ILIMIN PSYCHOLOGY


Saikoloji(Psychology)
Abubuwan Da Darasin Yakunsa:
1-Ma'anar Saikoloji

2-Ma'anar Idukeshinal Saikoloji(Educational Psychology)

6-Kammalawa

EDUCATIONAL PSYCHOLOGY

•Menene Ilimin Karatun Halayyar Dan Adam❓

•Taya Masana wannan fannin(Psychologist) suka dauki kalmar ta Psycholo❓

•Menene alakar Psychology da Education❓
Ku, Kasance Tare da Arewa Student's Orientation Forum! 

Menene Saikoloji(Psychology)❓ 

Kalmar Saikoloji Ansamota ne Daga Yaren girkawa(Greek) Kuma ta kasu gida biyu: ('psyche‘da 'Logos) 
Kalmar 'Psyche' tana Nufin Ruhi ‘soul’ da ‘Logos’ tana Nufin ‘science’ a yaren girkawa, Bisa Wadannan Ma'anonin An Bayyana Saikoloji a Matsayin kimiyyar Ruhi/Rai.


Wasu Masana Saikoloji (Psychologist) Na baya Bayan Nan Sun yi Bayanin Saikoloji a Matsayin
Wani ilimi Dayake Taka muhimiyar Rawa; "a, yanayin Kai komo Na Ruhi, (Nature) Asalin Ruhi, (Origin) Dakuma kaddarar Ruhin Dan Adam"

 Sai dai Kuma Shi Ruhi ko Rai Wani Abune (Metaphysical)
Ba'a iya ganin sa ko a taba Shi Kuma Baza'a iya Aiwatar da gwajin Masana kimiyya ba Akan sa.(Ruhi)


A Karni Na 18(18th) Masana sun Fahimci Saikoloji a Matsayin 'kimiyyar abunda yashafi tunanin Dan Adam' (Mental) 
Kokuma Tunanin Dayake Cikin kwakwalwa (Mind).

William James (1892) yayi bayanin Saikoloji; a Matsayin "kimiyyar Kai komo Na kwakwalwa wajen Yin Tunani Dakuma karbar Abubuwa" (So, Ko kuma ki) 

B.F. Skinner, Shahararren Masanin Saikoloji ya Fassara Saikoloji da
“kimiyyar Halayya da kwarewar Dan Adam, wajen Sarrafa abubuwa a, Cikin Ransa. 

A Takaice dai ilimin Saikoloji ilimi ne Dayake Bibiyar Halayyar Dan Adam a kimiyyance ko a ilimance, tun daga zuwa ko kafin Zuwan Dan Adam Duniya(Zero Years to Death) Har Zuwa ga Barin sa Duniyar.

Misali; A, Saikoloji Za'a Fahimci Halayyar, jarirai(Infants), Za'a Fahimci Halayyar Matasa, Manyan Mutane Dakuma Tsoffi, da ma Banbance-banbancen Dai Dai kun Mutane (individuals differences) 

✅Menene alaka tsakanin Ilimjn Psychology da Kuma Education❓

Mun dai fahimci Menene shi kanshi Saikoloji (Psychology) a Yanzu Zamu Fara Fahimtar Shima Education Menene?


•Educational Psychology;

Idan Muka Duba Kalmar Educational+ Psychology, Zamu Ga Saikoloji din Damuka sanshi ne, ko Mukayi Bayanin sa a Baya, Kuma aka kara hada shi da Education; Hakan Yana Nuna Sunada wata Alaka ta ilimi.

Bari Mufara Sanin Ma'anar Education Sai mu hada Ma'anar sa Da ta Saikoloji, yanda, Mu Zamu Fahimci Alakarsu Da Juna.

Kalmar Education; Asalin Kalmar a cirota ne daga 'Latin' 'educare' ko 'educatio'
Wanda a turance Kuma ana kiranta da educate a karni na 16 (16th)

Ma'anar Kalmar Education Da Hausa Muna Cewa "ilimi"

Kalmar Education Kokuma ilimi Da Hausa yana Nufin "Hanya ce ta Saukaka Koyo, ko Samun kwarewa da Dabaru ko Halayya, Dakuma Imani da Wani Abu ko yadda, da kudurcewa a Zuciya. 

A fannin koyarwa Kuma akwai wasu salailai ko Dabaru Da'ake bi Wajen koyar da ilimi shi kanshi: daga cikin su akwai dabarar Koyarwar bayar da Labari, Tattaunawa, Dakuma Bincike. D.s.

A Takaice Duba Abubuwan Biyu(Psychology Da Education)
Suna tare da Juna Basa Rabuwa, Domin ilimi yana tare Da tunani Kokuma abunda Rai/Ruhi Yaso Kokuma Yakeso, Hakanan Shima ilimi ba'a ganin sa ko a taba shi.

Shin ilimin Psychology, Shine Yake Qunshe Da ilimi (Education) Kokuma ilimi(Education) Shine Yake Kunshe Da Psychology?

A Dunkule idan Mukace ilimi Ko Education, Mun Game Komai; Dukkannin Wani ilimi Yana Ciki.

Amman Psychology Kuwa, a, Dunkule Wani ilimi Ne Na Halayyar Dan Adam, a kowanne Matakin Rayuwar sa(Jinjiri, Matashi, babban Mutum, Dattijo, Mace da Namiji, Dss.)

Duk Dahaka ilimin Psychology Yanada Alaka Da kowanne ilimi, Domin kowanne ilimi yanada Alaka Da Tunanin Dan Adam Dakuma abunda Yake Cikin Ran Dan Adam,
Idan Kuwa Hakane tako Wacce Fuska ilimin, kimiyyar Sanin Halayyar Dan Adam (psychology) ba'a Raba Shi Da ilimi Gamamme(Education)

*Kammalaw;*

A Taqaice Bazaka Raba Saikoloji Da Idukashen Ba;
Education Yana chanja Halayyar Dan Adam ne, ta kyawawan Hanyoyi, Dakuma Shiryar da, Dan Adam ko Luratar dashi Abubuwan Rayuwa Masu Muhimmanci, a Zamantakewa.
Saikoloji(Psychology) Kuma Karatun ilimin, kimiyyar Halayyar Dan Adam ne.

Mu Hadu a Darasi Nabiyu, Domin Cigaba Da bayani akan Educational Psychology.

@ASOF2020 Whatsapp 08038485677
Post a Comment (0)