kill the soul which Allah has forbidden [to be killed] except by [legal] right……' 
"Whoever rejects lawful obedience to the leader and divides the community and dies in this state will have died upon ignorance. Whoever fights under the banner of one who is blind, raging for the sake of tribalism, or calling to tribalism, or supporting tribalism, and is killed in this state will have died upon ignorance. Whoever rebels against my nation, striking the righteous and wicked alike and sparing not even the believers and does not fulfill the pledge of security, then he has nothing to do with me and I have nothing to do with him.' Ibrahim quoted yet another Hadith but Bashir would not agree with him.

"I know you're saying all this because you married a Yoruba woman." Bashir accused Ibrahim of insincerity while Ibrahim shook his head.

"No, I am not saying this because I married a Yoruba woman. I am saying all this because I'm a Muslim and someone who practices the sunnah of the prophet (s.a.w) And because the prophet also says 'He is not one of us who fights for the sake of tribalism.' For this reason, I'll always sue for peace and not for war. Because I know that Islam is a religion of peace and taking life unjustly is prohibited in Islam. And not only is it prohibited, the prophet (saw), says whoever does, will not smell the fragrance of paradise. And of course, I have married a Yoruba woman also, I'll never support anything that'll harm her tribe." Ibrahim said lovingly while Habeebah grinned.

This got Bashir more furious.

'Nonsense, but your wife's tribe can do things that'll harm your own tribe isn't it? Shebi you have eaten efo riro. And as a matter of fact, you eat it on a daily basis, you'll never be able to defend your tribe." Ibrahim's friend said angrily while Ibrahim smiled.

"Don't be angry my darling friend. All I have quoted thus far are not my own words, they are words of the prophet whom you and I believe in. Besides, I don't follow blindly, I have a mind of my own like the prophet has admonished us. 'Do not be people without minds of your own, saying that if others treat you well you will treat them well, and that if they do wrong, you will do wrong; but accustom yourselves to do good if people do good, and not to do wrong if they do evil'. Ibrahim quoted yet another hadith.

"Okay o. Let them continue to kill us while we keep mute. I just pray you're not the next to be killed by them." Bashir said to Ibrahim while Habeebah who'd been watching them in silence quickly rebuked what Bashir had said.

"Audhu bikalimatillahi tammati min sharri ma khalaq. My husband will never be a victim of human brutality. Please let's always say what is good or keep quiet." Habeebah expressed, trying hard to hide her anger and be courteous to the best of her ability.

Bashir got Habeebah's message. He kept quiet and fixed his gaze on the TV screen. Ibrahim smiled and held Habeebah's hand in his.

"Don't get yourself worked up sweetheart. Bashir has always been a plain spoken person. Nothing undestined will happen to your husband, so relax." Ibrahim said to Habeebah.

"Aamin o. I'll never mourn over you. You'll not be a victim of human wickedness by the grace of Allah. Let me go and check on the kids upstairs." Habeebah said and excused herself.

After Habeebah had left, Ibrahim turned to Bashir.

"Bashirrrrr, how can you say such unkind words to a husband in the presence of his wife. Don't you know that a woman's most feared nightmare is losing her husband? My wife can tear you apart if she hears you talk about her husband being killed." Ibrahim said to Bashir who apologized for being insensitive.

"As a matter of fact, I understand your grievances. I know you're furious because our innocent people are being killed. But an eye for an eye is not the solution. It will only make the world go blind. Some of our people too are guilty of kidnapping and killing their people. But you see, instead of cutting off the guilty finger, our people are fond of general labeling. Since some Fulani herdsmen are killing are kidnapping, all Fulanis are kidnappers and murderers who should get a death penalty. This generalization should stop. It's doing lots of harms and no good at all. When there was a xenophobic attack on Africans in South Africa, all Africans came out to condemn the evil, not minding if one was Nigeria or Ghana. All Nigerians condemned the evil, regardless of whether it was the Ibos that were mostly affected in the xenophobic attack. Why don't we condemn evil together as one Nigeria, not minding the tribe that perpetrated the evil. And without labelling all the tribe as perpetrators. Let's condemn the evil, and not the tribe that committed the evil. Until then, our peace as a nation would continue to be jeopardized." Ibrahim concluded while Bashir nodded his head.

"I just hope this non-retaliation approach works." Bashir said, unsatisfied with Ibrahim's submission.

