YADDA ZAKA GANE MACE NA SONKAYADDA ZAKA GANE MACE NA SONKA
:
https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E
:
*TAMBAYA*❓
:
Aslm mlm allah yakarama mlm lfy da basira tamba yata itace mlm wanne alamomi zangane mace tan son tsakaninta da allah?
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Duk wanda yake tantamar soyayyar da ake masa, ta haka ne zai gane, duk da cewa dai soyayya ta gaskiya ba a gane ta a lokaci kankani kasancewar tana shiga ne sannu a hankali.

Ita soyayyar gaskiya tana toho ne da yaɗuwa a cikin zukatan mutane a yayin da ake zama ana fahimtar juna. Wani abin bakin cikin yanzu shine soyayyar gaskiya ba ta cika dorewa ba. Wani lokacin sai an yi nisa sai a ɓata ko ta lalace, Wannan bayani ya gudana ne ga duk wani masoyi da yake shakkun masoyiyarsa ko tana son sa ko ba ta son sa.

Idan kana son ka gane da gaske ana sonka, wadannan sune alamomin.

Wasu sukan shiga rudani akan rashin ko da gaske matan da suke so da aure shin dagaske suma suna sonsu.

Gano soyayya mace na gaskiya ba wahala ne da shi ba. Saboda ita mace bata iya doguwar yaudara a soyayya idan kana da hankali baka ganota ba.

Ga wasu alamomin da zaka iya gano macen idan tana sonka da gaske.

Da farko idan kana so ka fahimci mace na sonka sai idan kana cikin jarabawa na rashin lafiya.

Duk macen da take kaunar namiji da gaske takan shiga matsainancin damuwa a lokacin da aka sanar da ita bakada lafiya.

Ta hanyar sanar da ita bakada lafiya koda kuwa karya aka mata muddin ta kasa nuna damuwarta a hakan to ka tabbatar ba sonka take ba.

 A lokacin da ka shiga matsala na kuɗi a wannan lokacin ne zaka gane idan mace na sonka da gaske.

Mace koda batada halin tallafamaka da kuɗi a lokacin da kake tsananin buƙatarsu, zata nuna maka damuwarta tare da kawo wasu shawarwarin yadda za a iya samun mafita.
 
Wata hanyar kuma shine ka ƙirƙiro faɗar da babu dalili da ita.

Ka ɓata mata rai domin ganin yadda zata maida martani da kuma irin furucin da zai fito daga bakinta.

Ka nuna mata zaka haƙura da ita tunda kana ganin wasu na zuwa wajenta.

Duk macen dake sonka da gaske kana zuwa mata da wannan zancen zata shiga tashin hankali. Kana ji tace Allah Ya haɗa kowa da rabonsa to daman ta ƙosa da kai.
 
Ƙin yi mata abun da ta nema a lokacin data ke na iya sa namji ya gano na son shi da gaske ko hidimar da kake mata ne take so.

Mace idan tana sonka kuma ta nemi ka yi mata wani abun baka yi ba zata ɓata ranta ko nuna maka ɓacin ranta ba. Sai ma addu'a da zata maka na fatan wadata.

Amma idan babu soyayya na gaskiya a tsakaninku zata nuna ɓacin ranta ta kuma bika da mitar tsiya.

Ta hanyar abokanka da kuma ƙawayen wacce kake so zaka iya fahimtar idan mace na sonka da gaske.

Ta yadda take mutunta abokanka da na kusa da kai, da irin kalamai na yabo da suke yi game da ita zaka fahimci tana sonka.

Su kuma kawayenta zaka iya jin gaskiyar yadda masoyiyar taka ta ɗaukeka daga bakunansu.

 Yadda su ƙawayen nata suka ɗaukeka nan ma zai bayyana maka matsayinka a gunta.

Waɗannan sune wasu daga cikin dabaru da hanyoyin da zaka iya fahimtar idan mace da gaske take sonka.

• Idan tana yawaita fada maka tana sonka kuma ka tabbatar da hakan, tana jin son sosai a zuciyarta, sannan kuma tana jin son ba tare da tana rokonka wani abu ba, sakamakon
hakan ba ta jin bacin rai kuma ba ta bata maka rai.

• Idan tana magana ka rinka kula da idonta, wajen magana za ka iya gane mace in tana sonka idonta yana nuna alamun tausayi da soyayya ga wanda take so da kauna. Duk ta kwayar idonta za ka iya gane mace in mayaudariya ce ko dabara da wayo take maka. Shi ya sa aka ce abu mafi sauki da muhimmanci ka rinka kula da kwayar idonta wajen fahimtar son da take maka in dai tana matukar sonka za ka gani.

• Za ta rinka yin duk wani abu da ta san zai faranta maka rai. Mata suna nuna kulawa sosai ga wanda suka damu da shi, shine sai a yi maka abu ba tare da ka tambaya ba ko Ka nuna kana so ba, in dai an san ka damu da abin saboda son da ake maka. Za a yi don a faranta maka rai. Wannan duk alama ce ta ana sonka.

• In tana sonka babu ruwanta da wasu samarin, na san ba kowane zai yarda da haka ba. Amma soyayya ta gaskiya ido rufewa yake, in dai mace tana sonka idonta rufewa yake ba ta
ganin kowa a gabanta sai kai. Kar ma ka damu kanka a kan da namiji saboda idan idon sun rufe babu kowa da ya mamaye zuciyar sai kai. To ka ga kenan tunaninta, jinta da ganinta
duk naka ne.

• In tana matukar sonka za ta yi
kokarin ta ga ta magance duk wata damuwa da ta shafe ka, da duk matsalar da ta dame ka za ta rinka jin duk wata damuwa taka kamar tata.
Saboda haka idan dai har mace tana daukar damuwar wanda take tare da shi kamar yadda za ta dauki tata damuwar to a gaskiya wannan ita ma alama ce ta tana sonka kuma tana
tare da kai.

• In tana sonka za ta rinka tinkaho da alfahari da samunka, da kuma nunaka a gurin ’yan’uwa da abokan arziki,
kawaye da sauran su. Saboda in mace tana sonka gani take ka zama wani bangare na jikinta. Wannan ne zai sa ta rinka tinkaho da kai ba tare da jin
nauyi ko kunya ba.

• In tana sonka za ta rinka fifitaka akan ko wane abu, idan ma tana tare da wasu da suke tare da ita ka shigo kuma ta ji ta fi sonka to za ta fi fifitaka
a kansu kuma za ka gane, saboda za ta fi son ta ga tana tare da kai ba tare da gajiyawa ba, da son yin waya da
kai ba gajiyawa, sannan za ta rinka goya maka baya da nuna maka soyayya a kan za ta iya rabuwa da kowa saboda kai.

• Damuwa da kulawa da kai a duk lokacin da take tare da kai, mata suna son su rinka kula da wanda suke masa son gaskiya a cikin dadi ko rashin dadi, ko da lafiya ko babu lafiya kuma ba tare da nuna damuwa ko bacin rai ba. 

Wadannan alamomi
sun isa su nuna maka mace tana sonka.

Wallahu A'alam

ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)