Search This Blog

Saturday, 4 December 2021

FASSARAR WAƘAR TU... TU HAI VOHI


*FASSARAR WAKAR* _*Tu,tu hai Vohi*_

• Fim: Yeh vaada raha.
• Shekara: 1982.
• Jaruman shiri: Rishi Kapoor,Poonam Dhillon,Tina Munim.
• Sauti: R. D. Burman.
• Mawaka: Asha Bhosle,Kishore Kumar. 
• Fassara: Ikrama Lawal (Ikram khan Veer)
08167789840.La La La La La La... La La
La La La La La La...

Tu Tu Hai Wohi, Dil Ne Jise Apna Kaha

*Kai ne wanda zuciya ke Kira da mallakin ta*

Tu Hai Jahaan Main Hoon Vahaan

*Ina nan a duk inda kake*


Ab Toh Yeh Jeena, Tere Bin Hai Saza

*Yanzu rayuwa in babu kai azabtarwa ne*


O... Mil Jaaye Iss Tarah, Do Leharein Jis Tarah (x2)

*O...Mu hadu tamkar iska biyu masu kadawa*(x2)


Phir Ho Naa Juda, Haan Yeh Vaada Raha

*Kuma alkawari ne baza mu taba rabuwa ba*


La La La La La, La La La La La

Mai Aawaaz Hoon Toh,Tu Hai Geet Mera (x2)

*Ni sauti ne,kai ne wake na (x2)*


Jahaan Se Niraala Manmeet Mera

*kai ne ka cancanta da abokin rayuwa daga wannan duniyar*


Mil Jaaye Iss Tarah, Do Leharein Jis Tarah

*Mu hadu tamkar iska biyu masu kadawa*


O... Mil Jaaye Iss Tarah, Do Leharein Jis Tarah

*O....Mu hadu tamkar iska biyu masu kadawa*


Phir Ho Naa Juda, Haan Yeh Vaada Raha 

*Kuma babu rabuwa,eh wannan alkawari ne*Kisi Mod Pe Bhi Naa Yeh Saath Toote

*Tarayyar mu babu rabuwa a kowani irin hali na rayuwa*Mere Haath Se Tera Daaman Na Chhute

*Hannu na bazai taba barin mayafinki ba*
 
La La La La La, La La La La 

Kabhi Khwaab Mein Bhi Tu Mujhse Na Roothe

*Koda a mafarki ne kada ka taba Fushi dani*


Mere Pyaar Ki Koyi Khushiyaan Na Loote

*Wani bazai taba sace farin cikin soyayya na ba*Mil Jaaye Iss Tarah, Do Leharein Jis Tarah (x2)

*Mu hadu tamkar iska biyu masu kadawa(x2)*

Phir Ho Naa Juda, Haan Yeh Vaada Raha 

*Kuma babu rabuwa,eh wannan alkawari ne*


Tu Tu Hai Wohi, Dil Ne Jise Apna Kaha

*Kece wacce zuciya ke kira da mallakin ta*


Tu Hai Jahaan Main Hoon Vahaan

*Ina nan a duk inda kike*


Ab Toh Yeh Jeena, Tere Bin Hai Saza

*Yanzu rayuwa in babu ke azabtarwa ne*


Tujhe Main Jahan Ki Nazar Se Chura Loon

*Zan dauke ka daga idon duniya*


Kahin Dil Ke Kone Me Tujhko Chhupa Loon

*Zan boye ka a wani wuri cikin zuciya na*


Kabhi Zindagi Mein Pade Mushkilein Toh

*Koda akwai mawuyacin yanayi a rayuwa*


Mujhe Tu Sambhale, Tujhe Main Sambhaloon

*Ki kula da ni,nima in kula da ke*


O... Mil Jaaye Iss Tarah, Do Leharein Jis Tarah (x2)

*O...Mu hadu tamkar iska biyu masu kadawa(x2)*


Phir Ho Naa Juda, Haan Yeh Vaada Raha 

*Sa'annan babu rabuwa,eh wannan alkawari ne*

Tu Tu Hai Wohi, Dil Ne Jise Apna Kaha

*Kece wacce zuciya ke kira da mallakin ta*

Tu Hai Jahaan Main Hoon Vahaan
*Ina nan a duk inda kike*


Ab Toh Yeh Jeena, Tere Bin Hai Saza

*Yanzu rayuwa in babu ke azabtarwa ne*


O La La La La La La...

Phir Ho Naa Juda, Haan Yeh Vaada Raha

*Sa'annan babu rabuwa,eh wannan alkawari ne*


Yeh Vaada Raha

*Wannan alkawari ne*

*Ikram Khan Veer(08167789840)*

Friday, 3 December 2021

,

ZA A IYA KARANTA AL-QUR’ANI A SUJADA ?

ZA A IYA KARANTA AL-QUR’ANI A SUJADA ?
:
*TAMBAYA*❓


:
Assalamu alaikaikum warahmatullah malam dan Allah tambaya wai idan mutum yana cikin sallah a Cikin  sujjada saiya karanta ayar qur'ani wai sujjadar ba'adi tahau kansa

:
*AMSA*👇
:
Wa’alaykumussalam
Hadisin Aliyu bin Abi dhalib ya hana karanta Qur’ani a cikin ruku’i da sujada. Muslim ya fitadda shi cikin sahihin sa. Da wannan hadisin malamai suka ce makaruhi ne karanta alkur’ani a cikin ruku’i da sujada, sallah tayi ba za’ayi ba’adi ba. 

Wallahu a’alam

Malam :Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
,

ZAN IYA CIN BASHIN BANKI SABODA ZUWA HAJJI?ZAN IYA CIN BASHIN BANKI SABODA ZUWA HAJJI?:
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum, malam don Allah ina da tambaya kamar haka – ko zan iya cin bashin banki wato loan domin cika kuɗin kujerar maka,? Nabiya ma mahaifiyata sabida karin kuɗin da akayi ya wuce abinda muke zaton cikawa kuma ni ma’aikaciyar gwamnati ce. Na gode Allah yabada ikon amsawa.

:
*AMSA*👇
:
Wa alaikum assalam,
mutukar ba ki da hali to barin zuwa aikin hajjin shi ne daidai,, saboda Allah ya kwashewa kuɗin ruwa albarka a cikin suratul Bakara kuma ya yi shirin fito-na-fiton yaƙi da wanda ya ci riba, sannan Allah bai wajabta miki hajji ba ta hanyar bashi,, balle kuma ki biyawa wani.

Hajji yana wajaba ne ga wanda yake da iko da kuma isasheshen guzirin da zai wadatar da shi daga rokon mutane.

Allah ne mafi sani

*Amsawa*
*DR.JAMILU YUSUF ZAREWA*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
,

SHIN YA HALLATA NA YIWA WANI DAWAFI?

SHIN YA HALLATA NA YIWA WANI DAWAFI?
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum malam yayata ta jidda ta ce in tambaye ka menene hukuncin yin dawafi ga wani, saboda mutane suna yawan bugowa suna cewa a musu dawafi, kuma ta ce in gaya ma wai don Allah ka amsa a facebook, saboda ana bukatar sanin amsar.

:
*AMSA*👇
:
Wa alaikum assalam To ‘yar’uwa babu wani dalili ingantacce wanda yake inganta yiwa wani dawafi, sannan kuma ba’a samu magabata na kwarai suna yi ba, ga shi kuma dawafi ibada ce, ita kuma ibada ba’a yin ta sai da dalili daga Alqur’ani ko Sunna, amma dai ana iya yiwa wani addu’a lokacin da mutum yake yiwa kansa dawafi.
Akwai dalilai da yawa wadanda suke nuna ingancin yiwa wani Umara ko Hajji, saidai ba’a samu na dawafi a karan kansa ba.
Kiyasin dawafi akan Hajji da Umara ba zai yiwu ba, saboda dawafi tsantsar ibadar jiki ce, hajji da umara kuma ibadu ne da suka hada jiki da dukiya, duk ibadar da ta hada jiki da dukiya, tana amsar wakilci, amma wacce ake yin ta da jiki kawai ba ta amsar wakilci kamar sallah.

ALLAH NE MAFI SANI

Duba Fatawaa Nurun Aladdarb mai lamba ta : 87

*Amsawa*✍🏻
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ

,

BA YA HALATTA AYI RANTSUWA DA ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)BA YA HALATTA AYI RANTSUWA DA ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum Dr.ya halatta na ce na arantse da Annabi muhammadu maimakon na rantse da ALLAH ?

