LABARI

LABARI
A wani ƙaramin ƙauye, an yi wani mai sana'ar hannu, yana aikinsa, kuma yana samun riba mai kauri. Wata rana sai wani mutumin ƙauyen ya zo ya ce da shi: Ga shi ka tara dukiya mai yawa da sana'arka, ka riƙa taimakon talakawa mana! Ka yi koyi da mahauci wane mana! Duba duk da ƙaramar ribar da yake samu, kullum sai ya yi rabon nama!

Mai sana'ar hannu ya yi murmushi, bai ce komai ba. Sai mutumin ya ƙulu, ya shiga saransa a wurin mutane, cewa ya tara dukiya amma marowaci ne, ba ya taimako. Jama'a suka tsane shi, har ya kwanta rashin lafiya, ba wanda ya kula, ya mutu shi kaɗai.

Bayan ƴankwanaki, ƙauyawa suka lura an daina samun sadakar nama, da suka tambayi mahauci, sai ya ce: Da ma duk wata mai sana'ar hannun nan ne yake kawo kuɗi, don kullum a riƙa yanka nama ana raba wa mabuƙata, yanzu kuma ya mutu!

Lura:

* Wasu za su riƙa munana maka zato, to ba za su cuce ka da komai ba, wasu kuma su riƙa gani ka fi ruwan sama tsarki, to ba za su amfane ka da komai ba.

* Kada ka yi gaggawar yanke hukunci a kan mutum don ka san shi sama-sama, watakil akwai abubuwan da in da ka san su, hukuncin da kake masa a baya ya sauya.
Post a Comment (0)