TSANGAYAR KIMIYYA DA FASAHA

Special courses

Tsangayar kimiyya

Facultyn yan nigeria inji wani professor. Kashi biyu cikin ukun daliban qasarnan suna karatu ne a wannan tsangayar.tsangaya ce mai farin jini hakan baya rasa nasaba da karkasuwan ta da kuma yadda dole rayuwa a cikin duniyar nan yake da matsananciyar buqatar kwarewa a fannonin ta.
Tsangayar kimiyya a zamance ana kasa ta zuwa kashi kamar haka:

1-pure science
2-Physical science
3-life science
4-classical science
5-medical science

Duk da wasu na qarawa da social science sai dai haqiqanin gskya social science ba zallar kimiyya bane cikin sa. Bari mu kalle su d'aya bayan d'aya

1-PURE SCIENCE.
Dukkan wani fanni dake qarqashin tsangayar kimiyya to ancire shine daga nan shiya sa ake kiran shi pure science b'angarorin shi sun had'a

Biological science
Chemistry/pure and applied chemistry
Physics/pure and applied physics
Mathematical science

Kai tsaye kana iya cewa wayannan sune tsangayar kimiyya don in babu su to babu kowa ne fanni a science

2-Physical science
Wasu sashe ne aka cire qarashin pure science da suka shafi zallan abin da ya shafi physical aspect daga ciki akwai

Physics and electricity
Industrial chemistry
Geology
Computer science ETC

Wasu jami'oin na qara
Geography da
Astronomy a qarqashin yayin da wasu kuma suke kaisu Social science domin su ba zallar science bane.
Shima computer science wasu na aje shi a social science.

3-Life science
Ilimin kimiyyar daya shafi halittu masu rayuwa sun shafi

Botany
Zoology
Marine biology etc

4-Classical sciences
Sabin fannonin kimiyya da duniya ke tafiya dasu da yawa daga cikin matsalolin kimiyya musamman abin da yashafi harkar (lafiya da cututtuka,noma,hade haden magani etc) ana saka ran way'annan fannoni zasu kawo hanyoyin magance su.

Microbiology
Biotechnology

5-Medical sciences

Dukkan wani sashe daya shafi harkar lafiya to yana qarqashin nan

Sai dai qarqashin bangaren kimiyyar lafiya akwai wasu sashe da su ake kiran su para medical courses suma suna tsangayar harkar likitanci sun had'a da

Physiology
Biochemistry
Anatomy

Wadanda su kamar uwaye ne a dukkan wani medical course.
Daga cikin kwasa kwasan kimiyyar lafiya sun had'a da=

MBBS
Nursing
Pharmacy
Dental
Medical lab.sci.
Physiotherapy
Radiography
Veterinary Med.
Optometry
E.T.C


NB dan haka a matsayin ka na sabon dalibi ko mai niyan karantar kimiyya sai ka nutsu ka duba a cikin fannonin nan wannene kake sha'awar karanta sannan karka manta dukkan way'annan kashe kashe munyi ne dan ka fahimci idan ina neman course kaza sai ban samu ba dan marking dina bai kai ba ko kuma jami'ar da na nema basa yin wannan Course din sai ka duba wanda yake da alaqa dashi ka zaba
 misali =kana neman BIOTECHNOLOGY baka samu ba sai ka nemi MICROBIOLOGY

Ko kuma kana neman ZOOLOGY baka samu ba sai ka gwada neman BOTANY

Ko kana neman MBBS baka samu ba sai ka nemi wani course daza ka iya samu a cikin medical courses din

Sau da dama rashin chanjawa zuwa wanda zaka iya samu ko zaban wanda kake da requirement na saka jami'a ta dauke ka gaba daya ta chanja maka faculty .


M.A IBRAHIM
ABU MUBEENAH
08141919945

Post a Comment (0)