:
*AMSA*👇
:
Wa alaikum assalam Bai halatta ba.
Duk wanda zai yi rantsuwa, ya wajaba ya yi da Allah ko siffa daga cikin Siffofinsa kamar yadda hadisi ya tabbatar.

Allah ne mafi sani

*Amsawa✍🏻*
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ

WANDA YA MUTU YANA SHAN TAƁA SIGARI, BAI TUBA BA?WANDA YA MUTU YANA SHAN TAƁA SIGARI, BAI TUBA BA?:
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaykum, Ina fatan Dr yana Lafiya. Dan Allah menene Hukuncin Mai shan taɓa (sigari), har ya mutu bai tuba ba?. Na gode.

:
*AMSA*👇
:
Wa alaikumus salaam wa rahmatullahi wa barakaatuhu, Dukkan wanda ya mutu yana shan taɓa (sigari) bai tuba ba, yana karkashin ikon Allah, in ya so ya gafarta masa, in ya so ya kama shi da zunubin shan taɓar da ya yı, saboda shan taɓa haramun ne, saboda ta kunshi cuta, kuma duk abin da yake cuta ne tsantsa haramun ne, kamar yadda ayoyin Alqur’ani da hadisan manzon Allah ﷺ suka tabbatar.

Allah ne mafi sani.

*Amsawa*✍🏻
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
,

ZAN IYA SHAN MAGANIN TSAYAR DA HAILA SABODA AIKIN HAJJI?
ZAN IYA SHAN MAGANIN TSAYAR DA HAILA SABODA AIKIN HAJJI?
:
*TAMBAYA*❓
:
Tambaya garemu kamar haka? Ya halatta mace ta tsayar da jinin haila saboda hajj??

:
*AMSA*👇
:
To ‘yar’uwa Ya halatta, mutukar likita ya tabbatar miki ba zai cutar da ke ba, saidai tsayawa a Dabi’ar da Allah ya halicce ki akai shi ya fi kyau, saboda shan magunguna irin waɗannan yana birkita kwanakin al’ada, kamar yadda bincike ya tabbatar.

Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ

KIRAN SALLAH MA WAHAYIN SHI AKA YI ?KIRAN SALLAH MA WAHAYIN SHI AKA YI ?:
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum 
Malam, kira sallah (adhan) Allah ya saukar da shi kaman yan da YA saukar da Al Qur’ani zuwa ga Annabi Mohammad (S.A.W)? Ko kuma ya aka samota acikin addini muslinci?

:
*AMSA*👇
:
Wa’alaykumussalam, 

Hadisi ya inganta cikin swahihul bukhari 569 daga Nafi’u cewa ibn Umar yace lokacin da musulmai suka zo garin madina sukan taru su rika kirtatan lokacin sallah ba’a kiran sallah, wata rana sai suka tattauna wasu sukace a samu kararrawa irin kararrawar nasara, wasu sukace a’ah, a samu kaho ko wusir irin na Yahudawa sai umar yace ku fara aika wani yayi kiran sallah, sai manzon S. A. W yace ya kai bilal tashi ka kira sallah.
Akwai ruwayar data zo cikin sunan na abi dauda 420, wadda ta nuna cewa  Abdullahi bn zaid ibn Abdi rabbihi wata rana yana tsakanin bacci da falke sai wani yazo masa ya koya masa kiran sallah, da gari ya waye yazo wajen manzon Allah ya bayya masa, Ashe Umar bin khaddab ya dade da yin mafarki kiran sallah kusan kwana ashirin amma bai gaya wa manzon Allah ba sai ranar da Abdullahi ya gaya wa manzon Allah, sai manzon Allah bai ce umar me yasa baka gaya mun tun tunni ba. sai yace ya kai bilal tashi kaje ka kira sallah.

Wannan shine tarihin samuwar kiran sallah.

Wallahu a’alam. 

Malam *Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
,

YA HALATTA AMARYA DA ANGO SU SANYA ZOBEN ZINARI A RANAR AURENSU?YA HALATTA AMARYA DA ANGO SU SANYA ZOBEN ZINARI A RANAR AURENSU?:
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum
Dan ya halatta Amarya da Ango su sanya zoben zinari a ranar aurensu?:“`

:
*AMSA*👇
:
وعليكم السلام ورحمة الله.

ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ

Haramun ne ga Namiji yasa zobe ko wani abu na zinari a kowanne irin yanayi.
_*Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam)* ya haramta zinare ga mazan wannan al’umma. Yaga wani mutum yana sanye da Zobe na zinare sai shi *(Manzon Allah)* ya cire zoben daga hannunsa (mutumin) sannan yace:  *Shin dayanku zai dauki garwashi daga wuta ya rike a hannunsa*_
_*(Muslim ya ruwaito shi, Al-Libaas wal-Zeenah , 3897).*_

Saboda haka bai halatta ga Namiji yasa Zoben zinari. Amma idan zoben azurfa ne ko sanholama ko wani karfe mai kyalkyali babu laifi Namiji zai iya sanyawa a hannunsa.
Amma ya halatta ga mata suyi amfani da Zoben zinare da kayan da akayi su da zinare.
Saka Zobe tsakanin amarya da ango ko tsakanin Mata da Miji ko tsakanin masoya masu niyyar yin aure, idan an sashi ne da sunan zai kara karfafa soyayyar junansu. To wannan haramun ne qada’an!!!. Saboda ya zama wani nau’in ne na shirka.
_*(Al-Fataawa al-Jaami’ah lil-Mar’ah al–Muslimah , Mujalladi na 3, shafi na 914-915)*_

والله أعلم،

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
,

YA ZAN FAHIMTAR DA IYAYENA IDAN ZAN KARA AURE ?YA ZAN FAHIMTAR DA IYAYENA IDAN ZAN KARA AURE ?:
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum
Malam Aure nake son karawa kuma alhamdulillah Na sami fahinmtar juna da matata. 
Malam. kaban shawara Ina da mahaifi ya zan yi na fahimtar da shi da kuma mahaifiyata?Sannan se shawarwari akan hanyoyin da zan kara auren
Na gode

:
*AMSA*👇
:
Wa’alaykumussalam
Shawara:
1. Ka samu lokacin da suke cikin walwala da farin ciki na wani alhari da ka taba musu, sai ka sanar dasu cikin natsuwa da ladabi.
2. Ka yi kokarin samun gamsassun hujjoji don gamsar dasu, sannan ka ta naji amsar duk tambayar da zasu iya maka.
3. Ka yi kari akan kyautata musu da kake yi, hakan nada tasiri wajen karbar duk abida ka je musu da shi ba tare da sun maka inkari ba. 
4. Kana iya wakilta wadan dan da kasan cewa iyayen ma na ganin mutuncin su, sai je suyi ma iyayen ka magana.
Hanyoyin kara Aure:
1. Ya zamana kana da hali wato kafi karfin wurin zama da abinci da sutura da sauran su. 
2. Ya zama zaka iya Adalci a tsakanin su
3 ya zama bazaka samu ci baya ba ta fuskar addini ka misali ka auri wadda zata hana ka yin addini. 
4. Ya zama kafi karfin mace daya wato kana da karfin sha’awa. 
5. Ya zama manufar ka shine yi don Allah da tsaida sunna, ba don wani abu na duniya ba. 
6. Kayi istikhara/addu’a 
Insha Allah idan akayi riko da wadannan muna fatar Allah zai kawo maka sauki da mafita. 
Wallahul Musta’aan

*Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ

CIWO YA DAMENI, ZAN IYA AMSAR BASHI DA RUWA DON NA YI MAGANI?CIWO YA DAMENI, ZAN IYA AMSAR BASHI DA RUWA DON NA YI MAGANI?:
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum, mutum ne yake cikin halin rashin lafiya, kuma al’ummah da suke tare ba masu taimakawa ne ba,gashi wannan ciwon nason ya hallaka shi, shi kuma ba shi da kudi kuma ba shi da hanyar kudi, malam shin zai iya karbar kudin LOAN na govt don surika cirewa duk wata, ko babu halin haka nagode Allah yakara karfin imani da basirah

:
*AMSA*👇
:
Wa’alaIkumus salam, Ya halatta ya amshi rancen mai ruwa, mutukar abin da yake damunsa, ya kai wancan halin da ka ambata, saboda larura tana halatta abin da aka hana, saidai ya wajaba ya amsa gwargwadon bukata.

Allah ne mafi sani.

