WAI SHIN SU FULANI BA ƳAN NIJERIYA BA NE?

Wai Shin Su Fulani Ba 'Yan Nijeriya Ba Ne?

Daga

Imam Murtadha Gusau

Lahadi, July 7, 2019

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Assalamu Alaikum

Ya ku jama'ar Najeriya! Lallai duk mai bibiyar abubuwan da suke faruwa a kasar nan ta mu yana kallo, kuma yana jin abubuwan da suke gudana kuma suke faruwa na raini, cin mutunci da wulakanci. Wani lokaci wadannan al'amurra su baka dariya, wani lokaci su sa ka kuka, wani lokaci su sa ka takaici, wani lokaci kaji kamar ka mutu ko ka hadiye rai, saboda bakin ciki da bacin rai!

Wadannan abubuwa ba komai bane illa kokarin da ake yi a mayar da wasu 'ya 'yan mowa wasu kuwa 'ya 'yan bora a kasar nan. A nuna cewa wasu shafaffu ne da mai, wasu kuwa ba haka ba. A nuna cewa wasu masu fada aji ne, wasu kuwa ba su da ta cewa. Koma sun ce din to baya da wani tasiri da girma a wurin hukuma!

Har kullum, a kasar nan Najeriya, mun dade muna yaudarar kawunan mu, da cewa MU KASA DAYA CE AL'UMMAH DAYA. Tabbas, ba shakka, mu 'yan arewa mun yarda da hakan, kuma tsakanin mu da Allah muna kokarin kamanta bai wa abokan zaman mu hakkin su. Shi yasa idan ka je yankunan mu na arewa, zaka ga dan wani yanki yana cin karen sa ba babbaka. Yayi kaka-gida shi da iyalan sa, ya mallaki gidaje, filaye, wurin ibada, ma'aikata, hotel-hotel, kai har da gonaki da sauransu. Bamu nuna masu bakin ciki ko sharri. Daga mu har manyan mu, sarakunan mu da 'yan siyasar mu muna buda masu hanya su samu arziki, wadata da rufin asiri. A manyan-manyan kasuwannin mu na arewa sun mallaki manyan shaguna na kasuwanci. Duk wannan yana faruwa ne saboda yarda da muka yi da cewa su 'yan kasa ne, kuma 'yan uwan mu ne, abokan zaman mu ne, don haka suna da 'yanci da hakki su rayu a duk inda suke so, kamar yadda tsarin mulkin kasar mu Najeriya ya ba su 'yanci.

Amma don Allah, ina so muyi wa kan mu adalci, mu tambayi kawunan mu, shin duk wannan gatan da damar da suke samu a yankin mu na arewa mu 'yan arewa a kudu muna samun sa kuwa? Amsa a wurin dukkan wani mai hankali shine, yasan cewa wallahi sam bamu samu. Mutanen nan basu bari mu gina wurin ibada a yankin su, basu bari mu mallaki shaguna a kasuwannin su, basu bari mu mallaki makabartu a kasar su, basu bari mu mallaki gonaki a yankunan su. Kai komai basu bari dan arewa ya mallaka. Wallahi idan kaga dan arewa a kudu, idan ba ma'aikacin gwamnatin tarayya ba ko ma'aikacin banki ko dan kasuwar da zai kama hayar gida, to mai gadi ne shi ko mai yankan farce ko shoe-shiner ko dan garuwa ko almajiri ko mabaraci ko dai wani lebura da sauransu. Mutane ne da ko gida suka baka haya wallahi sai sun gindaya maka tsauraran sharudda na takurawa da musgunawa da mu bamu sa masu ba a yankin arewa. Wannan bayani da nike yi, don Allah idan ba haka bane a fito a karyata ni. Ni nasan kudu ciki-da-wajen ta. Babu abunda za'a nuna mani!

