LABARIN WANI ATTAJIRI MAI HIKIMA

LABARIN WANI ATTAJIRI MAI HIKIMA Akwai wani babban Attajiri a birnin Istanbul na Qasar Turkiyyah. Watarana ya sayi Inabi 🍇 🍇 kilo biyu sannan ya bawa yaron shagonsa yakai wa matarsa dake gida, sannan shi kuma yaci gaba da hada-hadarsa. 

Sai chan bayan la'asar ya dawo gida, yace wa matarsa "Kawo mun inabin nan in ci kafin ki kawo mun abincina!"

Sai matar tace masa "Ai mun riga mun cinyeshi gaba dayansa babu saura".

Jin haka sai Attajirin nan ya tsaya yayi nazari sannan ya tashi ya fita da sauri, matarsa tana ta kiransa amma bai waiwayo ya kalleta ba. 

Bai zame ko ina ba, sai wajen wani abokinsa dillalin filaye. Yace masa "Ina so ka nemo mun mafificin filin dake gareka". 

Da wannan yammacin sukaje ya nuna masa wani shimfideden fili ya saya ya biyashi kudinsa sannan yasa aka nemo masa wani Injiniya ya nuna masa filin sannan yace masa "Masallaci nake so ka gina mun anan, kuma ina so ayau din nan a fara aikin ayanzun nan".

Nan take injiniyan ya kira leburori suka fara aiki, sannan Attajirin ya koma gidansa.

Komawarsa gida keda wuya sai matarsa tace masa : "Maigida ina ka tafi ne? Ina ta magana baka waiwayo ba?"

Sai yace mata "Zuwa nayi na yiwa kaina tanadi, kuma Ko yanzu mutuwa ta daukeni zan mutu cikin hutun zuciya da kwanciyar hankali.Tunda naga cewa tun ina raye atsakaninku kun kasa tunawa dani ku rage mun kwayar inabi, to ta yaya zansa rai cewa zaku rika tunawa dani kuna yin sadaqah gareni bayan rasuwata?"

Yanzu haka Masallacin yana nan a birnin Istanbul amatsayin SADAQAH JARIYAH ga wannan mutumin, Kuma Masallacin yana cin masallata mutum 200 ne. Gashi nan Tsawon shekararu dari hudu (400 yrs) ana gudanar da ibadah acikinsa yana ta samun ladansa. 

Wannan Attajiri mai basirah ya dauki darasi ne daga kwayar inabin da matarsa ta manta bata rage masa ba, don haka ya yiwa kansa wannan kyakkyawan tanadi kuma gashi nan har yau yana cin gajiyarsa in sha Allahu.

Da yarensu na turkiyya suna kiran sunan Masallacin SANKI ÜZÜM YEDIM (KAMAR NACI INABI).
 
Kaima ya dan uwana, yi kokari ka yiwa kanka wani babban tanadin tin kana raye kafin mutuwa ta riskeka. Wallahi idan ka mutu ka bar wa iyalinka dukiya, ba lallai ne su sadaukar maka da 5% (kashi biyar kachal) na abinda ka bari ba!!

FASSARA DAGA ZAUREN FIQHU.
Post a Comment (0)