*Amsawa*
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
,

ZAMAN MAKOKI A MUSULUNCIZAMAN MAKOKI A MUSULUNCI:
:
*TAMBAYA*❓
:
Malam mahaifina ya rasu, sai wani malamin islamiyyarmu ya ce min ba kyau zaman makoki, to gaskiya kaina ya daure, saboda na taso na ga ana yi, kuma idan ban yi ba za’a ce ban damu da mahifinmu ba, malam yanzu yaya zan yi ? Allah ya datar da kai zuwa dukkan alkairai .

:
*AMSA*👇
:
To dan’uwa Allah ya ba mu dacewa gaba daya, tabbas malamai sun tattauna akan hukuncin zaman makoki, saidai sun kasu kashi uku :

1. Akwai wadanda suka tafi akan makaruhi ne, saboda hadisin Jarir RA wanda Imamu Ahmad ya rawaito cewa: “Mun kasance muna kirga taruwa yayin mutuwa da kuma yin abinci ga gidan da aka yi mutuwa daga cikin rurin da Allah da ya haramta” , Musnad : 6905, don haka suna cewa, saidai a hadu da wadanda aka yiwa rasuwa akan hanya ko a kasuwa, ko masallaci ayi musu ta’aziyya, wannan ita ce maganar Shafi’i a cikin Umm 1\318, haka Nawawy a Majmu’u 3\306 .

2. Akwai wadanda suka ta tafi akan cewa bidi’a ne, kamar Ibnul-kayyim a zadul ma’ad 1\527

3. Akwai malaman da suka tafi akan halaccin zaman makoki, saboda hadisin da nana A’isha ta rawaito cewa, lokacin da aka kashe Zaid dan Haritha da Ja’afar dan Abu-dalib Annabi s.a.w. ya zauna a wani wuri, duk wanda ya gan shi zai ga alamun bakin cikin tare da shi, sai wani mutum ya zo ya ce masa : ga matan Ja’afar can suna ta kuka, sai Annabi s.a.w ya umarce shi da ya je ya hana su, su kuma yi hakuri” Bukhari hadisi mai lamba ta : 1299. Wadannan malaman suna cewa : Za’a iya fahimtar hallacin zaman makoki a wannan hadisin a wurare guda biyu :

A. Fadin nana A’isha cewa : ya zauna ana ganin alamun bakin ciki tare da shi da kuma zuwan wancan mutumin, dalili ne da yake nuna cewa : yana zaune ne a wurin da mutane suka sani kuma suke zuwa su same shi.

B. Kasancewar bai hana matan Ja’afar taruwar da suka yi ba, kawai kukan ya yi umarni da a hana su.
Wannan magaanar ta hallaci an rawaitota daga Imamu Ahmad kamar yadda ya zo a Insaf 5\565 da kuma Ibnu-Abdulbarr na Malakiyya,, kamar yadda ya zo a littafinsa na Alkafy 1\283, sannan wasu daga cikin Hanafiyya sun tafi akan haka kamar yadda ya zo a Binaya 3\303
Prof. Khalid Al-mushakih (daya daga cikin manyan daliban Sheik Bn Uthaimin) ya rinjayar da zance na uku, saidai za’a guji abubuwa kamar haka a lokacin wannan zaman :

1. Yawaita yin abinci, da masu karbar gaisuwa, zai yi kyau ya zama makusantansa ne kawai za su amshi gaisuwa.

2. Nisantar yin laccoci a wurin, domin hakan na daga cikin bidi’o’in da ba su da hujja.
3. Nisantar tsawaita zaman, a yi shi gwarwadon bukata.
Don neman karin bayani duba : Fiqhunnawazil na Khalid Al-mushaikih shafi na : 75

Allah ne mafi sani.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ

Tuesday, 30 November 2021

MIJINTA YANA KALLON HOTUNAN BATSA (BLUE FILMS)

MIJINTA YANA KALLON HOTUNAN BATSA (BLUE FILMS)
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun bakin ciki shine shi da kansa yake tambayesu su aiko masa dashi. idan yagani sai kaji yace yayi missing dinsu kuma dasuna kusa da sai yayi making love dasu, duk lokacin da na buɗe wayansa zanga ire-iren wannan pictures a wayarshi. wanima zakaga mace da namiji suna sex ni kuma narasa ta inda zan masa magana saboda zaice ina masa bincike awaya.kuma zamuyi fada da shi, kullun hankalina atashe yake bana samun isashshen barci.idan na tuna halin da mijina yakeciki, malam tambayata anan ya halatta narika daukan nawa hoton tsirara ina tura masa a waya kozai rage kallon na matan banza ko kuwa? ina neman shawara da adduarka Mal. wassalam.

:
*AMSA*👇
:
Wa alaikis salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Hakika abinda mijinki yake aikatawa, ko kaɗan bai dace ba. ya kauce ma hanyar Allah. Kuma ya afka cikin manyan manyan ALKABA'IR.
Shi dai kallo izuwa ga matar da ba taka ba, haramun ne koda ba tsirara take ba. Shi kuwa kallon tsaraici, Allah (Swt) ya la'anci masu yi, kuma ya la'anci masu nuna tsaraicin nasu da gangan don akalla.
Mijinki yana nuna miki Qarara cewa Shi mazinaci ne kenan. Saboda haka shawarar da zan baki anan it a ce : Ki bi abun ahankali. kar ki sanya gaggawa ko husuma acikin sha'anin. in ba haka zai iya rikicewa.

1. Ki samu mijinki kiyi masa wa'azi cikin murya mai sanyi. Ki gaya masa cewa Allah (swt) ya umurci muminai maza su rintse idanuwansu, su kiyaye al'aurarsu daga zina da dangoginta.
Manzon Allah ﷺ acikin wani hadisi yana cewa :
"SHI KALLO, KIBIYA NE MAI TSANANIN GUBA DAGA CIKIN KIBIYOYIN IBLIS. DUK WANDA YA BAR KALLON DON TSORON ALLAH, TO ZAI SAMU (QARUWAR) IMANI WANDA ZAI RIKA JIN ZAQINSA AZUCIYA".
Kiyi masa wa'azi sosai ki tsoratar dashi game da mummunan Sakamakon da zai riska idan bai tuba ba. Ki gaya masa yaji tsoron ranar tashin Alqiyamah, ranar da Allah zai sanya gabobin jikinsa su rika magana suna bada shaida akan laifuffukan da ya aikata.

2. Idan yaki kin wa'azin naki, to babu laifi ki hadashi da wani mai hankali daga cikin abokansa domin yayi masa nasiha. Insha Allahu zai ji kuma zai yarda.

3. Kar ki dauki irin mummunar hanyar da wadancan matan suka bi. Domin kuwa idan kika zuba masa Hotunanki Tsirara acikin wayarsa, zata yiwu watarana wani daga cikin abokansa ko 'yan'uwansa ya dauki wayar, kuma ya leka ciki ya ganki tsirara. kinga wannan bai yi daidai ba.

Babban abinda mijinki yake bukata daga gareki shine ladabi, biyayya, da nasiha agareshi cewa yaji tsoron gamuwarsa da Ubangijinsa.

4. Ki matsa ma mijinki ya rika halartar jam'in sallolinsa a masallaci, kuma ya rika karanta Alqur'ani ayawancin lokutansa.

5. Ki sanyashi cikin addu'o'inki ako yaushe. Kuma muma muna yi miki fatan Allah ya shiryi mijinki ya cire masa son zina. ya cika masa zuciyarsa da tsoron Allah.

WALLAHU A'ALAM.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ


,

HUKUNCIN HAPPY BIRTHDAYHUKUNCIN HAPPY BIRTHDAY
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum.
Dr ina yimaka fatan alkhairi
Gameda hukuncin  murnar zagayowar ranar haihuwa [Birthday].
Wasu na ganin bidi'a ne, wasu kuma na ganin ba bidi'a bane tunda ba addini bane kuma wanda yayi baya tsammanin samun lada daga ubangiji
To malam yaya Al'amarin yake?
Kahuta lafiya

:
*AMSA*👇
:
Wa alaikum assalam, a zahirin gaskiya happy birthday ya fi kama da al'ada, saboda ba wanda yake yinsa da nufin ibada ko neman lada da kusanci da Allah,  ita kuma bidi'a tana shiga addini ne kawai.

Ya halatta a farar da abin da babu shi a zamanin manzon Allah,  mutukar ba'a  ibada ba ne ba'a kuma nufaci lada da shi  ba, wannan yasa amfani da Radio da Makirfon da jirgi da carbi ya halatta duk da cewa babu su a zamanin mazon Allah (SAW) .

Saidai duk da haka barin HAPPY BIRTHDAY shi ne ya fi zama daidai saboda duk lokacin da ranar haihuwar mutum ta zagayo yana kara kusantar kabari ne rayuwarsa kuma ta ragu,  don haka yin bakin ciki a irin wannan yanayin shi ne ya fi  fiye da  nuna farin ciki.