A matsayin mu na 'yan Najeriya, dukkanin mu, 'yan arewar da 'yan kudun, duk mun yarda, kuma munyi alkawari, kuma mun amince cewa, zamu zauna da juna lafiya cikin hadin kai da amana da walwala da mutunta juna da yiwa juna adalci ba tare da fifita dan kudu ko dan arewa ba. Mun amince mu zama 'yan uwan juna, 'yan kasa daya, mu amfana da juna, kowa yayi rayuwar sa da addinin sa babu tsangwama, kowa ya samu hakkokin da ya kamata ya samu a matsayin sa na dan kasa, kowa ya samu 'yanci da mutuntawa, kuma ya mallaki dukiya da kaddarori, ba tare da kallon kabilarsa ko addininsa ko yaren sa ko jinsin sa ko jam'iyyarsa ko yankin da ya fito ba. Kuma ba tare da la'akari da inda aka haife shi ko shi mai arziki ne ko talaka ba. Kuma kowa zai samu kariya daga wulakanci da tozarci ko wane iri ne. Kuma kowa yana da 'yanci da hakkin a saurare shi. Kuma tsarin mulki ya ba kowa damar kadaici da sirri da 'yancin addini. Kuma ya ba kowa damar fadin albarkacin bakin sa, amma ba tare da tada hankali ko shiga hakkin wani ba. Kuma ya ba kowa damar taruwa domin gudanar da wasu al'amurran sa, amma da sharadin ba zai jawo fitina ba. Kuma ya ba kowa damar yawo tare da zama ko rayuwa a duk inda yake so a kasar nan. Amma abun bakin ciki, abun takaici, duk wannan sam a wurin wasu 'yan kudu ba haka bane. Kawai abun a takarda ne kawai, amma idan anzo dabbakawa basu yarda da hakan ba. Irin damar da muke basu sam su basu bamu ita!

Ya ku 'yan Najeriya! Kamar yadda kuka sani, a kokarin da gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi suke yi na ganin cewa an samar da dawwamammen zaman lafiya mai dorewa tsakanin Fulani da makiyaya a kasar nan, sai gwamnatin tarayya ta yanke shawarar samar wa da fulani rugage na zamani da zasu taimaka wurin takaita tarzomar, ko da dai yin hakan bai magance dukkan matsalar ba to watakila a samu dan sauki. Wasu jihohin arewa goma sha biyu har sun amince da wannan kuduri nan take, kuma sun yi alkawarin za su bada duk hadin kan da ya kamata, domin ganin an ci nasarar wannan aiki mai muhimmanci. Wadannan rugage anyi niyyar gina su, a samar masu da wurin kiwo, ruwan sha, makarantu, wutar lantarki, asibitoci da sauran kayayyakin more rayuwa, domin takaita yawon da fulani suke yi tare da samar masu da ilimin addini da na zamani, la Allah ko za'a samu zaman lafiya. Gwamnati na fitar da wannan sanarwa sai kawai muka ga 'yan kudu sunyi caa a kan gwamnatin tarayya, suna cewa su sam kar a kuskura a kawo wannan magana. Su basu yarda ba kuma basu amince ba. Kungiyoyin kudu na yarbawa da na inyamurai irin su Afenifere, Yoruba Elders Council, Ohanaeze, Gwamnonin kudu, lauyoyinsu, 'yan siyasar su, kungiyoyin su na matasa da dukkan wani mai fada aji a kudu, da 'yan bokon su, kai har da ma kungiyar kiristoci ta Najeriya, wato CAN, duk sun fito sunyi Allah waddai da wannan kuduri na gwamnati game da kirkirar wadannan rugage!

Sunyi zage-zage, sunyi rubuce-rubuce, sunyi batanci; kai wallahi ba irin cin mutuncin da basu yi ba ga fulani da 'yan arewa, akan maganar rugar nan. Kai wasu jihohin ma har sun fara korar fulani daga jihohin su, sun kai masu hari da farmaki da tsangwama iri-iri, duk dai kawai akan gwamnati ta ce za tayi masu rugage. Sanadiyyar haka, kawai kwatsam, sai muka ji cewa wai gwamnati ta jingine maganar gina wadannan rugage tun da 'yan gatanta sun koka, sun nuna basu son ayi!

To abin tambaya anan shine, wai shin don Allah su fulani ba 'yan Najeriya bane? Shin basu da 'yanci da hakkin su amfana da gwamnatin Najeriya kamar ko wane dan Najeriya?Wadannan tambayoyin da ire-iren su masu tarin yawa, wallahi suna bukatar amsa cikin gaggawa domin samun dawwamammen zaman lafiya. Domin Allah shine shaida, ba zamu sake yarda da irin wannan raini da wulakanci ba.

Wai shin kun manta da cewa irin cin mutunci da tsangwama da musgunawa da raini da wulakanci da ake yiwa 'yan uwan mu fulani a kasar nan shine yake sa suke cewa bari su dauki makamai domin su kare kawunan su ko? Wato dai har yanzu bamu dauki darasi daga abunda yake faruwa a jihohi irin Zamfara, Plateau da sauransu ba ko? Wato zamu ci gaba da tozarta su da nuna masu banbanci da wariya ko? To shike nan, babu komai, muci gaba dayi. Ni dai nasan wannan ba zai taba haifa muna da mai ido ba wallahi a kasar nan. Allah ya kiyaye, amin.

