RAMUWAR AZUMIN FARILLA A SHARI'A



RAMUWAR AZUMIN FARILLA A SHARI'A

*TAMBAYA*❓

Salam shin ya alatta mutum ya ringa skiping yayin yin rankon azummi? Misali kana yinshi litinin da alhamis kuma ranko ne.


*AMSA*👇

Wa'alaikumussalaam Wa Rahmatullahi Wa Barakaatuh.

Babu laifi akan hakan shine abin da mafi yawancin mallamai suka tafi a kai wanda yake da ramuwa na azumin Ramadan yayin da zai rama su, ba dole sai ya yi su a jere ba, saboda fadin Allah(SWT):

(فمن كان منكم مريضا أو على سفر فعدة من أيام أخر)

Wanda ya kasance daga cikin ku bashi da lafiya ko a hali na tafiya to sai ya biya adadin a cikin wasu kwanuka na dabam.

-Haka an ruwaito daga Aisha Allah Ya kara mata yadda tace da an saukar da àyar

(فعدة من أيام أخر متتابعات)

Sai aka goge kalmar (متتابعات)

-Haka an ruwaito hadisi daga Abdullahi binu Umar (RTA) Ya ce manzon Allah(SAW) yace:

(أن النبي صلى الله عليه وسلم قال في قضاء رمضان إن شاء فرق وإن تابع)سنن الدارقطني.

Manzon Allah(SAW) ya ce: Wanda yake da ramuwa na azumi idan ya so ya yi su a jere idan ya so ya yi su a rarrabe.

والله تعالى أعلم.

DR, NASIR YAHYA ABUBAKAR BIRNIN GWARI

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)