Magabata nagari sun kasance suna bakin ciki duk lokacin da suka tina wani bangare na rayuwarsu ya shude, Hasanul-basry yana cewa: (Ya kai dan'adam ba wani abu ba ne kai sai yininnika, duk lokacin da  wani yini ya wuce wani bangarenka ya tafi .

Haramta Birthday da bidi'antar da masu aikatata yana bukatar dalilin sharia,  saboda babin al'adu a buɗe yake har sai an samu dalilin haramci, don haka ya halatta, tare da cewa nuna bakin ciki idan ranar haihuwar ta zagayo shi ya fi fiye da nuna farin ciki saboda abin da ya gabata na aikin magabata na kwarai.

Allah ne mafi sani

*_Dr. Jamilu Zarewa_*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ

SALATIN ANNABI S.A.WSALATIN ANNABI S.A.W
:
*TAMBAYA*❓
:
_Wannene Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam Wanda yazo daka gareshi?_
:
*AMSA*👇
:
_Salati Ga Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yana cikin ayyukan dake kusantar da bawa ga Ubangijinsa, aikine maɗaukaki wanda shari'a tai Umarni dashi,_ 
.
 _yana daka cikin Mafi Amfanin addu'ar dazata Amfani bawa duniya da lahira, yana daka cikin Ababenda suke nuna cikar sonka ga Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam, dakuma girmamashi dabashi hakkinsa._
.
_Anruwaito ruwayoyi masu yawa ingantattu na kala-kalar salati ga Annabi Sallallahu Alaihi wasallam, Zaka iya Komawa garesu acikin littafin *Sifatul salatin Nabiyyi Na shaik Albany shafi Na (165) bugun Maktabatul Ma'arifi riyaazh)*_ 
.
_Daka cikin Mafi ingancin sifofi wanda sukafi shahara sune sigogi guda biyu:_
.
_Wanda *Annabi Sallallahu Alaihi wasallam* yakoyar da sahabbansa Allah yakara musu yarda lokacinda suka tamabayeshi ._
.
_*‏« ﺍﻟﻠﻬﻢَّ ﺻﻞِّ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤَّﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﻣﺤﻤَّﺪ، ﻛﻤﺎ ﺻﻠﻴﺖَ ﻋﻠﻰ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ؛ ﺇﻧَّﻚ ﺣﻤﻴﺪٌ ﻣﺠﻴﺪ . ﺍﻟﻠﻬﻢَّ ﺑﺎﺭِﻙ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤَّﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﻣﺤﻤَّﺪ، ﻛﻤﺎ ﺑﺎﺭﻛﺖَ ﻋﻠﻰ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ؛ ﺇﻧَّﻚ ﺣﻤﻴﺪٌ ﻣﺠﻴﺪ‏»*_ .
.
_*Bukhari (3370) da Muslim (406)* daka hadisin Ka'ab Bin Ujrah Allah yakara masa yarda._
.
_*Dakuma:*_
.
_*‏« ﺍﻟﻠﻬﻢَّ ﺻﻞِّ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤَّﺪ ﻭﺃﺯﻭﺍﺟﻪ ﻭﺫُﺭﻳَّﺘﻪ، ﻛﻤﺎ ﺻﻠﻴﺖَ ﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ، ﻭﺑﺎﺭِﻙ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤَّﺪ ﻭﺃﺯﻭﺍﺟﻪ ﻭﺫُﺭﻳَّﺘﻪ، ﻛﻤﺎ ﺑﺎﺭﻛﺖَ ﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ؛ ﺇﻧَّﻚ ﺣﻤﻴﺪٌ ﻣﺠﻴﺪ ‏»*_
.
_*Bukhari (3369) da Muslim (407)* daka hadisin Humaid Assa'idy Allah yakara masa yarda._
.
_Annabi Baya zabar Abu sai mai daraja da falala._
.
_*Duba Rauzatul Dhalibeen Na nawawi (11/66) da fat-hul baary (11/166) da Sifatul salatin Nabiyyi Na Albany shafi na (175) da Mausuu'ah fiqhiyyah kuwaitiyyah (27/97).*_
.
_Abunda yafi shine caccanzawa wajan yin Salatin yau kayi wannan gobe kuma kayi wannan. dan bin sunnah, dan kada kuma amakalewa ɗaya, sauran kuma aqaurace musu, dakuma falala maiyawa datake tattare acikin wani wanda babu acikin dayan,_
.
_Bai halatta kuma hada dukkan lafuzzan sigogin asiga dayaba dan mutum yace yahada dukkan lafuzzan asiga guda danya dace da kowacce siga, wannan yasabawa sunnah, kamar yanda Malamai dayawa suka tabbatar da hakan,._
.
_*Duba Maj-mu'u fatawa na Ibnu taimiyyah (22/335, 24/ 242-247- 458) da Jala'ul Afhaam na Ibnul qayyeem shafi Na (373) da Qawa'idu ibnu rajab shafi na (14) da Sharhin Mumti'i (2/56-65, 3/29-98).*_
.
_Wannan idan awajan yiwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam salatine atahiyar karshe asallah._
.
_Amma idan awajan Sallah ne sigar salati ga Annabi da *( Allahumma Salli Ala muhammad Wa'ali muhammad ).*_
.
_Ibnu hajar yace: Mafi yawan malamai suna ganin lafazinda zai bada abunda akeso na salati ga Annabi yawadatar, amma acikin sallah mutum zai takaita akan wanda yazo, kada kuma yarage akan wanda yazo daka Annabi, dan dacewa da sunnah, dakuma bin Abunda aka ruwaito daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam._
.
_Saidai Malamai Sunce makaruhine mutum yalazimci yiwa Annabi Salati batareda Sallama Agareshi ba. saboda Allah yace:***_
.
_*ﺇِﻥَّﺍﻟﻠَّﻪَ ﻭَﻣَﻠَﺎﺋِﻜَﺘَﻪُ,ﻳُﺼَﻠُّﻮﻥَ ﻋَﻠَﻰﺍﻟﻨَّﺒِﻲِّ ﻳَﺎﺃَﻳُّﻬَﺎﺍﻟَّﺬِﻳﻦ َﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﺻَﻠُّﻮﺍ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠِّﻤُﻮﺍ ﺗَﺴْﻠِﻴﻤًﺎ*_ .
.
_Allah da mala'ikunsa suna salati ga Annabi yaku wadanda Sukai Imani kuyi salati agareshi tareda sallama._
.
_Bai halatta koda yaushe mutum ya lazimci yin Salati babu Sallalama ga Annabi ba, ko yalazimci sallama babu salati._
.
_kodai yahadasu baki daya ko kuma yau yai salati babu sallama, gobe yayi sallama babu salati danyayi koyi da Ayar._
.
_*Fat-hul bary (11/167.*_
.
_Misali ( Allahumma Salli Ala muhammad Wa'ali muhammad)._
.
_da Allahumma Salli Ala muhammad wa'alihi wasallam)._
:
Wallahu A'alamu.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
,

ZAN IYA JIRAN WANDA NAKESO HARYA GAMA KARATU, SANNAN MUYI AURE....?ZAN IYA JIRAN WANDA NAKESO HARYA GAMA KARATU, SANNAN MUYI AURE....?
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamualaikum malam tambayata shi ne shin mace zata iya jiran namiji akan aure ma'ana ita ta Isa aure shikuma Yana karatu amusulunce ya halatta tajira shi?