"It will work. Two wrongs can never correct an evil. May Allah's protection never cease upon us all. Let's always sue for peace. The prophet (PBUH) also says 'Do you know what is better than charity and fasting and prayer? It is keeping peace and good relations between people, as quarrels and bad feelings destroy mankind.' 
We won't gain anything from war other than destruction. Those who have witnessed war know that it is not a child's play. The Muslims are one brother. Nigeria is one. From the north to the south to the east and west, we are one Nigeria. Let's live as one. Let's live in peace. Let's quit hate speeches. Let's quit inciting words. Let's stop fuelling the ember of war. We're one nation. Hausa, Yoruba, Igbo and other Nigerian tribes are all one Nigeria." Ibrahim concluded.
_____

Let's live in peace. Those who have read BEHIND MY SMILE will understand this addendum better.

Meanwhile, BEHIND MY SMILE is still selling fast. Get yours. Slide into my dm. We will get it across to you wherever you are in Nigeria.

GOD BLESS NIGERIA!

LATEEFAH ADEWUNMI JUMAH;LAJFINGERS
Share:

SALLAMA DA HUKUNCE-HUKUNCENTA

*Sallama Da Hukunce-Hukuncenta*

*✍️ Yusuf Lawal Yusuf* 

1) Sallama wata abace mai muhimmnci wanda Addininmu na Musulunci ya karantar damu a duk lokacin da muka hadu da daya daga cikinmu mu yi ta tare da yin musafaha (haɗa hannaye). Amma a yau mun wayi gari mukan fifita gaisuwa irin ta al'ada akan gaisuwar Musulunci. Tun daga kan manyanmu har k'ananunmu. Saboda haka yana da kyau mu rika tunasar da junanmu akan ta musamman ga dalibai a makarantu na Islamiyya da wasu wuraren karatuka.

2) Allah Ta'ala yana cewa: "Yaku da kuka yi imani, kada ku shiga gidajen da ba naku ba har sai kun nemi izini kunyi sallama ga masu gidan". 
Suratu Núr, aya ta: 27.

Allah Ta'ala ya sa ke faɗi cewa: "Idan zaku shiga gida, to kuyi sallama a kan kawunanku, gaisuwa daga Allah mai albarka, dadádã". Surah: Nùr, 61. 

Allah Ta'ala ya sake fadi: "Idan an gaishe ku da gaisuwa mai kyau to kuma ku gaishe su da wacce ta fita kyawu, ko kuma ku mayar da kwatankwacin wacce aka muku".
Surah: Nisa'i, aya ta: 86. 

3) Abdullahi dan Salam radiyallahu anhu yace Manson Allah (S.A.W) yace: "Ya ku mutane ku yada sallama, ku sadar da zumunci, kuma kuyi salla da dare, lokacin da mutane ke bacci, sai ku shiga Aljanna tare cikin aminci". Tirmizi.

Abdullahi ɗan Amru radiyallahu anhu yana cewa: wani mutum ya tambayi Manzon Allah (S.A.W) wani aiki ne mafi alkhairi? Sai Manson Allah (S.A.W) yace: Ciyarda abinci, sannan yin sallama ga wanda ka sa ni da wanda ba ka sa ni ba". Bukhari da Al-Imam Muslim. 

Abu Hurairah radiyallahu anhu yace: Manzon Allah (S.A.W) yace: " Ba zaku shiga Aljanna ba har sai kunyi imani, kuma ba zaku yi imani ba har sai kunso junanku, shin bana nuna muku abinda in kuka aikata shi zaku so juna ba? Ku yada sallama a tsakaninku". Al-Imam Muslim.

Imran dan Husain yace: wani mutum yazo wurin Manzon Allah (S.A.W) sai ya yi masa sallama "Assalamu alaikum" sai Manzon Allah (S.A.W) yace yana da lada goma, wani ga sake zuwa ya yi sallama da cewa: "Assalamu alaikum wa-rahmatullahi" sai Manzon Allah (S.A.W) yace yana da lada ashirin, sai ya sa ke zuwa shima ya yi sallama: "Assalamu alaikum wa-rahmatullahi wa-barakatuh" sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yace yana da lada talatin". Tirmizi.

4) Daga cikin hukunce-hukuncenta shine: Ya halasta maza suyiwa mata, haka suma mata suyiwa maza idan har an kubuta daga fitina, gabatar da ita akan gaisuwar al'ada, yin ta a duk lokacin da ka gamu da dan uwanka, ƙarami ya yiwa babba, jama'a kadan suyiwa masu yawa, nakan abin hawa ya yiwa na kasa, na tsaye ya yiwa na zaune.

