MATA A FINA-FINAN INDIYA 04


๐Ÿ’Ž๐Ÿ๐Ÿ’Ž๐Ÿ๐Ÿ’Ž๐Ÿ๐Ÿ’Ž๐Ÿ๐Ÿ’Ž๐Ÿ
MUJALLAR FINA-FINAN INDIYA 
๐Ÿ’Ž๐Ÿ๐Ÿ’Ž๐Ÿ๐Ÿ’Ž๐Ÿ๐Ÿ’Ž๐Ÿ๐Ÿ’Ž๐Ÿ

KE GABATAR MUKU DA SHIRIN


༄๐ŸŒผ༄๐ŸŒผ❄️✿๐ŸŒ€...♡...๐ŸŒผ༄๐ŸŒผ༄
MATA A FINA-FINAN INDIYA
༄๐ŸŒผ༄๐ŸŒผ❄️✿๐ŸŒ€...♡...๐ŸŒผ༄๐ŸŒผ༄

                 Kashi na (04)

                   Tare da

            •----------•✬(✪)✬•----------•
                   Haiman Raees 
           •----------•✬(✪)✬•----------•


            •┈┈••♡๐Ÿƒ♡••┈┈•
              17th August 2021 
            •┈┈••♡๐Ÿƒ♡••┈┈•


SHIN KO BOLLYWOOD TA CANJA YADDA AKE GANIN DARAJAR MATA A INDIYA DA MA DUNIYA BAKI ฦŠAYA? 


A duk lokacin da mutum zai tuna da wata jaruma daga Bollywood ko wata masana'antar fina-finai daga Indiya, sakamakon da zai samu ya dogara ne akan abubuwa da dama. Ta yiwu abin da zuciyarsa za ta fara hasko mishi shi ne jarumar da ya fi so, ko ฦ™warewar wata a wajen iya aiki, iya rawa ko kuma irin zamanin da yake ciki ko jarumar ke ciki. 

Misali; yadda mutanen zamanin 60s za su hasaso jaruma da ban da yadda mutanen 2021 za su hasaso. Me ya sa haka? Saboda jarumar fim a Indiya a koyaushe kayanta, kwalliyarta, manganarta tare da duk wani motsi nata suna isar da saฦ™o ne zuwa ga mai kallo, kuma yadda ya saba ganin ta a haka zai ษ—auke ta. 

Mutane da dama na ganin ฦ™ima da darajar matan fina-finan Indiya na da saboda yadda suke fitowa a ษ—abi'u masu kyau da kuma yadda suke girmama al'ada. Amma jaruman yanzu kuwa akasarin su ba sa samun komai face tofin Allah tsine, yayin da masu samun yabon kirkin ba su da yawa, masu samun yabon ba na kirkin ba kuma kun san inda maganar ta nufa. 

Hanya mafi sauฦ™i da za mu iya fahimtar wannan maganar ita ce: mafi yawancin jarumai mata na wannan zamanin akan kushe su da cewa ba su iya kwaikwayon abubuwa yadda ya kamata ba, wasu ma kawai ana sa su a fim ne saboda su gamsar da 'yan kallo da kyawunsu da kuma ฦ˜azaman ษ—abi'unsu waษ—anda a yanzu haka sun fara illa wa hatta 'yan matanmu na nan masu yawan kallon su. 

Duba da irin waษ—annan matsaloli, yanzu za mu yi duba ne zuwa ga yadda matan fina-finan Indiya suka canja daga jiya zuwa yau. 
 

KAYA DA KALAMAN JIKI 

Wato shi fim kacokan ya dogara ne akan abin da mai kallo ke gani a gabansa. Bayan labarin fim ษ—in, dole sai an samu abubuwa masu yawa da ke taimaka wajen isar da saฦ™on da ake buฦ™ata. 
Kusan ko da yaushe kaloli na yin tasiri a wajen abubuwan da mutane ke gani musamman a fim. Iya kwaikwayo, salo da kaloli suna taka rawa sosai a fina-finan Indiya, abin har ya kai ga a ฦ™asar Indiya, Bollywood tana da rinjaye sosai wajen irin kayan da mutanen ฦ™asar ke sakawa. 

To abin da mafi yawancin mutane ba su fahimta ba shi ne, irin kayan da jaruma ke sakawa a fim da irin yadda take kowane irin motsi shi ke bayyana dara ko rashin darajarta ga masu kallo. 

Bari mu dubi wasu misalai:


A shekarun 40s, jaruma Suraiya na cikin waษ—anda ake ji da su a Bollywood. Suraiya jaruma ce kuma mawaฦ™iya wadda ta fito a fina-finai irin su Jeet (1949) da Badi Behen (1949). A cikin waษ—annan fina-finan, jarumar ta fito ne cikin Sari kuma sau tari ba ta barin gashin ta a watse. Wannan ya dace da shiga irin ta matan Indiya a wancan lokacin. 

A shekarar 1994, a yayin wani taron masu watsa labarai, jaruma Suraiya da kanta ta nuna rashin jin daษ—in ta akan irin banbancin da ke tsakanin hukumar tace fina-finan da da na yanzu. 

Ga abin da jarumar ta ce; 
“Akwai wasu irin fina-finai da ake yi yanzu waษ—anda ina mamakin yadda hukumar tace fina-finai ke bari suna fita!”

Ba ta tsaya a nan ba kawai, jaruma Suraiya ta soki irin yadda ake nuna baษ—ala a cikin sabbin fina-finan yanzu. Duk waษ—annan abubuwa suna bayyana mana irin yanayi da kuma tsarin da mata ke fitowa ne a fina-finan 40s.

Zan ci gaba in sha Allah. 

©️✍๐Ÿป
  Haiman Raees 
# haimanraees 
Haimanraees@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring 
Post a Comment (0)