:
*AMSA*👇
:
Wa alaikumussalam 
To wannan yazama wahalar dakai domin ke kince kin isa aure, muqaddara kinkai shekara 20, shi kuma yanada shekara 25 kuma yana halin karatu kuma aqalla da kammala abinda yasamu dasamun aiki abarshi shekara biyar ataqaice, babu tabbas din zaisamu aikin ko akasin haka, kinga kenan kinkai 25 shikuma yanada 30 kuma ahakan ma babu tabbas alokacin kuma ke kina ganiyar quruciyarki kinada maneman. Dasuk fishi quality amma kince saishi.
.
Sannan kiyi tunanin zai iya mutuwa akowane lokaci domin bamida tabbas din zamukai anjima saidai mudinga sakarai, sannan kiyi tunanin zai iya ganin wadda tafiki birgeshi kuma kuma yadaina sanki qarshe kinyi zaman banza.
.
Duk Wanda yazo da niyyar aurenki aka samu duk wata nagarta da ake nema wajan namiji to ina baki shawarar ki aureshi kibar tunanin gaibu, idan kuma har izuwa lokacin baki samu mijin aurenba harya kammala yatarar dake azaune kuma Allah ya yaqulla shike nan amma karkisa aranki zaki jirashi domin wannan gurguwar shawarace wlh, Allah ya hada kowa da mazaje nagari

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ

MAMATA BATA KULA DA ADDINI KUMA GA YAWAN CIN BASHIMAMATA BATA KULA DA ADDINI KUMA GA YAWAN CIN BASHI
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Ailaikum warahmatullah
Malam ina da tambaya..
Ina cikin tashin hankali mamana bata kula da addini Sam..
1..bata rama Azumi na ramadan idan Tasha Azumi haka har wani Azumi zaizo bata rama bah yanzu haka lissafi nake A yanzu haka yakayi 50 Wanda Ake binta
2.. ya sheikh.. tana wasa da sallah sosai idan tayi asuba da wuya tayi sauran..
3 malam..ana binta bashi kusan 1 mil yanzu haka Wanda take kan ramawa..duk da yawan bashin ake binta baya hana ta dauka wani bashin
4 na karshe malam nayi duk wani hanya dan naga ta daina amma yagagara Akan wannan halin nata na zauna da mahaifina Akanta munyi magana Shima yace min yayi yaga ta chanza Amma ina yakasa 
Malam ina bukatan shawaran ataimakamin nagode Allah yakara hazaka da illimi Ameeen yarabbi🙏🙏 Allah yabada ikon Amsawa Ameeen✨

:
*AMSA*👇
:
 Allah kenan. Idan ya so sai ya jarrabi Mutum da Yayansa, wani kuma da matarsa, wani kuma da Mahaifiyar sa, wani kuma da Dansa. 
 Wanda duk Wadannan Sune Babbar Jarrabawa da Allah yake yiwa bawansa. Sabida babu yadda zaiyi da Al'amarin.
 Yaya zaka yi da Mahaifiyar ka?
 Yaya zakayi da Danka? 
 Yaya zaka yi da Matarka idan kuna da Manyan yara Irinka.?
  Sai dai Kawai kai da Mahaifinka. Tinda Kunyi kun kasa. Kuna yimata Addu'a. Domin Allah ya jarrabeku da ita.
 Ibada kuma da bata yi, wannan Tsakanin ta ne da Allah. Domin ba zai yiwu ku rama mata Azumin ba, haka Zalika ba zaku rama mata sallolin da bata yi ba. Alhalin tana Raye. Ko ta Mutu. Taki ta yi Azumi da gangan. Babu wani Maganar Ramuwa da wani Zaiyi Mata. Sai dai kawai Kuna Nema mata gafarar Allah.
  Bashi Kuma idan ta ci. Kar ku Biya mata. Ku bar ta idan Akayi mata Hukuncin da Shari'a ta Tanadar, sai ta dena. Daman dai Shari'a ta Tanadi Yiwa Mutum Hukunci ne dan ya Kiyaye.
 A baya wata Tayi min waya. Cewar sai Mahaifiyar ta, ta yiwa Mijinta waya, Wai ya kawo Mata Kuɗi Kamar dubu ɗari. Wanda ko a irin wannan lokacin da take yimasa waya ya kawo Mata wannan kuɗin, shi kansa ba shi da kuɗin da ya kai dubu biyu. Amma a haka zaici bashinya kawo mata. Tana ta zubar mata da Mutunci a wajen Mijinta, da sauran Al'umma.
  Sannan a haka zata ci bashin Mutane na kuɗi da yawa, Kamar dubu ɗari biyar, dunu ɗari Bakwai. Ita da Mijinta suna Biya mata. Gudun kar a wulakanta Mahaifiyar ta.
 Amma wannan baisa ta dena ba. Sai Dada cin bashin ma take yi. Idan an Biya wannan sai ta ci wani. 
 A haka Nace tayi Hakuri, ta bari idan ta ci kayan Mutane. An kulle ta a wajen Hukuma ta dena ci.
 Sabida su Kansu ta talautar da diyar ta. Ta talautar da Mijinta.
 Kai wallahi Wasu Mutanen ma basu san abinda ya kamata ba.
 Sabida haka ku ci gaba da yimata Nasiha. Idan ba zata dena ba. Sai ku Fita harkarta. Hukuncin da ya dace shi za'a yimata.
 Allah ya ce a kyautatawa iyaye. Amma kai a yanzu babu yadda zakayi da wannan Mahaifiyar ta ka. Sai dai Kuma Nasiha da Addu'a.

Allah shine Masani.

✍️
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08137783797

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ

ZAMAN MAJALISAZAMAN MAJALISA:
:
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
:
*TAMBAYA*❓
:
Mln mijina yakasance bayadawowa Sai cikin dare nikuma hakan Yana cutatar dani, Nagayamai Amman yakasa fahimtata Wai yana majalisa
Mln miye hukuncin majalisa aaddinance.

:
*AMSA*👇
:
 MAJALISSA...!!!
 Ita Majalissa Wuri ne da Maza suke taruwa Domin Karawa Juna Ilimin Rayuwar Duniya ko na Lahira. Mai kyau da Maras Kyau. Ma'ana Zancen Wuta Ko Aljannah.
 Sai dai a Irin wannan zamanin Namu a duniyance Kuma, zantattuka Marasa kyau din ya fi mai kyau yawa a MAJALISSAN Mu.
   Wannan ne ma yasa mata da yawa ba sa Son Mazajen su suna zuwa Zaman MAJALISSA. Sabida Wata Fitinar daga MAJALISSA Ake Kunno ta, ta zo ta same ki har Mazauninki.
 A MAJALISSA Ne fa zaka ji ance wane MATARSA TA FI KARFINSA, MATARSA TA SHANYE SHI, MATARSA TAFI KOWA A WAJEN SA, MATARSA SAI ABINDA TACE ZA'A YI, MATARSA SAI YADDA TAYI DA SHI, MATARSA KAZA-KAZA-KAZA. Musamman ma Wanda Aka Hango yana Zaman Lafiya da Matarsa. Ba'a ji yana kawo Complain din Matarsa MAJALISSA. Duk wannan suna Faruwa a zaman MAJALISSA.
  Wani Namijin kuma da ya ji an hakan. To fa Sabida Gidadanci Ko Rashin Zurfin Tunani, An Zuga Shi kenan. Sai yake ji a Zuciyarsa Ashe Haka mutane Suke Yimasa Irin Wannan Kallon, Matar sa tafi Karfin sa? Ashe daman mutane suna kallo na akan sai yadda mata ta Tayi da Ni. Ashe irin wannan Kallon Mutane Suke Yimin. Anan ne kuma Shaidan Zai Shiga Cikin Wannan Tunane-tunanen Nasa. Shikenan kuma idan ya Shigo gida, Sai Rashin zaman Lafiya da Matarsa. Da Sauransu. Ya Tsokano Chan, ya Tsokano Chan. Wai shi Dan dole sai yayi Rigima da Matarsa ya Korata gida, Domin ya Nunawa Duniya, Shi Matarsa ba ta fi Karfin sa Ba. Inba Allah ya Kiyaye ba, ton daga nan Za'a hana Gidansa Samun zaman Lafiya.

  A MAJALISSA ne ake Baiwa Wani Shawara ta Banza. Domin wani baya Iya Boye Surrun Zuciyarsa. Da zarar ya zo MAJALISSA. Anan zai Amayar da duk Abinda yake Cikin Zuciyarsa. Sai kuma ace ga yadda zakayi. Wani lokacin ma, babu Tunani. A haka zai je ya yanke Hukuncin da MAJALISSA ta Umarce shi. Daga baya kuma sai ya zo yana da na sani.

 Wallahi Billahi Ina Wata MAJALISSA, Wani bawan Allah ya zo da Complain Na Matarsa, akan ga abinda tayi Masa, Kawai Sakinta Zaiyi. Ake Famfa Shi. Cewar ya Kore ta, yayi mata Kaza da Kaza. 
 Anan ne fa Na Takarkare Nace da shi, wane, kayi Hakuri. Wannan ba wani Abu bane. An yiwa wani abinda ya fi wannan ma yayi Hakuri. Ka da ka sake ka saki Matarka. Kar ka Koreta. Ana son Namiji da Juriya idan Anyi masa ba Daidai ba. Sai Allah ya taimaka ya dauki bayani na. Amma Wallahi da zai dauki Hukunci Ne maras kyau. Kuma ba Mamaki daga baya ya zo yana Nadama.

