AMBATON ALLAH LOKACIN SHIGA BANDAKI (TOILET) DA LOKACIN FITA.

AMBATON ALLAH LOKACIN SHIGA BANDAKI (TOILET) DA LOKACIN FITA.


Bandaki (Toilet) yana cikin wajen da Sunnah ta koyar da Ladubban shigar sa da fita da kuma Ladubban biyan buƙata acikin sa, daga cikin akwai AMBATON Allah wato zikiri lokacin shiga da lokacin fita, domin bandaki wajene na matattarar shaiɗanu da aljannu, kuma babu abin da yake maganin su sai AMBATON Allah. 

Sakaci na rashin AMBATON Allah lokacin shiga bandaki yana janyo Shaiɗanu da aljannu su cutar da dan Adam, musamman mata da yara ƙanana saboda sun fi kowa sakaci.

Daga Sahabi Zaidu bn Arqam رضي الله عنه yana cewa, Daga MANZON ALLAH صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ yace:-

*_(Lallai kunga waɗannan Bandakuna "Toilet" Wajene na haɗuwa da matattarar Shaiɗanu, Idan ɗayanku zai shiga to yace:_*
*_{اللَّهمَّ إنِّي أعوذُ بِكَ منَ الخبثِ والخبائثِ}.*_
_*(ALLAHUMMA INNI A'UZU BIKA MINAL KHUBUTHI WALKHABAA'ITH) *_

@صححه الألباني صحيح الجامع "٢٤٤"

A wata riwayar yazo da karin BISMILLAHI 

_*(بِسْمِ اللهِ) اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعُـوذُ بِـكَ مِـنَ الْخُـبْث وَالْخَبائِثِ.*_

*_(Bismil-lah) allahumma innee a'u'zu bika minal-khubthi wal-khaba-ith_*

Kuma MANZON ALLAH صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ya kasance idan ya fito daga Bandaki (Toilet) yana cewa:-

_*{ غُفرانَك}* _

_*(GHUFRANAK)*_

@صحيح الترمذي(٧)

◼ابن عثيمين رحمه الله:
Yana cewa:

*"Fa'idar yin zikiri da neman tsarin Allah akan shaiɗanu lokacin shiga bandaki, domin bandaki wajene na zaman aljannu da shaiɗanu kuma wjene marar kyau kuma shaiɗanu suna saurin cutar da mutum acikin sa saboda rashin tsarkin wajen da rashin ambaton Allah acikin sa, domin wajene marar tsafta ba'a ambaton Allah acikin sa, amma idan ka ambaci Allah lokacin shiga kuma ka nemi kariyar Allah daga sharrin shaiɗanu, to sai Allah ya kare ka daga shariinsu gaba daya har ka gama biyan bukatun ka..... ".*

@الشرح الممتع (١/٨٣)":

*ALLAH NE MAFI SANI*

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)