LADAN DA AKE SAMU KAFIN DA KUMA BAYAN SADUWA DA IYALI.

LADAN DA AKE SAMU KAFIN DA KUMA BAYAN SADUWA DA IYALI.


An ruwaito cikin littafin "Shifa’us Sudur" cewa: Annabi S.A.W Yace; idan mace ta shiga cikin sha'anin hidimar mijinta ko tayi kwalliya domin neman yardar sa, ALLAH S.W.T zai rubuta mata lada guda goma kuma ya daukaka mata darajarta idan mijinta ya kirata tayimasa biyayya har ta dauki ciki zata kasance tanada ladan mai yin azumi da sallolin dare kullum a wajen daukaka kalmar ALLAH S.W.T wato jihadi.

Sayyidatuna A'isha R.A Tace: hakika an baiwa mata alheri masu yawa to menene ku agareku maza? sai Annabi S.A.W Yayi murmushi Yace;

"Babu wani mutum da ya riki hannun matarsa da nufin yin jima'i da ita sai ALLAH S.W.T Ya rubuta masa kyawawan ayyuka guda biyar idan yahada wuya da ita yanada lada guda goma idan ya sumbaceta yanada lada guda ashirin idan ya sadu da ita ALLAH S.W.T Zai bashi ladan da yafi duniya da abunda yake cikinta idan yatashi domin
yin wankan janaba, ruwan wankan bai gudanaba a wani bangaren jikinsa sai an shafe zunubansa an kuma daukaka masa darajarsa ana bashi ladan abinda yafi duniya harda abinda ke cikinta saboda wannan wankan da yayi kuma ALLAH S.W.T Yana yima mala'ikunsa kirari yana cewa:

"ku dubi bawana acikin dare mai sanyi yana wankan janaba ya sakankance nine Ubangijinsa, to ina shaida muku na gafarta masa".

MUNA ROKON ALLAH S.W.T YA BAMU IKON SADUWA DA MATANMU NA SUNNAH AMEEN.

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)