5) Yana daga cikin tasirin da sallama ke da shi a cikin rayuwar musulmi: Aminci, samun yarda, sanya soyayya a tsakanin juna, hada zumunci. Allah Subhanahu Wata'ala ya bamu ikon yada sallama a tsakanin junanmu.

Share:

NA TSINCI ZOBEN ZINARE AMMA NA SIYAR DA SHI


*NA TSINCI ZOBEN ZINARE, AMMA NA SIYAR DA SHI?*

*Tambaya*

Assalamu alaikum. Allah kara ma malam lfy,tambayata itace shekara 3 da tsintan zoban zinare har yau ba,asami me zoban ba sai akakai kasuwa aka saida to wannan kudin ya za,ayi dashi? .


 *Amsa*

Wa alaikum assalam, Idan aka yi tsintuwar da ta Kai cigiya, ya wajaba a sanar da sifofinta tsawon shekara guda, daga nan sai ayi amfani da ita in ba'a samu mai ita ba , kamar yadda ya tabbata a hadisi. 

A bisa hadisin da ya gabata za ki iya amfani da kudin da kika siyar, saidai idan mai ita ta zo daga baya za kı biya ta, in kuma ba ta zo ba, to arziki ne, Allah ya koro miki daga falalarsa. 

Allah ne mafi sani.

6/04/2016.

*Amsawa:* Dr. Jamilu Zarewa.
*Gabatarwa:* Abu- Unaisa.

👉🏾 Darussunnah Foundation, 07035888158.
Share:

SALLAR MAI YOYON FITSARI

*SALLAR MAI YOYON FITSARI !*

Tambaya
Assalamualaikum, An yi min aiki a mara ta, aka samun robar Fitsari, yanzu an cire robar, amma in na yi Fitsari a toilet, Ina ganin danshin Fitsari a wandona, Yaya hukuncin alwalata da sallata ?

Amsa
Wa alaikum assalam, Ka yi kokari wajan fitar da Fitsarin da tsanyewarsa daga mafitsararka gwargwadon iyawarka, duk lokacin da za ka yi Sallah ka yi alwala, bayan haka duk abin da ya fito ba matsala, ka karasa sallarka, kar ka yanke.
Allah Yana cewa a ayar karshe a Suratul Hajj "Kuma bai Sanya muku kunci a cikin addini ba"
Allah ne Mafi sani

Amsawa 
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

16/02/2021

ZaKu iya Bibiyar Mu a
 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248


Share:

HUKUNCIN WANDA YA SAKI MATARSA A CIKIN MAYE
اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎

Daga Zauren 
📌 *Albahral Ilmu*🌴

✍🏻Rubutawa
      Abdulkadeer Umar Alshinkafawy.

*HUKUNCIN WANDA YA SAKI MATARSA A CIKIN MAYE* 


 *TAMBAYA* ❓

Assalamu alaikum malam, tambaya ce dani. Mijina ne yasake ni sau biyu, sai yasha abin maye yace na zo nasameshi, ni kuma banzoba saboda bana son abin da yakesha na maye, shine yace idan banzoba a bakin aure na. Shin yaya auren mu? Allah ya saka da alheri.


 *AMSA* 👇

Wa'alaikum assalam

 Malamai sun yi sabani game da aukuwar sakin wanda yake cikin maye:

1. Mafi yawan malamai sun tafi akan cewa idan ya saki matarsa, tabbas sakin ya auku, saboda shan giya sabon Allah ne, kuma shi ya jawowa kansa, don haka ba za'a yi masa uzuri ba, wannan ita ce maganar Abu-hanifa da Malik da Shafii a daya daga cikin zantukansa.

2. Sakinsa bai auku ba, saboda lokacin da Ma'iz ya zo ya tabbatarwa Annabi ﷺ ya yi zina saida ya tambaye shi ko ka sha giya ne, kamar yadda Baihaki ya rawaito a Sunanul-kubrah, hakan sai ya nuna mashayin giya ba'a amsar maganarsa.
Sannan an rawaito daga sayyadina Usman da Ibnu Abbas cewa: sakin mashayin giya ba ya aukuwa, kuma ba'a san wanda ya Saba musu ba a cikin Sahabbai.
Wannan ita ce maganar Imamu Ahmad da Zahiriyya da Ibnu Taimiyya.
Babban Muftin Saudiyya na waccan lokacin Sheik Abdulaziz bn Bazz da wasu Malaman suna rinjayar da magana ta biyu saboda mashayin giya bai san abin da yake fada ba, hakan sai ya sa ya yi kama da Mahaukaci wanda Alkalami ya saraya daga kan shi, kai har sallah ma an hana mashayin giya ya yi saboda ba ya cikin hayyacinsa, kamar yadda aya ta (43) a Suratu Annisa'i ta tabbatar da hakan.
Allah ne mafi sani.
Don neman karin bayani duba: Al-Mugni 7/289 da kuma Sharhul Munti'i 10/233.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Share:

HUKUNCIN TARA FARCE


*HUKUNCIN TARA FARCE💅🏻* 

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

*TAMBAYA*❓

SHIN KOYA HALATTA BARIN AKAIFA ( FARCE)?
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ .
*AMSA*👇

 Yanke farce yana cikin sunnoni na dabi'a da'aka dabi'antar da mutum akansu saboda fadin
Annabi Sallallahu Alaihu wasallam ( Abubuwa biyar
suna daka dabi'ar da'aka halicci mutum dasu, kaciya, da aske gashin gaba, da rage gashin baki ga ( maza) da yanke farata, da tsige gashin
hammata) Bukhari da Muslim.
Yatabbata awasu hadisai sunnonin fidra guda gomane daka ciki akwai yanke farce, yazo ahadisin Anas dan malik Allah yakara yarda dashi yace:
( Annabi Sallallahu Alaihu wàsallam ya iyakance mana lokacin yanke gashin baki dayanke farce da
aske gashin gaba da tsige gashin hammata kada mubarshi yahaura kwana arba'in bamu kawar dasu
ba).
Ahmd, Bukhari, Nisa'i
Wanda bai yanke farcensa ba yasabawa sunnah, hikimar hakan shine tsafta da kuma fitar da abundake karkashinsu na dauda da datti, da dauke
kamanceceniya dawanda basa hakan cikin kafirai, dakuma kama da dabbobi,
Fatawa lajnatul da'imah ( 5/173).

Mafiya yawan mata ayau sun fada cikin
kamanceceniya da dabobi da dakafirai wajan tara farce, sannan sai su rinashi💅🏻 dajan farce baiki ko jah, wannan yakai makura wajan muni, da abun kyama acikin zukata, ga duk wani mai hankali mai
dabi'a kubutacciya.
Haka yana daka cikin mummunar dabi'a wajan wasu mutane saisu bar wani sashi nafarcen yai tsawo bakyan gani, dukkan wadannan sun sabawa sunnah da kuma fidira ta dan adam, saboda haka
bashi halatta tara farce gaba dayansa ko barin wani daka cikin faratan domin kamace dakafirai kama dakafirai kuma haramunne acikin dukkan komai na al'adunsu, Muna rokon Allah kubuta daka
wadannan munanan halaye, Allah yashiryar damu hanya madai-daiciya.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻻ ﻋﻠﻢ ﻟﻨﺎ ﺇﻻ ﻣﺎ ﻋﻠﻤﺘﻨﺎ ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﻌﻠﻴﻢ
ﺍﻟﺤﻜﻴﻢ .

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Share:

YADDA AKE KAWAR DA BUSHEWAR JIKI


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*


*_Yadda Ake Kawar Da Bushewar Jiki_*

yar’uwa kada ki bar jinkinki ya dunga bushewa da yaushi kamar ba jini a jinkinki kuma bai kamata jikin mace haka ba, ki zama mai taushi fata da laushin fata.

 Zaki nemi kayan hadi kamar haka;
* Man zaitun
* Ruwa
* Zuma
* Garin alkama
* Kwaiduwar kwai
*Bayani;* Zaki samu zuma mai kyau sai ki zuba ruwa tare da kwanduwar kwai danya da kuma garin alkama tare da man zaitun sai ki hada su waje daya ki jujjuya ki dunga shafawa fatar jikinki.


Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a shiga ta wannan link din* 👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/CzHKa3hRV7DDAAqmz8T1WZ
Share:

HUKUNCIN AMAFANI DA KAYAN KWALLIYA A CIKIN WATAN RAMADAN

HUKUNCIN AMFANI DA TOZALI, DA KAYAN KWALLIYA A CIKIN YININ RAMADHANA


– Tambaya: Menene hukuncin amfani da tozali ko wasu kayan kwalliya ga mata a cikin yinin ramadhana, kuma shin yana vata azumi ko a’a?

