MATA A FINA-FINAN INDIYA 06πŸ’ŽπŸπŸ’ŽπŸπŸ’ŽπŸπŸ’ŽπŸπŸ’ŽπŸ
MUJALLAR FINA-FINAN INDIYA 
πŸ’ŽπŸπŸ’ŽπŸπŸ’ŽπŸπŸ’ŽπŸπŸ’ŽπŸ

KE GABATAR MUKU DA SHIRIN


༄🌼༄🌼❄️✿πŸŒ€...♡...🌼༄🌼༄
MATA A FINA-FINAN INDIYA
༄🌼༄🌼❄️✿πŸŒ€...♡...🌼༄🌼༄

                 Kashi na (06)

                     Tare da

            •----------•✬(✪)✬•----------•
                   Haiman Raees 
           •----------•✬(✪)✬•----------•


            •┈┈••♡πŸƒ♡••┈┈•
              31st August 2021 
            •┈┈••♡πŸƒ♡••┈┈•


SHIN KO BOLLYWOOD TA CANJA YADDA AKE GANIN DARAJAR MATA A INDIYA DA MA DUNIYA BAKI ƊAYA? 


CI GABA


Tun daga shekarun 70s sutura da kalaman jarumai mata suka fara canjawa a cikin fina-finan Indiya. Canji kuma na a zo a gani. A cikin fina-finan 80s zuwa 90s kuwa, ana iya ganin jarumai irin su Rekha, Sridevi, da kuma Madhuri Dixit sanye da kayan turawa irin su jeans, skirts, da kuma kaya masu kaloli sosai da nuna sassan jiki. 

Misali; a cikin shirin Kuch Kuch Hota Hai (1998) Rani Mukherji ta sha watayawa jikin shiga irin ta turawa a matsayin Tina Malhotra. Matsayin da ta hau dama yana nuni ne da cewa shahararriyar Kyakkyawa ce a makarantarsu, kuma irin shigar da take yi ya tabbatar da hakan. 

Zuwan shafukan sada zumunta da kuma ci gaba da aka samu a harkar kimiyya da fasaha shi ma ya jawo Ζ™ara lalacewar jarumai mata, domin irin abin da wasunsu ke sakawa a shafukansu, su suke sawa amma kai ne kake jin kunya. To amma in da matsalar taje shi ne, da yawan 'yan kallo suna son hakan, shi ya sa yanzu a fina-finai da dama za ka ga ana sumbatar juna tare da yin aiyuka na rashin Ι—a'a. 


A shekarun baya, an taΙ“a yin hira da jaruma Kareena Kapoor Khan, in da ba ko kunya ta bayyana cewa a shirye take ta fito a yanayi irin wannan matuΖ™ar labarin ya buΖ™aci ta yi hakan. 

Jarumai irin su Mandakini, Zeenat Aman, Rekha, Kajol, da ita kanta Kareena duk sun taΙ“a tuΙ“e kayansu a yayin Ι—aukar fina-finai a lokuta mabanbanta. 

Sai dai kuma fa, wasu da dama irin su Suraiya ba sa jin daΙ—in irin yadda ake fidda tsaraicin mata a cikin fina-finan Indiya. Don haka muna iya cewa abin dai ya ta'allaΖ™a ne da irin yadda 'yan kallo ke ganin abin. 


Wani babban sashe na samun nasarar fim shi ne irin matsayin da jaruman ciki suka fito a cikinsa. A wasu lokutan ma suke babance tsakanin nasara da faΙ—uwar shirin. Tun daga 40s aka fara samun manyan fina-finan Bollywood da ke magana akan nata ko kuma waΙ—anda matan ne ma ke jan ragamar su. Daga cikin irin waΙ—annan fina-finan akwai Vidya (1948) da Andaz (1949). Duk waΙ—annan Fina-finan mata ne a gaba-gaba cikinsu. Ko da yake ba kasafai aka cika yin irin su ba kamar na waΙ—anda maza ke jagoranta, a 1957, jaruma Nargis ta jagoranci wani fitaccen fim wanda ya kafa tarihi mai suna Mother India. 

Jaruma Madhubala ita ma ta haska sosai a cikin shirin Mr and Mrs 55 (1955) a matsayin Anita Verma. 

Zan ci gaba in sha Allah. 

©️✍🏻
  Haiman Raees 
# haimanraees 
Haimanraees@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring
Post a Comment (0)