  A zamanin Magabata. Basa Yin Zaman MAJALISSA, sai wadda za'a Tattauna akan Abinda ya Shafi Addini. Itama sai a cikin Yini, ba da dare ba. Da dare Idan anyi sallar Isha'i, kowa Cikin Iyalinsa yake Tafiya.
 A nan baya baya ma, MAJALISSIN Imam Ahmad Ibn Hambal. Ba'a yimasa Zancen Duniya. Sai dai Zancen Lahira. Duk wanda yayi masa zancen Duniya. To ba zai kara zuwa masa Majalisinsa ba har Abada. Sai dai ko idan ka Nemi Alfarmar ka dena zancen Duniya ne. Sai a Baka dama ka ci gaba da Zawa Majalisin sa. Amma dai ba zancej Duniya ba.
  A irin wannan zamanin Namu. Idan ka je wata MAJALISSAR ma ba zaka sake komawa ba. Sabida Abinda zaka Tarar na Rashin dacewa.

 Wata MAJALISSAR ta Masu Girman Kai ce. Sabida haka idan kai ba mai Girman kai bane Irinsu. Rena ka zasu yi. Daga nan Zaka gane ba Irin Tsarinka bane da da su. Sai ka dena Zuwa. Idan kuma ka ci gaba da zuwa, Kaima Irinsu zaka zama.

 Wata MAJALISSAR idan ka je, zaka Tarar yan Duniya ne. In banda zancen Banza babu abinda zaka Tarar Anayi. Idan kar Na gari ne kai. Wannan ma zai hana ka cigaba da Zuwa wannan MAJALISSAR. Idan kuma ka ci gaba da Zuwa, Kaima Irinsu zaka zama.

 Wata MAJALISSAR zaka tarar Fasikai ne. Sabida haka idan kai ba Fasiki bane. Ba zaka sake Zuwa wannan MAJALISSAR ba. Idan kuma ka ci gaba da zuwa. Kaima Irinsu zaka zama. Ma'ana Kaima zaka zama Fasiki.

Manzon Allah saw baya da wata MAJALISSA sai ta Sahabbansa. Idan ya fito za'a kwashi Ilimi. Sai kuma ya Koma Gida cikin Iyalinsa.
MAJALISSAR Manzon Allah ﷺ ba irin wannan bace za'a dakko zancen wannan a ajiye na wannan. A kwaso na waccan a ajiye na matar Wancan ko na Mijin Waccan. Manzon Allah ﷺ baya yin haka. Idan ya Zauna a MAJALISSAR sa, Sahabbansa zasu Kewaye Shi. Sai ya dinga Karanta Musu Irin abinda Ubangiji SWT ya Karantar da shi.
 Asali ma Manzon Allah ﷺ Ya Kyamaci Yin Shira bayan Sallar Isha'i. Domin Mutum ya samu yayi Barci da Wuri, ba Mamaki ko zai dace ya tashi yayi sallar Dare.
 Sannan Manzon Allah ﷺ Yace da wani Sahabinsa. "GIDAN KA YA WADACE KA". Sai Manzon Allah ﷺ ya Umarceshi da zama a gida. Tin daga Lokacin da Manzon Allah ﷺ ya gaya masa haka. Akace baya zama a wani MAJALISSA Sai a gidansa.

 Kaɗan daga Sharrin zaman MAJALISSA Shine. 
 YIN JAYAYYA/MUSU DA WANI. Wanda kuma manzon Allah ﷺ ya hana yin Musu. Harma yana cewa, duk wanda ya bar yin jayayya/Musu Akan wani Abinda yake da gaskiya Akansa. Allah ya Tanadar Masa Gida a Tsakiyar Aljannah.
 Sannan Manzon Allah ﷺ Yace Allah yana Fushi da Mutumin da yake da yawan Jayayya/Musu.
 WANI LOKACIN, ZAMAN MAJALISSA YANA KAWO GABA A TSAKANIN MUSULMAI. Duk Mutumin da Jayayya ta Hada ku da shi. Wannan jayayyar zata Iya zama Fada da Gaba da kuma Fushi a Tsakanin ku.

 WANI LOKACIN, ZAMAN MAJALISSA YANA KAWO HASSADA. Idan Mutum ya zo yana bayar da Labarin irin Ni'imar da Allah yayi masa na ci gaba a Rayuwar sa, ko irin kuɗin da yake samu a kasuwarsa ko wani Abu na daban. Sai kaga Wasu daga cikin Mutanen da yake Baiwa wannan Labarin. Da Zaka Bude, Zukatan Wasu daga Cikinsu. Ba daɗin labarin suke ji ba. Sabida ya samu wani abinda su basu Samu ba.

 WANI LOKACIN, ZAMAN MAJALISSA YANA KAWO GULMA. DA YADA SURRUN WANI. Manzon Allah saw Yace Duk wanda ka ci Fuskarsa ko ka ci Mutuncinsa ko kayi Gulmar Sa, Za'a dakko Ladanka na Sallah Ko na Azumi ko na kyautatawa Iyaye da kayi a nan gidan Duniya, Sai a bashi. Ko kuma a dakko Zunubinsa da ya Aikata a nan gidan Duniya a Dora Maka. 
 Kaga Kenan wannan Ba Karamin BALA'I bane. Ace Baka Aikata Lefi ba Anan gidan Duniya. Ka guji Aikata wannan Lefin Anan Gidan duniya. Gashi Kuma an kama ka da shi a Ranar Alkiyama. Asali ma sai kaga shine zai kaika ya zuwa ga Gidan Wuta.

  ZAMAN MAJALISSA YANA CINYEWA MACE LOKACIN DA TAKE DA SHI A WAJEN MIJINTA. SHIMA MIJIN YA CINYE MASA NASA LOKACIN. Wannan Ne ma yasa mata da yawa basa son zaman MAJALISSA. Sabida suna son samun lokacin ishashshe, domin Tattaunawa da Mazajensu. Amma kuma MAJALISSA ta Cinye Musu wannan Lokacin. 

 Wani lokacin ma idan Mutum bai fito ba. Har waya MAJALISSA take Yimasa. ☎️WAI KAI YA AKAYI KA JE KA SA TSOHUWAR MATARKA A GABA KA KASA FITOWA. Wai a dole sai MAJALISSA ta Tsofar Maka da Matar da kai kake ji da ita.
 WANI LOKACIN A MAJALISSA AKE ZUGA MUTUM YA KARA AURE. Wanda kuma wannan Shine Babban Masifar Matan da suke Gidan Mazajensu. Ba sa son a Karo Musu Kishiya. Kaga kenan dole ne mata zasuyi Adawa da MAJALISSA. Duk da Cewar Shi Aure Alkairi Ne.
  Sai dai kuma ta wani bangaren. 

MAJALISSA tana Taimakawa wajen Dubiyar Maras Lafiya, ko daukar Dawainiyar dan MAJALISSA idan bashi da Lafiya har zuwa Asibiti da Sauransu. Musamman ma idan mai Karamin Karfi Ne.   

  MAJALISSA tana shiga Al'amarin duk wanda yake Member Nata ne idan ya shiga halin da ya kamata a Taimaka Masa. Sannan idan an Baiwa Mutum tension a gida. MAJALISSA tana Iya Baka Labarin da zai sauke maka wannan tension din.
 Sai dai Ni Ina Bayar da Shawara ga Wanda yake Magidanci. Ba Za'a Ce ba zai Zauna a Wata Majalissa ba. Amma Dan Allah idan Mutum ya Fito, ya kamata ya Koma gida da Wuri. Minti Talatin ko Ashirin ko Goma ya Isheka Ku gaisa da Mutane. Kar Ace Kwana biyu ba'a Ganinka. Ko ba a gaisa da kai ba. Kayi kokari ka Koma Cikin Iyalinka da Wuri. Domin Suma suna da Hakki Akanki. Asalima Sune Suka Fi Kowa Hakki Akanka, ba yan MAJALISSA ba.

