TWEAKING 01


"Tweaking" (1)

Daga: Salisu Abdulrazak Saheel

Bayani akan "Tweeking": idan akace "Tweeking" shine kamar canjawa, wato canja wani abu zuwa wani abu daban, Misali: Canja "Imei" na wayar "Android", idan akace " Imei " to sune wasu lambobi guda 15 wanda ake kiransu da serial number wanda kowace waya tanada nata lambobin wanda ake ganinsu ta hanyar danna *#06# dan haka kowa ya danna a wayarsa domin ya ganewa idonsa..😀
To da zarar kundanna zakuga lambobi guda 15 to wannan sune "Imei" kuma su ake kira da Serial Number, kuma kowace waya tanada nata lambobin sannan sunada matiqar amfani a waya domin idan babusu a waya to waya kwata-kwata network dinta zai dauke babu damar yin kira ko browsing da sauransu.
To wani lokaci wannan numbobin suna yawan gogewa a wayar android sai kaga wayarka kwata-kwata takiyin kira ko browsing kuma gashi da service sai ka kasa gane matsalan har sai ka kai wajen masu gyara to da ace zaka danna *#06# zakaga wannan lambobin ne suka goge.
To Amma Alhamdulillah insha Allah indai kuna biye da "Arewa Students Orientation Forum" zaku koyi yadda zaku canja wasu lambobin.

Bayan haka kuma wasu lokutta zakuji anata maganar "MB" ko "GB" masu yawa wanda zakuji har sayar da sim din akeyi a kasuwa kokuma kuji ance akwai wata sabuwar waya tafito wanda idan kasiyeta ka aika (sending) sunan wayar zuwa wasu lambobi zaka samu wata garabasa ta data mai yawa da sauran ire iren wadannan to duk anayinsu ne ta hanyar "Tweaking" Misali: Misali abinda yasa ake samun Mb ta hanyar Tweak shine akwai sabbin wayoyi masu tsada wanda zakuga an rubuta a jikin kwalin wayar kan cewa idan kasiya wannan wayar kasanya Sim dinka zaka samu wani Mb mai yawa, to sai kuma wayoyin sunyi tsada babu dama kasamu wannan Mb data din kanaji kana gani sai dai ka haqura to ana hakane sai kimiyya ta gano ai abinda yasa ake samun wannan Mb mai yawa irin a wannan sabbin wayoyin saboda "Imei Number" din ne, inda ace zaka iya sawa wayarka irin wannan "Imei" to kaima zaka iya samun wannan Mb din..😀😍
To a haka ne sai "Programmers su Abokina Biggiey" suka kirkiri wani Application mai suna "Mobile Uncle Tools" ko "MTK-Engineering" da sauransu.
Wanda da wannan apps din zaka iya canjawa wayarka "Imei Number" dinta kaima kasamu Data Mb.
Sai kuma irin wayoyin da zakuji ance tana zuwa da kyautar Data. Misali: Kamar Techno P5 tana zuwa da kyautar 2GB idan ka dora layin Airtel ka aika (Sending) Data zuwa 141, haka Infinix tana zuwa da kyautar 1GB a layin MTN idan ka aika Ifinix zuwa 131, wayoyi da dama suna zuwa da irin wannan kyautar to idan kasamu "Imei number" din wannan wayar da take zuwa da wadannan kyautar to idan kasanya wa wayarka sannan ka aika wannan saqon da ake turawa kaima zaka samu wannan Mb din.
Misali: kanada waya Gionee P4 ko P5 to zaka canja mata "Imei number" dinta zuwa na Techno C8 ko na Airtel ko na Blackberry haka zalika suma na Techno din zaka iya canja "Imei number" nasu zuwa na kowane waya.

Amma fa canja "Imei number" din anaso ace wayarka takai Version 4 zuwa sama idan kuma baikai Version 4 ba to wani lokaci "Imei Number" din baya canjuwa.

Wannan shine takaitaccen bayani akan "Tweeking".

Mu hadu kashi na 2.

Whatssp only: 08137350232
Post a Comment (0)