DUNIYAR GEOGRAPHY

DUNIYAR GEOGRAPHY TAREDA 


AREWA STUDENTS ORIENTATIO N FORUM.
DAGA: Usman Umar Dagona
(Winner Of Imaging National Chemistry Competition 2019/2020).

ASALIN NIJERIYA DA YAN NIJERIYA

Najeriya na zaune ne kusan a tsakiyar
nahiyyar Afirka, Shi yasa yake daukan lokaci Kadan a tafiyar jirgin sama zuwa kowanne
Yanki a nahiyar Afirka. Daga Legas zuwa Dakar na kasar Senegal sa’o’i kadan ne, haka zalika kuma daga Kano zuwa Tripoli ko Aljeriya a arewacin Afirka duk kasa da sa'oi hudu (4) zakaje. Tafiyar sa’a uku ne daga Kano zuwa Alkahira; babban birnin kasar Masar.
Kuma daidai da lokacin zuwa Addis Ababa na
kasar Etofiya.

Kasar Nijeriya tana zaune ne akan layukan longitude
digiri 3 zuwa 15 gabas da Greenwich, Najeriya
na zagaye da kasashe masu Magana da harshen
Faransa, inda kasar ke da iyaka da tekun Atlantic.
Najeriya na da iyaka da kasar Benin ta yamma,
kasar Nijar ta arewa da
kuma kasar Kamaru ta gabas.
Najeriya na zaune har ila yau akan layukan latitude digiri 4 zuwa 14 a arewacin equator.
Haka yasa Najeriya ke karkashin iskoki biyu na “westerlies” da kuma "easterlies” wanda hakan yakeda tasiri wajen kawo sauyin
yanayi a kasar. Wannan yankin latitude da
Najeriya take kai na mata amfani wajen samun ruwan sama, sanyi, zafi, da kurar hunturu. Wurin da kasar take wuri ne mai amfani
saboda ba'a kulle take ba watau "landlocked",
saboda tanada iyaka da teku wanda ke da matukar amfani wuri safara, samun ruwa don aikace-
aikace daban-daban, hakan ma'adinai
musamman man fetur, gwalagwalai da sauran su.

GIRMAN KASA

Mafi nisan tafiya daga gabas zuwa yamma a Najeriya kimanin kilomita dubu daya da dari
hudu ne (1400), sa’anan daga arewa zuwa
kudu kimanin kilomita dubu daya da dari daya
ne (1100). Najeriya na da fadin kasa da ya kai dubu Dari tara da ashirin da uku da dari bakwai
923700 Sikwaya Kilomota, Najeriya tayi girman
kasar Ghana sau hudu, sa’anan tayi girman
kasar Saliyo sau goma sha uku (13).

YADDA AKA SAMU NIJERIYA.
 
Najeriya ada ba kasa daya bace kamar yadda
muka santa a yau, Yankin ada na kunshe da garuruwa da dauloli manya da kanana. Daga
cikin wadannan dauloli, Daular Usmaniyya tafi
kowanne girma da shahara. A inda ta shafe gaba dayan arewacin Najeriya a karni na sha
tara. A yankin kudu kuwa akwai Oyo da Benin. A
kudu maso gabas akwai Inyamurai da Ibibio a kananan kauyuka. An samu Najeriya ne a
shekarar ta 1914 bayan hade kudanci da
arewacin Najeriya wanda turawan mulkin mallaka suka yi mutanen da suka fara amfani da sunan Nijeriya Sune: 
01- Flora Shaw da kuma 
02- Lady Lugard.

 A shekarar 1953 mutanen Najeriya sun kai miliyan
talatin da daya, a shekarar 1963 mutanen Nijeriya sun kai miliyan hamsin da biyar. A Kidayan
shekarar dubu biyu da biyu (2002) yawan yan Najeriya ya kai miliyan dari da arba'in. Tabbas Najeriya ce kasa mafi shahara da yawan mutane a nahiyar Afirka.

WASU DAGA CIKIN KABILUN NIGERIA.
Nijeriya na dauke da kabilu sama da dari uku da sittin, kadan daga cikin many an kabilun kasar sun hada da:

01- Hausawa wanda suke zaune a arewacin Najeriya musamman jihar Kano, Kaduna, Katsina,
Sokoto, da Naija.

02- Fulani: suna zaune tare da Hausawa ne amma sun fi yawa a jihar Filato da Adamawa. Fulanin asali dogaye ne, marasa jiki, suna da siraran hanci da gashi baki mai tsawo, Fatan jikin su nada haske.

03- Kanuri : suna zaune a arewacin Najeriya a
jihar Barno, Bauchi da Adamawa.

04- Yarbawa : Suna zaune a jihar Oyo, Ogun, Ondo da Legas. Dadin dadawa: Akwai Yarbawa a jihar Kwara
da kasar Benin.

05- Inyamurai : suna zaune a jihar Anambra, Imo,
Rivers da Delta

06- Inyamurai suna zaune a jihohin Anambara, Imo, Cross Rivers da sauransu.

07- Badawa: Suna zaune a Jihar Yobe da wasu Yankuna a Kano da Kaduna.

Sauran kabilun Najeriya sun hada da: Nufawa, Jukunawa, Gwari, Katafawa, Ibira,
Igala, Gwandara, Kaje, Tibi, Ijaw, Kabba, Ikulu,
Efik da sauran su.

Allah ya kara hada kan kasarmu NIJERIYA 👐👐👐
Domin tambayoyi da Shawarwari 09036547648
Usman Umar Dagona.

1 Comments

Post a Comment