Amma wannan zaman da Mutane Suke yi, har su kai karfe sha biyu ko sha daya ko karfe Goma ko tsakiyar dare a waje. kai ba saye ba, ba sayarwa ba. Menene Wannan Din? Gaskiya ba Daidai bane. Ka Koma Cikin Iyalinka.
 Musamman ma wanda zai dawo daga kasuwa. Ka tafi Kasuwa Tin da Sassafe ko wurin Aiki tin Sassafe ko ka wuni a kasuwa kana Zirga-zirga, kuma idan ka dawo Gida kayi wanka ka sake Fita MAJALISSA. Ba zaka dawo ba, sai Cikin Dare. Menene Amfanin irin Wannan.? Kai kenan Baka da Hutu. Kuma iyalinka basu da lokacin ka? 
 Wani Namijin zai tafi yawonsa. Ko zaman MAJALISSA, Wai sai idan dare yayi, matarsa tayi Barci, Wai kuma Anan ne zai ce zai zo ya neme ta. Idan bata Kula shi ba, Sabida bacci ya dauke ta. Sai ya ji Haushi ko kuma wannan ma ya zama Abin fada. Wanda kuma ba Lefinta bane. Kai ne da Lefi.
 Ta yaya Mace zata ji dadin Jima'i bayan barci ya dauke ta. Ta yi wajen Awa Ukku Ko Sama da haka tana yin barci. Lokaci daya kazo kace sai ta bude maka Kafafunta.? Ba zai Yiwu ba...
 Sabida haka, dan Allah Maza Muna yin Abinda ya dace. Muna Fita Hakkin Wadannan Bayin Allah. Za'a Tambayemu Akansu fa a Ranar Alkiyama...
 Wacce irin amsa kake Tsammanin zaka bayar a gaban Allah ta yadda zamanka ya kasance tare da su a nan gidan Duniya.
 Allah ya datar da Mu Duniya da Lahira.

Allah Shine Masani.

✍️
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08137783797

GROUP ADMIN:👇
Mal. Khamis Yusuf
+2348087788208
+2348054836621
,

MAFARKI A LOKACIN JININ HAILAMAFARKI A LOKACIN JININ HAILA
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum Mallam dafatan kana lafiya.
Mal. ina cikin yin jinin al'ada ta ne sai nayi mafarkin da ban gamsu da shi ba (wato mafarkin Jima'i) kuma ban san ko na fitar da wani abu ba.

Toh mallam in na tashi wanka niyya biyu xanyi ko daya? Nagode.

:
*AMSA*👇
:
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

In dai lokacin da kika farka baki ga komai ajikinki ba, to wankan janabah bai wajbta akanki ba.

Shi wanka ana yinsa ne idan aka hakkake (tabbatar) da fitar Maniyyi ko ta dalilin mafarki ko afarke tare da jin dadi. Ko kuma ta dalilin boyuwar kan gaban Namiji ajikin Mace, koda bai yi inzali ba.

- Don Qarin bayani aduba wadannan litattafan : Matnul Akhdariy, Matnul Al-Ashmawiyyah, Iziyyah, RISALATUL QAIRAWANIY (Dukkansu aduba cikin babin dake magana akan Janabah).

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
,

MATSAYAR SHARI’A DANGANE DA ADDU’AN UKU GA MAMACIMATSAYAR SHARI’A DANGANE DA ADDU’AN UKU GA MAMACI
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum
Allah ya qara ilimi, ya bada ladan fatawa. 
Malam don Allah, taron addu’a da sadakan uku da akeyi bayan zaman makoki na kwana uku yana da hurumi a musulunci???

Shin akwai wani amfani da wannan adduar take dashi ga mamaci? 

Har akanyi abinci, kamar waina, a dinga rabawa ga duk wanda yazo wurin zaman makokin a ranar, da sunan SADAQA.

Don Allah Malam ayi min bayanin matsayar musulunci akan wannan al’amarin na *SADAKAR UKU*. 
Nagode kwarai, Allah ya saka ma Malam da alkhairi.

:
*AMSA*👇
:
Wa’alaykumussalam.
Sadakar uku ba karantarwar manzon Allah bane, hakanan ba aikin sahabbai da tabi’ai bane, shari’a bata iyakance lokuttan da ake yiwa mamaci addu’a ba, dazarar mutum ya rasu yana bukatar addu’a har iya rayuwar shi mai Addu’ar.

Tara mutane bayan kwana uku, da dafa abinci da raba waina duk waɗannan bidi’o’ine da aka kirkiro daga baya, *Babu wani dalili na shari’a akan haka*.

Manzon Allah ya fada cewa : …. “duk wanda ya kirkiro a cikin  al’amarin mu  (Addini/shari’a) abinda baya cikin addinin/shari’a toh an mayar masa”…. Don haka nisantar aikata haka shine dai dai.

Wallahu A’alam

*_Malam Nuruddeen Muhammad Mujahid_*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
,

IDAN UBA BAI YIWA DANSA YANKA BA RANAR BAKWAI, MENENE MAFITA?IDAN UBA BAI YIWA DANSA YANKA BA RANAR BAKWAI, MENENE MAFITA?
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum. yaa shaikh mutun ne Allah ta'ala ya bashi karuwa ta (haihuwa) bai samu hali yin yanka ba, har sai bayan wata huɗu tukunna Allah ya hore mashi, shin yankannan tana kanshi ko tafdaɗi???

:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikum assalam, Ya tabbata a cikin hadisin Tirmizi cewa ana yiwa abin da aka Haifa Akika ranar 7/wata.

Wasu malaman daga cikin Sahabai da wadanda suka zo bayansu sun yi karin bayani cewa: in ba'a samu damar yi ba ranar bakwai ana iya yi ranar 14 ko kuma ranar 21.

Duk wanda bai samu damar yiwa dansa yanka ba a kwanakin da aka ambata a sama, to babu wani kayyadajjen lokaci, zai iya yi duk lokacin da ya samu dama.

AKIKA hakki ne akan Uba zai yi kyau ya yiwa ɗansa a lokacin da Annabi S. a. w ya ambata, wato ranar bakwai ga haihuwa, in kuma ba shi da dama, ya yi masa da zarar Damar ta samu.

Allah ne mafi sani

Don neman karin bayani duba: Daka'iku Ulin Nuha 1/615.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ

Sunday, 28 November 2021

Yadda Ake Hadin Dayake Kara Ni'iman MaceSIRRIN MALLAKAN MIJINKI*


Yadda Ake Hadin Dayake Kara Ni'iman Mace

 
Zaki nemi kayan hadi kamar haka:
* Kirfat 
* Na'a-na'a
* Kanunfari
* Citta
* Zuma
*Bayani:* Zaki samu wadannan kayan hadin ki hadesu guri daya ki tafasa ki tace ruwan ki sa Zuma ki dunga sha.

 
Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai su tura da cikeken sunansu tare daga in da suke, ta wa'innan numban;* 👇 👇 👇

08162268959,08038902454
,

HUKUNCIN SHAN TABAR SHISHA

HUKUNCIN SHAN TABAR SHISHA
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum malam dan Allah minene hukuncin shan shisha a musulunci? Dan yanzu naga maza da mata yan mata da samari ta zamo musu sana'a.
(Daga K. Lawal Magaji).
:
*AMSA*👇
:
W/SALAM WA RAHMATULLAH.
Hakika dukkan abinda 'Dan Adam yake Ci ko sha, sun kasu ne zuwa gida biyu.
1. Akwai Tsarkaka Masu Daɗi.
2. Akwai kuma Marassa daɗi, Ko masu Najasa.
Su Tsarkaka masu daɗi sune waɗanda idan Ɗan Adam yayi amfani dasu zasu amfani jikinsa.
Su kuma Marassa tsarki sune irin su Giya, taba, Wiwi, Shisha da Sholisho da duk sauran kayan Maye. Saboda idan kayi amfani dasu ba zasu amfanarka da komai ba. Sai dai ma su cutar da lafiyarka, kuma su cutar da Hankalinka..
Kasancewar tabar Shisha batta amfanar da Ɗan Adam sai dai ma ta cutar dashi, Kuma gashi ana sayenta ne da kudade masu tsada, shi yasa sayenta ya zama Almubazzaranci.
Ubangiji (SWT) yana cewa:
"KAR KUYI ALMUBAZZARANCI. HAKIKA SU MASU ALMUBAZZARANCI SUN KASANCE 'YAN UWAN SHAITANU NE. SHI KUMA SHAITAN YA ZAMANTO YA KAFIRCE MA UBANGIJINSA NE"
Hakika duk musulmi mai hankali ba zai so ya aikata abinda zai mayar dashi ya zama 'Dan uwan Shaitan ba.
Hakanan zukar tabar Wiwi ko Sigari ko Shisha, yana haddasa ma mutum cutar Daji acikin Hunhunsa. wato LUNG CANCER. Wanda yakan zama sanadiyyar mutuwar matasa da dama.
Allah (SWT) YACE : "KAR KU JEFA HANNAYENKU ZUWA GA HALLAKA".
Bai halatta mutum Mai hankali kuma mai Imani ya rika shan irin waɗannan abubuwan ba.

