BAYA HALATTA GA MUSULMI YAYI BUKUKUWAR HAPPY NEW YEAR

BAYA HALATTA GA MUSULMI YAYI BUKUKUWAR HAPPY NEW YEAR.


Baya halatta ga musulmi Wanda yayi Imani da ALLAH shine Ubangiji Kuma ya yadda da Musulunci shine addini, Kuma ya yadda Muhammad (ﷺ) Annabi ne Kuma Manzo ne, bazai tashi ya aikata wasu bukukuwa ba na taron idi na shekaran da ake yi Wanda bayi da asali acikin addinin Musulunci... Kuma baya halatta ga musulmi yaje irin wannan taron ayi musharaka da shi, Kuma bazai bada taimak i akan wannan taron ba tako Wani bangare, domin wannan taro da basu da asali laifi ne Kuma me tare iyakokin ALLAH ne. ALLAH (ﷻ) Yace:
.
وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ ۖ إِنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ 
.
“Kuma kada ku taimaki juna a kan zunubi da zãlunci, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.” [Ma’idah: 02] [Fatawa Lajanatud da’imah p: 3825]

BABU RIKO DA WATA SHEKARAR MILADIYYAH.
.
Misalin wannan ayyuka kamar riko da shekarar miladiyya yana daga cikin sunnar Ahlul kitab daga Nasara wanda kuma shari'a ta tsoratar damu game da binsu saboda nassoshi da suka zo akan mu saba musu akan wasu abubuwa da nisantar kwaikwayonsu. Saboda haka ya kamata ayi riko da littafi da sunnah. A kudurce da ilimi da kuma a aikace domin shine hanya kawai da za'a kaucewa bidi'a da mummunan tasirinta. [Fatawar sheikh Muhammad Ali Farkus]

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)