MENENE CUT OFF MARKS?

*AREWA STUDENTS & ORIENTATION FORUM*

17th June, 2020.

 *Menene Cut Off Marks?*
Cut Off Marks wani Tsari ne Da Jamb Take Amfani Dashi Wajen Kayyade Adadin Makin Da Take so Dalibi Ya Samu Domin Kafin Abashi Admission A Makarantun Gaba Da Secondary.

Jamb Ta Bayyana 160 a Matsayin Cut Off Marks Domin Samun Damar Shiga Jamio'in Gwamnati, 

Saidai Kuma Naga Mafi Yawancin Dalibai Suna Tambaya Cewa Shin Harda BUK? 
Wasu kuma Suna Cewa Harda ABU dadai Sauran Makarantu,

Dalilin Wannan Rubutun Nawa Domin In Sanar Daku Cewa Wannan Cut Off Marks Na Hukumar Jamb Ne Ba Makarantu ba, 

Maana Jamb Ba Zata Yarda Abaiwa Kowanne Dalibi Damar Shiga Jamia ba Har Sai Makinsa Yakai 160.

Amma Fa Yanada Kyau Ku Sani Cewa Ko wacce Jamia Tanada Damar Da Zata Kara Adadin Makin Da Take so, 

Idan Jamia Taga Dama Ta Barshi a 160 Kokuma Ta Maidashi 170 ko 180 Kokuma 200 amma Babu Jamiar Gwamnati Da Zata Ba Dalibi Admission Muddin Baici 160 ba.

Sannan Ina Kara Jan Hankalin Dalibai Akan Mu Kara Dagewa Da Karatu Da Kuma Addua Domin Tunkarar Post Utme. 
Sannan Kada Mu Sakankance Kokuma ka Saka Rai Akan Cewa Makarantar Da kake Nema Zata Bar 160 A Matsayin Cut off Marks Dinta, 

Mafita Shine Ka Chigaba Da Bibiyar Asof Domin Jin Bayanai Da Kuma Cut Off Marks Na Makarantarku Idan An Fitar. 

Abdulkadir Anas Malumfashi 
©Asof 2020.


Post a Comment (0)