NA'URA MAI ƘWAƘWALWA 01

Na'ura Mai kwa-Kwalwa;
       Kashi Na Daya. 

Yadda Ake Hada Android Da Computer Ta Zama Modem;

Daga Salisu Abdulrazak Saheel 


Mutane da yawa suna tambayata da kirana a waya cewa tayaya zasu hada wayansu Techno Android da Computer a matsayin modem suyi browsing da ita
Allah yabani sa'a nasamu wasu hanyoyi guda biyu wanda zaka iya hada ta da computer sune kamar haka: WiFi da USB Cable..😀

Yadda zaka hada techno android da computer ta WiFi hotspot.
Idan kana buqatar hadata da computer ta WiFi, sai kabi wadannan matakan:
1. Kaje Settings> Wireless & Networks> Tethering & Portable Hotspot.
2. Sai ka duba Portable WiFi Hotspot, sai kabude shi.
3. Bayan wasu yan dakiku WiFi Network din zai bayyana akan wayar daga sama.
4. Sannan se kaje Portable WiFi Hotspot Settings> sannan kayi configure din WiFi hotspot.
Wato wurin (blank space) dukansu ka cikesu, Username da Password.

<Network SSID = Kasa abinda kaga dama, kamar sunanka ko inkiyarka haka.

<Security == WPA2 PSK.
<Password naka ya kasance guda takwas zuwa sama.

Idan kabude shi yana dauke da sunan kamfani, sai kabashi naka kasa mashi password yadda kana hadawa zaifara, amma fa idan kabude kabarshi kara zube, kukuma baka bude WiFi din ba to bazaiyi Connect ba, zaita cewa a sanya Password.
Kabarshi a bude karka rufe, sannan kayi search nasa idan ya kamo sai ka danna connect shikenan sai kafara Browsing..😀😍

✍️Salisu Abdulrazak Saheel 
 08137350232
@ASOF2020 Whatsapp 08038485677


Post a Comment (0)