No title


#HUMAN-ANATOMY

Meyakamata Kasani Dangane Da Human Anatomy?

HUMAN ANATOMY :- Na Nufi Wani Karatune Na Sassan Jikin Dan Adam, Dabbobi Da Kuma Sauran Halittitu, Anatomy Wani Bangarene Na Biology Wanda Ya Ta'allaka Akan Sassan Jikin Dan Adam Dakuma Rabe Rabensu.

 Ko Kuma 
HUMAN ANATOMY:- Na Nufin Karatun Jikin dan Adam Kama Da Ga Jijiyoyi Wanda ake Kira { Vains} Zuwa Sassan Jiki Wanda Ake Kira { Organ} Har IzuwaTsari Wanda Shine ake Kira { System }

Shima Dai Karatun Sassan Jikin Dan Adam Wato ANATOMY Yazama Dole Dalibin Science Ne Kawai Zaikaranchi Wannan Bangaren Saboda Wannan Karatun Shi Ake Kira Da Hantsi Leka Gidan Kowa A Bangaren Karatun Lafiya, Saboda Duk Wani Bangare Nakaratun Lafiya Dole Ne A Wannan Bangaren Kasamu Chewa Akwai Anatomy Kaman Kashi 60% bisa 100% Saboda Wannan Shi Zai Bawa Ma Aikachin Lafiya Damar Sanin Ya Yanayin Mutum yake Kuma Daga Ina Matsalar Sa Take.

Shima Dai Anatomy kamar Sauran Kwasa Kwasai Ana Iya Karantarsane Ta Hanya Biyu, Hanya Ta Farko Ita Che Wanda Aka Kira UTME Wato Shiga Jami'a Kai Tsaye Bayan Gama Karatun Sikandire, Sai Kuma Hanya Tabiyu Wato DE { Direct Entry } Ita Kuma Wannan Hanya Ita Che Bayan Mutum Yagama Sakandire Kuma Yashiga Wata Makaranta Datake Gaba Da Sikandire Misali Kamar NCE, Diploma, Amma Dai Shi Wannan Karatun Mafi Yawanchi Amfi Badashine Ga Daliban Da Suka Yi JAMB Ne. 

ABUBUWAN DA AKE BUKATA KAFIN KARANTAR SHI WANNAN KARATUN
Ga Dalibin Da Zai Karanta Wannan Karatun Ta Hanyar JAMB: Dole Ne Mutum Yazama Yanada Five Credit A Science Course Wanda Suka Hada Da Biology, Chemistry, Physic, English, Mathematics Sannan Kuma Yazama Yachika Ka'idar Maki Da Makarantar daya nema Ta Fidda.

A WANE FACULTY AKE KARANTAR ANATOMY?

Shide ANATOMY Ana Karantar Sane A Faculty Na Basic Medical Science A Wata Makarantar , Yayinda A Wata kuma Ake Karantar Sa A Faculty Na Medical, Pharmaceutical & Health Sciences.

Daga Naku: YUSUF MUHAMMAD

@ASOF2020 Whatsapp 08038485677
Post a Comment (0)