WALLAHU A'ALAM.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ


Yadda Ake Hadin Tsumin Bawon Abarba Don Karin Ni'iman Mace*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*


Yadda Ake Hadin Tsumin Bawon Abarba Don Karin Ni'iman Mace


Zaki nemi kayan hadi kamar haka:
* Bawon ruman
* Garin citta 
* Garin kanunfari
* Garin mazarkwaila
* Zuma
*Bayani:* Zaki samu wadannan kayan hadin sai ki hadesu guri guda ki tafasa idan ya tafasa sai ki tace ki zuba Zuma ki dunga sha.


Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai su tura da cikeken sunansu tare daga in da suke, ta wa'innan numban;* 👇 👇 👇

08162268959,08038902454

Yadda Ake Hadin Dayake Karawa Mace Ni'ima*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*


Yadda Ake Hadin Dayake Karawa Mace Ni'ima


Zaki nemi kayan hadi kamar haka:
* Dabino 
* Kwakwa
* Aya 
* Abarba 
* Kankana
* Madarar ruwa
*Bayani:* Zaki samu wadannan kayan hadin sai ki hadesu guri guda ki gauraya sai ki markada ki zuba madara peak ki dunga sha.


Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai su tura da cikeken sunansu tare daga in da suke, ta wa'innan numban;* 👇 👇 👇

08162268959,08038902454

Yadda Ake Hadin Dayake Magance Matsalan Rashin Sha'awa*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*


Yadda Ake Hadin Dayake Magance Matsalan Rashin Sha'awa


Zaki nemi kayan hadin kamar haka;
* Garin citta
* Garin kur-kur
* Garin tafarnuwa
* Tsamiya
*Bayani:* Zaki samu wadannan kayan hadin ki hadesu guri daya ki tafasa ki tace ruwan ki dunga sha sau biyu a rana, in sha Allah zaki samu mafita.


Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai su tura da cikeken sunansu tare daga in da suke, ta wa'innan numban;* 👇 👇 👇

08162268959,08038902454

Yadda Ake Hadin Tsumin Baure*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*


Yadda Ake Hadin Tsumin Baure


Zaki nemi kayan hadi kamar haka:
* Sassaken baure
* Garin kanunfari
* Garin citta
* Garin minannas 
* Garin mazarkwaila
* Zuma
*Bayani:* Zaki samu sassaken baure ki tafasa idan ya tafasa sai ki tace ruwan ki maida kan wuta ki zuba duk sauran kayan hadin har ya tafasa sai ki tace ruwan ki dunga sha.


Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai su tura da cikeken sunansu tare daga in da suke, ta wa'innan numban;* 👇 👇 👇

08162268959,08038902454
,

HUKUNCIN MACE TA BIYAWA KANTA BUKATAHUKUNCIN MACE TA BIYAWA KANTA BUKATA.
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalama Alaikum. malam matar aure ce tana son mijinta ya sadu da ita, amma sai taga yana jin bacci sosai saita biyawa kanta bukata harta fitar da maniy.To bayan ta kwanta sai tayi mafarki shima ta farka taga maniy.To idan ta tashi wanka ɗaya zata yi ko biyu?.
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. 

Janabah ce ta sameta ta hanyoyi biyu daban-daban amma dai hukuncinsu ɗaya ne. Wanka ya wajaba akanta. Kuma wankan guda ɗaya ya isar mata. 

Sai dai gaskiya ta aikata babban kuskure ko laifi wajen biyawa kanta bukata din nan. 

Biyawa kai bukata (istimna'i) haramun ne bisa nassin Alqur'ani mai girma. Allah Madaukakin Sarki yana fa'dar siffofin bayinsa muminai mutanen kirki, sai yace. :

"DA WADANDA KE KIYAYE FARJOJINSU, SAI DAI BISA MATAYENSU KO ABINDA DAMSHINSU YA MALLAKA (WATO KUYANGI). 

DUK WANDA YA NEMI WANI ABU BAYAN WANNAN, TO (WADANNAN) SUNE MASU QETARE IYAKOKI".

Wato duk namiji ko macen da yake biya wa kansa bukata, ta hanyar da ba saduwa da matarsa ta aure ko mijinta na aure ba, to hakika ya Qetare iyakar da Allah ya ajiye masa.

Mafiya rinjayen Maluman Fiqhu sun tafi akan haramci wannan aikin, in banda Mazhabin Hanafiyyah su ka'dai sukayi sassauci akan wannan mas'alar suka ce makruhi ne.

Sannan kuma yin wannan abun yana iya janyo miki matsaloli ta fuskar lafiyarki. Kamar daskarewar maniyyi, ciwon mara mai tsanani, rikicewar tunani, ciwon makanta, rikicin jinin haila, da sauransu. 

Ya zama wajibi kiji tsoron Allah ki dena biyawa kanki bukata. Idan sha'awa ce ta dameki, gara ki tashi mijinki koda barci yakeyi, kin san hanyoyin da zaki bi kija hankalinsa domin samun biyan bukatarki. 

Sannan kiji tsoron Allah ki guji kallon finafinan batsa ko karanta labarun batsa domin suna iya zama dalilin watsewar tarbiyyarki. 

WALLAHU A'ALAM. 
DAGA ZAUREN FIQHU 

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ

CIKA ALWALA DA KUSHU'I A CIKIN SALLAH SUNA DAGA SABUBBA SHIGA ALJANNAH! (02)

CIKA ALWALA DA KUSHU'I A CIKIN SALLAH SUNA DAGA SABUBBA SHIGA ALJANNAH! (02)

•┈┈┈••✦💦✦••┈┈┈•

Daga Humraan Ƴantaccen bawan Usman bn Affan cewa shi yaga Usman bn Affan yasa an kawo masa abin alwala, sai ya zuba ruwa akan hannayen sa guda biyu daga kwanan alwalan sa, se ya wanke hannayen sa sau uku, sannan ya shigar da hannunsa na dama a cikin abin alwalan ya kuskure baki ya shaƙa ruwa kuma ya face, sai kuma ya wanke fuskansa sau uku da hannayen sa zuwa gwiwar hannu sau uku sannan se ya shafi kansa, sannan sai ya wanke kowace ƙafa sau uku sannan sai yace; Naga Annabi yana yin alwala kwatanmwacin wannan alwala tawa, sai (Annabi) yace: "Duk wanda ya yi alwala kwatanmwacin wannan alwala tawa sannan ya yi sallah raka'a biyu, bai tattauna wasu abubuwa ba (a ransa) Allah zai gafarta masa dukkan abinda ya gabata na zunuban sa. 

-BUKHARI&MUSLIM
  Dariqus-Silihin 15pg

Note:
• Cikin wannan alwalan ba'a ambaci shafar kunne ba, Malamai suka ce shafar kunne tana cikin shafar kai (ana haɗe su) shi yasa Humraan bai ambaci kunne ba. 

• Duk wanda ya yi alwala da irin wannan siga sannan ya yi sallah raka'a biyu ba tare da tunanin duniya ba za'a gafarta masa zunubansa baki ɗaya.

• Malamai suka ce, barin tunanin, ai idan tunanin yazo masa cikin sallan se ya danne ya fuskanci sallan sa. 

#Zaurenfisabilillah

Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah

CIKA ALWALA DA KUSHU'I A CIKIN SALLAH SUNA DAGA SABUBBA SHIGA ALJANNAH! (01)CIKA ALWALA DA KUSHU'I A CIKIN SALLAH SUNA DAGA SABUBBA SHIGA ALJANNAH! (01)

•┈┈┈••✦🌹✦••┈┈┈•

Daga Uƙbata bn Aamir Aljuhaniy, Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: "Babu wani Ɗaya da zai yi alwala, kuma ya kyautata alwalan sannan ya yi sallah raka'a biyu, yana mai fuskanta da zuciyar sa da fuskarsa akan su face ta wajaba a gareshi ALJANNAH!

 - MUSLIM

Note:
• Idan kana so ka sami wannan garaɓasa to se ya zamto tunanin ka da nutsuwanka yana kan wannan sallah. Zaka iya wannan sau Ɗaya Allah ya baka Aljannah.

Allah Ta'ala ya bamu Aljanna.

#Zaurenfisabilillah 

Telegram:https://t.me/Fisabilillaaah

MABIYANMU

NA MUSAMMAN

MUN BUƊE AJIN KOYAR DA HARSHEN HINDI A WHATSAPP

🏮🛕 HAIMAN INTERNATIONAL SCHOOLS (HIS) 🛕🏮  Admission ❗ Admission ❗❗Admission ❗❗❗ Makarantar Haiman International Schools Online classes ...