– Amsa: Tozali baya karya azumin ‘ya mace, ko na namiji, a mafi ingancin zance guda biyu na maluma, a kowani irin hali. Saidai kuma ayi amfani da shi da daddare shi ya fi dangane da mai azumi mace ko namiji. Haka kuma abubuwan da mata ke ado da su na sabulu ko mayuka, ko makamancin haka na dangin abubuwan da su ke alaka da fata kawai, misalin su kunshi (lalle), da kayan barbade-barbade da makamantan haka, dukkan wadannan babu laifi ga mai azumi mace, ko namiji su yi amfani da shi, tare da cewa baya halatta a yi amfani da kayan shafe-shafe matukar zai cutar da fiska (kamar canza mata kala). Allah ne majibincin dacewa!
Share:

FATAWA AKAN AURE


*``````📌 Albahral Ilmu* 🌴 *```*
*FATAWA A KAN AURE*
===================
 _*HUKUNCIN MACE TA YAFE WA MIJI KWANA A DAKIN TA, SA'ANNAN IDAN TAYI HAKAN ZATA CI GABA DA GIRKI NE?*_ 
===================

 *_Tambaya_* :

Assalam alaikum. Mal. Menene sharudda da hukuncin mayar wa miji kwana daya raba tsakanin matan sa?. Shin zata ci gaba da yin girki ma kan ta ne ita kadai koko har da shi zata yi ta aika mishi na shi 


 *_Amsa_* :

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah.


Bayani ya gabata cewa rabon kwanan aure daban, girki kuma daban, ga mai mata biyu ko abin da ya fi haka.


Don haka ramakon kwana dole ne sai dai idan ita matar ce ta yafe wa mijin domin haƙƙin ta ne.


Amma girki na iya kasancewa tare da ke, ko da yana ɗakin wata. Wannan baya nufin mai kwanan bata da ikon ta bashi abinci, ko ke ki aika mashi da abinci ba, kowace daga cikin ku na iya bashi girki, ya halatta, ko yana ɗakin wata ba naki ba. Dalili shine wani sashe na matan Annabi na aika ma shi da girki alhali yana kwanan wata ba wacce ta aiko girkin ba, kuma bai hana hakan ba, har ma wata rana Nana Zainab ta aika mashi da abinci alhali yana ɗakin Nana Aisha, ma'ana lokacin kwanan ta, sai Nana Aisha ta kaɓar da abincin har ta fasa kwanon, sai Annabi ya ɗauki sabon kwanon ta ya biya Nana Zainab da shi ya kuma ci abincin kuma yayi mata tayi. 
Ga hadisin, riwayar Bukhari 


عَنْ أَنَسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ عِنْدَ بَعْضِ نِسَائِهِ، فَأَرْسَلَتْ إِحْدَى أُمَّهَاتِ الْمُؤْمِنِينَ مَعَ خَادِمٍ بِقَصْعَةٍ فِيهَا طَعَامٌ فَضَرَبَتْ بِيَدِهَا، فَكَسَرَتِ الْقَصْعَةَ، فَضَمَّهَا، وَجَعَلَ فِيهَا الطَّعَامَ وَقَالَ: ((كُلُوا)). وَحَبَسَ الرَّسُولَ وَالْقَصْعَةَ حَتَّى فَرَغُوا، فَدَفَعَ الْقَصْعَةَ الصَّحِيحَةَ وَحَبَسَ الْمَكْسُورَةَ. 


Wannan riwayar Turmuzhiyy ke nan


عَنْ أَنَسٍ قَالَ أَهْدَتْ بَعْضُ أَزْوَاجِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ طَعَامًا فِي قَصْعَةٍ فَضَرَبَتْ عَائِشَةُ الْقَصْعَةَ بِيَدِهَا فَأَلْقَتْ مَا فِيهَا فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((طَعَامٌ بِطَعَامٍ وَإِنَاءٌ بِإِنَاءٍ)).Wallahu ta'aala a'lam.

 *29/10/2020*


 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*


*_Gabatarwa_* 
      *Abdulkadeer Umar Alshinkafawy * 
     
 
 *_Daga_* 
        *Zauren*
*📌Albahral Ilmu 🌴*
 Ga masu son shiga tura sunan ka/ki da number ta WhatsApp.
     *07064746551*
Share:

Total Pageviews

Translate

Featured post

DARUSSAN RAYUWA EPISODE 08

Darussan Rayuwa Episode 08 kenan, ku buɗe ku sha kallo lafiya. Ku shiga wannan link domin samun sauran bidiyoyin mu  https://youtube.com/cha...

Contact form