Yau a Najeriya idan kai fulani ne baka da 'yanci kamar kowa ne dan Najeriya. Yau a Najeriya akwai yankin da idan kai Musulmi ne 'ya 'yan ka ba zasu sa Hijabi su tafi makarantun gwamnati ba sai an tsangwame su, sai an tilasta masu sun cire Hijabin. Duk fa a Najeriya ake yin wannan! Alhali tsarin mulkin kasar nan ya ba kowa 'yancin yin addinin sa. Kuma duk muna kallon wannan munyi shiru, mun ki daukar kwakkwaran matakin kawo karshen wannan wariya da ake nunawa wata kabila ko masu wani addini. Kuma wai duk a haka muna ta kirarin cewa muna son zaman lafiya. Ta yaya zaman lafiya zai samu a haka? Mu daina yaudarar kawunan mu kawai!

Ya ku 'yan Najeriya! Dole indai har da gaske ne muna son samun zaman lafiya mai dorewa, to dole ne gwamnatoci suyi kokarin dakatar da cin mutunci, wulakanci da banbace-banbancen da ake nunawa fulani da 'yan arewa a kudancin kasar nan. Domin dan arewa ba mahaukaci bane. Yana ji, yana kallo, kuma yana ganin abubuwan da suke faruwa. Idan ba haka ba kuwa, duk lokacin da 'yan arewa suka dauki matakin rama abun da ake yi masu, ba fata nike yi ba, kasar nan zata rikice. Allah ya kiyaye, amin.

Koda yake a wani bangaren kuma wata karin maganar malam bahaushe tana cewa, 'IDAN AN BI TA BARAWO ABI TA MABI SAWU' a wani wurin kuma yace, 'IDAN BERA DA SATA DADDAWA MA TANA DA WARI'. Me wannan yake nufi, wato lallai mu sani, mu kan mu Hausa-fulani, ko kuma 'yan arewa muna da namu laifin da kuskuren da suka jawo muna wannan raini, kaskanci da wulakanci a Najeriya. Ga mu 'yan kasa amma ana neman a mayar da mu kamar baki. Don haka mun sani sarai inda muka kauce, mun sani sarai inda muka yi ba daidai ba, mun sani sarai laifukan da muka yiwa Allah mahaliccin mu, mun sani sarai laifukan da muka yiwa junan mu, har sanadiyyar haka Allah ya jarrabe mu da afkawa cikin wannan hali da muke ciki. Allah ya bamu dan arewa a matsayin shugaban kasar Najeriya, amma maimakon yayi amfani da ikon sa da damar sa da karfin sa, ya nemi taimakon Allah, ya hada kan 'yan arewa, ya mai do wa da arewa kwarjini da martabar da Allah ya bata a can baya, amma ina! Kawai yana nema ya zama inuwar giginya. Allah ya sawwake, amin.

Imamu Abu Dawuda ya fitar da Hadisi, a cikin Sunan din sa, lambar Hadisi na 4297, daga Thauban yace, Manzon Allah (SAW) yace:

"Anyi kusa taron al'ummomi da gungun makiyanku suyi maku taron dangi, su afka maku, suyi kaca-kaca da ku, kamar yadda karti majiya karfi, masu jin yinwa suke yin kaca-kaca da kwanon abinci. Sai wani yace, ya Manzon Allah, saboda rashin yawan mu ne a lokacin shi yasa wannan zai faru da mu? Sai Annabi (SAW) yace: a'a, ba haka bane, a lokacin kuna da yawa (sai dai yawan naku na banza ne), domin zaku zama kamar yayi ko kumfa akan ruwa (zaku zama taron tsintsiya ba shara kenan). A lokacin Allah zai cire kwarjini da duk wani girma da kuke da shi daga cikin zukatan makiyanku. Kuma wallahi Allah zai jefa rauni a cikin zukatan ku; sai wani ya tambayi Annabi (SAW) yace, ya Manzon Allah, wane irin rauni kenan? Sai Annabi yace, son duniya da kyama ko gudun mutuwa."

Kun ga wannan Hadisi ya nuna muna cewa da zaran mun kauce hanya, to lallai zamu samu matsala, zamu zama arha a idon makiyan mu. Allah ya sawwake, amin.

Wassalamu Alaikum,

Dan uwanku Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, jihar Kogi, Najeriya ne ya rubuta. Za'a iya samun sa a adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma +2348038289761.
Post a Comment (0)